EHSAAS

Epilogue

by @fatoumspassion

Aunty Ameerah, jin Mehtav tayi shiru, tace, "Mehtav, are you still there?"

"Eh Aunty, ina jinki."

Tace, "Kodai akwai wata matsalar ne?"

Dan jim tayi kamar bazata fada mata matsalar kiran wayar ba kuma sedai ta soma fada mata a hankali cikin nutsuwa. Aunty Ameerah tana gamawa tace, "Amman dai ke kam any mara wayo! All this while kina cikin wannan halin, kikasa bude baki ki zana masa warning?"

Dan waro ido tayi kamar tana gaban Aunty Ameerah tace, "Warning kuma? Prince ɗin zamma warning?"

Tace, "Eh, ba mijinki bane? Keni, in kina abu sometimes wondering nake, anya kuwa ke tamuce yarinya Baki iya makirci ba balle kirsa atsaye Kike haka gandandan, sekace bishiya! Allah, kinso kibata min rai. Bance kiwa mijinki rashin kunya ba, amman come out openly, ki fadamai bakyajin daɗin abinda yake aikatawa, yadena miki waya daa kishiyarki asashe! Idan kuma baijiba se muma musan matakin da zamu ɗauka akanta da kuma shi."

Tace, "Ayyah, Aunty Ameerah, itafa babu ruwanta. Kullum shi yake kiranta."

Tace, "Dallah, yimin shiru sekace keba mace bace! Idan yakirata, meyasa take dagawa? Munafuncin meyake sawa tadaga idan kince baruwanta? Ai tasan yana tare dake a adalci. Aise, tace masa yakoma gurinki. In ita mutuniyar kirki ce, bata kishin dake dagaske."

"Hmmmm," kawai Mehtav tace, don tasan ko ita yake kira, bazata taba kin hanashi ba. Batasan tasirin Prince a zuciyar mace bane ba, shiyasa take fadar haka. Ta mata uzuri.

Tace, "Aunty, kinga ba neman tashin hankali nake ba. Bata taba koda yimin kallon banza ba, balle bakar magana ta haɗamu. Banason wani abu yazo yashiga tsakaninmu."

Tace, "Bance kiyi rigima ba, amman inason kizama tsayayyiyar mace a gidan aurenki. Mijinki ya zama yana shakkarki. Duk abinda zeyi, yaringa tunawa zakiji daɗi ko bazaki ji ba. Don mun ce kiyi biyayya, kiyi haƙuri. Bamu ce kizauna aringa take miki hakki ba, kinjiko? Maza, inason yau-yau dinnan kifada masa, koda ba kwananki bane. Ki kirashi, kice kinada magana mai mahimmanci, yazo kuyita ta kare."

Tace, "Ai yana nan ma, base na kiraba."

Tace, "Yauwa. Sannan wannan makale, masan ma da kike yi da damuwa da rashin hira dake da baya yi, duk yanada alaka da rashin aikinyi. Toh miji, kullum yana ganinki gida available. Bance zaman gida baida amfani ba, amman yakasance ko kina gidan, bako yaushe kike inda yake ba. Find something to do. Ki kasance out of his reach; they become obsessed with what they can't have all the time. Ita yanzun bakince aikinta take yi ba, bama zama sosai take atareda shi ba."

Jinjina kai Mehtav tayi kamar tana gabanta, tace, "Shiyasa kema nakeso kikama aiki. The moment you get busy, zakiga yadda abubuwa zasu canza. Zega you're no longer always available for him. Duk time ɗin da kuka samu, ze ringa kokari yay making best out of it."

Cikeda gamsuwa take fadin, "In sha Allah, Aunty Ameerah, zanyi magana dashi akan hakan."

Cikeda mutuntawa sukai sallama. Tace, "Agaida mata da yara." Tunda ta ajiye wayar, taji kamar sabuwar hope aka bata a ranta. Tana jin courage yana zuwar mata. Kalaman Aunty Ameerah sun tsaya mata kai tsaye a zuciya: "Idan miji ya sakar maka, kana nan nokewa, gajiya yake, yadena ma bakan." Taji kamar an buɗe wani sabon page na rayuwarta.

Washegari, tun kafin EHSAAS ya tashi daga barci, ta tashi da niyyar yin wani abu daban. Kitchen ta shiga, ta gyara komai da kanta, ta dafa masa special breakfast, avocado toast, fresh juice, da classic Arewa fura milk mix da yafi so. Tana kammalawa, ta gyara kitchen ɗin tsaf, ta shirya abincin a tray ta nufi bedroom dinsu.

Fitowarsa daga wanka kenan, towel ne daure a kugunsa, da ƙaramin towel yana tsane gashinsa da ya ƙara mugun tsayi aciki. Ajiye tray ɗin tai saman center table, ta ƙarasa gurinsa tana murmushi.

"Enyeee, yau 'yanmata na tarigani tashi! Tell me, meye sirrin irin wannan kyau haka, in gani?" Ya faɗa yana kare mata kallo tun daga sama har ƙasa. Sanye take da wasu haɗaddun riga da wando da suka kama jikinta kamar dan ita aka yisu, musamman yanzu da komai na jikinta ya ƙara fitowa.

Kamar ita ta yi kanta, ta shiga jujjuya masa tana giggling.

"Awwwwn gaskiya nasiyi wankan nan," ya faɗa yana ƙarasa wa closet.

Bin bayansa tai, ya buɗe wata drawer yana ciro bundle na dollar notes ya ajiye mata. Haka yake mata saboda yasan bata aiki, kuma bata tambayarsa kudi. Kusan duk sanda yaga dama haka zai bata kudi a matsayin yasiya wankanta, bayan monthly allowance da yake saka mata a account ɗinta. Ita kanta yanzu bata san nawa gareta ba, na banki da wanda yake ajiye mata a gida.

Dauka tai, ta shiga falfala kudin tana faɗin, "Thank you."

Murmushi yayi yana kallonta. Ta taka stool, ta haura saman dressing mirror ɗinsa. Yace, "Careful, kin iya fitina wannan yarinyar Ko, in kika fado fa?"

Murmushi ta fara yi, ta shiga ɗaukar kayan shafarsa tana zaune dare-dare akai, take faɗin, "Ai nasan zaka tareni."

Dariya yayi yace, "Aiko wataran zan bari kifadi kitiku da ƙasa. Idan kikasha kuka bazaki sake ba."

Turo mai baki tayi, ta ɗauko body mist ɗinsa ta shiga shafa mai, tana kallon cikin idanuwansa. Cikin wani salon, sekace body massage take masa. Wani numfashi ya saki kafin ya raba kafafuwanta, ya tsaya a tsakiyarsu, yasa hannayensa ya sakalo wuyanta a hankali yace mata, "Be careful, karki tsokano kawarki tayi barci, indai baso kikeyi kuma ai sacking dina agurin aikina."

Giggling Mehtav tayi, cikin kunnensa take faɗin, "Who'll sack the boss himself?"

Tana jin sautin dariyarsa a wuyanta sanda tayi ƙasa da hannayenta cikin wani fitinannen salon, tana shafa mai cikinsa har zuwa wurin mararsa. Cikin kunne ya rada mata, "Yau da full energy kika tashi, da alama, Amor."

Sai a lokacin ta ɗauke hannayenta ajikinsa tana ƙoƙarin raba kanta dashi tana dariya. Kankameta yayi yana faɗin, "Kinma isa? You must finish what you start."

Yatsanta tasa cikin bakinta tana narkemai irin she's clueless of what she's doing ɗinnan, tace, "You have to go to work remember, kar ai sacking boss da kansa."

Murmushi yayi jin yadda take mimicking voice ɗinsa, yace, "Oya feed me first, sai atafi aiki with full energy."

Lips ɗinsa takama, ta shiga kissing gently, yana kallon idanuwanta yadda ta lumshe su, enjoying every bit of what she's doing. She looks so cute and innocent.

Kamota yayi gaba ɗayanta, ta daure kafafuwanta a saman jikinsa, ya shiga tafiya da ita yana kissing dinta back very slowly and gently, kamar yana taɓa the most delicate flower in the world.

Har suka ƙarasa saman gado, ya kwanta da ita yana kallonta hungrily. Hannayenta ta miƙa masa alamar yazo. Dage mata gira ɗaya yayi kafin ya haura saman gadon, ya shiga cire mata jeans ɗin jikinta, cikin rada yake faɗin, "I love how ready you always are for me," yana cusa fingers dinsa ciki.

Bugun ƙofar da sukaji ne ya dakatar da su daga abinda sukeyi. Mehtav ta dan mike zaune tana maida jeans ɗinta. Ganin ya lumshe ido, ya kifa kansa a gadon yasa abin ma yabata dariya. Tasan kuma duk wanda ke buga musu ƙofar nan, yau wuni zeyi yana mita akanshi.

"Who's there?" ta tambaya tana karasawa bakin ƙofa.

"Yah Mehtav, nice," tajiyo muryar Abeey tana faɗa.

A hankali ta buɗe ƙofar, amma ba dukaba ta fito, tana tambayar, "Fatan dai komai lafiya?"

Tace, "Ni bazanci abincin da masu aikinnan suka dafa ba. Nasan kin yiwa Prince girki, can I get some?"

Dan sighing tai kafin tace, "Yes, akwai a kitchen. Shine har se kinzo kin tambayeni?"

Murmushi Abeey tayi tana faɗin, "Ai ba kyau taba kayan wani seka tambayeshi."

Bude baki Mehtav tayi jin wani sabon gulmar, tace, "Okay, dacan tambayana kike in zaki ɗauka kenan?"

Tace, "Da kayan babanmune. Wannan kuma na mijinki ne. Is not right."

Tace, "Oh, su Abeey an fara hankali. Tohm ai shikenan, bari nasallameshi, yanzu zanfito."

Abeey kitchen ta nufa tana faɗin, "Don't worry, take your time."

Dakin ta koma, waya ta tarar dashi yana yi da Aman. Da alama akan aiki ne. Hakan ne yasa taga ya mike bayan sunyi sallama, yace mata, "Let me quickly get ready, I have to be there today."

Jinjina masa kai tayi kawai. Bandaki taga ya koma, ya sake wanka, ya fito da bathrobe, wannan karon a gaggauce ta taimaka masa yashirya. Suka fito, sai a lokacin ya lura da breakfast ɗin da ta kawo mai.

Zama yayi saman carpet, ta kawo serving dinsa.

Cike da nutsuwa yayi smiling yana faɗin, "Thank you baby, I love it. Hope baki wahalar min da kanki ba?"

Jinjina masa kai tayi tana faɗin, "Just felt like doing something nice for you."

Yace, "I appreciate it, Mehtav." Sai ya ɗan tsaya yana dubanta sosai, yace, "You've been quiet lately. Is everything okay?"

Shiru tayi na ƴan seconds kafin tace, "I'm fine. I was just thinking… maybe I should start something small, like my own food business."

Dan dage gira yayi cikin mamakin jin kalmar daga bakinta, yace, "Food business?"

Tace, "Yes. Not something too big for now, just a proper kitchen, maybe with a few chefs… with a small restaurant that will look like a culinary house. Something that reflects Nigerian culture da luxury style dinsu."

Wani irin murmushi yayi cikeda jin daɗi da farin ciki, yace, "That's interesting, Amor. That's the kind of thing I've been hoping you'd say. You have so much potential, you just need to channel it."

Ta murmusa kaɗan tace, "Aunty Ameerah ce ta bani idea ɗin jiya… and I've been thinking about it all night."

Yace, "She gave you good advice. Tell me what you'll need, and I'll make sure it's done. Even if you want to travel to learn from professionals, you can."

Tace, "Really?"

Yace, "Of course. I'll personally talk to Aman and have him link you with a consultant. We can get the space, interior, branding… everything you want."

Wani daɗi ne ya cika zuciyarta jin dagaske itama zata iya buɗe business ɗinta na kanta, and she's loving the idea of owning something herself.

A hankali tace, "Thank you, Mi Amor." cikin farin ciki ta lafe a gefensa yana cin breakfast ɗinsa.

Tace, "Uhmm, kuma akwai wani abu ma."

"Tell me, Amor. Ina sauraronki, don't hesitate please."

Mikewa tayi a jikinsa, tana kasa haɗa ido da shi, tace, "Daman, daman I've been wanting to tell you kuma kullum sai bana samun opportunity."

Dan dago kai yayi yana focusing all his attention akanta, yakama hannunta yace, "What's on your mind, tawan? Just tell me."

Ta ɗan tsaya shiru kafin ta fara, "Na dade ina son in fada maka amma kullum bana samun strength ɗin yin hakan. Amma yau ina so ka saurare ni, please don't misinterpret abinda zanje."

Gyada kai yayi cikin nutsuwa yace, "I'm listening."

Ta ɗan haɗe hannunta cikin nasa tace, "Mi Amor, na lura duk lokacin da nake tare da kai, especially when I'm cooking or when we're spending time together, you always end up calling Islam. Ko wani lokaci, kana cewa just to check on her project ko reviewing da kake mata. And I'm not saying this saboda kishi ko wani abu, I don't have any problem with your wife, kasani I respect her a lot. But it makes me feel invisible somehow, like… I don't matter enough. Kullum in kana tare dani, you don't feel whole sai kayi involving dinta."

Shiru yayi yana kallonta, kalmominta na shiga kwakwalwarsa yana ƙoƙarin analyzing abubuwan da yake yi ɗin.

Ta cigaba, "Ban ce kada ka kira ta ba, amma irin yadda kake yi koda yaushe, har lokacin da nake tare da kai, yana bani feeling kamar ba ni kake tare da ita ba. Har wani lokaci idan ina magana, sai ka ɗau waya ka dinga murmushi… sometimes I just stop talking. I feel small, EHSAAS, like I'm just an intruder acikin rayuwarku, kamar wata outsider."

Wani shiru yayi, ya jingina da kujera yana kallonta.

"Mehtav," ya faɗa a hankali yana jawota jikinsa, "ban taɓa sanin kina jin hakan ba, ban taɓa yi da niyyar sa ki jin inferior ba. Islam tana da projects da nake supervising, and I got carried away. Maybe I didn't realize how it was affecting you. I'm sorry, kinji, 'yanmata na."

Ta ɗan sauke numfashi tana kallon hannuwansu dake sarkafe jikin na juna. "I'm not angry, just hurt. I just want you to see me too. Nima inason ka ringa hira dani ako yaushe in kana dakina. Nasan I don't understand your world the way Islam does, but I promise I'll try and adjust, koda ban fahimci komai ba."

Shiru yayi na ƴan seconds, sannan ya tallafo chin dinta yace, "Kin san me?"

Lumshe ido tayi tana girgiza kai alamar a'a.

"You're not invisible, Mehtav. You're the calm in the noise I face every day. Maybe I've been too busy proving to everyone that I can balance both worlds, har na manta da kema kina buƙatar attention ɗina in person."

Ta ɗan yi murmushi mai rauni tace, "Attention da affection ba abu ɗaya bane, EHSAAS."

Ya kalle ta da idanu masu taushi sosai, "Toh yanzu kina da full permission ki koya min difference ɗin. Zan saurare ki."

Tayi dariya kaɗan tana girgiza kai, "I'm serious fa."

Yace, "Ni ma I'm serious. Starting from tonight, no calls, no distractions. Just you and me."

Sai ya mike, ya kamo hannunta, yajata yana ɗaukar jakar laptop dinsa yace, "Let's cook together tonight," yana murmushi. "You'll teach me something I can never learn from Islam, she's book smart while you are kitchen smart kinga anyi balancing,muyi karatu tare da ita ke kuma muyi girki tare dake"

Ta kalle shi tana dariya a hankali, tana jin zuciyarta tana sanyi tace, "Anya kuwa zaka iya girkin nan?"

Jinjina kai yayi yana faɗin, "Of course, ba ga 'yanmata na ba? Ai zata koya min, saboda itace best chef da na sani in the world."

Dariya tayi, har da rufe fuska. Yarungumeta ajikinsa yana shafa bayanta a hankali, ya cigaba da bata haƙuri yana faɗa mata kalmomi masu daɗi da suka wanke mata duk wani kunci da damuwar abinda ya aikata daga cikin ranta.

Kamar yadda ya yi alkawari, tun daga ranar bai sake kiran Islam yana tare da ita ba. Abin har mamaki yake bata, domin dama ita Islam ba ita ce take kiransa ba, shi ne yake kiranta. Duk da ta kan kamashi yana chatting, amma da ya fahimci ta lura yake, sai ya ajiye ya basar, ta lura sosai yadda yarage shishshigema kowacce daga cikinsu agaban kowacce koda haduwa akai abangaren Fulani zakaga yaja gefe shida Fulani lo Jr suna hira karshe sedai itada Islam din suma suyi nasu hirar wanda yakawo karin fahimtar juna atsakaninsu sosai.

Tafiyar Islam Oxford ta kara kawo wata irin muguwar shakuwa a tsakaninsu, domin ita ta fara tafiya kafin ya bita wurin Fulani Hajar ta bar Jr, wanda wata iriyar shakuwa ta shiga tsakaninsa da Mehtav. Kullum suna tare, bacci ne kadai yake rabasu.

EHSAAS kam, kullum yana manne da ita. Ko kitchen zata shiga yanzu, tare suke shiga. Duk wasu basic abubuwa na girki yanzu ya fara iyawa, domin da gaske yake sa kansa. Ya fara koyar girki sosai. Ita abin har dariya yake bata, amma da yake yana da sharp brain, nan da nan yake dauke komai.

Kamar yadda EHSAAS ya yi wa Mehtav alkawari, cikin dan kankanin lokaci ta bude babban gidan abincinta mai suna "Taste of Naija(Authentic Nigerian Cuisine in the Heart of Nuristan)."

Restaurant ɗin ya kasance ba kamar kowanne restaurant bane a Nuristan. The setting itself was a blend of home and royalty, handcrafted wooden carvings daga Nigeria aka kawo mata, sun haɗu da golden chandeliers by Baccarat, Hermès leather dining chairs, da Versace tableware collection. Yan Nuristan sunsha mamakin irin wannan combination, traditional elegance with luxury finesse.

Abincin da ake siyarwa awrurin na Nigeria ne kawai, na kowace kabila. Akwai Hausa tuwon shinkafa da miyan taushe, dambu, gurasa, masa da miya, sinasir, awara da dai sauransu, Yoruba jollof rice and asun,moi moi and so on, Igbo oha soup da fufu, har da abinciccikan kabilun Tiv, Ebira, Igala, da Kanuri cuisines, duk ana siyarwa. Kitchen ɗin an cika shi da state of the art equipment from KitchenAid, SMEG, and La Cornue Château ranges.

Catering section ɗin suna da signature juices and mocktails daga fresh tropical fruits, kuma pastries daga Maison Kayser recipes tare da Nigerian fusion sweets.

Kafin kace me, Taste of Naija ya zama trending topic a Nuristan. Kowane influential person sai ka ji yana magana akan gidan abincin saboda kwarewarsu da yadda suke tafiyar da komai cikin royalty da tsarance. Celebrities daga ko ina suna zuwa su ci abinci, sannan ana samun online orders daga ko ina, ta UberEats Nuristan, Glovo, da private royal orders.

Harta Mai Martaba, duk ranar Monday da Thursday idan yayi azumi, a Taste of Naija ake masa order kayan shan ruwa na musamman kamarsu royal hibiscus juice, tiger nut smoothie, da grilled honey suya platter. Duk da Mehtav tayi offering ta rika yimai agida, sai yace a'a, "Patronizing dinki nake son yi. Na gidan abincin nakeso."

Paa, ganin business ɗinta ya kara kankama, yasa ya kara mata jari akan wanda EHSAAS ya bata. A cikin kankanin lokaci, ta buɗe branch na biyu a Royal District, wanda ya fi na farko girma. Wannan branch ɗin yana da Michelin-inspired fine dining section, Chef's table experience, da private royal lounge inda manyan baki ke cin abinci.

Abubuwa kullum sai kara cigaba suke yi. Taste of Naija ta zama alama ta al'adun Najeriya a ƙasashen waje, tana kawo haɗin kai tsakanin heritage da luxury, kuma Mehtav ta zama daya daga cikin most celebrated entrepreneurs a Nuristan da beyond.

Seda Islam tai wata biyu tukunna EHSAAS ya bita Oxford. Ba ƙaramin kewarsa Mehtav ta ji ba, saboda muguwar shakuwa da sabon da suka yi a zamans tare, don alokutan mantawa ma takeyi tanada kishiya haka zalika itama Islam din saboda kowaccensu tanada abinda yake dauke mata hankali musamman yanzun ita Islam, she's a very busy woman, kwata-kwata azahiri gani zakai kamar ma mijin ne dameta ba. Karatunta ta saka a gaba da aikinta, domin Home of Hope shima kullum bunkasa yake yana cigaba. Duk da Aman ke mata managing rabin aikin kafin yabar NURISTAN, tana dawowa lokaci zuwa lokaci tana taimaka masa personally.

Ita da EHSAAS karatunsu suke, suna gina wata irin rayuwa mai cikeda yadda da shakuwa da juna. Kuma yanzu irin wannan zafin kishin da suke ji daga ita har Mehtav sun daina jin sosai, saidai dan abinda ba'a rasa ba. Musamman yanzu da suka nisa da juna, se suyi wata da watanni basu ga junaba.

Kullum Islam tana ƙasashen waje, gara shima yakan dan zauna saboda Mehtav, musamman da ta samu juna biyu. Farinciki gurinsa ba a magana, kullum cikin tattalinta yake, shi da Fulani Hajar. Nannan suke da ita, hatta da Islam da batanan, kulawa take da ita sosai domin takan kirata lokaci zuwa lokaci ta ji ya jikin nata.

Seda ta yi wata tara cif-cif sannan ta haifi 'ya'yanta, santala-santala yan biyu masu mugun kama da Jr, kamar kara aka yanka.

Mai Martaba kamar ya lashe yaran haka yake ji, domin shi burinsa yaga EHSAAS yatara masa zuria'a dayawa, wanda shi Allah be bashi. Haka zalika Fulani Hajar ma ta cika da murna, aka cika gida da annashuwa ga kyaututtuka iri iri akai decorating gidan da white lilies da orchids da ake kawowa musu na musamman daga Dubai da Doha.

maternity room aka warema aka mayar mata da shi kamar wani royal suite, dakin cike yake da Hermès baby blankets, Burberry crib bedding, Dior Baby bottles, da custom-made gold cot da aka yi da sunan yaran akan frame ɗin. Fulani Hajar ta tabbatar komai na ciki da wajen dakin baby ɗin yana da sophistication, har da Avent sterilizer, Mima Xari strollers, da Chanel mother's kit.

Abeey ta gudo Nuristan da zama tun zuwa sunan yaran da suka ci suna Ahmad da Muhammad. Ita da Inna suka zo dasu Aunty Ameerah, dasu Falmata, duk Paa ne ya biya musu kudin jirgi, harda Sarah da Baban Sarah.

Sosai Mehtav taji daɗin ganin 'yan uwanta, saboda tun da ta yi aure sau daya ta taba zuwa Nigeria kafin ta haihu.

Islam ma ta dawo, da ita aka yi shagalin sunan Mehtav, wani irin hadin kai yasake kulluwa atsakaninsu bazadai kace musu friends ba amman yadda suke treating eachother da respect kamar wasu surukan juna . Jr dai ya koma ɗan gidan Fulani da Mai Martaba, don har ya shiga makaranta, yana hannunta, sun bar masu shi.

An yi naming ceremony ɗin cikin cikakken alatu, Versace silk drapes, gold baby throne, da custom fragrance blend by Maison Francis Kurkdjian da aka fesa ko'ina a dakin taro. Gidan ya cika da manyan baki, sarakuna, da royal guests daga Abuja, Doha, da Paris.

EHSAAS ya saka designer suit daga Tom Ford, Islam ta saka Elie Saab couture, ita kuma Mehtav cikin custom Zuhair Murad maternity gown ta yi kyau kamar kasace ia gudu da yan fararen yaranta masu kama da yayansu da babansu sak sak. Yaran sunsha kyautuka da dama daga yan uwa da abokan arziki don daki guda Mehtav tai na gifts din Ahmad da Muhammad, haka zalika duk wanda yazo shima baya tafiya hannu rabbana suntanadi souvenirs na ban mamaki wanda Fulani hajar ce tashirya komai da kanta kowa dai dayazo ya tafi da labarin Nuristan Royal Twins Naming Ceremony,saboda wani biki wanda ak jima ba'a ga irinsa ba saboda yadda abin ya hadu kuma yatsaru da yadda zuriar EHSAAS suka nuna soyayyarsu ga juna da hadin kai da zaman lafiyan dasuke ciki wasuma har mamaki sukeyi idan akace Islam da Mehtav kishiyoyine saboda yadda suke interacting da eachother wannan Kenan.

Daga bangaren islam kuwa ji take da gayu, kana kallonta kasan ilimi da wayewa sun ratsa ta gaba ɗaya. Wata irin narkakkiyar soyayya EHSAAS yake mata, wacce bata iya boyuwa a ko ina suke. Ko magana take, idan ya fara kallonta, kamar zai hadiyeta haka yake ji.

Akwana a tashi har lokacin gama karatun Islam yayi takammala masters degree dinta afannin World Literature, haka suka je har Oxford University harda Mai Martaba aka tayata murna. Tare suka dawo Nuristan baki ɗaya.

Alokacinne kuma ta mai da cikakken attention dinta gaba ɗaya a Home of Hope Foundation, wanda yanzu ya zama babban ginshiƙi na taimakon mata da yara a duniya.

Kullum tana can, bata cika zama a office ɗinta ba, sai dai idan ka shiga Home of Hope, kaganta a tsakiyar yara tana rarraba musu littattafai, ko tana feeding marasa wayon da kanta, ko ta zauna tana karanta musu story books. Spending time da yaran ba ƙaramin farin ciki yake kawo mata ba.

King Nashwan ganin yadda kullum ake kawo mata yara da mata daga sassan Nuristan daban-daban yasa ya shiga gina mata babban gini bayan palace, mai ɗauke da modern classrooms, STEM labs, Islamiyya halls, da boarding hostels na yara maza da mata, duk daban-daban.

Akwana a tashi, Home of Hope ya zama ɗaya daga cikin manyan NGO organizations da ke da tasiri a duniya. A yanzu tana cikin jerin Top 100 Most Influential Women in Global Philanthropy bisa ga Forbes da UN Women Recognition Board.

Tana da haɗin kai kai tsaye da UNICEF, UNESCO, UN Women, Save the Children, da World Literacy Foundation. Sau da dama tana halartar Global Summits kamar World Education Forum (WEF) a Paris, Women in Leadership Conference a Geneva, da UN General Assembly Special Session on Women Empowerment a New York.

Tana kuma cikin board of advisors na Bill & Melinda Gates Foundation, tare da jagorantar panel discussions kan Sustainable Child Education a Dubai Expo, Qatar Global Aid Summit, da African Women CEOs Network da ake yi a Cape Town.

Bayan haka, Islam ta zama abin alfahari a duniya baki daya. Jaridun duniya suna kiranta da sabuwar lakabi, "The Golden Heart of Nuristan", saboda yadda take haɗa royalty da humanitarian service cikin nutsuwa da ilimi.

King Nashwan da mahaifinta Abraham Zion wanda akafi sani da Alhaji Ibrahim ayanzun duk sun bata goyon baya da cikakken tallafi da shawara idan ta taso sukan bata aduk sanda take bukata.

A gefe guda kuma, soyayyarta da mijinta EHSAAS kullum ƙara ƙarfi takeyi. Duk da cunkoson jadawalin tarurruka da tafiyoyi datake dasu, tana tabbatarwa cewa soyayyarsu bata raguwa. Yakan biyota wasu lokutan cikin private jet din Mai Martaba zuwa kasashen da take seminar, ko ya haɗu da ita a Zurich ko Istanbul don suyi weekend getaway kafin ta koma taron nata.

Ko a gidansu, sun kafa tsarin Royal Family Friday Dinners, inda kowa yake barin komai domin su haɗu su ci abinci tare da iyalin baki daya, Wannan tsarin ne yake daɗa haɗa kansu da wanzar da zaman lafiya atsakaninsu

A yanzu Islam ta zama wata irin fitacciyar mace, a symbol of grace, education, and compassion. Ko a duniya, idan ana magana akan matan da ake damawa da su, ana lissafa Princess Islam of Nuristan, Queen Rania of Jordan, Michelle Obama, da Melinda Gates a wuri guda.

Saboda taimako da ƙarin ƙarfin gwiwa da take samu daga iyayenta, surukanta, da mijinta baki ɗaya, ganin abin ya karɓu sosai yasa ta yi deciding ta fara Feeding Program ɗinta, kuma ba ta ƙarƙashin NGO ba. Ta tsara plan ɗin sosai; tana son ta riƙa feeding mutane dubu a duk ranar Juma'a a duniya, outside various masallatan da suke dasu a Nuristan.

Tana kira shirin da "Royal Kindness Friday Initiative" (RKFI) A karkashin wannan shiri, kowace Juma'a, motocin sukan fita daga babban masarauta, su raba abinci mai rai da lafiya da ruwa mai kyau, ga talakawa a kusa da masallatai. Abraham Zion ne ya ɗau nauyin rabin kuɗin shirin, itama ta ɗau rabin, watarana Suna hira da EHSAAS take tambayarsa wa zasu riƙa bawa aikin, yay musu abinci mai kyau, mai rai da lafiya. EHSAAS yana dariya yace, "Intabama Mehtav zata iya, ai that's a good idea, kinga, hanyace tasake bunƙasa mata kasuwancinta itama."

A daren ranar suka zauna da Mehtav sosai suna maganar. Tai farin ciki sosai. Ta ce ma Islam, "Wannan aikin ladan ai ba ma se sun biya ta ba.zata ɗau nauyin yi kawai, su dai aikinsu su yi providing mata da resource base, amma base sun biya kuɗin services ɗinba."

Islam tace, "A'a, tafison ta biya ta ai aikinta ne, kar taga don ita 'tagida' ce. Bai kamata ba." Mehtav ta ce, "Bazata karɓa ba." Haka suka yi haɗin gwiwa gurin aikin taimakon nan.

Yanzu, ko ina ka je a Nuristan kafin ka ji an ce Prince EHSAAS, an riga da an ce Princess Islam da Mehtav, su ne fuskar alheri. Shi kansa Mai Martaba yana alfahari da surukan nasa; gashi suna balancing tsakanin zama wives da career women.

Musamman Islam, yanzu zaka ganta a kasar anjima, ta bar gida saboda halartar tarurrukan kungiyoyin tallafawa mata da kananan yara daban-daban da take yi.

Lokacin da Mehtav ta sake samun ciki bayan haihuwar Ahmad da Muhammad, ita Islam shiru, amma abin baya damunta. Yanzu EHSAAS Jr shekararsa biyar a duniya; su Ahmad da Muhammad kuma shekaru uku-uku. Yaran mugun haɗin kai ne da su, duk inda zaka gansu suna tare.

Sojojin Mai Martaba kenan. Kullum yana tare dasu, musamman Jr, da ya zama kamar lamba biyar dinsa.

Prince Aman daga bangarensa, da ƙyar EHSAAS ya lallabashi ya koma Turkey. Kamar yadda ake tsammani, yana komawa babansa ya nada shi Crown Prince a kingdom dinsu.

Wata irin muguwar shakuwa ce tsakaninsa da Abeey. Ko da ya bar Nuristan, kullum suna tare a waya. Ayanzu tana SS3, an fara girma, an zama 'yan mata. She's now 17. Wata irin narkakkiyar soyayya suke batare da sanin kowa ba. Shi kansa Aman bai san lokacin da ya faɗa tarkon son Abeey ba, don tun tana ƙarama take mugun burge shi. Idonta a buɗe yake sosai, kuma awaye take ga wani girma da ta ke yi lokaci guda.

Mehtav idan ta kalleta, wani lokacin har mamakin girmanta take yi, ga tsayin kafa yanzu ma ta fita tsayi sai dai ta nuna mata jiki. Tana jin daɗin zama da ita sosai, don ta karfii da yaji takarbeta daga hannun Paa.

Yanzu daga shi sai amaryarsa Dr. Kafayat, wacce itama Abeey ce ta daidaita tsakaninsu har suka shiga suka fita. Ita da EHSAAS suka saka Paa ya aure ta.

Da aka yi auren, Inna ta koma Maiduguri. Daman ta ce zaman yaran take yi, tohm yanzu Mehtav tayi aure, Abeey ta ki zaman Nigeria, tana gurinta a Nuristan. Zaman wa zatayi? Ba yadda Paa bai yi da ita ba, tai tafiyarta.

Yanzu in kaga Abeey a Nigeria, tohm tareda Mehtav suka zo. An yi hutu , duk shekara suna zuwa su ziyarci mahaifinsu tare da dangi, wasu lokutan ma sau biyu a shekara. Indai suka zo, da EHSAAS da yaran duka da Islam Masarauta, se sun fara biyowa Abuja, an gaishesa da Paa, an kwana kafinnan, sannan atafi can Mai Dugurin.

Ko gidansu Islam za'a kai Jr tare da Ahmad da Muhammad ake tafiya, don yaran ba'a raba su, mugun haɗin kai ne dasu, ga son juna. Sai dai fa maganar kiriniya, ba'a cewa komai 😅.

Abraham (Ibrahim) zai ce, "A kawo su." Amma ana kaisu gidan, suke maida masa gidan upside down. In suka fara kiriniya, har Jr din sai ya ɗauko bulala tukunna suke nutsuwa.

Daman ita Veronica (Fatima) ai sun maida ita kakarsu. Musamman ake cewa, "Aje a tsokano ta." Sai ka ji ta kira Islam tana cewa, "Ai tazo ta ɗauke yayanta, ita bata haifa ba, karsu samata hawan jini."

Dariya Islam take, in tana ce mata haka. Ta ce, "Ai mommy, kunefa kuka kira a kawo muku sojojin Mai Martaba! Yarannan ba mai iya da su sai shi da Mehtav, nikaina bana iya dealing dasu."

Haka Veronica zata kira Mehtav, itama ta yi dariya, ta karɓi waya ta daddaka musu tsawa, sai su shiga taitayinsu, don sun fi shakkarta akan Islam, dukkansu har Jr din da yake yafi zama dasu.

Idan kiriniya za'a yi, idan itace agurin, sai ku ji sun ce, "Ai Ummi ce, a wurin duka takeyi!" Amma idan suka kyalla ido suka ga Islam ce, sai su ce, "Ai Momma bata duka, let's go."

Kuma kullum kamar batir ake samunsu kiriniyarsu karuwa takeyi. Duk wata maid da aka daura mata alhakin kula dasu guduwa take, bata iya.

Mehtav ce kawai take iya balancing aikinta da kula dasu. Wani lokacin EHSAAS ko Abeey idan Abeey batada school, tana gidan, tsit! Zakaji komai shiru, saboda bata musu da wasa.

In ta kama yaran, moresu take, musamman in ta faki idon EHSAAS, don duk zumuncin da suke da Abeey, duk sanda yakamata ta dakarmaisu sai sunyi faɗa.

Itakam Abeey ko a jikinta. Tace, "Ai duk shine yake lalata su. Yara sd kiriniya basajin magana, kuma yace baza'a taba su ba!" tace, "Haba yah Mehtav kiringa fada masa gaskiya fa. Yarannan dai ba da gwal akayisu ba." Tadora da, "Jiya fa dan marin Ahmad yaga nayi shine yau da safe damuka haɗu, nace ze saukeni a makaranta, yay tafiyarsa ya barni. Ainasan haushi yaji, kuma wallahi bazan fasa dukan yaro in yamin ba daidai ba." Mehtav ta ce, "Itaku ni, ina ruwana?"

Seda sukaga Mehtav ta sake haifa musu kanwa tukunna suka fara dan nutsuwa, musamman Jr. Wani lokacin har bragging yake ma twins ɗin, shi fa yanzu kannenshi uku ne, ba sa'an su bane ba. Kusan shi ya zama dan renon Aisha, domin yarinyar kyakkyawa ce tubarkallah,ta ɗauko kamannin Fulani Hajar saksak. Duk inda Mehtav take, zaka ga Jr a makale da ita, sanadin Aisha da suke cemata Noorur Rahma.

Harta da Islam tafi shiri da Aisha akan mazan, saboda nutsuwa ce da ita bata da hayaniya kwata-kwata. Seda Aisha ta shekara biyu sannan Islam ta sake samun ciki tare da Mehtav itama, don taji ma da yaye Aisha.

Farinciki gurin EHSAAS kamar me, domin sosai ya saka damuwar rashin sake ɗaukar cikin Islam a ransa, amma bai taɓa fitowa ya fada mata ba, haka zalika Fulani. Amman ita kwata-kwata bata damu ba, tasan lokaci ne, kuma gashi da yayi Allah ya bata. Domin tana ganin yaran Mehtav, samsam basa banbantata da mamansu. Indai tana gari, sun ma fi son su zauna inda take, saboda ita bata duka kamar Mehtav.

Ita kuma, ko sunyi rashin jima, seta saka su a ɗaki, ta fara musu nasiha kamar wasu manya. Suyi shiru kamar suna ɗauka, amma suna fita sai sun sake.

Idan EHSAAS yazo, yatarar da ita ta sa su a gaba tana nasiha, dariya yake mata, yana cewa: "Wato baby, you'll forever be a baby. Yarannan fa jinki kawai sukeyi."

Tace, "Tohm sire, me kake so in musu? Kana ganin sabon vase ɗinnan da Princess Jalila ta kawomin bayan sun dawo da mijinta daga Paris, sun fasa. Ga painting ɗin da nazo dashi daga Rome, shima sun lalata da colours."

Dariya yashiga yi yana karasawa closet, yana cire suit dinsa, yace: "Ba komai ai, Mommo dinsu is a rich pikin now, seta biya akawo mata sababbi."

Girgiza kai kawai tai tana murmushi. Ya tambayeta lokacin da likita yace za'a iya scanning, ta sanar masa sai zuwa next week.

Dayake kusan weeks ɗin cikin nasu daya da Mehtav, tare suke zuwa antenatal a asibitin cikin palace ɗin. Tunda cikin Islam yayi six months take mugun shan wahalar laulayi na tashin hankali, ga rashin lafiya.

Zuwansu na ƙarshe asibitin harda EHSAAS, domin ya ajiye duk wasu ayyuka dake gabansa don kula da ita musamman, ya lura cikin yazo mata a wahale ne. Likitan ne yace masa gaskiya, haihuwar Islam zata iya zuwa da complications in basuyi wasa ba. Don haka, zai musu recommending su nemi Dr. Mi'ad Talba, ƙwararriyar consultant obstetrician ce, wacce yanzu take daga cikin likitocin da WHO ke kira "Miracle Hands of Africa."

Zata iya mata wani abu na taimako don ceton rayuwarta da abinda yake ciki. EHSAAS yace ma doctor din ya haɗasu da ita, "Shi konawane, he's ready to pay, a kawo ta Nuristan ta kula da Islam."

Doctor ɗin cikeda girmamawa yace: "Ai money is not the problem. Yarinyar schedule ne da ita. Bata zama a kasa daya itada mijinta kwata-kwata saboda yanayin aikinsa. Tana aiki a asibitoci daban-daban, kuma mijinta ba zai barta tazo wata kasa daban da sunan aiki batareda shi ba."

"Don haka yanzu sedai anemi contact dinta a tambayeta a wace kasa take, sedai su subita."

EHSAAS yakalli Islam, wacce idonta ke lumshe tana sauraron abinda ake cewa, don sosai ta gama cire rai da rayuwa, ita kadai tasan abinda take ji a jikinta.

EHSAAS yace: "Itada mijinta duka, I can sponsor them suzo nan. Nidai indai zasu taimaka ma Islam, banida matsala. Kasan condition dinta, do you think it's healthy ta riƙa bin likita kasa-kasa?"

Girgiza kai doctor yayi, yace: "I won't recommend that. Amma ku baku da wanda kuka sani daya santa haka don reaching dinta. Ba wai kudi bane.matsalar saboda mijinta naji ance don ne nagaske. Sanayya zata iya muku abinda kudi baze muku ba ko mulki ayanzu, don an ce mijinta nada mugun zafin kai fa."

Mehtav tayi shiru kafin tace: "Mi'ad Talba... kamar naso nasanta. Yar Nigeria ce?"

Da sauri doctor yace: "Kwarai ma kuwa. Haifaffiyar birnin Kaduna, amma a Kano ta tashi."

Tace: "Ba ita nasani ba, kanwarta nasani. Ina ganin dai suna hotuna tare, tana tagging dinta a Instagram. Amma banaji blood sisters ne, don ita surname dinta Aragon ne ba Talba ba."

Doctor yace: "You must be talking about Nicky Aragon, right?"

Tace: "Tabbas. Yanzun yawanci itace takemin designing kayayyaki, mutuniyar Abeey ce." Ta kalli EHSAAS tana fada masa.

Doctor yace: "Kanwarta ce, uwarsu daya. Ai kuma Nicky ita kadaice zata iya fada mana direct location da zamu samu Mi'ad. Kitemaka a haɗamu da ita."

Da sauri Mehtav ta ɗau wayarta tana fadin: "Right away."

Fita tayi daga cikin office din, ta shiga kiran number Nikhat (Nicky Aragon). Amma as expected, da wuya ake samunta a waya, sai kai ta sameka ko ka ajiye mata message. Message ta ajiye mata, ta mata explaining halin da Islam din ke ciki, tace mata yar uwarta ce, da yadda suke bukatar taimakon Mi'ad cikin gaggawa.

Da ta dawo, ta sanar musu bata sameta ba, amma ta tura mata message. Ahaka suka hakura suka dawo gida. Da daddare, Nicky tai getting back to Mehtav wajan can dare. Aikuwa takira EHSAAS ta sanar masa cewa zata yi magana da Dr. Mi'ad din zuwa safiya, zata ji daga gareta. Washegari kuwa, sega video call din Nicky suna tare ma da Mehtav din.

Tace, "Ahadata da mara lafiyar," aka kaima Islam tambayoyi. Dr. Mi'ad tashiga yimata tambayoyi akan irin abubuwan da take ji. Islam ta fara sanar mata ahankali, nan da nan Mi'ad ta gane me yake damunta.

Kallon Mehtav tai tace mata, "Yanzu a wace kasa suke?" Mehtav tace, "NURISTAN." Dr. Mi'ad tace, "Zata iya zuwa Doha, tana aiki tare da St Mary Royal Hospital. Mijinta yana da aiki mai muhimmanci da yake gudanarwa a Doha. Da ba don hakan ba, da zata iya zuwa NURISTAN din ma."

EHSAAS ne ya tambayeta, "Ba matsala in ta hau jirgi ahalin datake ciki?" Dr. Mi'ad tace, "Babu matsala in sha Allah, but she must rest well."

Washegari suka wuce Doha, su uku, Islam, EHSAAS da Fulani Hajar, don likita yace Mehtav ta zauna saboda yawan stress is not good for her health itama.

Acan Doha din suka samu Dr. Mi'ad Talba, inda ta karbesu cikin mutunci da girmama juna. Aka kwantar da Islam, aka bata bed rest. Mi'ad ta tabbatar da cewa condition dinta Placenta Previa Type II ne, wato inda placenta ke blocking partial pathway din haihuwa. Wannan ne ke sa bleeding da tashin hankali a cikin wata takwas zuwa tara.

Dr. Mi'ad ta saka Islam a special ward, tana bata kulawa na continuous monitoring. Kullum dakanta take duba fetal movement da BP dinta, saboda risk din hypertension da anemia da aka gano zata iya samu inba'a kula anan gama. Shawara ta bama EHSAAS ya barta har lokacin haihuwarta don akwai complications da ka iya zuwa duk kalar maganin da za'ayi.

Amma EHSAAS ya dage, ya zauna tare da Islam a Doha, duk yadda ta ke lallabarsa ya koma NURISTAN, yaki. Fulani Hajar ma tana tare da ita, tana kula da ita kamar yadda uwa ke kulawa da 'ya.

Mai Martaba ganin haka, yay waya Nigeria aka siyawa Inna ticket ta taho NURISTAN domin kula da Mehtav, wacce bata nuna damuwa ko kadan ba akan tafiyar da EHSAAS yay gurin Islam. Don itama macece, kuma ta fahimci Islam tafi bukatarsa akanta a wannan lokacin.

Lokacin da cikinsu yacika wata tara, Mehtav ce tafara haihuwar santaleliyar yarinya ta budurwa wacce taci suna Nadira ma'anar "rare and precious gem". Sosai kowa yay farinciki da samun karuwa, amma kuma dukkaninsu sun shiga damuwa saboda due date din farko ai na Islam ne.

Amma ita har yanzu shiru, seda takara sati biyu akan expected date din sannan ta fara nakuda, aka yi haihuwar wacce ta dauki lokaci sosai. Haihuwa ce mai matukar wahala saboda placenta da position din baby din da suka rike juna sosai, aka yi Emergency C-section a cikin kulawar Dr. Mi'ad.

Alhamdulillah, ta haihu lafiya, kuma babynta ma lafiyayya ce, fara tas kamar babanta amman kamarsu daya da mahaifiyarta kamar an tsaga kara. Sanda aka mikawa EHSAAS yarinyar, kasa riketa yay saboda tsananin farinciki da jin dadi.

Gaba daya jikinsa rawa yake don farinciki Dr. Mi'ad tsokanarsa tashiga yi tana cewa, "kodai bayason babyn ne sumaida ita ko kishi yake tafi kama d mamanta akansa"

EHSAAS yay murmushi yakarbeta yana rungume yarinyar ajikinsa, tamkar ranar aka fara haifa masa da, Ya rungume Islam yana mata sannu, yana samata albarka da addu'a.

Fulani Hajar ta karbi yarinyar tana mata addu'a tana taiwa Islam sannu. Seda yanutsu tukunna yabuga waya NURISTAN yasanar ma d Mai Martaba, Nan fa murna ta dawo sabuwa akan wacce ake yi ta haihuwar Nadira, wacce Mehtav ta haifa.

Seda suka kara sati biyu a Doha kafin su dawo NURISTAN, aka hada hadadden naming ceremony din Nadira bint EHSAAS da Nora bint EHSAAS. Bayan haihuwar Nadira da Nora, Mehtav ta kuma mallakar wasu branches na "Taste of Naija" across Asia da Europe.

Shi kansa EHSAAS, yanzun yana da manyan publishing houses a London, Abu Dhabi, Abuja, Istanbul, and Seattle. Hakama a Nuristan, ya kafa babban literary hub mai suna "House of NURISTAN, Islamic Arts & Literature."

Cikin ginin akwai rare manuscripts, Islamic calligraphy galleries, da libraries da ke dauke da littattafan tarihi da falsafa iri-iri.

Littafin da ya fi daukar hankalin duniya baki daya shine sabon littafin da ya buga, wato "Echoes of Balance (The Polygamist's Soul)." Duk da fiction ne, amma sanin da kowa yayi cewa rayuwarsa da matansa ne ya zamar masa inspiration, ya kara wa mutane kwadayin son mallakar littafin.

Gashi kuma, ya shiga cikin jerin World Islamic Literary Awards, ya kuma zama best-selling book a kasashe sama da arba'in.

EHSAAS ya rubuta littafin cikin hikima don ya bayyana gaskiyar da yawancin maza basa fahimta a lokuta da dama cikin rayuwar iyalansu. A littafin, ya nuna cewa polygamy ba kawai wani privilege bane da aka bawa maza, it's a spiritual test.

Ya rubuta cewa:

"A man who cannot balance mercy and justice in his home has failed, even if the world calls him powerful. The true king is the one whose wives pray for him in secret."

Wannan kalaman nasa ya zama viral worldwide. Scholars daga Al-Azhar, Malaysia, da Qatar sunyi commenting akan littafin, suna yabawa irin zurfin tunanin da EHSAAS ya nuna da yadda ya hada real-life empathy, Islamic discipline, da masculine self-restraint cikin labarin.

Yanzun, publishing empire dinsa yana hada modern Islamic fiction, children's literature, women empowerment books, and spiritual essays.

Daga cikin abokan hulɗarsa akwai Penguin Arabia, Oxford University Press, da Al-Huda Publications.

Yakan halarci World Muslim Writers Conference a Istanbul, da kuma Faith and Art Forum a Doha. Yawanci kuma duk taron da ze je, Islam tana gefensa, don an fi saninta da shi a duniya baki daya saboda itama tana cikin masu ruwa da tsaki a harkar.

Hakan bai taba damun Mehtav kwata-kwata ba, saboda tasan ko ta ce zata bishi din, ba wai zata iya supporting dinsa bane intellectually, cause she still don't have any interest in reading.

Shi kuma baya takurata yace se tayi, idan suka tafi, haka itama zata tsunduma cikin harkokinta.

Bayan shekara biyu, Mehtav ta shirya musu tafiya ta musamman, vacation ne wanda ya zama kamar family tradition dinsu. Duk karshen shekara, sukan je to get their minds off work, iyasu kadai da yayansu, babu EHSAAS.

Yaran se jin dadi sukeyi, don dama kiris suke jira ace ga abinda ze fitar dasu daga cikin palace din. Mehtav ce ta dauki nauyin komai, sponsoring flights, hotels, luxury cruises, komai cikeda kyautatawa da kulawa. Daman kuma kusan duk shekara rige-rige sukeyi da Islam gurin ganin wacce zata fara biya.

Wannan karon kuma, Bora Bora Islands da Ireland sukaje, wata irin tafiya ce mai cike da soyayya, da annashuwa.

Tun daga lokacin da suka tashi daga Nuristan Royal Airfield, aka musu royal escort zuwa Emirates First Class Suite, an tanadar musu da abubuwan morewa iri-iri, caviar, fresh juice blends, honey-scented towels, da private suite lounge inda yaran sukaita kallo abinsu.

Da suka isa Bora Bora, aka tarbesu a The St. Regis Bora Bora Resort, wani wuri ne dauke da overwater villas masu private pools, da panoramic view na lagoon mai launin turquoise. Yaran se farinciki suke suna watayawa sun shafe lokaci suna wasa da ruwa, suna snorkelling, scuba diving, da banana boat ride tare da masu kula dasu.

Islam da Mehtav kuwa, relaxation sukazo yi don haka babu abinda sukeyi se relaxing don harta da breakfast in bed sukeyi,ga spa massage by the ocean, da peaceful evening walks a bakin teku, insuka fito walk din yaran kamar kara musu kiriniya akeyi don ko hotuna bama tsayawa sukeyi ayi dakyauba se Mehtav ta daddaka musu tsawa.

Daga Bora Bora suka tafi Ireland, inda suka sauka a Ashford Castle, ancient castle da aka maida luxury resort. Suka yi horse riding a cikin green fields of County Mayo, suka je Cliffs of Moher, suka dauki hotuna iri iri a bakin teku, sannan suka shiga Dublin domin ziyartar The Book of Kells Museum da Guinness Lake.

Saida sukai sati biyu cif-cif shakatawa kafinnan su wuceSaudi Arabi, inda suka gudanar da Umrah gaba daya, su da yaran, kafin su dawo Nuristan.

Tafiyar ta bar musu abubuwa masu yawa, memories of peace, family bonding, and deep gratitude.

Wata ranar Alhamis, Abeey ta tashi cikeda farin ciki. Ta shiga kitchen ta fara baking iri-iri, tai cupcakes, tai milk cake, sannan tazo ta yi birthday cake kato mai shape din "I love you." Ta kuma hada abinciccika da dama, domin babu abinda bata koya ba wajen Mehtav. Ta hada drinks iri-iri, sallah ce kawai take fitar da ita daga kitchen din.

Daga karshe dai, sai yamma likis ta kammala komai. Tana aikin ne Ahmad yashigo kitchen din yace mata, "Aunty Abeey, me kikeyi?" Tace mai, "Idon ma tambayi," lekawa yayi harda dage yana kallon yadda take designing cake din da ta kammala kafin tasa a fridge. Yace, "Aunty, happy birthday din wa kikeyi? Don happy birthday yake cema cake." Tana murmushi tace, "Na yayanku." Murmushi yay yace mata, "Yaya?" Tace, "Eh." Yace mata, "Zamuci?" Tace mai, "Eh, amman se yaya yafaraci tukunna." Murmushi yay, yana dariya yafice daga kitchen din yana fadin, "Zamuci happy birthday idan yaya yaci!"

Seda ta kammala komai sannan ta wuce dakinta don ta fesa wanka, saboda tasan duk inda Aman yake yanzun, ya sauka a Nuristan, don yace mata jirginsu da yamma ze sauka.

Shikam Ahmad, yana fita daga kitchen din, dakinsu yatafi. Yasamu EHSAAS Jr yana zaune yana karatu, don yanzun yayi hankali sosai, ba sosai yake shiga ayi kiriniyar dashiba, sai idan yan fitinar sun motsa. Yace mai, "Yaya." Yadago yace, "Madidi, yadai?" Yace, "Yaya, aunty tace tana maka happy birthday. Naganta tasaka a fridge a kitchen." Dasauri Muhammad yatashi daga kan tab dinsa da yake game. Yakalli Ahmad da idon mamaki irin "da gaske ne?"Jinjina kai. Jr yace, "Wai seka fara ci zamu ci, shine nakeso kazo muje kitchen ka fara ci, se mu ma kabamu muci. Happy birthday din looks very delicious!" Jr ya rolling eyes yadda kasan Islam yake yawan yi, yace, "Madidi na, can't you see I'm reading? And is not even my birthday! Meyasa Aunty Abeey zatamin cake, uhm?" Ahmad yace, "Yaya tace fa naka ne. Don't be stingy now!" Jr yace, "Okay, are you sure of what you're saying? Yace, "Of course! She even prepared a lot of sweets irin yadda akeyi in za'a yi happy birthday. Duk suna dining, muje ka dakko mana babban happy birthday din se muci!" Jr mikewa yay, yanufi kofa, kamar jiran shi suke suka take mai baya. Tsayawa kallon dining din sukayi, ganin an shake sa da kayan makulashe iri-iri, wanda Mehtav bata bari su ci a haka wai "ze bata musu hakora." Kayan zaki suka gani iri-iri, yay murmushi yace, "Our time has come!" Yace, "Ina babban happy birthday din kace?" Madidi yace, "Yana kitchen." Jr da kansa ya tafi kitchen, ya bude fridge, suka ci karo da hadadden cake din. Jr ne ya dakko musu, suka dawo saman dining din. Har zasu fara ci, Jr yace, "Ai bazamu ci mu kadai ba, tunda happy birthday ne. Aje a kirawo su Noorur Rahma, da Nadira, da Nora daga sashen Momma." Aikuwa haka akai. Muhammad da gudunsa yafice ya tafi har sashen Islam. Suna zaune tana tsifema Noorur Rahma kai, yashiga da sallama suka amsa. A kunne yace da Nadira, "Aunty tahada mana happy birthday!" Ta waro ido irin na mamaki, "Da gaske ne?" Ya jinjina kai alamar eh. Aikuwa da sauri ta rada ma Nora itama, suka fito. Noorur Rahma dake jikin Islam kuwa, ita bata da hayaniya,sai tai musu banza. Suka ce, "Momma, mun tafi, se anjima." Islam tace, "Ku da kukace min yau anan zaku kwana? Ina kuma zaku je?" Muhammad ne yay musu alamar da kar su ce komai, suka ce, "Zamu je dai canne kawai." Tace, "Tohm, Allah ya kiyaye hanya." Aikuwa da gudu suka fice. Islam dai tai murmushi aranta tace, "Allah yasa ba wata tsiyar suke kullawa ba."

Abeey tanacan tana kalkale-kalkale, wanke can, goge nan, shafa wannan, goge wannan. Bata gama shiryawa ba har sai da Aman ya kirata, yace mata ai gashinan yana cikin palace din, any moment from now ze karaso sashen aunty Mehtav. Aikuwa tace masa, "Sai ya karaso."

Agurguje ta karasa shiryawa, daman Mehtav batanan, ita aka barwa gidan da yaran duka. Fitowa tayi jin wayarta na ringing, tana tafe tana daura dan kwalli, don tasan duk yadda akai shine yake waje yake kiranta.

Harta nufi stairs, sai kuma ta watsa ido tana kallon saman dining. Da Ahmad idonta yafara tozali, yadakko katon cake da suka riga suka gama yayyankawa yana kaiwa bakin Nora, ita kuma she's busy sai sirka lemuka iri-iri take a jug kamar wata professional mixer. Nadira kuma tana saman dining din gaba daya tana kasaftawa kowa nashi. Muhammad yacika baki da cupcake, Jr kuma novel ne a hannunsa yana karatunsa, da baya-da-baya tashiga dawowa bata san lokacin da ta dura ashar ba cikin wata irin tsawa, tana fadin, "Kutumar uba!" Jin muryarta yasa gaba daya hankalinsu ya tashi, tarike kugu, ta rasa ma me zatai musu. Dankwalinta ta fizge, ta shiga tattara straight gown dinta.

Jr da karfi yace musu, "Run!" Dukansu ganin attacking dinsu take jiran yi amiliyan suka diro ridididi kake ji, suka fara gudu. Ana kare Abeey tabi bayansu, kifawa tayi saboda dogon takalmin da yake kafarta. Ta tsugunna ta cire shi ta bisu tana fadin, "Wlh sena karyaku acikin gidannan! Nizaku wulakanta wlh sekun biyani!"

Tuni suka bi daya benen sukai kasa. Allah ne kadai ya saukar dasu lafiya saboda irin gudun da suka yi. Bata dena binsu ba har bakin kofa, daidai shigowar EHSAAS da Aman.

Muhammad tai nasarar kamawa tadaga hannu zata kwadesa. Yafasa ihu tunkan hannunta ya sauka a jikinsa. EHSAAS besan sanda yay saurin fizge dansa ba; yaron ya kankameshi, yana kuka, tsabar yadda ta firgita shi.

Itama kukan ta fashe da shi tana kallon yadda yaran duk suka labe bayan kofa suna lekenta, Aman kuma yana tsaye yana kallonta. EHSAAS yadago, ganin tana kuka yasan ba karamin abu sukai mata ba.

Cikin lallashi yake fadin, "Meya faru? Kiyi hakuri. Duk me suka bata miki, zan biya. Please stop raising your hands on them, they are just kids."

Buga kafa Abeey ta fara yi tana kuka cikin tsantsar shagwaba, ta shiga nuna Ahmad dake lekowa tabayan kofa. "Wlh nasan kai ne kaje ka gayyatosu! Narantse da Allah zaka shigo hannuna, barganin babanka yazo kana wani lekoni da katon kanka kamar me! I'll punish you all! Jr, kaima karka bari in kamaka, harda wani cemusu 'run'! Ko narantse, merabani daku se Allah agidanna yau Sekun biyani! Kun san wahalar da nasha kafin ingama aikin nan? Zaku batamin?"

Aman ne yajuya strictly yace musu, "Come out, gaba dayanku."

Jin ba wasa a maganar tasa yasa duk suka fito, harda Jr, suka wuce cikin falo. Ahankali suka karaso, Abeey tafaki idon EHSAAS tai kan Jr. Dasauri yariketa yana fadin, "Waike bakida hakuri ne haba? Duk abinda suka miki bazaki hakuriba? Nawa suke dukkansu?"

Aman ta kalla ashagwabe, seta kara fashewa da kuka. Ahankali yakarasa gabanta, cikin taushin murya yake cemata, "Sorry kinji Princess, I'm so sorry. Daman haka suke troubling dinki, bansani ba."

Ta jinjina kai tace, "Natabbata idan aka dubani se anga BP na ya hau saboda yaranna sun isheni, Ni gidanmu zankoma, nagaji da wannan yaran!"

Duk zama sukai a falo, sunyi wuri-wuri sunsan basuda gaskiya. Dakyar Aman ya lallaba Abeey tazauna gefensa wai ai musu sulhu.

Daidai lokacin Islam na sallama tareda Noorur Rahma saboda taji shirun yaran yayi yawa, tasan kuma basa shirun banza se ana kiri niya.

Tace, "Meyake faruwa ne anan?"

EHSAAS rike dariyarsa yayi, yace mata tazauna a gefe. Aka tambayi Abeey me suka mata, tiryan-tiryan tashiga narrating mata abinda yafaru da kayayyakin da ta hada, sukaje suka ci suka lalata mata komai, har saman aka nufa, tanuna musu barnar da suka mata.

EHSAAS kasa rike dariyarsa yayi, yadurkusa harda rike ciki yana dariya. Kara kular da ita dariyar tayi ta fashe da kuka. Islam rungumeta tayi, tashiga bata baki tana cemata zatai maganinsu gaba daya.

EHSAAS yadago yana rike dariyarsa yace, "We are so sorry, Aunty Abeey. But all this work for whom? Nadauka daga ke sesu ne acikin gidan, kodai your expecting some guest ne?"

Banza tayi masa, taki cemasa komai don ta lura yayansa basa laifi a idonshi. Islam, dayake Aman dan gidanta ne, tuni ta harbo jirginsu tun yadda taga se lallaba Abeey din yake kamar shine yay mata lefi.

Takalli Jr tace, "Idan su basuda wayon sanin daidai da ba daidai ba, kai ba kai bane babba? Your supposed to show them what is right and wrong. Ko zakace min bakasan hardwork tasaka tayi abinnan ba? And me umminku take fada muku koyaushe akan taba abinda ba naku ba?" Takarasa cikin tsawa tana kallonsu duka. Dukkansu jikinsu rawa yafara, don bata fada bata duka amma duk sanda tai magana, seya shigesu.

"Ba magana nake muku ba!"

Jr yace, "Ba madidi ne yacemin wai Aunty tashiryamin birthday ba, kuma yanason ya ci cake, amma Aunty tace masa se yaya yafaraci zasuci. Shine yazo yakirani yace in faraci, suma duk se suci."

Islam tace, "Is it your birthday?"

Girgiza kai yay alamar a'a. Tace, "Meyasa baka fahimtar dashi abinda ya fahimta is wrong ba, uhm?"

Shiru yay, kansa akasa. Tace, "Ba magana nakeba kamin shiru?"

Ahankali yace, "They want to eat it, and ummi usually doesn't allow them to have sweets wai zebata musu tooth. So I thought Aunty Abeey wouldn't mind if they have few." Yakarasa yana satar kallon Abeey dake harararsa.

Islam tace, "Come here." Karasawa yay gabanta, kunnansa takama zata murde, dasauri EHSAAS yashiga bata hakuri yana fadin, "Say sorry Jr, ai bazaka sake ba ko?"

Dasauri yadaga kai yana kallon Abeey yace, "We are sorry Aunty, bazamu sake ba."

Duk sauran ma suka karaso gabanta harda rike hannayenta suna cemata they are sorry. Goge hawayenta tayi kafin tace, "Is okay," tana kumbura baki.

EHSAAS hannu yasa yadau cupcake daya, yakai baki yagutsira yana lumshe ido yace, "Wow, aikuwa akwai dadi! Tohm tunda tahakura, kuzo kucinye abinku."

Abeey wata super tai, tashiga gaban dining din tace, "Insunci inmutu!" Ba EHSAAS ba har Islam dariya tasaki.

Aman yakalli EHSAAS yana marairaicewa yace, "Uncle Prince, ga mari, ga tsinka jaka, this is not fair fa." Yakarasa yana kallon yaran yace, "Bazaku tafi kubamu guriba? Ana magana kuna kallon mutane."

Jr ne yasa kannensa agaba suka bar wurin.

EHSAAS yace, "Naji bakin hali Abeey. Tohm nasan dai bacin sauransu zakiba, kuma nasan shima yayan nasu bacin zeba," yakarasa yana kallon Aman, da be lura da yadda ya kamashi yana wani aikamata da kallon soyayya ba.

"Base abama yarana suciba, aimin bill zan biya konawa ne." Tace, "Better." Tashiga karanta mai account number, atake anan seda yabiya.

Yana girgiza kai yana fadin, "Islam, dafa kayan abincina ma fa akai komai, amma saboda fasha wai sena biya, kiji fa sanrai!"

Abeey najin alert tashiga tattare kayan dasuka fara ci, takira maid ta tace sudauka su kai sashensu su cinye.

EHSAAS yabude baki yana kallonta, ta dauke kai. Yace, "Wannan dai bakin haline kidena, bakyau." Tace, "Inna basu yau gobema sakewa zasuyi. Wllh baza su ciba." Takarasa tana sauka kasa. Aman ne yabita abaya.

Islam tashiga girgiza kai, tajuyo suna hada ido da EHSAAS. Yadage mata gira daya, yana dafe kirjinsa yace, "Yauda kin taba min kunne da da anfara jin kanmu a masarautar Nuristan baki daya."

Murmushi tayi tana fadin, "Yaran nakane, basajin magana, kai kuma seka ringa biye bayansu."

Yace, "Yarane fa in sun girma zasu dena. Stop stressing yourselves over them." Yakarasa yana jawota jikinsa, yashiga shafa cikinta yace, "Keda yar uwarki kunki kukara bani wasu babies din. Kinga Nadira da Nora fa sun girma. Abeg, I need more."

Kallon gefen ido ta bashi kafin tace, "Sedai Mehtav. Kamanta yadda nakusa mutuwa kenan, abeg rabani da batun sake haihuwar nan. Wanda nasamu Allah yasamusu albarka."

Takarasa tana tafiya, yabi bayanta yana fadin, "Wai dozen fa zata haifa mai? Haka sukai da ita tace tohm ta warware yin dasukai."

Ashekarar da ta kama ne akai auren Prince Aman d Abeey kuma acikin shekarar Allah yayi wa Mai Martaba King Nashwan Ehsaas rasuwa, mutuwar da ta girgiza Nuristan baki ɗaya. Saboda bai yi wata doguwar jinya ba, jinya yayi sama-sama, ba ma kowa yasan bashi da lafiya ba. Kwatsam wata ranar Juma'a aka tashi babu shi. Sosai iyalansa da al'ummar Nuristan suka yi bakin cikin rashinsa, musamman yan jikokinsa da Fulani hajar don Jr har wani irin mugun ciwo yakwanta kamar bazeyi raiba daya karshe dai seda aka daukeshi daga palace din yadan kwana biyi gidansu Islam kafinnan asamu yadawo hayyacinsa.

Bayan rasuwar aka nada Yarima Ehsaas bin Nashwan bin Ehsaas, a matsayin sabon sarki. Mulkin Ehsaas kuwa, kusan mulki ne wanda ya daura akan legacy ɗin da babansa ya mutu ya bar masa. Ya kasance adalin sarki na gaske, kuma uba nagari ga duk al'ummar da ke Nuristan baki ɗaya.

Ya kawo ci gaba iri-iri a fannoni daban daban na rayuwar al'umma a Nuristan, tun kafin ma ya zama sarki. Yanzu kuma, da yake kan karagar mulki a matsayinsa na jagoran al'umma baki ɗaya, matansa biyu da mahaifiyarsa ba ƙaramin support suke bashi ba wajen gudanar da mulkinsa.

Mulki suke yi cikin tsantsar ilimi da wayewa, inda abubuwa da dama da a da ba a yinsu a Nuristan, yanzu ya zama cigaba ya zo ana aiwatar da su baki ɗaya.

Sai da ya shafe shekara goma akan karagar mulki, sannan ya daura ɗansa a matsayin Crown Prince dinsa, kamar yadda mahaifinsa ma yayi masa a baya, Yarima Ehsaas bin Ehsaas bin Nashwan bin Ehsaas, Nuristan.

Tammat bi hamdulillah.

And with this, I bring EHSAAS (The lost prince) to a close. Any mistakes made along the way, I ask for Allah's forgiveness. I hope the lessons within the story will resonate with you and be of value.

I am deeply grateful to all the readers of EHSAAS. Thank you for every ounce of support that helped me bring this book to life.

Taku Fatoumspassion, I say goodbye, but not forever.

As with every ending, there's always a new beginning. Stay tuned for my next novel coming soon. Thank you again!