Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 12

by @mamanafrah3028

*AMINA*

Tun daga ranar da ta faɗawa Saddiqa cewar ta kai ƙaran Aminu, wurin su Yaya Sule a kan ƙazanta, shikenan ta ƙara ɗaura ɗamara a ranta cewa dama a ce ƙazami ta aura da babu ruwanta da fargabat ƴanmata. Amma yanzu gashi nan wannan mijin nata mai shegen muguwar tsafta da gayu ta san dole yake birge ƴan mata suna son shi, duk yana cika bakin cewa shi babu shi babu wata ƴa mace amma dai bata yarda da hakan ba don ta san namiji baka raba shi da ƴan mata.

Bayan an yi hakan da kwana biyu, da daddare suna zaune kowa ya duƙufa yana danna waya, wayar Yaya Sule ce ta yi ƙara, idanu ya shiga ciccicirawa gabansa yana faɗuwa, ta wutsiyar idanu ya kalli Amina da take latsa waya ya ga hankalinta bai kai kan wayar da ake masa ba. Da sauri ya kai hannu ya katse kiran, yana shirin mayar da wayar silent wani kiran ya shigo a karo na biyu, a wannan lokacin ne hankalinta ya kai kan wayar da ake masa, barin abin da take ta yi ta maida kallonsa gare shi ta ce

"Baka ji ana ta maka waya ba?" Alamomin rashin gaskiya ne suka bayyana a fuskarsa, duk da ya yi ƙoƙarin danne hakan amma sai da ta fahimta, ganin za ta harbo jirginsa ya yi saurin faɗin

"Wani abokina ne ya dame ni da kira, wai rancen kuɗi yake so ni kuma bana so in bashi saboda taurin bashi gare shi" Ya faɗa yana fatan ta yarda da maganarsa saboda ba zai iya da wannan ɗan banzan kishin nata ba, domin kuwa ya san muddin ta gane budurwa ce ya yi sai ya fi naman cikin oven gasuwa.

Kallon rashin yarda ta bishi da shi, don lokacin kiran ya cigaba da shigowa a karo na uku, wayar kuma tana hannunsa abin da ya ƙara bayyana mata cewar ba gaskiya yake faɗa ba yadda hannunsa yake karkarwa. Wayarta ta ajiye a kan kujerar da take zaune, ta ce

"Yanzu abokin naka ne zai rinƙa kiranka sai ka ce wanda ya baka ajiya? Rance ka ce yake nema fa, to a kan mai zai ke maka kira a jere- a jere kamar dai ya baka ajiya ko kuma shi ne yake binka bashin?" Ta faɗa don har ranta ya fara ƙuna don ta san ƙarya yake, addu'a ya fara a zuciyarsa yana cewa

'Allah ka fitar da ni, Allah ka rufa mini asiri kar wannan masifafiyar ta gano ni... Bai gama addu'ar ba ganin ta ƙaraso gabansa kamar an jefo ta sai ya ɗago kai yana kallon yadda take huci kamar wacce ta yi tseran gudu ya ce

"Ai ni blocking ɗin lambarsa ma zan yi in goge ta, yo ina dalili zai ke damuwa ina gida da iyalai na" Tana tsaye a kansa kiran ya sake shigowa MAMUDA shi ne abin da ta ga an rubuta da manyan baƙi, ajiyar zuciya ta sauke ganin sunan namiji har ta ji salama a ranta sai dai hanzari ba gudu ba yadda ƙwaƙwalwarta ta kai mata cewa kaf cikin abokansa bata san wani MAMUDA ba. Kallon tuhuma ta masa ta ce

"Daga kira ko ɗagawa baka yi ba, sai ka ce wani blockin da goge lamba anya kana da gaskiya kuwa?" Wannan tambayar da ta masa shi ya sa shi saurin cewa

"Bari na ɗaga na faɗa masa bani da kuɗin" Wani ɗan sanyi ta ji a ranta, don har ta yarda da shi ta ce

"Yawwa ɗauki amma ka saka a handsfree" Kallon ta ya yi ya ce

"Haka kawai kina matar aure sai na kunna miki muryar gardi ki ji" Ya faɗa yana muzurai da son nuna mata kishinta yake yi, ɗan kallonsa ta yi tana mai nazartarsa ta ce

"Ikon Allah, in ce dai muryar mace ce take haramun namiji ya ji, kenan yaushe muryar namiji ma ta zama al'aura?" Ta faɗa tana kaiwa wayar hannunsa farmaki, janyewa ya yi yana sakin yaƙe tare da wayincewa ya ce

"Yo ai ni bana son kike jin muryar wani ƙato sai tawa" Wani daɗi ta ji don ita dai maganar soyayya ce rashin aikin yi da ɓata lokaci amma dai in dai fagen kishi ne to ita ce lamba ɗaya.

Sai da ya gama saƙa abin da zai ce sannan ya ɗaga wayar gabansa yana faɗuwa, don ya san ko kiran nan da Salaha budurwarsa ce da suke shan soyayya, ya san yanzu ta ƙufula tun da har katse kiran ya yi, sannan tana ta kira bai ɗauka ba, sannan babban abin ma bai taɓa faɗa mata yana da aure ba saboda ita ɗin ma ya lura tana da mugun kishi, shi kuma wannan ce ƙaddararsa wato mata masu kishin jaraba wanda ya wuce hankali.

Yana tuna irin rikicin da zai shiga a wajen Salaha, in ya kira ta da MAMUDA amma haka ya daure don da wata masifar gwara wata, da ya shiga tashin hankalin Amina ta san budurwarsa ce take kiransa gwara Salahar duk bala'i dai a waya za ta masa ko in ya je wajenta zance, yana ɗagawa idanunsa a kan Amina da ta kasa ta tsare, taimakonsa da Allah ya yi volume ɗin wayar ba a ƙure yake ba, bare ta ji muryar mai magana. Yana kai wayar kunnensa Salaha cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta mai kashe masa jiki da saka shi yin nutso a kogin ƙauna ta ce

"Hello haba babynah tun... Ya san dai bai wuce ƙorafi bane za ta masa a kan ƙin ɗaga wayar da wuri amma haka ya yi ƙundunbala ya ce

"Haba MAMUDA in ce dai mun gama magaa da kai, na ce maka bani da kuɗi amma ka dage kana ta kirana, shin a inanka taɓa gani an bada babu?" Salaha da sauri ta cire wayar a kunneta tana ƙara duba sunan wanda ta kira, duk da ta ji tabbas! Muryar Sule saurayinta ne amma kuma yadda ya amsa mata yana kiranta da sunan namiji wai MAMUDA bayan kuma ita ta fara yin magana, da a ce shi ya kira ta sai ta ce ko bai san ya kira ba.

Amina kuwa jin abin da ya ce, sai ta ji ta ƙara yarda da shi, tana sakin wani murmushi sai kallonsa take ya cigaba da faɗin.

"Don Allah ka nema a wani wajen" Salaha kuka ne kawai bata saki ba amma ranta ya yi mugun ɓaci, ta buɗe baki za ta fara zazzaga masa rashin mutunci ta ji ƙit ya kashe kiran, shi kuma da ya katse kiran bai ɗauke yatsansa ba sai da ya tabbatar ya kashe wayar gabaɗaya, don Amina tana ganin ya sauke wayar daga kunnensa ta koma mazauninta don haka bata ma lura cewa ya kashe wayar ba.

Salaha kuwa a zuciye ta ƙara kiransa, don ta sauke masa kwandon rashin mutunci, amma sai ta ji wayar ma a kashe. Wurgi ta yi da wayar a kan gadonta da take kwance, zuciyarta tana ƙuna don ita ta fara tunanin ko dai Sule wata budurwar ya sake shi ne yana gaban waccen ɗin ita ya maida ta MAMUDA.

Sule kuwa tun da ya kashe wayar nan, hankalinsa bai kwanta ba gabaɗaya hankalinsa, yana wajen Salaharsa, yanzu kuma bai san ya zai yi ya fita su yi waya ya kwantar mata da hankali ba, ya mata bayani hakan ya sa ya ɗan kalli Amina ya ce

"Ni yaran nan duka sun yi bacci?" Bata ɗago ta kalle shi ba ta ce

"Eh duka sun yi bacci, kaima ka san da basu yi bacci ba da tuni suna nan" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce

"Ɗan haɗa mini ruwan shayi mai zafi sosai" Ɗan yatsina fuska ta yi don bata son tashi sai kuma ta tuna lipton ta ƙare cikin zaƙuwa ta ce masa

"Babu lipton fa" Wani murmushin gefen baki ya saki, don dama abin da yake hasashe kenan, shi ya sa ma ya ce a haɗa shayin, wani ƙaramin tsaki ya saki irin na kamar ba ya son ya fita sai ya ce

"Bana son fita, ga shi kuma ina son shan shayin" Kallonsa ta yi ta ce

"To ka fita shagon ƙofar gida ka siyo mana" Wani daɗi ne ya cika ransa ya tashi kamar ba ya so, yana riƙe da wayarsa ɗaya hannun kuma yana taɓa aljihu ya ce

"Bari na karɓo" Ya bata baya ya nufi ƙofar fita, sai murmushi yake matar sauti kamar daga sama sai ya ji ta ce

"Ɗan aramin wayarka, zan yi wani abu, ntwrk ɗina yana ɗaukewa, kafin ka dawo" Idanu ya zaro duk da bata gani, yana jin ta ruguza masa gabaɗaya shirin fita ya lallashi Salaha, ba a nan gizo yake saƙar ba ma, idan ta ga wayar a kashe sai ta tuhume shi dalilin hakan, wannan zai sanya ta zargi cewa da walakin goro a miya, ida kuwa hakan ta faru ya san tana buɗe wayar abu na farko da za ta fara yi shi ne kiran lambar nan mai ɗauke da sunan MAMUDA, cakwakiyar da zai shiga Allah ne kaɗai ya sani, don idan ta kira lambar MAMUDA Salaha za ta ɗauka, kowacce za ta ji muryar ƴar uwarta, da wane baki zai warware wannan badaƙalar, sannan ya san ma bai isa ya hana ta aron wayar ba, saboda hanawar ma wani sabon zargin ne.

Salaha bata san yana da mata ba har da yara biyu, ga shi ta ƙwallafa rai a kansa tana son aurensa, shi ma a nashi ɓangaren haka ne yana son ta da aure, amma yadda ya lura tana da tsananin kishi shi ya sa bai sanar da ita ba, ya bari sai abu ya zo dab amma gashi yau Amina za ta warware masa ƙullin da ya ƙulla. Sannan ita ma Amina bata san ma yana da wata budurwa da yake soyayya da ita ba, ita da kullin burinta ya dawwama da ita kaɗai a rayuwarsa bs tare da kishiya ba, kuma sai yake ɗora ta a kan cewa daga ita babu ƙari kuma duk da mugun kishinta amma yau da alama asirinsa yana dab da tonuwa, wannan shi ake kira rana zafi inuwa ƙuna.

*SUMAYYA*

Zaune take a bakin gado, tana ɗaure da zani ɗaurin ƙirji, Yaya Shafi'u ne ya shigo yana kallonta wani ɓacin rai ya turnuƙe shi, haka ya danne ya ce

"Ranke daɗe Hajia Sumayya" Wani kallon sheƙeƙe ta masa, don ta san wannan maganar da biyu ya faɗa ta ce

"Faɗi da ihu ka ƙara da wayyo, na san dai duk ranar da Allah ya kira ni babu wanda zai hana, don haka sai dai in ce Allah sa ka faɗa da bakin mala'iku" Kallonsa ya mayar kan Ruma da ta taso ta nufo shi za ta kama shi, da sauri ya riƙe hannun yarinyar don kar ta daƙuma masa kayansa ya ce

"Sumayya don Allah kalli yarinyar nan, wallahi wannan ko ƙauye aka je sai an bincika za a samu wanda zai bar ƴarsa a haka dagaje-dagaje da ƙazanta, kalli kwantsa a idanunsa, hanci duk majina, hannunta ta ci abinci duk manja ba a wanke mata ba, sannan shi kansa kayan jikinta babu tsaftacewa. Yanzu a haka kike ganin in ta girma ita ta tsafta ce jikinta bayan uwar da ta haife ta bata tsafta mata ba, duk abin da ake wa yaro shi yake kowa, kalli wandonta Allah kaɗai ya san adadin maimaicin da aka masa" Ya kai ƙarshen maganar yana ɗagowa ya kalleta jin bata ce komai ba, ganin ta zuba masa ido tana wani jijjiga jiki ya san kalamansa basu samu shiga ba, bare su samu matsugunni. Kallon ɗaya saura kwata ta masa ta ce

"Ka gama? Na ce ka gama? Sau nawa kake so na maimata maka cewar duk wanda ya raina tsayuwar wata hawa yake ya gyara ba, kullum magana ɗaya kamar karatu yanyanyanyan tun da ba ɗauka zan yi ba ya kamata ka haƙura ya shafa mini lafiya" Ta kai ƙarshen maganar taba sakin wata gyatsa, da alama ta yi over feeding saboda shegen ci kamar gara.

Hannun Ruma ya kama ya fita da ita, wanka mata hannun ya yi ya dawo da ita ɗakin ya cire mata kaya, banɗaki ya shiga zai mata wanka, pant ɗin Sumayya ya gani rataye babu wanki abin haushin ma jinin period ne a jiki amma saboda tsabagen ƙazanta ba za ta wanke ba ta rataye a haka.

Ji ya yi tamkar ya yi kuka, yawu ya tofar a daddafe ya yi wa Ruma wanka suka fito, lokacin Sumayya ta tashi tsaye, priod ɗin ya gani ya ɓata mata zani daga baya sannan har inda ta tashi ma gashi nan ya taɓa bedshet ɗin, kallon bedsheet ɗin ya yi yana jin wani haushi zanin gadon da ya yi oder wajen Maman Afrah ne yadi mai kyau da inganci ba ya tashi bare koɗewa amma saboda tsabar rashin gyara da ba ya samu duk ya fita hayyacinsa.

Ita ko a jikinta ma, kayan wanki ta birkita ta kwaso panties ɗin ta masu yawa, duk babu wani mai wanki sun yi duƙun-duƙun wasu da priod a jiki, zazzagawa ta shiga yi ta ɗauki wani ta mayar da sauran, baya ta juya ta saka pant ɗin tare da ɗaukan wata doguwar rigar bacci marar wanki ta saka ta cire zanin gadon ta haɗa da zanin da ta cire da pant ɗin, ta tuƙunƙuna ta tura su kayan wanki.

Wayarta ta ɗauka a kan madubi ta koma bakin gadon ta zauna. Shafi'u sai da ya shirya Ruma dakyar ya samo wankakkiyar riga ya saka mata, ya ɗakko turare ya fesa mata, tuni ta shiga murna don yaro ma yana son gayu amma ita bata samu saboda ƙazantar uwarta.

Drower Sumayya ya buɗe ya ga yadda ta jera pad(Always) Kowacce yadda ya siyo ko buɗewa bata yi ba, idan wani watan ya yi sai ya ƙasa siyowa amma saboda rashin tsafta shi ne take tarawa kamar wanda za ta siyar.

Kamar zai yi kuka ya ce

"Sumayya ƙazantarki ta ishe ni wallahi, yanzu a matsayinki na mace bakya jin ƙarni ma a ce kina priod amma babu pad a jikinki kin gwammace jini yake ɓata miki jiki, bakya ma kunyar kike shiga cikin mutane babu wanka babu tsafta ce jikin ki matsayin na mai haila? Maimakon daga pad ɗin ta jiƙe ki sauya amma ke sakawa ne na bakya yi" Jin yana ta zuba cikin ƙufula ta ce

"Faɗawa kunne ƙeya ta baka amsa" Tana gama faɗar haka ta juya masa ƙeya.

Kallonta ya yi ya ce

"Haka kika ce ko?" Yatsina fuska ta yi ta ce

"Ni wallahi na kasa gane maka, anya ba haushina kake ji ba saboda ina mace Allah ya ɗaga mini yin sallah idan ina priod, ai ina lura da kai ko a watan azumi idan ina fashin azumi saboda priod sai in ga kana ta ɓata rai, da alama baƙinciki kake saboda ku maza bakwa fashin yin sallah" Wani takaici ne ya cika shi, ganin ana ga yaƙi tana ga ƙura, bata san cewa shi tsabar ƙarnin da take yi in tana priod ne ba ta so ba saboda bata gyara jikinta.

Ruma ya kama zai fita da ita falo, sai ji ya yi Sumayya ta ce

"Bari dai in je in watsa ruwan nan, kar a jima a ga bana nan na ɓace" Juyowa ya yi don ya san da shi take ya ce

"Tun da ga maye ba, mai zai hana a rasa ki" Baki ta taɓe ta ce

"Ni dai ban ce ba" Tana faɗar hakan ta faɗa banɗakin, Ruma ya ce ta je wajen Aunty wato Saddiqa tana fita ya koma ɗakin, ganin vata rufo bayin ba karowa ta yi ya ƙarasa bakin ƙofar bayin ya tsaya yana kallonta da yake ta bashi baya ne yana gani ta ɗauki sabulu wankan ta goga a pant ɗinta, ta wanke pant ɗin ba wani fita ya yi ba ta matse ta rataye ta fara watsa ruwa ko sabulun bata saka a wankan ba bare a yi zancen soso.

Tana gama sheƙa ruwanta ta janyo pant ɗin da ta wanke da lema ta saka, ta ja zaninta ta ɗauro, da sauri ya matsa daga bakin ƙofar, tana fitowa ya ji wani ƙarni ga fatar nan tata sai sheƙi take alamar an tado dauɗa.

Yana ƙare mata kallo a fusace ya ciro belt ɗin jikinsa, idanu ta zaro ganin ya ɗaga fuskarsa a murtuke babu alamar wasa ya ce

"Ko ki koma ki yi wankan kirki, ko wallahi na zazzabga miki" Ganin ransa ɓace sosai ta ga babu wasa ta juya tana gungune, yana tsaye ta yi wankan ya koma ya kwaso panties ɗinta guda goma sha biyar na Ruma goma, ya watsa mata banɗakin, ya ɗauko klin ya jefa mata ya koma gefe ya kama ƙugu, tuni ta shiga wankewa tana sake saɓawa har sai da suka fita ta ɗauraye sannan ta shanya ya bar wajen, da yake tana da abin shanyar panties a banɗakin.

Ɗaya daga cikin wasu sabbin panties da ya shigo da su jiya ya ajiye a drowersa ya ɗakko, always ya buɗe ya ɗakko ɗaya ya buɗe ya manna a jikin pant ɗin, bayan ya goga miski a jiki. Miƙa mata pant ɗin ya yi sannan ya gogo muskin ya shafa mata a mara ya ce ta saka pant ɗin.

Tana sakawa ta shafa mai, ya bata rigar abaya a drower sa saboda ƙazantar ta, yanzu ko ya sayo kaya ba ya son ya bata don duk dafe su za ta yi da dauɗa. Sai da ta saka sannan ya ji wani sanyi a ransa ya kalle ta ya ce

"Ina sonki Sumayya halayenki ne ba na so" Murmushi ta saki, ya ce ta kwaso kayan wankin nasu su je ya taya ta ta wanke, bata yi gardama ba saboda yau ta ga ya sauya kamar dai ba Yaya Shafi,un da ta sani ba.

Washe gari ya yi wanke-wanke ya lallaɓata ta musu abinci ta ce shinkafa da miya za ta yi ya je ya iyo markaɗe ya siyo salad, ya dawo ya ji ɗuriyarta a kicin can ya je hakan ya yi daidai da sheƙa shinkafa da ta yi a cikin tukunyar kan wuta. Da mamaki take kallonsa ganin ya tsaya bakinsa a buɗe yana binta da kallo, ta yi ƙarfin halin faɗin

"Lafiya dai?" Kamar zai yi kuka ya ce

"Haba Sumayya shinkafar na ga kin zuba a haka fa" Cike da mamaki take kallonsa ta ce

"To ba ita za a dafa ba dama?" Wai baki ga abin da kika yi ba" Ta ce

"Ni ban ga komai ba" Ledar hannunsa ya ajiye yana faɗin

"Shinkafar fa kika zuba ba tare da kin wanke ba" Kasaƙe ta tsaya tana kallonsa ta ce

"Ikon Allah na kwance ya faɗi, amma kai ban da abinka har a nunawa na ringingine farin wata, ina mace za ka nuna mini aikina wannan fa shinkafar gwamnati ce wacce ake kira daga buhu sai tukunya, ko a cikin sunan da ake kiranta ka ji an ce daga buhu sai ruwa sai tukunya?" Jin bai ce komai ba ta ɗora da faɗin

"Shinkafar gwamnati ba a wanke ta, shinkafar hausa wacce ake tsince tsakuwa da datti ita ce ta dace da wanki" Tsabar takaici ya rasa bakin magana sai komawa ya yi ya jingina da bango.

*AMINU*

Dariyar da Zulaiha take yi ce ta dakata da yi, jin ya ambato mata sunan kishiyarta a ɗakinta tana aika masa harara ta ce

"Me ka ce, Saddiqa ka ambata Aminu" Idanunsa ya buɗe warai sai yanzu ya gane suɓutar baki da kuma katoɓarar da ya yi, ya san dai zafin faɗuwar da ya yi ne da kuma kewar Saddiqa da ya ji tana masa dabaibayi yau ɗaya.

"Ba ce wa ka kira a tsakar ɗakina" Kallonta ya yi sai yanzu ma ya ga ashe babu kaya a jikinta a ransa yana fatan Allah sa dai wankan sabulu za ta yi, ganin tana tsare shi da ido a ransa ya ce

'Gaba da gabanta aljani ya taka wuta, wato baba ma da babansa kenan'" A fili kuma sai ya ce

"Cewa zan yi fa Saddiqa ta fara zama tarihi a gidan nan tun da kika bayyana, to ke kuma baki bari na ƙarasa ba" Shiru ta yi tana nazarin maganarsa sannan ta juya ta koma ta rufo bayin, yana nan yana naƙudar tashi saboda yadda kwakwason sa yake ji tamkar kakkaryawa ake yi sai gata ta fito, tana cewa

"Yo ni mantawa na yi amarya tana shiga ruwan ɗumi, shi ne ma yanzu nake ɗan jin raɗaɗi sannan kuma ina jin tafiyata tana sauyawa shi ne na juye ruwan flaks ɗin na shiga" Kai kawai ya gyaɗa mata jin bata ce ta yi wankan sabulu ba.

Haka ta karɓi katin ta koma ta zauna, ko taimaka masa bata yi ya tashi ba, ta loda kati a waya ta shiga kiran ƙawaye da ƴan uwa tana faman cewa su taho gidan amarya mana a zo a dafa a ci a sha. Aminu fa sarewa ji ya yi kamar ya ce kar kowa ya zo masa gida amma dai babu yadda ya iya, haka suka rinƙa zuwa kamar mai suna taruwa wasan mai kuwa da suka ringa soye-soye duk sun yi wa man gara lahani.

*BAYAN SATI GUDA*

Sannu -sannu halayen Zulaiha sun bayyana, ƙazama ce fitik ta ajin ƙarshe wannan ya sanya Aminu yi da na sanin aurenta don ya lura ta dame shi ta shanye a ƙazanta. Yanzu duk abin da ya ga Zulaiha ta ɓata sai ya tuna yadda Saddiqa take gyarawa.

Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya yanzu bai wuce yadda bata iya girki ba kwata-kwata, kuma baban tashin hankali da ƙalubalen da yake gabansa shi ne, zuwan abokansa gidansa jibi, akwai abokinsa Kabiru, Lawan da kuma Bukhari wanda yake aikin soja, ba a garin yake ba don haka ko lokacin da ya auri Saddiqa ba ya nan sai yanzu ya ce tun da ya zo gobe za su zo da sauran abokanan nasa guda biyu Kabiru da Lawan.

Da yake Kabiru da Lawan su a gari suke, kuma sun zo lokacin amarcin Saddiqa ta musu abinci na gani na faɗa, ko ina a gyara ko ina yana ƙamshi.

Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya shi ne, tun saura kwana huɗu ɗaurin aurensa, ya samu Saddiqa ya ce mata idan amarya ta tare sai ta yi sati biyu tana girki, duk da Saddiqa ta ji haushi amma sai ta ce ta amince tun da dama ita har murna take za ta samu salama da kwana da Aminu a gado ɗaya.

Yau kuma da ya ji gobe zai yi baƙi sai yake da na sani, tun da, da a ce bai cewa Saddiqa Zulaiha sati biyu za ta yi ba, da tau tun da Zulaiha ta cika sati ɗaya da Saddiqa ce za ta karɓi girki, kuma baƙinsa za su zo a girkin Saddiqa ne ya fita kunya, sai dai su je su gaisa da Zulaiha.

Amma ganin abin yana damunsa, kuma ba ya so ya kunyata a gaban abokai a je ana masa dariya ana gulmarsa, tun da shi ma ana haɗuw da shi a yi ta wasu, amma shi da yake Saddiqa ta fitar da shi kunya shi ya sa wancan karon bai kunyata ba, don haka yanzu ma ya ce a ransa zai je ya lallaɓa Saddiqa ta shiryawa baƙi girki su sauka a wurinta yana fatan Allah ɗora shi a kanta.

Zaune take a kan kujera tana duba hadisin bulugul maram, ya shigo da sallama, amsawa ta yi tana shaƙar wani dummm daga jikinsa, sai ta ji duk warin yana neman hargitsa mata ciki amma a haka ta dake tare da danne mamakinta na ganinsa yana washe mata jajayen haƙoransa da basa samun wanki, tana ta tunanin ko ya amarya take yi? Bata san cewa duk kanwar ja bace, da shi da amaryar zani ce ta tarar da mu je mu.

Ɗan murmushi ta saki ta ce

"Barka da yamma" Ƙurr ya mata da ido sai ya ga kamar an ƙara mata kyau, haƙoranta ya kafe da ido yadda suke tas a wanke gasu nan a jere kamar masara, ƙamshin da yake tashi a jikinta da kuma ɗakin sai ya ji har wata hamma ta fara suɓuce masa, yana kallonta kamar yau ya fara ganinta ko dai hakan bai rasa nasa ba da kwana biyu da bai ganta ba wai shi mai sabuwar amarya ya ce

"Barka dai Hajia Saddiqa mutanen gayu da tsafta" Wata dariya ce mau sauti ta kuɓuce mata jin sunan da ya kira ta da kuma kirarin da ya mata ta ce

"Yau ɗin kuma" Ta faɗa a ranta tana mamakin ashe dai tsafta tana da rana, tun da shi ya tsani tsaftar da take komai ta yi bata iya ba amma yau ga shi yana yabawa, kawar da tunanin ta yi da sake faɗin

"Ko dai ɓatan hanya ka yi, nan fa ba ɗakin amaryarka ba ne" Maganar da ta faɗa ta gane kamar ta ɗan sosa ransa don har a fuskarsa sai da ta fuskanci hakan, amma ta nuna kamar bata gani ba. Shi kuma kawar da maganar tata ya yi ya ce

"Don Allah alfarma na zo nema wajenki" Da mamaki take kallonsa wai ita Saddiqa ce Aminu zai nemi alfarma a wajenta, saurin kawar da tunanin dalilin hakan ta yi ta ce

"Allah sa zan iya" Cikin sanyin murya ya ce

"Dama baƙi ne zan yi, kin gane Bulhari abokina soja?"

Ta ce "Eh na gane shi"

Sai ya ce" Shi ne ya zo gari, to gobe zai zo shi da Kabiru da Lawan shi ne za ki musu abinci" Wata ƴar dariyar rainin hankali ta yi ta ce

"Ni ɗin? Gaskiya bani da lokaci" cike da mamakin kalamanta ya ce

"Baki da lokaci, ni mijinki kike faɗawa haka Saddiqa? Kin manta zamana kike?"

Tsaye ta miƙe daga zaunen da take, kafe ta ya yi da ido ganin body hug ɗin jikinta ta kama ta ga ɗan cikin nan da ba a gani sosai ya zauna ɗas kamar a wajen yake tun asali. Taku ɗaya biyu ta yi ta sauya wajen zama don hamamin hammatarsa ya dame ta, sai da ta koma ɗan nesa da shi ta zauna cikin haɗe fuska ta ce

"Ka manta ba bakina bane? Kai fa ka ce amarya sai ta ci amarcin sati biyu, don haka wallahi ko ruwan zafi babu wanda zan dafawa" Tana kaiwa nan ta hau gado ta naɗe ƙafa ta shiga latsa waya, ɗiff ya yi ya kasa cewa komai don ji yake ya shiga tara ba ma uku ba, din abin ya fi ƙarfin uku sai dai uku sai uku.

Siyam-siyam ya tashi ya fita, da harara ta bi bayansa tana ƙarewa rigar jikinsa kallo, duk saitin hamatar gumi ne daga ganin rigar ma babu wanki.

Yana dawowa ɗakin Zulaiha, ya ganta, zaune tsakiyar gado da ɓawon lemon fata a kan gadon, lemo uku ta yanka da ayaba biyu ta cinye amma ɓawon a kan gado. Wani ɓacin rai ya ji ya linku da wanda Saddiqa ta masa amma ganin so yake ya lallaɓata ta wa baƙi abinci sai ya danne ɓacin ran ya zauna ya ce

"Amaryata, bakya laifi" Kallonsa ta yi tana mai kai hannu tsakiyar kanta da babu kitso ta sosa, garin susar ribom ɗin ya faɗo ai kuwa ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da susa, tana mai cewa ina jinka

"Baƙi zan yi gobe abokaina" Ta ce

"Sai aka yi yaya" Danne takaicin da ya ji na maganarta ya yi ya ce

"Dama sun ƙosa su zo su ganki" Ta ce

"To baka nuna musu hotona, ai ba sai sun ba kansu wahala ba" Shiru ya yi ya ce

"Don Allah ki taimaka abinci suka ce za su ci a nan fa" Ya faɗa yana son ya ce ta taimaka ta musu mai daɗi don ya san babu abin da ta iya dafawa ko jiya sai da ta yi ɗanwake ya narke a ruwa, haka ya dawo sai wani ɗanmalili wanda ake yi da masa a ci da manja da yaji ta yi suka ci ai kuwa ya ɓarke da gudawa, yana tuna abincin Saddiqa baiwar Allah, da ba ya gode mata.

"Allah kawo su lafiya" Ta faɗa tana saka hannu a bireziya ta ringa susa, kallo ɗaya ya mata ya san ba komai bane yake mata ƙaiƙaiyi sai ƙazantar rashin wanka, yau sati guda da zuwanta gidan amma bata taɓa wanka da sabulu ba, wai wankan baƙin ruwa ya wadatar, sai ta ce fatar da za a mayar da ita cikin ƙasar kabari mene ne na wanke ta da sabulu.

Nan dai ya lallaɓa ta, ta ce za ta musu tuwon shinkafa miyar kuka, sai ya ce zai siyo zabuwa ta musu farfesu. Da wanann suka bar maganar.

Washe gari da safe tun da suka yi wankan tsarki, suka yi sallah, ta koma gado ta kwanta, tsintsiya ya ɗauka ya shiga share ɗakin saboda ya san dai a nan baƙin za su sauka, ita kuma ba gyarawa take ba, tana baccin ya shiga share ɗakin, ya sunkuya yana sharo ƙasan gado sai ya hango wani plate da mamaki ya janyo ya ga abinci aka ci aka suɗe kuma aka tura ƙasan gado saboda tsabar ƙazanta, da ganda ba za a fita da shi waje ba.

Kai ya girgiza yana jin ya gamu da gamonsa, fita ya yi da shi ya dawo ya cigaba da sharo ƙasan gadon, abin mamaki sai ya sharo pad, wacce aka yi amfani da ita, ko a leda ba a saka ba, jinin jiki har ya yi wani baƙi-baƙi kore-kore. Da tsintsiya ya janyo pad ɗin har tsakiyar farin tiles ɗin da ya ci uban datti kasancewarsa fari, tamkar ba sati ɗaya ta yi a ɗakin ba, a ƙufule ya shiga faɗin

"Yar aljanna, ƴar aljanna, Zulaiha ke" Idanu ta runtse da ƙarfi jin kitan har tsakar kanta ta tashi a zuciya tana cewa

"Ni fa a kan wasu banzayen abokanka, ba za ka damu rayuwata ba, wallahi in ka taɓo ni sai na fasa mutu tuwon" Ɗif ya yi jin za ta shuka masa salalan tsiya, idan ta ƙi karɓar abokan nan ai ta jaza masa raini da dariya a cikin abokai.

Kai ya karkata gefe kamar maraya ya sassauta murya ya ce

"Ba wannan maganar ba ce, haba Zulaiha leƙo ƙasa ki ga abin da na gani nake kiranki" Fuska ta yatsina tana cewa

"Ka san bana so ake tashina " Ta faɗa tana leƙowa, ya ɗauka za ta nuna wani yanayi in ta ga pad ɗin amma cikin halin ko in kula ta ce

"Lah wai wannan abar ce dama, ai ranar nan ina kwance na ji ta ishe ni, kuma dai na ji kamar jinin ya bar zuba, shi ne na fisgo shegiya na jefa ƙasan gado, na cigaba da baccina" Tana kaiwa nan ta koma ta kwanta ta cigaba da bacci abin ta.

Sakaka yake kallon pad ɗin yana kallonta ita ma, a ransa yana raya cewa ya gamu da gamonsa, tabbas ya auro wacce ta dame shi ta shanye a ƙazanta.

Pad ɗin ya ɗauka a makwashin shara, fita ya yi ya jefa a shara, ya dawo ya cigaba da share ɗakin, dama rabar da ta yi kwana biyu ne priod ɗin ya zo kuma kwana uku ta yi, sai ta yi wanka.

Mopping ya yi ya yi goge -goge, ya kunna turaren tsinke ya saka a kusurwa-kusurwa.

Banɗaki ya shiga, wanka yake so ya yi don ya ga yanzu goma ma ta yi, babu sabulu don tsawon satin nan daga shi gar amarya babu wanda ya yi wanka da sabulu, fitowa ya yi ya zo ya ɗan taɓa ƙafarta yana tsoron ta tashi ta ce an tashe ta, sa'arsa ɗaya bata yi ƙorafi ba ya sasaauta murya ya ce

"Don Allah ina sabulun wankan nan na cikin lefe" Sai da ta tashi ta zauna ta ce

"Sabulun wanka kuma? Dama kana wanka da sabulu ne" Ya ce

"Kin san baƙin nan za su zo shi ya sa gwara na yi wanka, don Allah ke ma ki taso yau ɗaya dai ki yi wanka da sabulu, kar su zo ni wari ke wari abin zai yi yawa shege da hauka" Ya faɗa yana ɗan lallaɓa ta.

Ta ce" To tun dare bai maka ba, ka tafi shago ka siyo, sabulun kayan lefen ne zan fitar ka suɗe shi ai na lefe na amarya ne, saboda adani shi ya sa tsawon sati ban ɗakko ko goga na yi na wanke fuska ba, wannan ajiyewa zan yi har ɗan da zan haifa a wanke shi da sabulun kayan auren ubansa, kuma ni ma dai in ina jego ai sai na ɗan wanka ko banza na wanke ƙarnin jego" Har sai da idanunsa suka kawo ƙwalla wai sabulun ne saboda adani za a ajiye har sai an haihu an yi wa ɗa wanka da shi, ko cikin ma babu kai jama'a.

Magiya ya shiga yi mata, a kan cewa zai mayar mata da haka ta ɗakko guda ɗaya ta bashi, tana cewa sai da ta danne zuciyarta.

Lallaɓata ya yi suka yi wankan tare don sai da ya dirza mata bayanta, suka fito suna ɗan ƙamshin sabulu. Bayan ta shafa mai ta buɗe drower ta ɗakko atamfarta, wacce tun tana gida dama ta kwaso wasu daga cikin kayanta don ta ce va yanzu za ta fara ɗinka na lefe ba, saboda adani.

Kallon atamfar ya yi duk ta sha jiki, ta koɗe ya ce

"Mu da za mu yi baƙi" Daƙayar ta yarda ya ɗakko mata wani leshi daga cikin kayan fitar biki, tana ta mitar ita da ba wani waje za ta je ba, zai sa ta saka sabon kaya. A nan ma sai da Saddiqa ta faɗo masa wacce kullum cikin ado da kwalliya take.

Bayan sun shirya shi ma ya saka wankakken kaya, ta shiga kicin ta fara ɗora ruwan tuwo, tun kan ruwan ya yi zafi bare a yi zancen tafasa, ta kwaso shinkafar tuwon ta zuba. Ta rufe ka ruwa bai ishi shinkafar ba, ta rufe ta koma ɗaki bayan ta haɗa kayan miyar ta tsayar da ruwan miyar. Jimawa can ta dawo, tana buɗe tuwo ta ga har ya fara ƙauri, ga shi shinkafar ta jiƙa babu batun dahuwa, wani wajen ma ɗanye ne haka ta sauke ta tuƙa ta mulmule. Miyar ta kaɗa da yake da bushashen kifi ta yi tana saukewa ta zuba a food flaks ta ajiye. A daidai nan Saddiqa ta shigo kicin ɗin ɗaukan kofi, ganin Zulaiha a ciki sai ta shigo da sallama, amma Zulaiha bata amsa ba, sai ma ta tsiri ƴar waƙa tana faɗawa Saddiqa magana ko ta kanta Saddiqa bata bi ba sai ta ba bango ajiyarta, ta ɗauki abin da ya kawo ta ta fita don gabaɗaya ƙaurin kicin ɗin ma tada mata zuciya yake.

Bayan fitar ta suka ci karo da Aminu, ya dawo riƙe da ledar zabuwa, ko kallonta bai yi ba, tana gaishe ya yi banza, don haushinta yake ji bata wa baƙinsa abinci ba ga shi kuma dai ashe amarya za ta share masa hawaye.

Yana shiga kicin ganin sabbin flaks a kan tire wani daɗi ya cika shi, gar da saka mata albarka ya rungume ta, yana aika mata da sumbata, ita kuma sai ta ji kanta ya yi wani gingirim ita ala dole ta birge miji.

Nan ya fita sayen lemuka ya barta tana dahuwar nama, tana gamawa ta kai ɗaki ta jera. A ɓangaren Aminu yana ƙofar shagon lemuka wayar Bukari ta shigo, yana ɗagawa suke sanar masa suna hanyar gidan nasa, nan ya faɗa musu inda yake suka je suka taho da shi. Yana gaba suna binsa a baya suka shigo gidan, tun daga nesa ya hango Zulaiha a ƙofar ɗakinta tana zaune a baranda, abin da ya gani ne ya mugun ɓata masa rai, shikenan ya san ta wargaza masa mutuncin da yake tattali a wajen abokan nasa, gashi su duka sun ganta....

ME TA YI? MAI YA GANI? AKWAI CAKWAKIYA FA MU HAƊU A PAGE 13 DON JIN AMSAR DA YADDA BAƘI ZA SU SAMU KANSU A ƊAKIB AMARYA

*GABAƊAƳA ZAN BAKU BOOK 1 DAGA FARKO HAR ƘARSHENSA A FREE, IDAN MUKA GAMA BOOK 1 GA WANDA YAKE DA HALI KUMA YAKE BUƘATA ZAI IYA BIYAN KUƊIN BOOK 2* *INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI LAYINA *** YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI ****

~NA GODE MAMAN AFRAH~ [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****