BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----2 

"Amin" suhail ya ce
tashi sukayi zasu tafi bayan sunyi wa suhail godiya suna fita ya kira nadia akan ta basu dubu hamsin suyi kudin mota koda ta basu Baba ya ce"wannan fa" nadia ta ce"Yallabai ya ce a baku kiyi kudin mota" tsabagen farin ciki baba ji yayi kamar yayi sujjada dan raban da ya riƙe kudi irin wannan har ya manta godiya sosai suka yi suka tafi,suhail na zaune a office din sa ya jingina da kujera yana ta tunanin ta idan zai fara fuskantar wannan case din wayar  sa da dake ajiye a gaban  sa ta fara Ringing sunan zeenah ya bayyana jikin screen din dan ƙaramin tsaki yaja tare da saka wayar a silent dai-dai lokacin Abokin sa sameer na shigowa office din zama yayi kan kujera yana kallon fuskar Suhail da alamun ransa a bace ya ke 
"Suhail what's wrong"
kai ya girgiza masa alamun ba komaii 
sameer ya ce"su waye suka fita yanzu daga office dinka"
suhail ya ce"wasu innocent client ne sun kawo karar Tahir dan gidan Alhaji Sani Dan kasuwa kan yayi wa yarsu Fyade har ta rasa ranta"

Zaro ido Sameer yayi  ya ce"again kasan kwanaki ma haka yayi wata yarinya fyade,iyayen ta suka kawo kara inda daga ƙarshe sai korar case din akayi a cewar su ai babu wata sheda da ta nuna shi ya aikata laifin"

gyara zama Suhai yayi ya ce"nayi Alkawarin ba tahir ba ko shi Alhaji sani dan kasuwan ya aika haka wallahi sai na ga karshen sa sai ns tabbatar da doka tayi aiki a kan su"
sameeer ya ce"i trust You guy"
wayar ta sake Ringing a karo na biyu bai ɗaga ba Sameer  ya ɗauki wayar ya miƙa masa ya ce"zeena ce fa ke kiranka"

haɗe rai yayi ya ce"i'm not in mood din da zan iya daukar kiranta ta yanzu"
taɓe  baki Sameer yayi ya ajiye wayar suka cigaba da magana akan yadda zasu tunkari case din. 

knocking kofar office din akayi duk tunanin Suhail nadia hakan ya sa ya ce"come in" murɗa kofar akayi yarinya ce yar kimanin shekaru Ashirin da biyar ta shigo fuskar ta sanye da niƙaf kallo ɗaya yayi mata ya tabbatar da zeenah ce Sameer dake gefe ya tashi ya kalli Suhail ya ce"see you Later" ƙara sowa tayi ta zauna kan kujera ta buɗe fuskar ta suhail ya miƙe tsaye ya ce"zeenah so how many times should i warn You akan suwa office dina without my permission"

ƙasa tayi da murya ta ce "yanzu suhail dan zanzo wajen ka dole sai na nemi izini,infact kira nawa nayi  maka Baka ɗaga ba kasan zuciyata bazata iya jurewa ba because ina sanka suhail,san na ni kaina basan iyakar saba why i you treating me like this,miyasa duk Duniyar nan baka da abin wulakanta wa sai ni shin dan nace ina sanka ya zama laifi miyasa ku maza haka kuke da mace ta nuna tana sanku shikenan kun samu damar mata wulakanci hawaye masu zafi suka soma sauka kan fuskar ta.

Suhail ji yayi bai ji dadi abinda yayi zeenah ba shi shaida ne akan san da zeena take masa kuma shima ba wai baya san ta bane kawai yanayin aikin sa ke hana shi bata lokacin daya kamata zagayo yayi kusa da ita ya dafa ƙafadar ta cike da lallashi ya ce"i'm sorry zeena i don't means to hurt kinfi kowa sanin yadda aiki na yake i'm always busy but i'm sorry ki tashi ki tafi anjima zanzo"

ɗago jajayen idanun ta tayi ta zuba su cikin na Suhail ta ce kora ta kake"
"No zeenah bana so wani yazo ya ganki ne "
tashi tayi ta gyara nikaf din fuskar ta Suhail ya ce"muje inyi drooping dinki"
kai ta girgiza masa ta ce"da mota nazo"
bata jira ya kara cewa komi ba tayi fice war ta zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya a ransa ya ce"zeena rigimar duniya"

take ya fara cike forms da zai tura court kan case din tahir bashi ya bar office din nan ba sai wajen karfe ukku na yamma dakin sa ya nufa yayi wanka  ya nufi part Mahaifiyar sa Zaune ya sameta a dinning tana cin launch joining dinta yayi suka ci tare  anan tace masa idan ya gama yaje gidan kanwarta ya amso mata maganin ta ko da ya gama dai-dai ana kiran la'asar mallacin dake jikin gidan su ya nufa,yana gama sallah ya dauki keys din motar sa ya nufi gidan Aunty Aisha kanwar mahaifiyarsa a bakin gate yayi parking mai gadi ya buɗe masa a compound din gidan ya iske meerah da ƙawar ta zaune kan resting chair wani harara ta wurga masa tare da jan tsaki sarai suhail ya jita ta murmushi yayi dan shi lamarin Meerah ma dariya yake bashi ta gabasu ya wuce kawar ta kadai ta gaishe shi hannu kawai ya ɗaga mata bayan ya shiga ciki ƙawar meerah ta kalle ta ta ce"Miyasa baki gaishe shi ba ,ba Cousin bro dinki ba ne"

Meerah ta ce"and so ke da kika gaishe baki ga kalar amsawar da yayi maki bane"
ƙawar ta ce"anya Meerah ban san yayan nan naki kike ba ganin yaƙi baki dama shiyasa kike masa haka"
ƙaramin tsaki meerah taja ta ce"Allah ya sauwake nayi soyyaya dashi wlh"

shiru kawai ƙawar tayi ba tare da yarda da abinda Meerah ta ce ba kallo ɗaya zakayi mata kaga tsantsar soyyayar Suhail a cikin idanun ta

Suhail na shiga falon ya iske aunty Aisha zaune tana kallo har ƙasa ya risina ya gaishe sai da ta bashi izini kafin ya zauna akan kujera aunty Aisha ta ce"Suhail ya aikin"
"Alhamdullilah aunty"
mai aikin ta kira ta kawo masa drinks da snacks ya ce "a'a a koshe yake"
maganin ta basa  ta ce"gashi ka kai mata zanyi mata bayanin yadda zatayi Amfani dasu gaba ɗaya"

godiya Suhail yayi mata ya tashi zai tafi har compound din ta raka sa su meerah na zaune inda ya barsu bai bi ko ta kansu ba yayi ficewar da daga gidan 


MUTANEN FACEBOOK INA GODIYA SOSAI DA LIKE DA SHARE DA COMMENTS 
MASU SO A SAKA SU A WHATAPPS GROUP ZAKU IYA MIN MAGANA TA SANNAN LAMBAR DUK NAMIJIN DA YA DAUKA ALLAH YA ISA BAN YAFE BA 

***