GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 11

by @nusybee143

Page 11



Hajiya Ruƙayya da ta kusa ƙwarewa da bayanin Arfa ta yi saurin kora ruwa tana zare idanu,a ɗan firgice ta ce"ban...ban fahimta ba Arfa,ki yi min bayani yadda zan fahimta,me kike nufi da abin da kike faɗa?"

Cikin kuka sosai Arfa ta ce"na gaya miki Aunty kama shi na yi yana kallon hotunanta,dama tunda muka yi auren ba wani ba ni hankalinsa yake yi ba, gaskiya Aunty da sake,ya kamata a san yadda za'a yi,don ba zan iya zama yana wulaƙanta ni akan wata kilaki ba"

Hajiya Ruƙayya ta numfasa ta ce"ki kwantar da hankalinki Arfa,da kin gaya min tun farko da tuni na yi wa tufkar hanci, yanzu ma dai bata ɓaci ba,sai na yi masa abin da ba zai sake sha'awar ko da kallon wata mace ba sai ke,ko da uwarsa ce kuwa,don ba zan ɗauki wargi irin haka ba"

Arfa ta ja numfashi tana faɗin "to na gode aunty,sai na ji ki"suka yi sallama, Arfa ta miƙe tana goge hawayenta 






*TIJUANA, MEXICO*

*CLUB SAFARI*

A hankali take kwantar da kanta a bayan kujerar da take zaune tana sauke numfashi a hankali bayan ta gama zuƙar hayaƙinta na shisha, David da yake tsaye a bayanta ya sunkuyar da kanshi daidai saitin nata,murya ƙasa-ƙasa yana faɗin"Ma!

Are you okay?"

Shiru ta yi ba tare da ta yi magana ba,ba wannan ne karo na farko da David ya ganta a wannan halin ba, wanda har zuwa yanzu babu wanda ya san abin da yake jefa ta cikinsa 

Kafin ya sake yin wani yunƙuri ta buɗe idanunta da suka sauya kala tana miƙa masa hannu,ya san me take nufi,a take ya zaro ƙwayoyin da take sha idan tana cikin wannan halin ya miƙa mata, ba tare da tunanin komai ba ta afa su gaba ɗaya,ta mayar da kanta ta kwanta tana sake lumshe idanunta 

"Is everything alright ma?"ya tambaya a hankali 

Buɗe idanunta ta yi, waɗanda suka sake birkicewa tana lumshe su,da muryar maye ta ce"I want..... let's go home.....ppplease!"

Ba tare da ɓata lokaci ba ya taimaka mata ta miƙe tsaye sannan suka fice daga club ɗin,bakinsa fal tambayoyi,ya san zuwa suka yi don su gudanar da irin kasuwancin da suka saba,amma ta shiga wannan halin, wanda ta saba shiga a duk lokacin da wani ƙunci ya mamaye zuciyarta, wanda har zuwa yanzu ba su san menene silar ƙuncin ba,don ko da wasa bata taɓa faɗawa wani ba

Washe gari Roxy tana tsaye a bakin window ɗin ɗakinta tana kallon shuke-shuken da suke bayan ɗakin nata, sai dai kuma hankalinta ba ya tare da ita,asalima ya luluƙa can tunanin baya




💫


"Yaya! wallahi ina sonshi!don Allah ka yi haƙuri ka ƙyale ni,idan ban aure shi ba zan iya mutuwa 

Yaya saboda ni ya musulunta fa!yaya kar ka yi silar da za mu yaudare shi,bana son ya kalli musulmai a matsayin mayaudara,don Allah yaya ka yi mana addu'a, please yaya na!ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamun roƙo

"A'a baby girl! don Allah kar ki yi min haka!

Na fara sonki tun ba ki san kanki ba,tun kina yar jaririya, wallahi sonki zai kashe ni,zai yi min illa,don Allah!don Allah baby girl!kar ki juya min baya ki auri wani, Please!!!"

"Please yaya!zuciya ta tana wajen shi,idan na aure ka ba zan so ka ba,ba zan yi maka biyayya ba,Ni tashi ce, zuciya ta tana gare shi, Please! please yaya!!"

"Baby girl!

Are you telling me kina son wani?da shi kadai za ki rayu?all in before my eyes?what the heck!!!

Baby girl wake up!nine fa yayanki,abin alfaharinki,abin sonki,amininki tun kina ƙarama,kin manta da haka?"

"I'm sorry yaya!stay in your lane,but I will never marry you, I'm not in love with you!"





💫


"Roxy are you okay?"da sauri ta juyo tana kallon Hanna da ta zuba mata idanu tana yi mata kallon tuhuma 

Ɗaure fuska ta yi,ta ce"kin ga wata matsala ne, I'm okay mana"ta ƙarasa faɗa tana juyawa ta koma bakin window ɗin da take tsaye 

"But kukan me kike yi?"Hanna ta jefa mata tambaya, Roxy ta juyo ta kalle ta tana faɗin "kuka kuma?"

Hanna ta ce "ga hawaye nan a idanunki,kuka kike yi mana"Roxy ta yi ɗan murmushi,ta juya ta sake fuskantar windon tana goge hawayen da ke fuskar tata, kafin ta ce"I need space,can we discuss later?"

"But Carlos yana jiranki fa Roxy!"

"Tell him I'm not available today!"ta faɗa ba tare da ta kalli inda Hanna take ba

Hanna ta gyara tsayuwarta tana harɗe hannayenta a ƙirjinta ta ce"okay okay!

Shikenan to,amma ki gaya min menene yake damunki haka?"

Cikin isar da ta zamewa Roxy jiki ta ce"its none of your business!"

"But Roxy Why na?me yake faruwa ne?kina da wasu aminai bayan mu ne da ba za ki iya gaya mana matsalarki ba?

Please Roxy!"juyowa ta yi tana kallonta, kafin ta ce"kina da wata alaƙa da abin da ya dame ni ne?"Hanna ta girgiza kai,kai tsaye Roxy ta ce"so ba Ni waje!

Maganar Carlos kuma ki ce ya dawo anjuma,idan ya wuce anjuma kuma shi ya rasa, I'm leaving this country first to thing tomorrow morning "Hanna ta kalle ta kawai, kafin ta juya ta fice daga ɗakin don isar da saƙonta, Roxy ta faɗa kan gadonta ta lumshe idanunta,tana jin da zata yi kuka ma da ta rage raɗaɗin da yake taso mata







*DSS HEADQUARTERS, KANO STATE, NIGERIA*


"CSO Haisam Abdulmalik Madaka!

A last meeting da muka yi da kai mun yi magana,inda ka tabbatar mana za ka iya kama yarinyar nan ka dawo da ita,ta fuskanci doka,amma abin mamaki har yanzu shiru,babu wani feedback na a zo a gani,me yake faruwa ne?"

Haisam ya ɗaga kai ya kalli state director jiki a sanyaye,bai taɓa jin ya muzanta irin na yau ba,amma ɓacin rai da shan alwashin da yake ciki sun haura muzantar da yake jin ya yi

A hankali ya miƙe don bayar da ba'asi

"Operation ɗina ya yi failing,amma zan sake trying in sha Allah "

"Amma an ce ka bi ta har ƙasar Spain har kuka haɗu da ita,me ya faru baka kamo ta ba?"

Kai tsaye ya ce"wani slide mistake ne ya faru,amma very soon zan yi fixing ɗinsa"

Shiru office ɗin ya yi,sauran abokan aikin nashi suna jifansa da wani kallo,kafin state director ya cigaba da faɗin"yanzu ka yarda yarinyar tana da kaifin basira fiye da tunanin ka?"

Babu ko shakka Haisam ya jinjina kai 

SD ya yi murmushin takaici ya ce"to yanzu za ka bar mu mu yi aikinmu ko?tunda zuwa yanzu ka gane ba gazawa muka yi ba,da kake neman nuna mana ba mu iya komai ba"

Haisam ya ce "I'm sorry sir!ko a baya ma ba raina iyawarku na yi ba,kawai dai ina da ƙwaƙwƙwaran sanin cewa zan iya kama ta,kuma...."

"Sai kuma gashi ta rusa kwarin naka!

Ko sai na gaya maka abin da ta yi maka,kowa ya ji sannan za ka bar cika mana baki?"

Shiru Haisam ya yi ba tare da ya yi magana ba, kanshi a ƙasa, SD ya ja tsaki ya ce"wannan operation ɗin ya bar hannunka,zan mayar da shi hannun wanda ya dace,kuma zai iya abin da ya dace

SO Shuaibu Ahmad musawa,kai za ka yi taking over na wannan aikin"Shuaibu ya sara yana faɗin "noted sir!"

A Ranar dai haka taron ya watse zuciyar Haisam sam babu daɗi,kuma kai tsaye ya nufi gida ba tare da ɓata lokaci ba

Yau bai nemi Amna ba,don ya san tana makarantar islamiyya,bai nemi mamy ba saboda ya san bata dawo daga aiki ba,bayan ya je masallaci ya yi sallar azahar ya koma gida ya kwanta akan gadonsa,yana cigaba da danne danne a wayarshi 

Kira ne ya shigo,ya ɗaga wayar yana faɗin "ya dai Saleem?"

A buɗe yake a gare shi cewa bayan yaran Roxy da suka raina masa hankali akwai wanda ya ci amanarshi a cikin nashi yaran,a dalilin haka ya sa ya ji sam ba zai sake yarda da su ba, gashi kuma yana zargin a cikin hukumarsu akwai masu fitar musu da sirri

A dalilin haka ya saka Saleem ya yi masa bincike akan Roxy, Saleem ba jami'i bane,mutumin gari ne, ko zurfin karatu bai yi ba, iyakar shi diploma a fannin political science,amma sama ta ka Allah ya ba shi ilmin computer da na sarrafa harshe,ga wayo da hikima da dabara, Haisam ya ja shi a jiki, kasancewar shi yana da alaƙa da shi ta wajen mahaifiyarsa,ya ba shi jari, sannan idan yana son yin bincike mai wahalar irin wannan Saleem yana taimaka masa su warware shin

Daga ɗaya ɓangaren Saleem ya amsa yana faɗin "Barka da warhaka Oga!ya aiki?ya fama da mu kuma?"

Haisam ya ce"alhamdulillah Saleem,ya batun aikin da na saka ka?"

Saleem ya ce"Oga ai na jijjiga da abin da na gano game da yarinyar nan,a kaf abubuwan da ake zargi babu wanda yake a yadda ake kallonshi"

"I don't get what you are saying Saleem?"Haisam ya tambaye shi 

"Da farko dai,na fara bincike akan wadannan letters ɗin da take amfani da su,kuma na gano ma'anarsu"

Da sauri Haisam ya ce "I'm all ears Saleem,me suke nufi?"

Saleem ya cigaba"wadannan letters ɗin ba ƙungiya ba ce,kuma ba wata alama ba ce,barazana ce kawai sai kuma yin wani abu da ta san zai ɗauke hankalin mutane

Yawan amfani da su da take yi ga mutum a yayin da ya shiga gonarta shi zai saka mutum ya fara zargin wani abu a ƙarƙashin waɗannan letters,bayan kuma a zahiri babu komai a ciki,ta yi amfani da su ne don ta rainawa mutane hankali 

A taƙaice dai NOCCM full meaning ɗin shi shine NO ONE CAN CATCH ME!

Kalmomin ba na wani abu bane sai na fariya kawai, shine abin da na samu game da kalmomin NOCCM 

Sai kuma abubuwa da yawa da na gano,amma kafin nan ita wannan yarinyar tana da wani tarihi da yake ɗauke da wani tabo, kusan dai na ce shine silar faɗawarta halin da take ciki 

Sannan kuma akwai sirri sosai a tare da ita wanda na yi nasarar ganowa, shine MUBARAK!

MUBARAK kuma ya kasance........"

"No Saleem,na san wannan cigaba da gaya min abubuwan da ka gano"babu musu Saleem ya saki batun Mubarak ya cigaba da bayanin abubuwan da ya gano game da Roxy, wanda har ya yi bayani ya gama Haisam yana ɗan murmushi 

Sai da ya gama tsaf Sannan Haisam ya ce"na gode Saleem,zan kira ka later "bai jira amsar shi ba ya kashe wayar 


Gyara kwanciyarshi ya yi yana murmushi sosai,a hankali ya furta"Roxy!or whatever your name is, your end has began!"ya janyo laptop ɗinsa ya buɗo wasu hotuna yana kalla yana murmushi 





*NNAMDI AZIKWE AIRPORT,ABUJA, NIGERIA*


Miƙewa ta yi don zuwa wajen da Bolt ɗin da ta tsare yake,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga suka nufi suleja 

A can suleja bayan ta sauka kai tsaye ta kunna kai ta nufi gidanta, Amra da ke zaune tana shan kayan mayenta,gefenta wani saurayinta ne,ta ɗago tana kallonta cikin mamaki

Waje ta samu ta zauna tana kallonta, kafin ta daga gira,alamun kallon fa?

Amra ta yi dariya irin tasu ta yan maye ta ce"surprise!

Yaushe kika sauka a ƙasar?"Roxy ta mayar da kanta ga wayarta da take cirewa a flight mode ta ce"yanzu na sauka,ina sauka kuma na yo nan,ko gida ban je ba"

"Gaskiya ne tawan!

To ina su David ɗin?"

Roxy ta yatsina fuska ta ce"suna can"

"Yaushe za su taho?"Amra ta sake jefa mata tambaya 

Banza Roxy ta yi mata, saurayin Amra ya cewa Roxy "Hi beauty!"

Ɗagowa ta yi ya watsa masa wani kallon wulaƙanci sannan ta cigaba da danna wayar hannunta, kafin ta ɗago ta kalli Amra ta ce"ya ne?

Ina buƙatar hayaƙi fa,kin san kai kogo ne"

Amma ta ce"bari na ɗauko na haɗa miki welcome"ta mike ta fice daga parlourn tana faɗin "bad boy see you later,ka ga ina da baƙuwa"bad boy ya miƙe yana faɗin "see you letter Hajiya ta,amma wannan baƙuwar taki zazzafa ce,ina son kayan idan babu damuwa "

Dakatawa Amra ta yi daga fita,ta juyo ta kalle shi tana faɗin"hattara dai! wannan kayan ya fi ƙarfinka "sannan ta fice daga parlourn 

Shima bad boy ficewa ya yi daga parlourn yana faɗin"see you letter!"

A ɗakin Amra kuwa,da sauri ta dauki waya ta danna kira,babu jumawa ta fara magana 

"Hassy!

Tana nan fa "daga ɗaya ɓangaren Hassy ta ce"a haba!ki ce tana nan

To kwana zata yi?"

Amra tana leƙe ta ce"no ban tabbatar ba dai tukunna,amma kuma na san Roxy bata da alƙibla, yanzu zata iya chanjawa ko da ta yi niyyar kwana

Ita kaɗai ta zo ba tare da mutanenta ba"

Hassy ta ce"daidai kenan,ki tsare mana ita,ko da a ce kin ga alamun zata gudu ki jefa mata ƙwayar nan da na ba ki a lemon ki ba ta,kin san yadda za kiyi dai,amma dai na kwaɗaitu da jikin yarinyar nan over,kuma na rantse sai na kwanta da ita,ina tsananin sonta,amma ita sai jiji da kai da wulaƙanci"





#Nusy_bee