LABARIN AISHA

PART 17

by @queenofsurprise1

Abba ya dinga kallona ni ban ma san ya shigo ba, musamman gashin kaina dake bakinkirin har gadon baya, ga shi ya sha gyara sai sheƙi yake yi. Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ne da ta ga ya tsaya cak yana kallona sai ta ce. "Yallaboi lafiya?".

Da sauri ya ɗauke kansa daga kallona, sannan ya matsa ya miƙo mun Muhammad, sannan ya juya ya fita bai yi magana ba. Ya koma cikin mota ya zauna, ya kifa kansa da jikin steering, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.

After 30 mins da dawowansa na fito daga cikin wajen, tamkar wanda yai barci, bai ga fitowana ba, yai nisa a cikin tunani, sai da na shigo cikin motar, ya ji rufe kofar ne ya ɗago kansa, idanunsa sun kara ciza ja sosai tamkar ya fara barci. Ya ɗan saci kallona ta wutsiyar ido kafin ya nufi tada motar. Sai kuma ya dakata, ya buɗe kofar motar ya fita.

Cikin wajen gyaran gashin ya shiga, jim kaɗan ya fito hannunsa rike da ATM card ɗinsa. Yana shigowa cikin motar na ce. "Nawan, wai yanzu yaushe ka je ka yi payment na gyaran nan? Na je biya wai ka biya, dama ATM ɗinka ka basu ne?".

Kai kawai ya jinjina mun bai yi magana ba. Na sake cewa. "Nawan wai a ina ka samu kuɗi, ka kashe kuɗi sosai wajen shopping, a nan ma haka, ina ka samu kuɗin"........... Ya cire password na wayansa tare da shiga kan sms sai ya miƙo mun wayar, ina karɓa ya tada motar bai yi magana ba, kuma bai sake ɗagowa ya kalleni ba.

Ina shiga naga alert na kungiyarsu ta kwallon kafa ce ta biyasu kuɗi, coz yana cikin zakarun da suka ja ragamar wasan, ya samu kyaututtuka sosai da sosai. Na ɗaga ido na kallesa kafin in ce. "Bawan to sai ka karar da kuɗin dukka a kaina? Ba zaka sayi wasu abubuwan bane? Ga su Mama, and na ji ana cewa Hummaira zata yi aure, akwai abubuwan da zaka yi da kuɗi sosai, kai da Abbie ne kawai maza, kuna da ƴan uwa mata sosai, kada ka manta tamkar mahaifinsu kuke yanzu, and ga su Ummin Aunty Farida kannen Khalifa, duk sun tasa aure nan ba da jimawa ba, kaga bai kamata ka dinga kashe mun kuɗinka ba".

Yadda kuka san da steering motar nike yi, bawan ALLAHN nan bai amsani ba, yana driving yana ɗan dafe kansa, ciwo take mashi sosai, na so sake tambayarsa me yake damunsa, amma na share saboda naga bai amsa tambayar farkon da na mashi bama.

Kai tsaye gida muka wuce. Yana parking a gida ya buɗe motar ya fito. Ya buɗe gidan baya ya ɗauki kayan da muka saya, ya nufi ciki. Na fito na bi bayansa, a parlo na iskosa tsaye, ya ajiye kayan a tsakar parlon, ya ɗan riko waist ɗinsa da hannayensa. Ina zuwa na ce. "Ka je ka huta bari in yi mana girki".

Ya miƙa mun hannunsa alamar in bashi wayansa bai dai yi magana ba, kuma taki ɗagowa muga juna. Na miƙo mashi wayansa, ya karɓa, kamar zai juya, sai kuma ya tsaya, yai ƙasa da murya, a natse sosai ya ce. "Duk waɗan da kika lissafa a ɗazun babu wanda ya tsaya mun a lokacin da nike fafutukan neman cinwa burina, duk cikinsu babu wanda ya taɓa taimaka mun da Naira ɗaya, kome zan zama a rayuwa kece sula, da kuɗinki, da lokacinki, da damarki, kina da damar komawa makaranta kika zaɓi in koma, duk wata wahalata ke kika sha shi, idan har zan samu kuɗi, to ki sa a ranki naki ne, kafin kowa ya ci sai kin rigasa, ke ta daban ce a rayuwata, ba zan taɓa mantawa dake ba, sunanki ba zai taɓa fita daga bakina ba a lokacin yin addu'ata, ina maki fatan alkhairi a kodayaushe tawan". Ya kai karshen maganar tare da juyawa.

Na jima ban ga ɗan halak irin Abba ba a rayuwata, na bi bayansa da kallo, lallai ɗan halak baya manta alkhairi, duk abubuwan da na mashi wlh na mance ma da na mashi su a rayuwarmu, amma shi suna ransa, tabbas a lokacin na zaɓi ya koma makaranta ni in hakura dan a lokacin ba zai yiwu mu koma mu dukka ba, duk na manta da wannan ma, ashe shi yana nan a ransa.

Na zauna a zauna a kan kujera ina ta mamaki, na yi wa yayansa abin da ya ninka wanda na mashi sau goma, amma daidai da rana ɗaya Yayansa bai taɓa ce mun even ALLAH yai maki albarka ba, sai dai idan muka samu ɗan saɓani ya ce bana tausaya mashi, hmmmmm rayuwa kenan.

After 20 mins ina zaune na miƙe na shiga kitchen, haɗaɗɗen abinci na girka mana mai rai da lafiya, yau ina fashin sallah, so ina gamawa na tsara wanka sosai, na shirya cikin wani doguwar riga da babban yayanmu ya kawomun zuwansa Makkah last year, sai tashin kamshi nike yi. Na duba time 2:30, na fito daga bedroom ɗina rike da Muhammad, shi ma na mashi wanka tas da shi.

Ina fitowa sai ga Abba ya fito daga nasa ɗakin hannunsa rike da key ɗin mota. Baki a ɗauke da sallama Fahad ya shigo parlon, yana ganin Abba ya ce. "Kai, kawu yaushe ka dawo".

Abba ya saci kallona ta wutsiyar ido kafin ya ce. "Ɗazun". Ya faɗa tare da wucewa zai nufi waje. Fahad ya ce. "Sannu da dawowa ya hanya?"........ Abba bai amsa ba, ya yi wanka ya canza kaya zuwa ƙanana jeans and t-shirt, ya nufi ficewa, da sauri Fahad ya ce. "Kawu bani key ɗin motar na dawo zan je in ɗauko su Hassan ne daga school".

Can ƙasa Abba ya ce. "Bari in ɗaukosu". Ya faɗa ya fice ko juyowa bai yi ba. Fahad ya kalleni, cikin girmamawa ya ce. "Ina wuni Aunty"........ Na amsa da. "Lafiya lou, kaga ubansu ya dawo ya huttasheka ɗaukosu"..... Yana ɗan murmushi ya ce. "E wlh, bari in koma shago"....... Na ce. "A'a, tun da ka zo ga abinci nan, idan ma kana sauri kasa a kula ka je da shi".

Ya amsa da okey ya gode, a saka mashi a kula, na amsa da to, na matsa na zuba mashi abincin a kula, sannan na koma na zauna a kan kujera ina jiransu Abba su dawo mu ci abinci, azumi ya kawo kai, ana ta shirye-shirye, na yi zama rubuta kayan abincin da zan sayawa dangin Abbie da mabuƙata, na shirya komai na kammala kamar yadda aka saba, har na sanya yayana ya biya kuɗin, coz sadaka zan yi, baya hanani sadaka da kyauta, dan shi ne sirrin arzikina, sadaka na yelwata arziki sosai, jama'a ku lizimci yinta zaku ga daidai sosai.

A wannan lokaci Abbie ya shigo parlon a fusace, ɗakinsa ya wuce tun kafin in yi magana, na bi bayansa da kallo ko a jikina, ban tashi na bi bayansa ba. Ina zaune ya fito, a saman kujera ya zauna tare da cewa. "Jeki kawo mun abinci". Ya faɗa tare da ɗago kai ya kalleni, ya wani ɗan zaro mun idanunsa, ya ga na haɗu, na sha gyara, skin ɗina yana wani irin sheki sosai, ga henna da na sha, ya Salam, na haɗu na karya, gagara ɗauke kallonsa daga kaina yai.

Sai ya ce. "Ki kawo mun abincin ɗaki"...... Kamar zan ki bashi abincin in ce ban dafa ba kayan abinci ya kare, amma da na tuna iyayena basu koya mun hakan ba, kuma shima yana daga cikin sadaka, sai na miƙe na nufi dining area ɗinmu. Ya wani bini da mayen kallo, yana jin tamkar ya jawoni jikinsa. Ni kam tsabar iyashege har da kara jujjuya mashi mazaunai na dan ko ban juyo ba nasan yana kallona, saboda nasan halinsa sarai.

Gabaɗaya lokaci guda ya birkice, ya fara haɗiyar yawu, maƙogwaronsa tana wani sama ta sake yin ƙasa, da sauri ya miƙe ya wuce cikin ɗaki. Na zuba mashi abinci na bi bayansa ɗaki, na ajiye mashi saman carpet na gaban bed ɗinsa, na ɗauko mashi ruwa da cup, na juya zan fita ya ce. "Habibiya waye zai ciyar dani kenan?". Yana zaune a gefen gado.

Na wani kallesa bayan na juyo, na ɗan taɓe baki kafin in ce. "Sodangi mana, ba part ɗinta zaka koma ka ci ba, coz naga ba a nan kake ba".......... Ya ce. "Ban gane me kike nufi ba"........ Na bisa da wani kallo mai kama da na rainin wayau kafin in ce. "Wai Abbie yanzu kwanakinka nawa rabonka da side ɗin nan?".

Cikin kwantacciyar murya saboda yana son abi a wajena ya ce. "Kefa kika ce in zauna a side na Zainab na wata huɗu, shi ne kuma kike jin haushi dan ban zo wajenki ba?"...... Na yi wani irin murmushin kafin in ce. "Awwww ALLAH? Abbie kenan, amma da na ce ka zauna a side nata sai na ce da ciyarwarmu dake kanka duk ka haɗa ka mayar da shi kanta kenan ko?".

Ya girgiza mun kai tamkar kara min yaro alamar a'a. Na ce. "Right, yanzu ma dan ALLAH ka koma side ɗinta, dan sai mun cika alƙawarin watanni huɗun nan"...... Da sauri ya ce. "Matsalata dake kafiya habibiya, dan ALLAH bar dukka wannan magana, zoki ji wata magana"......... "Ina jinka". Na faɗa ina tsayem

Ya sake yin ƙasa da murya wajen cewa. "Please Habibiya ki zo jikin mijinki sai in faɗa maki"......... Na girgiza kai. "A'a ni ba zan zo gaskiya, hakan cin amanar matar so ce watau sodangi"......... Da sauri ya ce. "Amma Habibiya kin san matsala shi ne kike hukuntani da raunina a kansa ko? Kin san da cewa ALLAH yana tsinewa duk macen da mijinta ya nemeta taki yarda ko?".

Na saki murmushin takaice game da cewa. "Haka zalika ALLAH yana tsinema mai karya alƙawari, alƙawari muka yi da kai zaka kasance a ɗakin matar so a wajenka na wata huɗu, dan haka sai waɗan nan kwanaki sun cika, ka je ta kwantar maka da buƙatarka mana, duk abin da nike da shi tana da shi, awww na manta na ta fini, ka ce a wajenta kawai kake gamsuwa, sannan idan ka ga kirjinta kawai kana jin ka biya, ni da bani da su, ni da nawa suke ƙanana me zaka yi da su? Ka manta ka ce mata ta fi komai daɗi a duniya? Duk ka manta waɗan nan kalamai? Ka mance ka ce mata baka taɓa gamsuwa ba ka matsu ta shigo dan ita kaɗai zata gamsar da kai, ka manta ko? To ni ban manta ba, ka je ta gamsar da kai, ni da bani da komai, and idan ka cika matsa mun billahil lazi zan jingine auren nan tun da dama ba wajibi bane sunnah ce!". Ina kai karshe na juya na fita, hawayen da nike ƙoƙarin dannewa suka cika mun ido, amma ban bari ya gansu a idona ba, sai da na fita ɗakin suka fara zubowa.

Jikinsa yai wani irin mangariba bama la'asar ba, ya ji tabbas bai kyauta ba, shi da kansa yasan wlh ba wata mace da yake gani feeling ɗinsa ta motsa sai ni, wlh ko zai kwana da Zainab tana tsirara sha'awar tasa baya tashi, amma ni da zarar ya ganni abar zata motsa mashi, ni'imata dana Zainab daban-daban, tabbas Zainab tana iya jure ko sau goma zai yi, amma matsalar bata taɓa bashi gamsuwa ne, yana yi ne kawai dan lafiyar jikinsa, ni kuma kalar ni'imar da ALLAH ya mun sau ɗaya idan ya yi zai samu gamsuwa, amma saboda ni'imata sai ya kara dan bala'i irin nasa, son zuciya ce da ruɗin soyayya yasa ya dinga faɗan abubuwan da ya faɗa wa Zainab, yanzu ya shiga nadama.

Jiki a mace ya sauƙo ƙasa ya fara cin abincin da ta zame mashi dole ci, yunwa yake ji sosai, ga shi ya ganni abar ta tashi, sai ta haɗe mashi biyu. Ni kuwa ina fita na shiga ɗakina, na ɗan yi kukan huce haushi kafin in shiga toilet, na wanke fuskata na fito, a parlo na zauna tare jawo wayata. Daidai lokacin Abba da su Hassan suka shigo, ai yaran nan yau ko kallona basu yi ba small daddynsu ya dawo, ɗakinsa suka bisa da gudu, ina kiransu suna gudu wajensa.

Ina zaune anjuma suka fito da uban niƙi-niƙinnkaya a hannunsu, suna sanye da sabbin sportswear a jikinsu, da alama shi ya saya masu. Zazzaro ido na yi ina tambayansu. "Wannan kayan fa"...... Hassan ya fi iya magana shi ne ya ce. "Uncle daddy ne ya ce mu kawo maki"....... Basu ƙariso in da nike ba suka daɗi saboda ledojin kayan ya fi karfinsu.

Da sauri na tashi na taresu ina mamakin wannan uban kaya haka ne da me a cikin ledojin? Watau tsaraba aka kawo mana, shi kuma Abban yana ɗaki a kwance. Da sauri ya hau buɗe ledojin, su kuma suka juya da gudu suka koma ɗakin nasa.........

A tunaninku me uncle daddynau Hassan ya kawo mana matsayin tsaraba? Me a waɗan nan ledoji?

labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.

FATEEMA ZAHRA MUSA

A-K-A

QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥

LABARIN AISHA.🥹💔