Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 4

by @mamanafrah3028

Tun daga wannan rana da ya ƙi maganar askin nan sai tattara lamuran sa ta yi ta ajiye saboda ko kaɗan ta lura ba shi da ra'ayin yin hakan. Abin da yake bata mamaki bai wuce yadda daga ta toshe waccan kafar sai wata ta kawo kai ba, shi kullum da kalar ƙazantar da zai fito da ita, da abin ya dame ta ne wata rana ƙanwar sa Fatima ta zo take faɗa mata wasu daga cikon halayen masa da yake sun shaƙu da Fatimar tana son ta, a nan ne ta ji abin mamaki cewa wai ashe Aminu dama haka yake don dik gidan su shi ne ƙazami na ajin ƙarshe.

Ta ce mata yana gida ma sai ya yi sati bai yi wanka ba bare wanki kuwa kaya sai ya maimaita shi ya fi sau huɗu, ɗakin sa kuwa dama a gidan su taron yuyuyu ake cewa saboda tarkace da kuma kayan wanki in ka shiga ɗakin sa ko ina kaya ne a zube, haka zai tattara su gefe guda idan zai kwanta, saboda ba zai gyara ba.

A nan ne ma Fatimar take ce mata, da suka fara soyayya ne ma ya fara ɗan yin wanki da ɗan gyara jikin sa, shi ma sai ranar da zai je hirar ne zai ɗauki kala ɗaya ya wanke. Sannan ta ce mata akwai lokacin da suna junior secondry school ma wani malamin su a gaban asambili ya fito da shi lokacin ana fito da ƙazaman makaranta, ta ce a gaban kowa aka tuɓe masa riga prefect suka masa wanka da soson buhu saboda rashin tsafta, amma hakan bai sa ya saduda ba.

Saddiqa tun da ta ji wannan batu sai jikin ta ya ƙara sanyi kasancewar ta mai tsafta amma kuma ga shi cikin jarabawar ubangiji ta auri ƙazami lamba ɗaya.

"Ni fa Fatima ba wannan ne damuwata ba, shi fa ko kayan na wanke sai ya ga dama zai saka, ga wankekken kaya amma sai ya ce in zai tafi wakem sana'ar sa ba zai saka ba saboda in ya saka ma asarar wanki ne tun da awon fulawa zai yi da su ɓaci za su yi, to in ya dawo kuwa hallaw ba zai cire wanda ya je aikin ba ya saka wasu sai ya ƙara zaman sa da su sai ya ce wai tun da la'asar ma ta yi ba zai canja kayan ba saboda ɓata kaya ne a ce rayuwa kai ba za ka ga mijin ka cikin tsafta ba ka ji daɗi a ranka?"

"Ai fa Aunty Saddiqa sai dai ki yi haƙuri amma Yaya Aminu kam lamba ɗaya ne a ƴan ƙazanta"

Furucin Fatima ya sa ta ƙara ɗaura ɗamara don magance wannan matsala tata don ba zai yiwu a ce su cigaba da rayuwa a haka ba.

*BAYAN WATA BIYU*

Yanzu kam abin na Aminu ya daina bata mamaki da al'ajabi ya koma bata tsoro domin yanzu gabaɗaya halayen sa na ƙazanta ya bayyana tun tana ganin za ta iya magance matsalar da kanta har ta kai ta fara tunanin shigo da manya cikin lamuran. Hakan ya sa ta fara tunanin wanda za ta tunkara da maganar da farko ta so zuwa gidan su ta kai ƙaran sa amma kuma sai ta fara tunanin kar hakan ya zama matsala don yanzu a iya wannan watannin ta lura yana da zafin kai ga shi yana da girman kai yanzu ya rufe duk wata kafa da za ta masa maganar gyara jikin sa ko tsaftacewa yanzu ya zamar mata kamar dodo ma don sai yake nuna mata abin da take masa tamkar raini ne ta raina sa ne shi ya sa har take ganin za take masa irin abin da take masa, ko kaɗan ba ya ganin tana yin hakan ne don kawo masalaha a zamantakewar auren su saboda tana cutuwa da ƙazantar sa.

'Saddiqa yadda Aminu yake da taurin kai kin san dai kowace uwa za ta yi ƙoƙarin ganin ta tsaftace ƴaƴanta ko kuma basu tarbiya da nusar da su tsaftace jikin su da nisantar ƙazan ta duk da wasu iyayen su ne mafarin farko na koyawa ƴaƴan nasu ƙazantar misali kamar Sumyya yadda take ƙazanta ba ta tsaftace jikin ta da na ƴarta da kuma muhallin ta wannan kaɗai zai sanya Ruma ta koya tun da yara sun fi koyar abin da idanun su suke gani.

Wasu iyayen kuma sun iya bakin ƙoƙarin su na ganin sun koyawa yaran amma daga sun kai munzalin da za su yi komai da kan su sai hakan ya fasakara ake ta fama da su wani sai dai ka gaji ka ƙyale shi, kamar Aminu dai kin ga Fatima ta faɗa miki shi kaɗai ne ya fita zakka a gidan su kuma an yi fama da shi amma ƙazantar har ta zaune masa, dama Fatinar ta ce mata mahaifiyar su ta ce matar Aminu ta shiga uku da ƙazantar sa ashe kuwa hakan ne. Idan kika je gidan su kika faɗa hakan zai haifar da matsala tsakanin ku tun da yana ganin kin raina sa amma ko ki samu Yayan sa ki faɗa masa ko Allah zai sa a samu maslaha'Ta ƙare maganar a zuciyar ta tana jin hakan ya kwanra mata a zuciyar ta.

Da safe bayan ya shirya ya fita wajen kasuwancin sa ganin Yaya Sule bai fita ba sai ta shiga jiran fitowar sa daga sashen su, don bata so matar sa ta san abin da yake wakana, duk da ta san ba lallai su kasa sanin hakan ba amma sai dai in su lura da iya ƙazantar jikin sa tun da zama gida ɗaya ba wasa ba amma dai ba za su san abubuwan da suke a ɓoye ba wanda iya ita da take matsayin matar sa ne ta san da hakan. Saboda ita mutum ce mai riƙe sirri bata yarda da yaɗa sirrin mijin ta ba musamman ma irin wannan sirrin da wani in ya ji sai ya maka dariya a bayan idanun ka ko kuma ya je yana faɗawa wasu.

Shi ya sa ma sai Fatima ta faɗawa kaɗan daga cikin matsalar ita ma don ta ga ƙanwar sa ce sannan kuma ta san Fatimar ba za ta kasa sanin hakan ba tun da ƙazantar ba ta wasa ba ce.

Ƙaran ƙofar falon su Aminar ne ya dawo da ita daga ɗan guntun tunanin da ta tafi, da sauri ta taso ta ɗan ɗaga labule ta leƙo ai kuwa ta hango Yaya Sule ya fito da alama fita zai yi. Da yake part ɗin su Saddiqa ne a wajen hanyar fita, sai sa ta bari ya zo zai yi hanyar wajen ta taso tana sanye da hijabi ta leƙo.

"YAya ina kwana" Muryar Saddiqa ta katse masa tafiyar da yake don har ya bada baya.

"Lafiya ƙalau amarya" Ya ce cike da sakin fuska.

"Yaya dama, uhm, d

"Akwai wani abu ne Saddiqa?" Ya katse mata maganar ganin tana ta inda -inda ta kasa faɗar komai tana wasa da yatsun ta.

"Eh, dama akwai maganar da nake so mu yi" Ta faɗa tana ɗan jin nauyin sa sannan gaban ta yana faɗuwa.

"To ba damuwa mu je" Ya ce yana mata nuni da hannu alamar su shiga daga falon don ya lura kamar bata son yin maganar a wajen. Ta ji daɗin maganar sa hakan ya sa ta juya suka shiga falon nata ya zauna sai ya ce

"Ina sauraron ki"

"Yaya dama a kan maganar Aminu ne"

"Mai ya samu Aminun?"

"Dama dai ba ya son tsaftace jikin sa ne, ni kuma abin yana damuna wallahi, na yi ƙoƙarin nusar da shi amma abin ya ci tura!."

Iska ya furzar daga bakin sa yana kallon ta da tausayawa shi ya ga ƙoƙarin ta ma da har ta iya kai wa wannan lokacin bata nemi maslahar faɗawa kowa ba, saboda ya san in ba mai matuƙar haƙuri ba babu mai iya zama da ɗan uwan nasa, sai dai kuma ko ƙazama kamar shi.

"Saddiqa abin da nake so ki gane Aminu ya wallahi mutum ne da yake da taurin kai, dama na san wataran wannan zai iya biyu baya saboda babu macen da za ta iya jure zama da shi ko da tsawon kwana sati uku ne, kin yi haƙuri da jarumta da kika iya kai wa har wata biyu ba tare da kin yi ƙorafi ba" Ya faɗa cikin tausayawa da tausasawa. Idanun ta ne suka tara ƙwalla tana tuno irin warin da bakin sa yake wanda idan ta shaƙa sai ta ji har wani juyawa kanta yake, tabbas!. Babu abin da ya fi ciwo a nata ganin sama da auren ƙazamin miji, duk da kowace mace akwai tata matsalar da take fuskanta a gidan aure amma dai kowane mai ɗako shi ya san inda yake masa yoyo.

"Na masa magana shi ne ya yi biris da maganata na rasa yadda zan yi ne amma don Allah Yaya in za ka masa magana kar ka ce ni na faɗa maka"

"Haba Saddiqa magana fa ake ta gyaran aure ai tun da ke ce iyalin sa kuma ke kika fi buƙar ya gyara dole a faɗa masa, sannan idan har kina ganin zai ji babu daɗi in kin faɗa mini to ki cire wannan a ranki domin kuwa Aminu wannan ba wani baƙon abu ba ne a wajen sa sannan ba abin kunya ba ne, abu ne da ya saba ko da za a yi bikin mun zauna an masa faɗa sosai kuma ya nuna ya ɗauki hakan amma dai dama na san da wuya wai gurguwa da auren nesa

"Amma Yaya abin ya yi yawa"

"Ki yi haƙuri zan same shi" Da to ta amsa ya mata sallama ya fito yana ɗan waiga ɓangaren su kar sarkin ƴan kishin nan ta hango shi cibi ya zama ƙari.

Tun da ta faɗawa Yaya Sule maganar sai ta ji wani daɗi da sanyi a ranta ji take tamkar ta sauke wani nauyi. Ɗakin ta koma ta cire bedsheet ɗin kan gadon ganin duk ya dafe da ƙafar sa da ya kwanta jiya, wani wankakke ta ɗauko ta shimfiɗa.

Bayan ta gama komai ta ɗakko freshner mai ƙamshi ya feshe ko ina tuni ɗakunan suka buɗaɗe da ƙamshi sai ta ɗakko qur'ani tana tilawa cikin kwanciyar hankali.

Da yamma ta ƙara shiga ta yi wanka ta sanya kaya marar sa nauyi ta zauna tana jiran dawowar ogan nata, duk tana jin babu daɗi a ranta don ta san daga ya dawo yanzu ɗakin zai sauya daga ƙamshi zuwa wari, don duk ƙamshin nan daga Aminu ya dawo ɗakunan za su yi wani gumus.

"Assalamu alaikum amarya ya ango" Ta tsinkayi muryar Sumayya a falo. Tana daga cikin bedroom ɗin ta amsa mata kafin ta fito zuwa falon tana ɗan sakin dariyar yaƙe.

Ƙarasowa ta yi za ta zauna a kujerar mai daf da Sumyyar amma wani warin gumi da ta shaƙa a jikin ta sai ta ɗan wayinci ta koma ɗayar saboda ba za ta juri shaƙar wannan warin ba, duk da tana ganin mijin ta ma ƙazami ne amma ai shi namiji ne duk da mazan ma akwai masu tsafta amma mace an santa da gayu da tsafta koman ta tsaf-tsaf.

"Saddiqa amaryar Aminu wato wannan kwalliyar yamma ce aka yi wa ango?" Ta tambaya tana kallon ta tare da washe baki kamar gonar auduga. Kallo ɗaya Saddiqa ta yi wa haƙoran Sumayya da ta washe yadda duk suka dafe ta ce

"Eh mana yo ina da wanda zan yi wa kwalliya da ya wuce shi" Ta ce tana ƴar dariya.

"Gaskiya babu, ai na farko-farko ne duk amare ai suna wannan gayun a farkon aure amma daga baya sai ki ga komai ya zama tarihi"

"A kan me zai zama tarihi"

"Dainawa sume yi"

"Ni ka in Allah ya aramin tsawon rai har tsufana"

"Muna nan da keSaddiqa duk za ki watsar"

"Ina Hajiya Ruma" Ta tambaya don kawar da maganar

,"Tana can tana bacci'

"Baccin la'asar?"

"Eh"

"Ai kuwa babu kyau" Saddiqa ta ce tana jingina da jikin kujera

Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai suka ji sallamar Aminu gaishe da shi da shi Sumayya ta yi ya amsa suna ɗan wasa irin na ƙanin miji. Sallama ta yi wa Saddiqa ta fita.

Bai shigo da komai ba yau don haka yana shiga ɗakin ya hau gado ya kwanta, shiga ta yi tana masa sannu da zuwa ya amsa dakyar.

"Bari na kawo maka abinci"

"Na ƙoshi" Ya furta tare da juya mata baya ya kwanta ga jikin sa dirnis da farin filawa.

"Ƙoshi kuma?" Ta tamabaye shi jin wani sabon abu don bai taɓa cewa ya ƙoshi da abinci ba. Danne abin da ta ji ta matsa kuda da shi ta zauna daga gefe ta ce

"Ko baka da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau kawai dai ba na ra'ayin ci ne" Ya ce yana zaro wayar sa a aljinu ya shiga latsawa. Shiru ta yi tana mamakin kalaman sa ganin yana amsa mata dakyar kamar wanda ya sha magani mai ɗaci, tonowa ta yi da yanzu suka gama gaidawa shi da Sumayya yana faram-faram da washe baki har da wani washe baki yana zolayar ta.

Bai ƙara mata magana ba tana ta satar kallon sa yadda ya mayar da hankalin sa kan waya, sai wani sakin murmushi yake wanda wannan murmushi yana da alaƙa da abin da yake a wayar. Ranta ne yake ƙuna ganin duk lokacin da ta ɓata wajen gyara da kwalliyar da ta masa ko kallo bata ishe shi ba, amma yana zuwa ya washewa ƙazama haƙora sannan yanzu yana yi waya murmushi ita ta zama kamar wani hoto a wajen.

Ganin bai san tana kallon sa ba sai ta ɗan yi dogon wuya kaɗan tana hango mai yake yi a wayar gabanta ne ya faɗi ganin ya yi zoomin na hoton wata mace da take murmushi kanta ɗauke da kitson atach ko ɗankwali babu a kanta. Da sauri ta kawar da idanun ta daga fuskar wayar ta mayar fuskar sa har lokacin dai wannan murmushin yana kwance a saman fuskar sa.

'Ikon Allah dama abin da yake a waya kenan, ni ina zaune basho ashe ba ta ni yake ba?' Ta jefawa kanta tambayar a zuciyar ta.

"Aminu" Ta kira shi da kausashshiyar muryar ra da take cike da jin kishin abin da ta gani.

"Ina jin ki" Ya ce ba tare da ya amsa ba kuma ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba.

"Me kake kallo a waya kake dariya?"

"Wani abu ne na abin dariya nake karantawa shi ne ya bani dariya" Kallon sa take tana jinjina ƙaryar sa amma sai ta ce

"Gaskiya ne"

Falo ta koma ta bar masa ɗakin don ta lura yau kwata-kwata ba ya son zaman ta kusa da shi. Sai da aka kira sallah ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta fito ta yi sallaha. Amma shi ko gizau bai yi ba, ita kuma bata masa magana ba don yanzu daga ta masa maganar yin sallah sai ya ce mata kabarin su ɗaya?.

Har aka kira sallar isha'i amma Aminu bai tashi ya yi sallah ba, ranta in ya yi dubu ya ɓaci. Bayan ta idar da sallar ta fita tw zubo abincin ta zauna tana cikin ci sai fa shi ya fito falon.

"Ni sai na roƙi abincin za ki bani?" Bata ce komai ba ta fita ta kawo masa, yana ci yana danna waya duk ta kasa sukuni ganin yanzu ya fi ba wayar sa muhimmanci a kanta.

Yana gamawa ta kawar da kayan, jin almajiri yana bara ta fita ta karɓi kwanon sa ta juye masa sauran abincin. Bedroom ta koma ta kwanta tana tunanin ko akwai wani laifi da ta masa amma iya tunanin ta bata tuno komai ba.

"Sallamar Yaya Sule da Yaya shafi'u ta jiyo a sashen nasu, wani irin bugawa ƙirjin ta ya yi da ƙarfi, don bata taɓa tunanin zuwan su ba, sai ta fara jin da na sanin sanar da shi ta da so ta yi ya masa magana kamar dai hannun ka mai sanda ashe dai har wani zai gayyato tabbas!. Suna shirin ɗora mata jakar tsaba kaji su bi ta.

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA

WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYATAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****