LABARIN AISHA

PART 10

by @queenofsurprise1

Ina fitowa na samu Abba a cikin mota zaune yana jirana, har sun shirya kayanmu a cikin motar. Na shiga gidan gaba, Hassan da Hussaini suna baya, ya miƙo mun Muhammad dake hannunsa, still bai ɗago mun haɗa idanu ba ya ce. "Aunty mu je ne?".

Na amsa da yeah, ya tada mota muka nufi garin Kaduna, sai surutu su Hassan suke yi, da yake ban yi barcin safe ba yau, sai muna kama hanya na langwaɓar da kaina a jikin kujerar motar na hau barci abina, Abba yana driving yana juyowa ya kalleni, coz ya ga Muhammad idanunsa biyu, kada yaron ya faɗi, sai ya raba hankalinsa gida biyu, daga karshe ma sai ya faka motar a gefen titi a wuraren tsakanin jaji da Zaria, yana tsayawa ya miƙa hannu ya ɗauko Muhammad ɗin, ya ɗaura shi a kan cinyarsa, ya ɗan zuba mun ido kaɗan, sai kuma ya saki murmushin shi kaɗai, a ransa ya ce. "Fuskan Aunty babu banbanci dana Safiyya fa, gaskiya I'm very very lucky idan na samu Sofi, family ɗinsu ga kyau ga kyan zuciya".

Ya tada mota dan mu karisa Kaduna. Kafin mu isa Hassan da Hussain ma sun yi barci abinsu, Muhammad ma ya yi barci jikin Abba. Bamu san lokacin da muka isa ba, sai ji kawai na yi Abba na hura mun iska a fuska yana faɗin. "Sarkin barci tashi ki kira su Mammy mun iso su yi umarnin a bamu hanya".

Ina buɗe idanuna na sauke a kan fuskansa, da farko ma sai naga kaman Abbie nike kallo, ganin babu saje a face ɗinsa yasa na gane Abba ne, coz Abba na aske sajensa kaff baya bari. Na turo baki tare da cewa. "Kai me zaka wani tadani? Kai baƙon gidan ne? Ko basu sanka bane da sai na kira ciki na sanar mun zo?". Na faɗa ina ɗan miƙa game da tamke fuska.

Yana ta kallona bai yi magana ba, amma kuma bai kalli fuskata kai tsaye ba, dan baya son mu haɗa ido. Na ce. "Danna horn na motar mai gadin ya fito".

Shiru bai danna ba, sai da na juyo da kallona kansa ina ƙoƙarin gyara zamana, sannan ne yai saurin ɗauke kallonsa daga kaina tare da danna horn na motar. Sai ga mai gadinmu ya fito da sauri.

Da hannu naiwa mai gadin alama da ya buɗe gate, da gudu ya koma ciki ya buɗe, na dawo da kallona kan Abba, sai na ga alamar kamar ɓacin rai a kan fuskansa, ya ɗaure fuska tamau, ya tada motar da sauri muka kutsa ciki, da mamaki nike kallonsa, coz yanzu fa ya mun murmushi, to me yake damunsa ne?.

Ya nufi parking space na gidanmu, yana faka motar bai yi magana ba kuma bai juyo ya kalleni ba, a natse na ce. "Nawan lafiya? Ya na ganka haka?"..... Kai ya ɗan girgiza. "Babu komai". Ya faɗa a dake. Still bai juyo ba.

Zan sake yin magana ya ɗaura mun Muhammad a kan cinyata ya buɗe kofar motar ya fita, ya buɗe gidan baya ta ɗauki Hassan, daidai lokacin Safiyya ta fito waje da saurinta tana faɗin oyoyo rabin rai, masoyiya ta zo. Yana ɗauko Hassan yana juyowa suka yi kiciɓis da Safiyya, tana sanye da simple abaya mara nauyi a jikinta, kai ba ɗankwali, gashinmu na fulanin nan bakin kirin har gadon bayanta.

Suka kalli juna da Abba, ya ɗan ɗauke kallonsa yana faɗin. "Yauwa zo ga babana nan ki shiga da shi ciki". Hassan takwaran babansu ne dama......... Tana satar kallonsa ta matso zata karbi Hassan, tai ƙasa da murya wajen cewa. "Dama da kai za'a zo?".

Kai kawai ya jinjina mata bai yi magana ba, still dai baya cikin mood mai kyau, kome ya canza mashi mood a ɗan ƙanƙanin lokacin nan, oho........... Ta karɓi Hassan tana sakar mashi murmushi, shi kam fuska a tamke ya juya ya fito da Hussain, ya miƙawa House girl ɗinmu da ta fito yanzu.

Sannan ya dawo driving seat ya zauna bai ko kalli in da nike ba. Su Safiyya suka tsaya jirana in fito, ni kuwa na ƙasa fitowa dan naga kamar Abba baya jin daɗi, hakan yasa nima ban ji daɗi ba, ni mutumce da duk wanda yake tare dani in baya farinciki nima ina shiga damuwa, sai da na jira ya dawo cikin motar sannan na kallesa game da cewa. "Nawan please menene?".

"Babu komai Aunty, ki je ciki bari in je gida nima in gai da su Mama"....... Zan yi magana ya ce. "Please my Aunty"......... Hannu na kai na ja uban sumar da ya cika a kan nan nasa, sai sheki sumar take yi, ta sha gyara, na ce. "Nawan yau ni kake yi wa haka?"...... Ya ɗan tsuke fuska, sai kuma ya kara tamke fuska ya ki yai magana, na yi juyin duniyar nan yaki yai magana, daga karshe dole na hakura na rabu da shi, na haɗe rai tare da fitowa daga cikin motar, ban sake waigosa ba na nufi cikin parlo.

Ya bini da kallon ƙasan ido har na shige, ko waigosa ban yi ba, ina shiga ya tada motar ya fice daga gidan abinsa, zuciyansa cike da tunanin yadda za'ayi ya sanar da Mama tana son Safiyya har a nema mashi aurenta, coz Mama ta tsani jininmu a yanzu, ya rasa me yake damun Mama, coz ta sani mahaifina yana daga cikin sahun gaba-gana a masu kuɗin garin, nafi karfin na mallake wani namiji har ma na hanasa taimakawa ƴan uwansa, aurena da Abbie nufin ALLAH ne, amma ta ko'ina na fi karfinsa, mutane ma sai cewa suke yi asiri aka yi wa daddynmu ya aura mun shi, domin kuwa a lokacin manyan mutane na tashen zuwa neman aurena, kowa yana sona, na taso da farin jini, ga kyau da diri, amma kamar ba lafiya ba daddynmu ya kafe sai Abbie zan aura, Hajiyarmu bata so, ba irin faɗar da bata yi ba kan kada ayi wannan aure, daddynmu ya rufe idanunsa fir yaki, ya kafe sam, ko na so ko naƙi sai na auri Abbien, Hajiyarmu ta yarda asiri aka yi wa daddy ya yarda da wannan aure, amma da ALLAH ya ƙaddara akwai rabo, haka aka yi auren, ga shi har yaranmu, tsanar da dangin mijina suka mun yanzu abin yana bani mamaki, kamar ba lafiya ba, su da a baya suke tsananin sona, kai ya ALLAH.

------------------------

Ina shiga parlo na isko family an taru ana jiranan zuwana, ga daddymmu, babban yayana, yayana na biyu mai suna Abbas, sai Hajiyarmu da kanwar daddynmu Aunty Maryam.

Farinciki a wajen dangi ba'a magana, iyayena da ƴan uwana suna tsananin sona kamar su numfasa mun, take na shige cikinsu ina ta farinciki, wannnan ya ja Hassan ta nan wannan ya ja Hussain ta nan, su kuwa ƴan albarka sunan uncle Abba kawai suke kira, basu san dangina ba sai na ubansu, dan ko mun zo Kaduna a family house ɗin babansu suke sauka, ni da Muhammad kawai muke zuwa wajen iyayena, sai daga baya Abba yake kawosu su ɗan yi kwana biyu a wajen iyayena su koma wajen kakarsu, shiyasa basu saba da dangina ba, to yanzu kuma Abba ya ga abin da yake faruwa tsakanina da kakar tasu, shiyasa ya bar mun su a nan.

Bayan komai ya lafa na oyoyo da ganina, na ci abinci na ƙoshi, na nufi ɗakina a gidan dan hutawa. Na kwanta na sha barcina ni da Muhammad ɗina, sai yamma na farka, ina fashin sallah dan haka ba wani sallah da zan yi, ina farkawa nai wanka na shirya cikin doguwar riga ta atamfa na fito, kai tsaye side na yayana na nufa, yana zaune a parlonsa na iskosa, muka gaisa sannan na ce mashi gani nan. Ya ce. "Gobe zamu je Abuja ni dake, ki faɗawa Sulaiman, tafiya takama mu".

Na amsa da okey, sannan na labarta mashi yadda muka yi da Abbie kafin in zo da safe, ga kuɗin da ya bani, sannan na ɗauko gold ɗina da yake gida. Ai ba ƙaramin daɗi yaya ya ji ba, ya dinga saka mun albarka, ya karɓi kuɗin, shi kuma gold ɗin ya ce in kaiwa hajiyarmu ta ajige mun, na amsa da okey.

Na kira Abbie na faɗa mashi tafiya ta kamamu zuwa Abuja ni da yaya, ya amsa da ba damuwa adawo lafiya. Ina gama waya da Abbie zan ajiye wayar sai naga alamar sms da aka mun tun karfe 1:30 na rana.

Ganin number Abba da na yi saving da NAWAN ne yasa na buɗe saƙon. Messenge ne ya rubuta kamar haka. "I'm so so sorry Auntyn tawa, ɗazun ban kyauta ba kina magana na yi shiru, ban san me ya shiga kaina ba, kawai na ji ina jin haushin kowa a lokacin, amma ki yi hakuri ba zan sake ba, daga nakin Abbatiti".

Na ɗan yi murmushi, sai na danna mashi kira ina mikewa, na fito daga side na yaya, yana ɗauka na ce. "Mara kunya, watau kasan baka kyauta ba ko?"........ "E mana, nasan na yi laifi, to amin afuwa kin ji tawan? Ina matata my Sofi?".

"Ba zan yi afuwan ba, sai ka yarda zaka zo mu ci abincin dare a nan, Sofi ma tana jiran ka zo ku yi dinner a tare"....... Ya ɗan zare ido, yana kwance kan katifarsa a gida, ya ce. "Kai a'a, me ya kaini zuwa gidan surukai cin abincin dare? Rufa mun asiri, ni da so nike in zo neman auren Safiyya a bani ita cikin girmama juna, sai kuma in zo dinner can, gani ga Safiyya, ga daddy, ga Hajiya, gaki duk a parlo saboda bani da kunya ko? A'a ba zan zo ba ni kam".. ....... Tun da ya fara magana nike dariya, saboda nasan halinsa da shegen kunya, wlh Abba baya iya cin abinci a gaban kowa idan ba ni da yayansa ko mamansa ba, mugun kunya garesa, nasan kome zan ce wlh ba zai zo gidammu ya ci abinci ba, nasan halin kayana.

"To in dai ba zaka zo ba kada ka sake kirana, ban hakura ba, mun ɓata"....... Ya marairace murya game da cewa. "Please tawan, wlh ba zan iya bane, kin fi kowa sanin halina, dan girman ALLAH kada ki sakani abin da ba zan taɓa iyawa ba, ba zan iya kin maki abin da kike so ba, amma wannan ya yi tsauri dayawa, ina kunyar hajiya, ina kunyar daddy, ga su babban yaya ma, please Aunty ki yi hakuri ki duba lamarin".

Na ce. "Mara kunya, zan yi tunani a kai to". Ya amsa da okey ya gode a gaida mun da matata duk da yanzu muka gama waya, na ce okey, muka yi sallama, da daddare na sanya aka shirya mashi abinci mai rai da lafiya, na baiwa driver ɗin hajiyarmu na ce a kai mashi. Lokacin da aka kai mashi abincin ya kirani ya dinga zuba mun shagwaɓa da godiya, wai dama bai san ya za'ayi ya samu abincina ba, coz na ɓata shi da irin ɗanɗanon gidanmu.

Ina zolayarsa na ce. "Nawan ko dai saboda irin ɗanɗanon girkin gidanmu kake son aure mun Safiyyata?"....... Da sauri ya ce. "A'a Aunty, ALLAH sonta nike yi da gaske ba saboda girki ba". Na yi dariya, a haka dai muka yi sallama. Washegari Abba da Hassan and Hussain suka juya zuwa Kano, ni da yaya kuma muka tafi Abuja.

Jama'a yayana ya bani mamaki, ya cika cikakken ɗan halak, ya cika yaya na gaskiya. Muna zuwa Abuja aka kawo mun takarda in saka hannu, ya salam, mamaki ya kamani, yaya ya je ya saya mun fili har plot biyu cikin wani King estate a Abuja, duk plot ɗaya 10M haka ya saya mun plot biyu a jere waje guda, sabon estate ne fili babu tsada sosai a can.

Na sanya hannu a takarda cike da murna, ya ce. "Sai da na maki ciko, dama kuɗinki 13M ne, sai 5M da kika bani jiya, dan haka na maki cikin 2M shi ne ya haɗu 20M muka sayi filin"........ Na dinga murna ina tsalle, ya ce. "Yanzu wata mai zuwa za'a fara ginin fili, ki yi ƙoƙarin tattara kuɗaɗenki dake hannun mijinki, ki samu ki gina gidajen nan dukka biyu, ɗaya ki sayar in kin kammala ginin, idan kin sayar zaki samu kuɗi dayawa a dunkule sai ki buɗe babban shagon abayars a nan Abuja akwai samu, In Sha ALLAH taimakon da bai fi karfina ba zan dafa maki, ALLAH ya taimaka ya baki sa'a, ki mai da hankali"..

Farinciki tamkar in yi ihu, na rungume yaya ina murna, da haka muka dawo Kaduna da takardun filayena guda biyu, ɗaya zan gina in sayar, ɗayan yaya ya ce in gina in barsa ko dan yarana, bamu san me gobe zata zo da shi ba, ka gina gida a Abuja ka sayar ba ƙaramin kuɗi yake kawowa ba, yana ta mun fatan alkhairi, amma ya ja kunnena kan kada in yarda in faɗawa kowa, domin iya daddynmu kawai ya faɗawa shi ma.

Na amsa da In Sha ALLAH ba zan faɗawa kowa ba, sai addu'oi da godiya nike ta mashi, ya ce babu komai, daga wannan rana na ware cewa kowani sati a ribar da muke zamu zamu cire rabi da kwatan ribar mu sanya a asusun gini, sauran kwatan ribar kuma za'a ajiye domin biyan ma'aikata karshen wata, na yi wannan tsari ba tare da na faɗawa kowa ba face yayana da Ahmad dake shagona, Ahmad ya sanya albarka sosai, ya dinga mun faran alkhairi.

Na shirya na je gidan Mama na gaida ita, nan na samu wannan Zainab ɗin, ina shiga bayan mun gaisa da Mama na zauna gefe, sai wani hararans Zainab take yi, da alamar Abbie yasa yarinyar ta gama raina ni, dan wani irin ƙasƙantaccen kallo mai muni take mun, sai duk na sha jinin jikina, na ji wani iri tamkar, na takure waje guda ina nadamar zuwa na gidan.

Ina zaune ta yi picking call tana faɗin. "Mama baby ya kirani". Mama da su Aunty Khadija suna ta dariya, ta sanya wayar a H-free. "My happiness". Karaf muryan Abbie ya dira a kan kunnena. Na ɗauke kai tamkar ban ji ba. Zainab ta wani kashe murya, ko kunyar Mama bata ji ba, ko da yake dama bata da kunya ko kaɗan, ta ce. "Ina ka jefar da wayar nike ta kiranka".

Abbie ya ce. "Barci fa nike ta faman yi my happiness"........ Ta ce. "Ka zama gauro ba dole ka yi ta barci ba"...... Da buɗar bakinsa sai cewa yai. "Ai ni dama kullum gauro ne, me maraben dambe da faɗa, ke dai bari in yi sallah zan kiraki"....... Ta wani kashe murya game da cewa. "I love you my baby, ka kula mun da kanka".

Ya amsa da. "I love you too my happiness ne, ai kula maki da kaina yazama dole, ni naki ne ke kaɗai"........... Ban san ya aka yi ba sai na ji dariya ya kubce mun, wai ni naki ne ni kaɗai, maganar da kullum yake faɗa mun kenan, kai mutum ko ya mutu sai an ɗauresa, Abbie duniya.

Wlh sai na ji Zainab ta mugun bani tausayi, ita kuwa sai wani yanga take tana nuna mun ta isa ai ya ce shi nata ne ita kaɗai, tana wani fari da ido, har da hararana, dariya kamar zai kasheni, na dinga tikar dariya kamar na zare, har ban san time da suka yi sallama ba. Na miƙe tsaye ina yi wa Mama sallama, na ɗauko kuɗi 50k na ajiyewa Mama a kan hannun kujera na juya ko sauƙo Muhammad daga bayana ban yi ba, na nufi waje ina cigaba da dariya ƙasa-ƙasa, kai Maza, Maza, Namiji duniya, wai nata ita kaɗai, kullum na ALLAH ne sai ya faɗa mun shi nawa ne ni kaɗai, kai ALLAH ya yafewa maza ya shirya mana su.

To a taƙaice dai satina biyu a Kaduna na fara shirye-shiryen komawa Kano, Abbie na can na jirana in zo da gold mu sayar, saboda wannan gold ɗin yasa yake kirana kullum, da ya kirani mun gaisa sai ya ce mun su daddy sun bani gold ɗin nawa? Ni kuwa na ce mashi a'a sai na tashi dawowa.

Yau da zan koma kuma ban faɗa mashi yau zan dawo ba, Abba kawai na kira na faɗawa cewa driver Hajiya zai dawo dani, Abba sai murna yake yi, coz sun yi kewata a gidan, saboda school yasa basu zauna dani a Kaduna ba suka dawo, amma fa kullum sai Abba ya kirani ya ji yaushe zan dawo, wani lokaci a rana sai ya kirani sau 10, haka kawai sai ya kirani, wani lokaci in na ɗauka na ce ba ɗazun muka gama magana ba, sai ya ce bani yake son kira ba mistake ne, wani lokaci kuma sai ya kirani wai zai bani labarin abin da su Hassan suka yi, Abba da bashi da yawan magana amma sai ya zage a waya yana mun hirar abubuwan da su Hassan suke yi a gida.

Wani lokaci video zai kirani wai in ga abin da yarana suke yi na ɓarna a gidan suna saka shi aiki, shi yake shara ya ɓata duk abin da suka gyara, kunga dama ni nike aikin gudana, saboda zafin kishina yasa ban ɗauko ƴan aiki ba, kada ma wata ta aure mun Abbie, amma na gudu ban tsira ba ga shi Abbie zai yi aure, ALLAH ya kyauta.

So haka Abba zai kirani video call ya ajiye wayar a gaban parlo ina ganin irin wasan da su Hassan suke yi, duk sun watsa parlon, yai ta faman gyarawa, sun yi ciye-ciyen kayan kwaɗayin da ya saya masu sun watsar dana watsarwa, sun bar ledoji a ƙasa, yana tattarawa yana mun mitar shi lallai in dawo ya gani da aikin mata. In ta dariya ina murna, dan haka yau da zan dawo shi kaɗai na faɗawa zan dawo. Na shirya muka fito domin a mayar dani, muna fita gidammu da layin unguwarmu kenan muka kusa yin karo da wata dankareriyar mota mai mugun kyau. Driver hajiya ya tsai da mota tare da fitowa dan ya duba ko bai karcemu ba, shi ma mai motan can ya fito, yana fitowa wa zan gani? Ibrahim tsohon saurayina.

Shi ma yana fitowa idanunsa a kaina ta gaban glass ɗin mota, dan a gaba nike zaune, tabbas mun ɗan karci motarsa kaɗan, amma da ya ga nice a cikin motar sai bai ce komai ba, ya ce da driver Hajiya babu komai mu je tsautsayi ne ALLAH ma ya takaita, yana magana yana kallona, Ibrahim ya kara kyau sosai, kamanninsa na fulani ya fito sak, duk da yake ɗan siriri da yake yanzu kuɗi ya zauna mashi ya ciko ya yi kumari.

Amma fa batu na gaskiya Abbie ya fi Ibrahim kyau, coz Abbie mahaifinsu buzu ne, Mama kuma shuwa arab ce, kyansu kala biyu ya haɗe, ta ko'ina sun gado kyau, Ibrahim kuma irina ne, Babansa bafulatani, mamarsa hahausa, nima haka, daddynmu bafulatani, hajiya bahaushiya, shiyasa kyansu Abbie ya fita daban.

Na dinga kallon Ibrahim shi ma yana kallona har ya koma cikin motarsa, ya zauna, ya jingina da jikin kujerar motar ya lumshe idanunsa kamar mara lafiya, driver ɗin hajiyarmu ya tada mota muka koma baya, muka ratsa gefen Ibrahim muka wuce, yana jin mun tada mota ya waro idanunsa a kaina, bai ɗauke kallonsa ba har muka wucesa, ya nisa tare da cewa. "Ba zan taɓa daina sonki ba Aisha, har yau ban cire ran zan sameki ba". A fili ya faɗa, ya jima a zauna a wajen kafin ya kunna motarsa ya bar wajen.

To ga A'isha fa zata koma ba tare da gold ba, ko ya zasu kare da Abbie? Akwai case a Kano fa jama'a.

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

LABARIN AISHA.🥹💔