PART 8
Tun daga wannan lokaci wani irin kunya ta shiga tsakanina da shi, ko na fito mun haɗu bana taɓa yarda mu haɗa ido, shi ma baya yarda mu haɗa ido, ko magana yake mun kansa a ƙasa, komai ya ɗan canza tsakaninmu, mun rage wasan kanin miji da muke yi, na ɗan ja baya da shi saboda kunya, idan na gansa kalaman kawai nike tunawa.
A haka muka shafi sati muna wannan ɓoyewa juna. Yau takama Saturday, kowa yana gida har Abbie, mun haɗu a parlo muna hira, sai Abbie ya miƙe ya fita, ya ce yana zuwa, na amsa da okey, Abba na zaune Hassan da Hussaini sun haye jikinsa suna wasa, yaran nan shaƙuwar da suka yi da Abba ko ni uwarsu basu yi shi dani ba bare Abbie da ba zama yake yi ba, komai uncle Abba komai uncle Abba.
Ya zaunar da Hussaini a kan cinyarsa yana gyaggyara mashi gashi kansa, Hassan kuma ya haye bayan wuyansa yana lilo, sai dariya suke yi. Na zubawa Abba idanu ina kallonsa, yana kama da Abbie sosai, sai dai Abbie ya ɗan fisa haske, shi yai chocolate sosai.
Cikin zolaya na ce. "Nawan gashin gerarka ya kusa haɗewa, zaka zama dodon su Hassan, Safiyya zata raina mun kai, yakamata in gyara maka"....... Kamar yasan ina kallonsa, sai yaki ɗago ido, ya kara yin ƙasa da kai ma kafin ya ce. "Auntyn tawa bama ki ji me Sofi ta ce mun ba fa".
"Me ta ce?". Na faɗa ina murna na ganin sun fara magana da Safiyya, na ji matuƙar daɗi........ "Cemun ta yi wai na fi dukka yaran Mama kyau, amma na cika shagwaɓa kamar mace, ita bata son namiji mai halin mata, Aunty please ki faɗa mata wlh ba halin mata nike da shi ba, zama cikin matan ne ya lalatani, ki faɗa mata ke kike sakani yin aikin mata, ke kika ɗaura daga kan in da su Aunty Farida suka tsaya daga gida, sannan ki faɗa mata jarumin namiji ne ni". Har ya kai karshen maganar ɗan tahalikin nan yaki ɗago kai, yana ta fama da gashin kan Hussaini.
Na fashe da dariya, cikin zolaya na ce. "Ai ta yi gaskiya, kai mata maza ne, ni ban taɓa ganin namiji da shagwaɓa ba, kuma ban taɓa ganin namijin da ya iya duk wani abin da mace ta iya da kuma shiririta ba sai kai"........ "Aunty nine mata maza?". Ya faɗa a sanyaye, still bai ɗago ido ba........... "Kwarai kuwa, mata maza kake, rago kawai". Na faɗa ina dariya.
Ya ɗan jinjina kai game da ɗan ciza laɓɓa bai yi magana ba, zan sake yin magana wayata ta fara ƙara. Da sauri na jawota, Safiyya ce, ina ɗauka ta ce. "Aunty albishir?".
"Safiyya babu sallama sai albishir dan gidanku?". Na faɗa ina kallon Abba da ya ɗan turo lips ɗinsa na ƙasa kaman mai tunanin wani abin da ya shafi shagwaɓa, amma da ya ji na ambaci Safiyya sai ya ɗago waɗan nan dara-daran idanun nasa da suke ja kullum ɗin, yana ɗagowa muka yi four eyes dan shi nike kallo, da sauri ya ɗauke kansa tare da cewa. "Please Aunty ki ce mata ina sonta sosai, ta yarda dani". Ya faɗa yadda Safiyya ba zata ji ba.
Sai ya sake cewa. "Please Aunty ki sakata a hand-free, ni bata mun magana sosai, sai okey da uhm ta iya cewa, ina son jin muryanta, ko na kira bata ɗauka, please tawan". A wannan karon ma yai magana bai ɗago ba.
Aikuwa na sanya Safiyya a hand-free, daidai lokacin take cewa. "Aunty murna yasa na mance da sallama"...... Abba ya ɗan yi murmushi yana sunkuye da kai, har da sauke ajiyar zuciya na ya ji muryanta. Yadda Abba yake mugun kama da yayansa sai ɗan haske da Abbie ya fisa, haka nima nike mugun kama da Safiyya sai haske nima dana fita, and na fita manyan idanu kaɗan.
"To faɗi me yafaru ake murna haka?"..... Ta ɗan sheƙe da dariyar farinciki kafin ta ce. "Aunty Muhammad ɗin su Abbien Hassan ɗinki ya mun magana, ya ce yana sona, tun jiya na so faɗa maki, amma ban da lokaci saboda makaranta da hadda, Aunty ina son shi wlh, yana da kyau da hankali, kinga idanunsa irin na Abbie, kinga dimple ɗinsa mai kyau sosai, matsalar kawai ya fiye yin abu kamar na mata ne wani lokaci, ga shagwaɓa yana matsayin namiji, sannan wani lokaci akwai shi da shiririta". Yadda take magana cike da tsantsar farinciki kawai ya isa ya nuna da iya gaskiyarta take son na shi.
Oooooo, Abba ya saki wani irin musulmin murmushi da ya kara fito da kyansa tare da ajiyar zuciya lokaci guda, a fili ya furta Alhamdllh. Haƙiƙa ya ji daɗin jin tana son shi, coz raina mashi wayau take ashe, kawai wasa da hankalinsa take yi da ta ce bata son shi.
Ai da jin haka na ce. "Ki bari zan sake kiranki, yanzu ina aiki ne". Ban jira amsarta ba na katse kiran, na kalli Abba dake ta faman murmushi na ce. "Nawan ya zama lover boy, sai ka fara shirin yin aure, ka dai ji ta ce tana sonka".
Bai yi magana ba sai ya ɗan ɗago ido a ƙoƙarinsa na son satar kallona, amma sai muka haɗa ido, da sauri ya sauke nasa yana faɗin. "Kai Auntyn tawa, kin cika sa ido, da mutum ya ɗago kai zai ga shi kike kallo".
"Eyee angon Sofi, ni yau zaka cewa mai shegen sa ido? Ba komai, dole ka ce haka ai"...... Yana ɗan murmushi bai sake yin magana ba, coz yana cikin farinciki sosai, and yana jin tamkar ya tashi ya rungumeni saboda daɗi. Safiyya ta sake kirana, ina ɗauka ta ce. "Aunty hau Whatsapp bari in tura maki wani abin da Muhammad ɗin ya tura mun ɗazun ki gani, Aunty ya iya kalamai masu rikita ƙwaƙwalwa, kin ji me ya ce?".
Na ɗago ido na lallesa, daidai lokacin shi ma ya ɗago, saboda a H-free na sanya wayar, jin me ta ce ne yasa ya ɗago. Na wani hararesa ya sunkuyar da kai yana murmushi, na amsawa Safiyya da okey rabin raina. Katse kiran ta yi, na kunna data da nufin in ga me ɗan kanin nawa ya tura mata.
Ina ƙoƙarin buɗe sakonta sai ji na yi ya fisge wayar yana faɗin. "Ba zaki ga sirrin ma'aurata ba"....... Ai da sauri na zabura zan kwace wayata, ya ɗaga wayar sama wai idan na isa in kwace, coz na faɗa maku ya fini tsawo sosai, tsalle na fara yi wai zan kwace wayata ina faɗin. "Nawan ka bani wayata, sai na ga me kake shukawa". Ina magana ina haɗe rai.
Ya ce. "Gajera kawai, sai son ganin gulma da son shiga harkar iyali, idan kina son ganin gulmar jeki aro tsawo ki dawo". Duk maganar da yake yi bai yarda mun haɗa ido ba..... Na ɗan koma baya na hau kujera, na daka tsalle wai zan kwace wayar sai ya ɗan ja baya yana dariya, saura kaɗan in faɗi ƙasa yai saurin tareni da hannunsa ɗaya yana faɗin. "Ke ba karfi ba, ba tsawo ba, Auntyn tawa ke kaɗai ma fa idan kina tafiya faɗuwa kike yi, to dan ALLAH ki rufa mun asiri kada ki ja Yaya ya ɗaureni na karya mashi mata". Ya faɗa yana sakeni.
Na miƙe ina huci na wasa, na ce. "Ko ka bani wayata ko in kira yayanka"...... Yaki bani wayar sai da ya buɗe ya duba abin da Safiyya ta turo mun, chat da suka yi daren jiya ne, irin love stickers da ya turo mata, zafafan kalaman da ya dinga zuba mata, su ta yi screenshot ta turo mun. Yai murmushi a ransa ya ce. "Kuruciya da daɗi, daga ita har Auntyn nata yarintarsu ta yi yawa, bata taɓa soyayya ba kenan, shi ne duk ta rikicewa ƴan waɗan nan kalamai, a haka ma bata bashi damar ya saki jiki ya zuba mata kalamai ba amma duk ta rikice, bai san ita da Auntyn tata ma wacce ta fi kuruciya ba".
Da ya gama gani sai ya miƙo mun wayar tare da komawa ya zauna, ya ɗaga Hussaini ya mayar kan cinyansa, coz Hussaini irin halin Abban ne da shi, bashi da yawan magana, and yana da hankali da natsuwa, Hassan kam, ba'a magana, mafaɗaci ne na gaske, ga bakin zuciya.
Na karɓi wayata na koma na zauna a kan kujera, na shiga chat na Safiyya na fara dubawa, ina karantawa ina murmushi, Abba ya tsareni da ido dan bana kallonsa, ya dinga mamakin yarinta irin tamu daga ni har Safiyya, sai da na kammala karantawa tsab sannan na ɗago kai, da sauri ya ɗauke kallonsa daga kaina.
Zan yi magana wayata ta ɗan yi kara, na sake dubawa, sako ne ya shigo Whatsapp ɗin amma da sabuwar number, hotuna ne dayawa aka turo mun. Da sauri na shiga dan ganin wanene?. Ya Salam, wani irin fargaba da tashin hankali na shiga, jikina na rawa na fara bibiyar hotunan ina karanta chat ɗin, hankalina a tashe.
A kan wani hoton chat na tsayar da idona, zuciyata na rawa, duk wani murmushin dake kan fuskata ya kau, harshena na rawa na cigaba da karanta chat ɗin nan, wannan hoton da na tsayar da idanuna a kansa ya fi kowanne gigitani, ko ban san wacce ta turo mun ba yanzu na gane Zainab ce, chat ɗinta da Abbie tai screenshot ta turo mun. Ko a ina ta samu numberta?.
A wannan hoto da na tsai da kallona na karanta shi ya fi sau hamsin, Abbie ne ya rubuta mata saƙo kamar haka. "Na sani, nasan zaki iya, dan mu wannan a jininmu yake, nasan ko da nafi haka karfin sha'awa zaki iya ɗaukata, my happiness please ki cika alƙawari, dan wlh ni kaɗai nasan irin azabar da nike ciki na rashin samun biyan buƙatata yadda yakamata, Aisha kin san komai a kanta, ta yi karama a farkon aurenmu, har a yanzu ma, bata iyawa, shiyasa kika ga na matsu ayi wannan aure, ina cikin wani hali, please kada ki bani kunya".
A ƙasan wannan hoto Zainab ta rubuta mun saƙo kamar haka. "Ku dinga iya ɗaukar nauyin mijinku, ba ku barsu da ciwo a mara har sai ta kaisu wuya sun ji kamar zasu mutu su fita nemanwa kansu mafita wajen zafafa kamarmi kuma ku tashi kuna ihun baku son kishiya ba, ku dinga ƙoƙarin sauke hakkin aure, ba ku bar miji yana neman budurwar da zata iya da shi ba".
Wani irin sama-sama na ji numfashina na yi, a hankali na fara ganin duhu-duhu, wlh ban taɓa gaza sauke hakkin bawan ALLAHN nan ba, tabbas bani da sha'awa ko kwatan wanda yake da shi, amma bai taɓa zuwa da buƙata naki ba, ko bana so, ko bana ra'ayi ina dannewa in biya mashi dan gudun ya faɗa wani hali tun da nasan matsalarsu, amma yake cewa ina barinsa da ciwo a mara, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Wani irin sara mun mai tsanani da kaina ya yi ne yasa ban san lokacin da na saki wayata ta faɗi ƙasa ba.
Abba ya ɗago ya kalleni, kafin yai magana sai gani yai na sulale ƙasa na kwanta flat bana numfashi........... NAMIJI BUHUN ƘAYA.
Ai cikin zafa Abba yai kaina yana kiran sunana, ina, ai na suma, su Hassan duk suka yi kaina, ɗaukar wayata Abba yai dan ya ga me yafaru na suma shi da ya bari ina chat da Safiyya ina murmushi.
Shi kansa da yake namiji sai da waɗan nan chat suka buga kansa bare ni, wani irin ɗaci ya ji a zuciyansa, jikinsa har yana tsuma saboda ɓacin rai, cikin zafa ya goge dukka chat ɗin, ya yi blocking number Zainab, sannan ya goge number gabaɗaya daga wayan, bai taɓa tsammanin Zainab bata da hankali ba sai yau.
Ya ɗauki wayoyin da nawa da nasa ya shiga cikin ɗakinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya, da yake yana da karfi ina sume amma ya ɗaukeni cak muka nufi mota, ya shigar dani gidan baya, ya sanya Hassan da Hussaini a gaba, ya shiga driving seat sai asibiti
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔