Book 1 page 29&30
by @barista
*MUJARRABI*
***
Book 1
PG 29&30
Ƙarasowa ta yi dab dasu ta tsaya tana kare musu kallo suka sudda kai ƙasa suna share hawayen dake kan fuskar su.
Ɗagowa Hamrah ta yi ta kalli Ammie da ke kallon su cikin sanyin jiki ta ce
Ammie barka da fitowa da abin da zan yi miki ne?
Sauke numfashi Ammie ta yi ta ci gaba da cewa
"Ku zaman ku gabanmu ma ko gunduranku baya yi, fisabilillahi ku duba ƙannen ƙannenku ma sunyi aure sun rufawa kansu asiri sun zauna a gidajen su kuma muma sun rufa mana asiri, amma ku sai dai kuyi ta janyo mana zagi da abin faɗa abin haushin ma ku ko a jikinku baima dameku ba, kuji tsoron Allah ku fidda mijin aure kuyi aure ku tafi cen gidajenku ku zauna, ku kuhuta muma mu huta da gori da kuma nuna mu da ake yi wlh a ta dalilin ki Hamrah na janye jikina daga shiga cikin dangina da kuma dangin Daddyn ku to cewa ake ni ce na hanaki aure alhalin ina bakin ƙoƙarina wajen ganin kinyi amma kuma ke a koda yaushe sai zuba min ƙasa a ido ki ke to bari kuji na faɗa muku kuka da kuke yi yanzu kuka fara indai kun zaɓi zaman gaban iyayenku to ke shatu ba dole mijin uwar ta ƙi ya faɗa a sha'awar ki ba kin kai aure har kin wuce kuma kina gaban shi kina giftawa, duk abin da ya sameku ku kuka ja wa kanku, kun tsaya zaɓi ko to zakuga zaɓe"
Shiru sukai babu wanda yace ƙala mamaki ne ƙarara a fuskar Shatu tana duban Hamrah da ta sudda kai ƙasa tana watsa da zoben dake hannun ta jiki a sanyaye da alamu ba wannan ne karon farko da ta ke fuskantar wannan matsalar ba sai taji Hamrah ta ce
Za muyi in shaa Allahu.
"Haka dai ko da yaushe kuke cewa amma kuma ni banga alama ba to in kuma wani abin ake kullawa to ba a isa ba kuma anyi kaɗan"
Ammie na gama faɗin hakan tayi ciki abinta.
Ikon Allah, cewar Hamrah cikin zuciyata bata ji daɗin faɗin hakan da Ammie tayi a gaban Shatu ba, ai ko ba komai akwai girmamawa da alkunya a sakanin su sannan kuma bata so kowa yasan halin da ta ke ciki bayan ƴan gidansu, sannan kuma abin Ammie kullum ƙaruwa yake kalaman yau sun ɗaure mata kai wane abu kenan ake ƙullawa ko za a kulla....
"Bestie meyake faruwa dake wanda bansan dashi ba ko ince me yake shirin faruwa me kuma Ammie ta ke cewa ban fahimta ba yaushe kuka fara ƴar haka da ita me take cewa ne dake da kuma waye kuke kulla wani abin?"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta kwakulo murmushi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce
Babu komai Shatu kawai dai tana son nayi aurene shiyasa ki kaji ta ke faɗin hakan....
"Look Hamrah kada ki ɓoyemin komai kamar yadda nima bana ɓoye miki nawa, har tsawon yaushe hakan ke faruwa dake kike ɓoyewa?"
Shatu Ammie mahaifiya ce ban isa naja da ita ko nayi fushi da ita ba ko kuma na tuhumeta da wani abun balle kuma na tambayeta wannan dalilin yasa bana magana akan batun.
Sauke numfashi Shatu tayi ta ce
"Hamrah cewa na yi yaushe hakan ya fara kuma menene dalilin?"
Shatu bana ce ga dalili ba amma kuma rashin aure da banyi ba shine dalilin, zan iya cewa hakan ya fara faruwa ne a lokacin da aka sanya ranar bikina da Deeny akan za a haɗa dana Maryama to wannan abin ya farune ranar bikin da kuma a lokacin suka sami matsala da dangin Daddy a haka aka watse ko rakiyar Maryama basu yi ba suka bar gidan sai dai kuma naji suna ambaton sunan wata acikin musayar kalaman da suke yi wai ita HAJARA ban fahimci komai ba har aka watse aka barni da tashin hankali na fashin aurena da akayi bayan na kammala dukkanin shirina to zan iya ce miki tun daga wannan lokacin Ammie ta ɗauke min wuta bata shiga tsabgata, sannan kuma sakaninta da Daddy ma babu jituwa sai kuma kalaman da suke fitowa daga bakinta masu ɗauremin kai amma kuma abin da bansani ba shine dalilin da yasa Daddy ke cewa in ma akan wancan batun ne to tama daina tunanin zai faru. Nayi² na haɗa dukkanin maganganun waje guda na sami amsar su amma na kasa shiyasa ki kaga ban sanar da ke ba.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Shatu tayi tana kallon Hamrah tana nazari akan kalaman ta sannan ta ce
"Wacece Hajara?"
Ban santa ba.
Cewar Hamrah.
"Bestie duk abin da ya faru dake mukaddari ne babu kuma wanda ya isa ya kanza hakan, Ammie uwace amma kuma zan iya cewa bata miki adalci ba sbd kowa yasan asalin abin da ya faru ranar bikinki ba laifin ki bane daman cen Allah ya yi ke ba matar Deeny bace. To amma meyasa ta ɗau zafi cikin kwanakin nan"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Eh to wannan yana da nasaba da fitowar Alhaji Sama'ila neman aurena, da farko Daddy bai amince ba amma kuma yanzu ya amince sai dai ni ce hankalina bai kwanta dashi ba kuma matsalar na faɗa mata shine take ganin kamar ko auren ne banaso to shine ta ke faɗan waɗannan kalaman dan kada naja da baya dan yin hakan zaisa Daddyn ƙin amincewa da Alhaji Sama'ila ita kuma Ammie bata so ya sani.
Jikin Shatu ya yi sanyi tana jinjina lamarin ta ce
"To ke bestie meyasa baki son shi?"
Ƙawata ba wai bana son shi bane, kinga masaukinsa shine hotel kuma yace dani shi ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoshi Maiduguri sannan yana da mata ɗaya da kuma yara to duk irin wa'yannan mutanen baza su rasa wajen zama ba amma zama a hotel ba girmansa bane, rannan fah cewa ya yi naje na samesa a cen to ni bansan me haka yake nufi ba.
Sauke numfashi Shatu tayi ta ce
"Bestie shawarar da zan baki shine yadda kika ga Ammie ta ɗau zafi wannan karon ki amince ki auri Sama'ila, tunda da zancen aure yazo tunda niyyar sa mai kyau ce ki yarda ayi kawai a wuce wajen sannan kuma you have to find out who is that Hajara bcoz Ina da tabbacin tana da dangantaka da wannan matsalar da kike tare da ita maybe muji wani abin daga wajenta"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
To nagode ƙawata na amince zan auri Sama'ila sbd hankalin kowa ma ya kwanta to amma batun nemo wannan matar Hajara bansan wa zan fara tambaya ba Daddy ko Ammie dake fushi sani?.
"Daddy za ki tambaya ko ki tambayi Zeenat tunda kinga maybe ta sani dan suna tare da dangin Daddy"
To zan yi.
Suna fira tare da baiwa junansu shawa suka jiyo sallama daga bakin gate suka ɗago cike da mamaki suke kallon su tare da amsa sallama suka ƙaraso.
"Hauwa'u Jibrin!"
Cewar Shatu ceke da mamaki ganin ɗayar yasa tace
"Wai tab in ba a mutu ba za a haɗu, Zainabu Abu mai tagwayen suna"
Dariya sukayi suka haɗa baki wajen cewa
"Aishatu muktar ashe rai kanga rai, to har yanzu ana nan ana ƙawancen kenan ya yi kyau"
"Uhm ai ni da Hamrah aminya mutu ka raba ne"
Dariya sukai Hamrah tayi musu barka da zuwa tare da ce musu su shige ciki amma suka ce anan ɗin zasu zauna ta basu kujerun roba suka zauna, nan aka shiga gaisawa Hamrah ta ce
Zainab Ayuba kina nan a gari ikon Allah ko matsin ku ba a ji.
"Uhm pretty kenen ina nan fah harkoki ke riƙe ni"
Ikon Allah, ya yaran naki da mai gidan?.
Dariya Hauwa'u da Zainab sukayi lokaci guda sanan Zainab ta ce
"Ai ban yi aure ba har yanzu"
Cike da mamaki Shatu ta ce
"Kai da mamaki kenan yawancin ƴan set namu da muka kammala secondary School bamu yi aure ba ikon Allah"
"Uhm fah shine ma abin da ya kawomu sbd mu tattauna akai though we have already talked about it me and Hamrah Amma kuma she didn't respond to me, maybe bata fahimce ni bane shine muka zauna dani da kuma Zainab muka sake shawarar zuwa mata da zancen sai kuma gaki to hakan ma yayi kyau sai mu tattauna kan batun"
Hamrah ta miƙe tare da cewa
Let me find you some water.
"Ai daga Restaurant meke bamu da yunwa da kuma ƙishirwa, ki zauna muyi magana wannan karon da babban batu mu kazo"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta zauna tare da ƙurawa Hauwa'u idanu wacce ke cewa daga Restaurant suke sanye take da riga da wondo tashi kitson Attachment mai colour hulace wacce bata rufe gashin kan ba. Ta juya ta kalli Zainab wacce ta ke sanye da doguwar riga itama tasha cikon gashin Attachment ta yafa ɗan ƙaramin mayafi duk sun sha mai kamar ba ƴaƴan Musulmai ba, tayi ajiyar zuciya ta ce
Hauwa'u muna jinki.
"Da farko dai kamar yadda kuka sani ni ce hauwa'u ƴar goal mai lakaɓi da bini a hankali in kayi gardama kasha ƙasa, ina da kungiyoyina na kaina sun kai 7 amma kuma uku ne suke tashe wato ina da fannin ƴan mata waɗanda basu taɓa aure ba sannnan ina da na zaurawa da kuma matan aure. Zainab shugaba ce a ƙungiyata ta ƴan matan da suka jima basu yi aure ba to ita ke riƙe da duk yadda za ayi kuma adace akwai Rahama ita kuma ke riƙe da na zaurawa, ni kuma ina riƙe da na matan aure, sannan akwai masu tallafa mana manya manyan ƴan siya da nan gida Nigeria da kuma wasu daga cikin shahararrun ƴan kasuwa sai kuma ƴan outside.....
Tayi shiru ta sauke numfashi tana dubansu suma sun zuba mata na mujiya suna kallonta cike da mamaki da kuma son sanin shin wane irin kungiya ce wannan mai dubban mutane. Kamar tasan me suke tunani tasa ta cigaba da cewa
"Bari na tafi kai tsaye kan batun so muke mu haɗa kai daku wajen sake bunƙasa wannan kungiyoyi guda ukun musamman ma ke Hamrah pretty ba ƙaramin ƙaruwa zamu yi dake ba ina tabbatar miki karon farko ma Saudi Arabia zaki tafi acen za ku fara shan iskar ku"
Shiru da ta yi ne yasa Hamrah cewa
"Ƴar goal har yanzu ban fahimce ki ba wacce irin kungiya ce wannan wacce kuke taimakon ƴan mata, zaurawa da kuma matan aure kuma wane irin tallafi kuke bada har da kuna da masu taimakon ku"
Sauke numfashi Zainab ta ce
"Haba Hamrah pretty kada ki ce min kina da duhun kai mana, harkar ce baki sani ba zaki ce min ko kuma gwadamu ki ke son yi, to naga ita ɗinma taimako ce tunda tamkar business ta ke do me i do you ne, harka ce ta ƙaruwa da wannan zaman da kuke yi a gida ana matsa muku duk da ba sai kun faɗa ba nasan haka abin yake kuna cikin damuwa to duk wacce ke cikin irin wannan matsalar muke warware ta, yanzu waɗanda suka samu abin yi ta hannun mu suna da yawa dan zan iya cewa last 3month mun ya yi mutane dubu ɗari biyar daga cikin su akwai ƴan mata wasun su kuma akwai zaurawa sannan mata masu jinkirin aure yanzu haka suna da manya manyan shops su ke riƙe da kansu wasu ke riƙe da iyayensu, shine muka zo kema ko ince kuma ku shiga wannan harkar sbd mu faɗaɗa abin musamman ma ke Hamrah pretty da ki keyi...
Ya isa na ce ya isheku ƴar goal da Zee, lallai kun cika ƴan ta'adda masu cutar da al'umma amma to ku sani ko bamu da komai ko da yunwa meke kwana baza mu taɓa shiga cikin kungiyar ta ku ba Allah wadaran da da ƙungiyar ta ku.
Cewar Hamrah cikin ɓacin rai da tashin hankali.
Shatu ko tsuman zaune ta yi tana kallonsu kamar mutum butumi cen ta numfasa ta ce
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah yasa mafarki na keyi"
"Uhmm meyasa kuke bada mata ne abu kun sani mun sani amma kuna son wahalar damu, in zaku saki jiki muci arziki mu barshi a inda yake to ku amince kawai ba wai ku tsaya kuna wani nuƙunuƙu ba"
Cewar Hauwa'u Jibrin tana murmushi sbd ganin wannan karon za tayi nasara akansu.......
Comments and share fisabilillah