LABARIN AISHA

PART 5

by @queenofsurprise1

kuka mai karfi ya kwace mun, da gudu na shige ɗakina, ina zuwa na ɗauko wayana, a wannan dare na kira yayana, ALLAH yasa bai yi barci ba, ina kuka na faɗa mashi zasu saka in yaye Muhammad da bai kai yaye ba, ko shekara bai cika ba, kuma kowa yasan ingancin nonon uwa a jikin yaro, ba zan iya barinsa bai samu albarkar nonon uwa ba, dan ALLAH yaya ya taimaka mun.

Yayana ya ce in yi hakuri, kuma har yanzu yana kara faɗa mun kada in kuskura in yi wa mahaifiyarsa rashin kunya, in daure komai zai wuce, yanzu in ɗauro alwala in yi sallah in faɗawa ALLAH kukana, In Sha ALLAH ba zan tashi daga kan dadduma ba zai kawo mun mafita.

Bana cikin hayyacina sosai, amma haka na bi shawaran yayana, na tashi na shiga banɗaki, na yi alwala na fito, ina fitowa na shinfuɗa dadduma na tada sallah. Raka'a huɗu na yi sai shafai da witiri, sannan na zauna ina addu'ar ALLAH ya kawo mun mafita, ya dubi Muhammad da idanun rahama kada ya bari a tagayyara mun rayuwar yaro.

Ina shafa wannan addu'a na ji an turo kofar ɗakina, na ɗauki hasken wayata dana kifa a kusa dani, da sauri na haska dan ganin wanene?....... Abba na gani sanye da kayan barci a jikinsa yana rungume da Muhammad, yana tafiya a hankali. Wani irin zabura na yi na miƙe tsaye, zan yi magana ya ɗaura hannunsa a kan bakinsa alamar in yi shiru.

Ya tako har kusa dani, ya miƙa mun Muhammad, can ƙasa ya ce. "Ki shayar da shi sai in mayar mata dashi, ba zan so a rabasa da nonon uwa ba, kullum zan dinga kawo maki shi kina shayar dashi har lokacin da Mama zata gane su Aunty Farida basu da hankali ta daina biyewa zugansu".

Jikina har yana rawa na karɓi ɗana, lallai yau na kara tabbatarwa da ALLAH maji rokon bayinsa ne, ya fiddani daga bakincikin da nike ciki kan Muhammad a cikin ƙanƙanin lokaci, na dinga godiya ma ALLAH ina karawa, cike da tsantsar farinciki na zauna a gefen gado ina godewa Abba, ya ce babu komai. Na ajiye wayata ina ɗan jijjiga Muhammad dan ya farka, sai na sa hannu zan fitar mashi da nono.

A hankali na ɗago na kalli Abba dake tsaye, da sauri ya juya ya nufi kofa yana ce mun zai dawo anjuma ya ɗauki Muhammad, coz yasan bana taɓa shayar da yarana a idanun mutane, shiyasa ya fice, and ni matar yayansa ce, yana girmamani sosai, na so tambayansa ya aka yi ya ɗauko Muhammad daga ɗakin Mama, amma na basar tun da abu mai muhimmanci shi ne shayar da ɗana kuma ga shi dama ya samu.

Ina tada Muhammad ya waje baki zai yi kuka ya tona mana asiri, da sauri na danna mashi nono a baki. Haba da karfi bawan ALLAH ya kama, ya fara sha kamar ba zai bari ba, ya sa hannunsa dukka biyu yana matse nonon yadda kuka san baya fita mashi sosai, ALLAH sarki ya wahala, kwana biyu bai sha ba.

Bai ko ɗan sake ya huta ba sai da ya zuke na farko tas, na juyasa na bashi na biyu, ya hau sha, na dinga ruwan hawaye ina jin tausayinsa a raina. Muhammad yaro mai hakuri, bai cika kuka ba sai in yana jin yunwa, amma tsabar kukan da ya yi akwanaki biyun nan har kumbura idanunsa suka yi, na yi mashi kukan wannan ba kaɗan ba.

Haka na bashi ya ƙoshi sosai, sai ya koma barci abinsa. Na rungumesa a jikina ina kuka. Can Abba ya dawo ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa. Ina ganinsa na ce. "Shikenan Abba ka zo rabani da shi ko?".

Ya ji tausayina sosai, ya amsa da. "Aunty ba zan taɓa rabaki da ƴaƴanki ba, ko wani na gani zai rabaki da su sai in da karfina ya kare, please ki daina faɗa mun hakan, ba yadda zanyi ne yasa zan mai da shi, da ina da yadda zan yi da na hana a sake taɓa maki shi, uwa ce a rikici, uwa ta wuci wasa, duk zafan mutum dole ya sarara ya bi umarninta, ki mana afuwa ni da yaya a kan hakan, amma In Sha ALLAH ina tare dake! Kullum na yi alƙawarin in ta yi barci zan ɗauko maki takwarana in kawo maki, zai kasance tare dake ya ci abincin da ALLAH ya hukunta mashi".

Ina ai ban wani gamsu da kalaman Abba ba, na ƙanƙame Muhammad ban so bada shi, Abba ya matsa ya kai hannu na janye baya ina kallonsa, sosai ya dinga jin zuciyansa na mashi zafi, coz raba uwa da ɗah sai ALLAH, amma haka ya sake kai hannu yana faɗin. "Aunty kada ki ja takwarana ya rasa abincinsa kuma, please ki bari in mayar da shi ko dan gobe in sake ɗauko maki shi, nasan da ciwo, amma ki yi hakuri".

Ina kuka sosai, ba dan na so ba na miƙa mashi shi, yana karɓansa na fashe da kuka na kwanta, na kifa kaina a kan pillow ina shessheƙa. Abba ya kalleni cike da tausayi, sai ya juya ya fita dan kada Muhammad ya farka ya yi kuka asirinsa ya tonu.

Ina tsaka da kuka ban ji fitar Abba ba sai ji na yi ya kama hannuna yana ɗauko wayata dake haske a kusa dani. Da sauri na ɗago kai, yana durkushe a gaban gadon ta gabana, ya mai da Muhammad ya dawo. Cikin girmamawa da mutawa da yake bani ya ce. "Please Aunty ki daina irin wannan kuka, ki sani komai mai wucewa ne, ALLAH baya barci, yana sane dake, ki yi addu'a, nima ina tayaki, In Sha ALLAH zaki fita daga cikin wannan kunci, bana son ganinki kina kuka, kina tada mun hankali sosai, gidan nan yanzu ko sha'awar dawowa cikinsa bana yi saboda kada in zo in ganki cikin damuwa, please, yadda na sanki da hakuri, yadda kika jure kika yi hakuri da yayana, bashi da komai kika zauna da shi, yadda kika jure kika bi umarnin iyaye, kika rabu da wanda kike so, kika zauna da yaya dan ma iyayenki biyayya, na tabbata ALLAH ba zai barki haka ba, kuma ina son ki sani wanda ALLAH yake so shi yake jarabta, in baya sonki ba zai jarrabeki ba, ki daure ki ci jarabawar ALLAH na tabbata kece da nasara". Ya kai karshe hana sake hannuna da ya rike.

Ina ɗan shessheka, hawaye basu daina zuba ba na ce. "Nagode sosai Abba, zan yi ƙoƙarin ganin na daure na ci wannan jarabawar"...... Ya miƙe tsaye yana cewa. "Masha ALLAH, dama nasan Auntyna tsayayya ce mai hakuri, ALLAH ya kara maki hakuri". Ya ɗan rage tsawonsa, ya kai hannayensa saman kumatuna, ya goge mun hawaye, cike da kulawa ya ce. "Waɗan nan ruwan basu da gurbi a fuskan Auntyna, ki faɗa masu kada su sake fitowa, in ba haka ba zan datse alakarsu dake".

Ban san lokacin da murmushi ya kubce mun ba, maganarsa ta sakani murmushi. Ya ɗan yi murmushin shi ma kafin ya ce. "Wannan murmushi shi ne kawai yake da gurbi a fuakar Auntyta ba wancan ruwan ba"....... Na kara faɗaɗa murmushina tare da ɗan kai mashi dukan wasa a damtsen hannu kafin in ce. "Nawan baka ji, sai da ka sakani dariya ko? To tafi na sallameka".

Yana murmushi ya ce. "Ni ai ban sallami kaina ba, please Aunty ki jirani minti ɗaya kada ki rufe kofa". Bai jira amsata ba ya fice waje da sauri. Na bi bayansa da kallo ina tunanin da waye Abbie yake waya a wannan daren? Abin ya tsaya mun a rai.

A wannan hali Abba ya dawo ya sameni, hannunsa rike da plate na abinci da ya yi warning, tin da ya mayar da Muhammad sai ya sanya abincin a wuta dan ta ɗumamu shi ne ya dawo rarrashina. Ina ganinsa da abinci tun bai isoni ba na ce. "Ni fa ba zan ci ba".

Ya ce. "Please Aunty, ba dan ni ba, dan ALLAH da kuma soyayyar da kike yi wa fiyayyen halitta". Na hararesa, dan ya rufe bakina, dole na karɓa na fara ci, duk daɗin abincin nan amma ji nike tamkar tsakin magani nike ci, amma haka na dinga turawa, Abba yana bina da kalamai masu sanyani dariya, ya tsaya a gefe yana kallona. Har sai da na cinye abincin nan tas wanda yau tsawon kwanaki biyar kenan ban samu damar cin abinci haka ba.

Ya karɓi plate ɗin yana faɗin. "That's my Aunty, to yi addu'a ki kwanta, sai da safe"......... Ina hararansa na ce. "Ka dai mun ɗure"..... Yana murmushi ya amsa da. "Hakan ne daidai"....... Da haka muka yi sallama ya fice daga ɗakin, ma rufe kofa na sha ruwa sannan na kwanta. Na samu natsuwa, amma tunanin da waye Abbie yake waya yaki barin zuciyata, tsabar yana raina har mafarkin hakan na yi.

Washegari da safe yana fita kasuwa na kirasa, sau biyu bai ɗaga ba, sai daga baya ya zo ya kirani, na ce magana nike son mu yi amma na fi son gani ga shi ba a waya ba. Ya ce. "Ai kin san Mama ta hanamu kasance tare"...... Na yi shiru ban yi magana ba, jin cewa bai dace kalaman da ya faɗa mun bane yasa ya ce. "Ki zo kasuwar mu haɗu". Daga haka ya katse kiransa. Wani irin tashin hankalin da na shiga ban taɓa shiga irinsa ba, wlh Abbie bai taɓa mun magana irin haka ba sai yau, magana ba soyayya ba komai, sai ma alamar masifa a muryansa.

Amma haka na miƙe jiki ba kwari na yi wanka na shirya, su Mama suna ɗaki ko sallamarsu ban yi ba na fita, ban nemi Abba ya kaini ba, kuma ya kai su Hassan school, bashi da class sai 2, dan haka yana kwance a gidan a ɗakinsa, ban nemesa ba na fice, na hau adaidaita sahu. Zuciyata tamkar zata fashe saboda ciwo.

Haka na isko Abbie a kasuwa, na yi bala'in mamakin ganin shagonsa a cike da kaya sosai, sabbi gal-gal, designers, ga takalma da jakunkuna abin ba'a magana, ciniki yake yi tamkar ba gobe, a raina na ce kenan yana da kuɗi ya barni nike ɗaukar nauyin gidan? To ko dai yau ya samu kuɗin? Ni dai nasan shagonsa kaya kaɗan ne, sati uku da suka wuce na zo shagon ai, to me yake faruwa ne?. Amsar da na gaza samu kenan.

Ya kama hannuna muka shiga can cikin shagon wajen kujerar Manager, saboda ya ga sai kallon shagon nike na gagara karisawa ciki. Ya zauna a kan kujeransa tare da nuna mun kujerar visitors wai in zauna. Na zauna ina ta kallonsa, wlh har na yi muguwar rama kamar bani ba, ni fara ce sosai har na yi duhu, duk ina firgice.

Ya ce. "Me kike son ganina? And me kike son mu tattauna?". ..... Da kyar na iya cewa. "Ina wuni ya kasuwa?"...... Ya amsa da lafiya ya sake tambayar me nike son ganinsa....... Na daure na danne zuciyata kafin in ce. "Dama a kan maganar Zainab ne, na ce ka yi hakuri ka bi umarnin Mama dan shi ne zai sanya kaga daidai a rayuwarka, ka aminta kawai ka aureta sai ka haɗamu me a ciki, ALLAH zai buɗa maka yadda zaka iya rike mata biyun, sai maganar shagona, Mama ta ce lallai su Khalifa su fara zama a shagon". Ban nuna mashi kamar naga arziki a shagon ba, tun da yana ikirarin bai da shi, sai na ce ALLAH zai buɗa mashi.

Da buɗar bakinsa sai cewa ya yi. "Yarinyar bata mun bane habibi, bana sonta, batun shagonki kuma zan yi magana da Mama su Khalifa ɗin su dawo nan ne"..... Na fahimci da na yi maganar ya auri Zainab ya ji daɗi sosai, dan tun da na zo yana haɗe da fuska, amma dana ce ya auri Zainab har ajiyar zuciya na ji ya sauke tare da ɗan sake fuska.

"Ko da bata yi maka ba ka aurenta tun da Mama ta ce, please Abbie ka cika umarnin Mama". Na faɗa cikin raunin murya game da zafin cewa yau ni nike baiwa mijina shawarar ya kara aure, ya ALLAH........ Abbie ya kalleni kafin ya ce. "Idan kinga na auri Zainab sai dan ba yadda zan yi da iyayena ne, amma wlh bana sonta, bata daga cikin irin tsarin matan da nake so, ina da zaɓi kan mace".

A daidai lokacin kira ya shigo wayansa. My happiness shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin, sai yai maza ya kashe light na screen ɗin, na gani, kuma shi ma ya san na gani, sai ya yi saurin ce mun. "Mama ce take ta kirana tun kafin ki zo, wai lallai in zo gida yanzu".......... Na haɗiyi wani kululun bakinciki kafin in ce. "Uhm to ni dai yanzu in ka je ka amsa mata zaka auri Zainab komai ya wuce, zan tafi gida dan kaina na ciwo, amma kafin nan bani ruwa in sha".

Ya sauke ajiyar zuciya dan a tunaninsa na yarda cewa Mama ya sakawa my happiness a wayansa, bai san na yi shiru ne kawai ina bin umarnin yayana ba. Ya ɗaga murya zai kira yaron shagonsa wai ya kawo mun ruwa, sai na ce. "Abbie yau wani zaka ce ya kawo mun ruwa? Ina kishin naka yake? Ko ka manta A'isha ce ta zo?". Idan na zo shagon baya barin kowa ya kawo mun komai, shi yake kawowa da kansa.

Da na ce haka sai ya fasa kiran yaron shagon, ya miƙe da kansa zai je ya ɗauko, sai na ce. "Abbie bani wayanka kafin ka dawo bari in ɗan yi wani abin".

Ba musu ya miƙa mun, sai ya wuce da sauri, ina dubawa naga ya canza password wanda tun da muka yi aure bai taɓa canzawa ba, nasan password ɗinsa yasan nawa, coz wayansa ma yana wuni a hannu wani lokaci, amma yau ya canza password, to me yake ɓoyewa?. Jin da na yi zuciyata na barazanar tarwatsewa ne yasa na ajiye wayar a kan table na miƙe, da sauri na nufi waje tamkar zan kifa, kai tsaye na fita kasuwar ina neman abin hawa, a daidai lokacin daga bayana ina tsaye a bakin titi na ji an kirani, da sauri na juya dan ganin wanene, ina juyawa sai naga........

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

LABARIN AISHA.🥹💔