TALES OF THE WAZEERIS

new life

by @surayyahms

14....🦋🦋🦋

Kwana uku na yin jinya kawai aka kara musu acikin dahrul zahra a rana na hudun sukayi bankwana da juna inda wani naval officer of the highest oder yazo yawuce da itban bin maleek U.S naval commision for special syndicates, a tight, elite circle within the naval training. zaiyi training da aikinsa da kungiyar sirri na NBI wato Naval Blackwater Initiative na wasu yan shekaru.

bayan wucewarsa da kamar awa guda aka wuce da shamsan U.S private royal boarding house mesuna Cresthall Royal Conservatory institute acikin garin connecticut wanda shiba makaranta na yau da kullum bane private royal college ne mai tsananin sirri da tsari na musamman a Turai, inda shamsan ya shafe watanni 8 yana karanta harkan Real Estate, family business Strategy da Royal Asset Management, wani irin horo na musamman da ake baiwa ‘ya’yan sarakuna da masu manyan dauloli kaɗai.

A wannan mataki aka gina masa foundation na fahimtar dukiya azamnnce, mulki da yadda ake sarrafa manyan kadarori na duniya.

Bayan kammala wnn karamin karatun within 8months yagama aka turashi Massachusetts Institute of Technology dake Massachusetts domin fara karatun Civil Engineering, inda zai kwashe shekaru 4 masu kyau shima yana zurfafa ilimi a fannin gine-gine, tsare tsaren birane da manyan infrastructures na zamani.

yana karatun yana hadawa da aiki da Real estate group dinsu na london, dubai, doha, instanbul,..na lagos da nairobi ne kawai bai taɓa zuwa ba sbd sun masa nisa sosai.

A nan ne karon farko da ya tsinci kansa cikin yanayi da envirnments dake dauke da mutane irinsa saidai hakan bai girgiza shi ba sai ma yakara masa kaifin basira da natsuwa.

acikin shekarun 6 da wata 8 inan nan dayayi baije gida ba saiharda yafara karatu a MIT snn yake iya samun daman amsa waya da yin video,facetime da iyayensa da kanwarsa rihanna waxeeri data ke balain girmama shi da kaunarsa aranta

duk dama kowa yasan shidin murdadedn mutumne tun yana karami amma kuma kanwarsa rihanna bata taɓa ce masa tanason wani abu na duniya awajen shi ya hanata ba. ata dalilinta ne ma leelah tafara samun daman magana dashi once in a while tana kiransa awaya suna gaisawa sama sama intaci sa'a ya dauki kirarta kenan.

leelah is desprate about him amma tana da kama ajinta sosai...

ta lura kamar he only care nd protect his sister in a weird way

zakaga kmr ma basa shiri da kanwar tasa sbd yana da mugun halin kyaliya, shariya, da zafin masifa saidai duk dahaka bai dameta ba, itade tana mugun sonsa sosai, rihannar ce ta tafara gaya masa cewa ai cousin dinsu leelah aka zaɓa masa amatsayin potential bloodline wife dinsa daga gida.

saidai yadda yake shareta inta kawo masa batun leelab yasaka tagaji ta dena masa hiran, sai takyale leelahn da aikin cusa kanta a rayuwarsa sam taqi yin saurayi tana nan tana baza mulki da tunanin cewa itace kawai shamsan din zai aura inya dawo she was very sure of it.

within d yrs tsabar kanwarsa rihanna tana shakkarsa dakyar tabari yazo haryagane cewa tafara soyayya da farees salman, a farko baice mata komi ba face saida yafara lura da cewa kmr itace take son yaron sosai ba shine yake sonta ba

yay kkrin nuna mata haka amma taqi sam har taso ace itama a egypt zataje tay karatu kurkusa da masoyinta farees salman amma dake shamsan din yaki ya amince da hakan yasaka dan dole ta haqura aka kaita can da nisa University of Amsterdam a kasar netherlands inda zatayi karatun cosmetics nd jewery business tare da estate management din itama sbd core business din babansu da kakansu khaleefa kenan.

lokacin sosai taji haushin yayanta shamsan daya hana a aikaita karatu egypts dan saida tay watanni biyu tanakan fushiiii bata son magana da shi koda ya kira gida

gashi tagama kai kararsa wajen farees salman cewa talura kmr yayanta shamsan bayason alaqarsu shikuma sai ya dau abin da zafi sosai dan yasan inhar bai auri rihannan ba bazai taɓa samun dama har yay irin daraja da arxikn dayakeso yay a duniya ba.

atake farees yafaraji kamar duk duniya babu wanda yakamata ya tsana kamr shamsan waxeeri sabida last 2 yrs haka yanaji yana gani Aka kawo sarauniya Areesha murad zamkora nan egypt din domin itama tay karatu, yaso ya shaku da yarinyar sosai sbd Allah ya zuba masa neman mata, daga karshe ya lura kmr rayuwarta da hanklinta gaba daya yana ga kan shamsan da ko cikkken sunansa bata sani ba, she alwys use to refer to him as yariman tharim vale.

adalilin sarauniya Areesha zamkora farees ya kara zurfafa shekarun karatunsa a egypt sbd yaga koda zai iya samun dama na jan raayinta suyi soyayya acan dan yana balain son mata masu abun mamaki, kasaita da rawan kai irinta.

saidai firr haka taki kulashi duk dama sun dawo abokai daga karshe ma yagane cewa ashe tazo egypt din ne ma dan tasamu dama tana komawa gida akai akai dan tana kulawa da komi na zamkora sbd tuni ƙarfin ikon masarautar babanta ya fadi kasa sunshiga halin bankruptcy, da talauci da matsalolin yawan yunwa agarin.

cikin salon makirci tahana yar uwanta ushna dawowa gida tsawon shekaru da sunan tana kareta ne daga wahala alhali so take kawai jamaar gari da kewaye su cigaba da kallonta a matsayin wanda Jajircewanta ne kawai yake kan haska ƙima d darajar gidansu har yanxu shiyasa bata zaɓi taje nesan duniya domin yin karatu ba..

daga fannin shamsan kuwa abu dayane yazo ya bashi bala'in haushi da kwasam yaji cewa wai har uwarjini ta amince ma nana A da ummu salma har anyi baikon kanwarsa rihanna wazeeri da farees salman a tharim vale tunma kafin ta wuce karatu aka kulla musu alkwarin aure.

farees dayakejin babu wanda yakaisa tsanar shamsan ynxu tuni yafara kkrin hure ma rihannan kunne akansa tare da zugata akan wasu abubuwa game da ikon da shamsan yake dashi arayuwarta while he is in egypt obsessing abt princess Arisha batasani ba.

Duk wani kudin da rihanna zata bashi hakanan zai kawowa sarauniya Arisha dan kawai tana kulashi

ita kuma Arisha da wann kudin take komawa gida tay hidima wa talakawa da marasa karfi dan ayabe ta sosai, duk tana haka ne dan abada shaida mekyau akanta idan akazo zaben matan yariman tharim vale

Bayan shamsan ya gama karatunsa a MIT, bai tsaya nan ba aka sake tura shi zuwa Harvard University inda ya karkata gaba ɗaya zuwa fannin morden Architecture, domin hada ilimin gine-gine da fasahar kirkira, ya zama cikakken masani mai iya hada fasaha da tsari a matakin duniya.

2nd year dinsa a havard university kwasam aka yi ma kanwarsa rihanna aure da farees salman a tharim vale while she is just 21yrs old sai aka hada da auren dana dayan cousin dinsu mareeda, lokcin rihanna tana aji uku ne a universty bata ko gama ba dan koda akayi komi na auren bada shawararsa ba sai bai zo ba baikuma kirata ba.,

akan haka tay ma iyayensu bori, taji haushi amma bai kulata ba kuma baizo auren ba, dan koda yazo ya kirasu daga baya baibada kowa hkri ba saidai taga kawai ya gaisa da iyayensa amma baza gansa ya kawo musu mgn akan auren ba

tuni yasaka amininsa itban bin maleek ya bincike masa halin farees, sun gane cewa yaron mayaudari ne kuma manemin mata sosai na fitar hankli, ko kadan basu yarda cewa yana son rihanna tsakani da Allah ba.

kuma ya fahimce cewa farees salman ya riga ya gama poisoning in kwakwalar yar uwarsa akansa da tunanin cewa intay sake zai iya hana yuwar aurensu.

farees salman has maniputalated nd deceive her cewa ai shamsan dinne baiya kaunar farincikinta, har da nuna mata cewa tsabar son ta dayake ya saka yakeji aransa inhar bai aureta ba zai iya mutuwa dan haka kar ta bari girman kan yayanta yana rabasu

hakadai ya zugata akay auren batare da shamsan ba kuma tun bata wani shirya ba, farko farko rayuwar auren nasu me dadi suka farayi dan har amsterdam yake zuwa wajenta hutu.

suna daf da cika shekara lkcin zata gama karatu takama aiki kuma sai ta fara gajiya da uban rokon kudi da wayo dayake nuna mata waishi saidai yayita cewa tasaya masa abu me shegen tsada amma shi bai taɓa mata ko irin surprise packages din nan na lovers ba.

wani bin intaga dabiunsa na yawan chat da kallon mata yafara yawa sai tarasa uban waye zata kira ta kai kararsa..

da kudinta yake sponsoring din rayuwar Side chicks dinsa da uwa uba Areesha zamkora dayake balain so ta amince masa ya kulla alaqa da ita.

shamsan barely picks her call tunda ta aure farees, koda ta kirashi saidai su gaisa sama sama baison adamesa da surutu sbd yana da aiki agabansa sosai.

saidai kawai inyaji ta kirashi tana koke koken banza sai yakashe wayarsa yasaka accountant dinsa ya tura mata kudade.

wani bin leelah zatayi ta roqa akan tazo wajenshi ta tayata lallabarsa ya yafe mata amma inaaa ita kanta leelahn duk jiji dakanta bata taɓa samun sakin fuska a wajensa ko na minti daya

ba koyaushe ne zatazo office ko gidansa abarta ta shiga ba, inkaga leelah ta samu daman zama a inuwar shamsan toh babu shakka abokinsa itban yazo masa hutu ne sbd shi itban maleek dama bayada matsala he is friendly nd soft yakan zauna suyihira harma yakan iya nema mata wasu alfarman awajen shamsan nawani abun duniya ko kyalkyali datakeso saikaga ya rokeshi har ansaka accountant anbata.

daga tabar gidan kuma zataje tayi ta burga da cewa saurayinta sultan yana shagwabata da kudi da gifts masu tsada.

Duk tariga ta baza cikin kawayenta cewa sultan din bloodline dinsu shine fa future mijinta,...

...kusan kmr yadda Areesha take rayuwa da wnn burin itama haka take kwana take tashi dashi.

A havard shamsan ya kammala gina kansa a matsayin cikakken expert dayake da cikaken ilimi mai hade bangarori daban daban amma masu alaka da juna.

Sakamakon yawon karatu da rayuwa a kasashe daban-daban, hakan yasa yake da zurfin tunani da cikakkiyar wayewa.

.....Ilimin da ya samu bai tsaya a littafi kadai ba yahade da yadda yake mu’amala da mutane, da yadda yake kallon duniya da yadda yake yanke hukunci.

bayan babban abokinsa itban ko maids da servant bai yason fiye ganinsu agidansa, he prefer to be alone. yana gama harkan karatunsa kuwa kai tsaye ya tattara komi nasa yakoma qasar dubai da zama inda babban headgtrs dinsu na real estate din yake...

Babu wanda yasan ya koma dubai da zama face saida yaci kusan wata biyu yana aikinsa acan snn ya sanar da iyayensa cewa he now fully controls komi na wazeeris real estate holdings a dukkan manyan kamfanoninsu a kasashe guda shida,

cikin dabara ya zame kansa yabar dayan bangaren family business dinsu na energy, luxury da pharmeceuticals wa kanwarsa da iyayensa shikadansa yake riqe da 6 global branches na real estate dinsu wanda yana hawa kan kujerar ya sauya wasu abubuwan yazamana babu sunan familynsa na wazeeris akan komi ya maidashi off shore secret accts nd names inda bazasu na biyan taxes ba kuma sharia, ko wani fine bazaina shafar kamfaminsu ko tattalin arzikinsu ba.

Daga tharim vale kuwa

tsawon shekarun nan abubuwa dayawa sun auko, ummu zulaiha ta haifi ɗa namiji da kyar tarayu, dan saida aka cire mata mahaifarta gabadaya aka sama yaro mesuna suleiman wazeeri amma kuma bata jima da haihuwar ba ummu bilqess ma ta haifi tsala tsala yan biyunta maza Aliyu da kamal haka uwarjini tasaka akay musu wani kalar gagarumin hidima meji da lafiya aka kankambasu.

.... yanxu haka kishiin balai ummu zulaiha da ummu bilqess din suke da juna kamar xasu kashe kansu.

kowa kuma maqircin sa ya motsa wajen Nana A yake zuwa neman mafita gabaki daya gidan babu wani wanda nana A batasan kan sirrikansa ba face sashen marigayi shugaba khaleefa dan daga kan nana hafsa har gimbiya hajarat sakeena basu taɓa zuwa neman wani taimako awajenta ba hakan yasa batasan komi akan sirrikansu sosai ba.

tun ranar da shamsan yacika 29yrs a duniya akayi ta tsammanin zai aje aikinsa ya dawo gida azo afara batun aurensa amma inaaa sai shiru har age 31 yana qasar waje, har kowa ya gaji da jiransa, kusan kowa yanxu ya kammala karatunsa agidan kaf an kama aiyukan dake gabansu kai hatta leelah datake yawan matsa makanta tana zuwa inda yake a dubai har tagaji ta hakura takoma wajen aikinta a brazil tana zama time to time haka tana tahowa nigeria hutu.

is not even easy to chase him around sbd yawan tafiye tafiye da aiki dake gabansa ynxu

da wuya ake samunsa awaya sai tay watanni 4-5 basujishi ba wani bin ma saitayi ma kanwarsa rihanna wayo tasaka ita kirashi sai itama ta karba.

wann karon auren rihanna da farees ya cika good 5yrs amma tsabar matsalar da suke samu sau biyu kenan tana samun ɓari sbd ciwon hawan jini

kullum case dinta da mijinta kenan neman mata, he is spending her hard earn money on hook up girls nd his secret crush princess Areesha tay tay tasan wacece amma inaaa

danko saving lambarta baiyi awayarsa ba haddacewa kawai yay.

duk da yasan Areesha batashi take ba amma sun shaqu a asiirince to the extent that ko wani wata zaina turata mata kudi bana kadan ba, bata amsar kasa da 500k dollars to 1million dollars awajensa, ita batama san uban waye doluwar matarsan ba kawai de tasan kudin matarsa yake kwaso mata tay abunda ke gabanta dasu, haka suka gama karatu a egypt takoma nigeria ta cigaba da aikin royal philantrophy shikuma yanata gantali da short term projects irin adan bashi 3-6 month or 1yr contract dinnan, yanaji aransa matarsa tana da uban kudi bai damu da neman aiki ba....

Haka rayuwa ta kasance, daga fannin Ushna kuwa wnn karo ne take rubibin kammla duka karatunta, ynxu tana kkrin cika 21yrs kenan a london amma iyayenta basu bari ta taɓa komowa gida sbd haryau Areesha bata amince ba, ko kadan batason wayewa da kyaun da ushna taje takarayi a london yazo yana dauke hankalin mutanen zamkora data jima tana musu hidima

share ur coments sabida asamu kari anjima🦋❤️

SURAYYAHMS

tales of the wazeeris

2026/***