PART 13
Sai kuma dariya ya kubce mun na ce. "Yaushe ƙanina ya zama malamin duba?"......... "Ban zama malamin duba ba, kawai dai na ji hakan ne a jikina"........ "To ba wani kukan da nike yi"...... Ya ɗan yi murmushi tare da cewa. "Na maki farin sani fa Aunty, to amma shikenan, tun ban yi nisa ba har kewanku na neman yi mun illah, shiyasa na kiraki".
Ina murmushin ga sauran hawaye a fuska na amsa da. "Uhm nawan ni kaɗai nasan irin kewarka da zan yi, please ka kula mana da kanka, idan ka samu lokaci ka dinga kiranmu muna gaisawa"........ "Kiranku ai ya zama dole my Aunty, zamu yi waya anjuma, ki kula kin ji?".
Na amsa da In Sha ALLAH. Muka yi sallama, na buga uban tagumi ina tunanin yadda zan rayu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, na kara kwantar da kaina ga Abbie, ban taɓa nuna bana son auren nan nasa ba, na dage na mayar da hankali kan karɓar kuɗi a hannunsa domin kaɗa kayan lefe.
Batun gold kuma in ya tambaya sai in ce mashi Yah Abbas bai dawo ba, ba su yi hutun school ba, ranar da ya matsa mun na ce to ya kira Yah Abbas ɗin mana ta tambayesa, nasan ba zai iya kira bane yasa na ce haka, dole ya hakura yana ta fushi, na yi shiru ban kula ba.
Sai da ya sauƙo daga fushin nasa ne na sake kai mashi lissafin kuɗin lefe, ya sake bani kuɗi, na dinga nuna mashi ina tausaya mashi, dan haka kayan lefen na nuna mashi ai ɗan daidai zamu haɗa domin tausayinsa da nike ji. A tunaninsa Aisha mara wayau da ya sani a baya ce, sai ya yarda ina mugun tausaya mashi kamar a baya, so duk abin da na kama mashi kuɗin sai ya biya dan yana ganin na kure neman mashi sauƙi, kun san maza ba sanin kuɗin abubuwa suka yi ba, ba komai suka san farashinsa a kayan mata ba, bare kuma quality, aikuwa na ce in kasan wata baka san wata ba.
Na dinga zare kuɗina a hankali a ciki, ya gama sake jiki ina ta haɗa mana kayan, do na haɗa kayan Zainab yadda na yi ra'ayi, amma ba yadda ya zata ba, sai na tsuga mashi kuɗi kan abu, dan in zare dukiyata, saboda duk da kuɗina ake wannan, abin 50k sai in ce mashi 70k ko 80k, to kun san za'a kara aure lallaɓa uwar gida ake yi, ba'a son amun ba daidai ba, ya samu ma ina tayasa neman auren ai wani farinciki yake ji da kara girmamani, duk shawarar da na kawo zai ce e hakan ma ya yi, duk abin da nike ganin ya dace in yi, na nuna mashi tamkar nice uwar biki.
Sai da shirye-shirye yai nisa na bijiro mashi da batun canza kayan ɗaki. Sai ya ce to in yi wa daddyna magana mana tun da dama dangin mata ke masu kayan ɗaki. Aikuwa na nuna mashi raina zai ɓaci, na ce sun mun ma farko yanzu ina gidansa shi ne da alhakin yi, na ce in dai ba zai mun kayan ɗaki sabbi kamar yadda Zainab zata zo da sabbi ba ni wlh ba zan zauna a gidan ba.
Ya ce in yi hakuri, in samo kujeru na 1M da gado ma na 1M sai ya saya mun, na dinga nuna mashi sun yi local, na mashi daɗin baki, na ce habibi kana son Zainab ta shigo ta rainani ne? Ya ce a'a, na to ai gara in yi abubuwa masu kyau. Ya ce haka ne, da kyar na kwato 3M na kayan ɗaki a hannunsa, 1.5 na kujeru, gado ma 1.5, na turawa yayana kuɗin dan a satin nan za'a fara mun gini, na share batun canza kayan ɗaki, ai ba compaction nike da Zainab ba, dan za'a mata abu sai nima in yi? A'a, ni gina kaina in tsaya da kafata nike ƙoƙarin yi, ki gina kanki ki tsaya da kafarki shi ne zaki wuce raini ba ki tsaya cewa duk abin da mutum ya yi kema zaki yi ba, idan kika gina kanki kika tsaya da kafarki zaki sayawa kanki abin da ya fi na amarya, amma mata dayawa in za'a maku kishiya ku tashi kuna haukar neman sabbin kayan ɗaki, duk kuɗin da kuke da shi ku kashe a shaye-shayen kayan ɗaki da maganin mata wai dan ku yi daidai da ita. Calm down Madam, ki bari lokacinta ya wuce, kafin nan ki gina kanki, sai ki zo da salon da bata taɓa gani ba, amma mu bi Aisha mu ga ya zata yi, fatana ku ɗauki darasi ku daina wannan shirme da kuke idan za'a auro wata, ku kashe duk kuɗin da kuke da shi a shirme wai dan ku fita, ina batun finta bayan biki kin zo baki da ko sisi miji yaƙi baƙi kuɗin cefene ki zauna kina zazzare ido mutunci ya zube? Ku dai mu bi Aisha mu ga nata salon.
In taƙaice maku labarin nan kada yai tsawo sosai, ranar juma'a sati uku da tafiyar Abba kenan aka ɗaura auren Zainab da Abbie. Wlh na ji tsananin azaba a zuciyata, amma na daure, na cije, ko kaɗan ban nuna na ji wani abu ba. Tun ranar Monday su Safiyya da Aunty Maryam kanwar daddynmu suka zo Kano wai tayani zama, iyayena basu san da batun zai kara aure ba sai satin da za'a ɗaura, Hajiyarmu ta dinga faɗa daddy yana tausarta. Suka kirani suka mun nasiha mai ratsa jiki, na dinga godiya da hamdala ga ALLAH da ya bani iyaye nagari.
Washegari ranar Saturday dangin su Abba suka dira a Kano da amarya Zainab rasa kunya. A lokacin da suka zo ina kwance a ɗaki, na manta ban faɗa maku ba Abbie yai gyara gida, an yi fenti an yi komai, ya tambayeni sabbin furnitures ɗina na ce ba'ayi ba tukun nan, mai yi ya ce sai next week, alhalin dukka kuɗin yayana na turawa har an fara mun gini.
A wasu ciki da parlo dake ta bayan side ɗinmu mai kama da BQ Zainab zata zauna, dan babu wadatattun ɗaki a side ɗinmu, ta ji takaici, wai ita a babban part ɗin nan take so, Abbie ya dinga dannarta yana bata hakuri, bata hakura ba, a lokacin dai ta yi shiru ne, amma ta ci alwashin bayan jama'a sun watse sai tasa ya dawo dani ƙaramin part ita ta koma babba.
Tun da family ɗinsu suka diro Kano bamu haɗu ba, suna ta hidima ta baya, basu nemeni ba nima ban nemesu ba, duk sun bi dangi sun shafa mun bakar fenti, kowa baya sona yanzu. Ina jinsu ta bayan window suna ta gulmace-gulmacensu wai bakinciki ne ya hanani fitowa, wata har da cewa kila ma na haɗiyi zuciya na mutu.
Ni kuwa ina kwance rike da wayata, tabbas na ji zafi, zuciyata na suya, amma ban bari ya bayyana a kan fuskata ba, Safiyya na kwance kusa dani tana dannar waya ita ma, Aunty Maryam da yake ita babbace tana waje tare da su, su Hassan suna wajen Fahad ɗan Aunty Farida, da yake Fahad ɗin yana da hankali sai yai ƙoƙarin maye masu gurbin uncle Abba da suka rasa.
Muhammad sarkin rashin rigima yana ta barcinsa. A haka muka wuni a gidan har dare, da daddare around 9 muna tare da su Aunty Maryam a ɗakina muka ji sallama a parlo, Aunty Maryam ta fita dan dubawa. Jim kaɗan ta dawo tare da cewa. "A'isha ki zo zangin mijinki ne, wai zaku gana da amaryarki".
Safiyya ta yi caraf ta capke da cewa. "Ba zata je ba gaskiya Aunty Maryam, bamu buƙatarsu, su tafi"........ Na saki wani irin murmushi, na kalli kayan barcin jikina, dogon wando ne da riga mai dogon hannu da suka fito da kyauna sosai, headband ne a kaina wanda iya gaban goshi ya rufe, yelwataccen bakin sumar kaina a kwance har gadon bayana yana wani sheƙi, na yi shirin kwanciya ne ma, dan ban tuna wani abin zai haɗani da su ba.
Ƙasan bed ɗin na sauƙi tare da ɗaukar wayata, na nufi parlo ban yi wa su Safiyya magana ba, zuciyata cike da tunanin irin gulmace-gulmacensu da suka dinga yi ɗazun wai takaici ne ya hanani fitowa, sai na ce bari ni basu takaicin da suke ikirarin ina ji, bari in barsu da abin tunani a zuciya.
A yadda nai shirin kwanciyata na fito, ga wani musulmin kamshin da nike bugawa. Na daka masu cikakken sallama irin ta addini a natse, duk suna zazzaune a kan kujeruna suna ta kalle mun parlo, sai ALLAH kaɗai yasan me yake a ransu.
Na wuce na zauna a saman one seater da babu kowa, na kalli Aunty Farida fuska da ɗan murmushi kaɗan na ce. "Aunty sannunku da zuwa". A wani irin natse nai magana, muryata babu wata alamar ina cikin damuwa.
Ai take suka sha jinin jikinsu dukka, su Khadija iyayen rashin kunya sai aka natsu, da sun zaci zan so da faɗa ko fuska a haɗe ne su zuba mun habaici da rashin kunya, amma sai suka ga garau nike.
Na ɗauko wayata tamkar mai duba wani abin, sai na ce. "Khady ba zaku gaishe da ni bane? Ko dai yanzu kun mai da Abbie ƙaninku ne kun zama surukaina?". Na faɗa ina ɗan murmushi ina ɗan danna wayar da ban san me nike dannawa bama, kawai dan in nuna masu ni fa ina da abin yi ne.
Ai bakin su Khady mutuwa yai, sai ido. Daidai lokacin Safiyya ta fito ta zauna a hannun kujerar da nike, ta ce. "Sannunku da zuwa". Aunty Maryam ma ta fito ta zauna a kujerar gefena.
Aunty Farida ta ce. "Aisha amaryar Sulaiman muka kawo maki dan ku fahimci juna". ..... Na ɗan ɗago kaina irin cike da mamakin nan, sai kuma na ɗan yi murmushi game da cewa. "Kai Aunty Farida kina nufin ki ce satin nan aka ɗaura auren ne? Ai na ɗauka tun satin da ya wuce aka yi? To wai me ya shiga kaina ne na mance?".
Ai sake baki suka yi suna ganin ikon GOD, na kuwa sake faɗaɗa murmushina kaɗan tare da cewa. "Sorry yama sunan amaryar? Na zaci tun last week aka kawo mana ke, har ina cewa Auntynsu Hassan ɗin nan bata son mutane bata taɓa leƙowa mun gaisa ba, ashe ni ce ban sani ba, yi hakuri, abubuwa ne duk suka sha kaina, ban zauna na natsu ba bare in fahimci me ake ciki".
Kam bala'i, yau sun ga abu, watau tsabar ina busy ban ma san ranar auren mijin nawa ba, a tunanina ma an jima da yi, gaskiya na goge masu hadda, wlh duk sai da jikinsu ya yi sanyi, masu cewa takakci yasa zuciyata ta buga duk sai da suka sha jinin jikinsu su ka yi tsit. Na kalli Safiyya game da cewa. "Kawo masu ruwa ke".
Sauran dangi sai kallona suke yi, musamman dangin Mamar Zainab, sun ga na fi ƴarsu kyau da fasali, ga jiki mai kyay ɗan cas.
Safiyya ta miƙe ta shiga kitchen. Aunty Farida sai ta ji harshenta yai mata nauyi, Zainab jiki yai evening, ta ga ashe ni bama kishi bane a gabana, a yadda ta fahimta ma mijin ma baya gabana kenan, kam bala'i, wannan ai faɗa dani ma ita ce da ciwon zuciya.
Safiyya ta kawo masu ruwa, rasa kunyar cikinsu watau Amina mai bin Abbie a wajen haihuwa ce ta iya cewa. "Mu ba zamu sha ruwa ba, ga dai so dangi nan mu kawo maki ku fahimci juna, ruwa kuma mun sha a side na so dangi".
Ka ji wata suna wai so dangi, duk dan in ji haushi, watau wacce dangi ke so, to ai shikenan, ni kam sunan ma dariya ya bani, na ɗan saki murmushi game da cewa. "To so dangi barka da zama ɗaya daga cikin member na gidan Sulaiman, muna maki lele, ALLAH ya taimakemu ya shige mana gaba, ƙaramar nasihata a gareki shi ne ki sani aure ƴar hakuri ce, sai ki daure kin cije, sannan sai kin haɗa da kula, ALLAH ya wanzar da farinciki da zaman lafiya a rayuwarmu".
Zuciyata yadda kuka san ana soyata a cikin mai, amma haka na daure nike wannan jawabi, duk jikinsu Aunty Farida ya yi evening, ta gagara magana ma, daga karshe haka suka kwashi Zainab suka fice, na bisu da murmushi da fatan alkhairi ina to sodangi a rike batun hakurin nan dai sosai.
Suna fita Safiyya ta watse da dariya tana maimaita sunan sodangi, sai da na ɗan bugeta tare da cewa. "Ke ban son shirme, sodangin Sulaiman ɗin kike yi wa shakiyanci?".
Haba ai Safiyya sake fashewa da dariya ta yi, ni kuwa na wuce cikin ɗaki, na shiga toilet na sha kuka tamkar raina zai fita, na wanke fuskata, na jawo towel ina ƙoƙarin goge fuskata sai ga call ɗin Abba ya shigo wayata da na ɗaura a kan wash hand base.
Na goge fuskata kafin in ɗauki kiran. Ina ɗauka ya ce. "Auntyn tawa zuciyata ya bani kina kuka".......... Sai kawai nai murmushin yaƙe zuciyata na ƙara ƙuna na amsa da. "Ni kam Abba anya kai ba aljani bane? Kawai sai ka dinga cewa mutum yana kuka".
A natse ya ce. "Wlh ina zaune kawai na ji zuciyata na faɗa mun kina kuka, daga wajen training muka dawo ba jimawa, my Aunty please me ya sakaki kuka bayan kin ce ba zaki sake kuka ba?"........ Abba da yasan yau ake auren yayansa, yasan dole zan shiga damuwa, shiyasa ya kirani dan ɗebe mun kewa, ya dinga jana da hira, na dinga kauce mashi kan bana kuka, daga karshe dai dole na yarda kukan nike yi, ya tambayeni dalili, ban ɓoye mashi komai ba na faɗa mashi har chat ɗin da yayansa yake da Zainab kafin auren, ban ɓoye mashi komai ba.
Sai ya ce. "To bari ki ji wani abu, kinga ita wannan Zainab ɗin ko?"........ Na amsa da e.
Ya cigaba da cewa...............
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔