EHSAAS

Chapter 66

by @fatoumspassion

hannunta rawa ya farayi jin wayar na ringing, kirjinta bugawa yake ba kakkautawa saboda batasan wace kalar tarbar EHSAAS zeyi mata ba, seda ta kusa tsinkewa tukunna taji andauka, Ahankali tashako muryarsa cikeda nustuwa yace Assalamu Alaikum, Mehtav ta kasa daurewa tai, kawai tasaki wani irin kuka hawaye daya nabin daya kamar tana gabanshi ta amsa sallamar tashi da "Ameen....Wa...alaikum .... Assalam" Jin yayi shiru tashiga fadin "Mi Amor" Nan ma shiru yay kamar baya sauraronta tasan kuma sarai yanaji "EHSAAS… please say something" tafada tana kallon screen din wayar don tanason ta tabbatar yana kan layin har lokacin, "I'm so sorry for everything Mi Amor… it was just something that came over me… I swear I didn't mean to hurt you," ta ce da muryar kuka, tana shessheƙa kamar ƙaramar yarinya "Please, kada ka yi fushi da ni, I'm so sorry…talk to me pls"

Shirune yasake biyo bayan maganarta, sai saukar numfashinsa kawai take ji ahankali daga tacikin phone ɗin. Shi kuma EHSAAS daga daya bangaren ahankali ya lallaba yafito daga dakin da Islam take yasamu kujera anan farfajiyar corridor din kafinnan yasamu nutsuwar sauraron kukannata da yakeji har kasan ransa.

Seda yaji tadan tsagaita kafinnan yasauke ajiyar zuciya cikin murya mai taushin yake faɗin

"Mehtav… it's okay. Ki daina kuka." Ya ɗan yi shiru kadan kafin ya ci gaba, "Ni ma I'm sorry. Na tafi a ranar dinner ɗin ba tare da wani explanation ba… I didn't mean to hurt you, I know it pained you."

hawayenta tashiga sharewa da bayan hannunta tana jin daɗin jinsa yasoma magana and it seems his not as angry as she expects. Ashagwabe take fadin "But pain? Which pain? You didn't do anything wrong anyone a position dinka zeyi acting thesame"

Murmushi taji yayi ahankali yana fadin "Pain ɗin da zuciyar mutum ke ji idan wanda yake so ya nuna kamar bedamu dashiba Mehtav you still didn't trust what we have, shine babban matsalar da muke samu a alakarmu kina tinanin bandamu dake ba amman bakisan yadda na damu dakeba how I wish zan iya bude miki zuciyata kigani, and no relationship is perfect nataba fada miki hakan wancan karon ma right, sometimes relationship ba sai komai yazama perfect ba,we are all humans we make mistakes and we learn from them, akwai times da zamu ringa samun misunderstanding sosai amma bai kamata hakan ya zame miki dalilin rabuwa dani ba, it pain me each time nai miki lefi baki tsayawa ki hukuntani daidai laifin nawa se kice zaki barni gaba daya Mehtav this is wrong,banaso kidena,pls karki kara"

Shiru tai tana sauraron yadda yake magana daki daki cikeda nutsuwa, sosai yay calming mind dinta Yaci gaba da fadin "ita Alaka kamar itace ne, idan ba'a kula ba yana iya bushewa Amma idan kuna forgiving juna, it will grow stronger. Ba sai kowa ya zama perfect ba. What matters is love, patience and forgiveness."

hawayenta ta goge gaba ɗaya, ta nisa sannan tace "Na gane yanzu… and I forgive you. Allah ya yafe mana baki ɗaya, kuma in sha Allah bazan sake cewa zan rabu dakaiba"

EHSAAS ya yi dariya kaɗan, yana fadin "Ameen. Ni ma na yafemiki Mehtav. No grudges, kinji?"

"Na ji," ta ce tana murmushi.

Shiru sukai nawasu seconds kawai suna sauraron numfashin juna tacikin wayar kafin Mehtav tai breaking silence din ta hanyar tambayarsa "How is Islam? I heard what happened...Allah yabada na mora, Allah yajikan wanda aka rasa, I'm really sorry for the miscarriage, please tell her I'm so sorry."

Lumshe ido yay yanajin dadin yadda tanuna concern dinta akan Islam da abinda suka rasa yace "Ba komai Mehtav, Allah yasa hakan shine alkhairi . She's getting stronger, zan sanar da ita sakonki in sha Allah" Shiru tai shima yay shiru kafin ya canza murya zuwa salon tsokana yake fadin "Amma gaskiya na yi kewarki fa matata..…"

Dariya tai tana fadin "really?" Yace "uhmmm ko nafara listing miki abubuwan danai missing ne," Dasauri tashiga girgiza kai kamar tana gabanshi, Tana fadin "Nidai uhmmm uhmm" Dariyar shima yayi yana fadin "Meye nasaurin cewa a'ah bafa abinda kike tinani zan fadaba naughty girl" Koda bata gabanshi yasan rufe fuska tai kuma hakantai as he expected Yace "Kinfara rufe fuskarnan koh kamar budurwar kauye" Murmushi tai tana kumbara mai baki "Wai itace ma budurwar kauye?" Yace "Eh mn ai nakusa cire kunyar nan" Dariya tashigayi ahakannan seda sukai kusan awa biyu suna waya batareda sunsan lokaci yawuce har hakaba, harseda EHSAAS ya hango likita da nurses biyu suna tahowa alamar suna zagayen darene kamar yadda suka saba badon yasoba yay sallama da Mehtav don yanason adubata agabanshi atabbatar komai lafiya kafin asallamesu don yasan arigimar Islam inba asallameta gobe ba komai zai iya faruwa.

Koda safiya yai washegarin ranar likitan kin yarda yayi ya sallami Islam haka tagama kuncinta yace seta sake kwana daya dakyar EHSAAS ya lallabata ta hakura,dawowar su hjy jannat ne yasaka ma tasake jikinta anan suke cemata tarefa zasu koma NURISTAN dan jim tai kafin tace musu itafa daganan itada sire ba NURISTAN suka nufaba can Seattle zasuje amman kwana daya tak zasuyi su koma NURISTAN basu wani damuba suka ce mata seta dawo su zasu fara wucewa NURISTAN adaren ranar, don tsabar rigima haka tasa EHSAAS agaba sanda zasi tafi da ita akaje har airport din suka rabu cikeda kewar juna tana musu alkawarin itama tana nan tafe in sha Allah tare dashi suka koma asibitin batareda sanin likitan ba don fada zeyi in yaji labarin tafice batareda yasallameta ba, EHSAAS seda ya tabbatar tayi barci yauma yazagaya yafice harabar asibitin yasha wayarsa tareda Mehtav,seda dare yaratsa yadawo kuma cikin ikon Allah har lokacin barci takeyi bata koyi motsiba saboda yana kyautata zaton a alluran da likita yake mata akwai ta barci aciki.

Islam yau tunda tafarka sai murmushi takeyi saboda yau dai an ce za'a sallame ta daga asibitin dagaske. tun sassafe parents dinta sukazo tareda Jr se murna takeyi ganinshi tare da ita yau, tun dazun suke wasa kafin ya gajiyar da ita ta makalashi da EHSAAS suka cigaba.

Ta zaune agefen gadonta tana magana da dad dinta nurse tashigo da murmushi ta tareta itama nurse din ta mayar mata tana fadin "Good morning Princess Islam, congratulations, doctor said you're fully stable now, you can go home today! Yaudai shikenan ba mita" Dariya tafarayi wato har nurse dinnan tagane batason zaman hospital dinnan, duddubata tashiga yi, sega doctor shima yashigo dakin yana murmushi yashiga tsokanar Islam din shima yakarasa mata final check up yana ajje mata discharge papers dinta yace "Congratulations once again, Her Highness, your strength is back and your vitals are perfect. You can continue your recovery at home." Cikeda farinciki tamike tana fadin "Thank you doctor" tanufi kayanta tafara hadawa, EHSAAS mikama doctor din hannu yayi yana fadin "Thank you doctor,I really appreciate everything you've done for her." Doctor yay murmushi yana cemai "bakomai ai aikinsane yakeyi."

Cikin mutunci sukai sallama dashi Islam harta kammala hada kayanta, se dariya suke mata ana tsokanarta. bata kulasu ba itace akan gaba har suka fito daga asibitin, EHSAAS na rike da ita akofar asibitin taga flowers tace tanaso seda ya tsaya yasiya mata bouquet yabata se kalla take tana murmushi.

yabude mata kofar motar tashige tana shinshina flowers din da kamshinsu yay mata dadi sosai, EHSAAS ne yakarbi key hannun abraham Zion yashiga driver sit, Abraham kuma yashiga front sit Islam da mom dinta da Jr suna baya, Suna fara tafiya Islam ta sauke glass din sashenta baki daya tashiga kallon gajimare take fadin "Finally, I'm going home with my family," ta fada tana lumshe ido, Veronica tace "aidaman nakine bana wasu ba peace wayace ba family dinki bane dakike emphasizing," dariya tashigayi tana fadin "oh mommy bakiso in kwace miki family koh,nadena fada nakine," Dariya kawai mommy tai tana fadin "kyaji dashi, " seda sukai nisa sannan Islam tadanyo gaba tana leka dad dinta dake front sit kafin tace "Daddy,… Sire da ni muna da wani plan. We want to go to Seattle tomorrow. Chimamanda Ngozi Adichie has a book tour there, and you know what tun ina cikin Jr I've been dreaming to attend one of her tours."

Veronica cikin tsokana take fadin "You and your love for Nigerian writers, kai EHSAAS you better prepare yourself ooo."

EHSAAS ya murmusa, "I'm ready ma. Anything to make my wife smile."

Abraham ya ɗan yi shiru kamar yana tunani, kafin yace "Hmm, Seattle? You're just getting discharged Islam… are you sure you're strong enough?"

Tace "Daddy please, I'm okay now. The doctor said I'm fine and I've been resting for days. I just need something refreshing, you know? Something that will bring back my spirit."

Abraham ya kalli EHSAAS, kafin yace "Alright, but make sure she doesn't over-stress herself."

EHSAAS ya murmusa, "I promise, sir."

beach house ɗin Abraham Zion dake bakin teku suka koma, Gidan na da windows masu girma nagaske, iska tana shiga tako ina tana kada curtains, ga wani kamshin kasar gurin datake kawowa mai dadi.

Islam jan EHSAAS zuwa dakinta na gidan tai,tashiga nuna mai littattafan ta dake karantawa tun suna zuwa garin hutu kafin ta hadu dashi suyi aure har inda take zama tak karatun seda ta nuna mai, da tsofaffin teddy bears dinta, tanata murmushi, ya taya ta tana fadamai sunayen yar tsanonin da yanzun takejin they sound super silly tashiga dariya tana fadin "can you imagine,senai spending two hours inawa wadannan teddies din karatu bakina duk yabushe kuma afili thinking this whole time suna jina ashe ashe suda dutse babu maraba" dariya yashiga yimata yana jajanta mata irin asarar lokacin datai akan teddies this whole time,seda tagaji dan kanta da bashi labarin da mai nune nunen sannan ta baje akan gado gefen Jr shima daketa wasansa, EHSAAS yakaraso yana wasa dashi yashiga cemai "See your mommo smiling again… finally!" Islam gyara kwanciyar ta tai tana kallon su duka biyun cikeda admiration take fadin "You two are my whole world," Takarasa tana rungume su duka biyun ajikinta.

Adaren ranar su Abraham Zion da Veronica suka wuce London,saboda wani meeting mai mahimmanci da Veronica din zatai attending sukabar Islam da EHSAAS a Santorini suka tafi cikeda kewa da kaunar yar tasu.

Washegari da safe suma suka shirya don tafiya zuwa Seattle. Flight ɗinsu first class ne kamar yadda Islam take son komai ya zama classy da comfortable.

Sanda suka sauka a Seattle Jr yayi barci, yana kwance akirjin EHSAAS suka fito suka fara cin karo da fresh breeze na garin,wanda ke cike da sababbin ganyayyaki da iska mai sanyi. EHSAAS ya kama hannunta yana fadin "Welcome to Seattle, my Queen."

Already yamusu booking hotel din dazasu zauna is not far from gurin da za'ai book tour din saboda baya son tawahala ko kadan, taxi suka hau zuwa hotel din

wanka sukai, suka ci abinci acikin suite din nasu kafinnan ta azalzaleshi ganin lokaci yaja batason tai missing afara ba'a gabanta ba shine yakarasa shirya Jr suka fito already yayi order din Uber suka wuce hall din wanda ya cika da mutane, cameramen suna ɗaukar hotuna tako ina mutane suna ta clapping yayin da Chimamanda ke magana akan "The Power of Storytelling." already tafara amman da yake ticket dinsu VIP ne suna daga cikin sits din gaba gaba. Islam sauraronta takeyi with full of admiration tana jindadin yadda take bayani, ko kifta ido islam batayi idonta akan chimmamanda. dariya EHSAAS kawai yake kasa kasa yake zungurin kafarta amman bata kulashi ba don batason any form of distraction shima da yaga taki kulashi seya bada hankalinsa yana saurarar bayanin wanda yasan one way or the other dole ze amfaneshi musamman da rubuce rubucensa shikuma is total opposite from hers, ahaka har aka gama event din, tana ganin writer din tai sallama da masoyanta tawuce. Islam takalli EHSAAS tana fadin "Isn't she adorable" Jan hancinta yayi yana fadin "But your more adorable than her," Turo mai lips tai tana fadin "Dama baka yinta" Hango wani bature yana zuwa ta wurarensu yasa Islam tadan taba EHSAAS yajuya shima kallo daya yaywa baturen yamaida hankalinsa kanta har baturen yakaraso cikin girmamawa yake fadin "Sir, this way please, Madam Chimmamanda will meet you now." Islam dan waro ido tai takalli baturen kafin ta kalli EHSAAS dake mata murmushi tasan is his doing, Cikeda mamaki takasa boye farincikinta take fadin "Are you serious?"

EHSAAS ya dage mata gira daya yana fadin "You think I'll bring you here and not make your dream of meeting her in person come true?" Rungumeshi tai tana pecking cheeks dinsa, "That's why I love you so much sire your the best" Murmushi yayi yana fadin "Let's go my lady" Kama hannunta yay suka bi baturen zuwa wani private room inda Chimamanda take zaune tana signing books. Tana ganin Islam, ta miƙe da fara'a, "Oh my God, you're so beautiful! Mrs EHSAAS right?"

Islam kasa magana tai, tashiga murmushi kawai tana kallonta sekuma takalli EHSAAS, murmushi itama chimmamanda tai tana bude mata hannayenta alamar tazo ta rungumeta, Islam tace "can I?" Jinjina mata kai tai aiko takarasa dasauri tana rungumeta anitse take fadin "I've been your fan for years," Chimmamanda godiya tashigayi mata da nuna nata kaunar datai! itama tai hugging dinta back kafin Islam tasaketa tana murmushi, Chimamanda tai signing a kan littafinta "The Thing Around Your Neck" ta rubuta: To Princess Islam, may your story always be powerful and kind.

Islam ta karɓa tana murmushi, ta kalli EHSAAS tana cewa, "Thank you, Sire, You've made one of my biggest dreams come true."

EHSAAS ya lakace hancinta da yatsansa cikin wasa yake fadin "And I'll keep doing that, so long as I live." Sallama sukaima chimmamanda bayan EHSAAS ya musu hoto tare, Suka fito daga cikin hall ɗin cikeda farinciki baby Jr yana kwance a stroller yana bacci cikin nutsuwa, iska mai sanyi tana kadawa.

Da daddare Islam ce ta fito daga bathroom cikin short satin nightgown mai launin cream, kanta cikin towel tana goge gashinta, shikuma yana zaune a balcony yana shan tea, yana kallon city view yayi shiru kamar wanda yay nisa cikin tinani.

Ahankali Islam ta taka zuwa gurinsa, ta jingina da ƙofar balcony tana kallonsa tana murmushi, "Sire, tunda muka dawo, you've been so quiet. What are you thinking about?"

Juyowa yay suka hada ido yasakar mata murmushi me sanyi kafin yace "About how peaceful this moment is… and how I wish we could freeze it forever."

ƙarasawa tai ta zauna a saman lap dinsa tana kwantar da kanta a kafadarsa, tace, "It's been long since I saw you this relaxed. Thank you for everything you've done for me… you've made me feel alive again." juyo da hannunsa yayi yana shafa kumatunta ahankali yace, "You deserve it all, baby. You've been through a lot." Kafin suyi shiru nadan lokacin suna kallon city lights,daga nan EHSAAS ya janyo ta sosai ya ɗora mata kiss a forehead, sannan ya kama hannunta cikin tsantsar kulawa yake fadin "I've got something for you,"

Islam ta ɗan kalleshi da mamaki, "For me? What again, sire? You've done enough already."

Murmusawa ya danyi kafin yace "No, this one na musamman ne. Something you've been asking me for months…"

Ya tashi ya shiga cikin ɗakin, ya dawo da wani brown envelope mai kyau, wanda aka rubuta 'For my Queen, Open with a Smile' a jiki.

Islam ta karɓa tana dariya, "Sire… what's this now? You and your surprises."

"Just open it, baby." yafada yana kallonta yana murmushi.

Tana bude envelope ɗin, ta zaro wani stack na papers, tana duba su ɗaya bayan ɗaya. Sai taci karo da takardun Yale University,Oxford, Princeton, Harvard, Stanford, University of Cambridge, University of Edinburgh,WSU, Brown, University of Toronto, da kuma University of California, Berkeley.

Ta ɗaga kai cikeda mamaki take fadin, "Sire… are you serious? Are these what I think they are?"

Jinjina kak yay yana tabbatar mata "Application forms, baby. From the best universities in the world. I printed them all out for you to choose the one you want. Oxford, Princeton, Yale, Cambridge… any one of them, Islam. You've always dreamt of studying literature in a real academic environment, right? Well, here's your chance."

Ta riƙe papers ɗin in disbelief take fadin "Ya Allah, I can't believe this… Sire, you're serious?"

Ya gyada kai yana kallonta cikeda soyayya kamar ze cinye ta, "I'm serious. Choose any of them. I've already spoken to some people that can help us with the process. Wherever you choose, I'll go with you."

Ta buɗe baki cikin mamaki, "Wait… you'll follow me?"

Ya murmusa yana ɗan jinjina kai, "Eh mana, ai kafata kafarki. Besides, masters da PhD ba kamar undergraduate bane.We can balance it with our duties in Nuristan, in zai zama necessary We travel back once in a while, besides I've always wanted to continue my PhD anyway."

Islam ta fashe da dariya cikin mamaki da farin ciki, "Wato dai baza'a barni inje ni kaɗai ba ko? You just can't stay away from me!"

dariya yayi yana cewa, "Never. I'm not that foolish."

Tana dariya take fadin, "Amma wallahi you're unbelievable. You used to say 'No, Islam, it's too risky, it's too far' yanzu kai da kanka kake kawo min schools that are far away from home sef!"

Ya ce, "Because I realized how much it means to you. And I want you to keep growing. Education is a lifetime gift, and you deserve the best."

Kissing forehead dinsa tai tana fadin "Sire, I don't even know what to say. I love you so much."

Lumshe idonsa yay yana fadin "Just say you'll fill the forms. That's enough and yoy know I love you more right"

duba sunayen jami'o'in tashiga yi tana girgiza kai, "Oxford, Princeton, Yale, Cambridge… all these places nafiso that's tun kafin in hadu da kai. But Oxford is special. It's where I met you first."

Ya ɗan murmusa yana janye hannunta, "I knew it. Oxford, right?"

Ta ɗan turo baki tana tsokanarsa, "Of course, Mr. Oxford Boy. Kai fa mayen old English literature ne. Shakespeare dai kamar kai yamutu yabarma duniyar."

Dariya yashigayi yana fadin "You Gen Z people don't understand greatness. Oxford is not just a school, it's history, legacy, intellect. You see, the foundation of literature itself"

Ta katse shi tana dariya tana cewa, "Haba sire! Stop lecturing me. Ka bari ai inje in gano greatness ɗin nan da aketa zuzuta min tuntuni da idona!"

"Good," ya ce yana murmushi. "Toh, Oxford it is."

Ta ɗan kashe masa ido tana cewa, "Oxford it is. Back to the place where it all began."

Suka yi shiru suna kallon juna na daƙiƙa biyu, kafin EHSAAS ya matsa yadaura lips dinshi saman nata cikin natsuwa, ya rungumeta a jikinsa kamar wata jaririya, tai luf.

"Thank you, sire," ta faɗa a hankali tana shafa kirjinsa.

"Don't thank me, baby. Just promise me one thing ,no matter where life takes us, we'll always come back to each other." Ahankali tace " I promise."

Iska mai sanyi tana ta kadawa, suka shiru tanan balcony suna hango Jr dake bacci asaman gadon cikeda kwanciyar hankali.

Washegari da sassafe jirginsu yadaga se NURISTAN, saboda bawani transit dasukai babu wanda suka sanarma zasu dawo agidan sai Aman shima don EHSAAS yanason yakasance shine ze daukoshi daga airport ne. Aman bakinsa har kunne ganin Islam healthy on her feet har suka shiga mota yana mata sannu, yana tuki seya juya yakara cemata sannu seda EHSAAS yabugi keyar tasa yace yakalli gabanshi karya zubar dasu anan gurin.

Ta kofar bayama suka shiga palace din direct sashen Fulani suka nufa EHSAAS na satan kallon sashen Mehtav sabo kal da yashaci fili dakansa yasa akai gininsa cikin kankanin lokaci, wata irin kewarta yakeji har cikin kashinsa saboda zuwansu Seattle kashe wayarsa ma yay baki daya saboda throughout yana tareda Islam bama yason yaraba attention dinsa gida biyu.

Ababban falo suka samu Fulani tareda su Queen layla,anata fira cikin mamaki ta mike ta rungumesu duka musamman Islam kamar zata maidata ciki EHSAAS ganin kato dashi ta rungumesa duk ana kallonsa ana mai dariya yasa yay saurin raba hug din yana dan kasa dakai alamar jin kunya, takalli Islam tana kissing forehead dinta tashiga hamdala tana nunama su Queen layla wai suga yarta is back yarta taji sauki Masha Allah. Islam murmushi kawai takeyi ajikin Fulani tashiga tambayarta ya karfin jikin? kamar wata likita, wai metake ji,? is she alright? badai abinda ke mata ciwo ko? jinjina mata kai tai tana fadin "eh maama," queen layla tuni ta amshe mutumin nata Jr agurin EHSAAS tana tai masa wasa, hjy azeeza tace ma EHSAAS "aina dauka daga Seattle din sabon honeymoon zaku karayi," dan sosa keya yay yakasa mayar mata saboda yana kunyar Fulani. announcement din shigowar Mai Martaba sukaji nan danan duk matan suka dan gyaggyara galensu yashigo shima Islam yanufa yana fadin "welcome back my daughter sannu" yana bude mata hannayensa adan kunyace takarasa tai hugging dinsa yay hugging dinta yana murmushi yana bubbuga mata baya yace "sannu kinji kiyi hakuri, Allah daya baki wannan shiya karbi abinsa in sha Allah ze mayar miki da dubunsa, next time yan hudu zaki haifa mana," wata irin kunyace taji ta rufeta taduka tana rufe fuska,fulani ta durkusa tana kamota akaima mai Martaba irin hararar nan da zakafi kira ta soyayya tace "kaga kabawa yata kunya koh don't mind him taso mutafi" sumsum tamike tana rufe fuskarta wiyan Fulani EHSAAS ya tsaya yana watching dinsu with full of admiration kafin yakalli Mai Martaba yakalli Fulani yace "da alama nazama dutse nifa babuma wanda yakalleni ballema atambayi yanake koya nakwana," dariya duk dattawan sukai, Mai Martaba yace "atakaice dai kishi kake da diyata?" yace "gaskiya kwarai Allah ya temakeka nifama ina bukatar kulawarnan," dariya Fulani tai tana riko kunnensa take fadin "sake maimaitawa inji," cikeda raha yake fadin "na tuba rabin ran nadena kishin na barmata naci girma," Islam gwalo take mai kasa kasa yacije baki irin zan kamakine dinnan Mai Martaba ya kamo kafadarsa yana fadin "zomuje inbaka sirrin yadda zaka kwace mu daga hannunta," murmushi yayi yabi bayansa suka dan yi gefe kasa kasa yake cemai "badai wata damuwa koh naga kundawo dawuri," jinjina masa kai EHSAAS yay yana fadin "babu komai tawarware likitan dakansa ya sallamemu" yace "toh Masha Allah is she fine? Ba dai tayin koke kokennan koh," jinjina mai kai yay yana fadin "she's stronger than you think nikaina nayi mamakin yadda ta hakura da wurwuri" murmushi Mai Martaba yayi yana fadin "addu'a ce kawai yarima, yanzun abinda nakeso dakai shine kashirya katafi ita gurin amaryar taka kaga yanzun sati kenan da kawota gidannan bakanan kar itama mushiga hakkinta koh dukda dai ansan lalurace tasa baka zaunaba din," jinjina masa kai yay yana fadin "in sha Allah zanje Allah ya temake" yace "yauwa kuma idan kaje kasameta koh zuwa gobe koh dare idan Allah ya nuna mana ka hadasu guri guda kai musu nasiha kaji kasan sha'anin mata yarima sekayi hakuri ka kauda kanka alokuta da dama kaji, kuma ka kasance mai adalci atsakaninsu duk rintsi duk wiya kaji koh," "in sha Allah Allah yatemakeka za'a kokarta," murmushi yay masa yana fadin "Allah yay maka albarka" da Ameen EHSAAS ya amsa yajuya yana kallon Islam dake tsakiyar iyayensa sunata magana tana murmushi hada ido sukai tamai murmushi shima yamaida mata.

Tareda Mai Martaba suka fice daga sashen itakuma islam su hjy jannat suka rakata dakinta nasama tanajin Fulani na tambayarsu "ba sashenta zata tafiba," hjy azeezat tace "tazuba musu ido kawai ai Islam na nan ba inda zataje wani sashenta anan zata zauna se EHSAAS yagama satin cin amarcinshi tukunna sukuma they'll use that chance su sake gogar da ita," murmushi Fulani tai tana cemusu "ai shikenan tohm sukarata ai yarsu ce," gaba daya mood din Islam canzawa yay murmushin yake kawai takeyi don taji abinda suka fada yanzun sati zeyi adakin wata ba itaba,wani irin bugawa kirjinta yakeyi dakyar take iya faking in anmata magana se uhm ko uhmmm uhmm kawai take iya fada, kamar yadda sukai mata lokacin aurenta haka suka shiga yimata wani irin fitanannan gyara tun ranar da suka dawo Nigeria,kuma nan danan abin yake karbarta saboda jikinta danyene har lokacin.

EHSAAS kuwa tunda ya karasa sashensa wanka ya fesa yashirya cikin hadadden yadi yana daya daga cikin kayayyakin biki da yadinka don burge Mehtav kawai,ya tsaya gaban mirror yana kallon kansa bayan daya kafa hula yay murmushi don yasan batasan yadawo ba he just want to see that surprise akan saman fuskarta, and the most amazing thing da in yatina yakejin kansa kamar a aljanna shine she's now his legal wife,feshe jikinsa yashiga yi da signature perfume dinsa, kafinnan yafito yana daura agogo yadau wayoyinsa yasakko kasa Aman ya tarar yana kallon ball a falon Islam, kallon EHSAAS tundaga sama har kasa ya shigayi cikin mamaki yake fadin "ango kasha kamshin daganan se ina?" harararsa yayi yana fadin "tohm dan sa ido taso karakani" yace "ni rakaka ina din?" Dan bata fuska yayi yana fadin "gurin amarya mana," Aman mikewa yay yana diremai key din motarsa yace "inka ganni alahira kaini akai aikuma nayi iya yina badani za'ai ma aunty Islam irin wannan cin amanar ba," yana karasa fadar haka be jira me EHSAAS zece ba kawai ya nufi kofa yay ficewarsa EHSAAS kwafa yay kafin yace "I don't have your time, gurin matata zantafi" yakarasa yadau makullin motar yafito ba Aman ba dalilinsa har yafice agidan baki daya.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Like Share Comment Vote [15/10, 18:50] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.