Chapter Three
Shiru ne ya mamaye ɗakin . A hankali Kuma Waheedah take share hawayen da suke gangaro mata wanda dama a koda yaushe basa rabuwa akan fuskanta.
Baba ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya miƙe a hankali yace
"Ki yi ƙoƙari ki kwanta ki huta Waheeda, kin ji?"
"To Baba."
Ya gyada kai sannan ya fita daga ɗakin.
Da fitarsa, Waheedah ta sake rungume ƙafafuwanta. Duk da gajiyar da take ji, barci ya ƙi zuwa idanunta. Tunani kala kala ne kawai ke yawo a zuciyarta.
Ta tuna ranar da mahaifiyarta ta rasu.
Ranar da duniya ta yi mata duhu.
Tun daga wannan rana rayuwarta ta sauya. Murmushi ya yi mata wahala, farin ciki kuma ya zama tamkar wani abu da ba nata ba.
A hankali idanunta suka fara rufewa har barci barawo ya ɗauke ta.
Washegari
Da asuba ƙarar zakara ta farkar da ita.
Ta buɗe idanunta tana jin sanyin safiya ya ratsa jikinta. A hankali ta miƙe ta gyara zanin jikinta sannan ta fito daga ɗakin.
Tsakar gidan nasu daya gama chabewa sbd ruwan da akayi jiya ta fita tana kare masa kallo kafin a hankali ta fara jan kafafuwanta zuwa gurin da wata katuwar tukunyan da suke taran ruwa a ciki take buta ta dauka ta debi ruwa sannan tayi hanyar da bayin su yake wanda wasu yan karare ne aka samu akayi bayin dasu.
Bata wani jima sosai ba ta fito ta daura alwala ta koma dakin da ta fito, cikin ganan da yake dakin ta bude ta dauko wani dankwalinta ta shunfuda ta tada Sallah a cikin nutsuwa bayan ta idar zaman ta ta gyara sannan a hankali cikin muryanta me sanyi ta fara karatun Qur'ani wanda a duniyan ta shi kadai take yi ta samu natsuwa a cikin ranta.
A haka baccin da bata samu tayi sosai ba ya dauke ta.
Karfe shida da wasu yan mintina aka dage buhun dakin wata matace ta shigo dakin baka ce sosai irin asalin bakin nan dan tsaban bakin ta har wani sheki takeyi sannan kuma bata da wani tsayi sai uban kiba fuskan ta yasha zane.
Karewa Waheeda da take kwance take bacci a inda tayi sallah kallo tayi tana wani yamutsa fuska a fili tace wato har wani bacci ma wannan shedaniyar yarinyar take yi kenan lallai zanyi maganin ki wllh tana gama fadin hakan ta juya ta fita daga dakin zuwa tsakar gidan kalle kalle ta farayi can ta hango wani bokati a bakin bayin gidan cikin sauri ta nufi bokatin ta dauke shi ta cikashi da ruwa ta wuce dakin da Waheeda take har yanzu kuma tana nan ya yanda take ko motsawa batayi direct kanta tayi ta daga duka bokatin nan ta juye mata uban ruwan da ta debo me uban sanyi.
A firgice Waheeda ta tashi saboda saukan ruwan sanyin da taji a jikin ta.
Matar kuwa tana tsaye a kanta hannaye a ƙirji tana kallonta da wata muguwar harara.
"Wato ke har kin samu daman da zaki kwanta bacci a gidan nan ko Dan uban? Uwar ki data ke kabari kike so ta taso tayi aikin daya ke gidan nan ko yaya?
Runtse ido Waheeda tayi saboda tabo mahaifiyarta da matar tayi kafin a hankali ta bude ta sauke su akan akan matar da har yanzu take tsaye sai huci take ta rasa me tayiwa Dada ta tsane ta haka a rayuwan nan.
Wai dan ubanki ba magana nake miki bane kin wani tsareni da shegun idanun kinnan.
Muryan Dada ya dawo da ita daga duniyan tunanin data lula.
Mike wa tayi tsaye tana rawan sanyi.
Kiyi hakuri Dada ta fada cikin sanyi murya kanta a kasa.
Wani shegen kallo Dada ta watsa mata kafin tace kinci gidan ku da hakurin zaki wuce kiji ki kamamin aikine ko zaki tsaya kamar wata munafuka.
A hankali Waheeda taja kafafuwanta da suka mata nauyi tabi ta gefen Dada ta fita daga dakin.
Kwafa Dada tayi tace wllh indai ina raye a duniyan nan babu ke babu jin dadin rayuwa sai kin gwammace ki mutu kibi shegiyar uwar ki wllh.
Please follow my Account
Like the Book
And Comment
Deejarth Abdoul 🖊️