MUJARRABI

Book 1 page 39&40

by @barista

MUJARRABI 

By Sayyada barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻
Book 1 
Page 39&40


Da mamakin su suka bi inda ƴar gold ke kallo, ƙurawa motar Alhaji Sama'ila idanu tayi tana rarrabe su, tana so ta san a inda ta taɓa sanin motar, Hamrah ta sauke numfashi tana mamakin ina kuma ƴar gold ta san shi, Shatu ce tayi magana cikin sauri tare da yin gaba ta ce 

"Ah to kisawa ranki cewa ba wanda kika sani bane wannan special man ne"

Tayi gaba abin ta, Hamrah tabi bayanta bayan ta ce da yar gold 

Sai nazo ko zuwa nan da kwanaki biyu.

Sukai sallama ta wuce cikin motar Alhaji Sama'ila ta tadda sai fira suke shida Shatu, ta sauke numfashi da ya sanya ya juyo ya kalleta itama ta ɗago ya ce

"Ya dai gajiya ne?"

Uhm to dashi ɗinma, 2 days ban huta ba.

"Kin kusa ki huta ma ai daga fita aikin, let it be next week, kawai kiyi bankwana da aikin kinga za ki sami hutu kamin ki fara hidimar bikin"

Ta sauke numfashi ko ita daman haka take son tayi zuwa next week ta sami OG suyi magana akan zata sake aikin, a hankali ta ce 

Inna samu na kammala wasu abubuwan zan sake aikin.

"Ok it's better kam"

Shuru ya ratsa har suka iso ƙofar gidan su Shatu yayi parking tare da cewa 

"A'isha mun iso bari na buɗe boot ki ɗauki kayanki ko"

"A'a duk siyyan Amaryar ka ce babu nawa a ciki"

Cewar Shatu tana kokarin fitowa Hamrah ma ta fito tana cewa 

Akwai wani white lada naki ne ki ɗauka.

Alhaji Sama'ila ya fito mata da kayayyakin ta, da ƙyar ta amsa tana godiya ta shige ciki bayan sunyi sallama da Hamrah. A nutse ta shigo cikin motar ya tada ta suka nufo gida, shuru babu mai magana a sakaninsu daman ita Hamrah bamai yawan magana bace har suka iso kofar gida yayi parking, juyowa tayi zata mai godiya taga ya kafeta da idanuwansa masu kwarjini sai ta kasa magana, shiru suna kallon junansu cikin sanyi jiki ta janye nata idanun tare da sauke numfashi, shima ajiyar zuciya yayi ya ce

"Kina bukatar wasu abubuwane da suka shafi biki nan kusa?"

Kai ta gyaɗa alamun a'a, murmushi yayi ya ce 

"A'a buɗe baki za kiyi muyi magana ai yanzu mun zama ɗaya, babu batun ma wata kunya ko jin nawi na"

A'a yanzun dai gaskiya bana buƙata komai.

Ta faɗa cikin sanyin murya ta sake ɗagowa a karo na biyu ta kallesa har yanzu shina idanuwan sa na kanta yana kare masa kallo duk sai taji ta takura ta ce

Ɗazu a bakin shop mun haɗu da wasu ƙawayena ɗaya daga cikin su ta ce ta sanka.

Murmushi ya sakar mata sosai yana yinsa ya ce

"Menene sunanta?"

Ƴar gold, Hauwa'u Jibrin.

"Ƴar gold"

Ya maimaita yana jinjina sunan, a hankali ya kai hannunsa zuwa kan nata hannun dake kan ciyarta ya rike tare da matsesa cikinta, ya sauke numfashi tare da kiran sunanta

"Hamrah"

Hannunta ne ya tsoma rawa, ta sudda kai ƙasa tana kokarin kwato hannun amma yaki sakewa cikin sanyi murya ya ce

"Are you doubting me"

Ta ɗago cikin sanyin jiki tana kallon sa sai kuma taji kunyar abinda ta faɗa ta girgiza kanta alamun a'a, murmushi ya sakar mata ya ce

"I don't know her, did you agree"

Ta sake gyaɗa masa kai, ya sake hannun nata ya fito ya buɗe boot cikin sanyin jiki ta fito ya kira yara su shigar mata da kayayyakin ciki, nan suka soma jidansu suna kaiwa cikin. Da mamaki take kallon yadda suke shigar da kayan ita dai siyayya kaɗan tayi yana nufin duk waɗannan kayayyakin nata ne, ta kallesa tare da cewa 

Wannan ai ɗawainiyar tayi yawa bansan mani kayiwa waɗannan shopping ɗin ba da ban bari ba.

Murmushi yayi ya ce 

"To ikon Allah, laifine dan nayiwa matata siyya, ai kin wuce hakan ma"

Thank you.

Ta faɗa, tana kokarin shigewa ciki ya ce

"Ba komai ki huta gajiya"

Ya shige motar ya tada ta ya tafi, ta dawo ciki ta tadda yaran sun ajiye kayayyakin a palour Ammie na tambayar su waya aiko su, ta ce

Ni ce fah Ammie, ta sallami yaran Ammie ta ce

"To ashe tare kuke tun yau kika fara siyayya haka?"

A'a Ammie Alhaji Sama'ila ne ya min siyayya.

"Yazo kenan, to yayi kyau"

Eh.

Ta faɗa shige ciki itama Hamrah ta wuce ɗakin ta da sauran kayayyakin sannan ta sake fitowa ta jidosu zuwa cikin ɗakin.

 *Bayan 1 week* 

A nutse ta shigo cikin hospital kamar yadda ta saba ta iso office nata ta buɗe ta shiga, duk jikin ta a mace a hankali take tattara duk abin da ya dace. Dr Mahmoud ya turo ƙofar ya shigo cikin sanyin jiki ya ƙaraso kusa da ya jin gina da jikin garu a hankali ya ce

"Good morning Dr Hamrah"

A hankali ta ɗago ta kallesa cikin sakin fuska ta ce 

Morning too Dr Mahmoud, how was your morning?.

"Not good at all"

Uhm but why?.

"You are going to leave us"

Ta dakatar da abin da take yi, jikinta yayi sanyi tunowa da yau za tayi handle off na aikinta, bata so ba tana son aikinta da Alhaji Sama'ila zai amince da ya barta anan garin Maiduguri sai ta dinga fitowa, amma ina last zuwan sa da yayi wajenta sunyi magana amma ya nuna sam a wannan ranar ta bar aikin, sbd shirye shiryen bikin, a hankali ta sauke numfashi ta ɗago ta kallesa tare da kwakulo murmushi ta ce

Dr Mahmoud ai indai ana raye wataran za a haɗe, ai ba a rabu ba.

"Uhmm baki san yadda zamu ji bane in dai baki nan, we are going to missed you, much our special Doctor"

Murmushi tayi ta ce 

Nima ina jin duk wanda yake cikin wannan hospital ɗin tamkar ƴan uwana na jikina nima zan yi kewar ku.

"Humm a bar zancen haka kawai, karfe nawa OG zai shigo?"

Ya ce 10:30.

Ya jinjina kai tare da sauke numfashi yana ci gaba da kallon ta har ta kammala tattara duk abin da ya dace ta ɗauke ta ajiye su cikin drower nata kuma ta maida shi gefe ta ajiye ta juyo ganin Dr Mahmoud kusa da ita yana tsaye ta tsaya tare da ɗan jada baya yayi saurin cewa

"Dr Hamrah ke mace ce wacce ke da kyawun zuciya da kuma kyaun hali da kuma kyaun fuskar maybe all this be the last in you, you are so special, duk wanda ya mallake ki yayi dace, ina miki fatan zama a ɗakin aurenki ya albarkaci rayuwar ki da ƴaƴa na gari. Because of that zan zamu mutumin kaina zan dawo cikin hankalina, you changed me thanks for that. Daga karshe ina neman ki yafe min duk abinda nayi miki a baya"

Sauke numfashi tayi ta 

Nagode da yabona da kayi, kuma nayi farin ciki da sauyawan da kayi. Ni ban taɓa ko da kwana da kai ba ban iya ba bansan yadda ake yi ba, Allah ya shige mana gaba.

"Ameen, thank you for the understanding till we meet at the meeting room"

Ya fice kamar zayyi kuka, ta shirya ta fito ta wuce general ward nan tayi sallama da wasu patients nata wasu har da kuka, cikin Doctor's da kuma Nurses ɗin ma sun zubda ƙwalla wasu kuma na farin cikin tafiyarta, dan Adam sai Allah. Ta dawo zata shige office MD ya kirata, ta juyo ta shigo ya washe jajayen hakwaran sa da zata iya cewa wannan fara'ar tun farkon dawowar aiki cikin Hospital ɗin dan haka batayi mamaki ba ta gaida shi ya amsa tare da cewa 

"Komai yayi farko zayyi karshe yau zaki bar Hospital, to sai a yayyafe mana zaman tare ban sani ba ko na ɓata miki"

Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba kanta na kallon gefe shi kaɗai yana ta surutan sa, ta ce

"Ba komai"

Ta miƙe ta fice, ta dawo office nata ta ɗan kishingiɗe jikin kujera tana sauke numfashi, Dr Aliyu ya shigo cikin sanyin murya yayi sallama ta amsa ya zauna tare da cewa 

"Our special Doctor tun yanzu muka fara kewarki"

Uhm Dr Aliyu ya za ayi ai kuma bazaku so ku ganni cikin wannan yanayin na rashin aure ba, tun da yanzu Ubangiji ya nufa sai muyi masa godiya.

"Haka ne amma kinsan sabo akewa kuka, mun zauna dake lafiyar kamar kema kin zauna da kowa da zuciya ɗaya baki damu ba duk abin da za ace you still help people, masu irin wannan halin kaɗanne basu da yawa. Ina miki fatan zama a ɗakinki na har abada. Allah ya albarkace da zuriya ɗayyiba"

Amin Dr Hamrah much appreciated with your dua. Thanks.

Kiran OG ya shigo a tare suka tafi meeting hall nan yayi dogon jawabi ya fara da yabonta da kuma irin cigaban da ta samar a wannan Hospital ɗin sannan yayi mata kyauta ta musamman na kuɗaɗe masu yawa bayan ya bata award na special Doctor kamar yadda yaji ake cewa kuma ya tabbatar, anan tayi handling aikin tare da bashi files da ya taɓa cewa ta haɗa masa na ci gaban wannan Hospital ɗin, bayan ya dubasu ya ce nan gaba duk kuɗaɗen da zasu shigo ta account nashi zasu shigo, aiko nan hankalin MD ya tashi what OG da kansa ya koma accounter shikenan ta kare masa yana murna bayan tafiyan Hamrah zai ci karensa babu babba ashe ma gwamma tana nan ɗin ma. A haka dai har aka fito daga meeting Dr Zalihat da kuma Nurse Laraba sukayi mata rakiya har bakin titi, tana fita sai ga Alhaji Sama'ila yayi parking ya fito ya buɗe mata alamun ta shigo duk jikin ta a sanyaye tana masa kallon mamaki bata ce komai ba ta shiga ta zauna ya shigo ya tada motar suka dawo gida a kofar gidan yayi parking bata ce komai ba, duk sai taji ta wani iri da tabar aikin duk da ta taɓa yin hakan a baya amma bata taɓa jin irin wannan ba, cikin sanyin murya ya ce

"Baby nah ya dai ko dai baki jin daɗi ne muje muga likita"

A'a, I'm doing well.

"To ki shige ki kwanta zuwa anjima sai muyi waya"

To.

Ta fito ta shige gida, ta tadda Ayshe da Zeenat sun iso suna ganin ta suka saka murna suna sukananta amarya, murmushi kawai tayi ta zauna a kan kujerun da suke palourn ta sauke numfashi tana bin kayan da ke jibge a zube ta ce

Na menene kuma waɗannan?"

Ayshe ta ce

"Wannan kayayyakin da za ayimiki gyaran jiki na aurenki da abubuwan da zaki amfani su, wadannan kuma ankon biki ne na family anko tunda kince ba zaki cire na kawaye ba shine mu mun siya yanzu haka mutane 70 muka sayawa ga kuma kuɗin mutum 40 ta dangin Daddy. Yanzu ma munzo ne zauna muga su me dame ya kamata a shirya"

Uhm ga Atm nawa kuyi duk abinda ya dace Please ku barni zanje na ɗan kwanta.

Cike da mamaki suka bita da kallo har ta shige ciki ta kwanta abin ta, duk sai take jinta wani abu haka to ita dai ba murna ba bakuma bakin ciki ba har bacci yayi awun gaba da ita. Sai bayan la'asar ta farka ta watsa ruwa ta fito ta tadda har sun kammala duk abinda suke so suna shirin tafiya su kayi sallama.

Biki saura 1week Hamrah ta shirya ta tafi gidansu ƴar gold ita kaɗai wannan karon, ta tadda rahama ce ita kaɗai a zaune a palour ƙasa da alamu shigowar ta kenan, tana ko ganin Hamrah ta saki murmushi tare da yi mata sannu da zuwa ta kawo mata ruwa, sun taɓa fira take tambayar su ƴar gold ta ce da ita ai suma suna hanya ba zai jima ba zasu dawo. Shuru ne ya ratsa sakaninsu a hankali Hamrah ta ɗago ta kalli Rahama dake ta danne dannen wayarta ta ce

Rahama da son jin karashin labarin ki na tafi kuma ina tabi a rai, in zayyu ko zaki ƙarashemin ne meya faru ne a lokacin da iyayen mijinki Ahmad suka shigo suka tadda Fateemah wacce mijinki ya kawo ta a matsayin ƴar uwarsa.

Ɗagowa Rahman tayi ta kalli Hamrah tare da cewa 

"Uhmm ki bari kawai pretty, ai Ahmad ya cuceni ko ince ya cuce kanshi, a lokacin da mahaifiyar sa da kuma ƙannensa suka shigo duk sai ya ruɗe jikinsa har rawa yake yana musu barka da shigowa, Fateemah bata palour suka zauna har suka sha ruwa sannan ta fito cikin shiri zata fita cike da mamaki suke binta da kallo tare da cewa 

"Ah bakuwa ki kayi Rahama ya mutun Kaduna?"

"Uhm daman jira nake so aje wajen na ce

Ah Ummah ai Fateemah ce ko baki ganeta ba.

"Fateemah ta ina kuma?"

Ahmad dake sugune duk ya jike da gumi ya ce

"Kuci abinci zuwa anjima sai a tsaya tambaye² teemah ki gaidasu mama"

Mamah?. 

Na faɗa a fili tare da miƙewa na tare ta na ce

Zo kiyi musu bayani daga gidan uban wa ki ke munafuka, kin ɗauka mahaukaciyar ce ni ko bansan me nake yi ba.

Ummah Ahmad ce ta miƙe take cewa

"Wai meke faruwa ne Ahmadu, me nake gani wacece kuma wannan?"

Tsilli² yake yi da idanuwa ya rasa abin cewa, na ce

"Ummah cewa yayi ƙanwarsa ce ƴar baffansa ce satin ta biyu a nan gidan"

Wawan mari umman sa ta ɗauke da dashi ya rage tsawo yana hawaye nan yake sanar da ita marainiyace an korota daga gida matar ubanta ce ta koreta sbd babu uwar ta....

Kan ya karasa ta sake wanke shi da mari ta ce

"Ah ka manta a kanta aka fara maraici, meyasa ka ɓoyewa matarka sai da ta bincika ta sani to ka sani  ta tattara ta fice  ta koma gidan ubanta"

Aiko Ummah bata tafi ba sai da ta tabbatar Fateemah ta tafi sannan ta fice cikin ɓacin rai ta ce kada Ahmad ya sake zuwa inda take. To sbd wannan abin da ya faru yasa ya ce tunda na haɗa sa da iyayensa babu shi babu ni kuma ba zai sakeni ba sai ya gana min azaba kuma ko ƙwandalansa ba zai kashe min a matsayin kayan abinci ba. Na jikata ya fice yayi tafiyarsa sai da ya ɗebi 3 month kafin nan ya dawo daman ba sana'a ce dani ba, nayi complain a gida suka ce ina tunda naji na kuma gani na zaɓesa bayan sun ce a'a na eh to na zauna dashi ko a wane irin hali nake ciki ni na sani. Shine na faɗa cikin wannan harkar har zuwa wannan lokacin"

Sauke numfashi Hamrah tayi ta kalli Rahama da take zubda ƙwalla. Lallai akwai darussa da dama cikin labarinta, a hankali ta ce 

Mu matsalarmu mu mata munayin abu ne da dawo mana dashi, akwai mu da hakuri da kuma juriya da kwallafa rai akan abu, duk da cewa shi yaba kyauta tukuici ne, amma bai dace a dinga kwallafa rai akan kinyi sai anmiki. kuskuren ki na faro shine bijirewa iyayenki da ki kayi tun farko akan cewa ke Ahmad ki ke so in ba a baki shi ba sai dai a rasaki, su iyaye suke da hangen nesa akan ƴaƴansu suna nema miki farin ciki ne na har abada amma ki kayi kunnen uwar shegu wai ke ga mai miji, to shine Allah ya barki da Ahmad ɗin kuma ai kinga aya. Sai kuma kin rufa masa a siri kina tunanin ba zai taɓa cutar dake ba kin miƙa masa dukkanin yardan ki sbd abinda ki kayi masa ya wadatar ba zai kyalla ido yaga wata ba sai kuma gashi yayi shine hakan ya sanya ki cikin depression. Nan gaba in zakiyi abu ki yi dan Allah bance Ahmad yayi daidai ba, yayi kuskure amma da yake shi na miji duk abinda yayi ado ne, nashi ya ɓoya naki kuma duniya ta sani, bakya tunanin makomar ƴaƴanki ko kina nufin ba zasu taɓa yin aure ba, sannan ma da wane irin idanuwana zaki kallesu a lokacin da suka mallaki hankalin su suka fahimci irin abin da ki ke aikatawa. Shawarata anan shine ki goma gida ki zauna kiyi nazari ki nemi mafita tun kan lokaci ya kure miki, sannan ki nemi mijinki ku sasanta da yanzu dake dashi kun zama daya tunda da kin aikata ma fiye da abinda ya aikata.......

"Hamrah pretty daman nemanki nake, mu zaki rainawa hankali ki ce zaki shigo cikin kungiyar mu ashe kina cen kina shirin yin aure to ki sani wallahi baki isa ba kinyi kaɗan"

Cewar ƴar gold a lokacin da ta shigo ta tadda Hamrah a zaune a palour nsu daman nemanta take ruwa a jallo..........




.
Comments and share