White, Gold, and Resentment
Bayan an shiga da Zara parlourn Baffa, ya yi mata nasiha sosai cike da soyayya da kulawa. Su Abbah da Baba ma duk suna taya shi, yayin da su Hajiya Mama dake zaune gefe sai faman tabe baki suke yi, their faces twisted in a bitter mask of envy. Dangi da ƙawayen Mamma gaba ɗaya babu wanda bai lura da negative energy din dake tashi daga wajen su ba. Mom ce kawai ke ɗan jefa baki tana amsawa da “Amin” duk lokacin da Baffa ya yi addu’a. Zara dai na zaune fuskarta a rufe, ta ɗan kishingiɗa a jikin Umma Deeza wadda ta rungumeta protectively. Bayan Baffa ya gama, ya kalli Yemma dake gefensa tana danna waya, completely detached as if she wasn't even part of the gathering. Baffa yace, “Toh madam, bismillah.” Yemma ta ɗago cike da izza, ta bi kowa dake parlourn da kallo, her cold gaze sweeping across the room. Cikin wani soft, nonchalant voice tace, “I have nothing to say, illa duk wanda ba alkhairi ba ne a rayuwar ɗana, Allah ya ciresa da gaggawa.” Ɗif falon ya ɗauki shuru, kowa ya yi stunned da kalaman nata kafin su Ummi su yi amsa da “Amin.” Mai ƙarfi. Ran dangin Zara ya ɓaci a wurin, musamman Aunty Hannah da Umma Deeza, amma suka danne kawai don martabar Baffa dake gurin. Mamma ce ta karɓi zancen cikin sanyi, “Toh ai shikenan, Amin ya Allah. Muma Allah ya kare mana ɗiyar mu daga sherin maƙiya. Mu zamu wuce mu kaita ɗakinta.” Hajiya Mama ta buɗe baki za ta yi magana, Abbah ya dakatar da ita da hannu, ya kalli Mamma yace, “Shikenan babu laifi. Allah Ubangiji ya ba su zaman lafiya ya haɗe kansu gabaki ɗaya.” Duk suka amsa da “Amin” Baffa yayi saurin dakatar da su, ya kalli Zara with warm fatherly voice ya fara magana, “Zara ki kwantar da hankalin ki, you are home. You have always been a daughter to me, and now that the bond is stronger, you are part of this family in every way. My heart and my sanctuary are always open for you. May you and my son always find peace in each other. May your home be built upon the solemn covenant of Allah, Allah ya sanya alkhairi da albarka a cikin aurenku da gidanku, Ya baku zaman lafiya da fahimtar juna, sannan ya albarkace ku da zuriyya ɗayyiba.. May your union be under the promise of Sakina. Rabbana hab lana min azwajina wa dhurriyatina qurrata a’yunin wa’jalna lil-muttaqina imama. Allah ya kade muku duk wani sharri da hassada, Ya kawo muku zaman lafiya mai dorewa. Tashi kuje, Allah yayi miki albarka, ki shiga gidanki da ƙafar dama da kuma basmalah. May your home be built upon the promise of peace and longevity. May you never find reasons to turn away from one another.” Kowa ya amsa da “Aminnnn” yayin da Yemma ta miƙe without any word ta nufi can cikin wing ɗin Baffan. Baba ne ya ɗaura da “Barakallahu lakuma, wa baraka 'alaykuma, wa jama'a baynakuma fii khair.” Nan ma kowa ya amsa da wata doguwar “Aminnnn.” Baffa ma ya miƙe yana yin ciki, da alama abunda matar tasa tayi ba ƙaramin ɓata mai rai yayi ba. Baba ne shima ya miƙe ya nufi ƙofar fita yana daga sandar sa, Abba na rufa mai baya. Suma yan kawo amarya duk suka miƙe suna fara fita. Umma Deeza ta miƙe da Zara a hannunta, Hajiya Mama ta dakatar da su da cewa, “Sai kuma muna jira mu zanin gado gobe in Allah ya kaimu koh?” Aunty Hannah ta juyo tana kallon ta, with a sharp, elegant smirk tana faɗin “Wannan kuma sai ku tambaye ɗanku, dan shi ya wankesa da hannunsa.” Ummi da Hajiya mama har da Aunty asma’u suka haɗa baki wurin cewa “Oho dai, bamu gani ba.” Aunty Hannah ta amsa da “Tunda shi ya gani ai magana ta ƙare, daman ganin nasa muke buƙata. Kuma ya gani, anbar ku da surutan hasada.” Daga haka tasa kai ta fice tana ɗaukan guɗa haka yan matan suka ringa tayata suka cika Manor ɗin da guɗa har suka fice gaba ɗaya… Gidan suka isa wanda ke kallon The Manor ɗin, idan ka cire manor ɗin babu gidan da ya kai shi girma acikin estate ɗin. Wani erin ƙaton mansion ne zaka iya kira da aljannar duniya. wani ɓacim rai ne ya ƙara turniƙe su Aunty dake leƙosu ta sama. da aka ce musu ba Salma ba ce zata zauna ciki, sun yi tunanin Muazzam da Zafar ɗin ne dai a ciki—Zara zata zauna da Zafar, shi kuma Muazzam da matar sa. sai yau dai suka ƙara tabbatar wa Zara ita kaɗai ce da wannan gidan, wanda duk a tunanin su Muazzam ne ya gina mata shi. haka suka shige gidan suna kallon su with hearts heavy with a mixture of shock and absolute resentment… Tun kafin ka taka kafa cikin ginin, compound ɗin ya riga ya gaya maka matsayin mai gidan. The landscaping is a lush, textured symphony of greenery. Gidan ƙaton compound ne da aka cika da flowers, and on each of the massive compound sides, jikin bangon ginin an cika shi da wani mix na bushy Areca Palms da kuma Thuja plants da suka ba da wani Exclusive green texture. Sannan wasu ƙanana Spider Lilies a ƙasa sun ba da wani kyakkyawan Layered garden effect. Dogayen Solar square lights ne dake da farin haske dal aka jere su kusa da bango, while a jikin bangon kuwa, fitilun Neoclassical Lanterns ne masu Seeded glass, suna fitar da wani Warm, golden glow dake ƙara fito da kyan ginin. A ƙaton filin gidan kuwa akwai Royal Palms da Traveler's Palms da aka baza su a warwatse—ba a jere suke ba, sai dai duk bayan kayi kamar 10 steps za ka tsinci guda ɗaya, either dogon full grown Royal palm ko kuma full grown Traveller’s palm. Akwai short Patterned lawn lights a gefen ko wanne palm tree dake baza haske a ƙasa kamar stars. Gaba ɗaya hasken fitilun gidan ya haske wurin kai kace da rana ne, dan babu duhu ko kaɗan a compound ɗin. A tsakiyar compound ɗin kuwa, wani Grand Floral Roundabout ne da aka cika shi da Ixoras da White Vincas, a tsakiyar flowers ɗin kuma Sunflowers ne a tsaitsaye. Sosai compound ɗin gidan ya haɗu, an architectural masterpiece that perfectly blended nature with modern luxury. Daga can gefe ƙashen ginin compound ɗin, kana hango service wing ɗin da housekeepers da housemaids ɗinta suke, a fully-equipped, detached unit designed to ensure the main mansion’s privacy remained absolute. Zara dai tunda suka shigo gidan ta buɗe fuskarta tana kallon ko ina da wani irin excited murmushi a fuskarta. Daga ɗayan side ɗinda ke facing service wing ɗinda yayi nisa dasu ba kaɗan ba, ta hango parking space, inda wani Ultra-modern Cantilever Carport ne mai ɗauke da Integrated LED strips a samansa. Dogon guri ne da yake ɗauke da motoci daban-daban, mostly SUVs ne which include a Black bespoke Karlmann King, Red Ferrari Purosangue, black Lamborghini Urus Performante, White Bentley Bentayga EWB Mulliner, Pink Brabus 800 Widestar, White Range Rover SV Long Wheelbase, da kuma Stealth Gray Rezvani Vengeance. Waɗanda ba SUV ba kuwa sun haɗa da wata black and white Bugatti Chiron sai pink Maybach ɗinta. They are all in awe; idanun kowa a zare daga iyayen har yara, yan matan sai video suke yi. Ba abun da ke tashi a gidan sai guɗa. Har suka ƙarasa entrance ɗin shiga, nan fa kowa ya sake zaro ido. Zara was just smiling. Wani Grand 3-story neoclassical mansion ne. Ƙofar shigan wani Towering Neoclassical entrance ne dake da triple-height arched ceiling wanda yake tun daga ƙasa har zuwa kololuwar gidan; gaba ɗaya an lulluɓe ceiling ɗin da intricate gold carvings dake walƙiya. Ƙofofin shigar kansu abun kallo ne; manyan Gold-framed glass doors ne da suka kai tsayin kusan hawa biyu na gidan. Ta cikin gilashin kofofin ana iya hango wasu manyan Grand Crystal Chandeliers guda uku a jere, suna ba da wani insane glow dake nuna irin luxury ɗin dake cikin gidan. Daga gefe da gefen kofar, akwai manyan Golden Urns dake ɗauke da wasu manicured trees, yayin da hasken Recessed wall lights ya fito da kyan fari da gold na ginin, ya maida dukan wurin wani soft golden palace. Heavy security glass doors ɗin Aunty Hannah dake gaba ta buɗe, the thick panels sliding open with a soft, expensive hiss. Umma Deeza dake riƙe da hannun Zara tace, “Toh sake Addu’a anan ma.” A hankali Zara ta fara furta addu’a, her voice steady despite the adrenaline racing through her veins: “Allahumma inni as’aluka khayral-mawliji wa khayral-makhraji, bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna, wa ‘ala Allahi rabbina tawakkalna.” Bayan ta gama ta sake cewa, “A’udhu bi kalimatillahit-tammati min sharri ma khalaq.” Daga haka ta yi ‘basmalah’ ta shiga da ƙafarta na dama, officially crossing the threshold into her new life, tana furta, “Assalamu 'alaina wa-'ala 'ibadillahis-salihin.” Tana shiga tare da Umma Deeza, aka ɗauki guɗa kowa na rufa musu baya. Grand foyer ɗin gidan ne farko; jikin bangon gaba ɗaya White and Deep Warm Taupe panels ne wanda ya dace da kalar manyan velvet armchairs dake ajiye a gefe. Gaba ɗaya bangon an baza masa wasu Stainless gold dividers da backlit mirrors dake ƙara haska wurin, yayin da hasken Integrated LED strips dake yawo gefen ceiling ɗin da bango ya bawa wurin wani soft Mocha-Gold glow. Cikin living room ɗin suka shiga, wani Massive Double-Volume Living Room ne wanda ya bawa gidan wani irin extraordinary scale da girma. Bangon falon gaba ɗaya White and Warm Taupe panels ne dake da wani smooth, velvety texture, wanda ya dace da ainihin kalar L-shaped modular couch ɗin dake tsakiyar falon. Tun daga Double-height Void Ceiling ɗin Apex ɗin gidan, wani Grand Rain-drop Chandelier ne dake sauka har zuwa tsakiyar parlourn, ƙwayayen glass ɗin jikinsa suna bada wani ethereal glow kaman stars. Shi kuma babban Marble Gold Center Table ɗin dake tsakiyar falon, an masa Under-lighting da warm LED strips, yana bada wani kyakkyawan floating effect akan babban plush warm taupe rug ɗin dake shimfiɗe. Abinda ya fi tafiyar da hankalin Zara shi ne babban floor-to-ceiling arched window ɗin da ya cinye side ɗaya na bangon parlourn. Ta glass window ɗin, kana hango compound ɗin gidan fili, inda wayan nan Royal Palms da Traveler’s Palms suke sheƙi a ƙarƙashin lawn lights. A side ɗin gaban bangon kuwa, wani kyakkyawan Abstract art piece ne, yayin da a ƙasa kuma wani Modern Linear Fireplace ne dake ruruwa a hankali, yana ƙara bawa wurin wani warm, intimate vibe. Daga saman hawa na biyu kuwa, wani Glass Balustrade balcony ne dake hango falon daga sama. Kusan kowane lungu an masa Golden Recessed lighting dake biyo gefen ginin. Sosai wurin yayi wani irin Luxury Masterpiece; kowa ya kasa magana sai kallo da video suke tayi. Zara was happy, exactly yanda ta tsara haka akayi mata. Daga bayan sofas ɗin kuwa, can bayan L-shaped modular couch ɗin, wani Avant-garde Indoor Water Feature ne ya zama ainihin focal point ɗin wurin. Ainihin ruwa ne dake kwarara daga cikin wani Sculptural Crystal Splash a sama yana sauka cikin wani ƙaton Black Circular Basin dake zaune akan floor ɗin, wanda aka zagaye shi da wasu Luminous rings dake fitar da wani Cool Neon Glow, ruwan na tashi daga ciki yana tartsatsi; sautin ruwan yana bada wani irin serene, spa-like vibe a duka falon. Daga can bayansa kuma, ana hango wani Sleek Sculptural Bar ɗin dake parlourn, inda wani tinted glass partitions ne gurin. Bar ɗin gaba ɗaya an jere masa High-end crystal decanters tare da non-alcoholic wines da high end champagnes a jikin wasu Backlit shelves, yayin da gefen bar ɗin kuma akwai wani Modern Pillar mai ɗauke da wasu Built-in display niches. Cikin niches ɗin cike yake da wasu Stunning Crystal Glass blocks dake ɗauke da Quranic verses da aka rubuta su da Pure Gold, suna walƙiya a ƙarƙashin hasken LED. A tsakiyar jerin akwai wani kyakkyawan Customized Crystal block wanda ya fi kowane ɗaukar hankali. A jikinsa an yi engraving ɗin kyakkyawan rubutun Arabic na Surah An-Naba, aya ta 8 in pure gold: "Wa Khalaqnakum Azwaja". Sannan daga ƙasan, an rubuta sunan 'Zafar and Zara' tare da wani ƙaramin gold heart a tsakiya. A can ƙasan rubutun kuwa, sai aka yi addu’a: “May Allah bless your home with eternal Sakinah, and grant you a Dhurriyyah Tayyibah that will be the coolness of your eyes.” Wannan ya ƙara nuna soyayya da fatan alkhairi da ake wa ma’auratan. Gaba ɗaya wannan side ɗin na falon ya haɗe da Mirror-finish ceiling ɗin dake sama, wanda yake reflecting duka hasken Rain-drop Chandelier ɗin da ruwan dake sauka daga sama, ya maida wurin wani Ultra-modern Sanctuary. Zuwa lokacin Masha Allah kowa ke faɗi. Gaba sukayi daga gefen bar ɗin, inda suka tsinci kansu bakin wasu massive floor-to-ceiling glass pivot doors; suka buɗe suka shiga cikin wani irin ƙaton Summer Kitchen. Wurin gaba ɗaya ya ɗauki kalar Warm Taupe and Pristine White, wanda ya sa kitchen ɗin ya yi wani irin haske ga lights ɗin duk farare ne. A tsakiyar kitchen ɗin, wani Massive White Marble Island ne mai soft taupe veining, wanda yake da haɗaɗɗen Integrated Induction Cooktop. Daga saman Island ɗin kuwa, a jikin White Vaulted Ceiling ɗin, wasu Four Slim Cylindrical Chandeliers ne a jere su huɗu cif suna ba da wani focused golden glow akan marble ɗin. Bangon kitchen ɗin kuwa, gaba ɗaya Taupe Matte panels ne wanda aka yi seamlessly integrating ɗin High-end appliances na cikin gidan da shi, irinsu Built-in Double Ovens da kuma wani Massive Integrated Industrial fridge freezer wanda ya saje jikin bangon kaman ba shi bane, sai idan ka taɓa handle ɗinsa. Glass doors ɗin da ke back door ɗin summer kitchen ɗin Umma Deeza da Zara suka nufa, inda suna buɗewa suka ga nan ne ainihin Outdoor Luxury ɗin ya fara. A bakin wajen kitchen ɗin wani expansive deck ne inda ainihin grilling station yake a gefe. Wani Extra-long Linear Gas Grill ne dake tafe da Infrared Rotisserie, an saita shi yadda hayaƙin gashin zai tafi kai tsaye zuwa sama ba tare da ya takura wa na cikin gidan ba. Daga nan gurin kuwa, suna hango wani endless view na wani Tropical Rock Waterfall Pool ɗin da different types of palm trees a zagaye jefi-jefi a filin gurin gaba ɗaya. Wuri ne dake da wani serene sound na ruwan dake kwarara daga kan Natural Rock Formations ɗin, yana faɗawa cikin Crystal Blue water dake haske da Cyan LED lights. Wutar dake cin Gas Fire Torches ɗin dake kan duwatsun tana ba da wani flickering reflection mai ɗaukan ido a saman ruwan, yayin da manyan Queen Palms dake zagaye da pool ɗin suke lilo cikin sanyin iskar daren nan. Ga Massive White Modular Sofas na musamman aka yi su da Weather-proof Performance Fabric. Bangon dake fuskantar kujerun kuwa, akwai wani ƙaton 85-inch Samsung 'The Terrace' Outdoor TV, wanda hasken rana ba ya hana hotonsa fitowa garas, yana ba da wani Ultra-bright 4K resolution kaman kana cikin gida. Ga kuma wasu Oversized Floor Lanterns dake haska waɗancan White sofas ɗin da wani warm, golden glow… Cikin gida suka koma inda suka shiga second parlour ɗin, inda daga nan kuma tsarin ya canza salo, shifting from the warm taupe tones to a more crisp and dramatic aesthetic. Daga nan everything is white and grey, with a little touch of burgundy that added a regal depth to the space. Kamar throw pillows da curtains ɗin floor-to-ceiling windows duk burgundy ne, the rich fabric pooling elegantly on the polished floors. Main kitchen ɗin is white, and some African Blackwood panels looking like something out of a high-end architectural magazine. Dining area ɗin ma white and some African Blackwood panels ne with burgundy royal dining chairs that stood out like jewels against the duochrome backdrop. Wani ultra-modern palatial vibe ne a cikin har zuwa double staircase ɗin da a gefensa fili ne sosai, a grand open space da akwai white Steinway & Sons piano a wurin, standing as a symbol of pure sophistication. Ɗayan side ɗin kuma wani crystal elevator ne, its transparent walls catching the light and promising a smooth, panoramic ascent to the upper floors. Stairs ɗin Pristine White ne; tun daga Marble steps ɗin dake sheƙi kaman madubi, har zuwa Custom Cast Brass handrails da aka yi wa high-polish silver finish. Metal ɗin nada shimmering, diamond-like sparkle wanda ya biyo organic curves ɗin railings ɗin yana shining. Ko wanne guda ɗaya an yi sa ne da wani sculptural fluidity, yana fitar da wani radiant sparkle dake sa kalar silver ɗin zama kaman lu'u-lu'u. Daga samansu kuwa, wani glossy white top-rail ne mai santsi wand ya ƙara fito da kyan benen, completing the ultra-modern palatial aesthetic na gidan. Sai siririn burgundy stair runner dake shimfiɗe a kan stairs ɗin, a sleek, high-definition silk-blend weave that felt incredibly firm and expensive underfoot. Farko a haɗe benen ya fara kafin ya rabu kashi biyu cikin wani Architectural curve mai masifan ɗaukan ido, the twin flights sweeping upwards in a symmetrical masterpiece of design. Ga jerin wasu Colossal Silver Crystal Chandeliers dake reto a saman suna fitar da wani brilliant, diamond-like sparkle, casting a thousand dancing reflections against the walls. Sam Zara ta ƙi taking staircase ɗinan saboda tsayinsa daya firgitata, the sheer scale of the climb feeling a bit too overwhelming in her condition. Ta shiga elevator tare da Umma Deeza, the sleek glass lift gliding effortlessly upwards, suka riga kowa isa sama. Abun da suka fara cin karo da shi a ƙaton filin dake saman shine wani Grand Library Atrium mai girman gaske, a breathtaking open-concept space that served as the crown of the upper floor. Wurin ya kasance a symmetrical masterpiece, inda wani erin ƙaton space ne gaba ɗaya aka mayar da shi massive floor-to-ceiling bookshelves dake shake da dubban littattafai, kalar bango da shelving ɗin duka Pristine White ne wanda ya haɗe da white marble floor dake sheƙi kaman madubi. Gurin ya girman gaske dan gurin sai da ya ɗauki two oversized sets of curved modular sofas a jere, waɗanda aka shirya su cikin wani mirrored layout dake fuskantar juna. A tsakiyar silin ɗin, wani Colossal Multi-tiered Crystal Chandelier ne dake reto, yana zuba wani ethereal golden light akan komai na wurin. The white marble pillars dake gefe da gefe sun ƙara bawa wurin wani palatial architectural depth, yayin da mirror-finish ceiling ɗin dake sama yake reflecting the entire library, making the room feel like an endless hall of knowledge. Gaba sukayi suka buɗe massive slide glaze doors ɗin da suka gani a faɗin filin gurin, suka faɗa wani ƙaton living room wanda ya sake firgita kowa da wani irin extraordinary scale da girma, a space designed with a dramatic, avant-garde edge. Abinda ya fi tafiya da hankalin kowa shi ne bango daya na falon; a masterpiece of architectural engineering where the elements of nature collide. Wani colossal built-in Marine Aquarium ɗin ya cinye gaba ɗaya tsawon wall ɗin gaban parlourn inda ake aje TV kenan, stretching from one end to the other, making the entire wall look like a massive window into the deep ocean. Ruwan dake ciki yana walkiya da wani deep sapphire-blue luminous light, stretching from one end to the other, making the entire wall look like a massive window into the deep ocean. yana haska wasu exotic marine creatures masu launuka daban-daban dake ta shawagi a cikinsa. Girman aquarium ɗin ya maida bangon ya zama a living, breathing piece of art wanda ya cinye duk inch ɗin front wall ɗin. Daidai ƙasan wannan babban aquarium glass ɗin kuwa, wani extra-long Modern Linear Fireplace ne dake ruruwa a hankali, the dancing orange flames creating a stunning contrast against the cool blue water dake sama. vibe ɗin na ‘fire beneath the water’ ya ba falon wani irin unique energy, domin girman aquarium ɗin ya sanya komai na falon ya zama ƙarami. Umma Deeza ce tayi gaba tana nufar ciki tare da Zara tana cewa, “Hannah, ki gaya musu ganin gidan nan gaba ɗaya ba zai yiwu ba a yanzu. Su bari gobe su dawo, dare ya yi yanzu; su fara komawa gida.” Aunty Hannah dake bayan su ta amsa, “Gaskiya dai, dan yanzu ma aka yi rabi.” Daga haka ta juya tana fara tattaro kan mutane tana ce musu, “Dare ya yi, mai gidan na iya shigowa ko yaushe. Gwara ku bari gobe sai ku dawo.” Daga haka suka fara yi ƙasa, yayin da manyan suka bi Umma Deeza ɗakin da ta shiga. Parlour ne babba shima, amma it is a bit cozy bai kai girman wancan ba. Wani Ultra-private Royal Lounge ne wanda aka lulluɓe shi da White and Silver-Gold elegance. Bangon wurin gaba ɗaya an lulluɓe su da massive white floor-to-ceiling drapes marasa kauri waɗanda suka ba wa wurin wani soft, ethereal feel kamar kana cikin gajimare. Ga wani recessed circular cove inda a sama inda babban UFO-style crystal chandelier ke reto, yana baza haske akan white marble floors dake ƙasa. Jikin bango kuwa, akwai wasu towering mirror panels dake tsakanin labulun, waɗan da suke reflecting duka hasken chandeliers ɗin, suna mayar da falon wani endless palace of light. A tsakiyar parlourn kuwa an jere wasu custom B&B Italia Beige Sofas. Masu wani irin deep, comfortable seating da kuma plush fabric dake fitar da tsantsar modern sophistication. Jere elegant set ɗin dake fuskantar juna suke, inda a tsakanin kowane sofa an ajiye wasu white Ottomans ko wasu Ornate Golden Side Tables dake ƙara haskaka wurin. Sofas ɗin sun zagaye wani Custom beige circular Chanel logo rug, wanda logo din is in gold. Akwai wasu sculptural lamps dake baza wani warm radiance a every corner of the room, yayin da akan kowane table akwai wasu Exquisite Golden Islamic Calligraphy Stands dake ɗauke da sunayen Allah (SWT) dana Manzo (SAW). Wanda bespoke art pieces ne akayi mata da zinari, waɗan da aka yi su da gold-finished steel and acrylic, sun ƙara ba wa wurin wani high-end, regal sophistication wanda ya dace da gidan Musulmi. Wannan parlourn ya kasance a serene retreat, inda sanyin iskar central AC da ƙamshin turaren wuta suka haɗe don samar da wani intimate and peaceful atmosphere… Basu tsaya nan ba, ciki suka wuce inda ba ƙofa bane, nan ma light white drapes ɗinnan ne suke tsakanin parlour ɗin da bedroom, so suna ɗaga su suka shiga ciki, shima dai kamar parlour, gaba ɗaya ɗakin ya kasan ce a limitless white sanctuary wanda ya sake burge kowa, the room is very simple yet elegant, few abubuwan dake cikin sa ba abu bane da kowa ke iya affording. Shima dai white drapes ne a massive windows ɗin da babban glass terrace door ɗin dake fuskantar waje. Labulen sun ba wa ɗakin wani irin ethereal, cloud-like atmosphere. Wani bespoke low-profile platform bed ɗin dake zaune akan wani glossy white pedestal, an sake zagaye shi gaba ɗaya da wasu translucent sheer white drapes waɗanda ke saukowa tun daga silin har zuwa ƙasa. Waɗannan labulen sun yi wa gadon kewaye, suna ba shi wani intimate and secluded vibe, kamar gado ne dake yawo a tsakiyar gajimare. An shimfiɗa wa gadon wani Bespoke Charlotte Thomas Maroon Silk Bed Linens masu masifar kyau da tsada. Wannan double-layer of drapes ɗin ya ba wa ɗakin wani unmatched palatial depth da kuma absolute privacy. Gaba ɗaya ɗakin ya kasance a serene, all-white heaven, wanda ke nuna masarautar da Zara ta buƙata aka gina mata. A tsakiyar gadon Umma Deeza ta zaunar da Zara, her movements gentle and motherly. Wata ƙawar Maamah da ake kira Hajiya Atine ta kalli Umma Deeza with a puzzled look, tana cewa, “Deeza, ba ɓangaren mijin ta ya kamata mu kai ta ba?” Umma Deeza ta yi wani short dismissive wave da hannunta, tana cewa, “A’ah, in ya zo shi sai ya ɗauke ta ya kai ta can da kansa, mu dai mun gama namu.” Hajiya Atine ta gyaɗa kai, though she still looked a bit skeptical, tana cewa, “Haka ne kam.” Daga haka suka hau yi wa Zara nasiha mai shiga jiki, their voices low and solemn in the quiet room. Aunty Hannah na taya su, periodically nodding in agreement. Cikin sauri suka yi komai saboda sha biyun dare da ya yi, keeping their movements efficient and brisk. Bayan sun gama, suka yi mata sallama; da yawan su Abuja zasu wuce washe gari, while some were heading back to their homes right here in Lagos. Bayan sun mata sallama suka fice gaba ɗayan su, leaving the room in a heavy, echoing silence. Now, Zara kadai aka bari all alone daga ita sai halinta a cikin wannan ƙaton gidan. A hankali ta saki wani soft, weary sigh, shifting her weight as she reclined against the silk pillows. Tana kwance kan gadon da Samsung Galaxy Z Tri-Fold ɗin Zafar a hannun ta, tana pressing cikin kwanciyar hankali. Fingers ɗinta na gliding over screen da mischievous smirk akan lips ɗinta… Zafar ne ya fito daga ɗakin sa cikin sauri, his movements sharp and hurried. Ya duba hasken agogon sa na Rolex Daytona 126502, ya ga har ƙarfe 12:30am ta gota. Saurin sa ya ƙara yana isa first parlour ɗin shigowa wing ɗinsa, ya fice yana shiga elevator. Duk inda ya wuce, ba abunda ke tashi sai ƙamshin Shumukh ɗinsa dake ratsa iskar wurin. Floor ɗin Salma ya isa, and he headed straight to her suite. Bedroom ɗin yayi knocking briefly kafin ya shiga. A kwance ya ganta da waya a kunnen ta tana kuka, idonta yayi jajir—it was clear she had been crying all day. Sallama yayi ya ƙarasa ciki, ita kuma ganin shi yasa ta kashe wayar tana kauda kanta gefe, avoiding his gaze. ƙarasawa ya yi inda take yana sauke ajiyar zuciya, ya zauna close to her, his presence dominating the space. Ya sa hannu yana janyo ta jikinsa, her body tense. ƙoƙarin kwacewa ta fara yi, her small frame struggling against him, tana fashewa da wani irin kuka. Ajiyar zuciya Zafar ya sauke yana kallon agohon hannun sa, periodically checking his watch. Ganin lokaci na wucewa, ya ɗago fuskarta with a firm yet gentle touch, forcing her to look into his eyes da idanunta dake fitar da hawaye. Bai yi wata-wata ba ya haɗe bakinsu guri ɗaya, initiating a deep, passionate kiss. Yayi kissing ɗinta da wani expert intensity, his fingers tangling in her hair to hold her steady. Salma saboda mamaki ta ƙame guri ɗaya ta kasa motsi, completely caught off guard. Tun idonta na a zare har ta lumshe su saboda salon da yake mata mai tsayawa a rai. Kissing ɗinta yayi for a good five minutes sannan yayi breaking kiss ɗin, leaving her breathless and panting. Hawayen da suka jiƙa mata eyelashes ya shiga goge mata slowly. Yana gama ya sake ɗago chin ɗinta, locking his gaze with hers kafin ya fara magana cikin wani low, husky tone. “I’m trying, okay? I told you that's all I could promise you. I'm gonna make mistakes, Salma. Buy that's what you signed up for when you were crazy enough to agree to marry me. But I’m trying for you, I promise.” Salma ta sunkuyar da kanta tana gyaɗa kai submissively, her heart racing at a frantic pace. Sonsa na ratsa kowace jijiyar jikinta. Shi ma kallon ta yake with a lingering intensity, kafin ya sakar mata wani soft smile da bai taɓa mata ba, yana cewa, "I’ll see you in the morning, and then you can tell me how to make it up to you, yeah?" Salma ta gyaɗa kai da sauri, a faint smile finally touching her face. Kissing ɗinta yayi a goshi kafin ya miƙe yana cewa, “Muje ki raka ni.” Miƙewa tayi tana murmushi, kama hannun ta yayi suka fito haka suka sauko ƙasa suka zo har anteroom ɗin. Suna zuwa ƙofar fita ya kalle ta yana cewa, “Lock the door, sai da safe.” Salma ta amsa da “Goodnight.” Ya gyaɗa kai yana fice ya nufi gate. Salma ta bi sa da kallo with a soft smile, watching him leave until he disappeared from sight…