Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 1

by @mamanafrah3028

Kwance take a jikin sa ta yi lifet tamkar mage, bacci suke mai cike da farin ciki Saddiqa da Aminu kenan ango da amaryar da suka tare a daren jiya. Cikin baccin nata ta ji wani uban wari ya baibaye hancin ta, kasa jurewa ta yi ta ɗan fara juye-juye jim kaɗan dai ta ji warin ya ƙaru tamkar an saka hancin ta a ɗakin da mushe yake a ciki. A ɗan gigice ta tashi zaune ita gabaɗaya yanayin warin ma ya sa ta manta cewa ita fa amaya ce kuma tare da ango suke kwance.

Da yake bata wartsake ba sai ta yi zaton a gidan su ne da yake a gidan su katifa ɗaya suke kwana da ƙanwar ta Noor hannu ta kai ta ɗakawa angon duka a baya duk tunanin ta Noor ce, tana ɗaga dukan ta buɗe bargon da sauri ta fito cikin sauri ta sakko daga kan gadon ta fito daga ɗakin don gabaɗaya warin ya hautsina mata ciki har wani ɗaci take ji a maƙoshin ta. Ƙololon amai take yi don a lokacin da ta sakko da ta buɗe bargon ta ankara da a she fa a gidan ta take kusa da ango, kunyar dukan angon nata ce ta kamata sai dai yadda warin ya cika ɗakin ba za ta iya tsayawa ba, don lokacin da ta kai dukan ma sai da ya saki wata tusar.

Ango kuwa cikin bacci ya ji an ɗaɗa masa duka a baya, sakin tusar da ya yi ya yi daidai da tashin sa zaune sai dai da yake amarya tana buɗe bargon ta fita sai ya zamana shi kaɗai ne a cikin bargon, shi ma jin warin da ya cika cikin bargon sai ya buɗe ya fito yana shaƙar gurɓatacciyar iskar ɗakin don gabaɗaya ma ɗakin ya haɗe da warin.

Saddiqa tana gama ƙolon aman duk da bata amayo komai ba haka ta dawo falon ta zauna a kujera tana mamakin warin tusar nan don ta kasa komawa bedroom ɗin. Tana zaune sai ga Aminu ya fito daga ɗakin da yake tun fitowar ta ta kunna fitilar falon yana fitowa ya yi tsaye a tsakiyar falon hannu biyu ya ɗaga sama yana miƙa bakin nan hangame yana hamma cikin hamma yana salati.

"Baby!" Ta kira shi tana kallon sa. Kiran da ta masa shi ya katse masa hammar ya juyo kawai sai ta ji ya ce

"Haba Saddiqa sau nawa kike so na maimaita miki cewa na tsani sunan nan haba tun kafin mu yi aure na ce miki ni fa ba na sha'awar wannan sunayen yahudawan ina dalili ga sunan da aka yanka mini rago amma ake wani kira ni Baby kamar yaron goye" Ya faɗa yana dawowa kusa da ita ya zauna. Bai jira ta ce wani abu ba ya miƙo hannu zai rungumo ta ta ɗan moƙe.

"Haba Saddiqa sai ka ce wani ba mijin ki ba za ki kauce daga rungumar da na kawo miki?" Ya tambaya yana kallon ta da ɗan mamaki.

"Wai yanzu Bab....

"Wai ba na ce ba na son sunan ba na yahudawa ba za ki daina faɗa ba, uhmm ke mai sunana na Aminu ya miki ne da ba za kike faɗa ba" Ya faɗa yana ɗan kallon ta irin na lallashin nan.

"Yanzu don ina kiran ka da sunan soyayya shi ne yahudanci? Yanzu daga tarewa ta a gidan ka jiya har za ka fara ɓata mini rai ashe abin da ake faɗa na cewa zaman haƙuri ake yi ashe haka ɗin ne? Sai in ji ana cewa wuyar ta a yi auren daga an yi auren shikenan, wasu ma su ce auren ya yi ƙarko bai fi ya yi wata biyu ba za a fara ƙunsa maka baƙin ciki shi ne ni tun daga kwana ɗaya abubuwan da nake jin su ya wai za su fara bayyana a nawa zaman auren" Ta ƙarasa faɗa tamkar za ta yi kuka. Kallon ta ya yi sai kuma ya ɗan sasauta murya ba kamar yadda ya yi magana ɗazu ba ya ce.

"Ni fa ba wani abu ba na ce kawai sunan nan ne na ce bana so kuma kin san tun kan mu yi aure ina faɗa miki ba na son iri-iren waɗannan sunayen.

"Tashi mu je mu kwanta, muna baccin mu mai daɗi kika fito kika bar ni har da dukana a baya ko bakya so na yi baccin irin na angwaye?" Ya tambaya yana kallon ta. Murmushin yaƙe ta saki tana tunanin shin bai san mai ya yi ba har ta tashe sa ɗin.

"Wallahi Bab..." Shiru ta yi ta fasa faɗar sunan Baby da ya hana ta, ba don tana so ba don ita mace ce mai son soyayya da nuna kulawa ga masoyi.

"Wani wari ne fa ya tashe ni, na ji duka ɗakin ya ɗumame da wari" Ta faɗa cikin wayincewa don bata so ƙiri-ƙiri ta nuna masa cewa tusa ya yi.

"Ko dai ɓera ne ya mutu?" Ya yi furucin yana kallon ta. Kai ta girgiza alamar a'a.

"Ina ga fa nine na samu sacewar iska(Tusa) Ina cikin bacci ba tare sa na sani ba" Ya faɗa yana ƴar dariya don ya gano ta gane tusar ya yi tun da ga shi da ya ce ɓera ne ta girgiza kai. Idanu ta ɗaga tana kallon cikin idanun sa.

"Jiya ne a gida suka yi faten wake shi ne na cika cikina da shi kin san ina son faten wake" Ya faɗa.

Idanun ta ta rufe tare da buɗe su a kansa ta ce

"Ango da cin faten wake a ranar ɗaurin auren sa" Ta faɗa tana murmushi.

"Kin san an ce zuciya da abin da take so"

"Haka ne"

Hannun ta ya kama a cikin nasa tana jin wani son sa a ranta tabbas tana matuƙar ƙaunar Aminu hakan ne ya sa ya yi fice tare da yin zarra ga sauran maneman ta.

Tashi suka yi ya kashe fitilar falon tare da riƙo ta suka nufi ɗakin, zuwa lokacin warin ɗakin ya fita sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Komawa suka yi suka kwanta cikin ɗorawa da cin amarcin su.

Da asuba suka shiga bayin cikin ɗakin wanka suka yi, tana yin alwala sai ta ga zai fita daga bayin.

"Ya na ga za ka fita baka yi alwalar ba?" Ta jefa masa tambayar don dama ko jiya ma da za su yi wanka da daren ita ce ta ga bai ɗaura alwala ba zai yi wankan tsarki don kai ya fara wankewa sai da ta tambaya ya wayince yana ɗaura alwala kamar yadda ake alwalar sallah sai da ta ce masa kai da za ka yi ɗai-ɗai ma'ana kowace gaɓa sau ɗaya za ka wanke a maimakon alwalar da ake ta yin sallah wacce ake wanke kowace gaɓa sau uku. Haa dai ya ce wai mantawa ya yi saboda kansa yana ciwo na taron ɗaurin auren da aka yi shi ya sa ya sha'afa. Duk da wankan ma bai wanke ɓangaren dama da ban na hagu da ban ba, duka jikin ya shiga wankewa sai da ta nuna masa ya ce wai duk mantawa ya yi amma dai yanzu ta ga ya yi wankan tsarkin daidai.

"Au da fa wai sai na je na shirya in zan yi sallar sai na dawo na yi alwalar"

"Kawai ka yi kayan ka" Da to ya amsa mata ya dawo ya yi alwalar suka fito kayan sa na jiya da ya zo da shi wacce ta ga ita ce shaddar da ya saka da yamma da suka je da abokan sa aka yi hotuna.

Bata tanka masa ba ta ɗakko doguwar rigar ta saka ta shimfiɗa sallaya tare da ɗakko qur'ani ta ajiye a kan sallayar daga gefe.

"Ya kika shimfiɗa sallayar ɗaya?" Da mamaki ta ɗago tana kallon sa.

"Nawa zan shimfiɗa?" Ta tamabaye shi.

"Ni kuma fa? Kin san dai ai mace da namiji ba sa sallah a jere a sallaya ɗaya tun da dai nine zan mana limanci"

"Wai kana nufin a gida za ka yi sallah?"

"A ina zan yi to?"

"Haba dai!. Kana namiji mai zai haɗa ka da sallah a gida kuma, ga shi can ana shirin shiga masallaci, don na ji an buɗe ƙofar gida ɗazu ma wataƙila ƴan uwanka ne suka fita( Da yake gidan ɓangare uku ne, nasu sai na Yayan sa Shafi'u wanda yake zaune da matar sa Sumayya da ƴarsa Ruma, sai kuma ɗaya Yayan nasa Sule da matar sa Amina, suna da yara biyu Yusuf, da Albani).

"Yo ni ba ango ba ne"

"Shi ango ba zai yi sallah a jam'i ba saboda kana ango sai ka yi asarar sallah a jam'i?" Ransa ne ya ɓaci ya ga alama in bai zage dantse ba Saddiqa za take juya shi a cikin gidan, amma ya bar wannan ɗin a farkon amarci amma da sannu zai fara nuna mata kudu ba arewa ba ce.

Bai ce uffan ba ya juya a ƙufule ya fita sani ne bata yi ba shi addinin kansa ma bai damu da shi ba bata san ƙasurgumin ƙazami ne kuma jahili wanda bai damu da ibada ba.

Tana idar da sallah tana zaune za ta fara karatu ta ji shigowar sa ko sallama bai yi ba, da alama ma ana sallamewa ya taso ko azkar bai yi ba don ta ji shi ne farkon dawowa don bata ji ƙaran shigowar sauran ba.

Ɗagowa ta yi ta kalle shi shi kuwa bai ma lura da kallon da take masa ba gadon ya haye da yake a bedroom ne take. Shame-shame ya yi a kan gadon ya ja bargo ya rufe iya jikin sa ban da kansa cikin wata murya ya ce

"Amarya ta ango to a taho a fara aikin lada" Bata tanka masa ba ta ɗauki qur'ani da yake irin mai izu goma-goma ne mai guda shida a ciki. Tasowa ta yi ta miƙa masa. Da mamaki yake kallon ta cikin ɗan diriricewa ya kalle ta don yana fatan dai ba ɗori za ta ce ya mata ba don idan haka ne ta ɗakko dala ba gammo.

"Ka karɓa ka karanta ko izu biyu ne" Amon muryar ta ya katse shi. Idanu ya kafe ta da su yana kallon ta ya ce

"Wai karatun ma sai kin saka ni Saddiqa? Lokacin muna yara muna zuwa islamiya in ban manta ba a hadisi na ɗaya da ake mana ana cewa dukkan ayyukan ibada basa iyuwa sai da niyya" Ganin ya hayyayƙo mata sai ta juya jiki sanyi ƙalau ta koma kan sallayar ta zauna tare sa yin bismillah ta fara karatun suratul yasin a bayyane.

Aminu da ya koma ya kwanta ya ja bargo ya ji karatun nata zai hana shi bacci ya ɗago ya ce

"Wai kike yi a zuciyar ki mana" Ko juyowa bata yi ba ta fara karatun a hankali don ta ga abin nasa ya fara wuce gona da iri a ce mutum hatta sautin qur'ani ba ya so.

"Ki rufe qur'anin nan ki zo mu kwanta" Maganar sa ta katse ta

HAJIYA BAKI DA LABARIN HAJIYA MEERAH ME KAYAN MATA KUMA LIKITAR MATA? IN KINA DA ZAN ƘARA MIKI SANI IN KUMA BAKI DA ZAN SANAR DA KE. BAKI TAƁA GANI ANA TALLAR KAYANMU A AREWA 24, KO TAURARUWA KO HIJRA BA? KAYANMU BABU INDA BASA ZAGAYAWA A FAƊIN DUNIYA MUNA AIKAWA KO INA SAYEN ƊAYA KO SARI HAUSAWA SUKA CE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA🤗 GA LIST ƊIN KAYANMU KAWAI IN KINA SO KI MINI MAGANA SANNAN AKWAI GRP DA MUKE TURA KAYAN GA MASU SON SHIGA DON SU GA HOTUNAN KAYAYYAKIN MU👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

MAMAN AFRAH *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****