Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 13

by @mamanafrah3028

*YAYA SULE*

Da sauri ya danne makunnar wayarsa, sai kuwa waya ta kunnu, duk da gabansa yana tsananta bugu amma dai da dama -dama a kan a ce ta ga wayar a kashe domin, a take za ta ɗora masa alamar tambaya haɗe da tuhuma. Hannu Amina ta miƙa masa a lokacin da ta tako zuwa gabanta, jikinsa babu ƙarfin tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Addu'a yake karatowa a zuciyarsa, ƙaran shigowar kira wayar wanda mai kiran tamkar jira yake a kunna wayar ya kira dama. Kaɗan ne ya rage Yaya Sule ƙwalla ƙara, saboda ya san kashinsa ya bushe, Amina kuwa har ta ƙagara ta ga mai kiran don har ta fara tunanin wannan anya kuwa MAMUDAN ne?.

Yaya Sule cike da fargaba ya duba fuskar wayar, amma cikin iko da hikimar ubangiji sai ya ga sunan Babansa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da sakin murmushin jin daɗin kuɓuta, cikin ƴar inda-inda ya ce

"Baba ne yake kirana" Ajiyar zuciya Amina ta sauke a fili, hatta Yaya Sule sai da ya ji saukar ajiyar zuciyar a zuciyarsa ya ce

'Yadda kike sauke ajiyar zuciya haka nake saukewa, bambancinmu kawai ni ɓoyayya na sauke ke kuma bayyananniya' Ya ce a zuciyarsa ita ma a zuciyarta ta ce

'Allah na gode maka, ashe dai Baba ne ya kira shi, har gabana ya faɗi ai bana so in ke ɗora zargi a kan mijina, duk da na san ba zai taɓa raɓar wata ƴa mace da sunan so ba, kawai dai sheɗan ne yake saka mini wasi-wasi saboda ba ya so a zauna lafiya' Wayar tana dab da tsinkewa ya ɗaga ya kara a kunne, bayan ya zauna ya ce

"Assalamu alaikum, barka da dare Baba" Daga ɗaya ɓangaren Baba ya amsa sallamarsa, bayan sun gaisa ya tambaye shi su Albani yake cewa sun yi bacci, nan ya shiga cewa

"Sule ni kuwa kun yi magana da Aminu, baka ji gidan su tsohuwar budurwarsa sun ce ya aika ba" Cike da mamaki Sule ya amsa da cewa Aminun bai tunkare shi da maganar ba, nan Baba ya kwashe komai ya faɗa masa, cikin sanyin murya ya ce

"Amma Baba da baka goyi bayansa ba, yanzu yaushe ma aka yi aurensa da Saddiqa, yarinyar nan tana ta fama da ƙazantarsa amma yanzu tun ba a je ko ina ba a ce zai mata kishiya" Amina da tun da ta fahimci bakin zaren zancen, ta saki wani murmushin jin daɗi da farinciki, a hankali ta ajiye wayarta, tasowa ta yi ta je kusa da Sulen ta zauna don ta ji ƙwal uwar daka. Baba ne ya ce masa

"Shi fa zai zauna da matarsa, ka ga bai kamata a tauye masa haƙƙinsa ba" Cike da tausayin Saddiqa Sule ya ce

"Wallahi Baba da ka ce masa ya haƙura ba... Hannun da Amina ta sakawa Sule a bakinsa, shi ya masa shamaki da ƙarasa maganar da yake son yi, kallonta ya yi take masa alamar ya daina cewa a hana Aminun, Baba kuma jin Sule bai ƙarasa maganar ba ya ce

"Ni dai na amince, kai ma ka amsa fatan alkairi, da a ce mutum yana bin mata gwara a ce yana da yawan aure-aure ka ga sai dai mutane su ce mutum yana aure ɗanɗane amma ba wai zina ba" Jin furucin nan na Baba, sai Sule ya buɗe baki don lokacin Amina ta ɗauke hannunta daga bakinsa ganin maganar kuramen da take masa ta yi tasiri, ya ce

"Haka ne Baba, to Allah tabbatar da alkairi" Wannan maganar da ya yi sosai farinciki da annashuwa ya bayyana a fuskar Amina.

Son haka yana cire wayar daga kunnensa ta ce

"Haba kai kuwa, ya za a yi ka hana sunnar ma'aiki" Ta faɗa tana dariyar farinciki, kallonta ya yi ya ce

"Ina ga fa Amina baki gane inda maganar ta dosa ba, magana fa Baba yake a kan Aminu ya je masa da maganar zai yi wa Saddiqa kishiya" Hannu ta tafa, tare da kai hannun ɗaya haɓarta ta ti tagumin mamaki ta ce

"To kuma mene ne, abin da mutum babu ruwansa ai daɗin kallo gare shi" Kallonra ya yi yana tuna irin yadda ta tsani kishiya, amma kuma ga shi tana so a yi wa wani, shi ya sa dama ake cewa mata su ne matsalar kansu da kansu, ya ce

"Amma Amina ya za a yi abin da bakya son a miki, kike so a yi wa wata? Kar ki manta fa yarinyar nan ba a daɗe da aurenta ba, amma yanzu a bijiro da maganar kishiya ai da damuwa" Tsaye ta tashi tana kama ƙugu ta ce

"To ai shi wasa ma waje yake samu, abin da zai iyu ma shi ake yi, ka san dai ai ni bani da abokiyar zama har abada!. Ita kuma in ita ce ƙaddararta waye zai hana a mata?" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce

"Allah bata haƙuri da dangana" Harara ta aika masa ta ce

"Dangana sai ka ce wacce uwarta ta mutu, ni sai wani tausayinta kake" Ɗan shiru ya yi ya ce

"Ba haka bane kin san yarinya ce kuma shi Amina zama da shi sai haƙuri" Baki ta taɓe ta ce

"Kowa ma zaman haƙuri yake da nashi mijin" Tana gama faɗar haka ta koma wajen wayarta, kawai sai ya ji tana voice tana cewa

"Eh mana Aminu ƙanin mijina, wanda ya yi aure kwanannan" Mamaki ne ya rufe shi, daga haka ya zame ya fita siyan lipton ɗin, saboda ko ta kan karɓar wayar bata yi ba hankalinta yana ga bada labari.

Yana fita ya kamo sunan MAMUDA ya doka kira, wajen sau uku wayar tana shiga amma ba a ɗauka ba, ba ya raba ɗayan biyu ya san fushi take da shi. Kiranta ya cigaba da yi a ransa yana cewa

'Mata biyu da alama zama da su zai yi wahala, ga shi dai kowacce bata san da zaman ɗaya ba amma a hakan suna haɗa mini zafi, ina ga na haɗa su waje ɗaya a matsayin matana, lallai akwai badaƙala, ni kuwa yanzu ba zan iya rabuwa da Salaha ba, kin ga Amina kenan taki kishiyar tana tafe kema, tun da har kina yin murna za a yi wa wata, shi dama ramin mugunta gajere ake ginawa' Yana wanann zancen zucin ya ji ta ɗauka, amma bata ce komai ba, cikin ɗan karya murya ya ce

"Baby nah, fushi da ni?" Nana ma shirun ne, amma tana jinsa, ya cigaba da faɗin

"Amma ai gimbiyar tawa ta bani dama, na kare kaina ko? Amma in aka ƙyale ni sai abin ya mini yawa wai shege da hauka" Dariya ce ta ƙwace mata jin karin maganar da ya yi, wani sanyi ya ji a ransa jin ta yi dariya ya san tana dab da sakkowa. Sai da ta tsagaita dariyar ta ce

"Dama ka iya karin magana amma baka mini?" Wani murmushi ya saki cikin zaƙuwa ya ce

"Ni in kullum ma kike so zan ke miki" Shiru ta yi sai kuma ta ce

"Yanzu ni za ka kira da MAMUDA? Bayan kiran da na maka ka ƙi ɗagawa, har da wanda ka katse" Dimmm gabansa ya faɗi, nan ya shiga haɗa kalaman ban baki yana cewa

"Kin san ya aka yi?" Bai jira ta amsa ba ya ɗora da faɗin

"Lokacin da kika kira da farko ba na kusa, da na zo kuma garin in ɗauka na katse, sannan kuma lokacin da na ɗauka, kiran MAMUDA ne ya shigo, ni kuma duk tunanina shi ne kuɗi ne da yake so in ara masa, sai bayan na gama magana na gane katoɓarar da na yi, sanin za ki yi fushi sai na kashe wayar ma baki ɗaya, na ce bari in bari sai kin ɗan huce in zo bada haƙuri, kar in zo ranki a ɓace ki ƙara tunzura" Shiru ta yi tana jinsa, tana kuma nazarin maganarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo sautin ta wayar, sa kuma ta ce

"Allah sarki, ashe duk gudun ɓacin raina ne ya sa ka kashe wayar ma, ba komai na fahimce ka" Daɗi ya ji sosai a ransa, nan suka shiga hirar soyayya, sun daɗe suna magana cikin so da ƙaunar juna, kafin daga bisani suka yi sallama suna masu yin kewar junansu.

Sai da ya ƙarasa shago ya siyo lipton ɗin, sannan ya dawo gida, Amina ko a jikinta da ta ga ya daɗe don bata kawo komai ba, hankalinta yana waya tana gulmar za a a yi wa facalarta kishiya.

Tun da aka yi haka shi ne fa Aminar, take yi wa Saddiqa wani gani-gani tamkar dai ita ce ta jawa kanta kishiyar, shi ya sa ko ranar auren Aminun ma ta rinƙa shiga ta alfarma tana fita, don murna take a ranta tana rayawa saura Sumayya ma, amma ita ta san ita da kishiya sun yi hannun riga.

*AMINU*

Kunya ce ta rufe shi gabaɗaya, yana jin tamkar dai ya je ɗakin Saddiqa ya ɗakko ta ta zo ta maye masa gurbin Zulaiha, ta karɓi baƙin nasa in ya so idan suka tafi ita Zulaihar ta zo.

Amma sai dai bakin alƙamai ya bashe, bai san ledar lemukan hannunsa ta suɓuce ba sai da ya ji Kabiru yana faɗin

"Aminu lafiya dai" Ya lura basu gane abin da yake gani ba, don ya san babu wanda zai yarda cewa Zulaiha matarsa ce, duba da cewa babu wata amarya da za a gani a yanayin da take yanzu. Sanye take da wani zanin atamfa roba, wanda ya ci uban datti tamkar na mai siyar da mai da ƙuli, don yadda ta zo da shi dama babu wani wanki zaninta ne tun tana gida, ita kanta t shirt ɗin da ta daka duk maiƙo ne a jiki ita ma babu wankin kan nan ,nata bucai da shi babu kitso amma ribom ɗin yana jikin gashin, wanda reto ribom ɗin yake kamar zai faɗi saboda gashin ba ya haɗuwa ya yi parking. Tun da ta zo dama bata yi kitso ba, ga kuma uban ruwa da kan yake sha na wankan tsarki.

Wainar fulawa ce a farantin take ci, ta wani barbaje. Haƙori ya saka ya danne leɓansa na ƙasa, yana ƙoƙarij saisaita nutsuwarsa, Lawan ne ya ɗauki ledar da ta faɗin ya riƙe.

Aminu kuwa tunani yake, mai ya sa ta cire les ɗin da ya saka ta saka a jikinta. Ki yake kamar ya je ya yi ta dukanta ko ya huce amma babu dama haka suka ƙaraso shi da abokan nasa yana dariyar yaƙe wacce ta fi kuka ciwo.

Ita kuma ganin suna dab da zuwa, sai ta haɗa tafukan hannayenta ta murza tamkar mai shafa mai, bata nufi ko ina da hannun ba sai kanta, ta shafe maiƙon a jikin gashin kan nata, sai kuma ta mulke ragowar maiƙon a jikin zanin nata ta janyo wata hularta da take gabanta ta saka a kan nata, sai dai wani daga cikin gashin kan nata ya fito daga gefe ɗaya a gaban hular, sai ya yi tamkar doron zabuwa.

Kuka ne kawai Aminu bai saki ba, shu damuwarsa ma Bukari don ya lura Bukarin bai gane cewa wannan matarsa ba ce amaryar da yake ta musu kurin za su je su gani ya yi babban dace, kuma ya yi babban kamu don ya auri muradinsa wacce ƙaddara ta sako Saddiqa a matsayin matar farko kafin ita.

Zulaiha kuwa tana gama saka hular ta miƙe tsaye, tana washe baki tana musu sannu da zuwa, don lokacin har sun zo barandar. Kallonta Aminu ya yi yana jin wani takaicin ganinta da abokansa suka yi a shiga marar kyan gani shiga ta ƙazanta wata irin kunya ta rufe shi yana jin dama bai kawo su ba.

Sai a sannan ya lula tunanin ranar da Khady ƙawar Saddiqa ta zo, yana rayawa a ransa kenan haka Saddiqa ta ji kunya da ƙawarta tw gan shi a haka? Lallai ya yarda cewa baka gane abu har sai an maka shi, amma dai ba za ka gane ciwonsa ba sai in kai aka yi wa.

Sai sannan ya ji ashe bai yi wa Saddiqa adalci ba. Maganar Bukari ne ya katse masa tunani da faɗin

"Wai ina amaryar ne" Kallon kallo aka shiga tsakanin Lawan da Kabiru, don su sun gane cewa wannan ta tsaye a gabansu ita ce amaryar.

"Gani kuwa" Zulaiha ta faɗa tana ƴar dariya irin ta amare, har da wani ɗan kauda kai irin tana jin kunya. Washe baki Aminu ya yi cikin wayancewa yana ƴar dariya ya ce

"Eh mana, ita ce, ai ka ji ma ta baka amsa, dama masu magana sun ce waƙa a bakin mai ita tafi daɗin ji" Bukari kallonta ya yi yana ɗan jinjina abin a zuciyarsa ya ce

"Sannu amarya" Ta ce

"Yawwa" Aminu kuwa ya ga alamar suna son su raina masa hankali, don sun ga amaryarsa cikin shiga marar kyau, ga kuma abin da ta yi na goge maiƙo a tsakiyar kanta da jikin zaninta, shi ya ma rasa mai ya sa ƙazanta ta zaunawa Zulaiha.

Ya ɗauka yadda ta cigaba da karatun nan, zai samu wayewa da tsafta ta fitar hankali, amma dai sai ya ga tana abu kamar dai bata shiga ajin ma kwata-kwata ba.

Ya ƙagara su shiga cikin ɗakin, don su gane ita fa ta rasa giɓi ne ta wani ɓangaren, amma ta fannin girki za su gane yau kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Gaba ya yi yana cewa

"Bismillanku" Suka take masa baya, ita kuma Zulaiha sai ta koma gefe suka wuce. Suna shiga ɗakin suka zazzauna a ƙasa inda ta shimfiɗa table mart ta jera abinci, Aminu sai washe baki yake yana so ya mantar da su abin da suka gani, dai da suka zazzzauna kamar an ce ya kalli gefe kusa da Bukari ya hangi breziyar Zulaiha yashe a wajen, gata ta ci uban dauɗa, hannun breziyar daƙwa-daƙwa kamar mai tallar kalwa, ganin hakan Aminu ya shiga faɗar hakan a zuciyarsa

'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakil, kin kashe ni Zulaiha'

Babu wanda ya lura da breziyar, shi ya sa yake fatan ya samu nasarar kawar da ita daga wajen, ba tare da idanun ɗaya daga cikinsu ba ya gani.

Amma dai ya san da wuya hakan ta kasance, sai a sannan ya tuna ranar da Saddiqa ta ce ya bar mata gajeran wando a falo, amma ya nuna ko a jikinsa ashe dai ko da kai ƙazami ne akwai abin da baka so a gani, bai ankara ba ya ji Lawan ya ce

"Abokina wai ya duk ka yi shiru ne?"

Yaƙe ya yi yana sosa ƙeya, amma hankalinsa yana kan breziyar nan ta Zulaiha, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangi kan gadon ma duk ta cukurkuɗa shimfiɗar, ga kayan da ta cire nan yashe a kan gadon. Sai ya ji dama dai ko durƙusawa Saddiqa ne ya yi ya roƙe ta a kan ta karɓi baƙin nan a wajenta, ya san ko ledar pure water ba za ta jefae a ɗakinta ba, bare kuma wata breziya, a zuciyarsa ya ce

'Allah na tuba breziya ko wankakkiya ce matarka ta jefar abokanka suka gani ai da kunya, bare kuma wannan daƙalƙalar ta ci datti ta more' Cikin kawar musu da tunanin ya ce

"Lah ba komai fa, da yake yau na tashi da ciwon kai" Ya faɗa yana ƴar dariya, tare da kallon Bukari yadda ya ga duk ya yi kamar dai a takure yake, da alama dai ganin Zulaiha ko ya sa ya ji ƙyanƙyami kasancewarsa mai tsantsani.

Zulaiha kuwa da suka shige ta koma ta zauna, har ta zauna ta tuna ba ta kai plate da cokula ba, tashi ta yi ta tafi kicin ɗin amma plate ɗin wainar fulawa yana nan da ɗan guntun yaji a kan farantin.

Riƙe ta taho da plate ɗin da colula a ka, sai kuma kofuna a kan wani plate ɗin, da sallama ta shigo tun da ta shigo wani haushi ne ya turnuƙe Aminu yana aika wa zanin jikinta harara ƙasa-ƙasa, sai lokacin ya ƙure ƙirjinta da kallo ya ga ashe dai breziyar da ya gani cirewa ta yi babu wata a jikinta.

"Barkan ku da rana ina wuninku" Ta faɗa tana daga durƙushen da ta yi, ganin Aminu ya yi fuska sai muzurai yake, ana haka Bukari ya ɗaga hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan breziyar Zulaiha, ya juya zai kalli wajen da sauri Aminu ya ce

"Ni Bukari baka bamu labarin wajen aiki ba" Wannan maganar ce ta ɗaukewa Bukari hankali, bai ga breziya ba, shi kuma Aminu sai tunanin yadda zai yi ya kawar da ita ba tare da sun ankara ba. Zulaiha kuwa bayan ta gaishe su, ta ɗauki zanin less ɗinta a kan gado ta yafa a kanta kamar mayafi don sai lokacin ma ta tuna suturcr jikinta tun da a gaban abokansa ne.

Aminu kuwa sai signa yake mata, a kan ta gyara gaban goshinta, wato hular nan inda gashi ya fito, don ganinta yake kamar bararoji.

Tana fita aka Lawan ya matso da plates ɗin yana faɗin

"Ya kamata mu fara cin abincin nan" Kowa da to ya amsa suka ma manta da batun Zulaiha, sai Aminu da yake kallon breziya lokaci zuwa lokaci yana fatan Allah sa kar su gani, shi ya manta yadda Khady ta ga gajeran wandonsa, Kabiru ne ya ce

"Ni fa a rayuwata ina son cin girkin amare, ban san mai ya sa girkin amarya ya fita da ban ba, shi ya sa ina son abokina ya gayyace ni cin abincin amarya" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, aka shiga buɗe flaks.

Lawan ne ya buɗe flaks ɗin tuwon, ganin tuwon bai mulmulu ba, alamar dai ruwa bai ishi shinkafar ba, sannan ina iya ganin shinkafar raɗo-raɗo alamar rashin tuƙuwa, lura ne ma basu yi ba da sun ga yadda wata take fari tas alamar tana ɗanyarta.

Lawan sakawa kowa tuwo guda ɗaya, a plate ɗinsa, Kabiru har ya ce

"Wannan ai zubin rowa ne, ni na fi son malmala biyu" Sai suka fashe da dariya, irin ta abokai, nan kowa ma ya ce biyu za a zuba masa, amma saboda tsokana sai Lawan ya ce

"Kai ango guda ɗaya za a bar maka, tun da kai kullum kana cin abincin amarya" Dariya ya yi, Kabiru ya buɗe flaks ɗin miya ta yi kauri kirtif saboda yadda aka kaɗa kukar da yawa, ga ɗan ƙarnin kifin da ta saka a miyar yana tashi, kasancewar bata saka corry da sauran kayan ƙamshin da zai kashe ƙarnin ba.

A haka dai aka zubawa kowa miya, basu damu da ƙarnin ba ko yadda miyar take koriya tsarrr tun da wani abincin a ido ne bashi da kyan gani amma a baki sai ka ji yana da ɗanɗano.

Kabiru ne ya gyara zama ya ja nasa farantin gabansa, da yake table mart ɗin tana da girma ya ce

"Gwara na jingina da kujera, kar na fara ci na yi santi ku ce a saka mini waigi" Ya faɗa yana haɗiye yawu. Lawan ne ya yi dariya ya ce

"Yo dama santi ai sai dai in baka fara ci ba" Bukari ya ce

"Ni dai na san da wuya in koma gida da kunnena, wataƙila a cin abincin zan cire kunne ɗaya" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, Aminu ya ce

"Idan kuka fiye yabawa ƴar aljannata abincin ta, ba zan ƙara kawo ku cin abincin ba" Aminu ya faɗa don yadda suke ta zuzuta abincin sai ya ji tamkar dai sun ci ne, a ransa ya san dai yau in suka ci za su kusa tsinke yatsa, Kabiru ya ce

"Kishi ne ya motsa Aminu, baka so a yabawa amaryar taka" Bukari ya ce

"Surutun ya isa haka, a ci abinci" Kowa cokali ya ajiye wai ba za su ci tuwo da cokali ba.

Aminu ne number one wajen gutsurar tuwo ya haɗo da miya, kafin kowa ya kai nasa ne ya fara isa bakinsa, wani irin ɗaci ne ya ziyarci bakinsa gabaɗaya bakin ya game da ɗaci tamkar ya tauna magani filajin, idanu ya ƙwalalo yana kallon abokan nasa a fakaice yana addu'ar Allah sa wani abu wanda zia dakatar da su daga saka tuwon nan a bakinsu ya bayyana, ko da a ce a waje ne za a yi ihun gobara a kawo ɗauki tabbas zai yi yadda zai yi ya sa su tafi taimako amma dai ba ya fatan su ci.

Haka ya daure yake mumulmumultu da tuwon a bakinsa, tamkar tsohon da babu haƙori a bakinsa, yana cikin wannan halin ya ga Lawan ya ɗago idanu ya kalle shi yana riƙe da tasa lomar tuwon da ya yi wa wanka da miya, da sauri Aminu ya yi yaƙi da zuciyarsa wajen sauya akalar fuskarsa, daga yamutsewar jin ɗaci zuwa walwala, muduk ya haɗiye tuwon babu shiri, gabaɗaya ɗacin har maƙogwaronsa. Maganar Lawan da Kabiru ce ta dawo da shi daga suman ɗacin da ya yi jin sun haɗa baki wajen faɗin

"Bismillah" Kafin wani yunƙuri sun kai lomar a kusan tare, Bukari ne na ƙarshe, yana sakawa ya yi fosta da lomar tuwo a bakinsa, shi bai haɗiye ba shi bai tofar ba. Wani tari ne ya ƙwacewa Lawan bakinsa da tuwon da sauri ya ce

"Kabiru lalumo ledar lemon can ka miƙo mini kashina" Kabiru kamar jira yake ya warto ledar ya ɗakko lemon, maimakon ya miƙawa Lawan sai ya buɗe robar ya kafa kai dakyar ya samu ya kora tuwon nan da lemo, yana zare idanunsa da suka yi jawur saboda tsabar wahalar ɗaci.

Kafin Kabiru ya gama shan lemon Lawan da yake ganin ba zai iya jumurin buɗe wata robar ba, ya warce sauran ya shiga kwankwaɗa, sai da ya ji faɗawar nashi tuwon bidik sannan ya shiga dawowa hayyacinsa, bai ankara ba Bukari soja ya karɓe saura lemon don shi ya fi kowa shiga tashin hankali saboda ya tsani abu mai ɗaci ko yaya, bare wannan ɗacin mai ɗaga hankali, Aminu kuwa shi a dole sai wayincewa ya yi da faɗin

"Kai gayu kuna yarfa ni fa, so kuke amarya ta shigo in ji kunya, ga lemuka nan kala-kala amma kun zauna kuna fasin-fasin da guda ɗaya kamar kun samu ƙwallon ball" Ya faɗa yana daurewa ya suri wata lomar amma wannan karon ƙarama ya ɗauka, su duka ukun kallon inda zai kai lomar suke, suna mamakin to ko shi bai ji abin da suka ji ba, haka Aminu ya yi shahadar aika lomar nan bakinsa, wani amai yana neman tahowa, haka ya daure ya haɗiye.

Abin ya haɗe goma da ashirin, tuwo ɗanye duk ɗanyar shnkafa a ciki, ga miya ƙarni ga kuma wani ɗaci mai shiga harshe.

Dakyar ya samu lomar ta shige cikin, a take cikinsa ya ji yana murɗawa. Yana ankare da sauran babu wanda ya sake gigin kai wata lomar bakinsa, sai juya hannu suke a farantin to shi ma da aka bashi malmala ɗaya da yaya, bare su kuma masu malmala bibbiyu. Ya san tabbas kara ce suke masa, basa so su nuna wani aibi daga tuwon shi ya sa kuma don kar ya ji babu daɗi suka ƙi ajiyewa. Cikin wayincewa ya ce

"Gayu dama fa basu son tuwo, gwara mu fara da zabuwar can da ta dha dahuwar amare, kuma dai na ɗan ji kamar hannun amarya ya ɗan goce a miyar nan wataƙila miyar ta ɗan kama ne, shi ya sa take ɗan ɗaci" Ya faɗa yana ture plate ɗinsa gefe, su duka ukun kamar jira suke suka turo nasu, fita ya yi zai ɗakko musu ruwan wankin hannu, don ba ya ƙaunar ƴar aljanna ta sake dawowa ɗakin, bare da ya ga ta ɗauki wani uban zanin leshi ta sha lulluɓi da shi.

Yana fitowa ko inda take bai kalla ba, kicin ya je ya ɗakko ruwa a wata roba mai ɗan faɗi, da ya dawo fuskar nan tasa a haɗe yana dab da shigewa ɗakin ta ce

"Ɗan aljannata, ya kuka ji tuwon? Amma fa don Allah kar ku cinye duka wallahi ban ɗauki nawa ba" Wani takaici ne ya sa ya kasa magana, kaɗa kansa ya yi a zuciyarsa yana cewa

'Indai wannan tuwon naki ne, mai kama da maɗaci ga shi nan an bar miki har na ɗumamen safe ma kya samu' Ya faɗa a zuciyarsa yana shigowa falon, da ya ji suna zance ƙusƙuƙus amma yana zuwa sai aka yi ɗif, kunya dai yau ya san ya kunyata daɗinsa ɗata ma sa ci naman ba sa zauna da yunwa ba, ko dai su zo basu ci komai ba.

Kowa hannunsa ya wanke suka ɗan fatsar, farantin da ta ɗoro kofuna ya sauke ya jirkice musu naman a ciki, sai turiri yake tuni kowa ya ɗan murmusa, suna jin daɗi an raba su da alaƙaƙai wato miyar maɗaci, don wanna sunann ne ya dace da miyar duk da babu wanda ya san dalilin da ya sa miyar ta yi ɗaci, wannan amsar sai Hajiya ƴar aljanna.

Wani ya ɗau cinya, wani haƙarƙari, wani kwankwaso, kowa dai da abin da ya ɗauka, a baki suka luntuma a tare, kowa ya shiga kokawa da naman da sai an yi yaƙi zai gutsuru saboda tauri, idanunsu ya ƙanƙance jin wani ɗanɗanon da ya bambanta da na miyar tuwo, ɗanɗanon da duk cikinsu su huɗun basu taɓa cin karo da shi a cikin nama ba, ba a nan gizo yake saƙar ba jikin haƙarƙarin hannun Kabiru wata ƙatuwar ƙusa ce wacce romon naman da ya baibaye ta, bai hana a ga tsatsar da ta yi ba.

A wannan halin ne Bukari da ya ɗora ɗaya hannunsa a kan breziya bai, ɗanɗanon naman ya sa ya ɗago hannun ashe hannun breziyar ya maƙale a jikin links ɗin hannun rigarsa, sai ga breziya tana reto a hannun soja, su duka ukun da kallo suka bi hannun soja, banda Aminu da ya yi saurin sadda kai ƙasa, a zuciyarsa yana cewa

"Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahilmazim"

*ZAN BAKU BOOK 1 A FREE BOOK 2 GA MAI HALI YAKE DA BUƘATA ZAI BIYA 500 ZAKU IYA FARA PAYMENT DAGA YANZU ZUWA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA ****

*INA SANAR DA KU WTSAPP SUN KULLE MINI WANNAN NO *** YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI ****

*AKWAI MAGUNGUNAN MATA, NA KAMFANIN MEERAH B HERBS,AKWAI NA GYARAN BREST AKWAI NA SANYI AKWAINSET NA AMARYA HAƊIN ME JEGO MALLAKOKI, LABULAYE ZANNUWAN GADO LESUNA, ATAMFOFI, LAFFAYA TAKALMA MAYAFAI MASU BEAD WORK DA NA SHAGO KAYAN YARA DA SAURANSU MAI SO YA MINI MAGANA TA **** [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su *****