Chapter 65
Inna ce ta shiga dakin tana kallon Mehtav dake kuka. Itama duk jikinta ya yi sanyi saboda yadda suka saba rayuwa tare shekara da shekaru; gashi yau za a ɗauketa daga gidan, ba ma wata unguwar za a kai ta ba wata ƙasa can daban, za a kai ta inda ba ta da kowa na danginta. Abeey ma, ganin Inna da aunty Ameerah sun riko Mehtav dake kuka a jikinsu, sun fito da ita maƙalewa tayi a bakin ƙofar tana leƙenta, don gani take kamar abu ne wanda ba ze taɓa yiwuwa ba ace za tai rayuwa ba tare da yah Mehtav ɗinta ba. Ganin sun yi bangaren Paa ya sa ta bi su a baya a hankali. Paa ta tarar tare da babansu Falmata da yah Tajuddeen. Gefe guda kuma wasu mata ne da Abeey bata saniba cikin shigar alfarma ta sarauta ko da ba a faɗa mata ba, ta san yan uwan EHSAAS ne waɗanda za su tafi da Mehtav.
Baban Falmata ne ya buɗe guri da addu'a. Ya shiga yi wa Mehtav nasiha kan zaman aure: hakuri, biyayya da juriya; sannan ya yi ta jaddada mata riƙo da ibada tare da girmama yan uwa da abokan arzikin mijinta. Paa kasa ma yadda ya kalli inda Mehtav take ya yi saboda wani irin rauni da yake ji a ƙasan ransa; yana jin ƙuncin rashin kasancewar mahaifiyarta tare da ita ayau din yasan shiba komai ze iya gaya mata dangane da zaman aureba amatsayin sa na namiji,seyanzun yake jin kamar "he's not ready to let her go". Yasan duk daren daɗewa wannan ranar zata zo, amma bai taɓa ɗauka this soon za ta zo ba.
Baban Falmata yana gama wa ya kalli Habib Bai yana faɗin, "Engr, babu abin da zaka ce mata" sai sannan ya ɗago idanuwansa sun yi jajir kawai; ya ɗan cire glass ɗin shi ya goge idonsa ya mayar, Ya dafa kanta, ya shiga yi mata addu'a yana sanya mata albarka. Kafin ya ciro wata jaka mai ɗauke da littattafan addu'o'in tsari da dama, ya daura mata saman cinyarta; fuskarta a rufe ta riƙe jakar gam tana haɗawa da hannunsa. "Allah ya yi miki albarka, Mehtav," ya kalli aunty Ameerah yana faɗin, "za ku iya tafiya da ita." Ita ta ɗaukar mata jakar. Da sauri ta ƙara sa ta rungume Paa, Akunne ta shiga rada mai ni banason hamisu nan Paa, katemaka min wallahi. EHSAAS nake so; idan ba shi aka auramin ba, mutuwa zanyi." Sai alokacin Paa ya ɗanyi murmushi yana kallon aunty Ameerah data zo tana janyeta a jikinsa. Silently take faɗin, "Ya isa haka Mehtav ai mutumin ƙirƙine." Tana kallon Paa da yake kallonta yana girgiza kai yana murmushi, trying hard to hid tears din dake kokarin sakkowa a idanuwansa.
Da ƙyar ta raba su. Inna ma se ga ƙwalla "yanzun yarnan shikenan kuma kin tafi, kin bar mu daga ni se wancan masifaffiyar ƙanwar taki, Allah sarki Mehtav, ga hakuri basawa ba fitarwa. Don Allah ku riƙe ta, amana." Ta shiga jaddadawa su Queen Layla da Mother Fariha. Murmushi Mother tai tana faɗin, "In sha Allah." Tana rungume jikin aunty Ameerah tana gursheken kuka. Aka fitar da ita a falon; aka sakata a mota. Sega Abeey dagudu riƙe da trolley ɗinta; tana ja, don daman tun tuni ta haɗa kayanta. Aunty Galala tai tana kallonta tace, "Ke kuma meye haka? Uhm?"
Tana wiqi-wiqi da ido ta shiga faɗin, "Ai raƙata zan yi. Tare zamu tafi." Inna tace, "Ka ji shashasha, kin taɓa jin inda aka yi haka? A wani gari ake haka daga kai amarya ahaɗa da ƙanwarta." Abeey ƙoƙarin shiga motar da Mehtav take tai da sauri aunty Ameerah ta riƙe ta tana faɗin, "Ki yi haƙuri, kin ji? Abeeda kinga yanzun za a kai ta,ki bari in ta kwana biyu da kaina zan ɗauke ki inkun gama jarrabawa ki je har can NURISTAN din ki ganta." Abeey ta san sarai wayo su ke so su yi mata hakan ne yasa ta fashe da kuka tana faɗin, "Yah Mehtav, ki yi musu magana! Ba kince dani zaki tafi ba?"
Daga cikin motar, Mehtav ta shiga miko mata hannu tana kuka,don su bilhakki da gaskiya so suke su tafi tare. Queen Layla duk yadda take ƙin Mehtav, seda ta ji zuciyarta ta ɗan tabu a hankali tace, "Ku kira maman yarinyar nan, ta shiga da ita kada mu yi missing flight." Tana kallon Abeey. Inna tace, "Amma dai baiwar Allah, ba ki saniba ko? Ai daga ita har Mehtav ɗin marayu ne; uwar ta mutu tun gurin haihuwar ta; su su kaɗai suka tashi Allah sarki, ba su taɓa rabuwa ba. Shi yasa..." Mother Fariha dake gaban mota ta leƙo tana kallon yadda Abeey take kuka; tausayi yarinyar ta bata anitse tace, "Indai tana da passport da visa, tabiyosu su tafi kawai."
Inna ta gwalo ido tana faɗin, "Ni kaɗai zaku bari kenan? Ke Abeeda, ba inda za ki..." Abeey jin abin da Mother tace tuni ta zagaya gurin driver tana ce mai ya buɗe mata boot zatasa kayanta. Taj ganin basu tafi ba yasa ya leƙo yana tambayar lafiya? aunty ganin da gaske Abeey take bin sun zata yi tashiga laburta mai abin da ya faru. A hankali ya zaga gun Mother; cike da girmamawa ya fara mata bayanin yarinyar: Tana promotional exams ne a makaranta idan ta tafi zata iya samun matsala. Suje ze san yadda zeyi da ita, in sha Allah, in sun gama zata zo hutu." Jin bayanin da ya yi yasa Mother Fariha ta kira Abeey da sauri ta tsaya gefen motar tana kallonta; idonta yayi wuri-wuri tace, "Yayanki YaceJarrabawa kuke?" Da sauri ta girgiza kai se kuma ta jinjina alamun eh. Tace, "Idan kun gama yace ze kawo ki hutu, Idan be kawo ba, ungo! ta buɗe jaka ta ciro complementary card ɗinta; ta ce, "Ki kira ni , I'll send people za a zo a ɗauke ki." Ba ɗon Abeey ta so ba, sedon ƙwarjinin da matar taimata yasa ta karɓa; tana gyada mata kai, hawaye daya na bin daya a idanuwanta.
Ta zagaya gurin Mehtav tana mata bayani. Mehtav ƙanƙame ta tai tana cewa, "Ita bata yarda ba da ita za a tafi." Daƙyar taj ya raba su. Aunty Ameerah ta shiga bayan motar tare da Mehtav. Convoy ɗin ɗaukar amaryar suka shiga wucewa straight zuwa Nnamdi Azikiwe International Airport. Har suka ƙarasa Mehtav bata daina kuka ba har suka damƙata a hannun Fulani. Ta ƙarɓe ta hannu biyu. Mehtav seda taji muryoyinsu Fulani tukunna ta gane waye ta aura, taji yan tsofaffinnan nata tsokanar ta. Kukan ɗaukewa ya yi gaba ɗaya, ta yi luf, taji wani relief nasauka a zuciyarta.
Gimbiya Hassana tunda tayi tozali da Mehtav take bin hannayenta da kallo; ganin babu awarwaron yasa ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Fulani da yan uwanta se sha'aninsu suke, duk da babu wanda ya bi takanta; amma gaba ɗaya ta tsargu, musamman da ta ga harda maman Maison a gaba-gaba wajen karbar amanar Mehtav. Gaba ɗaya ta tsangwami kanta, tace, "Kenan shima matsafin karya yake mata?" Ta na tina irin abinda ta bashi,wani irin bakin ciki ne ya tsaya mata a tsakiyar ƙirjinta.
A cikin airport din suka rabu. Su Hajiya Jannat da Hajiya Azeeza suka ce su Greece zasu je fara duba Islam kafin suje NURISTAN. Caraaf hassaana ta ce zata bi su itama saboda gani take kawai in ta bi su a cikin bikin nan asirinta zai iya tonuwa tace itace zata je ta wakilci Fulani tunda Fulani tana hidimar tarar amarya. Queen Layla ce ta dakatar da ita, tace, "Ita meye amfaninta? Su wuce kawai; su tafi za su zo daga baya." Ta na ji tana gani yan Greece suka fara gaba kafinnan suma su daga a private jet din Mai Martaba suka wuce dukansu, har da su aunty Ameerah, Se a cikin yan mata aka tafi da Falmata don zuwa gano dakin Mehtav da kuma halartar ɗan bukukuwan da suka ce ana bukatar danginta itama ko ɗaya ne awurin.
EHSAAS se can dare yasamu wayar Aman, inda yace mai ya bar wayar ne a villa. Sukuma sun je reception ɗin da baban Mehtav ya haɗa. fada ya shiga yi masa yana ce masa ya daina manta wayarsa a ko'ina, yasa duk hankalinsa ya tashi.
Calming ɗinsa down, Aman ya shiga yi yace masa "In shaa Allah zan kiyaye gaba." Nan ya shiga tambayarsa jikin Islam, sai yace masa da sauƙi in shaa Allah In two days ma likita yace ze iya sallamarta su tafi."
Aman ya shiga tambayarsa: "Shikenan vacation ɗin ya kare ko?"
Yace, "Eh, don ba ze sake sakacin barinta ita kaɗai ba. He will be with her and take good care of her."
"Hmmmm…" kawai Aman yace, kafin yace, "Da kabar ta gurin iyayenta, uncle prince, har seka gama satin cin amarcin naka saboda…" Sai kuma yayi shiru kamar me nazari.
EHSAAS yace, "Na fara wasa da kai ko Aman?" murmushi yayi kafin yace, "Kawai bana son aunty na taga abin da ze ƙara daga mata hankali ne kawai."
Yace, "Aman, I know what I'm doing." Kafin nan su shiga wata magana daban.
Ya ɗauka da yace ma Fulani kada wanda yazo, babu wanda ze zo ɗin, kawai base ganin tawagar manyan matan yayi, su uku sun zo duba Islam na musamman tun daga Nigeria.
Dawowar sa kenan daga hotel ya gansu a ɗakin asibitin, sun sata a tsakiyarsu. Besan me suke ce mata ba, sai dariya take. Rabon da yaga tayi dariya irin haka, an dade.
Gabansa sai da ya faɗi ganin Queen Layla ce kan gaba tana mata bayani. Yasan ko a da, Queen Layla ba wani son Islam take ba, amma ya fahimci yanzu ta gwammaci Islam sau dubu akan Mehtav.
Su daman su Hajiya Azeeza mutanen Islam ne tun kakarshi na da rai da su ta haɗa ta. Sune iyayen gidanta, duk wani ilimin zaman duniya da zamantakewar aure a gurinsu ta koya ta goge.
Ba shi da matsala da su ko kaɗan, amma yana tsoron Queen Layla a tare da matarshi. Kuma gashi yaga har da maman Islam a cikinsu, itama se murmushi take. Duk da turanci suke magana, alamar itama abin da suke faɗa yana mata.
Kamar ya juya haka yakeji amma kuma se ya daure ya buɗe ƙofar sosai. Islam murmushi tayi tana mika masa hannu alamar yazo.
"Look who are here!" ta faɗa tana nuna masa su cike da farin ciki.
Shima murmushi yayi, ya shiga gaidasu ɗaya bayan ɗaya. Suna amsawa ba yabo ba fallasa.
Ajiye kayan da ya shigo da su yayi yana musu sannu da hanya, suka amsa, suna mai ya mai jiki, kafin su mai jajen rashin da suka yi. Ya amsa da sakakkiyar fuska amma dai duk yayi sanyi.
Islam wata box ta ja a gefe tana buɗewa wata riga Sanyice ta saka mai kyau guda biyu. Ta shiga daga wa tana nuna masa ta yarace 'yan shekara guda kamar dai Jr.
Tace, "Mommy Jannat ce ta haɗa ma Jr, ka gani?" Amsa yayi yana nuna farin cikinsa, yayi ma Hajiya Jannat godiya. Ta yi murmushi kawai.
Islam ta ce, "Kina ji duk abin da nace miki, kinsan ita zero shugabar dukkan wata lamba ce."
Dariya yaga Islam tayi har da kwanciya jikin Hajiya Azeeza tana rufe fuska alamar ta fahimci abin da take nufi.
EHSAAS looking confused, dai bai ce musu komaiba.
Ta jinjinawa Hajiya Jannat kai alamar ta fahimta, tace, "Yauwa, mu ba wani bikin da zamuje. Munanan gurinki kafarki. Kafarmu har se kin warke zamu biki can."
Murmushi kawai yaga Islam tayi, ta ɗan saci kallonsa.
Gefe ya koma ya zauna saman couch, ya ciro wayarsa, ya fara dannawa ko ze fahimci inda maganar tasu ta dosa. Sai ya ji ma sun sauya hira zuwa bata shawarwari yadda zata kula da kanta yayin haihuwa da raino da yadda zata kula da lafiyarta da ta Jr.
Jin hirar nasu ba mai ƙarewa bane, kuma they are not talking about aurensa, sai ya mike yana tambayar Queen Layla: "Sunyi lounging a hotel ko kuma yakama musu a wanda yake zaune?"
Girgiza kai ta shiga yi tace, "Wane hotel kuma? Ana zaune kalau ai mijin Hajiya Jannat na da duplex a garin, kuma bama ya zuwa se karshen shekara. Don haka nan zasu sauka."
Jinjina mata kai kawai yayi tare da ce mata, "If they need anything, su mai magana."
Ya kalli Islam yace mata ze je, yadawo. "Bye bye." ta mai, ya fice ya tafi.
Yana fita, Hajiya Jannat tace, "Kinga makiri ko? Kashe fa ya zauna yayi mana, ya ji ko zamuyi magana akan kodaddiyar amaryarsa."
Dariya Queen Layla tayi, ta bata hannu suka tafa. Itadai Islam bata ji daɗin yadda suka sako EHSAAS a gaba ba.
"Ke Islam, kalleni nan," cewar Hajiya Azeezat, "Ko kin warke, kada kisake ki nuna mai kin warke. Se amarya tayi sati biyu zaki bar shi yakoma Nuristan, zamuga karshen rawar kai."
Girgiza kai tashiga yi tana fadin, "Ayyah big mummy, kada a shiga hakkinta itama."
Bude baki Queen Layla tayi tana fadin, "Ashsha! Ai indai Fulani Hajar ce ke tare da yar'nan kullum, duk kullin da muka mata se ya warware. Ina ruwanki da hakkinta? Kuma kece kika aurota ko EHSAAS?"
Dan jim tayi tana fadin, "Ai in sire ya shiga hakkinta, Allah ze kamashi da laifi koda nice na ja. Kinga, banason sire yayi zunubi saboda ni."
Jinjina kai kawai Queen Layla tayi.
Mom ɗinta Veronica da ta fahimci matan so suke su taimaka wa Islam ta mallaki mijinta, a tafin hannunsu, rankwashinta tayi tana ce mata, "You're still as foolish as I always knew." Ta ja tsaki tana mikewa, Islam rike kanta tai tashiga turo baki.
Hajiya Jannat tace, "Kuma Islam fa tafimu gaskiya. Ba zamuso Allah ya kama EHSAAS da laifin rashin adalci saboda mu ba. Amma Islam, kema yanzu kinsan kina buƙatar kulawarshi kamar yadda take buƙata, ko?"
Jinjina musu kai tayi tace, "Yes mommy."
Tace, "Kibarshi ya ƙara sati guda anan kafinnan angama bukukuwan da ake a can Nuristan ɗin. In yaso se kibarshi yakoma shi kaɗai. Inason mu zauna inmiki wasu karatuttuka wanda muka manta bamu daura miki lokacin aurenki ba har kika bari wannan baraka ta shigo gidanki."
Hajiya Azeeza tace, "Niko Islam, kodai duk classes ɗin da muke miki ba kya ɗaukane? Ba kya practicing? Don yadda na yarda da method ɗinmu, ban taɓa tunanin akwai wata macen da zata iya jan hankalin EHSAAS bayan ya ganki ba."
Hajiya Jannat ta murmushi tace, "Kema ki faɗa Hajiya Azeeza. Kinganmu shekara da shekaru ba me kishiya cikinmu in kika cire Layla. se Islam yarinya danya sharaf aure shekara biyu kwata-kwata. Wallahi maza dai basa kyautawa, duk da halal ne, amma daya dan bari ta kwan biyu."
Queen Layla tace, "Yabari ai zalamamme ne nagaske,wai bakiga kallon dayakema yarinyar da bikinnan ba,aini EHSAAS yagama barar min da mutunci aduniya."
Sam Islam sai ta ji duk abin da suke faɗa akan sire ba daidai bane. Saboda itace take zaune da shi, ita tasanshi, tasan kuma aurensa bai rage komai na daga soyayyar da yake nuna mata ba.
"I want to ease myself," ta faɗa tana mikewa a hankali ta nufi bathroom.
Tana shiga, Queen Layla tace, "Na faga alama yarinyar nan soyayya ta rufe mata ido. Duk abin da zaku ce, ku koya mata ta kori kishiyar, bazata koya ɗin ba. Ku kyaleta tunkan ta kwashe komai ta sanar mai mutuncinmu ya zube a idon yaro."
Hajiya Jannat tace, "Aini kinsan bazan taɓa daurata akan hanya mara kyau ba. Abinda nakeso nakoya mata gudane shine son kanta. Samsam bata son kanta yarinyar nan. Kuma naga she has a soft side for the kishiya, bayan kishiya ko ciki ɗaya kuka fito, duk mutuncin da kuke, burinta taga ƙofar dakinki a rufe kin bar mata miji kin tafi. Sonake kawai ta daina kallon yarinyar nan a matsayin 'yar uwa ko kawa, kawai ta tsaya a matsayin kishiya, I want her to be selfish koda kadanne"
"Islam nada baiwa iri-iri a tattare da ita, ba kissa, ba makirci. Koda iya kyawawan halayen da take dashi zesa ta zama mafi soyuwa gurin yarima. Amma abin da muke tsoro shine kada kishiyar tayi amfani da wannan weakness ɗinta ta kwace miji a hannunta. Tunda dai har ya sake aure duk soyayyar nan da yake nunawa yana mata, that shows akwai space a zuciyarsa for the other girl. In ta shiga kuma zata iya doke Islam."
Queen Layla tace, "Ba fa wai kuma baggara ce."
Hajiya Azeeza tace, "Ina ruwanki da kasancewarta baggara Layla? Ba ruwanki. Ko Balarabiyace, karshe kenan. Nasan Islam zata iya ƙarawa da ita, kawai dai seta fita daga wannan soft side ɗin nata."
Queen Layla tace, "Toh, tayaya kike tunanin za ayi hakan?" Tace, "By giving her husband space. Tabarshi ya gama gigin amarcin nan. Anan ze gane banbancin tsakanin aya da tsakuwa. Wallahi rantsuwa nake muku ba kaffara, EHSAAS ba zai iya sati guda be nemi Islam ba, saboda na yarda da kalar tarbiyyar dana daura yarinyar akai."
"Kuma kowace kalar mace kuwa ze samu."
Queen Layla tace, "Kada fa kije kisa yarinya ta bar mata miji. Wallahi ta rike shi kam ko ta koma ta zama hoto."
Murmushi kawai tayi tana fadin, "Badai Islam daughter na ba. Ku bari ta fito, kada wanda yasake koda fadar maganar banza akan prince a gabanta. Saboda tana sonshi, ko kaɗan batason taji ana aibata mata miji. Kuma tayi daidai, don uban ɗantane."
Mommy'n Islam dake sauraron bayanansu duka jinjina kai tayi.
Har Islam ta fito daga toilet bata tanka musu ba. Seda suka ci abinci sannan suka ce zasu koma masaukinsu.
Har bakin mota Mommy ta rakasu kafin taja Hajiya Azeeza gefe tana tambayar ta: "Wace kalar abu tayi ma Islam ɗin da take da wannan confidence ɗin da assurance a kanta? Yarinyar fa is super foolish ko bata sani bane?"
Dan jinjina kai tayi tana fadin, "Nasan batada wayo, amma ba sakarya bace ba Mrs Zion. Shi kuma abubuwan dana koya mataso kema I can give you a private class akan hakan. Sedai ke me kudi ce, the great V-level kudi zaki biya. Itama don diyata ce mommy sama mommy ƙasa take cemin." Takarasa tana dariyar wasa
Murmushi Veronica tayi kafin tace mata, "Ai ita business take so su kulla,dom haka batada matsalar kudi, Ita da take into all this kind of beauty industry, tana son itama su kulla partnership. Yazamana classes ɗin da take magana akai, V-level tayi raising ƙwararrun malaman koyarwa, ta koyar da su ta yadda zasu barbazu a different branches nata dake Europe."
Jinjina kai Hajiya Azeeza tayi jin kalar basira da business idea da matar takeda. Wato su suna ƙoƙarin tallafawa 'yarta wajen mallakar mijinta, ita kawai hanyar samun kudi tagani.
Hajiya Azeeza ita kanta bata taɓa tunanin yin aikin nan na kudi ba, duk da itama ba ƙaramin kuɗade mijinta ya kashe aka koyar da ita ba. Yanzun ma da tace Mrs. Veronica ɗin na kudi ne, zolayarta kawai takeyi.
Tace mata zatai tunani, complementary card ɗinta ta bata tace, "In nayi tunani, se muyi magana."
Murmushi tayi mata suka shiga mota suka wuce, ita kuma ta koma ciki.
Koda EHSAAS yadawo da daddare, duk yadda yaso yayma Islam wayo akan tafada mai abinda sukace, kinsanar dashi tai saboda batason ace yana kallon iyayen nasa somehow saboda ita. Kuma tasan duk abinda suke fada akansa suna kaunarsa saboda dansune, kuma da ba dan shiba da batasansu ba. Tasan kaunarsa dasuke ce tashafeta har suke kokarin juyamai baya suna nuna suna side dinta don suyi making dinta tai feeling at ease.
"Shikenan baby, tunda yanzun har ana iya yin sirri dake kiringa boyemin?" murmushi tai tana jawo wayarta tace, "Ai koya nai agurinka." Tashiga scrolling kamar ba ita tai maganar ba.
Yace, "Baby, ni menataba boye miki arayuwata?"
Still tana kallon wayarta take fadin, "Someone went to Nigeria ten days before the wedding without my knowledge." Tana fadar haka yasan da shi take, but yayi mamaki datai finding out how. Aransa yace definitely gurin wadannan matan taji one way or the other.
"Toh kiyi hakuri, I'm sorry I didn't say anything about it ne saboda banson ranki yabaci."
Turo baki gaba tai ta fadin, "Ga islam sarkin fushi koh? Sekace nace zan hanaka zuwa wurin matarka."
"Islam pls," yafada yana kokarin karbar wayar don yanason tabashi attention dinsa saboda jin yadda take talking about this issue to him casually kamar irin normal ne dinnan, "sometimes I don't care" attitude dinnan nata nabashi haushi.
Wayar ta takwace tana fadin, "Niso nake nakalli interview din Chimamanda Ngozi Adichie na shekaran jiya. Kaji zatai book tour ko? Sire, in ansallamemu daganan pls mubiya ta Seattle. Naji ance she'll be there, I want to watch her live... kuma kaga..."
"Pls Islam, let's finish what we are talking about first. Kinsan duk inda kikeso mubiya zamuje. Pls talk to me, tell me damuwarki."
Murmushi tai tana playing video din data kamo tace, "Bakada maganinsa, so stop asking. In kaima baso, kake kasa kanka adamuwa ba sire." Takarasa tana nuna mai screen din wayar da aka fara interview din.
Tamai alama da hannu yay shiru. Shirun yay kamar yadda tace, tai leaning ta kwanta saman kirjinsa badon yana jin dadin kallon interview din ba, saboda wani guilt feeling dayake hunting dinsa irin yasan yamata lefinnan amman tazuba mai ido tabarshi da halinsa irin bata damunnan ba, kenan shi bema kai tadamu dashi ba, ko kallon baganewa yakeba dukda idan da ace bata kawo mai batun zuwansa Nigeria ba, he'll be more excited to watch it fiyeda ita. Saboda shi dan adawar Chimamanda dinne, ita kuma fan dintace ta amutu. Haka zasu kalla, yayta pointing out inda tai fucking up yana criticizing, ita kuma tana kakkarewa.
Yau itace ke ke magana throughout kallon nasu. Ganin baya responding tadago tana fadin, "You're so boring." Ta turo baki tana sauka kasan gadon, tace, "Bari daddy yashigo semuyi dashi daidai."
Nan doctor nashigowa, murmushi tasakar mai, shima yamata yana gadin, "Enyeee, patient dina tasamu sauki kenan?"
Jinjina masa kai tai tana fadin, "I'm okay, nace muku nawarke ko? Yanzun kasallameni garaj nake."
Murmushi yay yace, "Takoma tazauna."
Ba musu tazauna gefen EHSAAS, yashiga mata tambayoyi yana rubuce-rubuce. EHSAAS duk yana sauraronsu har suka kammala.
Yace, "Masha Allah, jiki yayi kyau. Yanzun kidanyi hakuri zuwa gobe ko jibi musallameki da dan saura amman dan kadan," yafada yana mata misali da hannayensa.
Kallon EHSAAS tai tana fadin, "Sire, kaji doctor ko? Dan Allah kace yasallameni, Allah nawarke, inason naje gida naga babyna. I miss my Jr. Zansaka mai rigar sanyin da Mommy Jannat takawo mai."
Jinjina mata kai yay cikin lallabi, yake fadin, "I'm so sorry baby, kibari goben ai kamar yau take. Kuma Jr harse kingaji dashi. Kidaure kisake kwana dayan."
Turo baki tai amman dai batace komai ba. Likita yasake saka mata drip, yay mata allura yace takwanta tai barci intanason asallameta da wuri.
Cikin jindadi takwanta tana jaddada mai, "Base jibiba, ita gobe takeso yasallameta."
"Da tohm," ya amsa mata.
Yace tai barci. Bata wani jima da kwanciyar ba tai barci. Dayake su mom dinta sunkoma gida damman, shiyake kwana awurinta. Tsit dakin yayi, yatsaya yana watching yadda take barcin so peacefully. Betaba ganin mutum kamarta ba. He knows all this is eating her up but she's trying hard to be strong for him,toh kodai tadena sonshine yashiga tambayar kansa,dayar zuciyarce tashiga karyatashi alokaci guda, yanisa still Wata zuciyar tashiga saka masa tafishi gaskiya datace baida maganin damuwarta, don koya tirsasata tafada mai ainahin ra'ayinta ayanzun gameda auren, hakan bayana nufin ze iya rabuwa da Mehtav bama, tunda yanzun tana amatsayin matarshine.
Yau kwana biyu kenan, kwata-kwata beji daga gareta ba, Wayarta bata shiga kuma yafi kyautata zaton tabarta a Nigeria ne, tunda tun shekaran jiya Aman yace mai sun koma NURISTAN.
Komawa saman couch yay yana satan kallon Islam dake barci. Seda ya tabbatar barcin nata yay nisa, yakirawo Aman.
Bugu biyu yadauka, suna gama gaisawa yace mai dan aiki yakeso yasashi.
Yace, "Just give order, Uncle Prince."
Yacemai, "Sabuwar waya yakeso yasiyamai da sim da komai, da komai yahada yakaima Mehtav." Yana tinanin babu waya a hannunta har yau basuyi magana ba.
Aman harze fara korafi se kuma kawai yakai zuciyarsa nesa, beson dada sa Uncle dinshi adamuwa.
Yace, "Tohm, Uncle" kawai.
Yace, "Pls Aman, kai sauri."
"Da tohm," ya amsa masa.
Yakatse wayar, ya cigaba da kallon Islam kamar TV. Daga karshe dai yashiga yadauro alwala, ya shimfida sallaya, yashiga yin nafila.
Yau kwanan Mehtav biyu kenan a NURISTAN. Gaba ɗaya kewar gida da yar uwarta ta mamayeta tun tana saran ganin EHSAAS har ta cire. Duk da irin tattali da kulawar da take samu daga gurin both Fulani da Mai Martaba, amma gaba ɗaya bata jin nutsuwa a cikin zuciyarta. Don tunaninta EHSAAS yayi fushi da ita saboda abubuwan da ta aikata ranar daurin aurensu, kuma ta tuna komai, har texts ɗin da ta tura masa, ta rasa meye ya hau kanta ta yi wannan kalar rashin hankalin. Don da ace wani ne ya bata labarin zata aikata irin hakan a baya, ba zata taɓa yarda ba.
Tun washegarin ranar da aka kawota ake bukukuwan gargajiya a gidan bakalar bikin da aka yi ma Islam lokacin aurenta da ba'a mataba. Sai dai ɗaɗɗaiku wanda aka ware na musamman saboda matar fari. Dukiya kam ta tarasu iri-iri har abin ya soma bata tsoro, don ko boxes ɗin danyar gwala-gwalan da aka kawo aka ajiye mata tun daga Nigeria aka taho mata da su wai a matsayin sadakinta ta kasa ko tabawa ta kalla suna closets dinta.
Gashi ta bar wayarta a Nigeria, da ba dan su Aunty Ameerah dake tare da ita a mahaukacin katon sashen ba, da bata san yadda zata yi ba. Domin mansion guda aka bata wai a matsayin sashenta ita kaɗaifa. Har yau ta kasa zaga gidan duk da yadda Falmata ke zuzuta mata shi. Kowa yazo sai sambarka yake yi.
Yau tana fitowa daga wanka da safe, ta shiga shiri cikin dakakkun kayanta na alfarma da Paa ya dinka mata su akwati biyar saboda baya son ta yi depending da kayan aurenta. Ya kashe makudan kuɗade sosai gurin siyan kayan nan don komai tsadadde ya siya mata.
Tana kammala shiri taji ana knocking ƙofar. Tasan ambata maids har guda goma daga sashen Fulani, kuma a sashen nata ma sunada bangarensu inda suke zama. Ta fahimci basa taɓa shigowa dakinta sai ta musu izni. Yanzu ma ta san ɗaya daga cikinsu ce ke mata knocking, kuma ita ma daidai da rana ɗaya bata taɓa bawa kowacce damar shigowa dakinta ba. Duk da taji Falmata na ce mata ai ba ma wai shine master bedroom ɗinsu ba, na EHSAAS akulle yake kuma babu mai buɗewa sai ya dawo ƙasar.
Tana buɗewa kuwa ta ci karo da maid ɗin, ta yi ƙasa da kanta tana gaisheta. Amsa ta yi, ta tambayeta me ke tafe da ita. Box ɗin data miko mata tasa hannu ta karɓa tace:
"Sako ne daga gurin Yarima Aman. Yace Yarima ne ya bayar a kawo miki."
Jin an ce sako ne daga EHSAAS yasa cikin farin ciki tace mata, "Toh, ki ce mai na gode."
Ta shiga cikin daki da hanzari ta buɗe box ɗin, ta ci karo da sabuwar waya gal iPhone ce irin ta Abeey sak-sak. Gefe harda SIM card din ƙasar NURISTAN. Ta ciro ta ɗauko charger ɗin ta jona, tana charging tana ta murmushi. Don ta san finally this is her chance to speak to EHSAAS.
Zama tayi gadin wayar, nan Falmata tazo ta sameta, ta saka waya a gaba tana ta murmushi.
Falmata tace:
"Ke kuma lafiya kiketa murmushi kamar tababbiya? Ko angonne zedawo ne?"
Girgiza kai ta shiga yi tana nuna mata wayar.
"Shi ya bayar a kawo min. Nasan kila yana ta kirana, yaji baya samu."
Murmushi Falmata tayi tana fadin: "Ki ce Allah. Ingani enyeee!"
Ta daga wayar jikin charge tana jujjuyawa tace: "Tayi kyau sosai Mehtav, Allah yasa albarka. Don Allah kina kunnawa ki daure ki kirashi kiji ya jikn matar tasa. Kinji? Kinga dai abubuwan da kika aikata na rashin kyautawa yawa gare su. Make it up to him, dan Allah."
Jinjina kai tayi, a ranta tana fadin "Harma se kin fada min min." Amma a fili tace: "In sha Allah zanyi, nagode Falmata."
Zama tayi a gefenta tana nuna mata chat ɗinsu da Aman na dazun, don duk sha'anin bikinnan da zamansu shi yake ta jigila dasu duk wani abu da suke bukata, kafin ma suce ya kawo ya ajiye.
Tace: "Kinji shi? Ni bansan me yasa ba, se mita yake yi wai me yasa ba'a taho da Abeey ba."
Dan waro ido tayi tana fadin:
"Kaji munafunci ko? Ina ruwansa da Abeey? In yana son chatting dake, ai ba sai ya fake da wata Abeey ba. Straight yay chatting dake. Amma let me warn you beforehand, ba shi da mutunci."
Murmushi ta shiga yi tana fadin: "Aiko sai dai in wani Aman kike magana, ba wannan ba. Duk kirkinsa, kuma ba shine ya karɓi number taba nice na karɓa saboda tsaro. Kinsan zaman bakon guri, ba wanda muka dan saba sai shi. Kuma duk sanda naganshi ni nake gaidashi akan kari ta WhatsApp."
Tsaki Mehtav tayi tace:
"Amma kin yi asara, kanin naki kike gaisarwa. Kin bi kin bararwa da mutane mutunci a gabansa." Tace: "Keh Mehtav, don kinsamu EHSAAS ne kike ganinsa haka-haka? Aman fa hadaddan gayene, son kowa kin wanda yarasa. Kuma ba ni ba aikina ganinsa. Kinsan har ke ya girma wallahi."
Tace: "Toh wallahi bai girman ba. Ni da EHSAAS yace min ni yayarsa ce, though ba fadamin exact shekarunsa ba. Amma nasan ba zai wuce sa'an maman Jr ba." Tace: "Wai matarsa ta farko." Jinjina kai tayi tace: "Itama yarinya ce ai."
Falmata tace: "Ahhh, kice ke Mehtav in minutes zaki goge masa hadda, saboda kinsan yaran nan ba wata kulawar arziki da soyayya suka iya bama maza. Sai shirme."
Murmushi kawai Mehtav tayi tana fadin: "Na rabaki. Ni dai baruwana tsakanina da ita. Mutunci da girmamawa juna. Kema kuma in kinaso, ki ci gaba da gaida wannan uban miskilancin. Aman ya amsa, kiga mutuncinta. Don Islam mutum ce."
Ta karasa fadar tana murmushi ita kadai. Jinjina kai Falmata kawai tayi tana fadin:
"Lallai karatun Aunty Ameerah bai gama shiga kanki ba. Kishiya kike cewa mutum? Ai mu zuriyarmu kowa yasan ba ma zama da kishiya. Kuma kema muna nan, nasan sanda zaki koreta bawanda yaganki."
"Ko ni ta koreni ba," Mehtav ta fada tana jawo wayar data kasa hakuri ta cika. "Kiban guri, zanyi waya da mijina."
Cewar Mehtav tana kallon Falmata data rike baki tana fadin:
"Sannu masu miji toh. Ba inda zanje. Mijin da har yau ko keyarsa baki ganiba, kwana nawa da auren? Shine za'a min gori? Ƙofa fita daga layinmu baki ba."
Tace: "Kamar ya bangane ba?" Tace: "Matsayina da naki har yau ɗaya ne. Kibari idan ya maidake mace, sai kimin gorin dagayya."
Ta fada tana mikewa da pillow. Mehtav ta bita cikin kuri tana cemata: "Kwana nawa ne? Tajira ta gani."
Falmata ta rike baki tana fadin: "Lallai wato don kinga babu su Sarah masu tare min, shine bakinki ya bude ko? Allah yakaimu, in sha Allah, ina gidan nan, wannan lamari ze wakana. Sai na tuna miki wannan rashin mutuncin da kika min. Namiji ko gaki, gashi, sai ya fara baki kashi zaki gane Allah daya ne, se shegen rawar kai kamar wata 16"
"Bakinki yasari danyan kashi, me fatan tsiya kawai," ta fada tana hararar ƙofar da Falmata ta bi ta fita a dakin. Ta tura baki tana rubuta lambar EHSAAS da ta haddace a kanta cikin wayar bayan ta kunna, ta shiga kiransa.
It's Fatoum's Passion Don't forget to: Vote Share Like Comment [12/10, 21:12] Fatima Rufa'i Nasidi: It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.