Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 8

by @mamanafrah3028

Gabanta yana mugun faɗuwa ta ji yana cewa

"Haba ƴar aljannata ke kin san aure tsakanina da ke babu fashi, duk wata mace a doron duniya ai sawu take take miki domin kuwa bayanki take bi ke kin sani ina son ki!" Dam ƙirjin Saddiqa ya cigaba da bugawa, lokaci guda ruwan hawaye suka ciko a idanunta ta fara tunanin kenan har an ci moriyar ganga za a yada korenta.

A zuciyartw a ta ce 'Yanzu Aminu har ya fara tunanin yi mini kishiya daga yin auren namu da watanni? Wato duk wata mace bayanta take kenan har ita da take matsayin matarsa wata can banzar bazara ta fi ta?' Ta jefawa zuciyarta tambayar.

Ta ƙara jiyo muryarsa yana faɗin "To ya kike so in yi yanzu ma fa ina kicin na laɓe saboda kawai in yi waya da ke, don tun da na dawo take masifa in taƙaice miki ko abinci bata dafa ba saboda baƙin kishinki da take yi, wai saboda ta karanta saƙon ki da safe"

Jin sa ya cigaba da faɗin "Ai ni ban san haka take da masifa ba, rabu da ita an ce mata namiji mijin mace ɗaya ne? Ai duk abin da za ta yi ihu ne bayan hari" Bayanta ta jingina a jikin bango tana jin ciwon tononon sililin da yake mata a wajen budurwarsa duk da har da ƙari ya yi, amma a nata ganin bai kamata yake bankaɗawa budurwarsa sirrin gidansa ba.

Jin yana ta lallaɓa budurwar tasa sai ta ji ba za ta iya jurewa ba, hakan ya sa ta durfafi cikin kicin ɗin. Ganinsa ta yi ya juya baya yana can ƙarshen kicin ɗin ya saka kansa daga lungun tsakanin loka da bango.

Aminu da ya sha'afa yake hira abinsa don bai taɓa sanin za ta zo kicin ɗin a wannan lokacin ba. Jin motsin shigowar mutum kicin ɗin tsabar yadda gabansa ya buga sai da wayar ta suɓuce, don kaɗan ya rage ta faɗi amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai ya yi saurin wayincewa yana cewa.

"Ina jinka inusa dama idan na dafa ruwan zafin zan gasa wajen, tun da ina ga ƙashin wajen ne ya yi sanyi" Ya dage yana faɗa tare da juyowa ya kashe wayar ma. Kallon Saddiqa yake wacce ta baiwa bango ajiyarsa tea flacks ta ɗauka da kofi ta zuba suga da lifton ta ɗauka, tana daf da fita daga kicin Aminu da ya fara ƙoƙarin haɗa haruffa daƙyar ya yi ƙarfin halin cewa.

"Dama hannuna ne yake ciwo to sai na tambayi Inuwa shi ne ya ce in gasa wajen da ruwan dumi da ɗan gishiri" Ko kallo bai ishe ta ba don gani take ma ɓata lokacinta za ta yi, ko kuma idan ta buɗe bakinta bata san mene ne zai fito ba kai ta saka za ta fice daga kicin ɗin. Aminu da yake ganin kamar tana masa kallon tuhuma, duk da a ransa bai kawo cewa ta ji abin da ya ce ba don a nasa ganin in har da ta ji abin da yake cewa ya san da sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci.

Ƙaran da wayar ta ɗauka ne ya sa Aminu saurin danne makunnar kiran ya katse, ita kuwa ko kallonsa bata sake yi ba ta bar masa kicin ɗin. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana jin har lokacin gabansa bai bar faɗuwa ba, don shi abu ɗaya ne ma ya ƙara tsorata shi ne ganin a kicin yake kar ta ɗauki wuƙa ta burma masa saboda ya sha jin labarin matan da suke kashe maza saboda kishi.

Lallaɓowa ya yi sai da ya leƙo kansa a hankali, ya ga bata nan, sannan ya koma kicin ɗin, ganin kiran yana ƙara shigowa da sauri ya ɗauka, yana karawa a kunnensa ya ji ta ce

"Sannu ɗan aljanna yanzu ni ce ma Inuwan?"

Cikin son lallashinta ya ce

"Haba ƴar aljannata wa ya ce miki haka, wallahi Saddiqa ce ta yi wa kicin ɗin dirar mikiya kawai sai ganinta na yi kamar an jefo ta" Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa don ya ƙosa su yi sallama kar Saddiqar ta sake dawowa, saboda tun yadda ta sauya ɗazu da ya kusa kai hannunsa jikinta sai yake ɗan shayinta.

Sai ji ya yi ta ce"Ikon Allah na kwance ya faɗi, yanzu kai kuma mijin ta ce za ka zama ko mene ne wannan ɗin, kai da kake da tsarin mace biyu amma kake tsoro to wallahi tun wuri ma in bacci kake ka falka amma tabbas akwai aiki ja a gabanka"

Cikin ƙarfin hali ya ce

"Ba fa tsoronta nake yi ba ai ni daga ganina kin san cikakken namiji ne mai kwarjini da haiba, na fi ƙarfin mace ta juya ni"

Ƙwafa ta yi sannan ta ce

"To a dai juri zuwa rafi don watarana tulu zai fashe" Bai biya ta ba don burinsa yanzu su yi sallama saboda ya koma ɗakin, kar Saddiqa ta yi tunanin wani abu da ban saboda sai da ya ji dama fita waje ya yi idan ya gama wayar ya dawo.

Wani ƙaramin ƙyalle da ya gani ya ɗauka tare da wata ƙaramar roba, fitowa ya yi ya dawo falon, zaune ya same ta tana kurɓar shayin da take jin tamkar maɗaci ne take sha, gabaɗaya ranta a cunkushe yake ta kasa gane wane irin zaman aure take yi lallai ta yarda maza su ba ƙwarya ba ne bare a ƙwanƙwasa a ji. A yadda take kallon Aminunta bata ɗauka za ta samu wata kasawa ko gazawa daga gare shi ba, amma sai ga shi hakan ta faru a kwana kusa.

Ji ta yi ya ce

"Bari na tsiyayi ruwan nan" Ya faɗa yana ɗaukan flacks ɗin, a gefe ɗaya yana satar kallonta ta wutsiyar ido amma sai ya ga kamar dai bata ki mai yake faɗa ba, duk da dai yanayinta bai nuna masa ta nuna wata alama da za ta alamta masa ta ji wayar da yake yi ba, amma dai ya fi zargin abin da ya faru tsakaminsu ɗazu ne yake kai kawo a birnin zuciyarta.

Ɗan gefe ya matsa ya zauna ya shiga tsoma ƙyallan nan yana matsewa sai ya ɗora a hannunsa, kallon gefen ido ta masa tare da taɓe baki don ta fahimci babu wani ciwo a tare da shi. Tana gama shanye shayin ta ɗauki kofin da flacka ɗin ta mayar kicin. Ɗaki ta koma ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel ta shiga bayi ta yi brush tare da yin wanka, fitowa ta yi ta ɗauki wata rigar bacci iya gwiwa ta sanya.

Jikinta ta feshi da turare ta ɗauki wayarta da take kan madubi, har za ta hau gadon kawai sai ta ga duk dattin ƙafar Aminu da kuma farin fulawa ya ɓata zanin gadon ƙyanƙyami irin nata sai ta ji ba za ta iya kwantawa ba, cirewa ta yi ta ɗakko wani ta shimfiɗa ta ɗauki freshner ɗinta da ta ji ta kusa ƙarewa ta fesa ta hau ka ta kwanta.

Wayar ta cigaba da dannawa ta hau whatsapp, gani saƙon ƙawarta Khady ta buɗe ta fara karantawa kamar haka. "Gobe zan dawo" Tana daga kwancen sai da ta tashi zaune, sosai ta ji daɗin maganar dawowae ƙawar tata wacce bata gari aka yi bikinta ma tana can Niger dangin Babanta.

Amsa ta bata da cewa

"Da gaske kike ko wasa?"

Ita ma amsar ta maido mata don lokacin tana online.

"Wallahi da gaske"

Cike da zumuɗi ta ce

"Allah kawo ki lafiya" Sallama suka yi ta ajiye wayar ta ja bargo ta yi addu'a ta shafa bacci ya yi awon gaba da ita, don bata san shi Aminun yau ma ko kwanan falon zai yi ba, in ma a ina zai kwana shi ya sani saboda yanzu ta daina saka damuwarsa a ranta kar ta je ta cutu a banza tun da shi ba ta ita yake yi ba, wata ce a gabansa ba ta tata yake yi ba.

A ɓangaren Aminu kuwa tana shigewa ɗaki ya sauke wata ajiyar zuciya, bai san mai ya sa ba tun da ya yi yunƙurin marinta ya ga ɓacin rai ɓaro-ɓaro a fuskarta sai ya ji yana shayinta kaɗan.

A zuciyarsa ya ce

'Oh duniya mai juyi-juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi yau ni Aminu ne nake jin fargaba a kan mace, sai ka ce wanda bakin uwa ya kama' Hannu ya sa ya ture robar da ya zuba ruwan zafin ya ajiye ƙyallan ya koma ya jingina da kujera, wayarsa ya fiddo ya yi shige-shige ya gama ya mayar da roba da ƙyallan.

Sai da ya mayar da wayar silent sannan ya je ya buɗe drower ɗinsa ya saka wayar saboda tsaro ba don tsoro ba, ya san ƴar aljannarsa za ta iya ƙara kiransa, duk da yana jin saukar numfashin Saddiqa alamar bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayi ya shiga ya hau toilet ya rage nauyin cikinsa, bayan ya yi tsarki ya tashi ya mayar da murfin ya rufe ba tare da ya yi floshing ba. Tunowa da ya yi da abin da Saddiqa ta ce a kan bar mata kashi bai kora ba, sai ya yi floshin ɗin don yau so yake ya lallaɓa ya sauke buƙatarsa a kanta tun da dai jiya ma a falo a kujera ya kwana kamar wani gauro.

Yana fitowa ya haura gadon yanayin ƙamshin turaren da Saddiqa ta shafa da na freshner ya haɗe kan gadon, hanci ya ƙara buɗewa yana shaƙa, sai da ya kwanta ma ya ji ƙamshin duk ashe a jikin zanin gadon ma. Bargon ya ja ya shige ya rarumo Saddiqa da take cikin tsafta tana bacci cikin kwanciyae hankali. Cikin baccin ta tsinkayi muryarsa yana cewa

"Saddiqa ba dai har kin yi nisan zango ba" Wani irin hamami da ya ziyarci hancin ta daga warin bakinsa dai da kanta ya sara, a take zuciyarta ta tashi ta ji wani amai ya tasho mata, janye jikinta ta shiga yi shi kuma sai ƙara maƙalƙaleta yake kamar ƙadangare ya samu bango.

Fisge -fisge ta shiga yi don babu abin da ta fi buƙata yanzu sama da ta ganta a bayi, kokawa ce ta kaure a tsakanin ma'auratan biyu ita tana son ta je ta amayar da abin da ya taho mata, shi kuma duk tunaninsa gudunsa za ta yi saboda abin da ya faru tsakanin su, tana cikin kiciniyar ƙwatar kanta sai ya sake buɗe bakinsa ya ce

"Haba Saddiqa, ke yanzu saboda saɓani ya gifta tsakanimu sai ki hanani haƙƙina? Ko so kike mala'iku su tsine miki?" Kai kawai take jijjigawa alamar a'a don bata son ta buɗe bakinta amai ya zubo saboda maganar da yake ƙara hautsina cikinta warin bakin nasa yake, bata san adadin kwanakin da ya yi bai wanke bakin ba ga warin hammatar gumin jikinsa kaɗai ma ta sai tabbas ƘAZAMIN MIJI take aure.

Tana ta ture shi ta samu ta kuɓuta sau ya ce

"Na ga dai ban yi marin ba, kuma kowa yana kuskure ki tausaya mini a buƙace nake wallahi" Ya faɗa yana rungume ta. Ganin shi bai fahimci komai ba ta dage ƙarfinta ta tura shi baya, da sauri ta tashi tsaye a kan gadon tana shirin ta dira, sai ji ta yi ya saka hannu ya riƙo ƙasan rigar baccin nata. Hannu ɗaya ta saka ta toshe bakinta gudun kar aman ya zubo, ɗaya hannun kuma ta yi amfani da shi wajen yi masa zancen kurame alamar tana zuwa, sai sannan ya gane banɗaki take son shiga don ya ga tana masa nuni da jikinta hakan ya sa ya washe rinannun haƙoransa.

Har neman tuntuɓe take wajen yin gudu, takalmin ma a juye ta saka tana sauri tana shiga bayin ta shiga kelaya amai tamkar ƴaƴan hanjinta za su fito. Sai da ta gama ta wanke fuskarta tana cikin yin brush sai ganin mutum ta yi tsaye a bakin ƙofa yana kallonta kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai, bata ankara ba sai ji ta yi ya ce

"Haba Saddiqa wai ke kama sau nawa kike wanke baki a rana ne, a ce mutum ko fashin wanke baki ba ya yi kullum sai ya wanke, wankewar ma ba sau ɗaya ba sau biyu ba?" Ya faɗa yana riƙe da ƙugu.

Bata ce komai ba sai da ta gama brush ɗin don so take ta daina jin abin ƙarnin aman a bakinta, tana shirin ajiye brush ɗin ta ji ya ce

"Ina miki magana kin watsa yina Saddiqa, mace dai an santa da tattali da cancana abu amma ke baki iya komai ba sai almubazzaranci, ni bakin nan sai in kwana uku huɗu ban wanke ba, kuma ko da na tashi tatsar makilin ɗin ɗan kaɗan nake matsa, amma ke sai kin cika kan brush ɗinki da makilin gaskiya ya kamata ki iya tattali saboda rayuwa" Ajiyar zuciya ta sauke ta taho ta raɓa shi ta wuce ya biyo bayanta, tana zuwa ta zauna a bakin gado, zuwa ya yi ya tsaya a kanta yana hucin jin haushin ƙyaleshi ɗin da ta yi yana bambami, ita warin da take shaƙa daga jikinsa kaɗai aka barta da shi ba ƙaramin cutuwa take yi ba ta rasa sai yaushe zai fahimci cewa ƘAZANTA ba ƙaramin cutar da abokin tarayya take yi ba, amma haka ta danne zuciyarta ta ce

"Yanzu shi wankin bakin ma sai an tuhumi mutum? Kai yanzu tsakani da Allah daɗi ta maka kake ikirarin kwana huɗu biyar baka wanke baki ba? Har kake cewa wai tattali ne hakan?" Hannunsa ya mayar baya jin tamkar ya kwaɗe ta sannan ya ce

"Yanzu daga magana sai cibi ya zama ƙari Saddiqa kike neman faɗa mini baƙar magana, su baki dai mene ne don ka yi fashin wankewa?" Tsabar takaici sai da ta kai zuciyarta nesa ta bashi amsa da faɗin

"Babu komai" Ganin kamar dai ranta a ɓace kuma ya lura kamar ma tana ɗan kauda kai sai ya sassauta murya ya ce

"Yanzu dai ya wuce amma in zaki saka makilin ɗin kike lakutar kaɗan, ni ma duk ranar da na samu damar yin wankin bakin sai in lakuci kaɗan ɗin, ko kuma in lakuta mai ƴar dama kin ga na yi ƙara'i kenan har na sauran ranakun da ban yi ba" Ya faɗa yana ɗan ranƙwafowa ya miƙa hannu ya dafo kafaɗarta. Kai kawai ta iya gyaɗa masa ta tashi ta haye gadon shi ma ya hau, ji ta yi tamkar ta saki kuka saboda yadda ta ji ya gundure ta da tashin warin rana.

Daga haka ya matsa ya shiga neman haƙƙin nasa babu wani nuna soyayya hannu ta kai ta riƙe masa hannu, cikin sanyin murya mai kamar son lallashi ta ce

"Ba don ni ba don Allah ka zuba ruwa a jikinka" Kallon kin raina mini hankali ya jefeta da shi kafin ya ce

"Saddiqa idan haƙƙin nawa ne ba zai samu ba ki faɗa mini mana sai wani jan rai kike mini, kar fa ki manta sadaki na biya amma kina shimfiɗa mini wami sharaɗi din za ki bani halaliyata" Murya ta sassauta cikin raɗa, don ita in ma mai zai ce gwara ta lallaɓa shi ya raba jikinsa da ƙazantar nan kar a je ta cutu.

Sai da aka kai ruwa rana ta nuna ta yi fushi sa yake yana son biyan buƙata, a haka ya tashi ya shiga bayin wanda ya ga shigarsa shi ya ga fitowarsa, sai sheƙin rashin fitar wankan yake don kana gani ka san dai ruwa ya sheƙa bai saka sabulu ba. Idanu ta lumshi tana jin yadda ranta yake ƙuna, shi kuma fitilar ya kashe musu yana wani washe baki ya hau gadon yana cewa

"Na yi belin kaina dai na yi wankan nan da ake ta faman cewa in yi" Wani gumus ɗin warin gajeran wandonsa dabya cire, garin ajiyewa ya jefo saman fuskarta abin da ta shaƙa sai da ta gwammace kiɗa da karatu, da sauri ta ɗauki wandon ta cilla shi gefen gado.

Kamar dai wanda ya taso da dattin haka ce ta kasance, amma dai da dama-dama wai kibiya a ido, haka dai aka shiga ƙoƙarin aiwatar da sunna, ga shi da ƘAZANTAR rashin wankin baki amma sai masifar son yin sumbata tamkar ba,indiye aiki ya yi nisa ita dai babu wata nutsuwa, don aiwatar da sunna ma ya fi idan kowa a tsaftace yake. Hannu ya kai yake saka mata yatsa a jikinta, wani kartar ta da ya yi da zaƙo-zaƙon farcen da ba ya yankewa shi ne ya sa ta zaro ido tare da saurin runtse idon, duk ya bi ya karce ta, a haka ya gabatar da sunnar sai wani uban gashi da bai aske ba da take ji tana goga a jikinsa.

Lokacin da komai ya lafa sai ya ɓingire da bacci, ko jikinsa bai suturta ba sai bargon ta ja ta rufe masa jiki, ita kuma ta je ta yi wankan tsarki ta dawo ta kwanta don ta san idan ta ce ya yi wankan ma ba zai yi ba, baya ta juya masa ta ja rigar baccinta ta kai hancinta tana shaƙar ƙamshin turaren har bacci ya ɗauke ta.

***

TALLA TALLA TALLA

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE?

KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH *** [4/17, 9:33 AM] ***: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****