PART 6
A daidai lokacin daga bayana ina tsaye a bakin titi na ji an kirani, da sauri na juya dan ganin wanene, ina juyawa sai naga tsohon saurayina da na so a baya kamar zan mutu, na kallesa da kyau, ya canza, ya yi kuɗi ya yi kyau shi ma.
Fuskansa da murmushi ya ce. "Ina zaki je a tsakar ranan nan Aesh?"..... Shi naso a farko, na so shi tsakani da ALLAH, soyayyarsa har yau tana zuciyata, na ɗauke kallona daga kansa game da cewa. "Gida"......... "Okey, in ba damuwa mu je in rage maki hanya mana". Ya faɗa ba da wata manufa ba, shi ma ni ya fara so a rayuwansa, da alama har yanzu yana sona.
"Nagode ka bar shi kawai". Na faɗa tare da matsawa daga kusa da shi, na bar wajen kenan. Ya tsaya yana kallona, a ransa ya ce ko nan da shekara dubu ne ba zan daina sonki ba Aisha, coz yasan ba laifina bane, ban ci amanarsa ba, sai dai a lokacin kansa na rawa ne yasa aka hanani shi, dan a lokacin bai wuci 19 years ba, ni kuma ina da 14 da muka fara soyayya, shiyasa iyayena suka hana shi ni, wai yaro ne da bai san ciwon kansa bama bare ya san na wata, suna tsoron ya mayar dani karamar bazawara.
Ina tsaye a bakin titin dai sai ga Abba ya faka mota a gabana, ya sauke glass ɗin motar tare da cewa. "Aunty, sai ki fito ke kaɗai kuma ki hau abin hawa insert of ki tadani in kawoki"....... Na hararesa kafin in amsa da. "Yanzu waye ya faɗa maka ina nan?".
"Duk in da kike a jikina ina ji, shigo mu koma, in kuma baki gama abin da zaki yi ba, sai in fito in rakaki"......... "Na gama mu je". Na faɗa tare da zagawa zan shiga motar, unexpected idanuna suka sauka a kan Abbie dake tsaye a saman benen shagonsu yana kallona, coz tun tsayuwana da Ibrahim tsohon saurayina yana tsaye ashe yana kallonmu. Na yi gaggawar ɗauke kallona daga kansa ganin yadda ya tamke fuska, na shiga mota raina cike da tunanin me ya kawo Ibrahim Kano?.
Abba yana ta jana da hira, amma sam bana jinsa, a haka muka isa gida, cikin zolaya Abba yai saurin fitowa ya zo ya buɗe mun kofar motar yana faɗin. "Dole in buɗewa sarauniya matar babban yaya"........ Ina hararansa na fito, kai tsaye na nufi cikin parlo. Ina shigowa na isko su Mama, ina sako kafa Aunty Farida ta fara cewa. "Gata nan munafukar, ai nasan dole dama ta koma ta faɗawa malaminta mun karya asirin da yai mata a kan Sulaiman da Muhammad (Abba)".
Ban ce komai ba na wuce ɗakina ina ji a raina kamar dai lokacin mutuwata ce ta zo, dan zuciyata zata iya bugawa nike ji. Na zauna na sha kuka, sannan na kira yayana na faɗa mashi. Ya natsu ya gama saurarata sannan ya ce. "A shagonki na abayas jarinki zai kai nawa yanzu?".
Ina kuka na amsa da. "Zai iya kai 20M saboda na kwashi kuɗin kwanaki na baiwa Abbie ya juya dan ya farfaɗo da kansa"... Yayana ya ce. "A account ɗinki kuma kina ganin za'a samu nawa?". Da yake yayanmu namiji ne ya gane, using ɗina Abbie yake yi yana tara dukiya, Abbie ya fahimci na fisa goshin kasuwanci sosai, shiyasa yake amfani dani, amma duk ban gane ba, komai ni nake yi wa gida na yi wa ƴan uwansa, Abbie ya hanani yiwa kaina wani abin kirki, iya motar nan da Abba yake kai su Hassan school kawai na iya sayawa kaina, amma duk kuɗin da nike samu a kan Abbie yake tafiya, cikin dabara yake kwace mun kuɗi yana amfani da goshin kasuwanci da nike da shi yana gina kansa, yayanmu ya gano da kuɗina ya farfaɗo da kasuwancinsa haka, dan haka yayana da ya fahimci hankalina bai kai kan hakan ba, ban iya gane mai sona na hakika da kuma mai amfani dani ba, sai ya bini a yadda nike amma cikin dabara, bai gwada mun manufansa ba, dan yasan har yanzu ni yarinya ce, 20 years nike, sai ya bi dani yadda kananun shekaruna zasu gane.
Na amsa mashi da. "A account ɗina ba zai fi 5m, saboda na bashi tsabar kuɗi 5m last week, ya ce zai sari kaya bashi da kuɗi, in bashi aro ya cika ya saya, idan ya saya aka samu ciniki zai mayar mun"....... Yayana ya kara tabbatar da zarginsa a kan Abbie, kawai kwace mun dukiya yake son yi, sai kuma ALLAH ba azzalumin bawansa bane, saboda yana kwacewa arzikina na kara yawaita yana haɓaka, saboda mai bayarwa baya taɓa rasawa.
"Tom yanzu ki tura mun 5M ɗin nan dukka, dukka kada ki cire ko biyar, sannan yanzu duk kasuwan da kuka yi a shago kada ki kara sayan komai sai kin sanar dani"....... Da farko na so neman ƙarin bayani, amma da na tuna ɗan uwana ba zai cutar dani ba, sai na ce mashi to zan je bank sai in saka mashi. Muka yi haka da kwana ɗaya na samu na tura mashi kuɗin dukka.
Ranar dana tura mashi ya kirani, ya ce. "Duk abin da kike so daga yau ki tambayi Sulaiman tun da shi ya ajiyeki, ba ke kika ajiye kanki ba bare ki dinga rike kanki, kuma ki ce idan yai kasuwa ya baki 5M da kika bashi last week, sannan idan ya dawo ki sake jaddada mashi ya auri Zainab, and ki canza account na shagonki zuwa account ɗina na Gtbank, zamu dinga lissafi duk karshen sati".
Na yarda da yayana sosai, dan shi ma ɗan kasuwa ne na gasken-gaske. Na bi umarninsa, da Abbie ya dawo na saci hanya na je wajensa, still na samu yana waya, yana ganina ya katse kiran ba tare da ya sallami wanda suke waya ba, na zauna a kusa da shi, yana ta kallona, na kara jaddada mashi ya auri Zainab ya haɗamu ko dan in huta da wannan fitina da nike ciki na bala'in su Mama.
Da farko ya ce mun. "Habibi bani da kuɗin auren yarinyar nan, kuma bani da karfin iya rike mata biyu, da na aureta ta zo zata fara haihuwa nauyi ya karumin, yanzu haka kayan dake shagona duk bashi na ɗaukosu, ba hakkina bane, ya za'ayi in ɗauki hakkin mutane in yi aure?".
Na ce. "Duk da haka Abbie ka cika umarnin Mama In Sha ALLAH UBANGIJI zai buƙa maka"........ Ya amsa da ALLAH yasa kawai. A wannan rana ban bar ɗakin ba sai da ya amince da safe zai faɗawa Mama ya yarda zai auri Zainab.
Zuciyata tamkar zata fashe na miƙe na nufi waje, ya kira sunana wanda yasa na juyo ba tare da na dawo in da yake ba, a natse ya ce. "Amma Aisha kin tabbata ban cutar dake ba? Ban zalunceki ba?"...... Na kallesa cike da mamaki, sai na ce. "Me ya kawo wannan magana?".
"Ina son tabbatarwa da ban cuceki a zamanmu bane, kun mun halacci wanda gabaɗaya dangina basu taɓa mun ba dake da danginki, a lokacin da na shiga halin babu duk family ɗina babu wanda ya iya bani aron 1k banza, amma kika ɗebi kuɗi ke da danginki kuka bani, kuka ƴanta ni, so bana son in cutar dake ne, bana son hakkinki ya hau kaina, idan kina ganin kamar akwai abin da nike yi yake cutar dake dan ALLAH ki faɗa mun da wuri dan in gyara".
Na ƙaƙalo murmushin dole wacce ta fi kuka ciwo na amsa da. "Babu komai Abbie, baka taɓa cutar dani ba, bari in je in kwanta"...... Ya amsa da sai da safe, na juya na fita da sauri. Na shiga ɗaki na sha kuka na har tsakar dare, Abba ya kawo mun Muhammad kamar yadda ya saba, na shayar da yarona, sannan ya mayar da shi, ya tasani gaba in ci abinci kamar dai yadda ya saba, dole na ci kaɗan, ya ɗauki sauran ya fita yana mun sallama.
Washegari ranar kwanaki na bakwai kenan da zuwan Mama gidanmu, da safe ina ɗaki na ji kira a parlo, na miƙe na fita, gabaɗaya ahalin gidan suna parlo, na wuce na zauna a kusa da Abba, ina kallon Abbie dake ta faman dannar waya yana ɗan murmushi. Mama ta yi hamdala ga ALLAH, sannan ta ce. "Yau kwanaki bakwai kenan muna maganin wannan asiri, ga shi cikin ikon ALLAH asirin ya karye, yau Sulaiman da kansa ya sameni a ɗaki, ya bani hakuri, ya nemi afuwata sannan ya jaddada mun zai auri Zainab, lallai Liman ya yi gaskiya, lallai A'isha kin bani kunya, amma ba komai, albarkacin iyayenki, ba zan ce Sulaiman ya sakeki ba, amma yazama wajibi yarana su sha maganin kariya daga mugun nufinki".
Na sunkuyar da kai ina jin kuka na zuwan mun, zuciyata na barazanar tarwatsewa, saboda ni nasan gidanmu ahalin sunnah ne, wlh ban da karatun Alqur'ani bamu dogara da komai ba, bama zuwa wajen kowa neman komai face ALLAH da ya haliccemu, amma ana mana muguwar kazafi, ba komai rayuwace.
Abbie bai ce komai ba, sai Abba ne ma ya ce. "Mama dan ALLAH ki bar wannan magana haka, tun da yanzu Yaya ya yarda zai yi wannan auren komai ya wuce"..... Khalifa dake zaune kusa da uwarsa ne ya ce. "Kai kam Abba anya asirin nan ya sake ka kuwa?"........ Mama ta ce. "I wonder ooooo".
"Ban kasa da kai ba Khalifa". A cewar Abba, ya faɗa tare da miƙewa ya ɗauki Muhammad dake kusa da Mama, ya wuce ɗakinsa. Mama ta kalli Abbie ta ce. "Sai ka je wajen sauran kawunenka ka nemi auren Zainab, kada a saka lokaci mai tsawo, ni gobe zan koma Kaduna tun da komai ya warware"....... Abbie ya amsa da okey tare da mikewa ya nufi waje, yana fita na miƙe zan bi bayansa dan ina son yin magana da shi, ina miƙewa Mama ta ce. "Zai fita nema ma ba zaki rabu da shi ba sai kin hana shi fita a kan lokaci ne?"..
Aunty Farida ta ce. "Rashin kunya ne ai, ko kunyar idanunki bata ji"........ Ban ce komai ba na juya da sauri na shige ɗakina ina jin kuka na zuwanmu, ina tuna lokacin da mijin Aunty Farida yake hanasu abinci ni nike ciyar da gidan, ina tuna lokacin da yaranta suka gantalin basa zuwa makaranta saboda ubansu baya ɗaukar nauyinsu ni nike masu komai, amma yau Aunty Farida ni take zagi saboda mijinta baya yi mata abin da kaninta yake mana na kulawa, rayuwa kenan, dama duk macen da ka gani tana jin haushin zaman aurenka lafiya to wlh bata samun rabin kwatan abin da kake samu ne, da tana samun irinsa ko ta fika ko kallon in da kake ba zata yi ba bare ta takura maka, amma tun da ita bata samu ne bari ta hana ayi maka kai, mutum mugub icce.
Ina shiga ɗaki ƙanina ya kirani a waya. Ina ɗauka ya ɗaga mun gaisuwa, bayan mun gaisa sai ya ce. "Aunty jiya ƙarshen sati baki zo mun yi lissafi ba, dama jiya na ce in mun tashi zan zo gidanki in ga meyasa kwanaki biyun nan baki leƙomu a shago".
"Ahmad babu komai, zan zo anjuma mu yi lissafin, abubuwa ne suka mun yawa". Ahmad ya amsa da okey, muka yi sallama, na zauna ina tunanin rayuwa, saboda gudun fitinar dangin miji fa yasa na kamawa Ahmad haya a wani unguwa daban, dan ma kada su ce na kawo ƙanina gidan muna cinyewa ɗansu arziki mun ɗaura mashi nauyi da wahala, amma duk da haka ban tsira ba, ALLAH dai ya kyauta.
Yau da yake an gama maganin makarin asiri in ji Mama, sai ta barni na sake a gidana, an dawo mun da Muhammad, dan haka da yammma na shirya muka je shago da Muhammad, Abba ya tafi wajen kwallonsa, Hassan and Hussaini suna islamiya.
Ina zuwa shago muka yi lissafi da Ahmad, a wannan sati kasuwa ta yi kyau, Alhamdllh mun samu ribar almost 550k, sannan mun yi ciki sosai, dan a kallah tsabar kuɗi a ƙasa akwai 8M, na kira yayana dan in faɗa mashi, yana ɗauka ya ce. "Ke zan kira yanzu dama".
Na ce. "Sai kuma ga shi na kiraka".... Ya ce. "To fara faɗa mun naki dalilin na kira kafin in faɗa maki nawa"........ Ina murmushin yaƙe na ce. "Mun yi lissafi ne a shago, ga abin da aka samu, ga kuma tsabar kuɗin dake ƙasa".
Da buɗar bakin yayana sai ya ce. "Ki tura mun kuɗin dukka, da ribar da uwar kuɗin, ina son shagonkin nan sai ya zamana jarin 5M ne kawai a ciki zaki barsa"....... "Yaya meyasa?". Na tambaya a raunace.
"Kada ki sake tamnayata, kawai ki yi abin da na ce, idan lokaci ya yi da kaina zan faɗa maki abin da yasa". Ya faɗa, a cikin zuciyansa kuwa, yana tunanin yadda zai sakani in zame dukiyata dake hannun Sulaiman, idan har wannan shagon nawa akwai kaya, to lallai Sulaiman ba zai daina karɓar arzikina yana abin da yake so ba.
Na amsa mashi da okey tom, sai ya ce. "Ki nemi izinin mijinki ki zo Kaduna a satin nan, ina buƙatar ganinki"...... Nan ma na amsa mashi da to, muka yi sallama, na bawa Ahmad kuɗina dukka na ce ya je ya sakawa Yaya a account ɗinsa a banki. Ya ce okey, sannan ya ce yana son kuɗi akwai abubuwan da zai saya, na ce ya tambayi yaya, yadda suka yi dukka ni yanzu shago ya bar hannuna.
Daga nan na miƙe na dawo gida. Ina dawowa na ɗaura girkin dare, na dafa amma Mama bata ci ba, wai kada na saka asiri a ciki tun da na fita da yamman nan. Na ci abincina ni da yarana, ko Abbie bai ci ba Mama ta hana shi, tun kafin Mama ta hana shi ma ya ce ya ƙoshi.
Abba kuwa ya saci hanya ya ci girkina, domin idan akwai abin da za'a fi yabani da shi to shi ne iya girki bayan yawan ibada, na iya girki sosai, Abba ya ce girki idan ba nawa ba duk lami ne, shiyasa baya taɓa cin abinci wajen kowa sai wajena, idan yai tafiya zuwa Kaduna ya dinga damuwa kan abincin can babu daɗi, shiyasa bai cika yin tafiya bama.
Duk da an gama maganin makarin asiri ban kwana tare da Abbie ba, saboda ina shiga ɗakinsa na same shi yana barci, sai na dawo ɗakina kawai na kwanta, da yake ma bana jin daɗin jikina. Washegari da safe Hajiya Mama ta mana sallama ta koma Kaduna, amma kafin nan sai da ta mana nasiha sosai, ta dinga mun faɗa wai inji tsoron ALLAH in daina bin malamai, ni kan na ce mata to kawai.
Aunty Farida ma da guntun nata nasihar wai miji da makirci ake mallakesa bada asirai ba, a raina na ce shiyasa naga naki mijin ya gagara rikeki ai, duk makircin naki ga shi kina gantali a titi na neman abin da zaku ci, a fili kuwa na ce Nagode.
Mama ta jawa Abba kunne sosai, sannan ta ce ga su Khalifa amana, Abbie ya ce babu komai, suka mana sallama suka tafi, Abba ya kaisu tasha suka shiga mota. Suna tafiya na kalli Abbie dake zaune a kan kujera, na ƙaƙalo murmushi dole kamar yadda yayana ya ce kada in nuna mashi ɓacin raina, na ce. "Abbie ba zaka je kasuwa bane yau?".
Ya ce. "Yau ranarki ce uwar gida ran gida, yau zan zauna tare dake"........ Zuciya bata da ƙashi, na ɗan ji daɗin kalamansa, har da ajiyar zuciya na sauke, sannan na ce. "Abbie, amma komai iri ɗaya zaka yi mana da amarya ko?"........ Ya kalleni yana murmushi kafin ya ce. "Haka kike so? Ai kin san duk abin da kike so shi zan yi, kinga auren ma sai da kika nuna kina so zan yi".
Na kara faɗaɗa murmushina kafin in ce. "Kai Abbie, kai Abbie"...... Ya ce. "Wlh da gaske, a wannan hidima duk abin da kike so shi kawai za'ayi"....... Ba ƙaramin daɗi na ji ba, sai na ce. "To shikenan komai iri ɗaya zaka mana ni da amarya, sannan ni zan je in sayo mana".
Ya amsa da. "An gama uwar gida". Yana magana yana murmushi, mun wuni tare yau cikin farincikin da na jima ban shiga ba, sai around 3 ya ce zai je da kansa yau ya ɗauko su Hassan dan suma su shaida Abbie ɗinsu ya dawo garesu. Na ce adawo lafiya. Yana fita na ɗauki waya na kira yayana.
Na kyankyasa mashi duk abin da ya faru. Ya ce. "Yauwa ƴar albarka, tun da ya ce duk abin da kike so za'ayi bari in faɗa maki yadda zaki yi, kinga yanzu ba zai so rigima dake ba, dan hankalinsa na kan auren, lallaɓaki zai dinga yi, yanzu ne kike da dama, dan haka abin da nike so dake daga yau.........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔