PART 1
Sunana A'isha, na yi aure ina da shekaru 15 a duniya, mijin dana aura duk kusan na gida ne, makocinmu ne amma baya zama a garinmu, mazauni Kano ne, a can ya yi karatu. Ya nuna mun soyayya fiye da yadda ake zato a farko, ƴan uwansa sun nuna mun soyayya a farko, a lokacin ina tashen kuruciya, ina da wanda nake so wanda kuma iyayena basu kaunarsa, na nuna bana son wannan mijin nawa, amma iyayena suka kafe lallai sai na auresa, aka aaura mun shi ta dole, amma shi yana matuƙar sona.
A lokacin farkon aurenmu babu irin haukan da ban mashi ba kan ya sakeni, amma ya daure saboda yana ganin ni yarinya ce kuma yana girmama iyayena, a lokacin zai kai shekaru 30 a duniya, ni kuma ina da 15 kawai. Ƴan uwansa sun nuna mun soyayya a farkon aurenmu, mamansa ta so ni a farko, kome nake so shi suke so suma, yakasance yana da kanne mata huɗu da yayarsa mace dake gidan miji ɗaya, su biyu ne maza wanda ɗayan kaninsa ne, ƙanin nasa karami ne da bai wuci 20 years ba, mijina ɗan kasuwa ne, yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, shi yake ɗaukar nauyin gidansu da kannen nasa gabaɗaya saboda basu da uba.
Tun bana son shi ina haukar zan fita in auri saurayina da nake so, har na hakura na zauna da shi saboda kyautata mun da yake yi, baya son ya ganni cikin damuwa, yana lallaɓani da kula dani spsai. Watarana na je Kaduna gida iyayena suka ce yakamata in fara sana'a, zama gidan miji shiru ba sana'a ba nawa bane, iyayena suna da kuɗi Alhamdllh, mahaifina ya kawo kuɗi ya bani matsayin jari, a lokacin da na dawo Kano gidan mijina kenan, na sanar da mijina iyayena sun bani jari in fara sana'a, ya bani goyan baya, kasancewar ya yi karatu mai zurfi sosai sai ya bani business ideas kala uku, na zaɓi na ukun watau sayar da su zannuwan gado da su laces.
Na fara business a hankali, iyayena kullum suna kara mun karfin gwiwa da saka mun albarka, mijina ma haka, komai na tafiya mun daidai har na fara manta wancan saurayin nawa, na yi ƙiba na yi kyau hankali ya kwanta.
Ina da kyauta sosai, hakan yasa ribar kasuwancina a lokacin duk yake karewa a kan kyauta ma ƴan uwa, dangi da abokan arziki, mutane suna sona sosai saboda kyautata. Cikin ikon ALLAH kasuwata ta karɓu abubuwa suka bunƙasa, na fara samun manyan kuɗaɗe, mijina yana kasuwancinsa shi ma cikin kwanciyar hankali sai dai abubuwa sun ja mashi baya sosai, kuɗi sun rage shigo mashi.
Amma hakan bai bayyana ga ƴan uwa ba, saboda nawa kuɗin, na cigaba da tallafa mashi da nawa kuɗin domin rufawa juna asiri, a hankali soyayya mai karfi ta ƙullu a tsakaninmu, dama shi already yana tsananin sona, nima na kamu da sonsa sosai, sai na sallama mashi komaina, ina kasuwanci muna kashe kuɗinmu tare cikin haɗin kai, har ta kai ta kawo shi ya rasa nasa kasuwancin, amma bamu wani damu ba, na ɗebi kuɗi daga nawa kasuwancin na bashi ya sake cigaba da juyawa, nima na mai da hankali kan nawa kasuwanci sosai fiye da baya, nauyin gida ya dawo kaina, iyayensa da ƴan uwansa nike masu komai ba tare da sun san ni nike yi masu ɗin ba, sun ɗauka shi ne, idan suka zo Kano suna ɗauka komai na gidan shi yake yi.
A wannan lokacin ALLAH ya albarkace mu da samun ciki bayan shekara da aurenmu kenan, ƴan uwansa da nawa sun yi murna matuƙa, na cigaba da kasuwancina ina renon ciki, na fara saro kaya daga ƙasashen waje ina kawowa Nigeria, komai ya cigaba a gareni, a haka har cikina ya shiga wata tara. A ranar haihuwa na haifo ƴan biyu dukka maza, lamarin da ya yiwa zanginmu daɗi, anyi murna anyi shagali sosai.
A haka rayuwa ta cigaba, shekaran ƴan biyuna biyu a duniya na sake samun wani cikin na uku, mijina bai taɓa canza mun ba, a lokacin ƴan uwansa ma basu canza mun ba, arziki ya fara zaman mun sosai da sosai, na fi mijina kuɗi nesa ba kusa ba a yanzu saboda ni dik kuɗin da nake nema bana komai dasu face karawa a kan kasuwanci saɓanin shi dake ɗaukar nauyin abubuwa da dama a kansa, dik da ina taimaka mashi sosai amma dole wasu shi yake yi.
Cikina na biyu na sake haifan ɗa namiji, a daidai wannan lokaci yayan Mamar mijina wanda ya rike mijina ya girma a hannunsa ya faɗi ya rasu, dangi sun yi kuka saboda shi ne babba, shi ne jigon dangin. Mun je gaisuwar rasuwansa kenan ƴan uwan mijina suka rikesa wai sai ya auri babbar ɗiyar kawun nasa, ya duba maraicinta ya aureta.
Mijina ya ce bashi da ra'ayin auren mata biyu, kuma yanzu abubuwa sun mashi yawa a kai, ba zai iya ba, dangi suka ce bai isa ba, saboda uban yarinyar shi ya rikesa tun yana yaro, dan haka ko dan alkhairin ubanta ya duba ya aureta, shi kam ya ce a'a ba zai iya ba, bashi da karfin rike mata biyu a yanzu, mahaifiyarsa ta yi fushi, ta ce lallai yazame mashi wajibi ya auri wannan yariya idan ba haka ba babu ita babu shi.
Abubuwa sun ɗauki zafi, mijina ya shiga damuwa da tashin hankali, bai san tayaya zai ɓullowa lamarin ba, hasalima baya son yarinyar da ake son haɗasu, bata mashi ba, ga shi yana jin nauyi da kunyan iyayena, abin da baku sani ba shi ne, mahaifina ne ya biya mashi kuɗin karatun da ya yi dukka, mahaifina ya mashi komai, shi ya fara ɗora shi a kasuwanci, yaron shagon mahaifina ne a baya kafin ya tafi makaranta, saboda hankali da natsuwansa yasa mahaifin nawa ya aura mun shi ashe, ni duk lokacin giyar yarinta na ɗebata ban san mahaifina ya biya kuɗin karatunsa ba, ban san komai ba, so ya ji nauyin tinkarar iyaye na da batun.
Ni ma ba zai iya zuwa ya gaya mun zai auri yarinyar ba, saboda duk abin da ake yi a dangi ban sani ba, meeting suka yi a gidan kakansu ban sani ba, so ban san ance ya auri yarinyar ba. Ina zaune a ɗakin mamata a gida ya shigo hankali a tashe, ina son tambayarsa me yake faruwa ya ce. "Ɗauki jakarki mu tafi".
Zan yi magana ya hanani, dole na miƙe na haɗa kayana dana yarana,a wannan rana muka koma Kano bamu sallami kowa ba, duk abin da ake yi ni ban sani ba. Komarmu da kwana ɗaya na kira Mahaifiyarsa dan in kara yi mata ta'aziya, tana ɗauka sai cewa ta yi. "Kin rabani da ɗana, har ni Sulaiman zai bijirewa umarnina saboda ke? To ki koma ki faɗawa bokanki yayi kaɗan, in dai juranku bin malamai da raba uwa da ɗanta ne wajen kuka zo, ki jirayi sakamako".
Hankalina a matukar tashi na ce. "Mama ban gane ba?"........ Cikin faɗa ta ce. "Ba zaki gane ba ai munafuka algunguma, har ni Sulaiman zai kallah ya ce ba zai iya maki abokiyar zama ba saboda in yai haka bai yi adalci ba, nasan ba laifinsa bane, dan ɗana mai biyayya ne, shiyasa na kyalesa, amma ki jira wlh sai na warware kullin da kika masa dake da iyayenki!!". Tana gama magana ta katse kiran.
Cikin tashin hankali na kira kanwarsa dake binsa. Kira uku bata ɗauka ba, na kira ta biyun ita ma bata ɗauka ba. Ina ƙoƙarin kiran ta ukun sai ga ta farkon mai suna Amina ta kirani, jikina har yana rawa na ɗaga, ina ɗagawa kafin in yi sallama na ji ta ce. "Munafuka me kuma kike wani kirana bayan kin rabamu da ɗan uwanmu?".
Tun daga nan na gane akwai matsala, sai kawai na kashe wayan ba tare da na yi mata magana ba, jikina na rawa na kira mijina, yana ɗagawa na ce. "Abban Hassan me yake faruwa?". Ya nuna mun bai san komai ba, ya ce. "A ina fa"........ Na ce. "A gida mana, meyake faruwa, Mama tana ta faɗa, ko na mata wani laifi ne?".
Ya ce. "A'a ki kyalesu kada ki sake kiransu zuwa su huce su sauka daga kan dokin zuciya"....... Na yi na yi ya faɗa mun me yake faruwa, amma ya nuna babu komai in kwantar da hankalina. A haka muka yi sallama sai na yi maza na kira kaninsa mai suna Abba. A lokacin Abba ya tafi ɗauko su Hassan a makaranta, dama Abba tare muke da shi a gidan ɗaya.
Abba na ɗauka ya ce. "Aunty ina tuƙi bari in isa makarantar zan kiraki"....... Cike da tashin hankali na ce. "Abba ba zan iya jira ka isa ba, kawai ka bani amsata, kuma tsakani da ALLAH zaka faɗa mun, meyakefaruwa a dangi?"...... Muna da kyakkyawan alaƙa tsakanina da Abba, yaro mai hankali da natsuwa, yana sona tsakani da ALLAH.
Dan haka ya kwashe labarin dik abin dake faruwa ya faɗa mun, cikin tsananin tashin hankali na miƙe tsaye, ina da zafin kishi sosai da sosai, ban san lokacin da wayata ta faɗi a hannuna ba saboda tashin hankali, mijina zai auri wata bisa umarnin iyaye da dangi?....... Babban magana.
Wannan shi ne farkon kaddarar A'isha a gidan aurenta, shi ne farkon labarin, labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔