Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 3

by @mamanafrah3028

*SUMAYYA*

Zaune take a falo ta yi zaman dirshan sanye take da zanin falle ɗaure a jikin ta sai wata riga t-shirt , Ruma tana waje zaune a foo tana kashi, shigowar Ya Shafi'u falon sai da ransa ya yi mugun ɓaci ganin falon duk datti ga wata takarda da leda nan duk ya yaga ƙanana da alama Ruma ce ta yayyaga, gefe ɗaya ga farantin abincin da Rumar ta ci, ita ma kuma Sumayyar da nata kwanon a gabanta da alama abincin ta gama ci ko hannu bata tashi ta wanke ba.

"Ummi na gama" Ruma ta ce tana daga wajen. Wata uwar gyatsa ta saki ta ce

"Ki zauna zan zo in wanke miki"

"Wai mai ya sa Sumayya kullum lamuran ki gaba suke ba baya ba? Kin ga yadda ƙuda yake bin yarinyar nan kuwa, maimakon ki je ki raba ta da kashin shi ne...

"Dakata malam wai kai kullum a ganin laifina kake, komai na yi ban iya ba, shi wankin kashin ibada ne da za a ce lallai daga faɗa na tashi na wanke mata " Ta katse shi a zafafe, kallon ta yake da takaici falon duk ya haɗe da warin gumin ƙazanta in ba mantawa ya yi ba rabon da ta yi wankan yau kusan kwana uku kenan haka ma bata wa Ruma ba.

"Ya kamata ki wa kan ki faɗa duk abin da kike yi idan yaran ki suka taso su ma shi za su yi, yanzu ki dubi ƴaƴan Amina gwanin sha'awa tas da su kullum amma ke ƴarki sai ta kwana uku jikin ta bai ga ruwa ba daga ta zo kusa da mutuk sai zarnin fitsari, idanun ta kwantsa bakya wanke mata baki haba wannan wace irin ƙazanta ce Sumayya?" ,Wani uban tsaki ta ja, ta tashi tare da saka ƙafa ta ture kwanon gabanta da ta ci abinci bata bi ta kansa ba ta shige ɗaki ko hannu bata wanke ba ta je ta hau gado ta kwanta take danna waya.

Rumar ya ɗakko ya je ya wanke mata kashin ya yi floshin, hatta banɗakin sai tashin zarni yake duk bango da ƙasan tiles ɗin sun dafe.

"Ɗakko wandon ki a falo in saka miki" Ta ce wa Ruma hankalin ta a kan waya. Wandon ta ɗakko ta kawo mata, ta saka mata, shi kan sa zarnin yake duk ga wamdunan yarinyar nan babu wanki ga kayan wanki kamar su yi magana, ta gwammace ta zazzaga musu mai datti su saka idan ta ga banu hali sai ta tsakuri kaɗan ta wanke.

Falon ya dawo ya haɗa plate ɗin Rumar da kwanon Sumayyar ya fita ya je kicin kayan wanke-wanke tari guda ƙuda yana bi abin tsantsani tsayawa ya yi ya kama tsantsa.

Gabaɗaya shi dai ya yi da na sanin auren Sumayya saboda muguwar ƙazantar ta, ya rasa dalilin da ya sa bai fahimci hakan ba lokacin da yana neman auren ta ko don tana kwalliya tsaf-tsaf idan zai je zance, sai da suka yi aure abu da kaɗan-kaɗan yake bayyana har ta kai tun tana ɗan ɓoyewa yanzu abubuwa sun kai har bata ma jin kunyar ƙazanta.

Da dare tana zaune babu ɗanwakwali shi ma yana zaune yana danna waya lokaci zuwa lokaci yana ɗan satar kallon ta ganin yadda kitson kanta ya yi tsofa sosai har ba a ganin tsagar ko kaɗan duk ya cushe sai wani susa take.

"Sumayya" Ya kira ta da murya mai kamar lallashi, amsa masa ta yi ba tare da ta kalle shi ba.

"Yanzu Sumayya rayuwa ta yiwu a hakan anya? A ce wanke-wanke sai kwanuka su ƙare a kwando kin gwammace in xa ki yi amfani da kwano ki ɗauka ki wanke, haka tukunya ma? Wankin kayan ki da na Ruma har sai kun rasa na sakawa za ki tsakura ki wanke, yarinyar nan bata samun kulawa ta tsafta kullum ka ganta da ƙazanta don Allah ki gyara tun da dai dai gwargwado ina kawo komai kuma duk abin da kike buƙata ina miki" Ya ce cikin rausayar da kai amma ko arziƙin kallo bai samu ba.

"Magana fa nake miki ko?"

"Wai don Allah Shafi'u mene ne matsalar ka da ni ne da za kake takurawa rayuwata? Ni fa babu dalilin da zai saka kullum in ke wahalar da kaina, in ke wanki bai taru ba ko wanke-wanke ko in ƙare bauta a kan ƴa ɗaya ƙwallin ƙwal, haba ita mace bata da lokacin hutu sai na bauta a gidan miji idan abin da nake bai gamshe ka ba za ka iya ɗauko mai aiki take maka duk abubuwan da ba na yi"

"Haka mw za ki ce mai ya sa ke har kullum in dai hanya ta masalaha ce aka ce za a bi amma ke bakya yarda da ita? Ke ko kaɗan bakya son a miki gyara? Yanzu daga ni sai ke sai Ruma har sai na zauna ɗaukan mai aiki"

"To tun da har ba za ka ɗauki mai aikin ba, sai ka ɗauki na annabawa don ni ba zan ƙare a wahala ba wallahi" Tana gama faɗar hakan ta tashi fuuuu ta shige ɗaki, wani gumus ya shai warin kayan jikin ta da suke warin dauɗa da kuma warin gumi don ya san wannan maimaicin bai san na nawa ba ne, haka take ta maimaita kaya.

Sai da ya kammala da abin da yake a wayar ya tashi zuciyar sa duk a cunkushe, don dama ba komai yake gani a wayar ba illa hotunan ƴan mata yana ganin haɗaɗɗun mata da suka yi kwalliya hakan yake sawa yana jin shauƙi yana ji dama a ce Sumayyar sa ce take haka da babu ruwan sa fa kalle-kalle ya shiga ɗakin kayan jikin sa ya ɗan rage ya shiga ya yi wanka ya fito ya shafa turare, yana hawa gadon ya shaƙi warin jikin ta ga bakin nan da ta hangame tana bacci sai wari yake fitowa daga bakin, warin rashin wankin bakin don ita Sumayya abin ya mata yawa wai shege da hauka. A haka ya yi ta maza ya matsa kusa da ita don a buƙace yake sosai sai sai abin da yake shaƙa daga jikin ta ya sa ya ji tamkar ya toshe hancin ya biya buƙatar a haka don ya san ko mai za a yi ba za ta yarda ta watsa ruwa a jikin ta ba bare ɗan warin gumin da take yi ya kau.

Hannu ya kai ya ɗan taɓa ta, da yake ita Ruma shimfiɗar ta da ban, cikin bacci ta sanya hannu ta buge hannun, ɗan matsawa ya yi kusa da ita duk da yana jin hamamin yana damunsa ya kai bakin sa kusa da kunnen ta ya ce

"Sumy baby" Kiran da ya mata ya sa ta ɗan buɗe idanu tare da ƙanƙance su ta sauke a kan sa ta sauran hasken farin watan da ya haske ɗakin.

Wartsakewa ta yi tare da tashi zaune ta zauna daram, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ce

"Haba don Allah wannan ai ɗaukan alhaki ne ya ina baccina mai daɗi za ka zo ka tashe ni kana mini wata raɗa a kunne" Ta faɗa tana haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. Shafi'u ji ya yi kamar ya yi amai da ya shaƙi iskar da ta fito daga bakin ta wani irin wari, amma da yake a buƙace yake sai ya ji zai jure ko da kuwa yana kawar da kai ne ya samu ya kauda buƙatar sa. Sai dai inda gizo yake saƙar bai san ma ko za ta amince ba.

"Ki ɗan saki fuskar mana kin ji baby nah...

"Eh mana dama yanzu za ka kalailame ni da zaƙin baki, saboda kana buƙatata ai ɗazu ka rufe ido ka faɗa mini baƙar magana ka ga ai baka zo wajen ƙazama ba" Ta ce cikin hargowa. Ɗan marairaice fuska ya yi ya ce

"Ki yi haƙuri kin ji Sumy na daina"

"Wallahi yanzu bacci zan yi babu abin da zai sa na ɓata lokaci na ban yi bacci ba kaina yake ciwo, kai da in ka fara abu baka san ka tsagaita ba" Ta ce tana juya baya ta kwanta.

"Don Allah ki taimaka yau kwana nawa ina fama da ke ko so kike in faɗa halaka haba ke kuwa"

"Ka daɗe baka faɗa halaka ba, kuma babu wata halaka sai dai ka ce son zuciya in ba son zuciya ba mene ne kuma ko ma dai mene ne kabarin ka da ban nawa da ban" Ta ce tana jan abun rufa ta rufa ta bar shi, da ya kama bargon ma zai shiga ta daddanne ta hana shi ya shiga.

Jikin allon gadon ya koma ya jingina, ransa yana ƙuna ya gaji da abin da Sumayya take masa ban da ƙazantar ta har da hana shi haƙƙin sa. Bai yi fushi ba ya ƙara kai mata raruma ta kuwa balbale shi da masifa tana mai tashi fuuu ta suri bargon ta koma falo ta kwanta a doguwar kujera. Iska ya furzar daga bakin sa yana jin yadda buƙata take bijiro masa.

Filo ya ja ya runguma yana jin tamkar ya saki kukan takaici da haka bacci ya yi awon gaba da shi.

*SULE*

Zaune yake a falo yana sha tea yana duba news Amina tana daga gefe tama danna wayar ta, ɗago kai ya yi kalle ta cike da kulawa da nuna soyayya ya ce

"Annurin zuciyata, son ki ya daɗe da yon nutso a birnin zuciyata duk ranar da aka ce babu ke a wannan duniyar to ba na jin zan iya ƙara wasu kwanaki ina cikin hayyacina in ma dai ba mu yi mutuwar kasko ba" Kallon sa ta yi sheƙeƙe tana jinjinawa rainin wayo da ƙaryar tashi ta ce

"Abban Yusuf wai me ya sa kai ka zaɓi kullum kake faɗar abin da ba haka ba ne? Yanzu mene ne amfanin wannan tsarana ɗin da kake?"

"Tsarawa"

"Eh mana in ba tsari ba mene ne"

"Soyayyar ce tsari Amina yanzu ina matsayin mijin ki amma don na miki kalaman soyayya shi ne tsari?" Ya faɗa yana jon takaicin abin da take masa ita kullum magana ɗaya ce shi ne soyayya tsara zance ne ita kuma bata yarda da kalaman soyayya ba ya rasa gane wace irin mace ce ita

"To kai ma Abban Yusuf ka san dai an ce amfanin soyayya aure to mun yi aure a kan me za mu ke wahalar da kan mu yin wata soyayya da kalaman soyayya sai ka ce wasu farin shiga?" Ta jefa masa tambayar hankalin ta a kan wayar ta. Shiru ya yi don ya rasa ma bakin magana.

"Haka kawai ni ba budurwa ba ni ba amarya ba a ishe ni da wata kalamar ina son ki haba!. Ai na daɗe da sanin cewar kana sona ko sai ka yi ta maimaitawa kamar karatu, ƴaƴa biyu mai kuma ake nema a wata soyayya?" Ta ƙara faɗa har lokacin bai ce mata ko uffan ba don in da sabo ya saba, shi mutum ne ɗan soyayya yana son kulawa da nuna soyaya sai dai kash!.

Bai dace da mata ba wasu matan suna son kulawar miji da nuna soyayya amma sai ka ga daga an yi auren an gama cin amarci shikenan sai namiji ya ajiye soyayya a gefe sai dai kuma a fara zaman kurame ko zaman haƙuri amma ba na soyayya ba. Ita ga shi ta samu amma tana wofantarwa shi ya sa sai ya ringa jin babu daɗi kwata-kwata ya rasa ya zai shawo kan lamarin ga ta kuma da shegen masifaffan kishin tsiya amma bata iya kula da miji ba bata iya nuna masa kulawa ba ita ma in an nuna mata kulawar bata damuwa da hakan.

*SADDIQA*

Bayan sati uku abubuwa sun fara cunkushe mata, don babban abin da ta ƙara fahimta daga Aminu shi ne ba ya son yin aski daga askin matse matsi har aske kansa kuwa. Gashin hanatar sa ya taru haka na marar sa sannan uwa uba gemu da gashin kansa babu gyara duk sun cunkushe. Gashin Hammatar har wani tsatsa-tsatsa yake idan ya fita wajen sana'ar sa ya kwaso rana ya dawo tamkar ta yi irin yadda warin ana yake bugun ta daga jikin sa.

Haka zai dawo hajaran majaran busu-busu da fulawa amma a hakan zai turmusu a gadon ta wanda take gyarawa ta ɗame shimfiɗar gadon, kusamman wani farin zanin gadon ta duk ya dafe sai yanzu take tunawa a ranar da ta tare a gidan hatta jakar kayan sawar sa da ta zo shirya masa kayan a drower duk kayan basu da wankin masu wankin kaɗan ne duk sun dafe sai tashin warin dauɗa suke, tun a lokacin ta yi mamaki a ce sabon ango da zai tare a gidan amarya amma kuma ya zo da kayan marar sa wankin tun a sannan ta fara ɗora masa alamar tambayar anya ba ƘAZAMIN MIJI ta aura ba , sai ga shi da kaɗan-kaɗan abubuwa suna bayyana halayen suna fitowa.

"Ranka ya daɗe!. Na ce ka bani dama in maka aski" Ta ce tana ɗan murmushi hannun ta riƙe da sabuwar sheba ta aski wacce ta zo da ita tun daga gida dama siyen su take yi ta ajiye don ita bata yarda da barin gashi ko yaya a jikin ta ba. Wani kallon rashin fahimta ya mata yana mayar da kallon nasa kan shebar da takr riƙe da ita ya ce

"Wane irin aski?" Na marar da na hammata mana, sannan ko gashin fuskar ka yana buƙatar ka ɗan rage shi"

"Lallai Saddiqa kin ga makwancina da yawa wallahi, ni ne ma za ki yi wa aski sai ka ce wani ɗanki?"

"Haba mene ne na ɗaukan zafi ni fa matarka ce mene ne don na maka askin"

"To ban ga dama ba lokacin da na ga dama zan aske tun da ba a jikin ki yake ba" Ya ce yana haɗe rai.

Ta ce " Don Allah ka yi haƙuri ni ba da wata manufa na faɗa ba a ganina miji ɗan gata shi ne mace take ba kulawa har ma ta buƙaci masa wani abun don ta faranta ransa...

"To ni na yafe wanann kulawar, gashin da yake hammata da wanda yake mara da ba ganin su ake yi ba ina ruwan ki da su daga ka saka kaya zancen su ya ƙare ko ma ana gani ai wanda ya raina tsayuwar wata hawa yake ya gyara" Ya faɗa hankali kwance.

KAYAN GYARANMU NA MEERA B HERBS SUNA DA INGANCI

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

A MINI MAGANA A PC *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****