Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 10
Aminu dawowa wajensa ya yi ya zauna hankali kwance ya cigaba da cin abincinsa, Khady kuwa zuciyarta ce take ta tashi ganin abin da ya yi domin tun da ya tofar da yawun nan bata kai ko da loma ɗaya ba bakinta sai jujjuya cokalin take, Saddiqa kuwa kunyar duniyar nan ce ta ishe ta duk da ita ma abincin ya fice mata rai amma kuma tana jin kunya da nauyin abin da ya yi a gaban ƙawarta.
Ganin duk sun yi jugum-jugum bakinsa da abinci ya kalle su da mamaki ya ce
"Ƙawayen juna ya kuka dakata da cin abincin, ai ni wallahi Saddiqa yau kin biyani da wake da shinkafar nan, ya yi daɗi sosai" Ya faɗa yana ƙara cika cokali ya kai bakinsa, Saddiqa bata ce komai ba sai Khady ce ta yi ƙarfin cewa
"Ai kam ya yi daɗi ni da yake dama ban cika cin abinci sosai ba, yanzu ma ƙoshi na yi ba don abincin ya isheni ba" Ta faɗa tana sakin dariyar yaƙe.
Bai sake magana ba sai da ya cinye abincin nan tas, lokacin Saddiqa ta haɗa kwanukan ta fita da su tsintsiya da klin haɗe da ruwa ta ɗakko ta wanke ƙofar ɗakin ta ɗakko wani labulen ta cire wancan ta saka ta kai bayi ta saka a bokiti ta wanke ta fito ta je ta shanya.
Kiran sallar la'asar ne ya saka Khady cewa bari ta je ta yi alwala, tana fita Saddiqa ta kalle shi jin yana sakin gatsa haɗe da miƙe ƙafa a kan kujera bashi ma da niyyar tashi yin sallah ta ce
"Yanzu Aminu kai sai ka ce ƙaramin yaro a ce a ƙofar ɗaki za ka tofar da yawu? K...Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya katse ta da faɗin
"To sai aka yi yaya wai ku mutane mai ya sa ba a iya muku ne? Yanzu yawu ma don na tofar sai an tuhume ni? Idan ba a ƙofar ɗaki ba a ɗakin kike so in tofar hallaw cibi ya zama ƙari? To ni da gidana babi wanda zai mini wani iyayi wai ke sarkin ƴan tsafta" Idanu ta runtse tana jin takaicin maganarsa amma sai ta danne ta buɗe idanun da tuni sun yi jajur saboda takaici, ta ce
"Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah tun da mu ma sallah za mu yi" Shiru ya yi bai ce komai ba sai kuma ya ce
"Ko dai in yi alwalar in zo in ja ku jam'i?" Wani haushi ta ji ita da take so ya fita a falon ko sa samu damar shaƙar iska mai daɗi amma wai zai ja su jam'i ɗan rausayar da kai gefe ta yi ta ce
"Kamar na ga baka yi azzahar ba fa, kuma ta yaya za ka ja mu sallar la'asar" Shiru ya yi don tabbas ya san bai yi ɗin ba sai kuma ya ce
"Na rama ta daga baya" Kallonsa ta yi tana jinjina jahilci irin nasa ta ce
"A'a azzahar ai ita ya dace a fara yi sannan la'asar, wai ni kuwa anya Aminu ka yi islamiya?... Tun kafin bakinta ya rufu ya hayyyaƙo mata tamkar zai kai mata duka ya ce
"Ban yi ba Saddiqa tun da ke kika koya mini karatun sallar da nake yi, tun da abin ya zo da cin fuska ba zan yi sallar ba idan ke ake yi wa in na yi ki watso mini" Wannan maganar da ya faɗa a zafafe ya yi daidai da tahowar Khady don haka a kan kunnuwanta ya faɗa gabanta sai da ya buga jin hargowar da yake yi, a bakin ƙofar ta tsaya da yake labule ya shiga tsakaninsu.
Shi kuwa yana kaiwa nan ya tashi fuuuu ya shige ɗaki, jin sallar Khady sai ta yi saurin kawar da kai gefe ta amsa mata tana danne kukan da yake son ƙwace mata.
Ɗaki ta shiga da sauri a kan gadon ta gan shi ko kallo bai ishe ta ba, bayi ta shiga ta ɗauro alwala a can ta yi ɗan kukan takaici kasancewar ta mai zurfin ciki bata son Khady ta fahimci abin da yake faruwa, bata san cewa Khadyn ta ji abin da ya ce na ƙarshe kuma ko ba komai ai ta gama fahimtar Saddiqar tana cikin damuwa.
Bayan sun idar da sallar Khady ta dafa kafaɗar Saddiqa cikin ƙasa da murya ta ce
"Ƙawata na san kina da zurfin ciki, kuma duk da baki faɗa mini ba na san kina da damuwa, amma matsayinki da kuma kusancina da ke ba zai sa in kasa faɗa miki wani abu ba ina so ki yi watsi da zurfin cikin da kike da shi ma'ana ya zama kina faɗawa wani damuwarki saboda kar kike barin damuwa a zuciyarki hakan zai haifar miki da matsala" Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙwace mata, ita kanta Khady idanunta cike suke da ƙwalla domin tana jin Saddiqa tamkar ƴar uwarta ta jini ganin Saddiqar bata ce komai ba sai ta ɗora da faɗin
"Ban ce kike fitar da sirrinki ba, amma a ƙalla kike fitar da damuwarki ba a son ake tarawa zuciya damuwa saboda gudun matsala, sannan addu'a ita ce takobin mumini ki dage da ita sosai duk da na san baki da sakincin yinta abu na ƙarshe, kar kike bari namiji ya rainaki ko ya raina wani naki ke dai ki zama mai biyayya amma kar ki yarda ake miki cin kashi, domin shi itace tun yana ɗanye ake tanƙwasa shi abin da nake nufi idan har kina bari kpwace shara namiji ya watsa miki to za a wayi gari har girman ƴaƴanki a gabansu zai ci zarafinki, kuma ko da ya auri wata nan gaba ita in ta nuna ba za ta ɗauka ba sai ya zamana ke kalai ce jujin zuba shararsa, duk da bani da aure amma na san abubuwa da dama a kan aure" Saddiqa sai ta ji tamkar Khady ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi a take hawaye suke sintiri a kumatunta kuma daga hakan ta gane cewa kuka wani ma ya lallashe ka rahma ne, sai da hawayen ya tsagaita ta ce
"Na gode ƙawata kuma duk abin da kika faɗa haka ne, zan kiyaye kuma zan yi duk iya ƙoƙarina" Ta faɗa ita ma cikin raɗar don ta san Aminu zai iya kasa kunne, kuma ta ƙara gane cewa yanzu da yake tare da wata budurwar kenan in tana danne komai in ya auro wata ita ta zaɓa bola.
Ta jima tana lallashinta har dai ta ga ta saki ranta daga nan ta mata sallama ta raka ta ta tafi.
Khady tana tafiya ta tsaya a falo ta share hawayenta tas, tana shiga ɗakin ta gan shi yana sallah idanu ta sauke a kan gajeran wandon nan nashi na jikin drower bakin gado ta zauna har ya sallame sallar. Dama yana gama sallama yake barin kan sallaya saboda ba azkar yake yi ba. Kallonsa ta yi yana danna waya ta ce
"Aminu shin mai ya kai wandonka falo saman kujera?" Tambayar ta zo masa a bazata duk da ta yi kama da tambayar rainin hankali amma sai ya maje ya ce
"Kamar ya?" A ƙufule ta ce "Ya ina tambayarka kana tambayata?"
"Ra'ayi riga" Ya faɗa hankali kwance. Ƙwafa ta yi cike da ɓacin rai ta tashi za ta bar ɗakin ƙiiii ta ji ya janyota ta dawo waiwayowa ta yi ta ga ya haɗw fuska babu zato ba tsammani ya ce
"Daga yau da rana mai kamar ta yau kar ki ƙara gogin yi mini ƙwafa ni ba sa'anki bane" Yana kai wa nan ya saki hijabin nata da ya kama, bata ce masa komai ba ta juya ta bar ɗakin.
Sai da ya ga la'asar lis ya ƙwama uwar hula ya zo wuce ta tana zaune a falo ya ce
"Sai na dawo" Da banza ta yi da shi sai kuma ta ce
"A dawo lafiya" Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba tun da ta ga har zai iya fita haka yana warin rana shi abin ma ba ya damunsa ita kuwa har mamakinsa take yi.
Bai dawo ba sai bayan isha'i, lokacin ta shirya tsad cikin fararen kayan bacci, tana kwance tana game a waya, ganin yana washe baki yana wani nan -nan da ita ta san wani abu zai buƙata ita kiwa ta ƙudurce a ranta cewa, duk runtsi yau ba za su haɗa jiki ba har sai ya tsafta ce jikinsa ko dai ya haƙura.
Kamar abin kirki ya zauna yana ta zuba kamar kanya, zuwa can ya ce
"Amarsu ta ango daga ke babu ƙari" Kallon maƙaryacin banza ta masa kafin ta buɗe baki ta ce
"Namiji ai ba mijin mace ɗaya bane" Dammm ƙirjinsa ya buga, a take ƙwaƙwakwarsa ta shiga tariyo masa furucin da ya yi wa ƴar aljanna lokacin suna waya a kicin, tunani ya fara ko dai ta ji wayar da ya yi ranar sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar cewa
"Wani namijin ba" Wani murmushin rainin hankali ta yi ta ce
"Uhm in ji mai ciwon haƙuri" Daga haka ta mayar da hankali kan game ɗin pop game da take yi.
Shi kuma jin yana tsuma yana son kawar da abin da yake ji, sai ya ɗan matsa tare da miƙa hannu ya shafo kafaɗarta da yake wuyan rigar sleeping dress ɗin irin wanda yake da kafaɗa a buɗe ne. Laushi da santsin fatarta ya sa ya saki wani murmushin jin daɗi, ita kuma a nata ɓangaren ba haka bane domin kuwa garin shafo kafaɗarta ya karce ta da farce. Bata nuna masa komai ba tana jiran har ya ida nufinsa ta gabatar da tata buƙatar wacce take ganinta a matsayin sharaɗin da za ta gindaya masa na kwanciya da ita.
Ɗan matsawa ya yi yana sosa ƙeya ya ce
"To wai ni a ajiye wayar mana tun da ango ya zo kusa, ni fa saboda ɗokin kasancewa da ke yau ko abincin dare ba zan ci ba" Wani murmushi ta saki wanda ya bayyana kyawawan jerarrun haƙoranta wanda suke a jere kamar masara, suna sheƙi kamar bayan kwanon silba. Ganin kyan da ta yi ya ƙara fusgarsa zuwa gare ta ya matsa kusa, ganin tarkonta ya kama tsuntsu sai ta yi yunƙurin sauka daga gadon, cikin rashin fahimta ya ce
"Ina kuma zaki bayan buƙace nake" Idanu ta farfara tare da langaɓar da kai ta ce
"Ai ba wani waje zan je ba abu ne zan ɗakko maka" A ransa sai ya fara tunanin ko dai Saddiqa ta fara wayewa ne maganin ƙarfin maza za ta bashi, wannan tunanin ya sanya shi ya ƙara jin kansa ya masa gingirin gim.
A hankali ta tafi kan madubi cikin takunta na mace mai aji da nutsuwa, da kallo ya bita yana ɗan lashe baki kamar tsohon maye.
Baƙar ledar da ta miƙo ya karɓa, tana tsaye ya buɗe ledar ya leƙa abih da ya gani ciki ne ya sanya fuskarsa sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗako kai yana kallonta mamaki shimfiɗe a fuskarsa ya ce
"Mene ne wannan?" Ɗan murmushi ta yi ta ce
"Sheba da ake shebin da reza da ake yankan farce, Aminu idan ka ga yau ka kusanci ne to sai in har ka aske gashin hammatarka da na mararka sannan ka zauna ka yanke farcenka, abu na ƙarshe sai ka yi wanka soso da sabulu sannan sai mu yi abin da za mu yi babu cuta babu cutar...
"Wannan labarin ƙanzon kurege ne, ki ƙaddara tatsuniya kike mini" Ya faɗa rai a mugun ɓace don zuciyarsa har ta raya masa cewa, Saddiqa bata son bashi haƙƙinsa ne shi ya sa ta ɓullo ta wannan hanyar. Daga nan inda yake ya yi jifa da ledar kan madubin. Kallon abin da ya yi ta yi tana jin takaici ta ce
"Tun da haka ka ce za ka ga labarin ƙanzon kurege" Tsaye ya miƙe tamkar zai kai mata duka ya ce
"Indai har kina ganin kin kai ki saka doka ko sharaɗi in bi, to ki sani baki isa ba kin yi kaɗan kin yi tsarara kamar ruwan shayi, in dai har wannan abun naki kike taƙamar sai na yi aski da yankan farce haɗe da wanka to ki jiƙa ki sha ba a so, sannan ina so idan kin manta in miki tuni ni mijin mace huɗu ne idan kin hana zan iya kawo wacce za ta bani sannan ta tarairaye ni ba tare da ta yi la'akari da ƙazantatar da kike ikirari ba" Yana kaiwa nan ya juya zai yi wajen drower raina sai ƙuna yake ta shiga bayi ta ɗakko ruwa a hannunta tana zuwa ta kama hannunsa bai yi musu ba duk da ransa a ɓace yana son ganin gudun ruwanta.
A hannunsa ta zuba ruwan tare da nannaɗe hannun rigar ta shiga murzawa, aikuwa datti yake fitowa kamar wanda bai taɓa wanka ba, dirzawa take datti yana fitowa da sauri ya janye hannunsa cikin hargowa ya ce
"Wannan rainin naki ya yi yawa har ni kike yi wa titsiye kina son fito mini da dattin da ya ɓuya a jikina, ke baki san akwai dattin da yake zama kariya a jikin fata ba" Kallon raini ta jefe shi da shi ta ce
"Ba wani nan dauɗar rashin wanka ce wanann" Tsaki ya daka ya ƙara juyawa taku ɗaya biyu ya yi maganar da ta fara kamar haka ita ta katse masa tafiyar.
"Idan dai har kana ganin akwai macen da za ta juri zama da kai a wannan halin da kake ciki, to ga fili ga mai doki" Ko kallo bata ishe shi ba ya juya da nufin zuwa ya ɗauki gajeran wandonsa, saboda yana so ya saka sai ya kwanta tun da ya ga alamar haƙƙin nasa ba zai samu ba, kayan jikinsa ya cire duka don gajeran wandon zai saka ya kwanta.
Saddiqa da take jiran ganin abin da zai yi idanunta suka sauka a kan gajeran wandon da ya nufa zai ɗauka, cikin zafin nama ta ɗare kan gado ta dira sai gata ta riga shi zuwa wajen suka miƙa hannu kusan a tare za su ɗauka cikin rashin sa'a Aminu ya riga ta ɗauka, baki ta damƙe da haƙori ganin ya yi wa wandon riƙon sakainar kashi ta yi saurin tankwaɓe hannun wandon ya faɗi, duk da bai san dalilinta na son ɗaukan wandon ba amma dai ba ya so ta ɗauka.
Tana ɗauka yana tsaye sai gani ya yi ta ɗan sunkuya ƙasa, bai ankara ba sai ta bi ta tsakanin ƙafafunsa, cikin jin haushi ya ce
"Wai mai za ki yi da wandon nan" Ya ƙarasa faɗa rai a ɓace. Cikin hakin da take na cin nasarar zuwan wandon hannunta ta ce
"Aminu tun da wannan wandon ba shi kaɗai ne gajeran wandonka ba, daga yau ka rasa shi" Jin furucinta sai da gabansa ya faɗi, don shi babu wandon da yake so a duniya sama da wannan wandon nasa da ya mallaka tun kafin ya yi aure Cikin tsantsar mamaki ya ce
"Sakawa za kike?" Ya tambaya don shi a ganinsa in ba sakawa za ta yi ba mene ne na cewa ya rasa shi" Ko uffan bata ce ba sai ta juya ai kuwa ya take mata baya yana faɗin
"Wallahi kika sake wani abu... Bai ƙarasa ba ganin ta zura da gudu shi ma ya bi bayanta da gudun, har falo suka fito ganin ta nufi hanyar ƙofa sai lokacin ma ya lura tsirara yake, ga shi gida ba su kaɗai ba.
Da gudu ya juya ɗaki ya sako rigarsa jallabiya ya fito da sasaarfa, yana fitowa tsakar gidan ya hange ta ta yi hanyar kicin Sumayya da take hangensu daga windown tsabar tsegumi har ɗaɗɗage take. Kafin ya cim mata har ta shige kicin, Saddiqa kuwa tana shiga kicin ta shiga neman ashana da yake a rikice take sai ta rasa ina take jin takun gudu-gudu sauri-saurinsa ya sa ta shiga waige sai sannan ta hangi ashanar a saman loka.
Da sauri ta ɗauka ta fito daga kicin ɗin, yana shirin shiga ya ga ta fito tamkar an jefo ta, har bangaje shi ta yi, can ta yi wajen haryar bayin tsakar gidan ta jefar da wandon ta ƙyasta ashana t jefa masa a take ya kama da wuta. Aminu da sai lokacin ya fahimci abin da ta yi idanu ya zaro a guje ya ƙarasa ya saka ƙafa ya taka wandon wutar ta mutu da wata uwar harara ya bita ya nufi ɗaki saboda ba ya so ya fara mata a tsakar gidan.
Yana zuwa falo ya ɗaga wandon nan ya ga saitin mazaunai ne daga baya ya ƙone, sai ya fito ƙunar har gaban wandon kamar ya yi kuka ya ji saboda soyayyarsa da wandon nan, ɗaki ya shiga ya saka wandon ya cire jallabiyar ta mudubi ya juya ya hangi yagar mazaunan ya ga ana ganinsa, ya duba gaban ya ga mafitsararsa ta fito daga yagar.
Wani takaici ne ya turnuƙe shi amma bai ji zai iya cire wandon ba, yana nan tsaye sai ga Saddiqa ta shigo da mamaki ta kalli wandon a jikinsa ita kuwabta ƙiyasta ba zai sake saka wandon nan ba. Baki ya buɗe zai mata masifa ai kuwa bai kai ga magana ba ya ji ta saka hannu ƙiiii ta fisgi wandon da yake ba wani ƙwari gare shi ba ya tsufa ga dauɗa ta kashe masa ƙarfi kullum shi yake sakawa kamar rai, cikin yahar ta saka hannu ɓetttt yana ja tana ja saida gabaɗaya ta yaga shi shammatarsa ta yi ta fice da wanda ta riƙe ta bar shi sanye da wajen ƙafar wandon ɗaya wacce ta zamo wajen cinyarsa.
Tana fita ta ƙyasta ashanar sai da ya ƙone ƙurmus, Sumayya da take ganin komai sai dariyar mugunta take dukmda bata gane mene ne aka ƙona ba amma dai ta fahimci rigima suke.
Tun da ta dawo ɗakin yake masifa kamar zai cinye ta ɗanya, bango ta ba ajiyarsa ta hau gadon ta kwanta, shi kuma yana tsaye tsirara wai ba zai saka wani wandon ba sai ta maido masa da wanda ta ƙona, cikin bala'i ya ce
"In na saka wani wandon shege nake wallahi ki tashi tun dare bai miki ba ki dawo mini da wandona" Kallonsa ta yi ta ce
"Sai ka ɗaura zani in ba za ka saka wandon ba" Ta ce tana kallon yadda yake tsaye babu kaya kamar wani ƙaramin yaro. Tun da ta bashi baya bata bi ta kansa ba, yake ta masifa ƙarshe bata san yaya ya ƙare ba don bai kwana a gadon ba a ƙasa ya ajiye katifa ya kwanta.
Tun da ta ƙona gajeran wando kamar ta ƙona ɗan mutum sai ya zamana ya ɗauki wata muguwar gaba da ita, sannan kuma wandunan nasa ba ya amfani da su tun da ya nuna bata isa saka shi abin da bai yi niyya ba. Gidansu ya koma a ɗakinsa wani bakko da ya ajiye wasu kaya ya sake ɗakko wasu wandonan biyu wanda sun fi wanda ta ƙona tsufa, ya kawo su gidan yake sakawa sai idanu ta zuba masa.
*BAYAN SATI BIYU*
Jinya take zazaaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani, ga bata cin abinci sai abubuwan kwaɗayi yawan tashin zuciyar da take shi ya fi damunta dole sai lemon tsami take ajiyewa tana lasa, hakan yake kwantar mata da tashin zuciyar. Aminu ganin haka sai ya tsiri takura mata sannan magana ɗaya ce a kan cewa ba dai ciki ta yi ba, wannan kalmar tana ƙona mata rai sai ka ce ita ta yi wa kanta cikin da zai ke faɗin ba dai ciki ta yi ba.
Dakyar ya bata kuɗin zuwa asibiti yana cewa ya san ma ba ciki bane, don haihuwa ba yanzu ba shi a shekara biyar ma babu tsarin haihuwa a tsarinsa. Wannan dalilin nasa ya sanyata fargabar sakamakon asibitin tun da ta san dai bata ganin proid ɗinta, sakamakon farko da ya fito ya nuna cikin wata biyu kwance a mararta . Bayan ta dawo gida gabanta yana tsananta bugu ta miƙa masa takardar sai da ya taɓe baki bai karɓi takardar ba ya ce
"Ba panadol bane aka rubuta miki idan na fita zan sayo, ko ba shi kaɗai bane aka rubuta?" Ya faɗa yana maida hankalinsa kan wayar da yake charting da ƴar aljanna. Wani ƙululun baƙinciki ne ya tokare ta ta kalles shi ta ce
"An ce ina ɗauke da cikin wata biyu" A kiɗime ya tashi tsaye har wayar tana faɗuwa ƙasa ya kalle ta da mamaki cikin ɓacin rai ya ce
"Wane irin ciki wai? Ko dai suna nufin kina da fama da ciwon ciki" Wani kallo ta masa na takaici kafin ta ce
"Ba ciwon ciki ba ina da ciki na haihuwa... Tun kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"Wanann wasa ne ma, sannan idan har gaske ne ina so ki sani zan sayo miki magani ki sha cikin ya zube don ni haihuwa bata cikin tsarina a yanzu" Da tsananin tashin hankali shimfiɗe a koɗaɗɗiyar fuskarta irin ta marar lafiya ta ce
"Zubarwa? Cikin sunnar? To ni wallahi ban shirya yi kisan kai ba, kuma wannan cikin sai na haife shi, ka san baka shirya haihuwa ba ka aure ni? Ko ka san baka shirya haihuwa ba ka neme ni ka biya buƙatarka shin baka san cewa cikin zai shiga ba dama? To wallahi ko mai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa zubar da ciki ba ko da na shege ne bare ɗan sunna" Cike da takaicin shigar masa hanci da ƙudundu ne da take ya kalle ta ya ce
"Ki shirya zama cikun uƙuba kuwa a gidan nan" Kallonsa ta yi tana jin haushin kasancewarsa mijinta kuma uban ƴaƴanta ga ƙazanta ga jahilci ga rashin tsoron Allah, duk da bata da ikon tare ƙaddararta amma ta yi da na sanin auren Aminu!.
Tun daga wannan rana kamar yadda ya faɗa hakan ce ta faru kwata-kwata bata jin daɗin zaman gidan, duk wani abu da take so na kwaɗayi sai dai ta nemawa kanta taimakonta ɗaya idan ta je gidansu Abbanta yana bata kuɗi tun da ba wata sana'a take yi ba, da wannan kuɗin take samu ta sayi abu in tana sha'awa.
Bayan wannan siraɗin sai kuma wasu abubuwa suka fara fitowa lokacin cikinta yana da wata biyar ya fito amma ba sosai ba kasancewar cikin fara bai fiya girma ba. Ƙazanta dai sai abin da ya cigaba saboda shi dai mai hali ba ya canjawa.
Yanzu abin da ya tsiro da shi, ba ya siyan sabulun wanka tun da shi dama ba damuwa ya yi da sabulu ba wankan farin ruwa ma sai lokaci zuwa lokaci, sabulun wanki ba ya siya mata bare a zo ga turaren shafawa ko freshner makilin kuwa ba a ma batunsa duk waɗannan kayan ita take saya amma kuma in ta saya shi kuma zai yi amfani da su idan amfanin hakan ya taso.
Ganin hakan sai take ɓoyewa tun da shi ma da haƙƙin hakan yake kansa bai siya ba, babu dalilin da zai sa ta sarawa jaki ciyawa.
Abin da ta lura kawai ya tsane ta ne saboda cikin da take ɗauke da shi wanda ya so a zubat tun yana ƙarami ta ƙi.
Da yammacin wata ranar laraba tana zaune tana yanke farce a ƙafafun ta da suke kumbure, wayarsa ce ta yi ƙara ganin sunan ƴar aljanna sai ya washe haƙora, da tashi zai yi daga wajen sai kuma don ya ƙona mata rai ya ɗaga wayar a gabanta ya ce
"Hello ƴar aljannata" Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ta ce
"Na'am ɗan aljanna albishirinka" Ta faɗa cike da ɗokin sanar da shi. Baki a washe ya ce
"Goro fari ƙal" Cikin murna ta ce
"Babana ya ce ya amince a yi bikina, wai na cigaba da karatun a ɗakin mijina shi ne ya ce in faɗa maka ka turo manyanka"
*INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI WANNN ACCONT ƊIN *** YANZU DA WANNN NUMBER NAKE CHARTING ****
*DUK MAI BUƘATAR MAGANA DA NI YA MINI TA WANCAN ƊIN KAFIN SU BUƊE MINI ƊAYA, MAI SON LITTAFI KO KAYAN MATA NA KAMFANINMU NA MEERAH B HERBS KO KAYANA NA ZANNUWAN GADO TAKALMA ATAMFOFI DA SAURANSU YA TUNTUƁENI*
*MAMAN AFRAH ****
[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****