Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 11
Gaban Aminu ne ya buga da ƙarfi, jin wani ɗan jijjiɓin tashin hankalin kuma, a zuciyarsa ya ce
'Ana wata ga wata hallaw, ni da nake ta fama da matar ɗaya ma abu yana neman gagara, ita ma tana zaune da ciki turtsitsi ke ma ki zo da wanga batu' A fili kuma sai ya haɗiye wani yawu muduk, yana mai mayar da kallonsa kan Saddiqa da take yankan farcenta hankali kwance a zuciyarsa ya ƙara faɗin
'Saddiqa wannan abu ba ke kaɗai ya samu ba har da ni, mata biyu ni Aminu ta ina zan fara ɗawainiya da su' Ya faɗa yana jin tamkar ya kurma ihu. Saddiqa kuwa ganin ya tsare ta da ido sai ta ce
"Lafiya dai?" Ta faɗa tana kallonsa, yaƙe ya saki yana wani ciccira ido tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amayar ya ce
"Babu komai Saddiqa cigaba da yankan farcen naki, ni ma kya aramin rezar in yanke" Ya ce bayan ya ɗan kawar da wayar saga kunnensa yana sakin wani yaƙen a karo na biyu. Saddiqa kuwa mamaki ne ya kamata ganin mutumin da ko kaɗan ba ya son ya raɓi tsafta, amma yau har yana batun zai yanke farce, duk da haka bata yarda da maganarsa ba don ta ga rashin gaskiya ƙiri-ƙiri a tare da shi ga wani uban gumi da yake wanke masa fuska da wuya, tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya. Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ƴar aljanna ta katse shi da faɗin
"Wai ɗan aljannata ya na ji ka yi shiru? Ko baka yi murna da jin wannan kyakkyawan albishir ɗin ba" Jin abin da ta ce sai ya tattaro jarumta ya tashi ya fita daga falon,
Takalmi ya saka ya fice daga gidan, yana zuwa ƙofar gida ya buɗe baki ya ce
"Kai amma Baba ya kyauta" Wannan kalmar kaɗai ya yi ƙarfin halin faɗa, don shi gabaɗaya sai ya ji an rikita masa lissafi ai shi tun da aka ce sai ta gama karatu ya ɗauka shekaru ne a nan gaba. Zulaiha jin amsar ta yi banbarakwai don ta ɗauka ɗoki da murnarsa ya wuce haka, cikin jin haushi ta ce
"Ni ban gane maka ba, yanzu in zo maka da wannan albishir amma ka ce wai Baba ya kyauta, sai wani kame -kame kake anya kana da gaskiya kuwa? Ko dai tsoron matarka kake?" Jin ta harbo jirginsa tana cewa yana kame-kame kamar dai bai yi murna da jin maganar ba sai ya saki wata dariya yana mai bayyana farinciki ya ce
"A haba ita ɗin banza, yo har akwai wata mace da za ta sa in ji tsoronta saboda ke, ai kawai i cewa Baban zan aiko kawai ya shirya watannin aure in ma shekara zai saka to, in kuma yana ganin ma har kya gama karatun ai duk ana kan hanya... Jin furucinsa sai ranta ya ɓaci cikin harzuƙa ta ce
"In ce maka ya janye batun karatun kake cewa wai in har na gama karatun, kuma da kake cewa watanni ko shekara shi cewa ya yi wata ɗaya zai saka" Ta ce ranta yana ƙuna, gabansa ne ya faɗi wai wata ɗaya, dakyar ya shawo kanta yana lallaɓa ta bata san gabaɗaya shi ta saka shi a matsala ba, ba wai ba ya sonta ba amma riƙon matan biyun ne ya sare.
Washe gari da daddare ya nufi gidansu, da Fatima ƙanwarsa ya fara cin karo don ita ta amsa masa sallama, bayan ya shigo ta ce
"Yaya barka da dare" Hannu ya ɗaga mata bai amsa ba, saboda ya lura yarinyar nan ta ga makwancinsa don ko ranar da ya zo ɗaukan gajerinan wanduna sai da ta leƙa ɗakin nasa, tana tambayar ina zai kai wannan tsumman ko ƙonawa za a yi ya bata ta ƙona a murhu. Ita ma ta faɗi hakan ne saboda ta san wataƙila gidansa zai tafi da su saboda ta san mai hali ba ya canja halinsa, amma wata uwar harara da ya jefe ta da ita, hakan ya sa ta bar wajen ba shiri.
Falon Babansu ya wuce a can ya same su shi da Umma suna ɗan taɓa hira, bayan ya gaishe su Umma take tambayarsa Saddiqa ya ce tana lafiya. Kai ya sunkuyar yana son faɗar maganar gidansu Zulaiha Umma ce ta ce
"Aminu lafiya kuwa? Ko dai Saddiqar ce babu lafiya?" Murmushi ya saki yana mai sosa ƙeya ya ce
"Lafiyarta ƙalau, kawai dai ina tafe da wani batu ne" Kallon tsaf Umma ta masa tana jin bata yarda da batun nasa ba amma sai ta ji Babansa ya ce
"Mene ne Aminu" Jin abin da Baban ya faɗa ya shiga zayyana abin da yake tafe da shi cikin ɗari-ɗari.
Wani salati da Umma ta kwasa, shi ya sanya shi ɗagowa yana kallonta, tana dire salatin ta shiga faɗin
"Aminu ashe baka da hankali? Yanzu yarinyar nan mai ladabi da biyayya, tana ɗauke da ciki za ka je mata da batun ƙarin aure, kai yanzu ko wani ya ce ka yi aure ai ka ce ba yanzu ba am... Maganar da Baba ya yi ce, yana mai ɗaga mata hannu ita ta dakatar da ita daga faɗa da ta fara masa ya ce
"Yanzu ke mene ne na tada jijiyoyin wuya, kawai don ya ce zai ƙara aure, sunnar ma'aikin kamar dai ya ce zai yi saɓon Allah" Wani murmushi Aminu ya yi yana mai sunkuyar da kai, jin Baba ya goyi bayansa ji yake kamar ya tashi ya taka rawa. Kallon Baba Umma ta yi za ta ce wani abu amma ya ƙata dakatar da ita da faɗin
"Ku mata dama ai bakwa ƙaunar kishiya, kin ga idan kika yi amfani da kalmar bahaushe da yake cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ba za ki so a mata kishiya ba" Jin furucinsa sai Umma ta buɗe baki wannan karon bai dakatar da ita ba, ta ce
"Yarinyar nan ba ƙaramin haƙuri take da Aminu ba, amma kuma maimakon ya bari ma ta haihu duka yaushe aka yi auren?" Murmushi Baba ya yi tare da faɗin
"A rana ɗaya ma ana iya ɗaurawa namiji aure, da mace sama da ɗaya, kin ga kenan ƙara aure bayan watanni ba zai zama laifi ba, sannan a zaman aure ai kowa haƙuri ake da juna ba wai mutum ɗaya ne mai haƙurin ba" Bata ce komai ba don ta san ko kwana za a yi ba zai sakar mata ba, kallon Aminu ta yi ta ce
"Ka faɗa mata?" Cikin sanyin murya ya ce
"A'a so nake sai abu ya kankama" Tana mai jin takaicin furucinsa ta ce
"Allah tabbatar da alkairi" Baba ne ya ce amin don shi Aminu ya sunkuyar da kai" Gyara zama Baba ya yi ya ce
"Zan sanar da kai lokacin da za mu je sai ka faɗa mata, ita kuma sai ta sanar a gidan nasu, Allah baka ikon yin adalci" Daga haka ya shiga yi wa Baba godiya ya musu sallama ya fita.
Yana fita Baba ya kalli Umma ya ce
"Ki godewa Allah, da har aure ne a ransa ba wai neman mata ba, nawa suna da auren amma suna neman matan waje , kawai ki masa addu'a Allah bashi wuyan ɗauka tun da dai har yana sana'arsa" Kai kawai ta gyara don takaici ma ya hana ta magana, tana tuna Saddiqa da irin haƙurin zama da shi da take, fa shegiyar ƙazantarsa.
Aminu yana fitowa suka yi kiciɓis da Fatima, ta zo wucewa ta wajen falon Baba kallon tsaf ya mata kawai sai ya ji bai yarda da ita ba, cikin kakkausar murya ya ce
"Ke zo nan" Tahowa ta yi sai da ta zo cikin girmamawa ta ce
"Gani Yaya" Yana aika mata harara ya ce
"Ba ke uwar ƴan rawar kai ba, mai shegen surutu idan kika sake ƙaiƙaiyin bakin ki ya sa, kika faɗawa Saddiqa wata magana ni da ke ne" Kallon rashin fahimta ta masa ta ce
"Wace magana kuma Yaya?" Bai faɗa mata komai ba ya sake cewa
"Gargaɗi nake miki dai" Yana kaiwa nan, ya tafi ya barta tsaye tana ta mamaki wace magana ce wannan da yake ta faman faɗin kar Saddiqar ta sani.
*BAYAN KWANA UKU*
Su Baba sun je nema masa aure, sun bayar da kuɗin gaisuwa sannan a wajen aka tsayar da rana da yake har kayan sa ranar Baban Zulaiha ya ce su kai kawai a yi zama ɗaya. Fatima ta ji ciwon auren nan da Yayanta zai yi amma dai sai ta yi addu'ar Allah sa ta kirkice kuma mai tsafta kamar Aunty Saddiqa.
Bayan kwana biyu, yana zaune a falo tana shan garin kwaki da suga da madara, sai gyaɗar da ta saka a ciki. Aminu ne ya zo ya zauna a kan kujera da yake ita a ƙasa take a zaune ta miƙe ƙafa ɗaya, ɗayar kuma ta lanƙwasa ta. Cikin izza ya dube ta yana wani shan ƙamshi ya ce
"Saddiqa ina son sanar da ke wata magana, gabanta ne ya faɗi bata san dalili ba, amma hakan ba ya rasa nasaba da rashin sabo a ce Aminu ya zauna ya ce za su yi magana, cikin nutsuwa haka. Kofin ta ajiye ta saka cokali ta bashi hankalin ta, yana wani ɗaɗɗaga kai irin na rawar kan da ango yake idan zai yi ƙara aure ya ce
"Dama ba wata magana ba ce, ina so abin da zan faɗa ki ɗauke shi ƙaddara, idan kuma baki ɗauka ƙaddara ba, za ki iya ɗaukansa duk yadda kika ga dama" Kallon mamaki ta masa haɗe da na rashin fahimta kafin ta furta komai ya ce
"Aurena nan da sati huɗu" Gabanta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta danne ta ƙura masa ido tana mamaki, hanzarin katse ta ya yi da faɗin
"Za ki zaɓi guda ɗaya, ina nufin ko bedroom ko falo, don ɗaya za ki haɗe kayanki ɗaya ita ma ta zauna" Dummm kunnuwanta suka yi, ta ji zafin maganar amma sai ta mayar da komai ba komai ba, saboda ita yanzu ta rasa a wajen Aminu mene ne za ta yi alfahri da shi a tare da shi ɗin? Wanda har zai sanya ta ji kishinsa, duk wani abu ya toshe hanyar sai dai abin da ba a rasa ba.
"Kai ma sha Allah, amma na ji daɗi, kuma na taya ka murna matuƙa Allah sa abokiyar arziƙi ce" Ta faɗa hankali kwance tana mai ɗaukan kofin ta cigaba da shan garin, duk da tana jin garin a yanzu tamkar maɗaci take sha. Tsaye ya tashi da sauri sai kuma ya koma ya zauna, baki sake yake kallonta yana son gano maganarta da gaske take ko kuma ƙarfin hali ne, saboda abokinsa ya ce masa yau babu zaman lafiya wataƙila ma Saddiqar ta shaƙe masa wuya. Ransa ne ya ɓaci ganin bai gano komai ba a fuskarta sai kwanciyar hankali alamar dai maganar bata ɗaɗata da ƙasa ba, cikin ɓaci rai ya fara magana yana cewa
"Saddiqa anya son Allah da annabi kike mini? Ya za a yi bayan an ce kishi kumallon mata amma ke in zo miki da maganar kishiya ki mini addu'a, sona ne bakya yi ko kuwa? Don duk inda so yake akwai kishi" Daƙyar ta ci nasarar danne dariyar da take taho mata, ganin ya haƙiƙance yana faɗa da tada jijiyoyin wuya amma sai ta kalle shi ta yi fari da ido haɗe da murmushin fatar baki ta ce
"Kamar ya? Tambaya kake ko neman sani? "
Wannan yanayin da ta yi furucin ya sake harzuƙa shi ya ce
"Cewa na yi anya kina sona?" Wannan karon dariyar da ta yi sai da kyawawan haƙoranta suka bayyana ta ce
"Shafa ka ji" Tsaye ya ƙara tashi ganin ita ma ta miƙe, yana huci ya ce
"In shafa ina? Ai so a zuciya yake ke ya kamata ki faɗa mini" Kallon sheƙeƙe ta masa ta ce
"Ni ma ban sani ba, abu ɗaya dai na sani ni matarka ce, sanna kai mene ne damuwarka da ina sonka ko ba na sonka, kai da za ka kawo sabuwar amarya? Abu na gaba ka kira amaryar ka tambaye ta tsakanin falo da bedroom wanne take so, duk wanda ta zaɓa sai ka faɗa mini na ɗauki wanda bata zaɓa ɗin ba" Tana gama faɗar haka ta fice daga falon ta tafi kicin za ta kai kofin da ta sha garin.
Tsaye ya yi yana riƙe da ƙugu da hannu biyu, ransa ƙuna yake shi da ya zo ya ɓata mata rai, amma ido ya juye da mujiya tun da ga shi, shi ne yake tsaye ransa yana ɓaci. Kallon jikinsa ya yi yana rayawa a ransa to shi kuwa bai kai a yi kishinsa ba ko me? Shi da ake bashi labarin yanzu zai zama kamar ƙwai a wajen matan nasa, kowacce tana ririta shi, kowacce za take son shi ana rububinsa amma tun ba a je ko ina ba Saddiqa ta nuna shi bata kishinsa?.
Yana cikin wannan halin wayarsa ta fara ƙara, ɗakkowa ya yi ya ga sunan abokinsa, a ƙufule ya ɗaga daga ɗaya ɓangaren abokin ya ce
"Ango ka sha ƙamshi, ango ɗan gatan amarya da uwar gida" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare masa wuya, tsabsr haushi kasa cewa komai ya yi ya katse wayar, don ya san yanzu yana faɗa masa yadda suka kwashe da Saddiqa da ya sanar da ita auren, shikenan ya samu abin tsokana.
Saddiqa kuwa tana zuwa kicin ta ajiye kofin, wani irin ɓacin rai ne yake dabaibayar zuciyarta, ita ganin yaushe ma aka yi aurenta, yaushe ma ta ji daɗin zaman gidan mijin da har za a kawo mata wata abokiyar zama?.
Ta jima tsaye a kicin ɗin har sai da ta ji ta samu nutsuwa ta hanyar yin addu'a sannan ta dawo falon, bata same shi ba baki ta taɓe tana ƙarewa falon kallo, bedroom ɗin ta ƙarasa tana ƙare masa kallo ta tabbatar duka biyu babu wanda zai iya ɗaukan kujeru set da kayan gado, dole sai dai an rage kujerun.
Bakin gado ta je ta zauna, ta ɗauki wayarta ta kira, Mamyn ta, bayan sun gaisa ta shiga labarta mata abin da Aminun ya sanar da ita, sosai Mamy ta kwantar mata da hankali, duk da ta ji ciwon abun kuma ta lura tun ba yau ba Saddiqar tana cikin damuwa amma dai babu yadda za a yi da abin da Allah ya tsara.
Noor ƙanwarta ma da ta karɓi wayar, sai da ta kusa kuka jin za a yi wa Auntyn ta kishiya, gabaɗaya ma ita sai ta ji aure ya fita ranta, tun da dai tana ganin soyayyar da take tsakanin Aunty Saddiqa da Yaya Aminu amma tun ba a je ko ina ba zai mata kishiya.
Bayan sun gama ta kira Khady take faɗa mata, haushi ne ya turnuƙe Khady ta ce
"Ai gwara ma ya yi auren, kya samu salama ta wani fannin, ki yi haƙuri ƙawata mahaƙurci mawadaci, in dai aure ne ga wurin nan in kika yi haƙuri kwana nawa ne, maye ya yi amarya ya cinye kayarsa da sannu watarana za ki gan su a rana ke dai ki kame kanki ban da ɗaukan cin fuska ko raini" Sosai Khadyn ta kwantar mata da hankali hakan ya sa ta ji ƴar salama a ranta.
Ummar Aminu har gida ta zo ta lallashe ta, tare da bata haƙuri sosai Saddiqa ta ji daɗin kulawarta, ko ba komai ta ƙara kima da daraja a idanunta.
Aminu tun daga ranar ya shiga muzurai, shi a dole Saddiqa bata son shi, hakan ya sanya duk abin da zai yi da gayya yake don ranta ya ɓaci, amma ita sai ta yi kamar bata san yana yi ba.
Da yake Zulaiha ya tambaya ta zaɓi bedroom, hakan ya sa Saddiqa aka mayar mata kujerarta guda ɗaya gida, da yake bata samu waje a falon ba, ƙofar bedroom ɗin kuma ya rufe ta, aka fasa wata daga waje aka fara aikin amarya haiƙan duk da yana jin ciwon fitar da kuɗin amma ina ya tuna gwangwajewa zai yi da amarya, sai ya da dama-dama kibiya a ido.
Wani sabon salon wai kiran sallah da usur, Zulaiha ta ce ita ba za ta zauna a ɗaki mai siminti ba, dole sai an saka mata tiles har jikin bango, haka Aminu ya yi ƙuri ya saya aka gwangwaje ɗakin amarya uwar gida kwa ko oho.
Kasancewar bayin a bedroom yake sai ya zamana ya zama a ɓangaren Zulaiha hakan ya sa aka yi wa Saddiqa wani bayin a waje, tun da wanda yake tsakar gidan na kowa da kowa ne. Saddiqa duk da ta ga yadda yake kashe kuɗi ana aiki amma bata ɗaga hankalinta ba.
Sumayya da Amina suna gefe suna mata dariyar ƙetar za a mata kishiya, lamarin sosai ya tsorata Amina ganin Aminu zai yi aure, ita da take sha'awar miji ƙazami saboda tsabar kishinta amma sai ga shi ƙazamin zai yi aure.
Tun da bikin ya ƙarato yawancin kullum yana gidan su Zulaiha ƴar aljanna, ɗakin amarya kullum in zai fita ya garƙame da mukulli, sai dai ba a raba musu kicin ba don wannan guda ɗayan ne hakan ya sa Saddiqa ta tattara kayan kicin ɗin ta saka a lokokin kicin ɗin ta bar wanda za take amfani da su kawai.
Ganin bikin ya zo, sai Aminu ya fara ɗaga mata wani kai, yana jijji da kansa ki gidan ya dawo sai ya buɗe ɗakin amarya da aka gama ya shiga, wani lokacin ma sai dai in ta je kicin ta ga ya zuba abincinsa ya je ɗakin amarya ya ci, wai tun kafin amaryar ma ta tare.
Tun saura kwana biyu ɗaurin aure aka zo aka yi jere a ɗakin amayar, ango sai giggiwa yake yana bada faɗi shi ala dole mai amarya.
A ɓangaren amarya Zulaiha babu ya ita, don magungunan matan MEERAH B HERBS masu kyau da inganci, da farko maganin sanyi Mamarta ta saya mata na kamfanin MEERAH B HERBS, saboda duk wani abu da ya shafi maganinmata ba ya aiki, in har akwai sanyi a jikin mace. Magungunan mata da na hips, duk na MEERAH B ne suka saya a wajen Maman Afrah ga number ta mai buƙata ya tuntuɓe ta ***, don kama daga set na kayan uwar gida, set na amarya, set na mai jego babu abin da basa siyarwa.
Zannuwan gado da labulaye, tumtum da frame, duk a wajen Maman Afrah akansiyawa ƴar aljanna, jin yadda magungunan suka fara saukar mata da ni'ima ya sa ta gane tabbas magungunan kamfanin MEERAH B HERBS suna da kyau.
Yau ya akama asabar a yau aka ɗaura auren Aminu da amaryarsa Zulaiha.
Saddiqa bata yi wata gayyata ba, daga Khady ƙawarta sai Noor ƙanwarta sai kuma Fatima ƙanwar Aminu, sai Amina da kuma Sumayya. Leshi ta ɗauka na lefenta aka mata doguwar riga buba, wacce ta karɓe ta don gabaɗaya sai ya ƙara mata kyau, kasancewar cikin girmab jiki ya ƙara mata, ta ƙarw cikowa ta yi kyau, ga ƙirjin nan nata da duk ya cika bra, kamar ita ce amarya in ba wanda ya lura ba babu mai cewa tana da cikin wata shida.
Bayan an kawo amarya, kowa ya watse bayan wata Auntyn Saddiqa da suka zo, su ne suka mata nasiha haɗe da bata baki. Bayan kowa ya tafi tana zaune a kan kujera, tana jin shigowar Aminu da abokansa amma babu wanda ya shigo ɗakinta a cikinsu, tana jin suka wuce ɗakin amarya, duk da faɗan da su Yaya Sule da Yaya Shafi'u suka masa amma bata ga alamar zai saduda ko ya sakko ba, don yanzu a yadda ta lura da ita da rashinta uwar ubansu ɗaya a wajensa.
Ɓangaren amarya da ango kuwa, tun da abokansa suka tafi, ya shiga rawar ƙafa a wajen amarya, haka suka sha amarcida amarya duk da cewar wannan ne karo na farko da namiji ya kusance ta, amma dai sai ta ga kamar akwai gyara a lamarin angon nata.
A nashi ɓangaren sai ya ji ƴar aljanna, bata kai Saddiqa a komai ba na ɓangaren ƴa mace. Abin da ya bashi mamaki bai wuce yadda ya yi buzigir babu wankan tsarki ba ita ma haka ta kwanta ko a jikinta, haka ma da asuba babu wanda ya tashi yin sallah, da gari ya waye tangararai ya yunƙura ya tashi da yake ta saka pant da suka gama sunna, idanunsa ƙirrrr a jikin pant ɗin tun da bacci take, yadda ya ga datti a jikin pant ɗin ne ya bashi mamaki ganin pant ɗin ba sabo bane kuma akwai dauɗa a jiki.
Tambayar da ya yi wa kansa ta farko ita ce, ina panties ɗin da ya saka a kayan lefe har dozin biyu? Kanta ya kalla wanda babu kitso da alama shamfo aka yi don ya ga ribom ɗin kanta shi da ban gashin da ban saboda kan nata da alama dakyar ya yi parkin. Da wannan ɗan al'ajabin ya sauka daga gadon ya nufi bayi karon farko da ya ji Saddiqa ta faɗo masa, wacce bata kwanciya sai ta tsarkake jikinta sannan har shi take yi wa faɗan kawar da najasa, amma yau ga shi ita wannan sai bacci take hankali kwance.
Wankan tsarki ya yi ya fito bayan ya yi alwala, da yake ma ko sabulun wanka bai gani a bayin ba, yana fitowa ya ɗan taɓa Zulaiha ganin har takwas ta gota. Idanu ta ɗan buɗe tana yatsina haɗe da doka tsaki ta ce
"Haba Aminu ya za ka tashe ni, ka san ni ko a gida in ana son ganin ɓacin raina to a tashe ni daga bacci" Kasake ya yi yana kallonta, ya fara tunanin to wa ta yi wa tsakin? Sannan ina ɗan aljannan da take kiransa. Dannewa ya yi ya ce
"Ki tashi ki yi wanka da sallah mana" Ko gizau bata yi ba sai kuma dai ta ce
"Goma ta yi?" Da mamaki ya kalle ta ya ce
"Goma kuma?" Kallonsa ta yi tana daga kwancen ta ce
"To a gidanmu sai tara nake sallah, yanzu kuma nan gidan mijina ne ka ga sai goma ta yi na yi" Bakinsa ne ya ƙi rufuwa a zuciyarsa ya ce
'Yasin wannan ta fi ni jahilci da wasa da sallah, duk tsiya bana kaiwa goma ban yi sallaha ba, yanzu wannan ya kwaso a matsayin mata turƙashi'
Dakyar ya lallashe ta, ta shiga bayi ko minti uku bata rufa ba sai gata ta fito, kallonta ya yi tana ɗaure da tawul, fatarta sai sheƙin rashin fitar wanka take ya saba da ganin fatar Saddiqa ko tsayawa ruwa ba ya yi saboda fita a wanka ya ce
"Babu sabulu a banaɗakin ko?" Ya faɗa yana fargabar amsar da za ta bashi, don ba ya so ya gano wani abu na cewa ƙazama ce don ya ga alamomi sun fara bayyana. Fuska ta ɗan yatsina ta ce
"Sabulu kuma, kar ka damu kanka ni ba baƙuwar zafi ba ce, don a gidanmu kowa da sabulunsa, na kowa sai ya ƙare nawa yana nan" Wani yawu ya haɗiye ya ce
"Mai ya sa?"
"Wallahi sai in yi sati ban yi wanka da sabulu ba, ni a na yi amfanu da sabulu watarana na goga sau ɗaya a hannuna na wanke fuska, uban jiki kuwa idan na kwara baƙin ruwa ya wadatar, ai ni dama ina cewa mijina ya huta da siyan sabulu" Shi kaɗai ya san yanayin da ya shiga da ta furta kalmar baƙin ruwa ya wadatar, ashe dai ko kai ƙazami ne baka son ƙazamar mace? Wannan yake ta saƙawa a ransa sai dai ya dake ya ce
"Wai ni kuwa ina panties da aka saka a lefe, na ga na jikinki kamar ba wanda aka saka ba ne? " Tana saka riga ta ce
"Na rabar da dozin ɗaya, dozin ɗayar yana nan cikin akwatin, tun da ina da wanda nake amfani da su a gida ai ba sai na ɓata wani ba, shi wando da a ciki yake a rufe ba gani za a yi ba" Tana faɗar haka ta hau sallaya hankali kwance ta kabbara sallah, ba tare da ta sake cewa komai ba, shi kuma ta ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa saboda ya ga yanzu ma wandon jiyan ne ta mayar ta saka riga bata sauya wani ba.
Tun da ya ja tasa sallayar ya kabbara sallah, har ya idar bashi da nutsuwa sosai yana ta tunanin dama Zulaiha kura ce da fatar akuya ko yaya?.
Ko da ta idar kwanciya ta yi tana danna waya, shi kuma ya shiga tunanin ranar farkon aurensu da Saddiqa gyaran ɗaki ta shiga yi washe gari har yana hanata. Wai ita amarya ba za ta shiga kicin ba, haka ta saka shi zuwa ya dafa shayi ya ɗumama kazar ya kawo musu, ta hanƙare ciki tana ci tana korawa da shayi.
Inda suka gama break fast ɗin, a nan ta bar kayan, shi ma bai ɗauke ba yana son ganin gudun ruwanta. Wajen sha ɗaya ta ce ya siyo mata kati, haka ya fita ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Saddiqa yana ta waiwaye, don da ya zo giftawa ma sai da ya shaƙo ƙamshin turaren wuta. Zulaiha kuwa yana fita garin tashi za ta shiga banɗaki, ta tuntsurar da kofin da ta sha shayin ya zube, ko ta kanta bata bi ba ta shiga bayin.
Aminu da ya dawo daga siyen kati, yana shigowa bai lura da shayin ba ya ɗora ƙafarsa, ji kake suuuuu santsin sabon tiles da na shayi ya kwashe shi, sai da ya yi gaba-gaba ya yi baya, yana ta baza hannu inda zai dafa wani abu amma sai da ya je ƙasa, zaman ƴan bori ya yi yana jan salati.
Zulaiha jin faɗuwar abu ta fito daga bayin, ganin Aminu yashe yana riƙe da ƙudu sai kuwa ta fashe da dariya ta ce
"Ango garin yaya?" Wani haushinta da takaicin ƙazantar ta ya tsaya masa a maƙoshi, yana ganin ban da ƙazanta da ta goge ai da bai faɗi ba, tsabar takaici bai san ya yi suɓutar baki ba ya ce
"Saddiqa!!!"
*INA SANAR DA KU WTSAPP SUN RUFE MINI LAYINA *** YANZU DUK MAI NEMANA ZAI MINI MAGANA TA **** [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****