JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

White lie

by @zahrabmrs02


Tafiyar Switzerland ta zama babban kalubale ga Aliyu, ba kawai saboda binciken asirin Jannah ba, har ma da yadda zai shawo kan mahaifinsa, Abba, wanda ya riga ya tsani duk wata mu’amala da ta shafi Jannah Anderson.


Aliyu ya san cewa idan ya gaya wa Abba gaskiyar cewa Switzerland zai tafi tare da Jannah, to tabbas Abba zai hana shi tafiyar, har ma ya sa shi barin aikin. Don haka, ya durkusa a gaban mahaifinsa cikin ladabi.

"Abba, Zan tafi  wani aiki na gaggawa a kasar Ghana (Accra)," Aliyu ya fada muryarsa a sanyaye. "Zan tafi ne ni kadai don gudanar da bincike akan wasu kayayyakin kamfani da suka makale a can. Zan yi kusan mako guda kafin in dawo."

Abba ya kura masa ido, yana nazarin fuskarsa. "Ghana kace Aliyu? Ba tare da waccan matar ba?"

"E kwarai Abba, ni kadai zan tafi," Aliyu ya tabbatar masa. Ganin cewa ba zai kasance tare da Jannah ba, Abba ya sauko ya ba shi izini tare da yi masa addu'ar fatan alheri, ko da yake zuciyarsa har yanzu tana shakku akan Anderson Global.


Bayan ya bar wajen Abba, Aliyu ya nufi dakin Ummi (Laila). Ya bayyana mata gaskiyar cewa Switzerland zai tafi tare da Jannah. Ummi, wacce kullum take kwadayin ganin danta ya samu daukaka a wurin Jannah,  taji  ji dadin wannan labari.

"Masha Allah, tareeq Switzerland kuma?" Ummi ta fada tana sa masa albarka. "Ka ga dabarar da na gaya maka? Idan ka ci gaba da yi mata biyayya, duniyar nan ma kadan ce a wurinka. Allah ya tsare ka, ya kuma sa ka dawo da alheri."


Suna cikin wannan tattaunawar, sai wayar Aliyu ta yi kara—alamar sako (alert) ya shigo. Aliyu ya zaro idanu lokacin da ya ga adadin kudin da suka shigo asusunsa daga Anderson Global a matsayin albashinsa na farko da kuma alawus na tafiya.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!" Aliyu ya fada yana zare idanu.

"Lafiya tareeq ?" Ummi ta tambaya cikin fargaba.

Aliyu ya mika mata wayar, jikinsa yana dan rawa. "Ummi, duba albashin da aka biya ni. Wannan kudin fa sun fi albashin da nake samu a Wajan aiki na baya  na kusan shekara guda!"

Ummi ta kalli wayar, ita ma ta razana. Ta dafe kirji, tana mamakin irin karfin kudin Jannah Anderson. "Lallai Aliyu, duk wanda bai so aiki a Anderson Global ba, to shi makiyi ne ga kansa. Wannan ai fiye da albashi ne, wannan rayuwa ce!"

Aliyu ya yi ajiyar zuciya, ya dauki kashi mai tsoka daga cikin kudin nan take ya tura wa Ummi a wayarta. "Ummi, ga wannan kashi mai tsoka, a yi hidimar gida, a kuma saya wa Abba duk abinda yake bukata na magunguna da abinci. Sauran kuma zan ajiye mana don gaba."

Ummi ta kara sa masa albarka, tana jin dadi a ranta cewa danta ya fara zama babban mutum. Aliyu kuma ya fito daga gidan yana tunanin cewa, idan har Jannah tana da wannan karfin kudin, to tabbas asirin da take boyewa dole ya zama mai girma.


A cikin babban jirgin kamfanin Anderson Global da ke shawagi a sararin samaniya, shiru ne ya ratsa tsakanin Jannah da aliyu . Jannah tana sanye da bakaken gilashinta, tana duba wasu takardu, yayin da Aliyu yake kallon gajimare ta tagar jirgin.

"Naji kana waya jiya office Jannah ta fada muryarta a dake, ba tare da ta kalli inda yake ba. "Naima ce sunanta, ko? 'Yar shekara sha takwas."

Aliyu ya dago kai cikin mamakin yadda ta san sunan yarinyar da ma shekarunta. "Me kika ce, Ma'am? Ta yaya kika san..."

Jannah ta yi murmushi mai cike da aji, ta dan rage girman gilashin idonta don ya ga yadda kwayar idon ta take. "Aliyu idan zan dauki mutum a matsayin inuwata, dole ne in san kowane lungu da sako na rayuwarsa. Naima yarinya ce 'yar mutunci. A gaskiya, na ji dadin ganin kana da wacce ta dace da kai... Perfect match. Yarinya mai karancin shekaru, mai biyayya, wacce za ta iya baka rayuwar nan ta rufin asiri da kake so. Ba irin mata masu neman iko da mulki ba."

Aliyu  ya ji wani iri a ransa. Kalaman Jannah ba su nuna kishi ba, amma sun nuna yadda take kallon sa a matsayin wanda ya yi kasa da matsayinta.

"Na gode da yaba mata da kika yi, Ma'am," Aliyu ya amsa a takaice, yana kokarin danne shaukin da ya taba ji dazu a ofis.