PART 4
Ina tsaka da kwanciya sai ji nai Aunty Farida na kwala kiran sunana har ta shigo cikin ɗaki. Da sauri na miƙe zaune ina amsawa. A bakin kofa ta tsaya tare da cewa. "Sarauniya sarkin kwanciya, ina abincin Khalifa?".
Na miƙe ina kallonta, cikin raunin murya da takaici na ce. "Abincinsa na cikin kitchen"........ Ta wani harareni kafin ta juya ta fita, na rasa me yake mun daɗi, ban saba da irin wannan tashin hankali ba, wayana na jawo na kira mamana, na gagara faɗa mata halin da nike ciki, bayan mun gaisa ta tambayi lafiyar yarana, na ce suna nan lou. Muka ɗan taɓa hira, ta so ta fahimci ina cikin damuwa, amma da ta tambayeni sai na ce mata babu komai. Muka yi sallama na kira sisterta wacce take bina. Bugu ɗaya ta ɗauka tana cewa. "Masoyiya tun jiya ban jiki ba". Kawai sai na ji kuka ya kwace mun.
Katse kiran na yi ban amsa mata ba, ina jinta tana ta rattaɓa mun kira amma naƙi ɗagawa, daga karshe dole ta hakura ta barni. Haka na wuni a cikin wannan gida zuciya babu daɗi, na takura a ɗaki zuwa karfe 1 na fito na ɗaura lunch, Aunty Farida na ɗaki.
Na kammala abinci around 2:30, na ɗauki na Aunty Farida zan kai mata, dab zan shiga ɗakinta na ji tana cewa. "Wlh Mama komai a gidan nan akwaisa enough, sai wadakarsu suke yi, kawai umarninki ne Sulaiman ba zai bi ba, gara kawai ki tattara kayanki ki zo ki zauna har sai bayan auren, idan an yi auren ma ki tsaya tsayin daka dan kada wannan Aishar ta cutar mana da ƴan uwa Zainab".
Hankalina ya yi bala'in tashi, jikina yana rawa, ina ta addu'ar ALLAH yasa dukkan wannan abin mafarki ne. Daga in da nike tsaye ina jiyo muryan Mama a cikin wayar tana cewa. "Tabbas na sani dama, nasan Sulaiman yana da komai a wadace, kawai umarnina ne ba zai bi ba, amma barni da shi, nan da kwanaki uku dole in zo da kaina ba saƙo ba, amma sai na fara zuwa gidan Liman ya bani rubutun karya asirin nan dan in zo da karfina".
Aunty Farida ta amsa da. "Yauwa Mama, ki faɗawa Kawu Liman har da Abba ta yi wa asiri, ta mallake ba iya Sulaiman ba, dan wlh baki ga ɗazun Abba wai zai dagi Khalifa saboda ta zageni Khalifa ya ce zai daketa ba"......... Mama ta ce. "Ta zageki? Aishar ce ta zageki?"......... "Wlh mama zagina ta uwa ta uba ta yi mun, wai mun zo zamu cinyewa mijinta abincin gida, ni da farko ma fushi na yi na ce zan dawo, amma da na tuna abin da ya kawoni, na tuna ceto ɗan uwanmu zamu yi sai na hakura na shanye, amma baki ji irin zagin da ta mun ba, har da ce mun matsiyata ƴan yunwa". Ta kai karshen maganar tana matso kukan munafurci.
Na ji tsoron ALLAH na ji tsoron mutum, ban san lokacin da hawaye suka fara zubo mun tamkar an buɗe tap ba, haƙiƙa ban taɓa sanin ya makirci da munafurci yake ba sai yau, Aunty Farida ta gwada mun na gani, ban iya ɗauka ba a lokacin, sai nike jin tamkar zuciyata zata fashe, kafafuna suka gaza ɗaukana, na durkushe a wajen ina kuka, na ajiye abincinta a ƙasa.
Ban san lokacin da ta kammala waya da Mama ba saboda tashin hankali da na shiga, sai da na ji ringing ɗin wayata a ɗaki ne na farga, da sauri na miƙe, na bubbuga mata kofa, ta ce in shigo, na goge hawayena, kaina a ƙasa na yi sallama game da tura kofa na shiga.
Ban kalleta ba na wuce na ajiye abinci na fito, da sauri na dawo ɗaki na ɗauki wayana. Abbie ne yake kirana, da sauri na bi kiran, ya katse ya kirani, ina ɗagawa ya hau mun jajen wuni da Aunty Farida, dan yasan masifarta. Ban nuna mashi komai ba saboda yana kasuwa, na ce lafiya lou, amma ya fahimci babu wani lafiya lou kawai ina ɓoye mashi ne, sai ya kara bani hakuri yana dannata, mun jima muna waya har na manta da kuncin da nike ciki, ya dinga lallaɓani da kalamai masu kwantar da hankali.
Sai karfe 2:30 muka yi sallama, ina ajiye waya sai ga kiran Abba, na ɗauka, cikin zolaya ya ce. "Kada ki wani ja mun aji already na mallakeki na ajiye a gida, dan haka da na kira ki ɗauka da wuri"........ Na ɗan yi murmushin karfin hali kafin in amsa da. "Ai mu mata ko a ina muke jan aji dole ne".
"Duk ba wannan ba, ya kika wuni da Aunty Farida?". Ya faɗa yana driving a hankali............. "Uhmmm, ya baka dawo da wuri ba?". Na faɗa a ƙoƙarina na kawar da zancen Aunty Farida. Ya ganoni sai ya ce. "Canza topic zaki yi saboda baku wuni ta daɗi ba ko?"....... "Canza mun magana zaka yi? Ni na ce maka bamu wuni ta daɗi ba?". Na faɗa ina sauke ajiyar zuciya, coz hankalina ya kwanta, Abbie da Abba sun sakani farinciki.
"Nasan halin Aunty Farida ne ai, gani nan zuwa gidan ma, na gagara hakura ne kawai na ce bari in kiraki tun kafin na iso in ji ya kuka wuni, coz yanzu muka fito daga class zan je ɗauko su Hassan"........ "To ka mai da hankali ga driving ALLAH ya tsare sai ka dawo zamu yi magana, ni ina cikin ƙoshin lafiya". Ban jira amsansa ba na katse kiran, na buga uban tagumi ina tunanin rayuwa.
Abba ya wuce makarantarsu Hassan ya ɗaukosu suka dawo gida. Tun da suka dawo ban fita ba, a ɗaki Abba ya zo ya sameni, ya yi ta jana da hira mai kwantar da hankali dan in samu farinciki, sai lokacin sallar la'asar ya mun sallama ya fita. Na fito na kama Hassan da Hussaini yau da kaina na masu wanka, na saka masu uniform na islamiya, na basu abinci suka hau ci kafin Abba ya zo, na shiga ɗaki na yi alwala na yi sallah nima.
Ina idar da sallah sai ga Abba ya shigo, hannunsa rike da wani bakin leda, ya miƙa mun yana faɗin. "Kayan lambu sun fara shigowa, na sanki da son garden egg shi ne na gani ana tallah na saya maki". Na karɓa ina godiya, yau tun safe ban ci komai ba sai wannan yalon da ya saya mun, na karɓa na wanke, na yankasa, na zuba a plate na dawo parlo.
Ya kama hannunsu Hassan zasu fita kenan ya ganni a parlo da garden egg ɗin ina ci, ya zo ya ɗauki yanka ɗaya, ya ɗauki biyu ya baiwa Hassan ɗaya Hussaini ɗaya, ya wuce ɗakinsa ya shirya cikin kayan kwallon, suka fito tare da Fahad ɗin Aunty Farida dake ta faman barci tun ɗazun. Fahad ya gaidani a mutunce, na amsa, sannan suka mun sallama suka fita.
Haka na kwashe kwanaki uku da Aunty Farida a cikin gidan nan, daga ni har Abbie lamarin babu daɗi kullum muna cikin damuwa, a ranar kwanaki na ukun ne Mama ta diro garin Kano, daga nan tashin hankalinmu ya kara ninkuwa, a daren da ta zo babu wanda ya yai barci, ta dinga faɗa, ta zagi Abbie tas, ya zauna ya dinga bata hakuri, ni kam nawa zagin ko kuda ba zai tauna kalarsa ba, na ji tamkar in gudu a wannan dare in koma gidan iyayena.
Amma na daure, tun karfe 10 da mama ta iso bayan ta gama zaginmu tasa aka kunna mata wuta a bunner, ta hau banka mana hayaki a gida wai makarin asiri, ban isa in yi tari ba ta ce asirin ya fara komawa kaina kenan, ta zaunar damu a parlo wai dole hayakin ya shiga jikin kowa, maganin bashi da daɗin shaƙa sai warin ruɓaɓen nama, amma haka muka zauna, ta dinga zuba kala-kalan ganyayyakin har 2 na dare, da wannan ya kare zata saka wani.
Tun ina danne kukan dake raina har na kifa kaina da gwiwa na hau kuka ciki-ciki, kowa ya sunkuyar da kai ba halin ya yi magana. Mama ta ce ina kuka ne saboda asirin yana dawowa jikina, ban ce komai ba, na cigaba da addu'a a cikin raina har lokacin da ta gama abin da zata yi ta ce mu je mu kwanta.
Muna miƙewa Mama ta ce. "Kai Sulaiman dawo, ai ba zaka kwana da ita ba, dan kada ta sake maka wani asirin, ka shiga ɗakinka ka kwanta, ni ina nan parlo zan ga kome da zai wakana a gidan nan"....... Ban tsaya sauraren Mama ba, na wuce ɗaki da sauri ina rungume da Muhammad dake barci.
Abbie ya shiga ɗakinsa bisa umarnin Mama, haka ina ji ina gani muka kwana waje daban-daban. Ba shi ne babban tashin hankali ba, ashe tashin hankalina na gaba. Washegari Mama ta hana Abbie leƙa ɗakina, wai ta mashi iyaka dani har sai ta karisa karya asirin nan, na kwana bakwai za'ayi. Haka ya tafi kasuwa bamu gana ba, girki Mama ta hanani yi wai kada in barbaɗa masu maganin mallaka in mallake har da ita, Aunty Farida take girki, ni kam na zama tamkar hoto a cikin gidana, su girka son ransu, sai abin da suka bani zan ci.
Abbie yana zuwa kasuwa ya kirani a waya, ina ɗauka ya fara bani hakuri, na ce mashi babu komai watarana komai mai wucewa ne, Abbie yai ta saka mun albarka, muka ɗan taɓa hira yana kwantar mun da hankali, amma yana katse kiran na rushe da kuka mai ban tausayi.
Ina cikin wannan kuka Abba ya shigo ɗakina. Ya zauna a gefen drawer yana bani baki, na gagara danne kukan, sai na kifa kaina a jikin pillow, na gagara saba ɗaukar wannan ƙaddara. Ana haka Mama ta shigo ta samemu, ta hau salati tana sallalami, wai na mallake mata ɗanta Abba, shikenan Abba ma na rabata da shi, har zuwa yake yana rarrashina.
Abba zai yi magana ta daka mashi tsawa, ta korasa waje, sannan ta ɗauki Muhammad ta fice da shi wai ba za'a sake barina da kowa ba har sai an gama maganin makarin asiri.
A wannan rana na gagara hakura, na ɗauki wayata na kira babban yayana, ina kuka na sanar da shi duk abin da yake faruwa dani. Ya natsu ya gama saurarana tas, da yake namiji ne shi, sai ya ce. "Ki ce da Sulaiman ya karɓi auren yarinyar kawai, ya aureta ta zo ta ci me kike ci a gidan, ki kwantar da hankalinki ki natsu ki saurari abin da zan faɗa maki".
Ina kuka na ce. "Yaya ya aureta fa ka ce?".....
"Kwarai ya aureta na ce A'isha, ki natsu ki ji me zan ce maki"........ Sai na ji na tsani Yaya, na ji wani irin kuka ya sake kwace mun, na kirasa in samu sauki yana neman kara mun abin da zai fasa zuciyata, ta yaya zai ce in yarda Abbie ya auri wata?.
Yaya ya cigaba da bani baki har na yi shiru, sannan ya ce. "Ki tattare komai ki ajiye a gefe, da zafi na sani, amma idan kika daure kika bi shawarina ke ce da riba, ki bar Sulaiman ya auri yarinyar, ki nuna mashi kina son hakan kina goyan bayan hakan, kada ki taɓa nuna mashi baki tare dashi, ki kau da kai daga abin da ƴan uwansa ke cewa, nan da kwanaki biyu mu sake yin magana kin ji? Jeki yi abin da na sakaki, a hankali mataki-mataki zan dinga faɗa maki yadda zaki tafi da komai na rayuwarki, ki yarda dani kanwata".
A lokacin ba wai dan na yarda da shi ɗin ba na amsa da okey, sai dan kawai bani da zaɓi. Mun yi wannan shawara da kwanaki biyu zuwa uku ban samu damar magana da Abbie ba, ban faɗa mashi ya auri yarinyar ba, Mama ta rike mana wuta, ta saka mu a gaba, ta rabamu da juna, bana samun damar ganin Abbie.
A rana na huɗun ne cikin dare na fito na saci hanya na shiga ɗakin Abbie Mama ta yi barci, sai dai ina shiga na iskosa manne da waya a kunne yana waya kwance a kan gado. Yana ganina ya firgita ya cire wayar daga kunne. Na mashi kallo tuhuma ban yi magana ba, zazzaɓi tamkar zai kasheni, dan Mama ta ɗauke Muhammad, ta rabani da shi, nononsa ya cika tab amma ba damar ya sha, cikar nonon ya ja mun zazzaɓi, yau kwanaki biyu kenan bai sha nono na, sai kunu Mama take bashi, idan yaƙi karɓa ta mashi ɗure, su Hassan da Hussaini duk Mama ta hanasu zuwa in da nake, tana zaune a parlo ha mai shigowa ɗakina, masifar ta kusa fin karfin zuciyata.
Abbie yai saurin kashe wayansa switch off gabaɗaya yana faɗin. "Mama bata parlo ne?"....... Barazanar da kaina yake mun ne tarwatsewa ne yasa na juya na fasa yi mashi magana, saboda zuciyata na zargin da waye yake magana a wannan lokaci haka? Karfe 11:30 yanzu da waye zai yi waya? Wannan yasa na gagara yi mashi magana, da sauri na juya na fita.
Ban tsaya ko'ina ba sai ɗakin Mama, na shiga da sallama, tana kwance a gado tana barci. Sallamana yasa ta farka, ta dinga koran shaiɗan da sunan tana addu'a kada asirin da na zo da shi ya kamata.
Na daure na kariso ciki, a gaban gadonta na tsuggunna, cikin girmamawa na ce. "Mama dan girman ALLAH, ba dan ni ba, ki ji tausayin Muhammad ki bani ya sha nononsa, Mama ki tuna ko shekara yaron nan bai cika ba, ke uwa ce, kin san illar yankewa yaro nono, dan girman ALLAH ki tausaya mashi ki tausaya mun ki bani shi".
Buɗar bakin Mama ta ce. "Idan kinga na baki ɗan nan to an gama maganin nan ne, dan haka ki tashi ki fita mun daga ɗaki, kuma kada ki sake shigowa". Cikin faɗa ta faɗa. Ina kuka ina kallon ɗana, yana kwance yana barcin wahala bayan ya sha danna an ɗura mashi kunu, sai nike jin tamkar ba zan fita in barsa ba, amma haka na juya na fito na rufe mata kofa, kuka mai karfi ya kwace mun, da gudu na shige ɗakina, ina zuwa na ɗauko.........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔