LABARIN AISHA

PART 9

by @queenofsurprise1

Ban tashi farfaɗowa a asibitin ba sai can yamma, ina buɗe idanu sai kan fuska Abba dake zaune saman kujera rike da kwalayen magunguna yana dubawa. A wani irin slow ya ɗan kai kallonsa kaina, ganin na waro idanuna waje yasa ya juyo kai da kyau, sai dai bai yarda mun haɗa ido ba, a sanyayye ya ce. "Sannu Auntyn tawa".

A daidai lokacin Abbie ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin magani da fruits, shi ya kawo wanda Abba yake dubawa ɗin nan ma, coz ya ta fi sayo saura ne, magunguna ne da allurai. Hankali a tashe Abbie ya ƙariso kusa dani ganin na farka, ya zauna a gefen gadon tare da rike hannunna, ya ajiye ladar maganin hannunsa a kusa dani, cikin sanyin muryan nan nasu na gado ya ce. "Sannu habibiya, ya jikin? Akwai in da yake maki ciwo ne?". Cike da nuna damuwa yai maganar.

Na ɗan saci kallon Abba ta wutsiyar ido, ya tamke fuska tamau tare da miƙewa, bai sake kallon in da muke ba ya nufi waje, coz haushin yayansa yake ji, saboda koma me shi ya ja, and yasan irin rayuwar da muka yi ta amana da yayansa a baya, and ya ga abin da Zainab ta turo mun, gabaɗaya ya ji ya haushin ganin yayan nasa, dan ya ga wannan son kai ne da cin amana ƙarara, shiyasa ya tamke fuska ya fice daga ɗakin, saboda takaici ta kawo shi har wuya, baya zalunci kuma baya goyan bayan ayi zalunci, kowaye yai rashin gaskiya ba zai goya mashi baya ba, koda uwar da ta haifesa ne, shiyasa gabaɗaya haushin yayan nasa ya kama shi.

Ban ji daɗin yadda naga ya haɗe rai ya fice ba, amma na basar game da dawo da kallona a kan Abbie, muryata can ƙasa na ce. "Yaushe ka zo?"....... Yana kallona ya amsa da. "Tun ɗazun da Abba ya kirani, dama baki da lafiya ne baki faɗa mun ba? Meyake damunki? Ko dai batun auren nan ne? Na faɗa maki bana son yarinyar nan, ke kika matsa sai na aureta, and har yanzu ina kan bakata na bana sonta, in har zata sanya maki damuwa a ranki zan faɗawa Mama na janye maganata, farincikinki shi ne nawa".

A yadda yake magana billahil lazi da ace da baki Zainab ta faɗa mun chat ɗin da suka yi, tabbas da ba zan yarda da Zainab ba, da zan yarda da Abbie ne, amma ƙarara naga komai, har fa cewa yake watanni biyu sun yi nisa a saka aurensu, dan ya ƙosa ta shigo, amma ji abin da yake faɗa mun yanzu wai baya sonta, ya rabbi wani irin musifa ce wannan? Namiji, namiji, namiji, namiji zai kasheka lokacinka bai yi ba.

Amma kuma duk da haka, da soyayyar Abbie sosai a raina, sai dai na rasa yarda a tsakanina da shi, coz yanzu duk abin da zai faɗa karya kawai nike gani. Na wani kallesa, na ƙaƙalo murmushin yaƙe, ina tuna a lokacin da nike yarinya a makaranta lokacin da ake ce mun dila sarkin wayau, kuma sarkin rainawa mutane hankali da mannin hauka, tuna rayuwata na baya yasa na ce bari in gwadawa Abbie wancan halin nawa kaɗan.

Murmushin da ya fi kuka ciwo ne a kan fuskata, na ɗan nisa tare da cewa. "Me Abba ya ce maka?"......... Abbie yana shafa fuskata ya amsa da. "Ya ce kuna zaune kika yanke jiki kika faɗi, bai san me yake damunki ba".

Na ƙara faɗaɗa murmushin da nike jin tamkar wuta aka watsa mun a fuska, ina tuna kalaman yayana na kada in yarda mu yi faɗa, sai na ce. "Aure ai ni na aminta ka yi, wannan abu ne daban Abbienmu, ina son Zainab, ina son ta shigo, ko dan farincikinka dana Mama ya ɗaure da sakayyama, sannan ina son farincikinka fiye da komai mijina, duk abin da zai sanyaka farinciki ko menene zan tayaka nemansa, kasan ina sonka ko?". A yadda nike magana zaku rantse da ALLAH har cikin zuciyata ce, alhalin nan kawai ina yi ne dan makar da tunaninsa, tun da na gano Abba bai faɗa mashi komai na dalilin suma na ba.

"Nasan kina sona, nima ai ina sonki ko?".... Na jinjina kai. "Sosaima kake sona, son da kake mun ma ai ya fi wanda nike maka, na shaida, shiyasa nike sonka nike son farincikinka"....... Yai wannan murmushin nasu mai kara fito da kyansu, sannan ya ce. "To faɗa mun abin dake damunki yanzu in yi maganinsa".

Ina cigaba da murmushin dole zuciyata na kuka na amsa da. "Ina ganin fa gajiya ce kawai ta mun yawa"....... "Ko kuma damuwar abin da Mama ta maki ko?". Ya tari numfashina da faɗin hakan..... Na ɗan tsuke fuska. "Da wannan ma Abbie, coz a maka kazafin mai bin malamai ai babu daɗi".

Ya ce. "Haka ne my Habibiya, to dan ALLAH ki cire wannan damuwa a ranki, ki yi hakuri kin ji? Komai mai wucewa ne, ki sani ALLAH yana tare da masu hakuri". Na kallesa cike da mamaki, ya san ALLAH a baki tamkar da sunan a manne da bakinsa, amma yana karya dokokin ALLAH, yana fakewa da sunan ALLAH ya ci amana.

Na ce. "Ai komai ma ya wuce Abbiena, yanzu dai ina neman wata alfarma"..... Ya jinjina kai alamar yana saurarona, coz daga shi har Abba wlh basu da yawan magana, kuma basa son hayaniya, in kunga suna magana to da ni ne, ga dai su Khalifa a gidanmu suke kwana in sun dawo daga shago, amma ba zaka taɓa jin Abba yana magana da su ba, kuma ɗaki ɗaya suke.

"Abbie ina son zuwa Kaduna gobe, yaya baya jin daɗi, sannan please ina son wani abu ɗaya"...... Ya kalleni kafin ya ce. "Okey to ALLAH ya kaimu gobe sai Abba ya kaiki, amma da kin bari kin kara samun sauki tun da naga akwai allurai ma a cikin magungunar naki".

Na girgiza kai. "A'a, zuwana can shi ne samun sauƙin nawa, ka barni kawai in je". A cikin kwayar idanunsa na ga alamar farinciki da tafiyar tawa, watau a gidan ina takura mashi baya samun damar yin waya da Zainab tsakar dare. Ya jinjina kai tare da cewa. "ALLAH ya kai mun ke lafiya ya dawo mun dake lafiya Matata, menene abu ɗaya da kike so ɗin kuma?". Yana ɗan murmushi ya faɗa.

"Ina son dan girman ALLAH Abbie kada ka taɓa kama sunana a wajen macen da zaka aura, bana son ka taɓa magana a kaina ko ya yake, ku yi hirarku iya abin da ya shafi tsakaninku, babu ruwanta da batuna, please ba dan ni ba, dan ALLAH, kome zata tambayeka a kaina bana son ka faɗa mata, in short da akwai dama ma ko sunana bani da buƙatar ta sani".

Ya kara riƙo hannuna da kyau kafin ya ce. "Na yi maki alƙawarin hakan, dama ni ban taɓa maganarki ko da dasu Mama bane bare kuma wacce zan auro, sirrinmu sirrinmu ne, abu ne da yake a tsakaninmu".

Yau na kara tabbatarwa wasu mazan basa tsoron ALLAH, ya zauna ya gama faɗawa Zainab bana gamsar da shi ɗin, yanzu kuma wai sirrinmu sirrinmu ne, kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wai wasu mazan ina suke son kai haƙƙi a kansu ne? Wasu kuwa anya zasu ga Annabi? Waye yasan ma me dame yake faɗa mata, amma wai sirrinmu sirrinmu ne, kai jama'a.

Muryansa ta katse mun tunani da cewa. "Akwai abin da kike so ne kuma?"...... Da sauri na girgiza mashi kai alamar a'a, na yi shiru ina tunanin rayuwa. Muhammad na a kwance a gefena yana ta sharara barcinsa.

A ɓangaren Abba kuwa, tun da ya fita ya zauna a kan kujerun bakin kofa, ya haɗa kai da gwiwa, zuciyansa tamkar zata fashe, ya tsani cin amana da tauye yarda, zamba cikin aminci, shi da yake matsayin kanin Abbie ma ya shaida na tallabi rayuwansa, ni nake biya mashi kuɗin makaranta, komai yake so ni yake tambaya dan yasan yayansa ba zai bashi ba, Abbie mutum ne da bashi da kyauta sam, shiyasa ƴan uwansa suke kuka dani, wai yana da shi na hanasa taimaka masu, shiyasa suka shirya shigo da Zainab a tunaninsu ita tasu ce zata dinga kwasa tana kai masu, basu san ɗan nasu ne bashi da kyauta ba, ko wanda suke samu ake masu suna rainawa ma ni nike masu ba shi ba, shi kam ba'a cin kuɗinsa.

Ko batun kwallon Abba ni na tsaya mashi, yanzu haka zai shiga gasar kwallon kafa ta jaha, na kashe kuɗi a kan hakan ya fi a kirga, ko sutura ni nike sayawa Abba, na hanasa kasuwanci, na ce ya zauna ya natsu yai karatu, yanzu brother na Ahmad ya shiga hundred level a jami'a, ina ta fama da shi shi ma ya ajiye kasuwancin nan ya mai da hankali ga karatu, amma ya kafe zai kula da dukiyata, idan bai da class yana shago, Abba kuwa ya kafe zai kula da kwallon kafa, idan bai da class yana wajen training na kwallo. To shi da yake ƙanin Abbie ya raɓu da Abbie ma ya ci arzikina ya shaida na mashi kuma yana jin zafin abin da ake mun bare Abbie, amma Abbien bai nuna wani damuwansa a kaina sosai ba.

Ni kuma har yanzu fa bin shawarin yaya kawai nike yi, amma bawai bana son Abbie ko na yarda zai ci amanata ba, ina ganin kamar kawai yanzu Zainab na ɗauke mashi hankali da kafuran tsiraran kalaman nan nata marasa tsarki ne, a tunanina da sun yi auren shikenan hankalinsa zai natsu ya dawo jikinsa.

Abba na kife da kai yana tunanin rayuwa sai ga kiran Safiyya ya shigo wayana, ya fitar da wayar daga aljihunsa, yana ganin na rubuta half of my life ya ɗan sauke ajiyar zuciya, coz yasan itace, pick-up yai tare da kara wayar a kunnensa, cikin shagwaɓa Safiyya ta ce. "Aunty wai ina kike ne ban ganki a Whatsapp ba? So nike ki faɗa mun amsar wani abin".

Ya sake nisawa kafin ya ce. "Shagwaɓaɓɓiyata kuma rigimamma, to ba Auntyn bane, a haka kike cewa in canza hali ko my Sofi? Yanzu dai ga shi kina ji kin fini iya shagwaɓa sai rigima". A sanyayye sosai ya faɗa....... Dariya ta ɗan yi game da cewa. "Kaga Malam bawa Auntyna wayanta hai, kuma ni ba irinka mata maza bace".

Uhm ya furta damuwa cunkushe a ransa, zai yi magana ya ga Abbie ya fito daga cikin ɗakin, sai ya miƙe tare da cewa Safiyya. "Zan kiraki idan na koma in da take, bama tare". Bai jira amasarta ba ya katse kiran. Da sauri ya ƙarisa shigewa cikin ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama.

Tun da ya shigo na zuba mashi idanu, ban yi magana ba har ya ƙariso in da kujerar yake, shi kuwa tun da ya shigo kansa a ƙasa, saboda har yanzu baya iya haɗa ido dani tun wancan magana da muka yi.

A kujera ya zauna tare da cewa. "Aunty ya jiki?"........ Still ina kallonsa na amsa da. "Da sauki sosai nawan, Nagode ALLAH ya biyaka da jallatul firdaus, ina wayata?". .... Sai a lokacin ya ɗago kansa da kallonsa, ya ɗan saci kallona game da sauke idanunsa ƙasa da sauri, ya miƙa mun wayar dake hannunsa bai yi magana ba.

Na karɓa, jikina na rawa na shiga Whatsapp ɗina dan in sake duba da gaske ne abin da na gani ɗazun ko mafarki? Sai dai ina shiga ban ga komai ba, slowly na wurga eyes ɗina a kan face ɗinsa, da sauri ya sauke idanunsa ƙasa bai yi magana ba, dama ashe kallona yake yi dana karɓi wayan.

"Nawan ina chat ɗin da Zainab ta turo mun suke?". A ƙage na faɗa........ Can ƙasa ya amsa da. "Na gogesu, dan bana fatan ki sake ganin makamantansu su ɗaga maki hankali"...... Zan yi magana yai saurin cewa. "Please My Aunty, dan girman ALLAH ba dan ni ba, ki watsar da dukkan wasu al'amurran da suka faru da ma wanda zasu faru gaba, nasan da ciwo, amma ki gwada huda ganye ki zuba masu idanu ki ga me zai faru, please, ki mun alƙawarin ba zaki sake kuka ko shiga damuwa a kan wannan case ɗin ba?".

Ba dan na so ba na mashi wannan alƙawarin, na kuma sanya a raina zan yi ƙoƙarin cikawa, haka muka zauna muna ɗan hira har zuwa 5 na yamma, aka sallamemu, Abbie ya zo daga kasuwa muka koma gida. A wannan rana dai a ɗakina Abbie ya kwana, ya kashe wayoyinsa dukka biyu dan kada jarababbiyar can ta kirasa, baya taɓa kashe wayoyinsa da daddare, amma yau ya kashe, ina kallonsa, yana wani ɓoye-ɓoye dan kada na gane komai, nima ban nuna mashi kamar na gane ba, ko da ya kwana a ɗakina sam bai nemi kwanciyar aure dani ba duk da jaraba irin tasu, na yi mamaki amma na basar.

Washegari da safe muka yi shirin zuwa Kaduna, Ni, Abba, Hassan and Hussain da Muhammad ɗina, amma sai da na je asibiti na karɓi allurana na safe sannan muka zo muka fara shirin tafiya. Da na kammala shi na samu Abbie yana kwance bai shirya fita ba, sammakon zamu yi saboda mu kai da wuri dan haka ko girki ban yi ba.

A kusa da shi na zauna ina murmushi na ce. "Ango tashi zamu tafi"...... Yana kallona fuskansa wasau ya amsa da. "Kim cika zolaya Habibiya, to ALLAH ya tsare mun ku".

Na amsa da. "Amin". Sannan na ce. "Babu kuɗi a hannuna, ina son kuɗi please, zan yi tsaraba da sauran abubuwa ga kuɗin man mota"....... Ya ɗan haɗe da rai, dan shi baya son fitar kuɗi daga jikinsa sam...... "Ni ma yau bani da kuɗi habibiyata, saboda kinga jiya ina tare dake a asibiti ban mayar da hankali kan kasuwa ba, dubu goma ce kawai dani".

Hmmmm a raina na ce ko yana kasuwar ma fa yaran shagonsa ke kula da komai, amma dan kada ya bani kuɗi wai baya kasuwa bai kula da kasuwancin ba, aikuwa idan wayau ne bai fini ba, dan dila ake ce mun a school, sai na saki murmushi game da cewa.

"So nike dama in sayawa su daddyna abubuwa masu kyau da tsada ta yadda idan na je na kai masu zasu gani su yaba maka, kasan me nike so a wajensu ne yasa zan kai masu abubuwa masu kyau da tsada?". Ya girgiza kai alamar a'a.

Na ce. "Gold ɗin da daddy ya kawo mana a makka last two years ago da ya je nike son in na je in ɗauko kayana, kasan yana da muguwar tsada, ya kai 100M, to shi nike son zuwa in sayar mu kara jari a shagunanmu, kaga kaima baka da shi, sai mu farfaɗo da kanmu sosai, shiyasa nike son saya masu tsaraba mai kyau mai kuma tsada ta yadda zasu san na kara hankali da sanin yakamata, kaga daga nan idan na ce zan ɗauki gold ɗin ba zasu hanani ba, dan zasu ce ai na yi hankali, kuma kaga dama kai kam duk suna yabon kyawawan halayenka, zasu bani gold ɗin".

Ai yana jin haka fuskansa ya saki, ya saki murmushin tare da cewa. "E haka ne, idan suka ga kin natsu kin kara hankali zasu baki, zasu ce yanzu har kyauta mai tsada kike masu, gaskiya abu mai tsada da kyau zaki saya masu"....... Na ce. "To ka gani, shiyasa nace ka ɗan bani kuɗin nan, kaga idan na dawo da gold ɗin karuwarmu ne ai ko?".

Ya ce. "Kwarai kuwa ƙaruwarmu ne, dama kayan da na ɗauka a shagona ɗin nan duk bashi ne, yanzu abin da za'ayi ki sayawa daddyn abu mai kyau daga account ɗinki".

Na wani kallesa tare da jawo wayata, dukkan account ɗina na nuna mashi babu ko sisi a ciki. Ai take yai kicin-kicin da fuska, ya ce. "Ina kika kai 5M dake ciki? Har ina shirin karɓarsu in sayi kaya a satin nan! Me kika yi da su!". Cikin faɗa yaƙe tambayar.

Da yake neman yadda zan karɓi kuɗi a hannunsa nike sai ban tada hankalina ba, dan namiji idan kana son abu a hannunsa sai ka mashi wasu dabaru, sai ban nuna mashi babu kuɗin ba, dan in na nuna mashi babu ba zai bani wani kuɗin ba, sai na ce. "Kaya na saya a shago, kuɗin suna nan, kaga idan na zo da gold ɗin nan muka sayar ba shinenan sai ka ɗauki 50M ka zuba kaya naka na kanka a shagon ba bashi ba ko? Kaga 50M zaka samu bama 5M dakake tunanin karɓa ba".

Ya wani sauke ajiyar zuciya, sai ya ce. "Haka ne, amma fa ki kula da kayan da kika sake zubawa a shagon nan, baki tambayi shawarina ba ai da ba zaki kara kaya a ciki yanzu ba". A raina na ce watau kuɗin shagon ma na kula dasu dan ka zo ka sake kwashesu ko.

A fili kuwa na ce. "Lokacin da na zuba kayan Mama ta hanamu ganawa da juna ne yasa ban nemi shawararinka ba, amma ai kasan bana yin komai sai da izininka ko?"..... Ya ce. "Haka ne, to shikenan yanzu ya kike so ayi?".

Na gyara zama tare da cewa. "Yanzu ina son ka bani aron 5M ne, zan yi wa daddy sayayya masu kyau, idan na dawo da gold ɗin nan sai mu sayar in biyaka"...... Da yake yasan iyayena masu akwai ne, ko fin haka na ce ina da shi a gold ba zai musa ba, sai ya ce. "Kuɗin Sadiq ne fa a hannuna, amma tun da kin ce idan kin dawo zamu samu kuɗi sai mu mayar mashi, mu je ɗaki akwai cash in baki".

Sarai ba wani kuɗin Sadiq, dan wlh Abbie baya haɗa dukiyansa dana kowa na sani, ko lokacin da ya shiga talauci tamkar zai mutu ba yadda abokansa basu yi da shi kan ya dinga kwasan kaya bashi yana sayarwa ya cire riba ya mai da uwar kuɗi a manyan stores da suke ɗauka ba suma, amma Abbie yaki, dan haka duk kuɗin da za'a gani a hanunsa nasa ne, kawai bayarwa ne ba zai yi ba, idan kuna neman mutum mara kyauta to daga kansa an rufe kofa, sai ka rasa ina zai kai kuɗi, ko su Hassan fa baya saya masu sutura, ya sake mun komai na ragamar gida tamkar ni ce mijin, na ciyar da mu na tufatar damu, na yi wa iyayensa shatara ta arziki su zaci shi yake masu har suna rainawa suna faɗin na hana shi yi masu abin da ya dace.

Aikuwa muka je ɗaki ya jawo laptop bag a karkashin bed ɗinsa, ya buɗe ya ciro kuɗin nan sabbi gal-gal, makudai, rafan dubu ɗaiɗai na dubu ɗari kowanne, haka ya kirga 5M cir ya bani, yana bani yana kara jaddada mun in fa dawo da gold ɗin nan dan mu mayarwa da Sadiq kuɗinsa, na ce mashi babu komai, ai yasan ni kuɗi ba matsala bace a gidanmu, ya ce haka ne.

Watau namiji idan kana son samun kuɗi a hannunsa ka nuna mashi idan ya baka zai samu ninkin banikin abin da ya bada, shi ne zai saki jiki ya baka.

Aikuwa na ɗauki kuɗin nan, na shiga ɗakina na kwashe dukka sarkokin gold ɗina guda uku da suke wajena dama, kowanne a kallah darajansa zai kai 50M, hajiyarmu ce da ta je Makka ta kawo munsu, sarka ce da ƴan kunne masu kyau, aikuwa na kwashe kayana na zuba cikin jakar kuɗin da ya bani ba tare da ya sani ba, muka yi sallama na fito........... To fa yanzu labarin Aisha zai fara.

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

LABARIN AISHA.🥹💔