LABARIN AISHA

PART 14

by @queenofsurprise1

Sai ya ce. "To bari ki ji wani abu, kinga ita wannan Zainab ɗin ko?"........ Na amsa da e.

Ya cigaba da cewa. "Kafin Mamar Zainab ta zo gidan uncle ɗinmu mace daya yake da shi, bata taɓa haihuwa ba, ba irin abin da ba'a ce mata a dangi ba, amma ta jure, kakarmu lokacin tana raye, sai ta tursasawa baban Zainab kara aure daga cikin dangi, dole ya auro wata ƴar kawunsu, yadda kika ga suka maki, haka suka yi wa uwar gidan kawuna, wacce aka aurawa kawuna ɗin ita ma sodangi suke ce mata, suka takurawa uwar gidan kawuna, daga karshe dai zaman yaki daɗi, dole uwar gidan kawuna ta nemi ya saketa ba zata iya zama ba, ya rage iya wannan sodangin nasu a gidan. One day one time kawuna ya zo da batun karin auren, zai auri mahaifiyar Zainab, kowa a dangi da farko yaki, amma da kawunmu ya matsa, dole suka amince, kin san me ya biyo baya?".

Na girgiza mashi kai alamar a'a. Ya ɗan nisa tare da cewa. "Kawuna ya auro mahaifiyar Zainab, dangi duk sun tsaneta suna mata abin da suke so, amma da ta shigo, duk sai da kowa ya natsu ya shafa mata lafiya, dan Mamar Zainab bata da kunya ko kaɗan, duk wacce tai mata dakuwa zata yi, bata dariya kuma bata ɗaukar nonsense, da gangan kawuna ya auro masifaffa dan ya ga ita ce daidai da danginmu, coz iyayen Mamar Zainab suna da kuɗi sosai, dan haka dangina sun san idan suka taɓata daga nan har birnin sin zasu buga shari'a da iyayenta, cikin ƙanƙanin lokaci Mamar Zainab ta zama sodangi dole ita ma, dole suka sota, biyayya dole su yi mata, Aunty Amina da kike ganin nan a hannun Mamar Zainab ɗin ta girma ai, wani irin dakuwa ne bata yi ba? Da zata baki labari da kin daina damuwa, a kwana a tashi suka juyawa ƴar uwarmu da suka aurawa kawun namu baya, suka koma son Mamar Zainab, saboda batu na gaskiya Mamar Zainab tana da kirki, sai dai bata da kunya ga masifa, ko uwar miji ta mata a lokacin zata gyara mata, bata ɗaukar iskanci manya ma bare na yara, idanunta a buɗe yake".

Na yi mamakin, watau tun asalin danginsu masifaffu ne kenan, amma sai na ce. "To me ya fitar da Mamar Zainab daga gidan uncle ɗinka?".......... Ya ɗan nisa game da cewa. "Kawai rana tsaka ta ce uncle sai ya saketa, ba yadda ba'ayi ba ta ce auren ya isheta, da aka ce saboda me ta ce wai auren dole ne? Ai ba farillah bane, sunnah ne, dan haka ita ya isheta, ba duka ba zagi, sai ma biyayya da dangi suke yi mata, amma ta ce bata buƙatar auren yanzu, dole kawu ya saketa, yanzu da nike maki magana babbar ƴar kasuwa ce, tana yawonta a gari ba aure, ta ce auren nan ba dole bane, ba zata yi ba, idan akwai wanda take zaune a kansa to ya sauketa ya ajiye, mafaɗaciyar mata ce sosai da sosai, to dan haka ki fita harkar su Aunty Farida, su basu da aiki sai tada husuma da kike ganinsun nan, duk uncles ɗina ba wanda basu addabawa ya kara aure ba, duk da su kuntatawa wacce ba sodanginsu ba".

Ni kam na saki baki, sai kuma na ce. "Amma naga Aunty Farida ai ita kaɗai ce a gidan aurenta, and duk sauran su kaɗai suka zauna a gidan aurensu babu kishiyasa, sai su addabawa wasu a masu kishiya?"........ Ya amsa da. "E, a gidajensu su ɗaiɗai ne amma su addabawa gidajen wasu"....... Na ɗan taɓe baki ina mamaki hali irin ka dangin mijin nan nawa.

Haka muka yi ta hira da Abba, idan na ce mashi sai da safe sai ya ce mun a'a akwai abin da yake son faɗa mun, idan na tsaya sauraronsa sai ya jani da wata hira, ko kaɗan bayan son mu yi sallama, tun Safiyya na jiran mu kammala waya ta fara waya da shi, har ta hakura, tun ina toilet har na fito ɗaki kan gado na kwanta, na dinga tsokanarsa waye ya saka mashi kati, yaƙi faɗa mun, yana dai ta faman jana da hira.

Sai around 1 na dare, ya natsu, yai ƙasa sosai da murya, sannan ya ce. "Ban so barinki ki yi barci yanzu ba my Aunty, banƙi yau mu yi ta hira har 3 saboda in ɗauke maki hankali daga kan gidan nan ba, amma naga alamar da gaske barci kike ji, to zan barki ki kwanta, amma kafin nan kin san me? Magana ta fahimta nike son mu yi".

Na ce a'a ina jinjinawa hankali irin nasa, watau dama domin ya mantar dani yau aka kawo mun amarya ya kirani ya jani da hira, ALLAH sarki.

Ya ƙara yin ƙasa sosai da murya, cikin natsuwa ya cigaba da cewa. "Abbie zai gama duk abin da zai yi a duniya Aunty ba zai taɓa samun mace irinki ba, yanzu kawai na tabbata wasu abubuwa biyu zuwa uku ke ɗaukar hankalinsa a tattare da Zainab, amma batu na gaskiya babu ma mahaɗi tsakanin qualities ɗinki dana Zainab, ajiye wannan a gefe, ki sanya a ranki Abbie zai dawo, zai dawo gareki, nasan waye shi sosai, abinda yake ɗaukar hankalinsa a tattare da Zainab ba zai taɓa bashi abin da yake so ba, yana gani daga nesa ne kawai, duk karfin sha'awarmu akwai abin da ganinsa da ido kawai idan muka yi kaso 50 cikin ɗari na feeling ɗinmu sai ta motsa kuma muke jin daidai a zuciyarmu, kallonki kawai a lokacin idan ya yi yana biya bare a kai ga taɓawa, idan kika yi la'akari da tun farkon zamanku, kin fita daban da sauran mata, duk karfin feeling ɗinsa kina iya ɗaukewa a zuwa ɗaya, saboda kin haɗa duk wani qualities da irin jininmu yake so, amma Zainab fa? Sai ta tura mashi wani ɓangare na tsiraicinta ne yake iya motsa shi wanda ke fuskarki kawai a lokacin idan ya gani birkicewa yake ya fasa fita, kin manta ne in tuna maki? Kin manta yaya sai yai wanka sau uku a safiya wai zai fita kasuwa, kin manta sai kin rakasa waje ya sake kamaki ku dawo, kin manta tare da ku na karasa girmana, kin manta duk abin da yakefaruwa ina sane, kin manta sai ya fita ya sake dawowa, kin manta a safiya kawai yana iya wanka har sau uku duk saboda sai ya fita ya sake dawowa in kina ɗan mashi shagwaɓa kaɗan, duk kin manta wannan? To na tuna maki, kin fita daban da saura, zai gama duk tsalle-tsallensa ba zai taɓa samun gamsuwa wajen kowacce mace ba sai ke, ki yi zamanki zai dawo, macen da ta kai mace ita ce wacce fuskanta kawai idan an kallah komai na halittar jikin namiji sai ya motsa, kuma ALLAH ya baki wannan baiwa, shaukin sonta ne yake ɗebansa yasa in ya ganki sha'awa zata motsa, amma sai ya kirata a waya wai ta kwantar mashi, ki basu watanni uku zuwa huɗu, kina zaune zai dawo".

Abba ke magana kunya kamar ta kasheni, ban taɓa tunanin duk zamana da yayansa yaron nan yasan me yake faruwa a tsakaninmu, ashe duk abin da muke yi yana ganinmu, kai innalillahi wa inna ilaihi, yau ya gama bani kunya, da yana gari ina ga ba zan sake ɗaga ido in kallesa ba. Shi ma a nasa ɓangaren dan bamu ganin juna ne yasa yai waɗan nan maganganu dukka dan ya sanyaya mun zuciya, da ace muna ganin juna a irin kunyar nan tasa wlh ba zai yiwu ba. Amma kuma duk abin da ya faɗa gaskiya ce, haka zamana da yayansa ya kasance, sai ya yi wanka zai fita kasuwa da na rakasa haraba sai ya sake dawowa, mu ɗaura daga in da muka tsaya, sai yai ta sake wanka har sau uku huɗu, daga karshe ma idan ina son ya fita zama nike a ɗaki in ki rakasa ko parlo ne, dan gajiyar dani yake, and nasan yana dawowa da yamma zai dasa daga in da ya tsaya, ban iya wahala, ashe duk Abba yana ganinmu yaron nan, kai amma dai kam anyi shiryayyen yaro.

Zuciya da saƙe-saƙe ga sharrin shaiɗan sai na hau tunanin kenan shi ma Abba haka ne? Kenan shi ma idan ya ganni ina tada mashi da feeling? In ba haka ba ta ya aka yi yasan ganin fuskana kawai yana motsa duk wani lafiyayyen namiji? A ina ya sani? Sai na shiga tunanin irin zamanmu, tun farko yadda muka rayu cikin farinciki da shaƙuwa ga yarinta, tunanina ya tsaya ne cak a watarana da na shiga ɗakinsa ina kwala mashi kiran ya zo ya ciro mun wasu dinner set a saman drawer kitchen ɗina zan sanya abinci dan tsawona ba zai kai ba, ina shiga ɗakin na zame na faɗi a bakin kofa, da bakin kofar ɗakinsa dana toilet ɗinsa suna kusa ne, ya fito daga wanka kafarsa da ɗan ruwa-ruwa ya taka tiles ɗin ya wuce, shiyasa ina shigowa na taka ruwan nai wani irin mummunar zamewa na faɗi sai da na ji bayana ya tsaya cak tamkar ya fita daga jikina.

A lokacin yana tsaya wajen mirror yana taje sumar kansa irin na buzayen nan, ya gyarata sai sheƙi yake yi, yana sanye da kayan kwallo a jikinsa, ya ɗaura jacket a sama saboda ruwan saman da ake yi sanyi ya sauƙa. Da sauri ya ajiye comb da yake taje kai ɗin ya nufeni yana faɗin subhanallah.

Na runtse idanuna ina kuka hawaye bibbiyu dan na ji azaba, a lokacin ban fi 16 years ba, shi kuma 21 years. Ya tsuggunna a gabana yana mun sannu, ban kulasa ba, ya kama hannuna zai jani na miƙe na sake fasa ƙaran da yasa dole ya sakeni yana kallona, sai ya rage tsawonsa ya ɗaukeni cak, a parlo ya zaunar dani kan kujera, a wannan lokaci ya dinga kallona kuma yaki yarda mu haɗa ido, ya dinga ce mun sannu.

Haka na dinga tuna rayuwarmu na baya, sai na dinga jin kunyar wasu abubuwa da suka faru, musamman yadda a da can baya yake goyona, gaskiya yarinta akwai shirirtia, shiyasa aka ce kuruci dangin hauka, da gaske ne wlh, duk da ban ji kunya ba sai yanzu abubuwan suke bani kunya.

Katse mun tunani yai da cewa. "Baki jina ne my Aunty?"......... "Nawan kafi karfina, ka wuce tunanina, sai da safe, ga Safiyya na ta jiran mu gama waya ku yi waya har ta yi barci"........ Ya ɗan tsuke fuska tare da cewa. "Nima wlh tun ɗazun tana raina, amma na daure ne dan in sakaki farinciki, please Aunty ki mun wata alfarma mana".

Na ce ina jinka..... Ya ɗan nisa tare da cewa. "Aunty tun da yamma nike ta bin Safiyya ta tura mun hotunanta ko kuma mu yi video call amma taki, dan ALLAH zankiraki video call ki nuna mun face ɗinta, ina tsananin son ganinta".......... Na yi murmushi na amsa da okey, hankalina ya yi mugun kwanciya da kalaman Abba, kuma nasan gaskiya ya faɗa mun, da wuya a samu wacce zata iya gamsar da Abbie, ba ƙarin auren bane ai, wacce zata iya gamsar da kai ne, kuma ba jima'in bane, gamsuwar ne aiki, so kalaman Abba sun faranta mun rai over.

Ina ta sauke ajiyar zuciya da farinciki sai ka kiransa ya shigo, na tashi na kunna wutar ɗakin dukka ta yadda haske ya gauraye ko'ina kafin in ɗaga kiran, Aunty Maryam tana ɗakin baƙi ta shiga ta kwanta.

Abba yana zaune a sama kusa da wasu kujeru dake cikin hut tamkar wajen shaƙatawa ne, Abba ya ƙara kyau sosai, ƙasar ta ƙarɓesa, har wani ɗan haske ya yi.

Fuskansa ɗauke da ƙayataccen murmushi ya ɗan lumshe idanu kafin ya sauke ajiyar zuciya, slowly ya warosu a kan face ɗina sannan ya ce. "Ina kibar Auntyn tawa ya tafi? Kin saka damuwa a ranki ko? Dubi yadda kika dawo, fuskanki duk ya rame"......... Na hararesa game da cewa. "Ni ka kira ka gani ko Safiyya?"....... Ya ɗan shafa ga shi kansa game da cewa. "Sorry my Aunty, nuna mun matar tawa, kema ɗin dai dole in ganki ai dan in tabbatar kina cikin aminci".

Na ɗan yi murmushi game da matsawa kusa da Safiyya mai barci, na hau haska mashi fuskanta, a maimakon ya kalleta Abba ni yake kallo, amma ban lura da hakan ba dan ya sunkuyar da kansa ƙasa, sai zan kashe video call ɗin kuma ya sake ce mun minti ɗaya, na dinga ɗan biye mashi dai har 2:30, sannan muka yi sallama da kyar, na ajiye waya.

Da alama Abba yana jin wani abin a ransa game dani, amma saboda yayansa yana ƙoƙarin dannewa baya son ya fito fili, sai dai ni kwata-kwata ban san da hakan ba. Muna yin sallama nai addu'ar barci na kwanta, dama barci ya cika mun ido.

A wannan dare Abba ne ya ɗauke mun hankali har na manta da Abbie ya yi aure. A washegari danginsu suka koma, gida ya rage ni da Zainab sai su Safiyya. In takaice maku labari a kwanaki uku na kawo Zainab da aka yi daidai da dare ɗaya Abba bai barni na mai da hankali har na iya tuna cewa Abbie na can kwance da wata ba, da yake yasan danginsa sun koma Abbie zai shiga ɗakin Zainab, da anyi sallar ishai zai kirani, yaron da baya da yawan magana, amma sai ya zage ya dinga surutu dan ya kwantar mun da hankali. Nima mugun jin daɗin hiran da shi nike yi, har bana son mu yi sallama, sai 2:30 kullum yake barina in kwanta, a lokacin barci ya cika idona sai ya barni in kwanta, ina matuƙar jin daɗin hira da Abba sosai.

A kwanaki ukun nan kullum haka muke yi, wlh Abba ya taimakeni sosai, dan a irin kishin da nike da shi zan iya mutuwa idan na ji Abbie a ɗakin wata, Abba yasan da hakan, shiyasa ya bi dani ta wannan hanya, nakuwa ji daɗi na gode wlh.

After kwanaki bakwai da zuwan Zainab ina ɗaki kwance, su Safiyya sun koma, su Hassan suna school, Muhammad yana zaune tsakiyar gado ga kayan wasansa a gaba yana yi, ina rike da wayata ina rubutawa brother na Ahmad kayan cefenen da zai sayo mun, dama Abba nike aika kullum, to Abba baya nan sai nike faɗawa Ahmad ya sawo mun, karshen wata ta zo duk cefenenmu ya kare shiyasa zan yi sabo.

Tamkar a mafarki haka ka ga Abbie ya shigo ɗakina dakinsa ɗauke da sallama, yana sanye da wata dakakkiyar shaddarsa sky blue, sai wani murmushi yake yi, uhm rabona da shi yau kwanaki takwas kenan.

Tabbas na ji ciwo a raina na rashinsa, amma ban bari ya gane ba, ina ganinsa na ce. "Sannu da zuwa"...... Sai ya ɗan yi jim, dan a irin kishina da ya sani ya yi tunanin bala'i zamu yi dan wlh ni mafaɗaciya ce sosai a baya, har kona gidansa na taɓa cewa zan yi in bai sakeni ba, amma lokaci guda komai ya canza na zama shiru-shiru.

Kun san masu sunan Aisha kishinsu a jini yake, akwai mu da kishi, shiyasa Abbie yake shakkar shigowa part ɗina tun da aka kawo Zainab, amma ga mamakinsa sai ya ga ko a jikina, ina ma kwance nai mashi sannu, shi ne ya ɗan yi jim.

"Habibiya ban ji ɗuriyarki ba kwana biyu". Ya faɗa dan yana son buga cikina ya ji a wani hali nike. Sai na saki murmushin da ya fi mun kuka ciwo, na kara danne zuciyata game da cewa. "Kai da Habibi bari, ina can busy ya ɗauke mun hankali, shago da jama'ar online suna neman haukatani, ka san yanzu mun buɗe page na shagonmu a TikTok da saurin sassa na media, shi ne jama'a ke neman haukatani da oders". Kuma da gaske nike yi, Ahmad ya bani shawara mun fara tallar kayanmu har online, ALLAH ya sanyawa abin albarka, ta ko'ina oders muke samu sosai, abubuwa sun kara gaba, amma number shago ne a kan page ɗinmu ba numberta ba, sai na nunawa Abbie kamar numberta ce a wajen dan ma yasan na shiga busy da gaske.

Wlh take a wajen jikinsa yai sanyi, bai tsammaci haka ba, sai ya ce. "Watau habibiya baki damu dani ba kenan? Yanzu baki kishina?"......... A raina na ce watau maza fa ƴan rainin wayau ne wasu, so yake da kenan in ta hauka a kansa, aikuwa zan yi maganinka, sai na mai da kai kamar bola, zaka gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne.

Na mike zaune tare da cewa. "Sorry Habibi, abubuwan ne dai suka mun yawa, amma kana raina, ban samu isasshen lokacin dogon tunani a kanka bane"......... Duk jikinsa ta kara sanyi, yana ta kallon kayan jikina, wandon jeans irin palazon nan na sanya, daga sama daidai da ƙayataccen shape ɗina, daga ƙasa kuma kafafun ya buɗe sosai, na sanya ɗan karamin t-shirt daidai da jikina, na tara gashin kaina na ɗaure a tsakiya, kwanciyar da na yi yasa gashin ya watse abinku da gashi mai tsantsi.

A cikin kwayar idanunsa na fahimci yana kallona abar tasa ta motsa, amma sai yai ƙoƙarin kaucewa, ya so daina kallona amma ya gagara. Sai ya ce. "Zu mu je parlo ina da magana dake"....... Mamaki ya ɗan kamani, maganar ne ba zamu yi a nan ba?.

Ya wuce gaba, sai da ya fita na sauƙo ƙasa na bisa da tunanin shi kaɗai parlon, ina shigowa na ga ashe shi da sodangi ne. Tun da na fito take kare mun kallo, taga ƴar caras kamar ita ta yi kanta.

Ni kam ina kallonta na ɗan yi murmushi tare da cewa. "Ai sai kace mun kai da sodangi ne"...... Na faɗa ina ɗauke kaina daga kallonta, ta wani saka wani matsatten t-shirt dan ta gwada mun tana da manyan breast tun da ya nuna mata ni bani da shi, ta fito da halittar kirjinta sosai, sai dai kuma ta ji kunyar saka wando dan babu kwankwason, sai ta sanya irin buje sket ɗin nan, and tana da katon tumbi wandon zai tona mata asiri shiyasa ta sanya sket, iya breast da ta san tana da su ne ta bayyanosu a waje.

"Sodangi sannunki da shigowa". Na faɗa ina jawo wayata. Daga ita har Abbie sun fahimci nifa su basu ne a gabana ba, abin nan yai masu ciwo, Abbie ya so ya ga ana faɗa a kansa, watau maza daɗi suke ji su ga ana faɗa akansu, ita kuwa Hajiya sodangi ta so ne na tanka mata da faɗa ta yayyaɓa mun magana na abin da Abbie ya faɗa mata a kaina, har ta shirya irin gorin da zata mun, sai taga bata gabana ma.

Jiki duk ya yi evening ta amsa da. "Yauwa ina kwana"........ Na amsa da. "Lafiya lou Alhamdllh ya bakon wuri? Nasan sai a hankali zai maki daɗi ki saba".

Sai ta yi maza ta capke da cewa. "Baby yana nan ai dole waje yai mun daɗin zama, ban wani ji baƙunta ba, tuni ya mantar dani cewa na bar gida"......... Na saki murmushin karfim hali tare da cewa. "Ai nawan jarumi ne, kasan dama ba zaki fuskanci wani kaɗaici ko damuwar baki gida ba, Habibi ALLAH dai yai maka albarka".

Zainab ta sake jin jikinta ya yi sanyi, coz ta yi magana ne dama dan ta baƙanta mun sai kuma dai ban ji haushin ba.

Abbie ya ce. "To yanzu dai zan fita, na zo ne in maku nasiha da ku haɗa kai".... Na jinjina kai alamar to, ya dinga mana nasiha, ya dinga janyo ayoyi da hadisai tamkar wani malamin masallacin juma'a, ni kam yanzu Abbie ya daina bani mamaki.

Sai da ya gama nasihar ne ya ce. "Ya batun rabon kwana? Yau my happiness ta yi kwanaki bakwai kamar yadda shari'a ta ce, yakamata ku raba kwanan nan ko?".

A natse na ce. "A'a Abbie, kaga ita Zainab bata saba da baƙon wuri ba, zata ji kaɗaici idan ka fara barin ɗakinta tun yanzu, dan haka ni na ci girma, ku je na baka watanni huɗu, ka kula da ita tun da kaga amana aka bamu"........... Da sauri Zainab ta ɗago ta kalleni, na ɗauke kaina tare da mai da kallona kan Abbie da murmushi ta kubce mashi, ko kunya bai ji ba ya dinga zuba mun godiya.

A lokacin kiran Abba ya shigo wayata zai faɗa mun sun yi nasara kuma sun sha south Africa, sai daɗi yake ji. Na miƙe tare da cewa. "Sodangi ga Habibi ki kula da shi, ka baku watanni huɗu, kafin wata huɗun ki mayar mana da shi kato yai kiba". Na nufi cikin ɗaki ina pick-up na call ɗin Abba.

Zainab ta bi baya da kallo, sai take jin tamkar ta kwace shape ɗin jikina ta sanyawa kanta, ita da take mace ma sai da ta ji na tafi da ita bare kuma Abbie da tun da na miƙe yake ta faman bin bayana da ido, yana jin kamar ya bini ɗaki, amma zuciyansa na ingiza shi cewa Zainab ma tana da abin da nike da shi.

Sai da na shiga cikin ɗaki suka dawo da kallonsu kan juna, Zainab ta wani watsa mashi harara kafin ta ce. "Da kake wani kallonta binta zaka yi ne?"...... Ya ɗan haɗe rai game da cewa. "Matata ce fa, kallonta ya zama laifi ne a wajenki?".

Ta haɗe rai sosai tare da miƙewa, ba wani respect ta ce. "Amma ai a ɗakina kake ba a wajenta ba bare ka ce hakan, sai ka bari idan ka dawo wajenta ka yi abin da ya fi kallo".

Shi ma ya miƙe, ga abar tasu ta motsa ga tana neman ɓata mashi rai, a kufule ya ce. "Babu wacce ta isa gaya mun ga abin da zan yi a kan matana, babu wani shari'a da ya shata mun layi kan ganin matata, dan haka ki kiyaye wannan". Yana kaiwa karshe ya wuce fuuuu ya fita. Ita ma ta bi bayansa tana zazzaga masifar wlh bai isa a ranar da yake ɗakinta ya dinga kallona ba, ai na faɗa maku Zainab bata da kunya, ba respect ta dinga gaya mashi magana.

Dama yana sama, ya zageta tas, har da ce mata yai. "Uban me na tsinta a wajen naki da zaki ce ke kawai zan dinga kalla kada na ganta? Kin san dai Aisha ta fiki komai, duk in da ake kiran mace ta kai nan, dan haka ki kiyaye"........ Cikin faɗa ita ma ta ce. "Wlh bata fini komai ba, idan ta fini komai ba zaka je ka auroni ba, da waɗan nan ƴan ƙananan breast ɗinta kamar mangoron ne ta fini komai? Ka buɗe idanunka da kyau ka kalleni".

Ya nufi shiga bedroom ɗinsu yana faɗin. "Da yake dakikiya ce ke sai kike tunanin cewa manyan breast su ne mace? Kina tunanin sune daɗin aure?!". Aikuwa ta sake cika tamkar zata fashe, ta bisa cikin bedroom ta hau zazzaga masifa.

Duk abin da suke faɗe ina jinsu saboda sun ɗaga murya, ina waya da Abba amma ina iya sauraransu, kuma shi ma Abban yana jinsu sosai, har yake ce mun. "Daga aure sai faɗa kuma?"....... Na ce. "Nawan babu ruwanka, kai dai faɗa mun yaushe zaka dawo".

Ya amsa da. "A'a Auntyna da ruwana fa, saboda kece silar faɗar ai, kin ɗauki wankar nan naki mai gigitarwa ko? Shi ne kika kunna yayana ko?". A wata iriyar murya mai wuyar fassaruwa ya faɗa, ba zaka iya gane a wani hali yake ciki ba, but na ji kamar ya yi maganar cikin mood mara daɗi.

Na ce. "A'a ni babu ruwana nawan, kawai dai faɗarsu suke yi"........ Ya amsa da. "To shikenan my Aunty, zan ɗan kwanta kaina yana ciwo, zamu yi waya anjuma". Bai jira amsata ba ya katse kiransa. Ni kam na kwanta ina jin su Abbie har barci yai awon gaba dani, ban san lokacin da suka gama faɗar ba. Around 12 ina cikin barci na ji kamar hayaniya a harabar gidan.

A hankali na waro idanuna, jiki ba kwari na miƙe na fito, sai na ga Ahmad tsaye a tsakar gida Zainab ta taresa wai side ɗinta zai kawo cefenen. Shi kam ya ce a'a side ɗina zai kawo dan ni na aikesa, shi ne ta hanasa wucewa, dan a tunaninta Abbie ne yai cefenen, shi ne ta zaƙe wai ba za'a kaimun ba, dan tana tunanin za'a kawo mun ne ni in raba mana, shi ne wai ita zata raba, ta tare bawan ALLAH ta hana shi shigowa ya kaso mun kayana, da motarsa ya zo, ya gama fito da kayan daga bayan motansa kenan ta fito, shinkafa ne bugu biyu, mai jarka ɗaya, manja ma ɗaya, sai kaji guda 20 da aka fige aka gyara aka zuba a ledoji bayan an daddatsasu, da su maggi, su curry, har su tumatir da zamu zuba a fridge, kifi da dai duk wasu cefene, shi ne take tunanin ai Abbie ne ya aiko.

Ina fitowa na ce. "Ahmad lafiya?". Idanuna duk barci. Zainab ta wani watsa mun harara, dama a sama take na abin da Abbie yai mata da safe, shi ne take neman kan wanda zata huce.

Ahmad ya ce. "Aunty na kawo maki saƙonki ne wai ba zai shiga da shi ba sai dai in bata ta raba maku, dama ku biyu ne saƙon?".......... Na juya na kalleta kafin in ce........

Kai jama'a yanzu wasan zai fara fa, an zo daidai wajen.

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥

LABARIN AISHA.🥹💔