Tsakure!
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®AS-2024.
كل عام وأنتم بألف خير...
5Sᴛᴀʀs Exᴘᴇɴsɪᴠᴇ Cᴏᴍᴘᴀɴʏ..
*♡MAƘUNSHIN GISHIRI¸.•💥*
(Yᴀ Fɪ Gɪsʜɪʀɪɴ Zᴀғɪ)
Nᴀ.
*HAWWA__B__KU♏O.*
(Rᴇᴀʟ S♏ᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.*
*It's all about:#Daughter,#Jinn,#Mom,#Genders,#Fate,#Teen,#Shirk,#Muslims,#Nigerians,#Fame,#Politics..*
00
*TSAKURE!*
°°°°°Tsaye nake daf da ɗakin Yalwa a tsakar gidanmu dake ɗauke da ɗakunan bukkoki irin na rugagen Fulani,cikin faɗa da hargagi take magana tana faɗin "don ubanki bance miki ki bari namiji ya kusanceki ba,cewa nayi dai ki bashi haɗin kai,kuyi ƴan wasanni ya biyaki" muryar yayata Aslamiyya na jiyo tana cewa "Yalwa to idan na samu ciki fa?" Yalwa tace "kaiii! Wannan yarinya kina neman sa min hawan jini,ce miki nayi ki bari har ki ɗauki ciki? Ko kuwa na ce ki bari ya shiga can ciki?" Aslamiyya tace "a'a" Yalwa tace "ɗan wasa fa kawai nace miki,idan ya gusar da sha'awarsa shi kenan,ban ce ki bar kowa ya shigeki ba,saboda ke budurwa ce baki taɓa aure ba,idan nace ki bari wani namiji ya kusanceki yanzu,nan gaba kika zo kikai aure sai abun ya zamar mana gorin da in ba wasa ba sai mun tattara mun bar rugar nan,kina ji ko? Kinga dai duk masu kuɗi ne da ƴaƴansu suke zuwa nan karatu,bango kawai suke zuwa su tsaya,da sun saka ɗan katin nan sai kiga kuɗi suna fitowa,to idan ba muna alaƙa da su ba ta ina za mu samu har mu samu ƴan canjin da za mu ci abinci da ƴan buƙatunmu? Itama wancan shashashar banda baza ta fahimta ba da shegen taurin kai kuma ai da tare zan aikaku,amma a hankali dai ke ɗin ki fara kafin ta biyo bayanki,mene ne amfanin ƴaƴa mata idan ba su nemo maka kana kwance ba? Ai ni Allah ya kashe ya bani ku a matsayin jari,sai dai na ɗaga hannu naita gode masa,ina zaune a gida kuna kawo min kuɗi ina raɓarɓaka girkina son raina,na ci abunda naga dama a sanda naso.." Wani irin kuka ne ya taho min,da gudun bala'i na bar gurin na tafi ɗakinmu,saman tabarmata na kife na rushe da kuka,zuciyata banda ƙaiƙayi babu abunda take,a fili na shiga magana da kaina "Yaa Allah wace irin uwa ka bamu ni da ƴan uwana? Wace irin uwace da za ta so rayuwar ƴaƴanta ya lalace? Wace irin uwace wannan za ta dunga ɗora yaranta a gurɓatacciyar hanya? Wace irin uwace za ta zauna ta gurɓata tunanin ƴaƴanta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Ina magana ina gunjin kuka na sake cewa "anya Yalwa ke ce asalin mahaifiyarmu? Anya kuwa ke ce kika haifemu??"
```#Turƙashi! Anya da gaske Yalwa ce ta haife su? Me zai faru cikin rayuwar su Aslamiyya? Wane ƙalubale za su fuskanta nan gaba? Follow my pen,read happily and comment,feel free habiibaatiiy it's free ***
#Follow
#Read
#Comment
#Vote
#To be continued in the night
#Asli-Smasher.