The Conversation That Changed Everything
Bayan fitar Zara daga manor ɗin, tana driving slowly cikin estate ɗin. Ranta na ɗan fara ɓaci, zuciyarta na cike da tunanin mijinta da kuma tunanin Salma. Tasan ba’aje ko ina ba kuma ko tarewa batayi ba, amma har ga Allah ta matsu bata daina ganin Salma a matsayin matar Zafar ba; the persistent ache of jealousy gnawing at her. sam hankalin yaƙi kwanciya tun ranar da taji sun fara kwana gado ɗaya. She’s not dumb! Tasan Salma ba ƙarya take ba, Zafar ya ƙaryatata ne for peace to reign. Tunanin take, in har wannan abun da ya faru bai sa ace Zafar ya saki Salma ba, to me zaisa? Itakam kafin auren she thought the end of their marriage would be that easy. Ta ɗauka just a word or a little reaction from her Zafar zai saki Salma shikenan, amma taga alamar sai tayi da gaske. Salma is slowly becoming a big problem to her day by day, dole ta fita tun wuri, saboda zuciyar ta na raya mata abubuwa da yawa kuma duk acikin su ba mai dadi.. “Sai haƙuri Zara, indai Aziza ce muma haƙurin muke da ita shekara da shekaru,” kalaman da Mom ta jefo mata kenan a cikin motar, Zara dake cikin tunanin yanda zata raba Salma da mijinta, dan juyawa tayi ta kalli Mom, sannan ta sake maida idonta a hanya cike da takaici. Ita tace mata tunanin wata Yemma takeyi? Mtsww, taja tsaki ƙasan maƙoshi. Haka Mom ta ci gaba da maganganu akan Yemma, her words sharp and calculated, tana ƙoƙarin bugar cikin Zara wadda taƙi ce mata uffan. Zuciyar Mom ta cika da takaicin Zara; wayon duniya tayi, tayi shuru ta ƙi cewa komai har suka iso gidan. Zara tayi horn, aka buɗe gate ta shiga da motar. Bayan tayi parking, Mom ta fito a hasale—her face a mask of irritation—bata ce wa Zara komai ba ta nufi ciki. Zara ta taɓe baki, ta buɗe ƙofa tana ƙoƙarin janyo briefcase ɗinnan dake gaban mota, sai ta ganshi a ƙasan seat a ɗage—it was obvious Mom had been prying, wato dai sai da ta buɗe taga me aciki. Ita dai Zara ta rufeshi da ƙarfi ta fito dashi tayi locking motar sannan ta nufi ciki inda compound ɗin yasa deco, duk an shimfiɗa carpets ta ko ina da traditional ottomans da ake decoration da shi a biki. Gurin yayi kyau sosai, ba kowa sai yara ne kawai ke wasa a gurin, sai kuma workers dake kai kawo, the atmosphere still calm and expectant, amma kana jiyo hayaniyar mata daga ciki. Tana shiga ciki ta wuce parlour ɗin da tasan manya na zama. A tsakar parlour taci karo da Aunty Hannah da tana ganin Zara ta hau faɗa, “Ya za ayi kije ki zauna tun ɗazu ake jiran ki kuma inyi ta kira baki ɗauka?” Zara ta saki wani weary sigh, shoulders ɗinta na slumping yayin da mental fatigue ɗin ranar ya fara settling in. “Ban gani bane Aunty, bacci nayi, ina Anne?” Wani bedroom da Aunty Hannah ta fito ciki ta nunawa Zara tana cewa, “Menene a hannunki?” Zara ta kalli briefcase ɗin hannun ta, ta fara ƙoƙarin buɗe shi dan nuna mata menene aciki, tana cewa, “kuɗin masu henna ne.” Aunty Hannah ta dakatar da ita, tana cewa “No, karki buɗe, sauri nike. Zafar ɗin ne ya baki?” Zara ta gyaɗa kai tana kallon ta with a soft, submissive look. Aunty Hannah ma ta gyaɗa kai tana cewa “Toh an gode, shi dai bai gajiya. Je ki kaiwa Anne.” Zara da da daman haka take da niyya tace, “Toh.” Daga haka ta nufi bedroom ɗin da ta nuna mata. Tana shiga ta tarar dasu cousins ɗin Maamah biyu da kuma Umma Deeza; da alama wani sirri suke tattaunawa with their heads huddled close, their voices dropping into hushed, conspiratorial tones. Suna ganin Zara suka ɗago suna binta da kallo, musamman Anne dake mata kallon tuhuma. Zara ta nufi Anne ta miƙa mata briefcase ɗin. Anne na ƙarba, Zara ta nufi gurin wardrop ta janyo wani zanin atamfa na Umma deeza, daga haka ta hau cire kayan jikinta tass har bra ɗin sai da ta cire, sannan ta ɗaura zani duk suna kallon ta. Anne ta fara cewa “Zara kamar dai ciki gare ki.” Zara ta nufi bathroom, muryan ta light but dismissive ta ɗan turo baki tana cewa, “Haka su Mommy sukace.” Umma Deeza tace “nima dai haka nake gani.” Zara dai ta shige bathroom, the cool tiles refreshing under her bare feet. Tayi wanka da ruwan sanyi, sannan tayi brush don kawar da ɗan ƙarnin kifin da ta ci. Bayan ta gama, ta ɗauro alwala with slow movements, finding a brief moment of spiritual calm amidst the day’s chaos. Sanda ta fito, towel wrapped snugly around her hair, ta jiyo su har yanzu suna zancen cikin nata cike da murna da kuma hirar Yemma. Suna ta cewa Allah ya nuna mata abunta, their voices filled with a mix of genuine happiness and mockery towards Yemma. Zara dai na jin su, a subtle, bitter smile playing on her lips tana tunanin how little they knew—da kuma idan da sun san abin da ya faru a manor ɗin yau, da hirar tasu ta ɗauki wani salo na daban. Bayan tayi sallah ta idar, ta nufi kitchen. Bayan ta buɗe fridge, taga kunun da Umma Deeza tayi mata da safe tasa a fridge. Umma Deeza da ta fahimci Zara abu mai sanyi take so, shiyasa ko da safe da tayi mata sai da tasa ƙanƙara. Ɗauka Zara tayi tana ƙara sa ice cubes ciki, duk da sanyin da yayi. Ta fito daga kitchen ɗin da ƙaton cup ɗin kunun a hannunta, the cool condensation on the glass feeling refreshing against her palm. Ta koma ɗakin inda ta tarar har lokacin hirar gidan Galado suke, inda suke ta labarin rashin kirkinsu. Ta nufi gado inda suke zaune bakin gadon, ita kuma ta haura tsakiyar gadon ta zauna tana shan kununta, her posture relaxed despite the heavy topics being discussed. Anne, da sai a lokacin ta buɗe briefcase ɗin da Zara ta kawo mata, ta juya tana kallonta da baki a sake tace, “Zara, wannan kuma na menene? Daga ina?” Zara ta ɗago tana kallonta tace, “Anne, kuɗin henna ne inji Zafar.” Ƙara zaro ido Anne tayi, Umma Deeza ma ta ɗan zaro ido tana murmushi in pure disbelief. Ɗayar, wadda ake kira Mamma, tace, “Aaaa, wannan dai ya bawa dangin ki da abokkan mamanki, amma ina wannan kuɗin ina masu lalle?” Umma Deeza tayi dariya tana cewa, “Wallahi ko! Yanzu inama muka san nawa ne a nan? Wannan sai dai wani daga cikin mazan nan sun zo su faɗa muna adadin.” Anne na murmushi tace, “An gode gaskiya. Haka a Dubai ya ba Meryem kuɗin da sai da suka gigita Hannah; ta kira ni gigice tana faɗa mini.” Yayin da ɗakin ya cika chatter akan Zara just sipped her kunu quietly, content to let their awe fill the silence. Daga haka suka dawo hirar irin dukiyar da ya ɓarar a ginin gidan Zara. Kullum yan kallo basa ƙarewa, dan ma keys ɗin na komai yana hannun Anne, ita kuwa kowa shakkarta yake. gidan Zara gari guda ne kuma aljannar duniya, kaf estate ɗin manor ne kawai ya fishi girma. Gashi wani irin mix of modern and old money akayi wa gidan. Inda bangaren Zara akayi wani Neoclassical Palatial interior, har bedrooms ɗin anyi keeping ɗinsu simple yet royal, da gadajenta na modern ceiling-track canopies da aka zagaye kowanne da sheer curtains. Komai nata mai haske ne, inda white and grey yafi yawa sai kuma red. Shi kuma Zafar, komai nashi akayi shi dark and ultra-modern a matsayin Obsidian Noir glass Wing, kuma duk plan ɗin Zara ne—daga wing ɗin shi har nata komai taste ɗinta ne. Sosai suka yaba masa, har da ma Muazzam da shine architect ɗinda yayi komai da team ɗinsa, sai kuma Daddy da yasha yabo akan irin kayan ɗakin da ya saka wa Zara. Kaf wing ɗinta shi yayi furnishing, shi ma according to Zara’s taste. Hasali ma, Daddy instruction kawai ya ba Private Banker ɗinsa, shi kuma yayi disbursing funds ɗin duk lokacin da aka turo invoice ɗin Roche Bobois. Wing ɗin Zafar kuma Muazzam ne yayi furnishing da kayan Minotti da B&B Italia. Shima Muazzam, wiring funds kawai yake yi ta hanyar authorizing transfer kai tsaye daga Treasury Department ɗinsa dake Galado Nexus. Omar kuma shi yayi furnishing Private Wellness Suite ɗinta da Hammams, inda aka yi mata wani bespoke wellness fit-out. Shi ma direct wire transfer aka yi daga Family Office ɗinsa dake Galado Nexus kai tsaye zuwa corporate account ɗin The Elite Collective. Katherine, secretary ɗin Zafar, ita ce keda alhakin approving invoices da kuma communicating da duk companies ɗin da suke aikin. Maids quarters ma Ya M ne yayi furnishing ɗinsa, wanda shi ma part guda ne mai zaman kansa da aka tsara shi kamar Boutique Hotel, har da reception domin nan Executive Housekeeper ɗin zata ringa zama. Already maids ɗinta na ciki, inda duk Umma Deeza ce ta kawo su through wata ƙawar ta dake running wani Executive Recruitment & Domestic Staffing Firm mai suna Hampton & Cole a nan Lagos. Inda ita tayi musu headhunting professional Housekeepers and Housemaids da zasu ringa maintaining lafiyar gidan, tare da Expert Laundresses da zasu ringa kula da dukkan suturar Zara. sai Professional Private Chefs, sai kuma specialized beauty professional wadda Certified Resident Cosmetologist ce da zata ringa managing hair da skin ɗin Zara daily. Haka dai suka raba abun tsakanin su dan kowa ya ƙi barwa kowa yayi komai. Ginin gidan dai ba sisin su—komai Zafar ne yayi—amma furnishing, ko sisin sa ba su bari ya sa ba, har wing ɗinsa. Wannan dokar Muazzam ce, saboda sanin halin dangin nasu and his desire to protect his sister’s new peace. Haka sukayi ta hirar su, ita dai Zara har ta gama shan kunun ta, ta ajiye cup a ƙasa, ta gyara kwanciyarta kan gadon, drifting into a peaceful, heavy sleep yayin da su Umma Deeza suka ci gaba da tattaunawa. A ɓangaren Zafar kuwa, ciki ya koma. Inda ya tarar da Baffa na cin abincinsa; shima ya zauna ya fara zuba sabo ya hau ci. Bayan sun gama, Baffa ya kalli Zafar dake ƙoƙarin miƙewa yace, "Don't go just yet. Sit with me. We have things to discuss that require more than a passing glance." Zafar ya gyaɗa kai ya koma ya zauna with a sudden, heavy stillness, yana kallon Baffa da yanayinsa ya koma very serious. Baffa yayi shuru at first, yana tunani kafin ya sauke ajiyar zuciya yana gyaran murya, ya fara magana ciki da hikima. “Muhammad Zafar,” Zafar dake kallon sa ya amsa, “Na’am Baffa.” Baffa ya sake sauke ajiyar zuciya kafin yace, “Wata gaskiya zan gaya maka yau as your father, and I will offer you counsel—still as your father. Because the world only bows to those who listen before they lead.” Zafar ya gyaɗa kai yana ɗan sunkuyar da kai, his posture respectful. Baffa ya gyara zama yana kallon sa keenly ya fara magana, “Kaje ka duba Salma tun jiya?” Zafar ya ɗan ɗago ya kalli Baffa kafin ya ce ciki-ciki, “No, zanje ae.” Baffa yayi ɗan murmushi yana cewa, “Yaushe kenan?” Zafar yayi shuru yana ɗan ɗauke kai, his jaw tightening with a flare of suppressed irritation—da alama haushin Salmar yake ji. Baffa ya sake ɗan murmushi yana cewa, "Stop shifting the blame to her. Laifin na Aziza ne. Salma was merely a soldier following orders, ta yi abin da aka umarce ta ne kawai. Kuma idan ka kula, Salma was just a tool in a larger game. And honestly, ina jin idan kai ne, you would have done the exact same thing. Survival knows no loyalty but to the one who gives the orders." Zafar ya sauke ajiyar zuciya yana gyaɗa kai, the weight of the truth pressing down on his shoulders. Baffa ya ci gaba da cewa, “Abun da nake so da kai shine, kaji tsoron Allah. Let the fear of God be your compass. Sannan kuma abun da nake so ka tuna shine before, you didn’t even have an option. And thirdly, you don't have a choice when it comes to being fair. You must be just, whether your heart is in it or not, even if you wanted to choose a different path, you are already committed. Understand what I’m trying to say here?” Baffa ya ƙarasa raising an eyebrow, Zafar yayi shuru yana kallon sa. Baffa yayi yar dariya yana ci gaba da faɗin, “Kaima ka sani, before all these, you didn't even have the choice to marry the one you love, so don't act as if you have the luxury of choice now. Salma matarka ce, ba ruwan Allah da kana son ta ko akasin haka. It is a debt you owe, Zafar. Dole ne ka sauke mata duk wani haƙƙinta dake kanka. Dan haka kayi ƙoƙari ka ringa adalci a tsakanin matan ka. Make Salma your wife in every sense of the word; treat her with love and respect. Zaka ga idan kana bata kulawa, baza ta saurari Aziza ba. That is the only way you will find peace in your home. Shine zai sa hankalin mahaifiyar ka ya kwanta, sannan shine zai baka peace of mind. Amma idan kace zaka zama marar adalci, toh fa zaka ga komai baya tafiyar maka daidai. Inequality in the home breeds chaos in the soul, kuma ni bana fatan haka. Saboda haka kayi ƙoƙari ka rinƙa danne zuciyar ka har ka saba. Salma is not a bad woman, you yourself know that. Allah ya baka wadda kake so a gefen ka, but that is not a license to neglect the other. Allah doesn't judge based on your heartbeat; in His eyes, they are both your wives and your responsibility.” Baffa yayi shuru for a few seconds, letting his words sink in, Zafar ma yayi shuru yana kallon space, his expression unreadable, masked by a veil of intense contemplation. Baffa yaci gaba da magana. “Ita kuma Zara, you must find a way to make her understand. I know her heart; she will support you in your journey to be a just husband to them both. Daman she is not the problem—Aziza ce. What you don't realize is that being just to Salma is what will eventually calm your mother’s heart and ego. Amma ka kiyaye, musamman Zara. Make her understand your position cikin kwanciyar hankali. Idan ma ba za ka iya ba, ka kawo ta nan guri na; I know the words that will reach her. If you choose to speak to her yourself, then you must do it with tenderness and love, dan Allah. Ka kiyaye sa yarinyar nan kuka. When I saw her tears today, it pained me deeply. Na kuma jiyewa Aziza tsoro har kaima naji maka tsoro; kar biyayya ta kai ka wuta, kuma kar rashin biyayya ya kai ka wuta. The truth is, you are walking a thin line—kana cikin tsaka mai wuya. But try justice in your home; it is the only medicine for your mother’s restlessness. And never forget... Ita Zara marainiya ce. She is an orphan, an amana placed in your hands by Allah. Sa maraya kuka is a heavy sin that I don’t want my wife or son to have in their name. Always remember, your character is tested by how you treat those who have no one but you. So, even if it is only for Zara’s sake, establish justice. When your mother sees you embracing her choice, her heart and ego will settle, and Zara will finally be free from her storms. Dan haka ka kula sosai—Your legacy is not just the Galado Conglomerate, it is also how you manage your home. The peace of your family rests on your shoulders.” Zafar ya gyaɗa kai cike da yadda da abunda mahaifinsa ke faɗi, ya gyara murya yana cewa, “Na gode Baffa. Thank you for the counsel... and for the reminder of what truly matters. Insha Allah, I’ll try my best to establish that justice. I’ll make sure the Galado name remains untarnished, both in the boardroom and in my home.” Baffa yayi wani murmushi in pure fatherly pride. Sosai yake alfahari da yayan sa; seeing Zafar accept such a heavy responsibility with grace made him certain that the future of the Galado family was in capable hands, daman Muazzam kam bashi da haufi akan sa ko kaɗan. “You may go. Anjima da daddare, kaje ka lallashi mahaifiyar ka. You know how to reach her heart; find the right words to soothe her ego. Allah yayi maka albarka da kai da iyalinka.” Zafar ya miƙe cike da girmamawa yana ɗan sunkuyawa yace, “Amin, nagode, Allah ya kara girma.” Daga haka ya juya ya nufi ƙofa, his chest heavy, every step echoing the profound weight of his father’s final words, kalaman mahaifin nasa na yawo akansa… Karfe 8:10 na dare Zafar ya fito daga masallaci, wanda daga gurin Yemma ya wuce masallacin, as usual ya lallashe ta kuma hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, har da sa mai albarka da zai fito. Ta kuma ce mai zata je kai wa Baffa wayar sa in ya dawo daga masallaci; ya yasan ƙarshen ta haƙuri zata ba shi, dan shi Zafar bai ma san Baffa ya kira Sultan ba har sai da Yemma ta faɗa mai, duk da bata gaya mai yanda sukayi da Sultan ɗin ba. So yau bayan ya wuni a ɗakinsa yana tunanin maganganun Baffa sai ya yanke shawarar bin shawara kuma umarnin Baffa. So yana fitowa daga masallaci, kai tsaye ya hau tafiya cikin estate ɗin har ya ƙarasa gidan sa. Yana shiga, straight ya nufi wing ɗin Salma. Ba kowa a ƙasan sai wata maid da ke zaune tana kallon TV, gaishe shi da tayi, ya gyaɗa mata kai with a curt, distracted nod yana nufar sama. Yana hawa ya shiga lounge ɗin inda ya tarar da ƴan matan gidan su ne a parlour ɗin suna hira. Bayan ya gaisa da su, ya kalli Halima dake zaune cikin su yace, “Ke, when are you going back to your husband’s house? Baki san kin bar yara ba?” Halima ta ɗan sosa kai tana cewa, “They’re at the Shettima’s yaya. In two days zan koma.” Girgiza kai kawai yayi bai ce mata komai ba yayi gaba yana cewa “Ina Salma?” Duk suka amsa shi da tana bedroom ɗinta. Mistress suit ɗin ya nufa kai tsaye, inda yana zuwa ya shiga ya wuce parlourn ya nufi ciki, knocking ɗin ƙofar bedroom ɗin yayi kafin ya mirda ya shiga. Salma ce a kwance ga kuma wata yar gidan baba wadda daga gidan mijin ta tazo zaune a gefen gadon da alama magana suke, tana ganin sa ta miƙe cikin sauri tana gaishe sa with a nervous flutter, her hands smoothing her wrapper, amsa wa yayi cikin yar sakin fuska yana tambayar ta ya mai gidan ta da yara, bayan ta amsa ta fita cikin sauri tana basu guri. Salma ta miƙe zaune a hankali tana kallon sa da idanun ta da suka gama laushi, kana gani kasan bata da lafiya, she looks so pale and weak, her skin having lost its usual glow. Ƙarasawa yayi inda take, a hankali ya ɗaura hannun sa kan wuyanta, zafi yaji duk da ba sosai ba, but enough to know she’s sick. Ita dai kallon sa kawai take, shima yana kallon ta, in his natural voice yace “Doctor yazo?” Gyaɗa mai kai tayi a hankali kanta a ƙasa, ya sake cewa “Allah ya sawwaƙa, gobe ki sake shiga gonar matata.” Wani hawaye ne ya zuba daga idonta nan da nan, a silent, glistening track against her flushed skin, ta sunkuyar da kai tana sharewa with a trembling hand. Zama yayi gefen gadon inda Mufida Galado ta tashi, yana kallon Salmar with a complex gaze, his mind calculating how to bridge the distance between them. Ɗagowa tayi ta kalleshi, her lower lip trembling, ta fashe da kuka ta fara magana, “Yaya dan Allah kayi haƙuri. I’m sorry... I am so sorry. Nayi maka alƙawarin zan gyara halina; I won’t cross paths with your wife ever again. Ba ruwana da ita daga yanzu, Insha Allah. Just forgive me and give me another chance, Yaya, for the sake of Allah.” Zafar ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta for five good minutes, observing the genuine desperation in her watery eyes. A hankali, ya miƙa hannu ya janyo ta, pulling her frame toward him with a sudden, protective gentleness wanda hakan ya bata mamaki ba ƙaɗan ba. Jikinsa ya shigar da ita yana rungume ta tsam a ƙirjinsa, as if anchoring her against her own guilt. Cikin lallashi ya fara shafa gashin kanta yana faɗin, “Ya isa. I’ve forgiven you. As long as you keep your word, then we are good. And as for a second chance... you are my wife, it is my duty to do so. We are starting over now, and we are going to take things slow, yeah?” Cike da wani irin farin ciki da sauƙin rai, ta gyaɗa kai ta ƙanƙame shi as if afraid he might disappear. “Thank you, Yaya. I will not disappoint you. You’ll be proud to have me as your wife, in Allah ya yarda.” Kissing kanta yayi ba tare da yace komai ba, letting the heavy, comfortable silence seal the promise between them. Tsawon three minutes of silence suna haka, wayar shi ta fara vibrating cikin aljihu. Ya sake ta, ya ɗan miƙe yana ciro wayar, his expression shifting from soft empathy to focused alertness lokacin da ya ga sunan mai kiran. Ɗagawa yayi yana cewa, “Gani nan zuwa princess.” Daga haka ya kashe ya kalli Salma dake kallon sa cike da so, yace, “I have to go somewhere, sai na dawo.” Salma na murmushi tace, “Sai ka dawo, take care.” Gyaɗa kai yayi, ya juya ya fice daga ɗakin with long, purposeful strides. yana sauka ƙasa cikin sauri ya nufi parking space ɗin gidan inda ya ɗauki key ɗin motar sa dake gurin ya shiga, nan da nan sai gashi ƙofar gidan su Zara da babu abunda ke tashi sai kiɗe-kiɗe, gaba ɗaya titin estate ɗin ya cika da kiɗa da waƙe-waƙe irin na al’adar Tuareg. yana sauka ƙasa cikin sauri ya nufi parking space ɗin gidan inda ya ɗauki key ɗin motar sa dake gurin ya shiga, nan da nan sai gashi ƙofar gidan su Zara da babu abunda ke tashi sai kiɗe-kiɗe, gaba ɗaya titin estate ɗin ya cika da kiɗa da waƙe-waƙe irin na al’adar Tuareg. Wayar sa ya ɗauka ya kira Zara ya gaya mata ya iso. Kusan five minutes after sai gata ta fito, ta yi wani irin kyau sanye da kampala wadda akayi mata mayafi da ita. Cike da gajiya take tahowa, her steps slightly faltering, yayin da shi kuma yake kallon ta cike da so, his eyes tracing her elegant silhouette. Buɗe motar tayi cikin sauri ta shigo, dramatically take cewa, “Heee, Obim, I think I’m going to faint!” Shi da kallon ta kawai yake yana murmushi, a hankali ya kamo hannunta da ya sha henna baƙi da ja. He lingered on the intricate patterns, captivated by how the dark stain made her plush, soft, creamy hands look even more delicate. Zara ta ɗago tana kallonsa with a playful glint in her eyes, ganin yanda yake kallon ta yasa tayi murmushi. Ta ɗan miƙe, tana matsawa kusa dashi, tana go fuskar sa trying to give him a kiss. Amma kafin lips ɗinta su taɓa nasa, ta dakata cak—the air between them suddenly charged with a different tension. Wani abu ta ji. Fuskar sa ta kalla dake ƙoƙarin matsowa ya haɗe bikin su, cikin sauri ta zame ta kai hancinta kan rigarsa tana shinshina, her movements sharp and instinctive. Baƙon feminine perfume ɗin da taji a jikin sa ne yasa taja baya cikin sauri, the smile vanishing from her face, replaced by a sudden, icy clarity. Da mamaki Zafar yace mata, “What is it?” Cikin sauri ta girgiza kai, her eyes darkening with a mix of hurt and calmness, tace, “No… nothing, I think I’m gonna throw up, and I’m feeling dizzy. Just go, Obim, I’ll see you in the morning.” Bata jira ya ce uffan ba, ta buɗe motar ta fice kamar walƙiya. Kafin ma yayi processing abrupt shift ɗin, ta riga tayi vanishing cikin gidan, leaving him paralyzed in the driver's seat, yana bin receding figure ɗin ta da profound sense of confusion…