LABARIN AISHA

PART 2

by @queenofsurprise1

Gabaɗaya sai na ji jikina ya saki, na rasa me yake mun daɗi, kaina na juyawa, a wannan wuni na gagara koda girkin dare ne, na zauna da tunani fal cikin raina, shin da gaske ne zai aureta? Meyasa sai shi dangi zasu zaɓa? Meyasa zasu juya mun baya? Hakan na nufin a kodayaushe ɗan uwanka ɗan uwanka ne? Ɗan uwan wani ba zai taɓa zama ɗan uwanka ba har abada ba, dole watarana sai ya nuna maka cewa ɗan uwan wani ne shi.

Abba ya dawo dasu Hassan, da yake sun saba da bappan nasu ko wajena basu wani zauna ba, suna dawowa ya cire masu uniform yai masu wanka, ya canza masu kaya ya basu abinci, shi ma bai shigo side da nike ba sai can yamma, ya shigo sanye da sportswear a jikinsa zai tafi buga kwallo da ya saba.

Tun daga bakin kofa kafin ya karasa shigowa ya fara tsokanata kamar yadda ya saba, sai dai yana shigowa parlo ya tsaya shiru yana kallona, tun in da na zauna ban bar wajen ba har karfe huɗu saura yanzu, almost awa biyu ina zaune a wajen.

Ya kalli parlon da kyau ya kuma kalleni, sai ya fahimci ina cikin damuwa, dama sau dayawa idan ina cikin damuwa Abba ke sakani farinciki, ya ƙariso ciki yana cewa. "Hajjajo lafiya kika zauna kaman an sassakaki? Ko dai kewata kike yi ne?".

Na ɗaga ido na kallesa amma ban yi magana ba, ya faɗaɗa murmushin kan fuskansa tare da zama a kusa dani, ya fara tsokanana yadda ya zaba, dole ba dan na so ba na fara murmushi, saboda ya saba ya san hanyar sakani murmishi, zan iya cewa ya fi yayansa iya zama da mutane sosai.

Sai da ya sakani dariya na fita daga kunci ne ya ce. "Faɗa mun wanda ya taɓaki in je in rama maki"....... Ina ƴar dariya a lokacin na ce. "A'a, wannan kam ba zaka iya rama mun ba nawan, sai shiru kawai"....... Ya ce. "Yaya ne ya taɓaki ko?"........ Na ɗan hararesa cikin wasa kafin na ce. "Kai da kasan komai, waye zai taɓani idan ba shi ba"

"Gaskiya yaya baya duba mana, a kan me zai dinga ɓata maki rai?". Ya faɗa cikin zoyala. Na ɗan yi murmushi, da yake maganar dake zuciyata ta tsaya mun sosai a kahon zuciya, na kasa danneta sosai, sai na ce. "Yanzu Abba meyasa yayanka ba zai auri yarinyar ba to? Ya duba maraicinta mana?". Na faɗi hakan ne ba wai dan hakan ne a raina ba, sai dan bana son kowa ya fahimci bana son haɗin, bana kuma son kowa yasan kishina a fili.

Abba ya ɗan yi kicin-kicin da rai kafin ya ce. "Aunty idan Yaya ya auri yarinyar nan bai maki adalci ba, na faɗawa Mama tun lokacin da ta tado da maganar nan, na faɗa mata yaya bashi da karfin rike mata biyu, yanzu ma fama yake yi, amma taki fahimta, saboda tana ganin duk abin da yake gidan nan yaya ne yake yi, bata san ke kike yi ba, na yi ƙoƙarin faɗa mata haɗarin dake tattare da wannan haɗi, amma ta ce in mata shiru ni yaro ne da ban san komai ba, to ni wlh bana goyon bayan wannan haɗi, kuma ba zan taɓa goyon baya ba, bugu da kari wannan yarinya da aka ce yaya ya aura bata da kunya, bata ganin kowa da daraja, mamarta ma haka, kina ji duk dangi zagin mamanta ake yi, mamanta fa har kwalar rigar babanta take kamawa tana ya saketa in shi ɗan halak ne, ai da karfi maman ta kashe aurenta ta shiga yawon duniya, har kotu ta kai kawun namu dan ya saketa, to ya za'ayi barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe? Wai sai ace a duba maraicinta da rashin uwanta a gidan, hmmmmm kowa ma hakuri yake a duniyar nan". Da iya gaskiyansa Abba yai magana.

Hankalina ya kara tashi jin irin halin mamar yarinyar da kuma yarinyar, na shiga damuwa sosai mara misaltawa, amma a gaban Abba ban nuna damuwar ba, na danne game da cewa. "Abba ba'a ja da maganar iyaye fa, amma kuma iyaye basu isa tilastawa yaro yin aure ba, zasu iya saka shi ya saki matarsa, amma a batun aure basu da hurumin tilasta mashi ya yi, saboda shi kaɗai yasan karfinsa da lafiyansa".

Abba ya ce. "Aunty bar dukka wannan zance ma, wlh yaya ba zai auri yarinyar nan ba, saboda bata da kunya, a lokacin da muka je gaisuwar rasuwar nan da aka yi maganar auren yaya ya ce ba zai iya ba, da ya fita ya haɗu da yarinyar, ya kirata, ina jinsa a bayan window ɗina ya ce mata ta je ta faɗawa dangi bata son shi in ba haka ba ranta ne zai ɓaci, da buɗar bakinta sai cewa ta yi ko yaki ko ya so sai ya aureta, iyaye sun zartar da hukunci, kuma ita ba wanda take so sai shi, magana without respect take mashi, da isa da gadara".

Nan fa na ji hankalina ya sake tashi, amma na danne dan in kara jin me dame aka ce a dangi bananan. Abba ya cigaba da cewa. "Ina ji mama ta dinga yi wa yaya faɗa saboda yarinyar ta je ta cewa Mama yaya ya zazzageta ya ce mata mara tarbiya kuma ba zai aureta ba, mama ta mashi faɗa sosai, ta bashi number Zainab ɗin wai kullum ya yi mata magana in ba haka ba bata yafe mashi ba".

A lokacin da Abba yake wannan magana ji nake tamkar guduma ake buga mun a kai, tsabar tashin hankali ban san lokacin da na ce. "Abba gara ka je wajen kwallonka kada lokaci ya kure maka". Na faɗi hakan ne dan ya tafi, ba zan iya jurar jin abubuwan ba, ashe abubuwan da suka dinga faruwa kenan da muka je gaisuwar, duk ban sani ba ni kam, dan a lokacin a gidanmu na sauƙa, da yamma na je family house ɗinsu nai masu gaisuwar na koma gidan babana, washegari ma da safe na sake zuwa na koma da rana, ashe duk abubuwan da ake ta yi kenan ba gaisuwar rasuwar ake karɓa ba, ashe a lokacin duk kallon banza suke mun, kuma yarinyar da aka ce ya aura Zainab, yarinyar ina haɗuwa da ita a gidan rasuwar, ko magana bata mun nima bana kulata, ashe duk kallon banza take mun.... Tashin hankali.

Abba ya miƙe yana cewa. "Aunty kuma haka ne, bari in je kada a buga a barni, me zaki dafa mana da daddare?". Yana murmushi ya faɗa. Na ɗan hararesa kafin in ce. "Ka dawo ka yi girki dan ba zan maka ba, na gaji da wahala da kai"....... Ya ɗan haɗe rai, yana da mugun shagwaɓa kamar ba namiji ba, saboda shi ne auta, kuma ya taso cikin mata har guda huɗu sisters ɗinsa, dan haka sai ya shagwaɓe fuska kafin ya ce. "In ajiyeki a gidan ki ce ba zaki mun girki ba? Kin ma isa? To wlh sakwara zaki daka mun da miyar egusi kafin in dawo".

Na miƙe ina faɗin. "Na isa har ma na yi yawa, wuce ka bani waje, ba abin da zan girka"......... Da yake yana da tsawo sosai, duk ban fi kirjinsa ba dana miƙe, sai ya zunguri tsakiyar kaina yana faɗin. "Da kuwa na baki red card"......... "Yellow dai zaka bani ba red ba, wuce mun daga parlo tun wuri, kuma ka yi maza ka nemo matar aure tun ban gama gajiya da kai na watsarka a bola ba". Ina ɗaure fuska na faɗa, mun saba irin wannan wasa da shi sosai, har fin haka ma.

Ya ɗan shagwaɓe fuska kafin ya ce. "Please my Aunty mu bar wasa me zaki dafa mana?"....... Da yake ina son ya tafi sai na ce. "Abin da ka fi so, kai dai jeka, ai kasan wajen girki baka da matsala dani"..... Ya ɗan yi murmushi har dimple ɗinsa irin na mamansu ya lotsa kafin ya ce. "Shiyasa nake sonki matar yaya, ki saka mana barkono kaɗan".

Na hararesa ban yi magana ba, saboda ni damuwata kawai ya fita ya bani waje. Ya juya yana mun sai ya dawo, na amsa da a dawo lafiya, ya shiga ɓangarensa ya ɗauki Hassan da Hussaini suka wuce zai kaisu islamiya kafin ya wuce wajen buga kwallonsa.

Yana fita na shiga ɗaki na rushe da kukan da ban san yaushe ya kwace mun ba, kukana ya tashi jaririna daga barci, Muhammad ya tashi ya fara kuka shi ma, na ɗaukesa muka cigaba da kuka tare. A wannan wuni ban yi girkin dare ba. Karfe 6 Abbinsu ya dawo daga kasuwa, side ɗinsa ya shige kamar yadda ya saba. Ina jinsa ban fito na tarbesa yadda muka saba ba, ko wanka ban yi ba, in da na zauna rike da Muhammad ina kuka har ya mai da barci ban matsa daga wajen ba.

Abbinsu ya yi wanka, ya shirya zuwa masallaci ya fito, lokacin an tada hiƙama, tabbas ya so shigowa side na ya duba meyasa ban fito na tarbesa yadda muka saba ba, amma bai samu damar shigowa ba saboda an fara sallah, dan ya samu jam'i ya wuce.

Sai bayan sallah ishai suka shigo dukkansu har Hassan da Hussaini dake wajen Abba. Dama mun saba bayan sallar ishai muke haɗuwa mu ci abinci. Kai tsaye ɗakina Abbinsu ya shigo, ina kwance kan dadduma, sallar ma da kyar na yita, ban saba da irin wannan tashin hankali ba, na taso cikin gata da kulawa, kome nake so shi nike samu, ban taɓa neman abu na rasa ba, kullum cikin farinciki nike, yau ce bakincikina na farko a rayuwata dole hankalina yai mummunar tashi.

A gabana Abbi ya tsugguna tare da cewa. "Habibi lafiya yau ko motsinki ban ji ba?". Wani irin kuka na ji ya zo mun, amma na daure game da cewa. "Bana jin daɗi ne".......…... Ya kalleni da kyau kafin ya ce. "To meyasa baki faɗa mun ba?"...... Na yi shiru ban amsa ba, saboda maganar ma bana son yinta, haushin kowa nike ji.

"To tashi mu je ki ci abinci sai ki sha magani"........ Na yi banza da shi. Yasa hannu ya ɗagani, na ce. "Dan ALLAH ka barni, bana son cin komai, ni ban ma girka komai ba".

Ya ce. "Bar batun girki, me zaki ci sai in sayo maki, girkin zan mana yanzu"...... "Ba zan ci komai ba". Na bashi amsa a gajarce, na koma na kwanta. Ya sake kai hannunsa kumatuna. "Menene yake maki ciwo?".

A taƙaice na ce. "Abbi kaina ke ciwo kuma na sha magani hutu nake buƙata dan girman ALLAH ka rabu dani". Daga haka ban sake mashi magana ba, dole ya rabu dani dan ya yi ta yi ban amsa mashi ba. Ya miƙe ya fito parlo. Ya shiga side ɗinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya ya shiga kitchen yana faɗin. "Abba bari in maku girki Auntynku bata jin daɗi".

Abba ya amsa da okey, sai ya miƙe ya shigo ɗakina, ya ganni kwance in da yayansa ya barni, cike da kulawa ya mun sannu ya jiki, ina jinsa ban amsa ba, sai ya zaci barci nike yi, ya juya zai fita Muhammad ya tashi ya fara kuka. Da sauri ya zo wajen gadon ya ɗaukesa wai dan kada ya tasheni, ya fita parlo da shi, ya shiga kitchen ya haɗa mashi madara, ya fito ya zauna a parlo, yana bashi yana jijjigasa har ya ƙoshi. Sai ya kwantar da shi ya bi yayansa cikin kitchen dan tayasa aiki.

A tare suka yi girki suka gama, suka zuba mun, ba yadda yayansa bai yi ba naki ci, ya ce me nike so naki magana, dole ya hakura ya barni. Abba ya shigo da Muhammad, ya kwantar da shi a gado ya fita bai mun magana ba saboda yayansa na ɗakin. Ya je ya kama hannun Hassan da Hussaini suka wuce nasa side ɗin, dan tun bayan da na yaye yaran a side ɗinsa suke.

Ba yadda Abba bai yi ba naki faɗa mashi abun dake damuna, dole ya hakura ya yi shirin kwanciya, muka kwanta nai kamar na yi barci har zuwa lokacin da yai barci. Yana yin barci na miƙe na jawo wayansa, da yake nasan password ɗinsa, bamu ɓoyewa juna komai, harta account balace ɗinsa na bank duk nasan komai.

Kai tsaye na buɗe wayan na shiga Whatsapp dan duba maganarsa da Zainab tun da mamansa ta ce kullum in bai yi mata magana ba bata yafe ba. Ina shiga kan number Zainab na chat ɗinsu naga abin da ya yi matukar girgizani, hannuna har rawa yake wajen scrolling chat ɗin na yi sama, nan naga zafafafan................

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

LABARIN AISHA.🥹💔