Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 6

by @mamanafrah3028

Tun da ya fice ta juyo jiki babu ƙarfi ta dawo falo ko kallon kayan abincin bata yi ba wani kishi ya tokare mata maƙoshi, kan kujera ta faɗa ta kwanta tare da kifa kanta ta fashe da wani kuka. Sai yanzu take tuna irin yadda ake labarin irin yadda maza suke wujijjiga mata a gidan aure, sai ta ji ana cewa wuyarta a yi auren shikenan namiji zai juya maka baya.

Ga shi dai yanzu ba a je ko ina ba abubuwa sun fara cunkushewa, wai duk irin yadda Aminu ya nuna mata soyayya da kulawa amma yanzu daga yin auren a ce har ya sake wata budurwar wai har yana saving lambar ta da ƴar aljanna. Kenan me yake nufi da hakan? Ita ƴar ina ce tun da yana da ƴar aljanna.

'To kika sani ma ko tun kafin ya aure ki yake tare da ita, ai kaɗan daga aikin namiji kawai ki kalli namiji, don namiji karatun sa ba zai taɓa ƙarewa ba, ai namiji halayensa littafi ne guda mai ɗauke da tarin takardu da kuma dogayen shafukan da ba a ƙare karatunsa bare a gama fahimtarsa' Wani ɓangare na zuciyar ta ya bata amsa.

Sosai ta shiga damuwa ganin ita tana ta fama da shi ya sauya halayyarsa ta ƙazanta da tsakaninsa da ubangiji, amma bai ji maganar ta ba ko don haƙƙinta, sannan yanzu ya ɗauki kayan da ita ta sha wahalar wanke su da goge su duk don ta faranta masa, amma a ƙarshe sakayyar da zai mata da ya saka su wajen mace zai je, tun da gashi nan tas kamar dai ba wannan Aminun da yake zaune da ƙazanta ba yana warin dauɗa.

Tana nan tana ta saƙa da warwara ta kasa jurewa don sai zuciyar ta take ta raya mata cewar yanzu fa yana can tare da wata, wataƙila ma yana ta mata murmushi. Waya ta ɗaga ta shiga kiransa amma har ta tsinke ba a ɗauka ba, bata daddara ba dai ta shiga kira a karo na biyu amma amsar ɗaya ce no answer.

Tana riƙe da wayar bacci ya yi awon gaba da ita bata tashi ba sai sha biyu, ta yi mamakin irin baccin da ta yi. Haka ta tashi zuciyar ta duk ba daɗi, kayan abincin nan ta kwashe ta mayar kicin don yadda take jin zuciyar ta ba za ta iya cin wani abu ba.

Dawowa ta yi da nufin ta gyara ɗakin, tun da yau babu abin da ta tsinana, bedroom ta shiga tana shiga ta ji wani irin wari ya haɗe ɗakin. Fuska ta yatsina tana ɗaɗɗaga hanci tana son gano daga inda warin yake amma ta kasa ganewa sai take ma tunanin ko ɓera ne ya mutu.

Ganin gajeran wandon Aminu da ya cire da singlet da alama wasu ya saka, sai da zuciyar ta ta tashi ganin farar singlet ɗin ta yi wani irin datti har ta zama milk ta ƙarfi da yaji. Da tsantsani ta ɗauke su ta ta kai hancin ta wai ko warin su ne ya haɗe ɗakin amma sai ta shaƙi warin dauɗa da na gumi da sauri ta kawar daga wajen hancin ta.

Kayan wanki ta jefa su ta dawo tana duba inda warin yake. Sai da ta duba har bayan drower da ƙasan gado, ta yi ta duba ɓera amma ta sha binciken ta bata ga ɓeran ba.

Dakyar ta iya share ɗakin saboda yadda warin yake damun ta ta rasa daga ina ne kuma.

Da ta gama gyaran sai ta cire kaya za ta shiga wanka, tana buɗe banɗakin wani irin wari ya bugi hancin ta. Sai yanzu ta gane daga inda warin yake sai dai ta yi mamakin jin wari a banɗakin domin kuwa bata barin banɗakin da datti, dama yanzu ma nufin ta idan ta shiga ta wanke banɗakin sai ta yi wanka.

Sai da ta toshe hancin ta ta iya shiga bayin tana tunanin a banɗakin ne dama ɓeran ya mutu.

Duk ta duba babu ɓera babu alamar sa, ganin an rufe toilet (Shadda) Da murfin sai ta buɗe. Abin da ta gani ne ya ɗaure mata kai. Kashi ne Aminu ya yi bai yi floshing ba. Da sauri ta danna wajen floshing ɗin kashin ya tafi da ɗan gudu ta fito daga bayin, bata tsaya a bedroom ɗin ba sai falo ta taho saboda yadda ta ji warin duk ya ɗumame ɗakin.

Idanun ta har ƙwalla suka kawo tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce a ce mijin ka bashi da aiki sai ƙazanta, har ta kai a ce mutum ya yi kashi amma ba zai zuba ruwa ba ya tashi ya bar shaddar a haka, to wa kenan yake son ya yi floshing ɗin?.

Ta jima a nan sai da ta tabbatar zuwa lokacin warin ya fita sannan ta je ta wanke bayin ta yi wanka.

Bayan ta shirya ta fito sai ta nufi kicin ta dafa indomie ta dawo ta zauna ta ci, don ta lura in ta ce saka damuwar ɗa namiji a ranta ne zai sa ta daina cin abinci to tabbas!. Tana dab da komawa kamar tsinke don rama ko dai ulcer ta kama ta,.

Ana kiran sallah ta ɗaura alwala ta gabatar da sallah, don ita bata wasa da sallah ko kaɗan, lokaci yana yi take yi bata yarda ta saɓa lokacin sallah ba.

Har aka yi la'asar Aminu bai dawo ba, ganin zaman ya gundure ta kuma tana ta saƙa da warwara sai ta ɗauki hijabi ta saka ta nufi part ɗin Amina don ita Sumayya yau ta tafi gidan su wuni.

Da sallama ta shiga Amina tana zaune tana cin jallof na shinkafa wanda ya sha alayyahu.

"Inyee yau amarya ce da kanta" Ta ce tana dariya.

"Ni har wani kai gare ni" Ta faɗa tana zaunawa fuskar ta ɗauke da murmushi.

Sun shiga yin hira inda take tambayar ta Yusuf da Albani ta ce mata da Baban su zai fita ya tafi da su ya miƙa su gidan su. Suna ɗan tattaunawa Saddiqa sai ta ji Amina ta ce

"Kai gaskiya Saddiqa kina ƙoƙari"

"Ƙoƙarin me?" Ta tambaya cike da rashin fahimta.

,"Zama da Aminu mana"

"Ban gane ba?"

"To miji ƙazami ai sai ka jinjina zama da shi, don dai ni ina son ƘAZAMIN MIJI, saboda babu ruwanki da ciwon kai wato duk namiji mai ado da kwalliya ɗan ƙwalisa ƴan mata kullum suna kai masa farmaki" Bakin Saddiqa buɗe yake wayam tsabar mamaki ta rasa mai za ta ce.

"Ni yanzu da nake tare da wannan mijin nawa mai shegen tsaftar jaraba, koyaushe cikin ado da kwalliya kin ga kowace mace ta gan shi dole ta ƙyasa wallahi shi ya sa wani lokacin sai in ce duk macen da ta auri ƘAZAMIN MIJI ta huta"

'Ikon Allah wato dai ita magana sai ka barta iya kai kaɗai ne take sirri? Daga ka fitar ka faɗawa wani shikenan ba sunan ta sirri ba za ka iya tsintar ta a ko ina ma' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta tana mamakin ashe dai Yaya Sule ya kwashe maganar da ta faɗa masa ya faɗawa matarsa, saboda ita dai ta san bata taɓa wannan maganar da ita ba, sannan duk da suna zaune a gida ɗaya ko da za a ce ita Aminar ta ga wasu alamomi a jikin Aminu wanda ya danganci ƙazanta ai ba za ta tunkare ta da maganar ba.

Shi ya sa ake cewa kowa da abokin zancen sa, idan ka faɗawa wani sirrinka ko da ka ce kar ya faɗawa kowa shi ma in ya tashi faɗawa wani sai ya ce masa kar ya faɗa, shi ɗin ma idan ya ba wani labari sai ya ce kar ya faɗa, a haka maganar za ta yaɗu baka ankara ba sai ka ji ta je inda baka yi zato ba ko da bata dawo kunnen ka ba to wanda suka sani za suke kallon ka da abun.

"Ai ni tun da ya ce wai kin kawo ƙaran Aminu a kan rashin tsafta na ce masa dama ni ce" Maganar Amina ta katse mata zancen zucin.

Murmushin yaƙe Saddiqa ta yi ta ce

"Haka ne kam kowa ai da ra'ayinsa kuma ai da aka masa maganar ma ya ce zai gyara"

"Amma kuma ya ce mini baram-baram suka rabu bai Aminun bai amsa laifinsa bama?"

'Wato dai sai da ya kwashe komai ya faɗa mata?' Saddiqa ta ce a zuciyar ta.

"Bari in je kar ya dawo na ga lokacin dawowar sa ya yi" Saddiqa ta ce cikin sanyin murya ta mata sallama ta baro sashen ranta cike da haushin abin da Yaya Sule ya yi, dama an ce wasu mazan sai sun kwashe komai sun faɗawa miji, su ma wasu matan haka suke kwashe zance su faɗawa miji ko da kuwa sirrin gidansu ne shi ma mijin haka ne, amma bata zaci Yaya Sule zai faɗi sirrinta ba gashi facala ce watarana za ta iya yi mata gori.

Ta fito sai ga Sumayya ta shigo gidan.

"Amarya mai daɗin tuwo"

"Ni dai na rasa ranar da sunan nan zai canja zuwa asalin sunana" Ta ce tana ƴar dariya.

"Ina!. Ai sunan nan in kin ga an daina faɗa miki, sai ranar da Aminu ya rambaɗo miki amarya wato ya miki kishiya, sannan ne sunan ki zai tashi daga amarya ya koma uwar gida ita kuma ta zama amaryar" Sumayya ta faɗa cikin wasa.

Dammm!. Ƙirjin Saddiqa ya buga jin wannan furucin na kishiya, a take sunan ƴar aljanna da ta kira Aminu kuma ta turo masa saƙo ya faɗo mata, lokaci guda ta ji komai ya tsaya mata kishi kumallon mata.

"Gaskiya haka ne fa" Ta faɗa tana yin murmushin yaƙe.

"Ruma ƴan mata" Ta ce tana kallon Ruma da take cin biskit. Ta faɗi hakan ne don ganin ta kawar da waccan maganar.

"Gata nan!. Bari mu shiga mu fatsar don a ƙafa muka taho" Sumayya ta ce tana yin gaba. Ita ma nata ɓangaren ta nufa tana jin yau tamkar bata fito a sa'a ba don duk maganganun facalolin nata basu mata daɗi ba. Yanzu ta fara tunanin Allah sa dai shi ma Yaya Shafi'u bai faɗa wa Sumayyar ba, duk da ita ma ƙazamar ce.

Ta shiga kenan jim kaɗan sai ya shigo da sallama, da sauri ta fito falon amma abin da ya bata mamaki ganin duk fulawa a jikin sa. Tambayar kanta ta shiga yi kenan dama kasuwa ya tafi? Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ta yi tunanin ko dai bai je wajen ƴar aljannar ba.

'Ko dai sai da ya je can ya tafi kasuwa?,' Wani sashen na zuciyarta ya faɗi hakan.

"Sannu da zuwa" Ta faɗa ganin ya zauna a kujera yana ambaton wash!. Alamar gajiya.

"Yawwa" Ya amsa a taƙaice.

"Kawo mini abinci" Ya furta fuskarsa babu walwala don ta lura tun da ya shigo sai wani cin magani yake.

"Ban dafa ba"

"Kamar ya?" Ya ce yana wani yatsina fuska.

"Kamar yadda ka ji mana, da safe da na dafa abincin ka ci?

",Don banci ba sai a ƙi dafa mini wani abincin, wa yake nemo mini?"

Kalaman nasa sun daki zuciyarta kuma ta san ba ita take nemowa ba, amma da yake ita ma dama a cike take da shi sai cewa ta yi

"Ni ba baiwa ba ce da zan ke girka abincin da ba ci za a yi ba, idan na girka an ci zan sake wani in kuma ba a ci ba to ba zan sake yin wani ba" ,Kallon ta yake yana mamakin furucin ta.

"Saddiqa yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?" Kai ta ɗauke gefe ba tare da ta ce masa komai ba.

"Ni nake auren ki ba ke kike aure na ba, don haka abin da na shimfiɗa a cikin gidana shi za a yi"

"Ai ni tunanina inda ka tafi an baka abincin a can" Shiru ya yi yana nazarin kalaman ta.

"Kenan dama ke ce mai rawar kan da ta goge saƙon da aka turo mini a wayata? Har kina da damar taɓa mini waya da goge abin da aka turo?" Ya ce yana jifanta da wani kallon rainin hankali da ta ji tamkar ta wanka masa mari.

"Ashe dai an turo ɗin, ai na gani kuma na goge" Ta ce tana wani ƙanƙance ido don ta lura in tana ɗaga masa ƙafa kowane datti ya kwaso a kanta zai juye.

"Ina so ki sani babu wata mace da za ta juya ni, don haka in zaman aure kika zo yi ki yi abin da ya kawo ki, in kuma ba shiya kawo ki ba to sai ki yi sa idon, amma ki sani saka idanun ki ba zai taɓa amfanar da ke komai ba sai wahala da ɓacin rai, don saka idonki babu abin da zai sa kuma babu abin da zai hana" Yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe ya nufi hanyar ɗaki.

Sosai ranta yake zugi, take tunanin mai ya sa yanzu Aminu yake fito da wasu sabbin halaye wanda bata taɓa kawo yana da su ba? Shin daman da ake cewa sai zama ya haɗa ake gama sanin halayen juna hakan ne?.

Fuuu ta bi bayan sa cikin ɗakin ta ce

"In ba zaman aure na zo ba to me na zo yi? Mai ya sa za ka ɗauki tsauraran kalamai kake jifana da su? Ko dai har ka fara gajiya da zama da ni...

"Ba na son maganar banza ni ina da aikin yi, sannan daga yau sai yau babu ke babu faɗawa ƴan uwana zancena kin saka sun je gida sun faɗa an mini faɗa, to ke baki isa ki raba ni da ƴan uwa da iyayena ba, abu na gaba babu ke babu taɓa wayata don ban miki lamuni ba!."

Idanun ta ne suka ciko da ƙwallah amma ta maje, ta ce

"Ban ga wanda ya isa ya hana ni taɓa wayar ba, kuma laifi in ka ga ba a faɗa ba to ka tabbatar da cewa baka yi abin faɗar bane" Ta faɗa rai a ɓace don furucin sa na cewa babu ita babu wayar sa ya bala'in ɓata mata rai gani take ya hana ta taɓa wayar ne don yake cin karensa babu babbaka, wato yake ajiye hotunan ƴan mata yana waya da su, sannan suna aiko masa da message ita tana nan ya kasa gyara alaƙarsa da ita.

"To ga wurin nan za ki gane shayi ruwa ne"

"Kuma wallahi daga yau kar ka ƙara bar mini kashi a banɗaki don ni ba baiwarka ba ce" Ta faɗa cikin hargowa.

Banza ya mata ya hau gado ya kwanta wani haushi da takaicin sa yana cika mata zuciya. Musamman na rashin yin sallah ga shi kuma ya shigo da batun kula ƴan mata bayan ita kanta da take cikin gidan. Ba daɗinsa take ji ba a karo na ba adadi ta yi da na sanin auren Aminu don auren namini ƘAZAMI kuma marar addini ba ƙaramin abu bane.

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE?

KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH ***

[4/17, 9:33 AM] ***: *KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****