Chapter 10
by @nimcyluv
Turus Gana ta tsaya a bakin ƙofar tana nazari sai kuma ta juya da murmushi ta ce "Hindatu ina ganin ki bari zan shigo na kawo miki, tunda har man ya yi miki daɗi" a zuciyarta kuma ta ce "Sai na ba ki ƙanƙarar maitar ki ji idan maitar daɗi gare ta shasha" ta yi furucin haɗe da yin gatsine tana me haɗawa da ƙwafa a lokaci guda.
*
MD a baƙin ƙofar room ɗin da aka ajjiye Ahlam ya tsaya ya harɗe hannayensa a ƙirji zaka rantse da Allah ba sashin dasu Ahlam da nurse ɗin yake kallo ba. Hawayen azaba ne kawai yake fita daga cikin idanun Ahlam yana bin kumatunta. Nurse dake riƙe da kayan Treatment ta ce "Sannu Golden voice" "Kin sanni ne?" Ahlam ta furta da ƙyar tana cije laɓɓanta da yarfar da hannunta sbd zafi
Nurse ta ce "E. Bake ce Ahlam Abdallah Kurmi ba, me yin dandalin nishaɗi program ɗin samari da ƴan mata a Bright Fm? Ina bibiyar shafinki na Facebook da Tiktok" duk da a cikin halin ciwo Ahlam take sai ta ji wani irin farinciki mara misaltuwa bata taɓa tunanin zata je wani waje a nuna an santa ba a dalilin aikinta na jarida, sai ta ji wani irin courage da confidence sun haɗe mata waje guda, ga wani hope data samu a furucin Nurse. Ta ɗan yi yaƙe ta ce "Thanks"
"Muke da godiya ai Golden voice" ta faɗa da zumuɗi na farinciki
"Idan an kammala treatment ɗin sai ku ƙarasa hirar taku ko?" Cewar Dr yana riƙe almaƙashi a hannunsa. Shiru Nurse ta yi ita kuma Golden voice ta kalli Dr a hankali cikin ƙasa da murya saboda har lokacin jini ke zuba a wuyanta ta ce "Sister ko za ki ara mini wayarki na yi vedio sai ki tura mini ta WhatsApp?" Cikin sauri Nurse ta ce "da gudu ma, Golden voice guda yadda nake mutuwar son programs ɗinki babu wanda bai san sunanki ba a bakina musamman ƴan gidanmu" wani yalwataccen murmushi Ahlam ta saki cike da jin daɗi da alfahari ta ce. "Ai har photo za mu yi, zan yi inviting naki zuwa shirin dandalin nishaɗi sister"
"A wannan rana har party zan haɗa a gida" Tana faɗin hakan ta cire password ta miƙawa Ahlam wayar. Sun ɗauka wani nata zata kira ko gidansu zata sanar wa tsautsayin daya sameta. Sai su kaga akasin hakan, domin camera ta buɗe ta saita a kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka ta shiga faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Kamar yadda kuka sani sunana Ahlam Abdallah Kurmi matashiyar ƴar jaridarku wacce aka fi sani da Golden voice. A yau na tashi da babbar jarrabawa a sanadin aikin jarida, shigowata Bright Fm kenan wani ɗan balaja'u riƙaƙƙen ɗan daba ya kawo mini hari, wanda rayuwata ya nema kai tsaye Allah Ya kiyaye ni, ban san me na yi masa ba, amma ya yi iƙirarin ganin bayana kuma yace saboda rahotan matar da aka ƙonawa jariri ya yi mini haka. Kai ɗan'daba idan kana jina ka saurare ni da kyau, ni ƙadangaren bakin tulo ce ban fito ba sai dana shirya, aikin jarida yanzu na fara ko da kowa shi ne silar barina duniya ba zan tsagaita ba sai na cimma burina, yadda ka yi mini abin nan ka sake rura wutar abin, sai an ƙwatar wa matar nan haƙƙinta idan ma ubanka ne ya sa ka yi mini abin. Na gode jama'ata a tayani da addu'a hakan ma alamun nasara ne da ɗaukaka, zan zo muku da cikakken bayanin abin da ya faru da matar. Har kullum Golden voice ce taku"
Tana kammala vedion ta miƙawa Nurse wayar ta ce
"Na gode sister "
"Babu komai. Allah Ya cigaba da tsare wa" cewar Nurse ɗin
"Wayyo yayana, zan mutu wayyo Anty Jiddah" ta cigaba da ihu da yarfe hannunta saura kaɗan likitan ya fashe da dariya. Dukkan kuma abin da yake faruwa akan idanun MD baya ko motsi daga ƙarshe ma, juyawa ya yi yabar cikin room yana amsa kiran wayar da ake ta yi masa a lokacin. Treatment aka yi mata da allurai da drip Allah Ya taimaka yankan babu zurfi a jikinta
*
"Kan uba amma annarka uwar dukiya a gidan nan, Allah ka bamu mu taɓa, wasu sukan ce arziƙi kashi baka kwana dashi ba, sai ka tashi dashi. Kamar gidan ƴan Film" Tunda Emama ta shigo Baffas estate ta kasa yin shiru da bakinta saboda sambatu ganin daular gidan girma da arziƙinbgidan masu Jiha da juya wasu rassuna na ƙasashe. Gidan da ake ado da addini da taƙama da Musulunci gidan cikakkun mabiyan Izala (Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa lqamatis sunna). Ganin babban parlorn da ake ajjiye baƙi babu kowa sai su ya saka Emama zungurin Iftihal ta ce "Kalli gida ɗan ubansu, ba irin na gidanku ba wanda uwarku ta ja mana jarfa, ai Allah Ya isa tsakaninmu da Innti sau cikin carbi gantalalliyya matsiyaciyya" Iftihal ta runtse idanunta daga zaunen da take tun ɗazo ta ƙanƙame jikinta waje guda, wasu hawaye masu zafi suka shiga bin fuskarta. Idan ta buƙaci lallashin kanta da zuciyarta da zarar ta tuna wai an sakata a caca Alhaji Baita ta cita sai ta ji tsakanin rayuwarta da mutuwa babu tazara, walwala da farinciki sun sake nesanta kan su da ita. Iya rumbun cikin Alhaji Baita tsoro yake bata, balle ta kalli cikin bakinsa, gashi bata ma san ya kalar gidansa yake ba, babban abin da yake mata yawo a kanta bai shige rashin sanin aurenta zai yi ko kuma farkarsa zata zama a gidan?
Tana cikin wannan tunanin Emama ta ce "Idan kina so a soke batunki da Alhaji Baita ki yi ƙoƙarin sace zuciyar wani namijin a gidan nan, ko me gidanne ma. Ina nufin magajin gidan, idan hakan bata faru ba, da zarar kinga an ajjiye kuɗi ki yi wuf ki saka su a hammata ko cikin wando ko cikin hular kan ki, su basa jin kuɗin a iska suke ganinsa ina faɗa miki. Ɗan raguye-raguyen abinci da nama duk ki haɗo kan su ki juye a leda ki kawo mini har gida. Ke ko wani ne ya nuna yana buƙatarki ki amince" sai ta yi saurin rufe bakinta ta ce "Asstagafirullah! Nan gidan malamai ne na manta ba za'a samu me bin mata ba" ita kaɗai take da surutunta ci kan ki Iftihal bata iya cewa ba. Ina zata iya magana? Bayan ƙirjinta ya jima da yi mata nauyi yana rinjayar zuciyarta, ji take kamar zuciyar ce zata tarwatse gabaɗaya ta huta.
"Assalamu alaikum"
Wata kyakkyawar yarinya ta yi sallama ba tare data shigo ba.
"Maraba waye?"
"Zan iya shigowa?"
"Bisimillah"
Shigowa ta yi ta gaishe da Emama ta ce "Mamy ta ce ku shigo ɗaya parlorn"
"To to to babu laifi, ke tashi muje" tana faɗin hakan ta juya abinta. Emama ta ce tana kallon Iftihal dayin gaba.
Iftihal bata san ya aka yi ta iya miƙewa ba, balle tasan yadda aka yi ta iya taka ƙafafuwanta taje bakin ƙofar kamar yadda bata san mene ya tsayar da ita a wajan ba. Ta ji ƙamshi na dukan hancinta ta kuma ji ƙwayar idanu na bin jikinta wanda ya sake sakar mata da lakar dake riƙe da gadon bayanta zuwa ƙafafuwanta. Idanunta rufe kamar yadda ƙofar zuciyarta yaja ya rufe bata san kuma mene ya haddasa mata rawar ɗari ba, gabaɗaya ta yi baya ta nemi zubewa a wajan.
"Ki bi a hankali ko?'
Ta ji sautin muryarsa ya sauka a kanta. Ta buɗe idanunta da ƙyar ganinta ya sauka a farar fuskarsa me ɗauke da nutsuwa da kamala, nutsuwarsa kaɗai ta isa ta nuna yadda ibada ta zauna masa domin ta tabon sallah nan a tsakiyar goshinsa, wanda hakan ya tuna mata da nata tabon ta miƙa hannu kaɗan ta shafi nata tabon hakan ya saka ya kai dubansa ga nata.
"Ma sha Allah"
Ya ce a fili yana bin gefenta ya shige. Iftihal ta ƙarasa ta zauna kanta a ƙasa ta ce
"Ina yini?"
"Allahamdulillah"
Mamy ta amsa da kulawa.
"Ita ce me aikin?"
"E Hajiya ita ce kamar yadda kika nuna yarinya kike buƙata itama bata shige 17 ba"
"Age mate ɗin Nadiyaah da Diyanah ce ashe ma"
Mamy ta furta a fili kafin ta ce. "Shukràn alaiki. Waɗanda za ta yi wa aikin sa'ointa ne. Zata dinga musu breakfast, lunch da dinner. Ina ga iya lunch ne dinner bai wani dame su ba. Sai mahafinsu idan ya dawo" idanunta akan azkar ɗin hannunta take yin maganar. Da kamala a tare da ita. Emama ta ce
"Duk zata iya babu assha"
"Makaranta ta?"
"Na'am........?
"Bata zuwa makaranta ne?"
Caraf ta ce "Lahaula bokoko a wuta? Ai tuni suka yi mata korar kare bata fahimta sam a karatun data samu mijin aure za'a yi mata"
Daidai nan ya sake shigowa parlourn cikin sabuwar shiga wagambari ya saka ruwan sararin samaniya wanda ya kwanta a jikinsa ya ɗora hula me kyau ta zauna a sumar kan, bayan ya sake yin sallama ya nemi waje kusa da Mamy ya zauna. Mamy ta kalli Iftihal lokaci guda ta ji yarinyar ta shiga zuciyarta. "Ok. Per month kuke son salary ɗinta ko per year or daily? Wanne a ciki"
Emama ta zazzaro idanunta waje. Mamy ta ɗauki a ƙallla minti uku tana duba azkar kafin ta ce "duk wata za'a dinga bata dubu ɗari da hamsin in sha Allah, ki je ita zata dawo gida anjima ko?" Sallama Emama ta yi musu ta tafi. Bayan tafiyarta aka nunawa Iftihal wani kitchen daban da zata dinga aiki a ciki. Mu'allim ya dubi Mamy ya ce "Baffa be sanar dake garin da yaje da'awa ba ne Mamy?" Kai kawai ta girgiza. Bai sake cewa komai ba, domin ya lura itama Mamyntasa bata da ra'ayin cewa wani abu a yanzu ɗin. Don haka sai ya tattara nutsuwarsa wajan jan idanunsa ya lumshe yana sauraran kiran Liman duk da babu tabbacin zai kira shi a yanzu ɗin kamar yadda ya ce. Kasa haƙuri ya yi ya dubi Mamy ya ce "Mā ismuhā?" (Ya sunanta)" A hankali ta juya ta watsa masa fararan idanunta ta ce "kana da business da ita ne Mu'allim?"
"Mamy kika sani ko a haɗa bikina dana Akhy" azkar ɗin hannunta ta ajjiye ta kalli jaridar dake saman table ta miƙa hannunta tare da faɗin "Nāwilni" (Miƙo mini" ya ɗauki jaridar ya miƙa mata yana rusunar da kai gefe cike kuma da ladabi. "Mamy don Allah...," ta yi saurin katse shi da faɗin "Ina ga kamar ka san hanyar shiga kitchen ko Al'ameen?" Ya ɗan cire hularsa yana shafa kai bai sake magana ba, ya nufi saman bene Mamy ta bishi kallo har ya shige a hankali ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya me nauyi.
Tana tsaye a gaban haɗaɗɗan madubin dake cikin bedroom ɗin tana yin rolling da mayafin abayar hannunta, silver ce irin wacce bata da nauyi a jiki tabi jikinta ta kwanta. A hankali ta ɗan yatsuna fuska saboda ciwon dake ɗarsarta har yanzu. Daga bayanta aka ce "Ukhty ina zaki ne?"
Nadiyaah ta juya ta kalli Diyanah dake kwance saman kujera wacce take jikin gado, kayan shan iska ne marasa nauyi a jikinta sai data gama ƙare mata kallo ta ce
"Abinci"
"Yunwa nake ji.....
Taja idanunta wanda suke sak irin na mahaɗinta ta ce "Sosai nake ji Ukhty" Diyanah ta sakko daga saman kujerar ta ce "Muje na tayaki girkin ko noodles ce"
"Noodles dai?" In ji Nadiyaah.
"Yeah. Kin yi waya da Baffa?"
Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a tana sake jan idanunta wajan lumshe su. Diyanah ta kama hannunta suna ƙoƙarin fita aka yi knocking cak suka tsaya. "Assalamu alaikum" a tare suka amsa sallamar. Ya ɗora da "Ina neman izinin shigowa wajanku" Diynaah na shirin tambayar waye Nadiyaah ta rigata da faɗin "Khālī Al'ameen, Mu'allim"
"Bisimillah..." Ya buɗe ƙofa ya shigo. Gabaɗaya suka miƙa masa hannunsu alamar musabaha suka gaisa ya ce "Baffa fa?" Nadiyaah ce ta ce "Ya dawo ne? Ban ji Ƙamshinsa ba, jikina bai bani Baffa am yana kusa damu ba" Mu'allim ya girgiza kai ya ce "Bai dawo ba, ina tambayar ko kun san garin da yaje da'awa" Nadiyaah ta ce
"Ask Ukhty Diyanah" tana faɗin hakan ta fita. Diyanah ta ce
"Ban san sunan garin ba, amma dai garin babu sauƙi suna da wahalar sha'ani ya ce, koyaushe za'a iya jin dawowarsa a wayar da mukai dashi jiya" sai ta ɗan ɓata fuska kuma ta ce "Wait, meye ne kake nemansa har haka?" Mu'allim ya harareta kafin ya ce "kuɗin aure zai kai mini ne in sha Allah"
"Oh really?"
"Yeah.... In sha Allah"
"Allahumma barik, wace matar her name?"
"Ban san sunanta ba for now"
Da rashin fahimta Diyanah ta ce "Are you kidding me? Taya hakan zai faru?" Ya ɓata fuska ya ce "Ƙaddara. Yarinyar tana kitchen ɗinku, please ki sama mini sunanta da number waya har ma da address me gabaɗaya nake so a yi, rana ɗaya za'ayi bikinmu da Akhy Liman" sai Diyanah ta rage tafiya kaɗan ba tare data ce komai ba suka sauka ƙasa. Gidan babu hayaniya sanda suka sakko Mamy bata nan sai Nadiyaah da Azizah wacce take ta yi wa Nadiyaah magana tana amsata jifa-jifa yaran basa shiri da Azizah tunda suka ji ita zata auri Baffansu, suna ganin kamar age mate suke da Azizah a nasu tunanin,kuma bata dace da Baffa ba, infact basa buƙatar Baffansu ya yi aure idan akwai abin da Nadiyaah da Diyanah suka tsana suke yin kuka a kan shi sosai da kwanciya ciwo, su ji ance Baffa am ɗinsu zai yi aure, wani irin mugun son shi suke yi da kishinsa mai tsanani, kishin da ya kamata ace murgayiya mahaifiyarsu ita za ta yi wannan kishin, sai ta tafi ta bar musu suke damawa. Suna ganin abin kunya ne a gare su ace Baffa am ɗinsu ya yi mata kuma har ta haifi baby, ta haifi little sis or brother. Basu da sani da cewa, shi Baffa da kan shi baya ra'ayin auren, uwa uba bashi da lafiya ta kasance da mace a dalilin hatsarin da ya taɓa yi shekarun baya. Baya jin feelings na kowacce mace, kamar yadda bai taɓa ganin kyawun ko wacce ɗiya mace a idanunsa ba, babu wata mace data taɓa burge shi a rayuwa.
Diyanah ko Azizah bata kalla ba ta shige Kitchen tana shiga aroma ɗin girki na shiga hancinta, ta ƙarasa idanunta akan Iftihal ta ce "sannu da aiki sister?" Cikin sauri Iftihal ta durƙusa ta ce "Barka da yamma" sosai Diyanah ta ji rashin jin daɗi ta ɗagota ta ce
"Ki bar durƙusawa babu kyau. Sunana Diyanah Sayyadi Baffa. Kefa?" Ta ce
"Iftihal, sunana Iftihal"
"Ma sha Allah. Kin kammala ne?" Iftihal ta ce
"Eh Anty"
"Who's Anty abeg? Call me by my name" zuba mana abincin a babban plate with 2 spoon me and Nadiyaah than you, Nadia bata cin abinci da spoon irin Baffa am ce "A'a nikam Allahamdulillah, bari na zuba muku" Diyanah gefe kawai ta koma ta zubawa fuskar Iftihal ido, bakyau ne ke bata mamaki ba, itama kyau gadon nasu gidanne, amma ta rasa me take kallo a fuskar Iftihal. "Kina wacce unguwa ne?" A hankali ta ce "Kankarofi" sai Diyanah ta buɗe ido ta ce "Ya rabb, tun daga can sannu sister. Give me your number so that muke gaisawa lokaci zuwa lokaci" murmushin da ake kira da yaƙe kawai Iftihal ta yi ta ce "Bani da waya, sai dai ya yayana idan kina so" wani irin rashin jin daɗi ya wanzu a zuciyar Diyanah ta ce "Ba damuwa saka mini" wayarta ƙirara iPhone 15 ta miƙawa Iftihal ta ce "Saka mini number tasa, ki kira yanzu ki faɗa masa sunana ya yi saving" Bayan ta saka number Yaa Jaheed nan take kira, abinka da talaka wanda yake nema ya ɗauka customer ne tuni ya ɗauki kiran ya ce "Hello...." A hankali muryarsa ta sauka a kunnen Diyanah ta yi shiru tana saurare.
"Yaa Jaheed ni ce Iftihal"
"Masoyiyyar" ta ce "Na'am"
"Kina ina? Wayar wacece wannan kika kira da ita?"
"Wani gida Yaa Jaheed ka yi saving number nan ka ji" ta cikin wayar ya ce "Bangane ba, number wanne ƙaton kika samu da za ki ce na yi saving? Ya sunansa Tanimu ko? Wayar ma na san rakani kashi ce yasin, to ba zan saka number nan a Vivo ta me capacity ba" Murmushi kawai Diyanah ta yi, Iftihal kuma ciro wayar ta yi a kunnenta tana jujjuyawa ta kalli Diyanah ta ce
"Ya sunanta?'
"IPhone 15"
"Kan uba IPhone 15, masoyiya wayar waye wannan maza bashi a barsa kar ki fasa ki ja mana masifa muna lallaɓa rayuwarmu" a hankali ta ce "In sha Allah. Ka yi saving ka saka Diynaah" a fili ya ce "Wow, sunan larabawa ne, Diynaah wa kar Innti taga number ta ɗauka lalacewa na yi na fara kula ƴan'matan Kano" Diynaah ce ta amshi wayar ta ce "Ahky Jaheed ka saka Diynaah Sayyadi Baffa" ji ya yi komai nasa ya tsaya cak, Sayyadi Baffa kamar fa babban malamin da ake tutiya dashi a Kano da Nigeria bakiɗaya.
"To. In sha Allah" ya amsa a saɓule yana kashe kiran. Aka ce da Iftihal ko ta bar abincin za'a iya a sarar shi ta tabi dashi gida, da farko taƙi amma data tuna yanayin gidan sai ta tattara abincin da nama fal da kayan fruits. Lokacin ana kiran sallar issha ne, sai da ta yi sallah kafin nan. Da ƙyar Mamy ta lallaɓa Iftihal akan Mu'alim ya kawo ta gida.
*
Tunda suka dawo gida Engineer yake ta jera mata sannu, ita kuma sai langwaɓe masa take yi da kukan shagwaɓa. "Kin gani ko baby? Ai na faɗa babu inda ba'a san Golden voice ba a faɗin Kano, ina da tabbacin sai kin zama babbar ƴar jaridar da za'ayi ko yi da ita wacce zata shiga kundin tarihi kuma ta zama abar tunawa. Wannan ma ɗaukaka ce kuma ta ɓangarena ba zan bari abin da akai miki ya tafi a banza ba, tunda naga gidan rediyon taku ba ta yi yunƙurin komai ba" Ahlam ta ce "Abban Mufeed, ni wannan abin ya yi mini daɗi duk da ya cuce ni daya ɓare mini baki gida biyu ai daya cuce ni ya cuci masu ƙauna ta wallahi" Engineer ya ce
"Kuma da ya cuci mijinki ma" sai ta yi saurin sauya maganar da faɗin. "Zan koma gidan matar na yi hira da ita, zan ɗora hirar a wani sabon program ɗinmu na MU FARKA MATA" cikin jin daɗi da nuna goyon baya ya ce
"A'a ka da ki koma gidan nan baby, haka kawai su danne mini ke su yanka na shiga uku" ta ɗan murmusa kaɗan ta ce "Uhm"
"Be careful my love ok?"
"By the grace of God"
Miƙewa ta yi ta musu sai da safe ya shige ɗakinta, wayarta ta ɗakko ta kunna cikin sa'a tana shiga WhatsApp taga Nurse ɗin ta tura mata vedion, kai tsaye ta shiga Facebook ta yi positng vedion da caption ɗin. "Beging a Journalist isn't easy" cikin ƙaramin lokaci ta tara comments ɗin mutane sama da dubu biyu wanda kusan duka rabinsa jaje suke yi mata da ƙara mata ƙarfin zuciya da confidence, bata taɓa tunanin haka aka santa a social media ba sai yau ɗin nan. Ta shiga tambayar kanta kenan muryarta bata tafi a banza ba? Kenan duk ƙoƙarin da take yi bai shuɗe a banza ba, sannu a hankali take jin nutsuwa na sauka a zuciyarta, nutsuwar data haɗo mata da wani wish and hope, suka cure waje guda tare da zama big dream ɗinta na rayuwa, hakan ya sake tunatar mata da burinta na ɗaukaka a duniyar aikin jarida, ba zata taɓa manta wulaƙanci da cin mutumcin da Yussy ta yi mata. Ko kalaman data jefe ta dasu bata buƙatar tunawa, balle ita kanta Yussy ɗin. Sai dai me? Abin ya zame mata kamar yadda a duk sanda ta runtse idanunta ko kuma tazo kwanciya bacci sai maganganun sun dawo cikin kanta, sun maimaita kan su.
Hakan ɗin ce ta kasance a yanzu ma, ji ta yi kamar a daidai wannan lokacin ne komai ke faruwa tsakaninta da Yussy muryarta ta ji tana sauka a kunnenta. "Ai Ahlam ko za ki ƙarar da duk abin da kika mallaka ba za ki taɓa bin layin dana bi ba, balle ki huce ni. Na ba ki shawara ba ki ɗauka ba, zan sake ba ki a yanzu wataƙila ki yi aiki da ita zuwa gaba sai ki gode mini" a wancan lokacin Ahlam na tsaye fitowar ta kenan daga office ɗin Editor-in-chief taje kai masa wani labari data samu akan hanyarta ta zuwa gidan rediyon, lokacin tana matsayin News Gatherer, sai ya nuna labarin bai yi ba, ba balle ya samu ƙarbuwa ba. A lokacin har kuka ta kusa yi saboda baƙinciki labarin wani dattijo ne da ya yi wa yarinya ƴar 3 years fyaɗe, amma saboda bata ɗauki rahoton murya ba ya yi watsi da ita. "Sir wallahi yanzu labarin nan ya faru babu wata gidan jarida da suka wallafa ko gidan rediyon da suka sanar, Bright Fm ce zata zama ta farko ka yarda dani akan idanuna aka kama dattijon" wani kallo ya yi mata irin na bata isa ba, yaushe ma ta shigo aikin?
"Look Ahlam, bawai da ka muke watsa labarai ba, abu muke na ilimi wanda mutane za su yarda dashi. Idan muka yi saken da aka saka wannan labarin mutane da yawa za su daina sauranmu" cikin rawar murya ta ce "Sir don me ya sa za su daina?" A taƙaice ya ce
"Saboda ƙarya ce tsantsa a rahoton naki" Jiki a saɓule ta miƙe tare da ficewa daga cikin ofis ɗin, hawayen daya ciki idanunta ya tilasta mata tsayawa a wajan tana share su da shanyayyen hannunta, a daidai lokacin ne kuma ta ji sautin dariyar Yussy shine ta ɗora da wancan maganar ta sake faɗin. "Ki koma ki nemi tabarma da roba ki fara zaman bakin titi Ahlam, trust me za ki samu sadaƙa sosai. Nakasassu basu da wata sana'a ai bayan wannan. Amma kinga aikin jarida?" Sai ta yi shiru tana cije lips ɗinta da kallon Ahlam na wani lokacin. "Za ki ji fa kamar muguwar shawara nake ba ki, ki saka a zuciyarki ni me son ki ce, idan kuma kika tilasta a wannan sabgar to haƙarki ba zata taɓa cimma ruwa ba, babu inda za ki je a aikin jarida, ki duba kamar haka.....,"
Ta nuna ofis ɗin da Ahlam ta fito, tare da nuna rahotannin da suke hannunta ta ce
"Haka ce zata dinga faruwa dake daga nan har a kore ki daga aikin jarida wallahi"
Wani irin murmushi Ahlam ta saki bayan ta gama goge hawayen kallon sama da ƙasa ta yi wa Yussy ta ce "Ashe kina tara sani da Allah Yussy, ashe kin san me gobe zata haifar ko?" Cikin sauri Yussy ta ce "Ke kam gobenki ai ta jima da bayyana a idanun jama'a" A wannan karan ma murmushi Ahlam ta yi ba ta ce komai ba ta yi gaba.Har ta tafi ta ɗan tsaya ta ce
"Yussy ki rubuta ki ajjiye in sha Allah muryar Ahlam sai ta kare duniya ba iya jihar nan ba, ba iya ƙasar nan ba, duniya gabaɗaya. Na yi miki alƙawarin sai muryar Ahlam ta hanaki bacci Yussy, idan kin shirya na shirya shege ka fasa" tana faɗin hakan ta yi gaba abinta.
*Ajjiyar zuciya Ahlam ta sauke bayan ta gama tuna kaɗan daga cikin wulaƙancin da Yussy take ba, ta dubi hannunta dake maƙale a fili ta ce "Kai ina, Impossible wannan hannun ba zai taɓa hanani cimma burina ba" duk abin da zai faru tana buƙatar samun Outstanding Journalist Award. Sai ta fara tunanin wanne irin abu za ta yi in few days da zai saka ta samu wannan Award ɗin? Ta runtse idanunta ta sake buɗe su.
"Think Think.....
"Ahlam think"
Wayarta ta ɗakko ta kira Anees tasan yana da night duty bai yi bacci ba yanzu ba. Bayan ya ɗaga kiran ta cikin wayar ya ce "Baby ya jikin naki?" Da nutsuwarta ta ce
"Da sauƙi"
"Ma sha Allah. Akwai wani abu ne?" Ta sauke ajjiyar zuciya
"Anees"
Calmly ya ce "Na'am"
"Kana ganin idan na yi Interview da Sayyadi Baffa zan iya samun karramawa ta musamman?" Anees ya yi shiru domin a bazata ya ji maganar tata. "Ka yi shiru"
Ya ce "Wa kika ce baby?"
"Sayyadi Baffa"
Wani ƙarfaffan numfashi yaja a ƙirji ya fesar mata dashi ta cikin wayar, da ƙyar ya ce "Kin taɓa ganinsa ne? Kina da hanyar da za ki ganshi har ki yi Interview dashi? Hakan ba mai yiyuwa bane baby, ki sauya idea ba za ki taɓa samun dabar yin hira da Sayyadi Baffa ba" jikinta na wani irin rawa da ɓari cikin karyewar murya kamar za ta yi kuka ta ce "Don me ya sa? Shi ɗin ba mutum bane?"
Anees ya ce "Of course mutum ne, amma ba gamagarin mutum ba, to cut the conversation short da ace hira da Sayyadi Baffa abu ne me sauƙi to da tuni Bright Fm ta yi hakan. Daga nan jiharmu da ƙasar babu wata gidan jarida daya taɓa yin hira dashi wallahi Allah, mutumin da ko ganinsa ba'a taɓa yi ba, saboda taka tsantsan irin nasa" shiru Ahlam ta yi domin ita Sayyadi Baffa shine target ɗinta akan shi ta ɗora duka hope ɗinta. A hankali ta ce "Amma Anees mene dabarar hakan da yake ɓoye kan shi? Na ji ance kamar yana da raya ko?"
"Nima a haka na ji wai yana tagwayen yara amma babu tabbaci, domin babu wanda ya taɓa ganinsu. Kin ɓaro aiki babba baby"
"Uhmmm" ya ji taja numfashi ya yi saurin lumshe idanunsa yana sosa ƙirjinsa a nutse
"Trust me Anees zan yi shira da Sayyadi Baffa, zan zama ta farko zan ɗaga Bright Fm da hirata da Sayyadi Baffa ka yi mini addu'a"
"Best of luck baby, ki yi a hankali kuma"
"I will.... Definitely"
Ta sake cewa "Anees, I'll make my words"
"Idan ya tabbata haka ne daga Bright Fm za ki shige Special training opportunity NIJ Lagos, kina kammala sai BBC yin attachment" idanunta ya cicciko da hawaye cikin rawar murya ta ce "da har abada bani da bakin yi wa Ubangiji godiya daya ƙaddara mini cikar burina ina raye ina kallo, maƙiyana za su kalli ɗaukakata babu yadda suka iya, Anees bani da burin daya shige na ganni a BBC ko VOA" cikin ƙasa da murya ya ce
"Za ki cika burinki da yardar Allah baby" Ta ce
"Allah Ya sa. Good night"
"I love you... I so much love you Ahlam"
Ƙit ya ji ta kashe wayar ya yi murmushi yana ajjiye wayar shima. A hankali kuma ta shiga tunanin kalmar Tiv dake mata yawo a cikin kanta da zuciya.
**Tana tsaye a harabar masarautar jikinta sanye da wani ƙyalle da kuma wasu ganye manya, manyan mutane maza da mata sun kewaye ta suna mata kirari da kuka tare da roƙo da magiya, ga wani kaɗe-kaɗe da suke yi. Da rawar ɗari ta ce "Su waye ku? Me kuke buƙata a wajena, ina ne nan waye kawo ni nan wajan" ta shiga tambayar su, da alama basa jin hausa koma suna ji alamun hakan bai nuna a tattare dasu ba, ita sai taga kamar ma naman mutane suke ci. Wani daga cikinsu ne ya zube a ƙasa daidai ƙafafuwansa ya ce "Kakanninmu sun shuɗe suna zaman jiranki, Iyayenmu sun tafi da baƙinciki rashin ganinki, mun rasa rayuka da dama saboda ƙin bayyanarki, mun rasa dukiya mun rasa ƙarfi da iko, mun shiga cikin fushin Akombo. Ki cece mu MAMA ki dawo mana da kima da martabar TAJMAHAR, kece UWA MAMA a gare mu"
A kiɗime ta yi baya ta ce "Wallahi bani bace, ni ban san wata uwa mama ba, sunana Ahlam ku rabu dani bani bace wallahi" ihu da kuma kawai take yi
"Subuhanallahi baby ke da waye haka?"
Engineer ya shigo cikin ɗakin da gudu yana riƙe ta ganin yadda take fusge fusge tana cewa ba ita bace ihunta ya cika gidan nasu.
"Abban Mufeed anya ba za'a haƙura da aikin nan na Ahlam ba, mijinta me rufin asiri ne zai iya kulawa da ita, na fara jin tsoro gaskiya" girgiza kai Engineer ya yi yana rungume da Ahlam tare da tofa mata addu'a yana jin yadda ta ƙanƙame shi kamar ance za'a ƙwace ta daga wajansa sai numfashi da ajjiyar zuciya take saukewa.
"Sannu kakata, tsofan ne ya motsa?" Da ƙyar ta yi maganar saboda wani abu daya tsaya mata ganin yadda Abban Mufeed ya rungume Ahlam. Ahlam ta ce
"Tsoro nake ji Anty Jiddah"
"Baby ko za ki haƙura da aikin nan?" Engineer ya ce "Hawwa'u Ubangiji baya jarabtar bawa sai ace yabar abu? Sakaci ne irin na yaran zamani wataƙila haka ta kwanta babu alwala balle addu'a ba dole mutum ya dinga mugwayen mafarkai ba" ya duba lokaci ya ce "Zan tafi masallaci kar na makara ki tashi ki yi alwala ki tabbata kin yi lafila tare da azkar" Anty Jiddah ta ce
"Baka jin firgitar da na yi ba, har cikina ne ya juya na ɗauka ko biyota aka yi har gida" Bayan mijinta tabi suka fita a tare Ahlam ta yi shiru tana tuna mafarkin da ta yi.
*
Sanda Mu'alim ya sauke Iftihal akan corner ɗin unguwarsu bata jira sun yi magana ba, shi ɗinma da yake ƙoƙarin cewa wani abu sai ya samu rashin kuzarin tanka ta, ya fahimci tsoro da firgici a tattare da yarinya, bai san dalili ba, kamar yadda bai san wani abu na musamman da ya fusgi ra'ayinsa akan ta, ya ji ta yi masa, ya kuma gamsu ta yi ɗin, ya ji ta cancanci ta zama Mrs Al'ameen Hafizz Baffa, mata a wajan Mu'alim. Kamar ma bata taɓa shiga mota irin wannan ba idan ka ɗauke batun napep yana kallon yadda take takawa a hankali har ya isa corner. A hankali ya sauke gilashin motarsa ya ɗan leƙa, shi kamar ji ya yi ta ce "My Mu'alim" daidai lokacin itama ta juyo suka haɗa idanu sai ya jinjina mata kai alamar ta shige ciki.
Ashe dai kiran nasa ta yi, ba kira na baki ba, kira dake tsakanin zuciya da zuciya. Ya ɗauki lokaci kafin ya iya kunna motar ya yi reverse ya bar Kankarofin gabaɗaya ya nufi Maitama Sule, da zumuɗin ƙara ganinta.
Kamar mara gaskiya haka Iftihal ta shiga gidan nasu da sallama suka amsa mata, a cikin muryoyin da ta ji babu ta mahaɗinta cikin damuwa ta shiga rarraba idanu ta kalli Innti ta ce "Ina mahaɗita Innti?" A sanyaye ta ce
"Tana ciki, sai yanzu Iftihal?"
"E, ya gida Sahibarmu? Ya aiki da jikin mahaɗita?" Innti ce ta miƙa hannunta wajan riƙo hannun Iftihal ta zaunar da ita kusa da ita ta ce "Ita kam da sauƙi naga, Yaa Jadid ne jikin nasa sai godiyar Ubangiji, wankin ƙoda yake buƙata, babu kuɗi wajena na kuma rasa mafita da abin yi, ɗazo ma jikin tsoro ya bani, ganin yarona na sha wahala ga abu bane me sauƙi da zuciyata zata jure"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Iftihal ta faɗa tana runtse idanunta, another banger, another problem. Su kam me rayuwa take nufi da tasu rayuwar ne. A hankali ta ce "Innti kuɗin dashi, ki ari kuɗin dashin mana tunda daman Baba Bala za ki bawa ɗauka, zai yi miki lamunin rance zuwa ki samu ko?" Innti ta yi shiru domin bata son tace an sace kuɗin, babu ɓarawo a yaranta kai tsaye za su ce Daada ne
"Rabani da Bala ɗiyar arziƙi, Bala fa? Tabɗim" Iftihal ta zubawa Yaa Jadid dake kwance idanu kan shi a kan cinyar Innti tana masa addu'a da firfita da mafici. Da rawar muryar sosai jikinta na rawa Iftihal ta ce
"Ko za ki siyar da kan kekenki sai a nemi ciko?"
"Wanne keken? Kan nan ko dubu goma ba zai yi ba, asara ce siyar dashi, kuma dashi nake amfani me hamsin ɗari ina mana abin da ya sawwaƙe na kai wa baka, ga mai atamfar can da ɗinkin ya lalace tana ta sintiri na rasa mene ya lalata ɗinkin lafiya ƙalau na kammala" Iftihal ta fashe da wani irin kuka jikinta na rawa ta kasa cewa komai, Yaa Jaheed ma shirun ya yi yana lissafin rayuwa da inda zai iya samu kuɗi akai ɗan'uwan nasa asibiti, duk inda ya yi tunani sai yaga a rufe hanyar take babu sauƙi ko kaɗan a lamarin. Hatta ogansa na wajan aiki ya tambaya yace babu kuɗi a wajansa
A daidai wannan lokacin kuma Ana ce a cikin ɗaki zaune ta rungume hannayenta a ƙirji idanunta rufe, sai ka ɗauka bata da rai sannu a hankali ƙirjin nata ke ɗagawa. Tunani take yi ita da zuciyarta, wacce hanya za ta bi wajan ƙwatuwa Innti haƙƙinta, da matsayinta? Wanni littafi da Zainab Alƙali ta karanta ne ya faɗo mata, ta tuna yadda matar takai mijinta ƙara ofishin ƴan Hisba, har aka hukunta mijin akan kuskuren da ya yi, hukunci irin wanda Shari'a ta tanata. A fili ta ce
"Ina ne ofishin ƴan Hisba a nan? Ina zan samu kuɗin mota?" Ita kam ko a ƙafa ne zata iya zuwa muddin zata samu ganin jama'an hisbar.
Sallama ake ta rafkawa a ƙofar gidan sai Babban yaya wanda yanzu ya shigo ya miƙe domin ganin waye, yana fita ya yi turus ganin Alhaji Baita, kallo ɗaya ya yi masa ya kawar da kai, ba ɗabi'ar zuri'ar Innti bace raina na gaba don haka a ladabce ya gai da Alhaji Baita cikin kamilalliyar muryarsa wacce sai a lokacin Baita ya taɓa jinta. "Yawwa nace ina Ayshatul-Iftihal ɗin? Na biyo sawu ne na gaza haƙuri naga har war haka ba'a kawo ta gidana ba, kamar yadda muka yi da Daada"
Da rashin fahimta Babban yaya ya juya idanunsa alamar "Wacce Aysha? Wanne gidan kuma?"
A fusace Baita ya ce "kai bana son shiririta uban naku bai baku labarin ya saka Iftihal a caca ba, kuma nine wanda na yi nasara, idan baka da labari yanzu ina baka, akan naira miliyan ashirin ya saka Iftihal a caca, kuma nine wanda ya yi nasara na riƙe kuɗaɗena, kuma na ci yarinya. Ka shiga ka fito mini da ita yanzu mu shige, tun safe nake jiƙe-jiƙe a takure nake ta ciki, banda yayyu babu abin da nake yi. Yau ranar hutawa ta ce Allah ya kashe ya kuma bani"
Babban yaya ji ya yi komai ya tsaya masa ya kuma daina fahimta, ya kalli Alhaji Baita sama da ƙasa, iya haƙorinsa kaɗai tayar masa da zuciya yake yi, ga cikinsa kamar an yi masa ajjiyar yara goma, ko kuma wanda mayu sukai masa ajjiya. "Yanzu ita Iftihal kaza ɗauka?" Haka kallon Yaya ya bawa Alhaji Baita raddi. Alhaji Baita ya ce "A rubuce wannan take"
Sai ya yi baya kaɗan ya jinjina kai alamar "Tana ciki, jeka ɗauke ta" abu kamar wasa yaga Alhaji Baita yana ƙoƙarin shigewa cikin gidan da sauri ya saka hannunsa ya tura shi baya da wata kakkausar muryar data motsa zuciyar Baita saboda kwarjinin da take dashi ya ce "Ashe girman biredi ne kawai da kai, baka da saiti har haka? Bari na faɗa maka gaskiya, yadda kukai cacarku babu wanda ya sani haka yanzu zaku ƙare ta iya ku. Muddin ina numfashi kuma ɗan halak ne ni wallahi Iftihal ta haramta a gare ka, ni kaina da kake ganina ɗan wahala ne ni, rashin sanin waye ni zai saka ka yi maganar nan....," bai ƙarasa faɗa ba ya ji an ɗauke shi da mari, kafin Babba yaya ya dawo hayyacinsa cike da ƙonar rai Yaa Jaheed ya wankawa Alhaji Baita mari, ya rama marin da Daada ya yi wa Babban yaya, da gudu kuma ya arce cikin gidan.
Alhaji Baita ya kalli Daada ya ce "Ashe yaranka basu da tarbiyya?" Daada ya ce "Ina suka ganta daman? Ko wani ya faɗa maka suna da ita?" Sai ya juya kan Babban yaya ya ce "Kai kuma muddin kai ba ɗan shege bane, bada cikinka uwarka ta shigo gidana ba, ka yi gigin hana shi tafiya da ita mu gani, sakarai wawa tasono hanci duk majina, kana tafiya kamar mace lusari. Ai tunda ka fito daga cikin Innti babu yadda za'ayi ka zama wani abu a rayuwa, babu yadda za'ayi ka yi nasara a rayuwa sai ka lalace ka zama annoba wa jama'a, dukkaku lalatattu ne billahi" saboda tsananin ɓacin rai idanun Babban yaya har wani rawa suke bayan firfitowa waje da sukai jijiyoyin kan shi suka mimmiƙe, sai yanayinsa ya fara sauya da sauri ya fice daga cikin gidan gabaɗaya.
Daada ya kalli Baita ya ce "Jira na fito da ita"
A can cikin gidan kuma bayan Yaa Jaheed ya shiga a guje bai iya tsayawa a wajansu ba, ɗaki ya shige kai tsaye ya rufe ya fashe da wani irin matsanancin kuka, wai Iftihal aka saka a caca? Har lusari bagidajen mutumin na iƙirarin zai huta da ita. Ji yake yi kamar ya haɗiye zuciya ya huta.
"Sannu ƙaunata ba dai jikin bane ko?"
Cewar Iftihal tana kallon Ana.
A hankali ta lumshe idanunta cikin sanyin murya ta ce "Yaa Sam ya ce zai zo kuma shiru" murmushi Iftihal ta yi kafin ta ce "Allah dai ya nuna mana wannan rana"
Da rashin fahimta ta juya idanunta ta ce "Heee, wacce rana?" Harara Iftihal ta watsa mata kafin ta ce "Kinga wacce na yi aiki a gidansu yau" ta nunawa Ana picture ɗin Nadiyaah da Diyanah ta yi status dashi, a tunaninta Diyanah ɗince. Ana ta zubawa photon Nadiyaah idanu musamman idanunta a hankali ta ce "Idanunta manya masu kyau dasu" sai kuma ta taɓe bakinta.
Iftihal itama zubawa idanun ido ta yi a fili ta ce "Tubarakallah ma sha Allah kam dasu"
"Kina ina fito don uwarki wannan mara amfanin a duniya, wannan wacce ta yi asarar haihuwa duniya da lahira wannan mara rabon, sai kun farraƙa in sha Allah" muryarsa kaɗai tsayar da numfashin Innti da yaranta yake idan ka ɗauke Ana da Babban yaya. Wani irin masifar tsoron Daada suke yi kamar sun ga mala'ika.
Jikin Iftihal na rawa ta miƙe tsaye, ana kam ko motsi ba ta yi ba, domin hargagin zautaccen mutumin nan ya daina zama damuwarta. Ɗaki Daada ya shige yana sababi. Ana ta kalli Iftihal sosai ta ce
"Wai meye kike rawar ɗari, kifa daina saka damuwar bugaggen mutumin nan akan ki. Wallahi idan ba haka ba, watarana sai ya zama ajalinki sai ya kashe ki da baƙinciki ya rabaki da duniya. I'm telling you ki share shi" Da wani irin ƙarfi da firgitacciyar murya Iftihal ta ce "Mahaɗita na shiga uku, a caca Daada ya saka ni, yanzu haka gidan Alhaji Baita zai kai ni, ni Daada ya saka a caca kuma an yi nasara akan shi. Ya hanamu zuwa makaranta a sanda zamu rubuta jarrabawa ta shiga SS1. Burinmu ya rushe Ana, mafarkanmu sun zama tarihi Ana, ba zan taɓa zama ƴar jarida ba, ba za ki taɓa zama marubuciya ba. Ya ce zai tsine mana idan muka je makaranta ko a bayan idanunsa ne" zumbur Ana ta miƙe jikinta duka rawa da ɓari yake idanunta na lumshewa yana ƙaƙƙafewa numfashinta na ƙoƙarin tsayawa ta futar da kalmar bakinta a wahalce
"Kan uba, uban kuturu ya yi kaɗan balle na makaho, wallahi bai isa ya hanani zuwa....,"
Kafin ta ƙarasa Innti ta saka bayan hannunta ta make mata baki, nan take leɓenta na ƙasa ya fashe, da wani irin yanayi na sarewa da macewar zuciya daga abin da take so Ana ta ce "Innti duka?
"Me ya sa bakya so na ne Innti......" Ta kasa ƙarasawa
"Saboda mijinki kike wannan?"
Jajur haka idanun Innti ya yi gashi sun ƙanƙance tare da shigewa ciki tana wani irin haki da dafe ƙirji ta ce "Saboda duk abin da zuciya ta raya miki ne Nanaah, wallahi akan idanuna ko bayansa, ina duniya ko bana duniya kika bijirewa Daada, ki kai rashin biyayya a gare shi ban yafe ba, ban yafe muku ba duka. Mahaifinku ne yana da iko da hakan, duk abin da ya zartar akan ki ya zartu babu haufi. Mene don ya saka Iftihal a caca? Haka tunaninsa da lissafinsa ya bashi, hakan yake ganin shine dai-dai. Idan ƙaddararta ce hakan babu yadda za mu yi sai dai mu yi mata addu'a Ubangiji ya bata haƙuri da juriya ya sanya mata salama ko?" Cike da takaici da baƙincikin da ya yi mata yawa a zuciya take faɗin hakan
"A'a.... A'a Innti" Iftihal ta ce tana ƙanƙame jikinta da rusa wani irin firgitaccen kuka ta ce "Ba ruwan ƙaddara, idan ma akwai ta, Daada ne ya zaɓa mini wannan muguwar ƙaddarar da kan shi. Don Allah kar ki bari ya tafi dani, Innti ke uwa ce kin san ɗaci da raɗaɗin hakan, kin san zafin dake cikinsa. Wallahi idan Daada ya tilasta zuciyata zata iya bugawa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku, ki taimaka mini Sahibata"
Ana ma fashewa da kuka ta yi taje ta rungume Iftihal ta sumbaci goshinta da kuncinta ta riƙo hannayenta ta sumbata. "I promise you in dai ina raye babu inda za ki, idan dole sai kin je zani a madadinki, za'a maye gurbina dake, ki zauna da Innti ko ƙaddarar ce ni na shirya mata, ni na amshi ƙaddarar" kuka suke yi sosai sun ƙanƙame juna. Innti sulale wa ta yi a wajan, ta kasa fitar da hawaye balle kuka ta yi hooking ma gabaɗaya bata sam meke yi mata daɗi ba, bata hayyacinta balle ta lura da suman da Yaa Jadid yake yi.
Daidai ne Daada ya fito suna ganinsa suka ƙanƙame juna, Ana ta dafe hannun Iftihal ta ce "Daada zani a madadin Mahaɗita zan bika" kallon tsaf ya yi mata sai ya ce
"muje"
Ya miƙa mata hannunsa, hannun ta kalla sai ta miƙa nata zata ɗora akan nasa kenan ya cafke hannun ya fito da sabuwar reza ya kama tafin hannunta ya shiga tsaka hannun, wani ihu Iftihal ta kurma, ihun daya dawo da Innti daga hayyacinta ta miƙe ta ce
"Daada! Mene haka ka sakar mini ƴata"
"Kina matsowa a bakin aurenki wallahi"
Cak ta tsaya, ta zubawa jinin da yake tsiyaya daga hannun Ana yana sauka a ƙasa, Ana ko motsi ta kasa kamar yadda ko tari ta kasa, ta kafe Daada da manyan Idanunta, sai daya kammala rubuta sunan Daada a tafin hannunta sannan ya fusgeta ya cillata a wani ɗaki me masifar duhu ya rufe ya saka ɗan makulin a alijuhu da ƙarfin gaske kuma ya shiga jan Iftihal tana tirjewa haka ya jata har ƙofar gida inda Alhji Baita yake tsaye yana sake shanye haɗin tsumin da ya yi, duk da wannan robar ya sha kusan roba goma ta tsumin maza. "Gata riƙe ta ku tafi" Daada ya ce yana tura Iftihal waje yaja ƙofa ya rufe....
A cikin tafiyar HIYAAM ba'a fara komai ba, tafiya ce miƙaƙƙiyya me cike da sarƙaƙiyya, ayi kuka ayi dariya. Kasancewa dani a Arewapen kodayaushe shine zai dinga bani ƙwarin gwiwar yi muku positng sau biyu a rana. Ku faɗi ra'ayinku, ku yi mini liking a littafin ku yi following account ɗina.