Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 2
Babu yadda ta iya haka ta yi addu'a ta naɗe sallayar ta mayar da qur,anin ta je wajen nashi.
Gari yana fara haske ta shiga ƙoƙarin raba jikin ta da nashi, amma ya riƙe ta ya hana ta yinƙurin hakan. Jin bata daina kiciniyar ƙwatar kan nata ba a hankali ya buɗe ido ya ce
"Ina za ki je?"
"Wanka zan yi in yi gyaran ɗaki sai na dafa abinci" Galala yake kallon ta.
"Don wankan tsarki dai da ba wani wahala gare shi ba Saddiqa sai ki bari kya yi anjima, kuma yanzu ɗakunan nan sabbi ina suke buƙatae shara, kuma abincin sai mu ci kaza da lemon jiya in kuma bakya son ci ko waina sai na siyo "
"Ai har wankan sabulu zan yi ni dama daga gari ya waye nake wanka, don ni a ƙalla sai na yi wanka sau huɗu watarana har biyar ma" Cike da mamaki yake kallon ta can dai ya yi ƙarfin halin cewa
"Wai a wata kike wankan sau biyar ko a shekara?"
"Wata? Shekara?"
"To ai na san dai ko a sati ba a yi wanka sau biyar ba"
"To a rana nake nufi" Sai da ya ɗan ɗago yana kallon ta sosai.
"Wankan ne kike sau biyar kamar baki da aikin yi"
"Rashin aikin yi ne? Tsafta ce fa"
Bata ƙara magana ba ta shige bayi ta yi wankan tsarki ta ɗore wankan sabulu, yana ta jin tana ta dirzar jikin ta tamkar wacce ta yi wata jikin ta bai ga ruwa ba.
Sai da ta gama ta fito.
"Wai amma sabulu a gidan ku ba ya wata ko Saddiq"
"To ajiyar sa za a yi dama ba don a yi wankan aka siya ba" Shiru ya yi bai ce komai ba shiryawa ta yi ta saka doguwar rigar atamfa ta sha ɗauri sai bulbula ƙamshi take. A bakin gadon ta zauna tana ɗan jifan sa da kallon soyayya.
"Wai Bab... Bata ƙarasa ba ta tuno ya hana ta kiran sa da Baby.
Sai da ya tashi yana shiga bayin ta yi saurin gyara kan gadon ta ɗakko tsintsiya ta shiga sharewa kafin ya fito ta share ɗakin ta dawo falo tana sharewa sai ta ji ya fito kamar yadda ta zata hakan ce ta faru domin kuwa iya wankan tsarki ya yi.
Tana son cewa mai ya sa bai yi wankan sabulun ba amma tana jin kunya.
"Tun jiya nake wanka wannan ne na uku ita ƙazantar da kanta ta san bata isa tsayawa a jikina ba, ba sai na sanya sabulu ba" Ya faɗa tamkar ya san tunanin da take.
Ita dai tana ɗan mamakin a ranta amma sai take tunanin ko sai daga baya zai yi, kaya ya saka bayan ta gama gyaran ɗakin ta ɗakko sauran kazar jiya ta je ta ɗumama musu, tana ta ƙarewa gidan kallo, tana hango ɓangarorin facalolin nata.
Da yake dama ta taɓa zuwa gidan sau ɗaya amma sai dai da daddare ne da ya kawo ta ta yi musu sannnu da shan ruwa a ramadan, to ta shiga ɓangaren kowacce sun gaisa sannan da za ta tafi sun rako ta, wannan ne sanin junan da suka yi.
Haka suka yi ta hirar su sai wajen sha biyu ya fita zuwa gidan su. Bayan fitar sa ne tana zaune rana ɗan danna waya Sumayya ta shigo da sallama amsa mata ta yi suka zauna suna ɗan taɓa hira, cikin hirar tasu ne kamar an ce ta kalli kafaɗar Sumayya abin da ta gani ne ya bata mamaki, hannun bireziyar Sumayya da ya leƙo ne baƙiƙƙirin da shi daga gani kuma fara ce bireziyar amma tsabar datti duk ta dafe.
'Ikon Allah, ita kuwa wannan mai ya sa take saka abu da datti haka?' Saddiqa ta faɗa a zuciyar ta tana jin wani iri don ita a duniya ta tsani ƙazan ta, abin bai tsaya a nan ba tana sauke idanu a ƙasan zanin ta ga shi ma ya ci uban datti da alama ma an yi ta saka a atamfar. Mamaki take da tunanun ita kuwa bata jin kunya mijin ta ya ga hannun bireziyar ta ko ƙasan zanin.
"Amarya an kwana a baƙon waje" Muryar Sumayya ta katse mata tunani. Murmushi ta yi ta ce
"Wallahi kuwa, ni ina Ruma?" Ta tambayi ƴarta.
"Ruma bacci take ne"
"Amina fa?"
"Ban ji motsin ta ba tana ɓangaren ta" Haka suka cigaba da taɓa hira daga ƙarshe ta tafi.
Da yamma ta yi ta yin baƙi maƙota da ƴan uwa masu zuwa ganin gidan amarya, da yake shi ma angon tun da ya zo ya ci abincin rana ya fita ganin tana ta yin baƙi.
Sai bayan sallar isha'i ya dawo gidan.
*BAYAN KWANA BIYU*
Da yamma tana zaune tana yankan farce sai Ruma ƴar gidan Sumayya, da Yusuf da Albani ƴaƴan Amina suna wasa. Kallon yaran Amina ta yi tastas da su gwanin sha'awa amma Ruma hancin ta maji duk ta bushe ga kan nata duk kalbar da aka mata ta tsufa wandon ta kuwa sai zarnin fitsari yake, kwata-kwata ƙazantar jikin yarinya ta yi yawa ba don kar a ga baƙin ta ba da ta kora yarinyar wajen uwar ta don ita ba mutum ba ce da take son ƙazami ya raɓe ta, don ko tana gida in dai yaran maƙota suka shigo to kuwa indai kai ƙazami ne gidan ku take kora ka.
Da sallama ya shigo ta amsa, don dama danta masa maganar ya ɗan huta ko sati guda ne sai ya cigaba da zuwa kasuwar cewa ya yi babu wani hutun amarci da zai ɗauka ai maza ƴan su fita su nemo a ci ne. Jikinsa buɗuɗu da fulawa, da yake sana'ar sa aunar da filawa ce, a can kasuwa gaban wasu shaguna yake buɗe buhun filawa yana aunarwa, idan ya ƙare sai ya sake buɗe wani. Sannu da zuwa ta masa ta karɓi ledar hannun sa, sai kallon ta yake yadda ta masa kyau ta yi kwalliyar ta cikin baƙar abaya sai ƙamshi take bakin nan nata yana sheƙin lipstic.
Kicin ta nufa da ledar ta ware kayan miya ta saka a kwando ɗaya ledar kuma kayan marmari ne sai ta saka a frige, ta wanko wasu ta yanko a plate ta zo ta ba yaran, suna karɓa da murna suka fice.
Kayan abincin ta ɗakko ta ajiye masa a falon tare da ruwa sai ta nufi bedroom ɗin, kwance ta same shi a kan gadon. Ta ji babu daɗi ganin jikin sa babu yadda yake duk filawa amma ta hau kan gadon danne abin da ta ji a ranta ta yi, bayi ta nufi tana shirin shiga maganar sa ta katse ta.
"Baki yi sallah ba ne?"
"Sallah kuma?"
"Eh na ga kin nufi bayi" Ya faɗa yana kallon ta shi tana birge shi yadda take ƴar gayu.
"Ruwan wanka zan haɗa maka" Shiru ya ɗan yi sai kuma ya ce
"Wane irin wanka da la'asar ɗin nan, bakya ganin sanyi ake ai sai mura ta kama mutum" Da mamaki take kallon sa kawar da kai ya yi gefe ya kuwa maje.
"Yanzu haka za ka zauna kalli jikin ka fa, jiya ma fa da na haɗa maka ruwan cewa ka yi la'asar ta yi ba za ka yi ba, kuma fa akwai ruwan ɗumi ba na sanyo ba ne"
"Haɗa" Ya ce a taƙaice. Juyawa ta yi ta shiga ta zuba ruwan ta fito ta ɗakko na zafi ta haɗa masa, brush ɗin sa da ta goga masa makilin da safe ta gani bai yi ba ta wanke brush ɗin ta sake tatsa masa makilin ɗin ta fito.
"Na haɗa maka" Da to ya amsa da kamar ba zai tashi ba sai kuma ya tashi ya tuɓe kayan jikin sa daga shi sai gajeran wando ya shiga bayin ya rufo. Ya ɗan jima da shiga amma bata ji alamar kwara ruwa ba jim kaɗan ta fara jin alamar taɓa ruwa, can sai ga shi ya fito amma abin mamaki fuska, hannaye sai ƙafafun sa ne kaɗai suka san ya taɓa ruwa da alama wankin jiki ya yi ba wanka ba. Wani takaici ta ji a ranta ta rasa mai ya sa Aminu ba ya son yin wanka ta lura ko kaɗan ya ƙi jinin zuba ruwa a jikin sa.
Ita kuma tana ɗan jin kunyar sa shi ya sa ba ta iya faɗa masa hakan yana damun ta. Shi kuwa yana fitowa ya wani haɗe rai yadda ba za ta ga fuska ba bare ta ce wani abu mai ya ɗauka ya shafa abin sa ya ɗauki singlet ɗin da ya cire ya mayar ya ɗakko wata jallabiya ya saka.
"Mu je ki zuba mini abincin" Ya ce bai jira cewar ta ba ya fita falon, shiru ta yi tana zaune a wajen, ita da a gida idan Noor bata yi wanka ba in za ta kwanta ta ringa mata bala'i a kan ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da ita ba sai ga shi jiya ta kwana da wanda bai yi wanka ko sau ɗaya da sabulu ba a rana, yau ma kuma da alama tarihin jiyan zai maimaita kansa.
Kamar wacce aka tsikara haka ta tashi bayin ta nufa ta leƙa brush ɗin sa yana nan kamar yadda ta ajiye wai don ma kar ya ce bai gani ba a kan buta ta ɗora masa kusa da kwandon wankan amma bai yi ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin babu daɗi.
"Saddiqa" Ta jiyo muryar sa yana kiran ta. Amsawa ta yi ta nufo falon tana ƙirƙirar murmushin yaƙe.
"Amarya, amarya" Ya ce yana kallon ta. Bata ce komai ba ta zuba abincin ta tura masa, ya fara ci ruwa ta ɗakko ta zuba masa ta koma gefe tana ɗan tunani, ita yanzu damuwar ta bai wuce rashin wankan sa ba.
A daddafe ya gama ana magriba har ya miƙe a falon sai da ta masa maganar sallah sannan ya tashi yana ɗan jin kunya ya shiga bayi zai yi alwalar ita kuma ta fito da kayan zuwa cikin. Shafi'u ta gani ya fito daga part ɗin su ya zo da fita da alama masallaci zai je don a kallo ɗaya da ta masa ta ga alamar ruwa hakan yana nuni da alwala ya yi. Farin yadin da yake jikin sa wanda a kallo ɗaya ta gama tantance wanke yake tas ga karin guga, wani ƙamshin turare da ya buɗaɗe hancin ta mai sanyin ƙamshi ya sa ta ji a ranta ina ma Aminu mijin ta ne yake gyara kansa haka.
Tun zuwan ta gidan bata taɓa jin wani nau'i na ƙamshi daga jikin sa ba, ko da a ce ta ɗakko turaren ta ta ce ya shafa ko kuma ta yi ƙoƙarin shafa masa in zai fita wajen sana'a sai ya ce shi ba ya son asarar abu, wanda zai je ya sha rana wajen sana'a ina shi ina wani turare, haka idan za su kwanta tana ƙoƙarin ya shafa sai ya ƙi ko ya ce wai turaren juya masa kai yake ko kuma ya kawo mata wata hujja marar madogara.
"Yaya Shafi'u ina wuni" Ta gaishe da shi. Shafi'u kuwa tun da ya fito ya hango fitowar ta ya ƙura mata idanu haka kawai ya ji ta birge shi ganin ta cikin tsafta da kwalliya. Amsawa ya yi ta yi gaba tana jin yadda idanun sa yake yawo a jikin ta.
Ko da ta dawo shi ma ya fito ɗaure da alwala. Kayan da ya dawo da su daga kasuwar su ya mayar sai dai yanzu ta ga babu farin fulawar a jiki sosai da alama ya karkaɗe ne.
Murmushi ya sakar mata, bata ankara ba sai ji ta yi ya zo ya kawo mata wata wawar sumbata a kunci kusa da bakin ta, idanu ta ɗan runtse jin wani gumus ɗin bakin sa da ta shaƙa. Bakin sa ya janye yana ƴar dariya ya ce
"Kin ƙi sakin jiki da ni sai kike jin kunya, ina mijin ki mene ne na runtse idanu. Murmushin yaƙe ta ƙaƙaro ya juya da sauri jin an fara sallar, ɗaki ta shiga ta yi alwalar ta gabatar da tata sallar.
Haka da dare ma ya zo mata tashin wani hamamin gumi don ban da warin rana babu abin da yake tashi daga jikin sa, haka ya zo neman haƙƙin sa ita kuma tana ƙamshi ta tsaftace jikin ta da bakin ta, rungumar da ya mata kanta a wajen hamatar sa sai da ta ji har wani juyawa kanta yake saboda wari, da ya haɗe bakin su kuwa gabaɗaya numfashi ma sai da ya gagare ta tamkar an saka hancin ta a wurin kashi haka ta ji tabbas warin baki babu daɗi ga shi Aminu yana da rami a haƙorin sa irin abin nan da ake kira da kogon haƙori wanda wasu suke cewa tsutsar haƙori ce take cinye wajen.
Abincin yana shiga wurin idan har mutum ba ya wanke baki tare da fitar da abincin da ya maƙale to kuwa warin da bakin sa zai yi sai dai Allah
KAYAYYAKIN MU NA KAMFANIN MEERAH B HERBS 👇
*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .
*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*
MAMAN AFRAH *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****