Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 9
Daƙyar ta tashi da asuba don gabaɗaya jikinta ciwo yake mata, tana zaro ƙafafunta ta sauke a kan gajeran wandonsa da ta cillar tsakanin gado jiya, wani irin yamm jikinta ya ɗauka duk ƙyanƙyami ya kamata tunowa da ta yi da yadda ta shaƙi warin jikin wandon jiya da ya sauka a fuskarta. Sunkuyawa ta yi za ta ɗauke wandon amma sai ta kasa taɓawa don hatta zuciyarta sai ta ji tana tashi, ga wani yawu da ta ji ya taru a bakinta.
Fitilar ta kunna haske ya gauraye ɗakin, a kan Aminu ta sauke idanunta da yake bacci duk ya cika ɗakin da munshari, wani kallon tausayin kanta ta masa ganin wannan shi ne matsayin mijinta, a ce mutum ya samu janaba amma bai iya tsarkake kansa ba ya kwanta a haka, ko ba zai yi wanka ba ai ya je ya yi tsarki ya wanke najasar jikinsa.
Bayi ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ɗan guntun ruwan hannunta ta fatsa masa a fuska, ammma ko gezau bai yi ba sai sharara munshari yake kamar an danne wuyan rago. Ƙafarsa ta fara bugawa daƙyar ya buɗe idanunsa da suka masa nauyi saboda baccin ya sauke a kanta, yana hangota duru-duru don baccin bai wartsake a idanunsa ba.
Kallon takaici ta masa ta ce
"Ka tashi lokacin sallah ya yi, yanzu duk na yi ƙaran buɗe ƙofar gida da alama ƴan uwanka ne suka tafi masallaci" Wani irin yatsina fuska ya yi yana jin kamar ya mangare ta don ya ji haushi matuƙa da ta katse masa baccinsa mai daɗi, cikin haɗe girar sama da ƙasa ya ce
"Sai aka yi yaya? Ko ni an ce idan na falka ba zan yi sallar ba, wai sau nawa zan ce miki kabarinki da ban nawa daban Saddiqa amma sai kike shige mini hanci da ƙudundune kar fa ki manta mijinki nake ba ɗanki ba, ni ya dace na baki umarni" Ya kai ƙarshen maganar kamar zai fasa mata kunne da ƙaran maganarsa ganin yadda ya hayayyaƙo mata.
Cikin jin takaicinsa ta danne abin da ta ji ta ce
"Haba don Allah yanzu mene ne na tada jijiyoyin wuya da asubar fari, ka san dai gidan nan ba iya mu kaɗai bane, amma a ce da asuba ana jiyo hayaniya ai sai cibi ya zama ƙari, sannan ni ba umarnina bane yin sallar umarnin Allah ne ai" Kallonta yake mamaki yana bayyana a fuskarsa da alama mamakin kalamanta yake a zuciyarsa ya ce
'Kannan yarinyar tana shiga shirgin da babu ruwanta, ai wani lokacin ma auren mace uztaziya ko mai riƙe addini da alama matsala ne in ba haka ba yarinya kamar ƴar gidan malam Kabiru Gombe duk ta bi ta addabi mutane da magana ɗaya' A fili kuma sai ya ce
"To tun da umarnin Allah ne ba naki ba, ki sakar mini mara na yi fitsari" Yana kaiwa nan a maganarsa ya ja bargon ya rufa har kansa. Galala take kallonsa rufe cikin bargon tana tuna ko jikinsa fa bar suturta ba tsirara yake, ita ce ma ta sakaya jikinsa da bargon.
'Wane irin miji na aura ne na kasa ganewa, haka zan rayu ni da ƴaƴana ƙarƙashin wanda bai damu da addini ba a ce sallah sai mace tana fama da miji zai yi in ba haka ba sai lokacin da ya shirya a shelaƙe zai yi, shin mene ne fa'ida ko ribar auren namiji irin wannan ga muni ga cin zanzana wato ga ƙazanta ga jahilci' Ta faɗa a zuciyarta tana ta tunanin ina ma akwai yadda za ta yi ta sauya masa halayensa, da ta yi saboda tana ƙaunarsa kuma shi ma dai ta san haka ne ta ɓangarensa amma bata taɓa zaton za ta same shi da wannan halayen wanda ba na ƙwarai ba.
Juyawa ta yi ta koma ta saka kaya a jikinta ta saka hijabi ta shimfiɗa sallaya, raka'atainil fajr ta gabatar, bayan ta yi addu'o'in ta a cikin sujada ciki kuwa har da addu,ar Allah ya dawo da mijinta kan hanya madaidaiciya wato yake kiyaye salloli da kuma zama mai tsafta don su samu rayuwar mai ɗorewa haɗe da farinciki don watarana ƴaƴansu su yi alfahri da su matsayin iyayensu, domin ta fahimci in har zai ɗore a haka to tabbas babu wani yaro da zai taso ya ji daɗin ganin mahaifinsa yana wasa da sallah.
Miƙewa ta yi za ta gabatar da sallar asubar sai kawai ta ji wani haushinsa ya cika mata rai, tana tunanin a ce su uku a gidan kowacce mijinta ya tafi masallaci amma nata a kwance, shi ba da zuwa masallacin ba kuma bai yi a gida ba. A zuciye ta nufe shi tana zuwa ta cire masa bargon da ya ƙudunduna, can gefe ta warɓar da bargon sai ga shi ya bayyana tsirara, ita kuma sai ta kama ƙugu ta fara jijjiga jiki don ta ga alama sai ta yi da gaske gwara ma tun kan ta fara haihuwa ta yi wa tufkar hanci, kafin yara su zo su ga halin da ake ciki.
A ƙufule ya buɗe idon jin iskar da ta fara shiga jikinsa suuuu ya gane buɗe masa rufar ta yi, zaune ya tashi ya shiga ƙarewa kansa kallo ganinsa tsirara cikin dakakkiyar murya ya ce
"Wai ni Saddiqa sa'anki ne ni, ko don kinnga makwancina ne raini ya shiga tsakaninmu? Sabosa kina matata kin saba ganina babu kaya har hakan ya zama raini? Ina rufe ki zo don ƙarfin hali ɓarawo da sallama ki buɗeni tsirara ki tsaya a kaina?" Ya faɗa yana wani huci kamar kumurcin zaki.
Ganin haka ita ma ta maje ta ce "Mene ne na rainin a ciki? Ni ban ga wani abin rainaka ba, tun da wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, da kake cewa na buɗe ka tsirara shin dama ba haka ka kwanta ba? Ai ni ce dama na suturta maka jikin naka amma dama hakan ka kwanta ai"
Wani kallo ya jefe ta da shi ya ce
"Don kin rufa mini bargo shi ne kika buɗe, ai da kin barni na kwana a haka tun da ba roƙar ki na yi ki rufe ni ba" Ya faɗa yana waige-waige, bata san mai yake dubawa ba sai ta ga ya leƙa can gefen gado, sai kuma ya shiga ɗaga filillikan bata ankara ba sai ji ta yi ya ce
"Ina kika kai mini gajeran wandona?" Ji ta yi kamar ta yi kuka amma sai ta ce
"Tun da baka bani ajiya ba a kan mai za ka tambaye ni"
Kai ya jijjjiga alamar lallai wuyanta ya isa yanka tun da suka fara musayar yawu da ita, ɗaya gefen gadon ya leƙa inda wandon yake sai kuwa ya hango shi yamushe a ƙasa, ɗakkowa ya yi ko karkaɗewa bai yi ba ya saka kayansa ya koma ya kwanta yana mai gargaɗinta da cewa
"Wallahi kika kuskura kika ƙara tashina sai kin raina kanki" Yana faɗa ya kwanta. Hannu ta kai ta ja babban yatsan ƙafarsa, yadda ya tashi a fusace ya sa ta yi saurin ja da baya ganin ya miƙe tsaye a kan tsakiyar gadon. Tsalle ɗaya ya yi ya dira a gabanta, da baya ta ja don ta fara tunanin kar ya wanka mata mari, da hanzari ta ƙara matsawa har sai da ta jingina da bango sai da ya je dab da ita ya tura ƙirjinsa ya tokare ta idanunta ta ɗaga ta sauke a fuskarsa kasancewar ya fita tsawo. Baki ya buɗe ya fara magana cikin gargaɗi ya ce
"Saddiqa kar ki fara bari in ke sauke fushina a kanki, ina so ki sani ni rashin mutunci gaba na bashi ba baya ba in har kika ce ni za ki shigewa hanci da ƙudundune to za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke ne,na lur har yau baki san wa kika aura ba to ina so ki sani a cikin halaye na ko kashi ɗaya baki sani ba a cikin ɗari gwara ki lallaɓa amma in har kina so mu shiga zaman doya da manja ga fili ga mai doki" Tun da ya fara maganar gabanta yake faɗuwa da sauri da sauri don ita tsoronta ɗaya kar ya kai mata hannu, kawai kallon fuskarsa take mai ɗauke da farin abin yawun bacci da ya bushe sawun yawun baccin har haɓarsa, ga bakinsa da ya buɗe yana mata magana sai ta ji ta ƙosa ya bar kusa da ita. Cikin dauriya ta buɗe nata bakin ta ce
"Ka yi haƙuri" Ta faɗi hakan ne don ya janye jikinsa daga gare ta, don bata ƙaunar warin da take shaƙa daga gare sa" Hannu ya ɗaga ya kaɗa mata yatsunsa a saitin fuskarta ya ce
"Wannan ne karo na ƙarshe" Kai kawai ta iya gyaɗawa. Ƙwafa ya yi haɗe da jan wani gajeran tsaki ya juya ya shiga bayi ya banko ƙofar da ƙarfi. Wata ajiyar zuciya ta sauke, kasancewarta mutum marar son tashin hankali ita in ba bango aka kaita ba bata son yin faɗa ma sai dai in raina mata wayo aka yi.
Tana jin ƙaran ruwa a bayin ta juya ta hau sallaya ta shiga gabatar da sallarta, a raka'arta ta biyun tana sujjadar ƙarshe ya buɗe banɗakin ya fito dama wankan tsarkin ya yi ta ɗauro alwala, bayan ta gama addu'a za ta fara karatu ya ce
"Fita falo ki yi, zan yi sallah a sallayar" Bata ce komai ba siyam-siyam ta busawa rigarta iska. Yana saka jallabiyarsa ya kabbara sallah yana idarwa ya koma ya kwanta don daga sallama ko azkar bai yi ba ya tashi.
Tana karatun amma duk ta damu da halayen da Aminu yake yi, saboda karatun da ta yi ne ma zuciyarta ta yi sanyi da ta gama ta je ta ajiye ta dawo falon ta kwanta a kan kujera tunani barkatai yana adabar zuciyarta.
Ko da gari ya waye haka ta tashi suƙuƙu, ɗanwake ta kwaɓa ta yi don shi ta ji tana son ci haka ta musu ta soya manja ta ci da shi, shi kuma sai ta soya masa farin mai. Bayan fitarsa ta gyara ko ina ta shiga yin goge -goge sai da ta gama tas sannan ta shiga ta wanke bayin za ta yi wanka, amma yadda ƙasanta yake raɗaɗin karcenta ɗin da ya yi da farce jiya sai ta ji tana buƙatar shiga ruwan zafi ta gasa jikinta, ruwan ɗumin ta shiga sai kuma ta yi wankan saboda shi gogan kaya kawai ya saka saboda wannan wankan da ya yi ta wadatar a wajensa, ko ta kan brush ɗinsa bata bi ba domin ta san idan ta duba ma ranta ne zai yi ƙuna saboda ta san da wuya in ya wanke bakin.
Don ta ga ya sauya mata fuska ma duk da ta san hakan ba ya rasa nasaba da abin da ya faru a tsakaninsu.
Wajen shida na yamma tana zaune falo wayarta ta yi ƙara tana ɗakkowa ta ga Khady ce, cewa ta yi
"Assalama alaikum ƙawata ta kaina" Daga ɗaya ɓangaren Khady ta ce
"Ni na yi fushi, da alama angon nan ya sauya mini ke kin san na ce yau zan taho amma maimakon ki kira ki ji ko na taho shi ne baki kira ba" Ta faɗa cikin sigar zolaya, dariya ta yi don ta san da alama rigima take nema sai ta ce
"Yi haƙuri ta hannun damana ni na isa, kawai dai abubuwa ne suka sha kaina" Baki ta taɓe kamar Saddiqae tana ganinta ta ce
"To shikenan gani a gida na dawo"
Cike da murna Saddiqa ta ce
"Don Allah da gaske ko wasa" Dariya mai sauti Khadyn ta yi jin duk Saddiqar ta ruɗe da murna ta ce
"Wallahi da gaske nake don ɗazun nan na dawo"
"Amma na ji daɗi, ji nake kamar na zama tsuntsuwa in zo in ganki My Khady" Dariya ta fashe da ita ta ce.
"Haba amarsu ta ango ai ni zan kawo miki ziyara, in sha Allah gobe a gidanki zan wuni, mu sha hira in zo in ga soyayyar nan taku ke da Babynki Aminu ko na yi kwas nima" Ta faɗa cikin tsokana don ta san irin so da ƙaunar da suka shuka a neman auren.
Dimm gabanta ya buga jin wai za ta zo ta ga soyayyarsu, bata san tun tuni komai yana neman ya zama tarihi ko ma ya zama. Sai ta yi arfin halin cewa
"Sai kin zo kuwa" Haka dai suka yi sallama suna ta tsokanar juna. Tun bayan da suka yi sallama sai ta shiga taraddadin zuwan Khady tana fatan Allah daidaita tsakaninsu kar ta zo ta gansu, ba ma wannan ba tana addu'a da fatan Allah ya sa har ta zo ta tafi kar su haɗu da Aminu, don wannan tsaf sai ya ja mata raini wannan ƙazantar a yadfa take ƴar ƙwalisa a ce wannan ƙazamin ne mijinta daga ya gifta sai warin rana daga ya buɗe baki kamar ana kwasar kwata ai abin kunya ne wallahi.
Ko da suka zo kwanciya ma kadaran kadahan, domin baya ma ya juya mata. So take ta sanar masa za ta yi baƙuwa amma tana tsoro sai dai ta yi ƙarfin cewa
"Aminu gobe fa Khady ta ce wunin gidan nan za ta yi" Ta ƙarasa faɗa cikin sanyin murya. Banza ya mata har ta cire ran zai yi magana sai kuma ya ce
"Allah kawo ta" Haka kawai ya ce bai ƙara magana ba amin kawai ta ce ita ma bata bu ta kansa ba ta kwanta.
Ko da safe da ya tashi jugum ya yi ba dariya ba murmushi ba magana, duk sai ta ji ta rasa ya za ta yi, ko da ta kawo masa abinci ma sai cewa ya yi a ƙoshe yake haka dai da zai fita ta ce masa kayan miya ya ƙare babu a frige buɗar bakinsa sai ya ce
"Ki yi wake da shinkafa da mai da yaji" Shiru ta ɗan yi sai ta ce
"Amma ka san na ce maka zan yi baƙuwa ai da an kawo na mata wani abu amma kuma babu abu mai ɗan daɗi sai a ce wake da shinkafa" Kallo baki da hankali ya mata sai ya ce
"Shi ba abinci ba ne?" Bata ma samu damar bashi amsa ba, da yake dama yau bai fita da wuri ba lokacin ma wajen ƙarfe sha ɗaya da wani abu. Yana dab da bakin ƙofa ta tsinkayi muryar Khady tana sallama, kallonsa ta yi ta ɗan langaɓar da kai alamar ya saki fuskarsa kar a gano wani abu a tsakani, banza ya mata ya juya don yau da yake basu gabatar da sunna da dare ba ankan baƙin ruwan ma bai yi ba kaya kawai ya saka taimakonta ɗaya kayan a wanke, duk da cewa idan har aka ɗora kaya a kan dauɗa to duk ɗaya ne an ce wa makaho ga ido.
Fitowa ta yi tana amsa mata, shi ma sai ga shi ya fito abin mamaki sai ya washe jajayen haƙoransa suka gaisa da Khady tana ta musu tsiya wai sun yi aure sun manta da ita. Yana dariya yake tsokanarta kafin ya musu sallama ya tafi su kuma suka shige falo suna ta murnar ganin juna.
Zaunawa Khadyn ta yi Saddiqa ta zauna a kusa da ita suna ta hirar yaushe gamo, cewa ta yi bari ta ɗakko mata ruwa ta fita zuwa kicin. Khady fitar Saddiqa ke da wuya ta shiga ƙarewa falon kallo ganin yadda ya sha gyara ko ina sai ƙamshi yake sai dai abin da yake bata mamaki wani ɗan hamami da take ji yana tashi daban da ƙamshin.
Ɗan hura hanci ta yi amma sai ta ji warin har yana ɗan shigar mata maƙoshi, kamar an ce ta duba bayanta daga saman kujerar da take zaune ta yi ido huɗu da wani talallan gajeran wando wanda ya gaji da tsufa har ta fara tauyewa daga ƙugu, ya haɗa uban datti waiwayawar da ta yi ne ta ji warin har wani dumm ya sa ta ji a kanta da sauri ta tashi ta bar kujerar ta koma wacce take ɗan nesa da ɗayar. Mamaki take mai ya kawo wannan wandon haka amma jin takun Saddiqa sai ta kawar da wannan tunanin.
Saddiqa da ta shigo bata kawo komai ba da ta ga Khady ta sauya wajen zama ruwan ta akiye mata har da fruit da ta yanko mai sanyi.
Hira suka shiga yi tana cin fruit ɗin can ta ce
"Wai ƙawata kin ganku kuwa kamar ba amarya ba, maimakon in zo in ga kin yi ƙiba kin yi jawur dake amma sai in ga kin rame kin yi baƙi kamar wacce aka yi wa auren dole, ni gani nake babu abin da zai sa in yi rama in har masoyina yana kusa da ni" Ta ce tana kallon Saddiqa.
'Allah sarki Khady baki san mene ne zaman aure ba, a haka muje ganin gidan aure kamar babu matsaloli amma kowane gidan aure cike yake da matsaloli da ƙalubale birjik sai dai na wani ya fi na wani, babu sabon aure babu daɗɗe' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya ta ce.
"Kin jiki da wani abu, rashin lafiya fa nake fama" Idanu Khady ta zaro ta ce
"Don Alla da gaske? Ki ce an samu ɗan baba" Dammm ƙirjinta ya buga don sai yanzu ma ita ta tuna cewa wannan watan bata yi priod ba, kallon yanayin da ta shiga Khadyn ta yi ta ce
"Ya dai" Murmushi ta yi ta ce
"Babu komai"
Suna nan suna hira bayan ta ɗora abincin, lokaci zuwa lokaci tana fita kicin ta dubo, amma dai ta ɗan ji ɗan bashi-bashi a falon sai dai bata kawo komai ba, dama sai ta fita ne idan ta dawo sai ta ji falon ya sauya. Bayan an kira sallah Khady ta fita banɗakin tsakar gidan za ta yi alwala, ɗaki ta shiga ta ɗakko sallaya ta zo ta shimfiɗa mata kamar an ce ta ɗaga kanta saman kujerar da Khady ta fara zama ta tashi, aikuwa ta yi arba da gajeran wandon Aminu daƙyal-daƙyal da shi gabanta ne ya faɗi shiru ta yi tana ɗan nazari a nan ne ta ƙiyasta a zuciyarta cewa wannan wandon ne ya saka Khady tashi daga kujerar.
Wani takaici ne ya saka ta danne leɓen bakinta tana jin haushi da takaicin ajiye mata wandon da ya yi bata san ma ya ajiye ba. Jin takun Khadyn ya sa ta yi saurin ɗaukan wandon ta shige ɗaki tsabar haushi cilli ta yi da shi wajen drower Aminu, wandon kamar an nuna masa wajen zama sai kuwa ya maƙale a jikin hannun drower yake reto yana ta lilo.
Ƴar guntuwar freshner tata da ta rage ta ɗakko ta feshe a falon, ita ma Khadyn tana shigowa ta sauke idanunta a wajen gurbin wandon sai ta ga wayam hakan ya nuna cewa Saddiqa ta kawar da shi.
Sun idar da sallar ta zubo musu abinci har da sauran kabeji da albasa ta yanka musu, za su fara ci kenan kamar daga sama ta jiyo muryar Aminu yana rafka sallama, hatta Khady sai da ta lura da sauyin da fuskarta ta nuna, shigowa ya yi yana washe baki firi-firi da shi da fari fulawa yana shigowa falon ƙamshin freshner ɗin ya sauya zuwa wani abun daban saboda ya kwaso rana, kuma abin haushin yana zuwa ya yi wa kansa masauki a falon.
Murmushin ƙarfin hali Saddiqa ta yi ta ce
"Sannu da zuwa" Amsa mata ya yi ita ma Khadyn ta masa ya amsa sai ya ce
"Ai yau na ce tun da muna da baƙuwa gwara na dawo da wuri ni ma asha hirar da ni kar a yi babu ni kawo mini abincin nima" Ya ce yana dariya.
Tashi ta yi tana sakin murmushin yaƙe ta fita kicin, tsayuwa ta yi tana jin kamar ta nutse don kunya ya dawo daga kasuwa amma bai san ya je ya tsaftace jikinsa ba, zai zo ya saka su a gaba. Abincin ta zubo masa ta dawo.
Suna gefe guda suna ci shi ma ya cin nasa, ana haka sai kuwa ya yi wani kaki, ya kako majina sai kuwa ya tashi su duka da kallo suka bishi ƙofar ɗaki ya nufa yana zuwa ya ɗaga labule ya tofar a ƙofar ɗakin, don daga inda suke ma suna hango inda ya tofar da majinar, yana sakin labulen kuwa da yake labulen har ƙasa yake aikuwa iska ta ja labulen ya tsunduma cikin kakin majinar da ya tofar!
TIRƘASHI!!!
***
Kina neman zannuwan gado? Ko kuwa labulaye, kina son siyen frames, ko takalma, kina son siyan mayafai masu beat work ko leshi da atamfa kike so? Ina da kamfala sannan har da laffaya.
Hijabai kike so ko kuwa sarƙa da ɗankunne agogo ko warwaro, ina siyar da magungunan mata masu inganci har da na sanyi da basir babu abin da bana siyarwa har da wanda ban zana ba ki dai tuntuɓi
MAMAN AFRAH ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****