Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 5

by @mamanafrah3028

Ɗif ta yi kamar ruwa ya ci ta gabanta yana tsananta bugu, tana fatan Allah ya sa wani abu ne da ban ya kawo su ba waccan maganar ba.

Tana jin sa ya amsa musu ciki-ciki shigowa suka yi, tashi ta yi ta lallaɓo take ɗan leƙowa ta tsakanin labule. Kwance yake reran ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Bai bar danna wayar ba kuma bai tashi zaune ba har suka zauna dama sun san hali duk gidan su bashi da kunya ba ya girmama mutane.

"Baka ga mun shigo ba? Kana kwance kenan shigowar tamu ɓangaren ka bashi da wani amfani tun da ga shi ka nuna da shigowar mu da rashin ta duk ɗaya" Yaya Shafi'u da ya ƙulu ya ce yana kallon sa. Ɗan dim ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma dai ya tashi ya zauna ya ajiye wayar yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

"Akwai maganar da ta kawo mu shi ya sa ma ka ganmu a tare don haka kawai ba za mu zo ɓangaren ka ba" Yaya Sule ya ce

"To" Kawai ya ce a taƙaice.

"Kai yanzu Aminu ka yi aure ma ba za ka sauya ɗabi'un ka ba? Mutum yana da iyali amma in kana yin wani abu tamkar dai ƙaramin yaro wani abun ma da kake ƙaramin yaro ba zai yi ba" Yaya Sule ya faɗa.

"To in ban da ma ɓacewar basira ba, kai ma fa yanzu watarana uba ne kana so ƴaƴan ka su taso suke...

"Haba don Allah wai ya za ku zo kuke mini magana a rufe ai gwara ku faɗa mini asalin mai yake tafe da ku amma kuna magana a ƙudundune ina zan gane manufar ku" Ya katse Yaya Shafi'u

Saddiqa da take laɓe tana ganin abin da yake wakana gabanta yana dukan uku-uku, duk mamaki ya cika ta saboda ita sun saba girmama na gaba da su ko yaya mutum in ya girme ka to fa ko da baka san shi ba kana daraja shi amma shi ga shi yayunsa na jini ma tamkar dai shi ne gaba da su ta jinjinawa lamarin ƙurr ta musu da idanu tana jira me zai biyo baya.

"Maganar rashin sallah da baka fita, ko da asuba dukanmu sai mu je masallaci amma kai kaɗai ne baka zuwa" Yaya Shafi'u ya ce

"Kuma batun ƙazantarka dai ashe baka sauya ba sai abin da ya cigaba? Duk faɗan da aka maka ashe bai shige ka ba ta bayan kunnenka ya bi ya wuce..

"Allah na gode maka, yanzu a ce mutum ba zai makara sallaha ba har sai an tuhume sa? Ƙazantar me kuma?" Wannan tambayar da ya yi yana wani kallon jikin sa ita ce ta saka hanjin Saddiqa hautsinawa, tana addu'a Allah sa kar su ce ita ce ta faɗa don yanayin yadda ta ga yana musu magana kamar wasu sa'annin sa ta san ba ma lallai ya ɗauki maganar su ba bare har ya yi aiki da ita.

"Ƙarya za a maka ne, na ce ƙarya za a maka to matarka ce ta kawo ƙaranka a kan a maka maganar kake tsafta ka ga kuwa dole a faɗa maka don ba za a zuba maka ido ka cutar da ƴar mutane ba saboda ƙazanta ai cutar da abokin zama ne" Yaya Shafi'u ya faɗa cikin hargowa.

'Subhanallah! Shikenan sun saka ni a maganar' Saddiqa ta faɗa a zuciyar ta.

"Saddiqa?" Ya tambaya mamaki kwance saman fuskar sa.

"Eh ko kana da wata matar bayan ita?" Yaya Sule ya tambaya yana kallon sa.

"To ko da a ce matarsa bata kawo ƙaransa ba ai ko yanzu komai ya aka kalla wataƙila rabonka da sallaha tun ta asuba ko ma a ce tun ta safe tun da baka je masallacin asuba ba, amma yanzu bari a kira ta waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin ji" Cewar Yaya dama in za a yi sulhu mutum biyu ake haɗawa a ji ta bakin kowa abin da ya sa ma muka maka maganar kai kaɗai saboda wannan sulhun ba ya buƙatar ma sai an ji ta bakin wani don abu ne a bayya ne" Cewar Yaya Shafi'u.

"Wai ni baku san yanzu da kuma da ba ɗaya ba ne? Ni ma yanzu na yi aure don haka a daina biyo ni ana mini wani faɗa don na girmi faɗa, sallah kuma ai Allah ake yi wa ba mutum ba batun tsafta kuma ita Saddiqar za ta faɗa mini sauran bayanan" Ya faɗa a ƙufule yana komawa yadda yake tun farko wato ya kwanta ya ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tare da fara latsa wayar sa.

Lamarin Aminu ya fara basu tsoro ganin haka suka bambame shi da faɗa kamar za su ari baki don yadda ta musu ma in suka kira matar tasa wataƙila su ji kunya don ba ƙaramin aikinsa ba ne ya tsinkasu a gabanta duk da sun san tana ji tun da dai sun san tana cikin ɗaki, basu ƙara ma kallon inda yake ba suka tashi suka fita

Saddiqa da gumi ya gama wankewa tsabar tsoro ta juya da sauri ta koma bakin gado ta zauna, kamar jiran tafiyarsu yake sai ga shi ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi.

"Ashe baki da hankali?" Ya faɗa tamkar zai kai mata duka. Furucin nasa ya bata mamaki duk da ta tsammaci wasu abubuwan amma bata zaci har zai iya alaƙantata da rashin hankali ba.

"Aminu ni kake ce...

"An faɗa miki na ga alama baki san wa kika aura ba, har ni za ki je ki haɗa da ƴan uwana? Har kin kai ki fara bibiyar ƴan uwana kina kai musu maganganu ?Yaushe aka yi daren da har gari zai waye? Yaushe aka yi auren ma, tabbas hakan ya nuna mini ke ba matar rufin asiri ba ce kuma baki da riƙe sirri, tun da har kin kasa jure abubuwan nan tun tafita bata yi nisa ba" Ya tari numfashin ta yana magana kamar zai kai mata duka.

"Aminu ni ce ba matar rufin asiri ba?" Ta tamabaya ranta yana ƙuna tare da nuna kanta da yatsa.

"To matar rufin asirin ce? Har ni za ki je ki samu ƴan uwana ki musu maganar banza kina son ki shiga tsakanin mu ki haɗa mu dama ana cewa wasu matan idan suka auri miji burin su bai wuce su raba shi da kowa nashi shi ya dawo mallakin su su kaɗai. To ki sani ba dai ni Aminu ba har yau baki fahimci wa kike aure ba kuma ina so ki sani tun da har ni kika yi wa haka ƙazanta yanzu na fara babu sauyi ba irin mu ake yi wa abu ta ƙarfi ba"

Tun da ya fara maganganun ranta yake ƙuna ji take tamkar dai ta buɗe ido ta ga mafarki take, wai Aminun ta wanda yake lallaɓata tamkar ƙwai wanda yake son ta shi ne yau yake jifanta da munanan kalamai wai ita ce take son ta raba shi da ƴan uwan sa.

'Ashe dama gyara kayanka yana zama sauke mu raba?' Ta tambayi kanta a zuciyar ta idon ta har ƙwalla ya ciko ta takaicin maganganun sa.

Zuciya ce ta ɗauke ta don ta ga lamarin ya yi tsamarin da sai ta turbuɗawa idanunta toka, idan ta bari abun a haka zai ƙara girma ne ya bunƙasa tun da shi bai ɗauki ma abin da yake yi a matsayin kuskure ba.

"Aminu bari ka ji ni ban auri kafiri ba musulmi na aura don haka dole ka cigaba da amsa sunanka na musulmi ta hanyar kiyaye sallah da kuma tsafta ce jikin ka, shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne kana ganin har akwai matar da za ta jure wannna halayyar? A ce mutum ba zai tsafta ce jikinsa ba wanka wannan ba za ka yi ba bare wankin baki kayanka in wanke maka amma ba za ka saka ba na gaji da maka alkunya dole in fito maka a mutum...

"Kin gaji? To in har kina gani za ki ƙwaci abin da kike so ta ƙarfi ga fili ga mai doki, ko an faɗa miki ana haɗa gudu da susar ɗuwawu ne? Babu gyara haka na ga dama sai lokacin da na ga dama zan yi wanka sannan sallah ina yi kiyaye lokacinta kuma wannan tsakanina ne da wanda ya yi umarnin a yi sallah shi kuma yana gafara amma dai ki sani ba gudu ba ja da baya...

"Wallahi ba zan yarda ba don ƴaƴana ba za su taso su ga wannan rayuwar marar kai da ƙafa... Fuuu ya juya ya bar mata ɗakin, ji take ranta yana ƙuna wai ita ya ce ba matar rufin asiri ba ce, wannan maganar ta fi ƙona mara rai da kuma yadda ya tabbatar mata ba zai canja ba.

Tana jin fitar sa har ƙaran rufe ƙofar da ya yi ta ƙofar gidan hakan ya nuna ficewa ma ya yi daga gidan. Komawa kan gadon ta yi ta kwanta bata san lokacin da wani kuka ya ƙwace mata ba, dama al'adar ta ce matsawar ranta ya ɓaci wani lokacin sai ta yi kuka in ba haka ba bata samun sassauci a zuciyar ta.

Ta jima tana kukan sai da ta ji zuciyarta fess sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Tun tana saka ran dawowar sa amma shiru babu shi har ƙarfe goma ta gota amma bai dawo ba.

Har sha ɗaya saura idon ta biyu, daga nan bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba. Can cikin bacci ta yi juyi ta falka sai kuwa abin da ya faru ya faɗo mata da sauri ta tashi tana ƙarewa wajen da Aminu yake kwance kallo ganin babu shi babu alamar sa. Mamaki ne ya ɗarsu a zuciyar ta tana tunanin shin bai dawo ba ko dai bayi ya shiga?.

Sakkowa ta yi daga gadon bayan ta duba wayar ta ta ga ƙarfe uku da kwata, wutar ɗakin dama a kunne ta bar ta don haka bayin ta nufa ta ɗan ƙwanƙwasa jin shiru ta tura ƙofar amma sai ta ga wayam tsoro da mamaki suka ƙara rufe ta ko ƙofar bata rufe ba ta juya da sauri nufi wayar ta lambar sa ta kamo ta shiga kiran sa don kawai sai ta ji hankalin ta ya tashi don tuni ta manta da abin da ya mata, wataƙila ko son da take masa ne ya danne laifin nasa ko dai ruɗun da take ciki ne ya mantar da ita komai.

Sai da ta kira sau uku wayar tana shiga amma ba a ɗauka ba. Har ta yanke shawarar ta daina kira tun da ba a ɗauka ba sai ta ji ba za ta iya ba hakan ya sanya ta sake kira sai da ta yi sau biyu nan ma babu amsa.

Bata yi tunanin kiran ɗaya daga cikin yayun nasa a waya ta sanar da su ba sai kawai ta yanke hukuncin ta je part ɗin ɗaya daga cikin su ta sanar da shi kar wani abu ya biyo baya a ce da gangan ne bata faɗa ba cewa bai dawo gida ba.

Tana fitowa falon da yake a kunne ta bar wutar falon amma sai ta ga a kashe don ko ta ɗakin bata kashe ba lokacin da za ta kwanta tun da ta san bai dawo ba, ganin ta falon a kashe sai ta yi mamaki matuƙa.

Kunnawa ta yi haske ya gauraye falon kamar an ce ta waiwaya sai kuwa ta gan shi kwance saman doguwar kujera yana bacci hankalin sa kwance. Baki sake take kallon sa ganin ya shigo da wani sabon salo wai kiran sallah da usur.

Bata tashe sa ba sai kawai ta kashe fitilar ta koma ɗakin har za ta kwanta sai ta yi alwala ta yi sallah raka'a biyu ta yi addu'a ta koma ta kwanta a ranta tana mamakin wannan sauyin da ya shigo rayuwar su tun da tsawon lokacin nan basu taɓa raba makwanci da shi ba, amma yau ga shi ya raba musu makwanci.

Da asuba ta tashi ta yi alwala ta tafi falon ta shiga tashinsa ita ma da bata gajiya.

"Mai zan miki ne wai da kike katse mini bacci?" Ya tamabaya a ƙufule.

"Sallah aka kira"

"Za a saka mu kabari ɗaya da ke ne? Ba kin ne kin faɗawa su Yaya Sule ba na sallah ba to yanzu ma sai ki je ki ce gani nan kwance ban yi sallah ba sai su zo da bulala ko?"

"A'a" Ta ce cikin sanyi murya tana jinjina irin yadda yake mata magana cikin hargagi kamar dai ba wannan Aminun da yake son ta ba yake nuna babu mai raba su sai mutuwa babu wanda zai shiga tsakanin su, yana faɗa mata idan sun yi aure za su huta ba za su taɓa yin faɗa ba ba zai taɓa ɓata mata rai ba ba zai taɓa mata kishiya ba da ita kaɗai zai rayu.

Amma ga shi tun ba a je ko ina ba ayyukansa suna ƙaryata maganar sa, na farko dai ya ce ba zai mata kishiya ba sai ga shi tun auren bai je ko ina ba ta kama shi yana kallon hoton mace, sannan ga shi a jiya ya shuka mata kalmomin rashin mutunci tare da gasa mata baƙaƙen maganganu.

"Tun da kowa kabarin sa da ban ki je ki ji da naki kabarin" Maganar sa ta katse mata tunani, yana gama faɗar hakan ya juya mata baya ya kwanta. Jiki babu ƙwari ta juya ta koma bedroom ɗin tana tunanin wane irin miji ta aura? Shin jiya da ya fita ya yi sallar magriba da isha'in ne ko kuwa haka ya gama bulayi ya dawo ya kwanta? In kuwa haka ne ai da sake ta yaya za take zaune da miji ba ya sallah ga baƙar ƙazanta.

Tun da ta yi sujada take addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin lamarin tun da ta ga abu kamar wasa amma ƙaramar magana tana shirin zama babba.

Sai da ta gama karatu gari ya ɗan yi haske sannan ta kwanta. Bacci ya yi awon gaba da ita. Sai wajen ƙarfe tara ta tashi. Ta yi mamakin baccin da ta yi tana hamma ta sakko daga gadon amma tana zuwa falo ta ga Aminu kwance wannan karon ba bacci yake ba idanun sa biyu amma yana danna waya.

Ƙafarsa ta kalla ta ga babu alamar an saka ruwa alamar an yi sallah. Tsabar takaici bata masa magana ba ta koma ta shiga bayi ta yi brush ta wanke fuskar ta tana kallon brush ɗin Aminu har ya fara ƴar ƙura alamar ma ko ta kansa ba a bi.

Kicin ta shiga ta kwaɓa fulawa ta shiga soya musu waina. Sai da ta kammala ta tafasa ruwan shayi ta ɗakko ta taho. ta ajiye abin mamaki sai ta ji ƙaran zubar ruwa a bayi alamar ana wanka. Matsawa ta yi gaban bayin ta ƙara kunne ta ji da gaske wankan yake, hannu ta ɗaga sama tana yi wa Allah godiya, tana tunanin an samu sauyi tun da ga shi ana wanka don ta ji ƙaran dirza soso.

Falo ta dawo ta zauna tana jin daɗi a ranta tana fatan Allah sa maganganun da aka faɗa masa ne suka shige shi. Wayar sa da take kan kujera ce ta fara haske leƙawa ta yi sai kuwa ta ga kira ne yake shigowa da alama wayar a silent take shi ya sa ba a jin ƙaran.

"Ƴar aljanna" Sunan da ta gani yana yawo kenan a saman wayar, hannun ta har karkarwa yake tana mamakin a iya wannan ɗan lokacin da aka ɗauka da yin auren su wace ce wata ƴar aljanna wato saboda matsayin ta har an kira ta ƴar aljanna.

Kallon hanyar bedroom ɗin ta yi sannan ta kasa kunne tana jiyo ƙaran ruwan. Tana shirin ɗaukan wayar ta gudu kicin ta ci mutuncin ta a kan tana kiran mijin ta a cikin gida sai kawai kiran ya katse bata gama dawowa daga mamaki ba sai message ta ga ya shigo hannun ta har karkarwa yake ta buɗe.

"Ya ina kiranka ka ƙi ɗauka, kai da ka ce mini ƙarfe goma za ka zo yau ko wajen sana'a ba za ka je ba" Ganin wannan saƙon ya mugun ɗaga mata hankali tana cikin wanann yanayin ta ji ƙaran buɗe ƙofar bayi alamar ya fito daga banɗakin, message ɗin ta goge.

Da sauri ta tashi daga kujerar ta koma gaban kayan abincin da ta ajiye musu.

'Kenan wannan dalilin ne ya sa ya yi wanka wato wajen wata zai je?' Ta faɗa a zuciyarta.

Shi kuma dama kamar an ce masa ga abun da yake wakana a falon ya taho yana zuwa ya ɗauki wayar ko kallon inda take bai yi ba da harara ta bi shi a ranta tana cewa

'Aikin banza bata san ƙazami bane kai da bata ɓatawa kanta lokaci ba' Ta ce a zuciyar ta. Jim kaɗan zuciyarta ta ce ta leƙe ɗakin ko dai chatting suke tana zuwa ta same shi yana sallah, wai sai lokacin wannan yake sallar asuba.

Falo ta dawo can sai ga shi ya fito sanye da wata shaddar sa da ta wanke masa ta goge, da a ce bata san inda zai je ba da ta ce ya birge ta, yau amma tuno da abin da ƴar aljanna ta ce sai ta ji tana jin haushinsa.

"Ina kwana "Ta gaishe shi ciki-ciki.

"Lafiya" Ya amsa a taƙaice.

Ganin ya nufi ƙofa da alamar fita zai yi ta buɗe baki ta ce

"Ya na ga ka kama hanyar fita ina jiranka mu karya?"

"Ki karya kawai ni na makara a wajen sana'a ta" Ya ce ba tare da ya kalle ta ba kafin ta ce wani abu har ya fita.

Tasowa ta yi ta biyo bayansa ta ce

"Wannan ne shirin zuwa wajen sana'a?"

"Kamar ya?" Ya furta yana haɗe rai.

"Na ga ai ka yi kwalliya kuma ba haka ka saba ba in za ka je wajen kasuwa ba ko dai wani waje za ka je da ban? Kai da ka ce wajen sana'a ba wajen saka kaya wankakke ba ne amma yau har gogagge ka sanya"

"Tuhuma ta kike yi ne? Ni da kayana sai ana tambayata don na saka ba ke kike damuna kullum a kan in ke saka kaya ba"

"Amma da nake cewa ka saka ai baka taɓa sakawa ba sai yau?"

"Haka na ga dama'" Ya ce yana juyawa ya bar ta tsaye da tuƙuƙin baƙin ciki.

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE?

KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH ***

Akwai lesuna shaddodi atamfofi, frames, kayan yara, zannuwan gado, takalman yara da manya, mayafai, tuntu na kwalliyar ɗaki labulaye ga mai son siyen ɗaya ko sari. *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****