PART 3
hannuna har rawa yake wajen scrolling chat ɗin na yi sama, nan naga zafafafan kalaman soyayyar da Zainab take turo mashi, da safe misalin ƙarfe 6 tana turo mashi na barka da safiya, da rana around 12 tana turo mashi na barka da rana tare da tambayar ya kasuwa, da yamma karfe 6 tana turo mashi, sai kuma da daddare karfe 9 tana turo masu zafafa masu kwantar da hankali wai yai barci cikin salama sai kace an ce mata dan ubanta da a cikin azaba yake barci, babu abin da ya fi bani takaici kamar yadda a kasan addu'oi da kalaman soyayyan take rubuta ina son ka yi barci cikin salama da natsuwa wanda baka taɓa samun irinsa ba, wannan abin ya fi komai kona mun rai, a raina na ce dan ubanki da cikin azaba ko cikin jahannama yake barci ba salama ba?, sannan ba iya kalaman soyayya bane kawai take tura mashi, harda kalamai masu motsa sha'awa dan bata da kunya, ko ni da nike matarsa bana mashi wasu kalaman wlh.
(Kai Aisha zata kasheni da dariya, wai dan ubanta da cikin azaba yake barci ne, kai wlh matan da ake neman aurensu a wajen nan gani fa suke kamar na gida bata iya kula da miji ba shiyasa ya je neman aurensu, suna ganin kamar zasu fi kowa iya kula da shi, sun ɗauka auren wasan yara ne ko kalaman soyayyar da suke yi a wajen ne auren, sai sun shigo zasu gane wannan hakuri da ake cewa aure ɗan hakuri ne, sai sun shigo zasu gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne, amma dai mu bi Aisha ta cigaba da bamu labari, zamu ga shin da gaske uwayen gida basu iya kula da mazansu bane yake sanyawa a karo masu kishiya ko kuwa dai jarabace irin na mazan kawai!.)
Na duba yanayin reply da yake yi wa Zainab, iyakarsa uhm ko okey, Zainab zata mashi dogon voice note mintuna 5 zuwa 7, amma sai naga wlh bai buɗe voice ɗin ya ji ba sai ya rubuta mata okey a ƙasa, bai fa san me ta ce a voice ɗin ba, amma yake saka okey. Tsabar ƙoƙari irin nawa na zauna na dinga buɗe voices ɗin, na sanya earpiece na dinga jin voice ɗinta. Wani waje in ji tamkar in shaƙeta saboda takaici, na yi godiya ga ALLAH da yasa Abbie bai saurari voice ɗin ba ni na buɗesu.
Ta wani make murya, wani waje har da kukan makirci dan ta ja hankalinsa, wani voice da ta yi na tsawon mintuna 7 gabaɗaya halin kishiyar mamarta take faɗa mashi, wai tin da babansu ya rasu yanzu kishiyar mamansu bata bata abinci ishasshe, wai yanzu kaɗan-kaɗan za'a dinga cin abinci kar ya rinƙa karewa da wuri, a voice ɗin ta dinga rusa mashi kuka da nuna alamar tana cikin tashin hankali, a karshe ta ce kullum tana addu'a aurensu ya zo da wuri ya ɗauketa daga gidan nan dan tasan shi mai tausayi ne zai tausaya mata ya kula da ita.
A raina na ce shegiya makira, da can ba tare da kishiyar mamar taki kuke zaune ba, a lokacin duk baki san tana gana maki azaba ba sai yanzu kenan, kuma abin da ya kara bani takaici Zainab ta fini shekaru, dan a lokacin ina da shekaru 20 a duniya, na yi aure ina da shekaru 15, na haihu na fari ina da shekaru 16, na sake samun cikin na biyu ina da shekaru 18, Hassan da Hussaini suna da shekaru 2 kenan, na haifi Muhammad ina da shekaru 19, yanzu Muhammad ya kusa shekara ɗaya, kunga ina da shekaru 20, ita kuma Zainab ta girmi Abba kanin Abbie ma a shekaru, dan Abba yana da 25 years yanzu, ita kuma tana da 27, to shi ne abin da ya fi bani takaici, kallon yarinya karama take mun, dan a cikin chat ɗinsu na ga in da take ce mashi ai Aisha kanwata ce, da auren kauye nema da na haifeta, wannan abu ya bakanta mun rai matuƙa.
Amma danaga irin reply da yake mata, na gane he didn't pay attention to her, na samu peace of mind sosai, na goge duka voice da ta mashi waɗan da dama bai jisu ba, sannan na mayar mashi da wayansa na yi kwanciya.
Washegari da safe muka sake tashi da wani tashin hankalin kuma, Abba ya yi wa su Hassan wanka ya kaisu school ya biya kasuwa yai mana cefenen provision yana dawowa kawai sister ɗinsu ta kirasa wai gata ta shigo Kano ya zo ya ɗauketa. Muna zaune a kan gado ni da yayansa ina tuhumansa a kan me yake magana da yarinyar, ina faɗa mashi na ji duk abin da yake faruwa, meyasa bai faɗa mun ba ya bari na ji a gari, muna tsaka da wannan magana sai ga kiran Abba.
Abbie ya ɗauka Abba ya faɗa mashi ai Aunty Babba ta ce ta shigo Kano ya zo ya ɗauketa yanzu, Abbie ya ji takaici sosai, amma ya ce babu komai ya ɗaukota ɗin, bai nunawa Abba kamar akwai damuwa ba, amma hakika ya shiga damuwa saboda yasan ba alkhairi ne zai kawota ba, ashe basu yi rabuwar daɗi da ita ba lokacin da muka je Kano.
Abbie ya kalleni ya ce. "Saboda nasan ba auren Zainab zan yi ba shiyasa ban faɗa maki ba, amma ba wani abin bane"..... Na ce. "Na ji kamar Aunty Farida ce aka ce ta zo ko?"........ Abbie ya jinjina kai game da cewa. "Ita ce, ni zan fita kasuwa, ki mun addu'a, ki mance da wannan zance, ki ciresa a ranki, ni Zainab bata mun ba, bana sonta, idan buƙatar karin auren takamani da kaina zan nemo mai hankali da zata girmamaki ba sai an nemomin ba".
Na ɗan ji sanyi a raina, amma ba sosai ba, ya tashi ya yi wanka ya shirya fita kasuwa, a gurguje ya yi komai dan baya son haɗuwa da Aunty Farida. Kafin Abba ya daukota Abbie ya fice daga gidan. Na tashi nai wanka nima, ko breakfast dama ban girka ba, su Hassan ma ragowar abincin jiya uncle ɗin nasu yai masu warming ɗinsa suka ci ya ɗauka masu snacks da drink ya sanya masu a lunch box suka tafi da sunan mammynsu bata da lafiya kada a tasheni shiyasa yai masu hakan.
Ina ƙoƙarin shiryawa na fito daga wanka kenan na ji shigowarsu parlo, gabana ne yai wani mummunar faɗuwa. A hanzarce na shirya na fito. Ina fitowa sai da na ji kaina ya wani buga da karfi saboda ganinta da na yi da babban ɗanta da mai binsa. Dama wannan babban ɗan nata a farkon aurenmu da Abbie mun zauna da shi, ya zauna wa Abbie a shago kafin ya yi wa Abbie sata Abbie ya koresa, zaman shekara ɗaya muka yi da shi a baya, na rike yaron nan tamkar kanina, ina bashi duk abin da yake so amma shi bai rikeni haka ba, da Abbie ya koresa ne sai ya ɗauko kaninsa Abba ya ajiye a ɗayan shagonsa ɗin kafin ya haɗu da jarabawa ya rufe shagon Abba kuma na mayar da shi makaranta saboda jininmu ya haɗu, yanzu yana 4 hundred level, computer engineering yake karanta.
Na ji faɗuwar gaba ganinta da yaran nata, dukkansu manyan samari ne, babban ya kai 26 years dan ya girmi Abba, mai bi mashi 21 years yake da shi, shi ne mate ɗina ko in ce ya fini da kaɗan.
Na ce mata. "Sannu da zuwa Aunty Farida". Tana mun wani gani-gani, bata amsa ba sai da ta zauna a kan kujera tana wani shan kamshi, sannan ta amsa game da cewa. "Ina Sulaiman ɗin yake? Ya fito ga yaran nan na dawo mashi da su, dan ba zai yiwu yana da ƴan uwa ya bar bare suna shiga cikin arzikinsa ba"........ Na gane dani take yi, tana tunanin shagon abayars da nike da shi na Abbie ne, and ƙanina mai bi mun na saka a shagon da sauran ma'aikata, ƙanina Manager ne, yana zuwa school tare da Abba, idan ya dawo zai je shago ya duba me ya shigo me ya fita, sho kuma Abba burin kwallon kafa yasa a gaba sai ya tafi buga ball, to shi ne wai ta kawo yaranta su suka cancanci su rike wannan shago ba wasu bare ba tun da shagon ɗan uwansu ne a tunaninsu.
Na yi kamar ban jita ba, na wuce kitchen na ɗauko masu ruwa, ina ajiyewa ta ce. "Abinci zaki kawo mun ba ruwa ba, saboda kwanaki na zo yi ba wai na zo yau zan koma yau ba ne".......... Na ɗago na kalleta kafin in ce. "Aunty Farida ban taɓa tunanin jin irin waɗan nan kalamai daga gareki ba, a tunanina ko su Amina zasu canza mun ke ba zaki canza mun ba tun da ke babba ce a kansu, kuma kin yi aure kin san me auren yake nufi, ban san laifin da nai maku ba, and baki taɓa zuwa gidan nan in ce maki tashi ki koma ba, hasalima ni nike gayyatarku da ku zo mu yi hutu tare, meyasa kike jefana da kalaman dake nuna bana son ku raɓi ɗan uwanku?".
Ta kawo salati ta zabga, cike da faɗa ta ce na faɗa mata maganar banza, wai na zageta, kenan ita bata da hankali, tana matsayin yayar mijina zan zageta. Babban ɗanta ya miƙe yana wani bubbuɗewa wai a kan mahaifiyarsa babu abin da ba zai iya ba, babu wanda ba zai daka ba, ba'a haifi wacce zata zagi mahaifiyarsa ya kyaleta ba, yai kaina kamar zai kai mu duka, ga shi da kirar bujumaye. Da sauri na ja da baya ina kallonsa da mamaki.
Abba ya ce. "Khalifa kana da hankali kuwa? Giya ka sha ne kafin ku zo da kake ƙoƙarin kai mata duka?". Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri na juya na shiga kitchen na bar masu wajen, ina jiyo muryoyinsu suna musayan yawu da Abba, Khalifa ɗin ya ce zai dagi Abba, amma kuma Abba ya fisa karfi da jiki mai kyau, coz Abba ɗan kwallo ne sosai, kullum yana cikin buga ball, dalilin haka yasa yake motsa jiki, yana da burin zama shahararren ɗan kwallo a duniya, shi kuma Khalifa kaman wani ɗan daba haka yake, ba arabi ba boko sai shiga faɗan mata a gida, in short ɗan daban unguwa ne kawai Khalifa, amma baya shaye-shaye. Kanin Kalifa mai suna Fahad yaro ne mai hankali da natsuwa, ya yi karatu sosai musamman ɓangaren addini, so ya banbanta da Khalifa, sai ya koma gefe yana jinsu bai saka baki a rigimar ba.
Ban san ya suka kare ba daga baya na ji parlon shiru. A daddafe na yi girki na kawo masu parlo, sai na samu basa nan, Aunty Farida ta shiga ɗakinsu da suke sauƙa idan sun zo, Abba da Fahad sun fita, Abba yana da class karfe 11 dama, ya je shiryawa, shi kuma Khalifa kato da shi ya kwanta mun a saman kujera ya baje yana barci. Takaici tamkar in mutu, amma na daure.
Na bi Aunty Farida da abincin cikin ɗaki, tana ta wani bina da mugun kallo har na ajiye abincin na fita bata yi magana ba. Nima ban mata magana ba. Ina fitowa na shiga side na Abba. A bakin kofa na tsaya na yi knocking, ba jimawa ya buɗe, yana shirye cikin dakakkiyar shaddarsa fara tas, ya kammala shirin zuwa school.
Yana ganina ya yi murmushi har dimple ɗinsa suka lotsa game da cewa. "ALLAH ya ja da ranki hajjajo matar babban yaya, ALLAH ya kara maki hakuri, ya aka yi?"......... "Zo ka ci abinci". Na faɗa game da juyawa ina jin kaina na wani irin sara mun.
Da sauri Abba ya riko hannuna wanda yasa na juyo, ya ce. "Please Aunty don't mind what they're saying, kina da ilimi da hangen nesa, ki cigaba da hakuri watarana komai mai wucewa ne, and please keep smile like the way you are"......... Na ɗan yi one sided smile tare da cewa. "Yaushe nawan ya koma yin wa'azi?". Na faɗa ina ɗaga mashi gera guda....... Ya saki hannuna yana murmushi ya amsa da. "Ba dole in iya wa'azi ba ko dan saboda ke, and waye ya ce maki dama ban iya ba?".
"Ina ka yi to? Ban da harkar kwallo ai kai babu abin da ka saka a gaba, ko makarantar nan ma da ban tsaya tsayin daka ba ba yi zaka yi ba, ni dai fito ka ci abinci ka wuce kada lokaci ya kure maka". Na kai karshe tare da wucewa ina harararsa cikin zolaya. Yana murmushi ya koma ciki.
Na zo na fito masu da abincinsu parlo sannan na koma ɗaki, na gagara cin abinci saboda wannan musifa data kunno kai. Ina zaune a ɗaki Abba ya shigo yi mun sallama zai tafi, na mashi fatan alkhairi ya ce mun yana son kuɗi, na ɗauki dubu goma na bashi muka yi sallama, ya fice ni kuma na tashi Muhammad nai mashi wanka, na shiryasa muka sake kwanciya.
Ina tsaka da kwanciya sai ji nai Aunty Farida na kwala kiran sunana har ta shigo cikin ɗaki. Da sauri na miƙe zaune ina amsawa. A bakin kofa ta tsaya tare da cewa...........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔