EHSAAS

Chapter 64

by @fatoumspassion

Ahankali ta shiga bude idonta tana karema dakin da take ciki kallo, wanda ya yi mata kala da asibiti. Ta waiwaya, idonta ya sauka akan EHSAAS da ke kwance saman couch din dakin yana barci. Kana kallon shi kasan a wahale ya kwanta, duk ya takure jikinsa guri guda, alamar he's uncomfortable.

Ta rintse ido, trying hard to remember what happened har tazo nan, kuma me ya kawo EHSAAS nan din? Ta shiga tambayar kanta tana rufe idonta. Vividly ta shiga tuna abin da ya faru ranar fita suka yi ita da parents dinta zuwa Ireland din. Bayan gari da Jr sun yi rabin hanya, ta fara amai tana jin jiri. Hakan ne yasa dad dinta ya insisting su juyo su dawo baki daya. Amma sai ta ce mai she's fine, su je kawai, tunda already sun yi planning, an yi booking, komai da komai. Ita she'll be fine, zata juya. Duk da yadda ya yi da ita, ta ce mai she can handle it.

Uber ya kira su ya tafi da su. Ita kuma driver ya juyo da ita. A cikin motar tana jin jiri, taji wayarta na kara, alamar shigowar kira. Ta ciro tana dubawa, taga Fulani Hajar ce. Dama takan kirata duk safiya ta tambaye ta yata kwana da kuma Jr. Bata nuna mata bata jin dadi ba kwata-kwata. Sukai waya kamar yadda suka saba.

Tun suna cikin yin wayar, ta lura wayarta ba charge. Mayarwa jaka tayi, tace driver ya wuce da ita hospital saboda ta soma jin weakness din da jirin yayi yawa. Bayan ta fito daga ganin likita, shine ta koma gida, ta jona wayarta charge batare da ta kunna ba, saboda ta mutu tuntuni.

Ta shiga tai wanka, tai alwala, tai sallah, taci abinci. Ko minti biyar da gama cin abincin bata yi ba, ta shiga amayar dashi anan sink din wajen dining. Gidan bakowa sai ita, don da safiya sun sallami housekeeper din, sun ce mata yau basu nan throughout, sai gobe zasu dawo.

A galabaice ta koma dakinta ta kwanta tana wani irin barcin wahala. Bata tashi daga barcin ba sai bayan sallar magrib, gashi ko la'asar bata yi ba. Hakan ne yasa ta mike ta kunna wayarta da sauri-sauri, don ta san dole EHSAAS ze nemeta, kar yaji bata shiga hankalinsa.

Ta tashi, ta shiga ta dauro alwala, ta dan watsa ruwa, ta fito. Ko tsayuwa bata iya yi, azaune tai sallar la'asar, tai magrib sannan ta hada da isha'ee. Tai azkar dinta sama-sama saboda muguwar yunwar da take ji.

Ta mike tana dafa bango tana nufar kofa. Karar notifications din da suke ta shigowa wayarta ne yasa ta juya, tana ciro wayar daga charge. Ta nufi kofar dakin da ita. Tasan dama yayi connecting automatically da WiFi din gidan.

Tana dubawa, ganin almost 24 missed calls from EHSAAS ya bata mamaki. Take mood dinta ya yi cheering ganin yadda yadamu, yaketa kiranta don yajita shiru yau. Clicking tai zata danna ta kira shi back, kawai wani new notification ya sake shigowa wayarta. Ta Instagram ne, taga Favour ce ta turo mata shi two hours ago -

"Is this not your husband?"

Ta shiga scrolling, sai taga yawanci reels ne ma, few old friends din makarantarta suka tutturo mata ta IG and the same question. Bude message din Favour tai bata kawo komai a ranta ba, tai clicking.

Hoton EHSAAS da Mehtav ta fara cin karo da shi. Ta dan yi jim - don alamu sun nuna a gun bikinsu ne?

Ya kureta da ido yana kallo, itakuma Mehtav din idonta a kasa kamar ma bata san me yake ba. Scrolling tai, taci karo da reel din rawarsu a gurin cocktail. Takurama EHSAAS ido tana kallon how he looks super, super romantic.

This is not the first time data ganshi yana wa mace irin wannan kallon, ko yana mata irin wannan super gentle touch din - but this is the first time taga yanayi akan wata macen ba itaba. Like seriously, she felt like the whole world is crumbling akanta. Wani irin shock taji kamar she felt betrayed. Tasan EHSAAS na san Mehtav, amma bata taba tunanin he can ever look at another woman the way he always looks at her ba - sai yau.

Batasan cewa duk wannan jarabbaben kishin da ta dade tana dannewa ba, yana nan - sai yau kawai ta rintse ido tana tunanin if he can do this with her in public, what are they doing in private when they are alone?

Rintse ido tai tana tuna how EHSAAS is always clingy in private with her kaɗai - itama haka yake mata? Wani irin amaine ya shiga taso mata tana tunanin the same lips da yake bin ko ina na jikinta yana kissing, yake sawa akan wata macen itama?

"No…" tashiga girgiza kai tana saukowa daga steps ɗin tana haɗa bibbiyu daidai, tana jin wani ɗaci a ranta kuma tana gani vision din Mehtav da yadda ta taimaki danta tana saka rayuwarta cikin risk.

Does she deserve this from her? Jitai ta tsani kanta, ta kuma tsani EHSAAS a lokacin - for making her feel like a villain. Saboda tasan Mehtav is a good girl; ita ba zata taba jin tana jin tsanarta da haushinta kamar yadda taji tana ji yanzu akanta ba, sanadin EHSAAS.

Duka laifinsa ne.

Daidai tana karasowa final step din kawai taji kamar an jefota - jif! Faduwa tai. Taji shaf wani abu na fita ta kasanta mai dumi, goshinta da kansa taji zafi sosai. Tashigo kokarin mikewa, breathing heavily saboda zafin da take ji a zuciyarta - yafi wannan wanda take ji a fili.

Kokarin mikewa tashigayi tana dafa kasa. Idonta yakai kan tsintsiyar kafafuwanta da taga jini ya gangaro a hankali. Ihu takwala tana daga rigarta tana jin yadda take bleeding ba kakkautawa. Ta rufe idonta tana fasa kuka, asking for help with all her might - amma tasan ma ba lallai ne wani ya taba jinta ba.

Kukan da take yakara bada gudummawa wajen sarkewar numfashinta. Yana season blur vision take gani. A hankali tashiga laluben wayarta da ta fadi, ta daisan ta kira wani amma bata san waye ta kira din ba.

Kuma tasan taji heavy footsteps akanta as she's making the call. Bata san inda kanta yake ba, sai anan - tohm, waye yakawota asibiti? Kuma me EHSAAS yake yi anan bayan kamata yayi ace yana Nigeria yana tare da Mehtav gurin aurensu?

Motsi tashigayi tana kokarin tashi, pain din da taji yasa ta koma tana dan sakin kara, "Ahhhh…"

Da sauri EHSAAS ya bude ido yana kallonta. Ganin ta tashi yasa yamike da azama, yakaraso gurinta yana fadin,

"Baby, are you okay? How are you feeling right now?"

Yashiga kokarin taimaka mata don ta tashi, ahankali ya zaunar da ita. Kallo daya taimishi, ta dauke kanta akansa.

"Islam, bari in kira doctor," yafada yana nufar kofa.

Daidai Abraham Zion na shigowa, rike da wasu ledoji a hannunsa. Da alama siyayya yaje yayi, yanzu yake shigowa. Anan bakin kofa yabar kayan, yashiga dakin da sauri ganin Islam azaune, idonta biyi, yar karamar fuskar nan tayi fayau, kana kallonta kasan taji jiki.

EHSAAS tsayawa yayi a bakin kofa yana kallonsu. Yadda yaga Abraham yakaraso ya rungume ta with so much concern, yashiga bata hakuri,

"I'm so sorry, my child. I shouldn't have left you all alone on your own. I'm so sorry."

Girgiza kai Islam tashigayi, hawaye yashiga saukowa a idanuwanta. "My child," tafada tana shafa cikin, "Is the baby okay?"

Abraham wani tausayinta ne yashige shi ganin da alamar yanzu tatashi - ko sanin tayi miscarriage bata yi ba.

EHSAAS kasa watching dinta in so much pain yayi. Kawai yafito daga dakin yana jingina da bango. Shikansa yaji mugun bakin ciki da ɗacin rasa wannan cikin, saboda yadda ya kwallafa rai akansa. Inaga Islam da take dauke dashi.

Yashiga tambayar kansa, why did he even allow her to go on this trip?

Tausayinta yake ji sosai, saboda she suffered a lot. Da ace yana da ikon hana duk wani abin bakin ciki shiga zuciyar Islam, wallahi da zai hana.

Maganar likita yaji a bayansa yana fadin, "Is she awake?"

Jinjina masa kai kawai yayi, yace, "Eh."

"Kun ga naga ka anan, ko akwai matsala ne? Did you tell her already?"

Girgiza masa kai yayi yana nuna masa babanta da yake cikin dakin. Jinjina kai yayi alamar ya fahimta.

Tare suka koma dakin da likita, da alama Abraham yafada mata ta rasa baby'n. Tana rungume dashi tana hawaye amma baka jin sautin kukanta yanzu kwata-kwata. Suna hada ido ta dauke kai, ta cigaba da kankame babanta.

Likita yashiga dubasu ya tabbatar komai normal a jikinta. Yashiga sake rarrashinta yana fada mata, "She's strong. In sha Allah, she'll overcome this. Allah zai sake bata wani ɗan."

Dayake Doctor Murad musulmine, yakai kusan minti goma yana bata baki, harda tayi shiru ta daina kukan.

Tare da EHSAAS suka fita don zasu bashi prescription din magungunan da za'a sake siyo mata.

Seda suka fita sannan Abraham ke fada wa housekeeper dinsu su ce ta yi mantuwa ta dawo gidan. Alokacin ta tarar da ita a halin da take ciki, ta kira ambulance - shine suka kawota asibiti. Shine ta kirasu suma suka taho.

Dan kallon kofa tai kafin ta tambayeshi, "Shine kai ne ka kira EHSAAS? Taganshi anan."

Girgiza mata kai yayi yace mata shima bai san wanda yafada maiba, kawai ganinsa yayi. Dan jinjina kai take tashiga tambayar Abraham, "Ba aurensa ake ba, me yake yi kuma nan?"

Dan bude baki Abraham yayi, zai magana. Sanin ba magana mai kyau ce zata fito daga bakinsa ba yasa kawai yarufe, yana jan dogon numfashi, "Hmmmmm…" Yarasa wace irin zuciya ce Allah ya halicci peace da ita. Yadaisan da tashi tayi, ko ta kan EHSAAS ma bazata sake bi ba balle ta damu da wata second wife dinsa da ya baro a Nigeria.

Tambayar, "Ina Jr?" tai. Yace mata, "Doctor yace is not good a ringa zaryar asibitin dashi. Yabarshi a gida tareda mom dinta. Zuwa anjima in housekeeper dinsu tazo zata barshi a hannunta, tazo ta dubata."

Jinjina kai kawai tai. Seda EHSAAS yadawo sannan nurse tashigo don ta taimaka mata wajen sake gyaran jikinta.

EHSAAS sallamarta yayi, yakarasa yana taimaka mata. Still, she's avoiding his gaze, kuma ganin babanta yasa shima bai takura mata ba.

Suna shiga toilet din yakulle kofar yana rungumeta ajikinsa kamkam kamar wani zai kwace masa ita. Ahankali yashiga fadin, "I'm so sorry, kinji babynah? In sha Allah, Allah daya bamu, zai bamu wani, kinji? Ki kwantar da hankalinki."

Sanin shima yadda yake son cikin yasa ta sake fashewa da kuka a karo na biyu. Ta kankameshi tana jin tsanar kanta for making them lose the baby. Don tasan da ace bata ji wannan sharp bitterness da shock na hatred for her sire and Mehtav ba, da abinda yafaru bai faru ba.

Or is this her punishment for being selfish? For wanting EHSAAS all for herself?

Amman har yanzu, in ta rufe ido, view dinsa da Mehtav yakasa barin idonta. It's haunting her down. Sun mugun dacewa - kamar match made in heaven. Tana feeling like an outsider a cikin rayuwarsa for the first time.

Jin ta sakeshi ahankali tana dan turashi baya daga jikinsa yasa yasake riketa yana dogoda doguwar fuskarta yana kallonta.

Rintse ido tai, taki yarda su hada ido. "Baby, fushi kikeyi dani?" yatambaya.

Saboda he wants to confirm - da ace ba fushi take dashiba, yasan kukannan da tayi jikin babanta, ajikinsa zatayi adazun. "Baby, please talk to me. Did I do something wrong? Or is it the wedding pictures? Baby, nasan probably kema kingani. I'm so sorry baby, I didn't do it intentionally. Wallahi ban dauka zasu yada shi ahaka ba."

Shiya saka mata kayan nata duka kafin ya haɗa mata tea mai zafi. Da ƙyar ya lallabata tasha half cup, ta kwanta a saman kirjinsa. Kamar ta tambaye shi Mehtav da bikin nashi, sai kuma ta fasa kawai saboda ba ta son ta ji abin da zai sake daga mata hankali. Seda yamma ya bar ɗakin ganin iyayen Islam sun dawo, ya tafi. Sai asannan ma ya kama hotel ɗin da zai zauna.

Wanka yayi, ya saka phone ɗinsa a charge saboda he's just functioning, amma zuciyarsa cike take da damuwar matan nasa biyu - na farko rashin lafiyar Islam da kuma damuwar da ya ganta a ciki, ga baby'n su da suka rasa.

He knows Islam well - ko tari tayi yasan ma menene. Kuma duk kaffa-kaffa nan da take yi kar ya gane aurensa da Mehtav baya damunta, yasan sarai it's killing her inside. Wanda idan ya tuna da hakan, sai yaji inama bai taɓa yin haɗari ba, da bai je Nigeria har ya haɗu da Mehtav ba. Zuciyarsa ta yaudari Islam ta fara sonta ba, ga kuma rigimar Mehtav.

Don lokacin da ya karanta text ɗinta da safe tunkan Islam ta farfaɗo, baƙalar ƙoƙarin kiranta da yayi bai samu ba. Ya kasa samunta, sai Fulani ya samu, don yasan akalar itama nata taurin kai tsaf zata ce ta fasa auren nashi. Wanda yasan idan haka ta faru, tabbas za a iya samun gagarumar matsala. A da yana jin zai iya hakura da ita for Islam's peace of mind, amma yanzu tabbas yasan idan ya hakura da ita, Islam will never find peace - saboda peace ɗinta na tattare da shi, shikuma zarewa zeyo in ta ƙi aurensa.

Ganin wayar ta dan cazu yasa ya ɗakko ta, ya fara kira, har yanzu bata shiga ba. Hakanne yasa ya maida akalar kiransa gun Aman, shima bai ɗaga ba - three missed calls yamai amma shiru, bai yi picking ba.

"Dawiya ka kira Aman ka ji," ya faɗa da kansa, "bai ɗauka don ko barci yake, yanajin ringing yake ɗauka a magagin, musamman in shi ya kirasa." Amma yau har 3 missed calls bai ɗaga ba.

Sighing yayi heavily yana kallon agogonsa. Yasan definitely ya ci ace anyi daurin aure angama tuntuni. Kuma da kunya ya kira ɗaya daga cikin iyayensa, ya tambaye su ko an daura auren.

Akalar kiran ya maida zuwa gun Abeey. Seda ta kusa katsewa, ta ɗaga tana faɗin, "Hello, Prince." Yanajin kida a background ɗin, hakan ya tabbata masa ba'a tsaya da bikin ba, dan bayanan an cigaba.

"Abeey, are you hearing me?" Da ƙyar ya ji tana magana alamar bata jinsa sosai dakyau saboda hayaniya. "Mekace? Bana jinka sosai. Kana ina ne?"

Yace, "Abeey listen to me. Ina Mehtav take? Zaki iya kai mata wayar yanzun?"

Abeey dake ƙoƙarin fita daga filin DJ da akeyi a compound ɗin gidansu, ba abin da ta ji ya faɗa sai Mehtav tace, "Kace Mehtav?" Yace, "Eh, Mehtav. Is she there?"

Juyawa tayi tana kallon Mehtav dake tsakiyar filin su Aunty Ameerah. Su saki ta a gaba suna raye-rayensu suna jujjuya ta wai alallai sai tayi rawa, ita kuma kunci kawai takeyi, ta ƙi yi.

Tace, "Tana cikin mutane yanzun amma anjima zan kiraka in haɗa ku."

Dan jim yayi kafin yace, "Is she okay?"

Lokacin Abeey ta dawo cikin gida inda babu hayaniya kamar wajen. Da duk aka fice tace, "Uncle Prince, I can't say, amma dai ga taccan a filin rawa tare da su Aunty Ameerah, ana yin wuni."

Yace, "An gama daurin auren kenan?" Tace, "Tun dazun. Amma dai na ji tana tambayar waye angon. Kowa yace mata, shima me sani? Ba Uncle Prince, ai kai ne angon ko?"

Dan jim yayi yana tunanin me Abeey ke nufi. Yace, "Like how come again?"

Tace, "Yah Mehtav tun jiya take kuka, tace bazata aureka ba. Yau da safe ma ta faɗa ma Mai Martaba bazata aureka ba, bata sonka. Yace mata kuma bazata auri wanda bata so ba, za a canza mata miji."

Sosai gaban EHSAAS ya faɗi jin maganar da Abeey ke faɗa. Yasan kuma Mai Martaba bazai tsaya yana irin wannan wasan da Abeey ba.

Yace, "Abeey I don't understand." Tace, "Call Aman, zai maka bayani. Nidai bari natafi kar a ta ayi babu ni."

Daga haka ta katse wayar. EHSAAS ya tsaya yana kallon wayan - he's very confused. An daura auren Mehtav, abin da ya fahimta daga maganar Abeey kenan, amma kuma ba da shi ba, kuma ita kanta Mehtav bata san da wanda aka daura auren ba.

"Noo…" yashiga faɗa yana zagaye ɗakin. Straight number Fulani ya kira, itama seda ya kira sau biyu ta ɗaga, tana cikin hayaniya itama.

Tace, "EHSAAS, ana ta nemanka tun safe, ka kashe waya. Munaso mu ji ya jikin Islam." Yace, "Da sauƙi, alhamdulillah."

Tace, "Nima in sha Allah ana ɗaukko amaryar zantaho nan. Ga mutanen tawa su Hajiya Jannat da Azeeza duk sunzo nan. Sun ɗauka zasu sameta, suke samun abin da ya faru. Suma zasu zo Greece ɗin."

Jin gangamin da Fulani take yi zasuzo su takura ma matarshi, bayan yasan yanzu peace of mind take bukata, yace, "Maama, base kunxo ba ai. Bazamu jimaba, zamu dawo Nuristan gaba ɗaya please."

Tace, "Ka ji ni yaro? Yarinyar tawa ta bar maka, kace bazamu taho ba? Zanen kake yi?" Yace, "Uhmm Maama, yaushe zaku ɗaukota?" Tace, "Wa ɗin?" Yace, "Mehtav."

Murmushi tayi tana faɗin, "Randa mukaga dama."

Jiyay Queen Layla ta karɓi wayar tana faɗin, "Maza baku da amana. Yanzu kana can kana jinyar uwar gidanka, harma courage ɗin ɗaukar waya kake yi, kana tambayar mu yaushe matarka zata tare. Toh, bazata tare ɗin ba, kama bar rawar kannan amarya. Tace batayi, an canza mata ango!"

Duk da cikin barkwanci ta faɗa, amma EHSAAS bai san me yasa hankalinsa yaki kwanciya ba. Yace, "Afuwan Mommy, ba haka bane. Kawai dai…" Tace, "Kawai dai tafi can. Zamu kawota. Ka cika kashanye baggara dai, kaga gata kuma wallahi ka ci amanar yarinyar nan Islam, sai Allah ya kama ka. Na rasa me kagani jikin Mehtav ɗinnan? Diri dai, yata ta fita. Kyawun fuskar ma tafita, nutsuwa ga hakuri - duk fa ba magana. Ga ladabi, kodai kodaddiyar farar fatarnan ne yake burgeka da wannan shegun turarrukan aljanun masu kama da na yan tsibbu…"

"Hello? Hello?" Ta ji EHSAAS yana faɗa kamar bai ji ba. Kit! - ya kashe wayar, don sarai yana jinta. Kawai dai ba son yaringa jin ana aibata ɗaya daga cikin matansa ne kwata-kwata. Shi in yaji ana comparing ɗinsu ma abin mugun haushi yake ji, saboda shikadai yasan how special each one of them is in her own beautiful way.

Queen Layla ta kalli Fulani daga ɗayan ɓangaren tana faɗin, "Kingani ko, kashewa yay, aita shanye sa, ya zama sallamamme. Allah yasa dai karya koma kamar yayanki."

Shiru itadai Fulani tayi kawai saboda kar irin tata. Tace, "Baruwana, itaku ai ɗanki ne."

Queen Layla tace, "Hajara kenan, ki cigaba da tsayawa fillancin nan, in baki watsaba ba iya Islam yaron nan zata raba da shi ba. Har ke ma sai ganin sa ya miki wuya. Kina ganin iskancin da tayi dai dazu da safennan? Aini da ace dani akaje, da sena faffalla mata mari. Daga ke har su Mai Martaba din ace wai bawansa ya mareta, kuka tsaya kuna lallabata. Tohm, ita yar gwal ce wallahi. Ko yau ta rabu da Yarima, sai an daura mai aure da uku in ya so, wanda suka fita asali, kyau, ilimi, tarbiyya, uwa uba kuma ayi kwarya tabi kwarya."

Fulani ta miƙe tana faɗin, "Amman dai kamar ba agabanki Mai Martaba ya mana bayanin tabata aka yi ba?"

Tace, "Ba wani tabata, iskanci ne zalla. Ita tanuna ta isa."

"Fulani Hajar…" bata karasa ba taga Fulani ta wuce cikin sauran jama'ar da take ta amsar baƙuncinsu - yawanci 'yan uwanta ne da kuma matan abokan Mai Martaba dake Nigeria. Don zuriyar su na Mai Duguri, tsakinsu da kwarkwatansu babu wanda bai halarci auren EHSAAS ɗin nayauba ba. Musamman wadanda suke ganin Nuristan ya musu nisa, tohm yin na Abuja ba ƙaramin daɗi yayi musu ba.

Bayan anyi kiran sallar Magrib aka shigo da amarya don tayi wanka, a sauya mata shiga kafin 'yan uwan mijinta su zo ɗaukarta. Saboda Paa yana dawowa daga gurin daurin auren, ya sanar da Inna cewa yayi cancelling komawa Mai Duguri nan yau dinnan za'a wuce da ita, in Allah ya kaimu.

Aunty Ameerah kuka ta tarar da Mehtav tana yi ita kaɗai a ɗaki. Duk tabi ta tsangwami kanta cikin 'yan uwa kamar ba a bikinta ake ba. Kowa na farin ciki, ita kaɗai ce take bakin ciki.

"Mehtav, kukan me kike yi kuma? Ba wanka nace kisha kiyi ba? 'Yan uwan Hamisu sun kusa zuwa su ɗaukeki."

Kuka ta fashe da shi don tun safe Aunty Ameerah tace mata an daura mata aure da wani - Hamisu, limamin masallacin layinsu.

Tun bata yarda ba, amma ganin bata ga 'yan uwan EHSAAS ko ɗaya a gidan ba yau yasa taji ta yarda da maganar Aunty'n. Ta shiga raira kuka tana faɗin, "Ni ban taɓa ganinsa ba, ban sanshi ba. Me yasa za'a aura min shi? Wallahi banason shi. Dan Allah Aunty, kiyi haƙuri, ki taimaka, ki basu haƙuri. Wallahi bazan sake ba. Acewa Paa, natuba wallahi bazan ƙuma kinjin maganarsa ba."

Aunty tace, "Ke, ina miki wasa ne? Bazaki tashi kije kiyi wanka ba? Kintaba jin inda ake aure da wasa? Ai yanzu igiyar aurenki na kan Hamisu. Ko shi Paa ɗin da kike magana, ba shi da ikon da Hamisu yake akanki ba."

"Ina awarwarayenki?" Aunty ta tambayeta ganin babu awarwarayen gwal ɗin hannayenta da ta fita da su kwata-kwata.

Kuka ta shiga yi tana faɗa mata, "Suna fita Aman yazo yay min gori tass. Yace tabashi duk abin da tasan Fulani ta bata, saboda tace batason auren EHSAAS."

Cikin mamaki Aunty Ameerah tace, "Shi Aman din?"

Tace, "Eh, ai daman ba shi da mutunci. Yatsaneni, baki ga kallon da yake min ba? Baya sona da EHSAAS inajima, shine ya ziga EHSAAS ya tafi ya barni. Gashi nan an fasa, an aurar da ni ga wanda ban ma sani ba. Nidai mutuwa zanyi Aunty wallahi. Inason EHSAAS, dan Allah ki ce ma Paa ayi haƙuri, a dawo a aurar dani ga EHSAAS. Bazan sake ba, sharrin shedan ne. I don't even know what got into me. Shi kuma Aman, ki haɗa mai duk kayan da kikasan sun kawo, ai daman awarwaron kadai nasaka, amayar mai kar ya sake min gori. In ba haka ba, sanda zan mamare shi, bansani ba."

Da waro ido Aunty Ameerah tace, "Mehtav, baki da kunya? Aman din zaki girma ba girme ki ba?"

"Taina ya girme ni? Girman jikine kawai," tafada tana tura baki tana soma cire kayan jikinta. "Wallahi be girme ni ba."

Jinjina kai kawai Aunty tayi tana faɗin, "Tohmm, naji. Meyema abin ja in jar, abin da ba yayansa kika aura ba ai shikenan."

Raurau Mehtav tayi da ido tana faɗin, "Toh Aunty, ki roƙa min Hamisu ya sake ni kawai, sai inkoma EHSAAS. Nasan ba zai ƙi ni ba. Daman kawai misunderstanding muka samu, kuma bazan sake ba."

Tabe baki Aunty tayi tana faɗin, "Waye yace miki yayan sarki na auran bazawara? Lallai kin sha ƙwaya. Wuce kiyi wankan. Danace kifito ki shirya, wancan lafayar dana fito da shi shine zaki saka, kinjiko?"

Jinjina kai tayi kawai ta wuce toilet ɗin. Da ƙyar ta samu tayi wanka, ta fito, dama tayi alwala, sallar Magrib tayi. Tana idarwa tayi shiru tana jin hayaniyar jama'a - har lokacin baƙi ne suke shigiwa gidansu tako ina.

Abeey ce ta shigo tana kallonta. Ganin bata shirya ba yasa tace, "Yah Mehtav, why are you not ready yet?"

Kafe Abeey tayi da ido tana faɗin, "Yanzu har dake za'a haɗa baki aimin auren dole? Na ɗauka in duk duniya zasu haɗu su juyamin baya, Abeey bazaki ci amanata ba."

Abeey cikin mamaki tace, "Ba fa Prince ɗin aka aura miki ba. Inace shine kikace bakiso ko?"

"Niban ma san waye mijin nawa ba. Ke in kin sani, ki faɗa min. Ni nawa Allah ya sanya alheri ne tunda I did my best, amma kin watsamin ƙasa a ido."

Wani irin kuka ta fashe da shi tana faɗin, "Wai Hamisu aka auramin! Limamin masallaci dan Wara Iso!"

Abeey tayi dariya tace, "Wai Malam Hamisu dai, wanda nasani? Babansu Aliyu?"

Da waro ido Mehtav tace, jin sunan Aliyu - tasan Aliyu amma bata san babansu ba. Kuma tasan gidansu Aliyu gidan Gando ne, don babansu matansa uku.

Bata gama tunanin nan ba, aranta taji Abeey tace, "Kambalai, yau Mehtav, ke ce fourth wife kenan."

"Wallahi kam bani ba! Binki gidan nan, suma 'yan gidan ɗakunan basu ishesu ba. Da dai gidan Prince ne, nasan za'a bani ɗakina ni kaɗai. Abeey, ki taimaka ki kai ni gurin Paa, wallahi banason shi. Ni EHSAAS nake so, shi kaɗai nake son in aura. In ban aureshi ba, mutuwa zanyi."

Abeey tace, "Yah Mehtav, kin ma gama raina ma kanki hankali. Allah ki kajema da Paa maganar nan, seya sumame ki. Hmm, daman a kule yake dake. Baruwana wallahi. Dazun ma Prince ya kirani, shima da alama bai san ba da shi aka daura auren ba. Allah sarki bawan Allah. Nace dai zan kirashi in baki amma na fasa, kinga kin zama matar wani. Bai yi ace kin yi magana da wani daban."

Abeey ta miƙe ta nufi ƙofa. Da sauri Mehtav ta bi ta, ta riketa bakin ƙofa, ta shiga roƙonta, "Dan Allah, ki kira min shi suyi magana."

Ta rasa inda tayi misplacing wayarta. Abeey ta boye wayarta a bayanta tana faɗin, "Banda credit fa, bani za'a yi haramci."

Daidai Aunty tana dawowa tace, "Au Mehtav, shirin kenan. Ke kuma Abeey, me take so naji tana roƙonki?"

Tace, "Waifa Prince take so nakira mata. Nikuma nace mata bani za'ai haramcin nan Allah kuwa."

Aunty tace, "Kin burge ni ai. Kin fita hankali. Wuce kiyi tafiyarki, nice dai daidai sa ita Mehtav ban nan gurin kafin in bata miki rai."

Komawa ciki tayi, ta fashe da kuka. A ƙarshe sai Aunty Ameerah ce ta saka mata kayan da kanta. Tanata kuka amma ba ta kula ta ba.

A ranta tana faɗin, "Ai yarinya, sai na gama da ke kamar yadda kema kika min."

Zuciyarta tace, wato yayi, bai dauka zasu yada ba - da basu yada ba, she'll never even know.

Amman kuma tana tuna maganganun Fulani. Har yanzu acikin kunnuwanta suke. Sai yanzu take jin kewar rashin uwar soro atare da ita. She's confused - batasan yadda zatai da abinda take ji ba.

Tasan cewa da tanan, da zata taimaka mata. Tasan abinda EHSAAS yakeyi ba haramun bane, kuma Mehtav bata cancanci butulci irin wannan daga gareta ba. Amman yaya zatai da bakin kishin nan da take ji a cikin ranta?

Batason sanadin hakan ta barar da duk wata kima tata ta hanyar zama mai magana biyu a gaban mijinta. How could she accept this marriage wholeheartedly, yanzu kuma ta dawo tace masa bata so? "Baby, is it the marriage again?"

Da sauri tashiga girgiza masa kai tana goge hawayenta. "What are you talking about?"

Da sauri ta raba kanta dashi tana fadin, "I don't know what you're talking about, sire. I'm just sad that we lost the baby. I know how much kake son shi, and I know you must be very disappointed in me for losing it."

Da sauri yajawota yana rungumeta ta baya, yadaura habarsa gefen wuyanta "Kar inki raji haka, kinji Islam. Allah ne yabamu, kuma shiya karbi abinsa. I thought you know me well - kinsan bazan taba wannan tunanin ba, koh?"

Jinjina kai kawai tai tana fadin, "Jikina ba dadi, let me take a warm bath."

Dakansa ya taimaka mata, yana ta tattalinta kamar kwai. Yay mata wanka da ruwa mai dumin gaske, yana daidata cikin towel, yarungumota suka fito daga bathroom din.

Har lokacin Abraham na zaune a dakin. Ganin sun fito ahaka, yasake wa Islam sanni yace mata yana zuwa, yafice alamun basu guri su shirya.

Ledar da ya shigo da su EHSAAS yashiga dubawa - yaga duk kayan Islam ne aciki, har da su pad da inner wears. Already daman yakawo kayan tea tun dazu. Duk shiyake jigila da komai.

Flashback

"Aman! Aman! Aman!"

Yaji ana kiransa daga baya da dan karfi, lokacin daya fito daga harabar gidansu Mehtav, ze shiga motarsa. Don shi wannan dramar da Mehtav takeyi ba karamin ciwan kai take kokarin samai ba - duk hankalinsa yana kan halin da Islam take ciki a Greece.

Juyawa yay yana karema matar kallo, wacce ko a palace shida ita, ko kallon kirki basu ma juna, ko gaisheta yayi, se taga dama take amsawa. Tun sanda Yarima yaki auren yarta Maisoon, take gaba dashi da Yariman.

Kallonta yake harta karaso tana dan kare fuskarta daga ranar datake dukanta.

"Lafiya?" Yatambaya straight, don yasan haka kawai bazata rinka kwala mai kira haka ba.

Dan shiru tai kafin ta soma kalle-kalle tace, "Abinda zanfada maka sirrine. Inason yatsaya daga ni sai kai, Aman, saboda kasan halin masarautar nan. Nidai taimako zanyi, banson abin yajuye yadawo kaina. Kuma inna fada…"

Dan jim yay kafin yace, "Go straight to the point."

Jin ranar dake gasasu yasa tace, "Ko zamuyi dan inuwa ne, naga nan rana, ga jama'a nata kai-kawo."

Kallon Rolex watch dinsa yay, yana gyara zaman babban rigarshi, yashiga girgiza mata kai yana fadin, "Banida wannan lokacin. I need to be at the mosque right now."

Tace, "Ai shiyasama nakeson kasaurareni, don naji kamar Mai Martaba dagaske ya hakura, zebi ra'ayin yarinyar - bayan kuma ba a hayyacinta take ba."

Cikin dan mamaki, aransa yafara wondering; ashe bashi kadaine yadauka Mehtav na shaye-shaye ba. Amma yayanta yatabbatar mai babu abinda takesha.

Yace, "What do you mean by that?"

Wata yar karamar audio recorder ta ciro daga purse dinta tana mika mai. Yakarba, tadan yi gefe dan inuwa saboda farace kal-kadan, yarage bata zama albino ba, batason rana ko kadan.

Danna button din daya gani agefe yay, yana dan karawa akunnansa. Sai da yayi nisa cikin sauraranta sannan yama gane muryar me maganar sosai. Ya kadu da abinda take fada, yashiga kallon Maman Maisoon cikin kallon tuhuma.

Ganin yagama saurara yasa takaraso tana fadin, "Nima dakake jin muryata biye mata nai, saboda idan tagane ba bin bayanta nake ba, zata iya kullamin sharrin da Mai Martaba, seya koreni daga masarauta. Musamman da yanzun wanda nake zaune donshi agidan, shida gawa duk daya suke. Kaga kam dole na lallaba matar gidan. Aman, ba yin yarinyar bane, mugun tsafi ne, jikin wannan awarwaran da yake hannayenta."

Rintse ido yay yana tino jiya a mota - tabbas yaji EHSAAS da ita suna kamar ma fada akan awarwaran. Kuma tun jiya yay sensing kamar basa magana da juna sosai.

Indai maganar matarnan gaskiya ce, tabbas Sarauniya Hassana ta cika mara imani. Me wannan yarinyar da Yarima sukai mata, take kokarin hukuntasu ta wannan hanyar.

Wata zuciya ta zugashi, tafara raya mai - "Ai aura mata duk wanda akaga dama shikenan. Uncle Prince din sa seya zauna da Islam na har abada." Wata kuma zuciyar tashiga raya mai "Uncle Prince nasonta. Duk haushinta da nakeji, bekama kahada hardashi ba."

Vibration yaji wayarsa nayi. Da sauri yaciro yana saka recorder a aljihu. Ya kalli Maman Maisoon yana fadin, "I'll see what I can do. Kin fadama wani maganar nan?"

Dasauri ta girgiza kai tana fadin, "Ni? Asuwa!"

Yace, "Okay. Keep your mouth shut for the time being. Bari naje, ana kirana."

Ficewa yay daga harabar gidan baki daya. Yanufi motarsa daidai su Mai Martaba da Paa suma suna fitowa.

Da motarsa yashiga gidan, aka budema Mai Martaba gidan baya, yashiga tareda Habib Bai, se Mal Liman agaba don maganar sirri zasuyi wanda basason matansu suji.

Aman ganin kamar magana zasuyi yasa yay saurin bude murfin motar zefita, Mai Martaba yace yatsaya, "Yazauna mana, ya wakilci dan uwansa."

Badon yasoba yazauna, yanajin Baban Mehtav yafara magana yana bawa Mai Martaba hakuri akan abinda yafaru. Duk kunya tarufe shi.

Gyaran murya yayi yana fadin, "Engr, nasan kai babban mutum ne, nasan kuma baka magana biyu. Don haka, meyasa zaka bani hakuri? Abi abin asannu daga EHSAAS har Mehtav, duk yayanmu ne, kuma babu wanda zamuyiwa dole acikinsu. In sha Allah, tunda tace bataso din ai ahakura kawai. Ko Mal Liman?"

Kamar yadda kafadamin, Mal Liman murmushi yayi yana fadin, "Allah yaja zamaninka. Tabbas nafadama hakan, saboda yarinyar tasamu kwanciyar hankali. Idan har mukace zamu cigaba da tirsasata, zuciyarta zata cigaba da baki, wanda zata iya cutar da kanta dalilin hakan batareda sanin taba."

Engr cikin bacin rai yake fadin, "Allah yagafarta, Mal! Ai daka barta tabuga din, harmu zamu tsaya muna fada tana fada?"

Murmushi Mal Liman yay yana fadin, "Allah yahuci zuciyar Engr. Ai in zuciya ta baci, kada hankali yawuce. Su wadanda sukai mata turen sunsan zata hau, zaka hau, kuma idan aka hadu, za'ai batacciya. Kafasan halin diyarka - koda ancema zatai abu kwatan-kwacin wannan, kamata yay kai zaka fara karyatawa."

Cike da takaici Paa yace, "Toh Mal Liman, ba labari akabanba? Bagashi ta aikata agaban nawa ba. Bama nikadai ba - kowa ai yajita. Allah! Yau da ace Abeeda ta isa aure ita zan sauyawa da Yarima!"

Jin abinda Paa yace yasa Aman yakusa dariya, kawai seya soma hasaso EHSAAS, "Wai da Abeey tashin sense, aida yay aure da wuri ya haifeta."

Murmushi Mai Martaba yay yana fadin, "Nikuma bahaka naso aiba. Tunda tace duk wanda mukeso mu aura mata, tunda munada matasan dayawa - aigasunan su Aman, su Tajuddeen, asamu daya adaura mai auren da ita."

Jin abinda Mai Martaba yace yasa Aman yay saurin juyowa yana kallonsa. Yafara tarin dole don wata muguwar kwarewa da yayi. Daya bude baki zeyi magana, dariya Mai Martaba yashigayi, don shi kansa zolayarsa yake.

Mal Liman yace, "Wato Ranka yadade, ashe zolayar tana nan, ba'a daina ba."

Yace, "Bakaganshi ba, yaji ana neman yiwa dan uwansa kafa, harda kwarewa. Sannu - nasan dai ba namijin da za'a bawa diyata yakalla yace bataiba bayaso. Inkuma bakaso, se mubawa Tajuddeen."

Paa yagirgiza kai yana fadin, "Allah yaja zamaninka, aida kabarta kawai taita zama ahakan."

Mal Liman yace, "Ku tsaya ku saurareni mana, don duk yagirmesu, kuma yanzun amatsayin iyaye suke awurinnan. Wanda suka zauna don tattauna makomar yayansu, bawani mulki ko iko."

Yace, "Sambune - mai karfi ajikin yarinyar. Shiyasama takasa hada ido dani. Kusan irin sammun da akayiwa Fulani Hajar ne ajikinta, lokacin data kasa rike juna biyu."

Mai Martaba cikeda mamaki da tashin hankali yake fadin, "Itama?"

"Irin kofa shigowa dangin nasu bataiba," yajinjina kai yana fadin. "Muna bukatar daura aurennan cikin gaggawa. Idan ba haka ba, har abada baze taba yiwuwa ba."

Dan waro ido Habib Bai yayi yana tinanin, "Toh, waye ze yiwa yarshi sammu?" Ana zaune kalau.

Mai Martaba jiyay yanajin kunyar Habib Bai, ganin tunkan yarsa tashigo masarautar, tafara haduwa da kalubale irin na gidan sarauta.

Mal Liman yace, "Abu daya zamuyi yanzun. Aje adaura auren, amma har zuwa lokacin da za'a yimata magani, abin ya karye - kada wanda yasanar mata cewa shine ta aura."

Jinjina kai Habib Bai yayi, looking confused.

Aman yay dan gyaran murya yana fadin, "I think you got to listen to this."

Yamikama Mai Martaba recorder. Yana dauke idonsa akanshi, dayake volume din is not high. Yana kunnawa, yakai kunnansa, shikadai yaji duk maganganun da akeyi aciki. Yana gama saurara, yamikama Aman yana mai iznin suwuce kawai, don anfara kiransa - mutane sun fara hallara.

Villa yafara kaisu suka sake sabon shiri zuwa gurin daurin auren.

Karfe goma sha daya daidai, asafiyar ranar Lahadi, dubban al'umma - manya da kanana - from different countries and continents suka sheda daurin auren Prince EHSAAS NASHWAN da amaryarsa Mehtav Habib Bai. [11/10, 20:12] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.