PART 7
"Yauwa ƴar albarka, tun da ya ce duk abin da kike so za'ayi bari in faɗa maki yadda zaki yi, kinga yanzu ba zai so rigima dake ba, dan hankalinsa na kan auren, lallaɓaki zai dinga yi, yanzu ne kike da dama, dan haka abin da nike so dake daga yau ki koyi zame dukiyarki daga cikin nasa a hankali cikin hikima da basira, kada ki bari ya farga, kafin ya farga kin kwace dukiyarki, ba faɗa ba gaba, kada ki kuskura a ƴan tsakanin nan ki yi gaba ko faɗa da shi, ki nuna mashi kina tsananin farinciki da wannan aure, da fatan kin gane?".
Watau yaya ya gama gano cewa tun asali Abbie yana son yarinyar nan Zainab, kawai ya ɓoye mun ne, kun san maza sun san duk wani makirci na ɗan uwansu namiji, ba wani zancen baya sonta a nan, wayau kawai yake mun, ni kuma na yarda da Abbie, gani nike kawai ba zai taɓa cin amanata ba.
Na ce da yaya na karɓi shawaransa kuma zan yi yadda yake so In Sha ALLAH. Muka yi sallama na ajiye waya ina tunanin rayuwa, daga karshe na kwanta na yi barcina. Bani na farka ba sai 12 na rana, na tashi na shirya shiga kitchen, na haɗa mana lunch mai rai da lafiyar da na jima ban yi irinsa ba.
Ina tsaka da girki Abba ya shigo kitchen ɗin, ban ma san yana gidan ba, ashe da na yi barci ya dawo, da ya shigo yaga ina barci sai ya wuce room ɗinsa. Ban ji shigowansa kitchen ba sai ji na yi abu ya taɓani a bayan wuya. Razana nai game da sake ƴar kara saboda ina da tsoro sosai, na juyo da karfi.
Four eyes muka yi yana tsaye yana kallona, ya yi folding hands ɗinsa a saman kirji. Na dallah mashi mugun kallo ina sauke numfashi, duk tunanina wani abin ne ya taɓani, ashe shi ya saka mun wani ganyen flower a wuya...... Ya ɗan yi dariya game da cewa. "Sarkin tsoro kawai, ke Aunty ban san yaushe zaki girma ba, tsoronkin nan ya yi yawa, dole in karo mata jarumar da zata dinga tsare mun gida, haba, wannan ai da kin ji ɓarayi zaki shige ƙasan gado ne na sani".
Ina harararsa na ce. "Nawan! Nawan! Nawan! Sau nawa na kira sunanka?"..... Ya ɗan sunkuyo ta gabana kaɗan kafin ya ce. "Sau uku Auntyn tawan ta kirani......." Ban bari ya karisar da maganar ba na ɗebo ruwan bowl ɗin bayana na watsa mashi a fuska tare da cewa. "Dole in maka iyaka da wasu sassa a cikin gidan nan, dan yanzu ka girma ba kamar da bane, kada ka sake shigo mun kitchen!". Na faɗa ina ɗaure fuska.
Yana ɗan murmushi ya amsa da. "Eyyye, ni da gidan nawa? To ki shafawa kanki lafiya tun ma kafin raina ya ɓaci na baki suspension"........ Na juya na cigaba da aikina tare da cewa. "Nawan, ka daina yi mana yawo da gajeran wando a gidan nan, dan kana ɗan kwallo sai ka ishemu da sportswear, kuma wlh aure zaka zo ka yi in huta, dan ka isheni haka".
Ya matso kusa dani, ya ɗan jingina da jikin drawers na kitchen ɗin tare da cewa. "Ni da aure, tab, sai na girma, yanzu kam ban kai ba, kuma ni da gidana dole in yi yawo da sportswear". A ɗan shagwaɓe yai maganar, wani lokaci Abba ya iya shiririta saboda ɗan Auta ne, Mama ta shagwaɓa shi sosai, shi nan gani yake bai girma ba, kuma har cikin zuciyansa wlh yake ganin kamar bai girma ba, yaro yake ɗaukan kansa, shiyasa ma yake shagwaɓa sosai har yanzu.
"Zaka ga baka kai aure bane, sai na je na faɗawa Mammyna kana son sister Safiyya, daga nan manya su shiga lamarin, ni dama already na mallaka maka ita, sai aure kawai".
Da sauri ya ce. "Aunty wannan sister ɗin taki mai kama dake?"....... Na gyaɗa mashi kai game da cewa. "Ita fa, kaga yanzu tana da 14 years, kai kuma 25, zaku dace, sannan kaga tana SSS1, sai ayi magana, a saka rana, kafin ta kammala secondary school kai ma ka kammala karatunka ka fara aiki, sai ayi auren kawai".
Da sauri ya tari numfashina da cewa. "A'a Aunty, wani aiki kuma? Ni fa ɗan kwallo ne, meyasa baki son yin fatan alkhairi a kan burina?"....... Ina yanka ganyen ogu na amsa da. "To Malam ɗan kwallo, ni dai yanzu ka samu Safiyya ku fara gaisawa".
Ya sake matsowa kusa dani, ya fara tayani tsinke ganyen, saboda ya iya sosai, coz cikin mata ya taso, shiyasa wani lokaci yake da shiririta ga shagwaɓa, duk wani aiki na mata ya iya. Yana tayani tsinke ganye ya ce. "Amma Aunty anya zata yarda dani kuwa?".
"Meyasa ka ce haka?"...... "Naga ƴan gidanku basa saurin yarda da mutane, and suna da kamewa sosai, bugu da ƙari ba ƙaramin abu bane yake jan ra'ayinsu"..... Na ɗan kallesa kafin in ce. "Waye ya ce maka hakan? Ba ga shi ni na yarda da yayanka ba, na aminta da shi, dan haka ƴan gidanmu suna da yarda da mutane, kawai saurin sabo ne bamu da shi, kai ma da ka zo gidan nan ai kafin mu saba an kai watanni shidda, da muka saba kuma ba shikenan ba".
Yai ɗan dariya game da cewa. "Wahala dey for who is dating one of your family Aunty, yanzu sai na yi 6 months ina bin Safiyya kenan kafin in samu yarda?"......... Na hararesa kafin in ce. "Ni kam yayanka ya yi 6 months kafin in sauraresa ne?"......... Ya ɗan nisa game da ɗan canza mood, ya ɗan haɗe fuska kafin ya amsa da. "Yayana yana da saa sosai ne, amma kuma Aunty ai shima ya sha bakar wahala, sama da shekara kuna rigima a kan baki son shi, shiyasa yanzu nike tsananin fargabar ya ci amanarki, ku ƴan gidanku basu da saurin sabo, amma in kuka saba da mutum, to kun gama bashi yarda ne, ina tsoron yaya ya rasa wannan yardar da kika bashi, ina maku addu'a kullum, sannan ina maku fatan ALLAH yasa wannan abin ya zo da sauƙi".
"Kai nawan, waye ya ce maka yayanka zai ci amanata? Na san shi sosai, na yarda da shi, yana da hankali da ilimi, ya san me yake yi, ba zai taɓa cin amanata ba Abba, i trusted him more than your expectations".
Abba ya girgiza kai cike da tausayina, ya ji tsoron ALLAH ya ji tsoron yardan da na baiwa yayansa. Sai ya canza topic na hiran da cewa. "Aunty duk bama wannan ba, manta da batun yaya, please Aunty maganin can zaki sake saya mun, sannan ki bani number Safiyya ɗin".
Na juyo da kyau na kallesa kafin in ce. "Nawan, ban fa yarda da kai ba, wai wani irin magani ne kake saya duk wata, yaushe na bada kuɗin maganin nan 10k? Ka faɗa mun cutar dake damunka kaki, baka yarda dani bane?"......... Ya ɗan ja dogon hancina ƙaɗan game da cewa. "Idan akwai wanda zan yarda da shi to ya biyo bayanki Aunty, kawai wlh ba zan iya faɗa maki abin dake damuna bane, kuma wajibi ne in dinga shan wannan magani idan ina son zaman lafiya, maganin da na saya last week faɗuwa yai a school ban gansa ba, shiyasa zan sayi wani".
"Nawan, watau har yawo ma kake yi da maganin? Wani irin ciwo ne yake damunka haka? Please in har ka yarda dani ka faɗa mun damuwarka, ka sani ma ko nasan maganin da ya fi wanda kake sha kyau da amfani?".
Ya ɗan ɗauke kallonsa daga kaina, yana wani son dojewa kada ya faɗa mun, sai ya ɗauko zancen Safiyya tare da cewa. "Aunty bani number Safiyya ɗin". Ya faɗa game da ɗaukar wuka zai yanka ogu da ya gama tsinkewa........... "Nawan, in dai ba zaka faɗa mun abin dake damunka ba kada ka sake mun magana, ban taɓa tunanin akwai rana da zata zo wani abu na damun ɗayanmu mu gagara yin sharing problems ɗin da juna dan neman mafita a tare ba". Da iya gaskiyata na faɗa, coz ya kai shekara biyu kullum Abba sai ya sayi magani, kuma yaki faɗa mun me yake damunsa, baya son in sani, and kullum yana yawo da maganin a jikinsa, alamar cutar tana da karfi kenan, kuma tana da haɗari a garesa.
Shiru ya ɗan yi, gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, har cikin zuciyansa baya son faɗa mun abin dake damunsa, amma baya son ɓacin raina, jikinsa duk ya yi sanyi. Ban sake bi ta kansa ba na cigaba da aikina bayan na bashi number Safiyya. Ganin hakan yasa ya tayani komai bai sake yin magana ba shi ma, har muka kammala around 1:30 ba rana, muka fito, ya wuce ɗakinsa nima na wuce nawa ba wanda ya sake yi wa juna magana. Wanka na yi na ɗauro alwala, na zo na yi sallar azahar, ina idarwa na yi zaman askar.
1:40 daidai Abba ya shigo ɗakina bakinsa ɗauke da sallama, ciki-ciki na amsa mashi, ya zauna a ƙasa kusa da daddumar da nike kai, yana kallona ya ce. "Auntyn tawa, yanzu da gaske fushi kike yi dani kenan?". Na yi shiru ban amsa mashi ba.
"Shikenan zan faɗa maki abin dake damuna, amma fa ki sani ko Mama ban taɓa faɗa mata ba, daga ni sai ALLAH kuma ban yi niyyar faɗawa kowa ba, kema saboda kin ɓata rai ne, kuma bana son ɓacin ranki shiyasa zan faɗa maki, amma please ki rike mun amana, ko yaya kada ki faɗawa dan ALLAH"....... Na hararesa ban yi magana ba, ya ɗan sunkuyar da kai saboda tsananin kunyar maganar da yake ji, ya kara natsuwa kan wanda yake da shi, dan gaskiya Abba akwai natsuwa sosai kaman yayansa haka yake.
Yai ƙasa da murya can kafin ya ce. "Nasan kin san gabaɗaya yaran Mama muna da wannan matsala ta karfin sha'awa, daga matanmu har mazanmu haka muke, halitta ce, to wannan ne yake damuwa sosai, gudun afkawa wata ɓarnar yasa nike shan wannan maganin dan kwantar da shi, sau uku nike haɗiyar maganin a rana shiyasa nike yawo da maganin a jikina, dalilin da yasa wani lokaci zaki ga bana sallah a jam'i sosai har yaya yai ta faɗa, ina yawan zubar da sperm sosai, amma Dr ɗin yake bani maganin nan ya ce in dinga kallon fina-finan batsa zasu dinga taimaka mun, sai dai ba zan iya ba, saboda haramcin hakan, shiyasa nike wahala sosai duk da ina shan maganin". Tun da ya fara magana bai ɗago ya kalleni ba har ya kai karshe.
Gabaɗaya sai na ji na yi nadamar saka shi dole ya faɗa mun abin da ya fi shekaru biyu yana ɓoyewa, duk na ji wani irin kunya mai tsanani ya kamani, na gagara ɗagowa in kallesa nima, tabbas nasan gabaɗaya yaran Mamansu haka suke, harta matansu, dan wlh duk matan idanunsu jajir yake, suna da muguwar karfin sha'awa bare kuma mazan, haka Abbie yake, kuma dalilin mutuwar auren Khadija da Amina sister ɗin Abba kenan, wannan karfin sha'awar tasu ya kashe masu aure, saboda sun aurin mazan da ba zasu iya yi masu yadda suke so ba, duk gidan kanwar Abbien mai suna Homaira takwarata ce kawai nata da sauki, amma har Aunty Farida wannan abu yake addabama shiyasa kullum suke faɗa da mijinta ga yawan haihuwar da take yi, mijin ya ce baya son yara ita kuma jarababbiya, ya ce wlh idan ta sake haihuwa ba zai ɗauki nauyin yaran ba dan ba zai iya ba, so jaraba a cikin jininsu yake, and duk nasan da hakan, sai dai ban yi tunanin na Abba yai tsamari haka ba.
Ganin na gagara yin magana kuma ba zai iya ɗagowa ya kalleni bane yasa ya miƙe ya fice waje da sauri, ai yana fita na ɗauko wayata na tura mashi kuɗin maganin, ina dalili, haka kawai ya je ya kawo mana yaro daga waje, ai gara ya dinga shan maganinsa ya fi mana sauƙi, ai daga yau sayan magani ba fashi, ko bai tambayi kuɗin ba dole in bashi, ban isa ba, ahalin mutunci muke, a raina na kudurci niyyar idan Abbie ya dawo yau lallai zan yi mashi maganar yai maza a yiwa Abba aure, dan kada a samu matsala.
Tun daga wannan lokaci wani irin kunya ta shiga tsakanina da shi, ko na fito mun haɗu bana taɓa yarda mu haɗa ido, shi ma baya yarda mu haɗa ido, ko magana yake mun kansa a ƙasa, komai ya ɗan canza tsakaninmu.
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔