Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 7

by @mamanafrah3028

Saddiqa tun da ya hau gadon sai ta kasa ma zaman ɗakin, don yanzu sai ta ji ma kwata-kwata haushinsa ba zai bari ta zauna inuwa ɗaya da shi ba, saboda duk wata kafa da za ta samu farin ciki Aminu ya toshe wannan dalilin ya sa ta ji gabaɗaya auren ma ya fita a ranta.

Falo ta dawo ta zauna ta jingina bayanta da jikin kujerar, tunani ne barkatai suka cunkushe mata, babu abin da take nema illa mafita, tun da ga shi wannan mafitar da ta bi hanyar bata ɓulle ba, tun da ga shi dai Aminun tamkar wanda aka kaɗawa ganga ya nuna ma ba ta ita yake yi ba.

Bata tashi daga wajen ba sai sallah kawai take tashin ta, shi kuma yana kan gadon ya hakimce sai aikin latsar waya yake, ko kallo bai ishe ta ba don yanzu mugun haushinsa take ji.Tana jin sa sai da aka yi isha'i sannan ya tashi ya shiga bayi tana jin motsin ruwa da alama alwala ya yi, bayan ya fito ta ji ɗif bata jin motsinsa hakan ya alamanta mata cewa wataƙila sallolin yake jerowa tun da shi kiyaye lokutan sallah ba ya cikin ɗabi'arsa. Tana nan zaune sai ga shi ya fito, wuri ya zauna cikin dakkakiyar muryarsa wacce ya fara amfani da ita a kwanannan, ya ce

"Ki tashi ki je ki sama mini abin da zan ci" Ya faɗa yana haɗe rai. A ƙufule ta ɗago ta sauke idanunta a kan fuskarsa ta masa kallo ɗaya ta kawar da kanta gefe ba tare da ta furta komai ba, sannan kuma bata yi ko gezau ba bare har ya saka ran za ta tashi ta aikata abin da ya saka ta yi masa.

Sai da ya ɗauki kamar minti biyu bai ce komai ba, yana jiran tsammani daga gare ta ganin bata da alamar motsawa ya sake cewa.

"Saddiqa ba da ke nake magana ba?" Banza ta masa bata ce komai ba.

Ya sake cewa "Kurma ce ke ne?" Ganin bata ce komai ba, sai ya ga ta raina masa hankali a fusace ya tashi ya zo gaban kujerar da take zaune, tsaya mata ya yi a kanta tamkar yana jiran ta masa musu ya hukuntata.

Ya ce

"Saddiqa idan har ba za kike jin maganata ba ban ga dalilin aurenki ba, ina mijinki ina miki magana amma kin mayar da ni tamkar mahaukaci?" Ya kai ƙarshen maganar yana wani huci tamkar zaki. Cikin halin ko in kula ta ɗago kai ta kalle shi a raine ta ƙara kawar da kai.

Hannu ya kai ya dunguri kafaɗarta, kamar jira take ta zabura ta miƙe tsaye, hannu biyu ta saka ta riƙe ƙugu da yake ma kusa da kusa suke sai ya zama tamkar jikinsu zai gogi juna saboda kusancin.

Saddiqa ta ce

"Wai ya za ka zo kana mini magana cikin ɗaga murya? Magana kaɗan sai kake cewa ko ba zaman aure na zo ba? Wanann tambayar ai ba sai ka tambaye ni ba, kai kanka kana da amsarta in auren nazo in akasin haka" Ta faɗa cikin tsiwa. Baki sake yake binta da kallo kuma sai ya ji yana shayinta amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai ya kalleta cikin dakiya ya ce

"Ni kike wa magana haka gatsal kamar wani sa'anki Saddiqa?" Bata ce komai ba sai wani yatsina fuska take.

"Ki wuce ki dafa mini abinci"

"Ai tun da na dafa maka abinci da safe ka ƙi ci, ka fita ka tafi wajen wata banza ca... Kafin ta kai ƙarshen maganar hannun da Aminu ya kawo sai wanke kyakkyawar fuskarta da mari shi ya dakatar da ita daga maganar, cikin sauri ta durƙushe hannun nasa ya mari iska ɗagowa ta yi tana mai ƙanƙance ido ranta fal mamaki.

Aminu kuwa hannun ya mayar bayansa da sauri, gabansa yana faɗuwa ganin kuskuren da ya kusa yi, wanda hakan ba tare da saninsa ya yi ba zuciya ce ta ɗauke shi jin an kira masoyiyarsa da banza, wacce yake so da ƙauna kuma ba ya son duk wani abu da zai taɓa ta. Son da yake mata ne ya sa yake kiranta da ƴar aljanna, sannan abin da Saddiqa bata sani ba shi ne, a rashin uwa aka yi uwar ɗaki, ma'ana Aminu ba ita ya so ya aura ba sanadin budurwarsa Khady an ce karatu za ta yi a gidansu, wannan dalilin ya sa ya auri Saddiqa duk da ita ma soyayya suka yi amma ya yi wa Khady alƙawarin tana kammala karatu za su yi aure don ita ma Aminun ne zaɓinta.

"Aminu ni za ka mara?" Ta faɗa a ƙufule tana nuna kanta da yatsa, har lokacin tana cike da ɗinbin mamaki don bata taɓa zato ko a mafarki zai tarki kai hannunsa jikinta ba.

"Ba da niyya na yi ba" Ya faɗa yana ɗan wayincewa don ya san bai kyauta ba.

"Hmmm!" Ta ce tare da yin ƙwafa ranta yana mata ƙuna.

Ta ce "Wannan ya zama na farko sannan karo na ƙarshe da za ka yi tunanin kai hannunka jikina, babu wajen duka a jikina ko da kuwa ɗan yatsana ne bari fuska, wacce take cike da daraja" Ta ce tana kallon yadda duk ya diririce bata wani jira cewarsa ba ta raɓa jikinsa ta shige ɗaki, don bata jin akwai wani abu da ya yi saura wanda za ta saurara daga gare shi.

Tana shigewa ɗakin ya sauke wata ajiyar zuciya, zamewa ya yi ya zauna a kan kujerar yana jin rashin kyautawar da ya yi daɗin da ya ji ma shi ne da Allah ya sa hannun nasa bai samu fuskarta ba.

Saddiqa kuwa tana shiga ɗaki sai ta zauna a kan gadon ranta yana mata ƙuna, hannu ta kai ta shafo fuskarta mai laushi da santsi wacce a baya take ganin duk namijin da ya aure ta laushin fatarta kaɗai ma ya isa ya girmamata amma sai ga shi yau an kusa sauke mata yatsu biyar a fuskar.

A zuciyarta ta ce 'Mai hakan yake nufi ne, kenan Aminu banda ƙazanta, rashin kula da ibada hallaw namiji ne mai dukan mace?' Akiyar zuciya ta sauke a fili ta sake rayawa a zuciyarta ta ce

'Ba zan taɓa lamuntar hakan ba, dole da sake ni ba matar duka ba ce don ba zan zauna ina gani ba ya kashe ni da raina, da yarintata amma ya tsufar da ni da ƙazantarsa' Filo ta ja ta ɗan kishingiɗa zuciyarta tana tunano mata irin soyayya da ƙaunar da suke wa juna ita da Aminu wacce ta kai su har ga turbar aure. Juyi ta yi tana ƙara tafiya duniyar tunano wace ce ni.

Sunana Saddiqa ni ce ƴa ta farko a gidanmu sai ƙanwata Asiya muna kiranta da Noor. Mun taso cikin gata da tarbiya duk da iyayenmu ba wasu masu ƙarfi bane, amma dai suna da rufin asiri daidai gwargwado. Iyayanmu sun tsaya kai da fata wajen bamu ilimin boko da na arabiya.

Mahaifiyarmu da muke kira da Mamy, mace ce mai haƙuri da sanya idanu a kan ƴaƴanta duk abin da muka yi na kuskure sai ta nuna mana, idan kuma muka yi abin kirki tana yaba mana fiye da abin da muka yi wannan abin yake sanyawa, mu sake ɗaure ɗamarar yin wani abun kirkin. Mamy mace ce mai tsafta, tsaftar jiki da ta muhalli zan iya cewa ni ce na biyo ta don ni tawa tsaftar har ta so ta yi yawa don bana ƙaunar ƙazanta ko wanda ya haɗa hanya da ƙazanta.

Hakan ne ya sa, ƙanwata Noor take kirana da sarkin tsaftar gidanmu, duk da ita ma tana da tsafta daidai gwargwado amma ni na dame ta na shanye. Tin kafin in gama secondry school muka yi saukar qur'ani a islamiya, duk da Mamy ita ce makarantar farko da take koya mana karatu, saboda haka ma ko a makaranta za a karɓa harda sai a ji na fi kowa iyawa ita ma Noor a nasu ajin haka ne.

Ƙawata ɗaya Mubina, da yake ni ban cika son tara ƙawaye barkatai ba, ina kammala secondry school Abba ya saya mini waya sannan ya bami damar in kula samari sai dai ya gargaɗe ni cewa bai yarda in tara samari ba, duk da ya san ni ma ba abu ne da zan yi ba sai dai ya yi hakan nr don fita haƙƙina. Saurayina na farko sunansa Kabiru na haɗu da shi ne wataran Mamy ta aike ni gidan ƙawarta, tun da muka haɗu muka ƙulla alaƙar soyayya duk da ban ji ya kwanta mini ba, amma ganin yana ƙaunata sai na kasa bayyana masa, sai dai yana da aure da ɗansa guda ɗaya.

Muna waya sannan yana zuwa gidanmu zance, mun yi wajen wata huɗu da shi muna tare, don har yana shirin aiko da mayansa su yi magana da Abba, kwatsam mummunan labari ya riske ni daga abokinsa Hamidan Kabiru ya samu mummunan hatsari inda motar d yake ciki ta kama da wuta, sanadin buguwa da wata motar homa wacce ita ma ta ƙone ɗin.

Labarin nan ya gigita ni, ya hautsina mini tunani, inda na ji komai na duniya ya daina mini daɗi dama ai ɗan adam ba komai bane, sai nake tuna lokacin da ya mini waya yana faɗa mini tafiya ta same shi ashe dai ajali ne ya yi kira, tafiya ba ta dawowa ba ce.

Tun bayan mutuwar Kabiru sai na daina kula kowane namiji, sai in ke ganin kamar shi ma sai na saba da shi zai mutu ya bar ni, sai da Mamy ta dage sosai da mini nasiha sannan na fara kula wasu. A watarana da ba zan taɓa mantawa ba, ranar juma'a da yamma na je gidansu ƙawata Khady Mamarta da bata da lafiya, a hanyata ta dawowa na rasa napep ina tafiya ina son isa gida kafin magriba, wata daddaɗar murya ta mini sallama a bayana, da farko ban tsaya ba kuma ban juya ba. Jin mamallakin muryar bai daina bina ba don ina iya jin takun tafiyarsa sannan sautin muryarsa ina ji yana matsowa dab da ni, wannan alama ce ta cewa yana biye da ni.

Ganin dai abin nasa ba na ƙare ba ne, da yake kuma layin ma babu mutane sai jefi-jefi suna giftawa, dakatawa na yi amma ban juyo ba.

Sai ji na yi ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga wannan halitta, alkairi da albarka su lulluɓe ki ke da ahalinki baki ɗaya" ,Na ji sautin muryar yana shiga kunnuwana a hankali.

A karo na biyu ya ce "Ina neman afuwa na yin laifin tsayar da kamilar mace a hanya, ina neman yarda da amincewa domin a bani mintina biyu zuwa uku na bayyana abin da yake tafe da ni, ina fatan hakan ba zai sa a gajiya ba sannan ba zan shiga rayuwar gimbiya ba" Daɗin muryarsa da iya tsara kalamansa su suka sanyaya zuciyata har na ji ko da a ce abin da ya yi laifi ne to tabbas! Na yafe masa.

Ya sake faɗin "Ba don idan kika kuɓuce ban san ina zan sake ganinki ba, to da babu yadda za a yi in tsayar da kyakkyawar mace mai cike da kamala da haiba a hanya"

Ji na yi idanuwana suna son yin arba da wannan bawan Allahn, a hankali na shiga juyowa har sai da na juyo duka na, a kan fuskarsa na yi wa idanuna masauki inda na ga idanunsa a rufe sannan hannayensa biyu a haɗe waje ɗaya alamar roƙo.

Ban san ya aka yi ba sai na ji magana ta fito daga bakina kamar an fisgota na ce.

"Kai ma amincin Allah ya tabbata a gare ka" Na faɗa cikin sassanyar muryata. Idanunsa na ga ya buɗe a hankali wanda hakan ya sa ni kuma na sunkuyar da nawa idanun, saboda sai na ji nauyinsa da kunyarsa sun lulluɓe ni.

Sai ji na yi ya ce "Sunana Aminu don Alah ina neman alfarma idan ba damuwa ki bani lambar wayarki, sannan ki faɗa mini sunan unguwarku"

Kasa masa musu na yi, saboda ni ma sai na ji ya kwanta mini a rai. Lambar wwayar na bashi tare da faɗa masa sunan unguwarmu, godiya ya hau yi kamar zai ari baki. Murmushi kawai na masa tare da juyawa na cigaba da tafiya amma dai shi na ga ko gizau bai yi ba, a tsaye na bar shi a wajen kamar gunki na san kuwa ni yake kallo.

Tun da muka rabu bai kira ni ba, har aka yi kwana biyu ga shi zuciya da bata da ƙashi sai nake ta tunaninsa, ko kirana aka yi a waya sai in zaci shi ne, sai a rana ta ukun bayan magriba ya kira ni tun da ya yi sallama a wayar na gane shi ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Mun daɗe muna hira tamkar mun saba da juna daga ƙarshe muka yi sallama ya ce gobe zai kawo mini ziyara.

Wannan shi ne farkon alaƙata da Aminu, shi ne mafarin soyayar da har ta kai mu ga aure, duk da bayan mun yi nisa a son juna ya sha faɗa mini wai ba ya son sunayen soyayya mace take kiransa da su da farko na ɗauka ma wasa yake sai ga shi a ranar da na tare a gidansa ma matsayin amarya ya maimaita mini kalmar.

Ƙaran wayar Aminu da ya karaɗe falon shi ya dawo da ni daga nisan kiwon da na tsunduma cikin tunani, kwanciya na gyara ina jin duk jikina ya mutu don lamarin Aminu abin ya yi tsamarin da sai dai in ce Allah mini maganin matsalata. Tun da wayar ta fara ƙara ba a ɗauka ba saboda ina jin ƙaran bata daina ba, juyi na yi haɗe da jan ƙaramin tsaki a zuciyata.

Wani kiran ne ya shigo a karo na biyu wannan lokacin ƙaran bai wani ɗauki lokaci yana yi ba, sai na ji ɗif. Bayan kamar minti uku sai na yanke shawarar zuwa kicin in haɗa shayi in sha, fitowa na yi amma abin mamaki falon wayam babu Aminu babu alamarsa, baki ta taɓe ta fito ta saka takalmi ta nufi kicin ɗin sai dai tana dab da shiga kicin ɗin ta jiyo dirin muryar Aminu yana magana da alama waya yake, mamaki ne ya baibaye ta sai dai ba wannan ne ma abin dubawar ba kalaman da ta ji yana faɗa a wayar ne ya matuƙar razanata, ji ta yi tamkar an buga mata guduma a kanta nan take wani abu ya mata tsaye ya tokareta a maƙoshi, jikinta ya ɗauki karkarwa...

MAMAN AFRAH ***

*TALLA !TALLA!!!*

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE?

KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH *** [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****