Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi

PAGE 14

by @mamanafrah3028

Bakin Bukari kamar ƙofar gari haka ya buɗe tsabar mamaki, tamkar wanda aka ratayawa igiyar kashi hake yake ganin breziyar tana reto a hannunsa, ga wani tsantsani da ya hana rai da zuciyarsa sukuni.

Kabiru shi har wani idanu yake zarewa don son tabbatar da cewa breziyar ce a hannun soja, ganin duk sun raja'a a kallon breziyar hakan ya sa Kabaru fahimtar babu wanda ya lura da nasa gamon da ya yi. Hannunsa ɗayan ya sanya ya fincikon ƙusar daga jikin haƙarƙarin nan da ta yi nutso cikin tsoka, tana cake jiki kamar an buga ta a katako duk da har a wani lanƙwashe take.

Kabiru yana zaro ƙusar ya ɗagata sama, har lokacin Aminu kansa yana sunkuye a ƙasa ya kasa ɗagowa, Lawan salati ya kwasa ganin ƙusar da aka zaro daga jikin nama, shi Buƙari ya rasa bakin magani ji yake tamkar ya shaƙo Aminu ya yi ta duka saboda takaici.

Aminu kuwa jin an ɗauki salati duk sai ya ɗauka har lokacin, suna jimamin breziyar ne hakan ya sanya ya ƙara sunkuyar da kai ƙasa, idanunsa kafe da cinyar zabuwar da take riƙe a hannunsa, ga cinya har cinya saboda girma amma ɗanɗano da rashin dahuwa ya hana ya ci naman cikin kwanciyar hankali, uwa uba ga wannan tashin hankalin abin kunyar da Zulaiha ta jaza masa. A ƙufule Kabiru ya ce

"Aminu dama kawo mu gidanka ka yi don a kashe mu?" Wanann tambayar ta ba Aminu mamaki don ya zaci a kan breziya ake magana, kunya ta hana shi ɗagowa amma dai duk da haka bai zaci har za a ɗauki abin da zafi a sako maganar kisan kai.

Bai ɗago ba kuma bai ce komai ba, sai cewa yake a zuciyarsa.

'Allah ka ji tausayina, ka sa breziyar nan ta ɓace, sai in ce dama aljannu ne suka kawo'

Lawan ne ya ce

"Alamomi da dama sun nuna hakan, miya ɗaci firit ga kuma baƙar breziya a ajiye kusa da mu, sannan yanzu ga guba an tsinta a cikin nama" Dummm gaban Aminu ya buga, don dama da aka ce baƙar breziya har sai da ya runtse ido, yanzu kuma jin an ce guba sai gabansa ya tsannata bugu yana tunanin hallaw wace masifa ce Zulaiha ta jaza masa, da za a ce guba a nama, shi da ya san zai haɗu da wannan ƙaddarar a baƙar ranar nan da bai kawo su gidan ba.

"Aminu magana ake maka fa" Kabiru ya ce yana wani huce kamar zai kai masa duka.

A hankali ya ɗago kansa, gumi ya gama jiƙa shi, a kan zarɓeɓiyar ƙusar ya sauke idanunsa, kafin ya mayar da akalar ganin nasa zuwa hannun Bukari da yake rataye da breziyar, basu ankara ba sai suka ga Aminu ya fara gwala idanu yana cewa

"Jama'a duhu nake gani, bana ganin komai fa, jama'a a kawo ɗauki ko dai baƙar iska ake yi yau" Ya faɗa yana baza hannuwa kamar mai zancen kurame, sannan sai gwale idanu yake yana runtsewa ya buɗu.

Su duka da kallon rashin fahimta suka bi shi, shi kuma ya yi wannan dibarar ne saboda ya tsira daga jin kunya. Tun da dai ya san in ya ce ba ya gani dole su masa uzuri ko ma hankalinsu ya tashi, dole su manta da batun ƙusa da breziya tun da ya ga alamar babu sauƙi wai ciwon arne.

"Lawan ne ya karkata kai ya ƙare masa kallo, cikin hargagi ya ce

"Wallahi ƙarya kake mu za ka rainawa hankali, a'a ka manta ba baƙar iska ba ce ta taso, guguwa ce mai haɗe da ƙasa" Ɗif Aminu ya yi a ransa yana tunanin kar dai sun hango lagwansa.

Hannayen ya fara miƙawa saitin Bukari wansa yake a ƙufule, ya cika fam kamar zai fashe, yana miƙa hannun yana gwale idanun, yatsunsa ne masu zato-zaton farce da hannun yake riƙe da cinyar kaza ya kusa nutsawa Bukari a ido.

Lawan ne ya ce

"Kabiru nutsa masa ƙusar nan a idon da yake gwalewa, wataƙila idanun su washe ya daina ganin duhu" Da sauri Aminu ya ja baya, da jan mazaunai ya koma daga can gefe yana cewa

"Haba ku tausaya mini ga cutar makanta ga ta ƙusa ai sai ku tsiyayar mini da idanun" Bukari cikin kakkausar murya mai cike da takaici idanunsa sun kaɗa sun yi jajur yana jin amai yana yunƙuro masa in ya kalli breziyar hannunsa ya ce

"Aminu wallahi ka buɗe idanunka ka ɗauke mini wannan abar daga hannuna, in ba haka ba to wallahi zan manta matsayina na Bukari abokinka, in koma Bukari soja in lakaɗa maka na jaki, hatta ita matar taka ba zan barta ba" Ƙwuitttt wata ƙaramar tusa marar ƙara ta suɓucewa Aminu, don shi fa a duniya yana tsoron soja, dama abin da ya sa yake sakin jiki da Bukari ma saboda ya san abokinsa ne, kuma dai ba da unifoarm yake ganinsa ba, don ganin idanun Bukari sun yi ja sai ya fara tunanin ko allurarsa ce ta soja ta motsa, jin wannan batu sai ya saki wata ƴar dariya mai ɗan sauti ya ce

"Wallahi idanun nawa ma sun washe, yanzu kam ina gani raɗau-ɗau, subhanallahi wannan abar fa? "Ya ce yana kallin breziyar. Bai jira cewar kowa ba ya ce

"Wannan da gani aljannu ne suka mana ajiya, wataƙila ma yanzu suna zaune a ɗakin nan, donn wannan breziyar ko kusa ba ta amarya ba ce, kuma ko ƙusar cikin naman bata rasa nasaba da aljannu"

Kallon ka raina mana wayo suke yi masa, kunya yake ji har lokacin, bai taɓa zaton zai kunyata haka ba, tun da suka shigo gidan ake cin karo da abubuwan al'ajabi da bashi kunya ba zai gaji da faɗin Zulaiha ta tozarta shi yau ba. Bukari yana jefa masa wani kallo ya ce

"Ka ɗauke mini ita daga jikina, don wannan kayan nawa ma na gama saka su har abada" Ya faɗa yana wani irin yatsina fuska.

Ana cikin wannan yanayin ne, amarya Zulaiha ta shigo, har lokacin zanin leshinta yana yafe a jikinta sai dai wannan lokacin iya wuyanta ta yafe bata rufa har kai ba. Wata ƙaramar roba ce a hannunta mai ɗauke da yajin daddawa, dama tun daga gida aka niƙo mata shi, to sai ta manta bata kawo ba hakan ya sa ta shigo da sallama tana mai cewa

"Ga yajin daddawa, duk da na san ai yanzu tuwon ma kun ci ƙarfinsa, an ji miyar amarya zaƙwaiƙwai" Ta faɗa ba tare da ta lura da yanayin da suke ciki ba, da yake tana ɗan sunkuyar da kai ne, ta sunkuya ta ɗago kenan ta yi arba da naman kowa a hannu, sannan ga tuwo nan duk ba a ci ba, cike da ɗan mamaki ta buɗe baki ta ce

"Haba abokan ango abin har da zari kuma, wato bakwa bari ku gama cin tuwon ba ku ci naman, shi ne ake hannu baka hannu ƙwarya" Ta faɗa cikin sigar wasa irin na matar abokinsu. Bukari cije leɓe ya yi yana jin wani haushinta, a ɓangaren Aminu ma hakan ce ta kasance amma babu wanda ya bi ta kan Zulaiha, Aminu ne ya miƙa hannu ya ciro breziyar hannun Bukari wacce warin gumi da na dauɗa yake tashi daga jikinta.

Karaf idanun Zulaiha suka sauka a kan breziyar, cike da ɗan jin kunya tana ƴar dariya ta miƙawa Aminu hannu tana cewa

"Lah faɗowa ta yi, wallahi da na cire tare da kayan nan na ɗora ta a kan gado" Aminu da ya yi fosta jin ta ƙara tona masa asiri, shi da yake wayincewa yana cewa ta aljannu ce, amma ta gama faɗar komai. Har ta karɓi breziyar Aminu bai samu bakin magana ba, tana karɓa ta ɗauki rigar leshin da ta cire ta saka breziyar a ciki ta tuƙunƙune, ta ajiye tana cewa

"Ga yajin naku nan, ni bari na fita, sai ku ce gaba da gashi" Har ta juya Kabiru ya ce

"Amarya ni sai na samu ƙusa a cikin nawa kashin nama" Juyowa ta yi tana dariya irin ko a jikin nan nata ta ce

"Ayyo, wallahi kasan zabuwa da wahalar dahuwa, shi ne aka ce ana saka ƙarfe ko cokali, to shi ne na saka tsohuwar ƙusar nan don ta yi saurin dahuwa" Idanu Lawan ya ƙanƙance jin amsar da ta ba Kabaru, Kabiru kuwa zuciyarsa ce ta tashi saboda har ya fara hango inda aka samo ƙusar zai iya kasancewa waje ne marar tsafta.

Ganin hankalinta kwance za ta fita, Lawan ya ce

"Naman ma zaƙi cai" Shiru ta ɗan yi tana nazari, jin an ce zaƙi, sai sannan ta tuna waje ɗaya ta ajiye robar suga da ta gishiri kuma robobin iri ɗaya ne, sannan gishirin ma ba mai laushi sosai ba ne.

A zuciyarta ta ce

'Cakwakiya lallai kuna cin daɗi' A fili kuma sai ta yi dubarar faɗin

"Haba Lawan, to ni ina amarya ya zan yi in muki girkin ƴan ƙasarku baƙaƙen fata, ai ni da kake gani na yi girkin ƙasashe da ban da ban" Su duka ukun sai suka bi ta da kallo ban da Bukari da yake jin kamar ya shaƙo mata wuya, Lawan cikin son jin girkin ƙasar da aka musu ya ce

"Yanzu dahuwar naman nan ba na Nigeri'a ba ne" Murmushi ta yi jin tarkonta ya kama tsuntsu ta ce

"Kaima da wani abu, ai dahuwar naman nan na ƙasar indiya ne, ka san su da suga suke amfani ba gishiri ba, shi ya sa na ce wataƙila baku taɓa ci ba, shi ya sa na gwangwaje ku da shi" Kallon rainin wayo Kabiru ya mata ya ce

"Shi kuma tuwon nan mai miyar ɗaci na wace ƙasa ne" A zuciyarta ta ce.

'Na shiga uku, ɗaci?' A fili ta ce

"Miyar ƙasar Marocco ne" Kafin wani ya ƙara jefo mata tambaya ta fita daga ɗakin da sauri, kicin ta nufa tana zuwa ta ɗakko robar kuka ta duba, tana dangwala ta ɗanɗana sai kuwa ta ji ɗaci, a take ta tuno cewa daga gidan an ce mata ƙullin kayan miyar nan na baƙaƙen leda ɗaya kuka ce ɗayan kuma lalle, sai yanzu ta gane ashe lallan ta juye a robar ba kuka ba don haka shi ta kaɗa musu miya da shi.

"Ni Zulaiha yau na kunyata, waɗannan ƴan rainin wayon abokan Aminun sun zo suna wani damuna da mini tambaya ƴar ƙure, dole sai sun ƙure ni, to an yi ma da wane shegen ya kawo su ƙwalama" Ta faɗi hakan a fili tana fitowa daga kicin ɗin ko a jikinta

A can cikin ɗaki kuwa, kowa naman hannunsa ya ajiye Kabiru yana tsokanar Aminu da cewa

"Yo kai abokina ka ce girki sai na ƙasar da ka zaɓa za kake ci, ka auri ƴar Nigeri'a amma tamkar ka auri mata ne na mabambanta ƙasashe" Aminu bai yi magana ba, don gani yake ma da gangan Kabiru ya faɗa masa magana. Hannu suka saka suka wanke a ruwan robar nan, cikin ɗan ƙarfin hali Aminu ya ce

"Masallaci za mu je?" Harara Bukari ya aika masa ya ce

"Ni dai tafiya zan yi, sai dai su ku je masallacin tare da su don yunwa nake ji gida zan je" Cikin sauri Aminu ya ce

"Haba kai kuwa ga abinci an shirya saboda da ku" Lawan da Kabiru suka kwashe da dariyar irin ta abokai. Banza Aminu ya musu, nan suka miƙe su duka suna masa godiya hatta lemon babu wanda suka ƙara sha.

Suna fitowa suka farawa Zulaiha sallama, cikin sigar wasa ta ce

"Har an fito kenan" Amsa mata suka yi Lawan ne mai ƙarfin halin cewa

"To amarya mun gode Allah ƙara zaƙin hannu" Wani daɗi ne ya baibaye ra don tunaninta bayan fitarta sun ci abincin, tun da ta faɗa musu ba abincin ƙasar nan ba ne, ta ce

"Ba komai ai baƙon ka annabinka" Har za su tafi Lawan ya zaro dubu biyar ya bata, godiya take ta musu, Aminu kuwa yana gefe bai ce komai ba sai harara yake galla mata, ko kallonsa bata yi ba ta ce

"To godiya nake, sai kun ƙara dawowa, ranar kuwa girkin larabawa zan muku" Ta faɗa cike da wasa, Bukari kuwa fuuuu ya yi gaba don in ya tuna breziyar da ya gani a maƙale a jikin hannunsa zuciyarsa tashi take.

Suna fita ta shiga ɗakin, naman ta fara ɗauka ta ɗanɗana wani rin zaƙi kauuu, da sauri ta fito waje ta tofar da yawu ta wuce kicin ta ɗakko ruwa a wani kwano ta dawo, haɗe da maggi mai tauraro.

Zaunawa ta yi ta wanke naman tas ta barbaɗa maggi take ci, tana cikin ci sai ga Aminu ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Yana kallonta ya ji wani ɓacin rai, da sauri ya ɗakko rigar leshin nan yana zazzagawa sai ga breziya ta faɗo, ɗagawa ya yi cikin ɓacin rai ya ce

"Zulai wane irin rashin mutumci ne wannan, saboda tsabar rainin wayo za ki ajiyewa mutane wannan abar daƙalƙal da datti, har abokaina su gani" Tsaye ta tashi ta yi wurgi da hular kanta ta kalle shi ido cikin ido ta ce

"Aminu ni kake cewa Zulai? Idan ka daina kirana ƴar aljannar ne ai sai ka kirani da Zulaiha, sunan da aka yanka rago aka raɗa mini, ba wai Zulai ba sai ka ce wata tayar keke" A ƙufule ya kalleta idanunsa suna hasko lokacin da breziyar take maƙale a hannun Bukari ya ce

"An faɗa Zulai" Kallon kai aka bari da yawo da zance ta masa tana komawa ta zauna tare da ɗaukan wata cinyar zabuwa, ta shiga yaga dakyar kasancewar rashin dahuwa. Kallon takaici ya mata yana ganin yadda farantan suke cike da tuwon da babu abij da abokan nasa suka ci a ransa yana tunanin da Sadsiqa ce ba za a a samu wannan matsalar ba.

Tsabar takaici ficewa ya yi daga gidan, ya zo zai wuce ta gaban kicin ya ji wani ƙamshi tana tashi, a take yunwar cikinsa ta motsa, ya san Saddiqa ce take girki, amma tunowa da ya yi ko maggi ba ya siya mata sai ya kaɗa kansa, yana dab da fita daga gidan sai ga Sumayya ta fito ta ce

"Ango ka sha ƙamshi na Sumayya bada kanka a sare" Ta faɗa cikin sigar wasan ƙanin miji. Ransa ne ya ƙara ɓaci jin wai saboda Sumayya zai bada kansa a sare, ya ce

"Ina Ruma" Haka kawai ya faɗa kafin ta bashi amsa ya juya ya fice kamar zai tashi sama, baki ta taɓe a fili ta ce

"Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani"

Tun da ya fita bai dawo ba sai yamma, yana shigowa ya ganta tana bacci a kan gado, kwanukan nan suna inda suke babu wanda ta ɗauke, tuwon ma duk ya sha iska har ya fara ɗan bushewa. Kai ya dafe ya kafe farantin da ta ci naman duk ta ɗaye tsokar sai ƙasusuwan kwanukan ya shiga kwashewa.

Yana shiga kicin ɗin ya ajiye su, ganin tukunyar Saddiqa a rufe ya buɗe sauran jallof na shinkafa da wake ne a ciki, bai fi ka ba yaro ƙarami ɗan yaye ba, amma haka Aminu ya shiga cin abincin da hannu a tukunyar, yana jin wani daɗi yana ratsa shi a fili ya ce

"Yanzu da abokaina wannan suka samu, ai da babu ni babu jin kunya, amma har zabuwa na saya aka kasa fitar da ni kunya" Ya faɗa yana jin daɗin girkin har tsakiyar kansa.

Saddiqa wacce ta taho za ta ajiye plate a kicin ɗin, kawai sai ganin mutum ta yi kamar almajiri yana ƙanƙare ƙanzon tukunya, Aminu jin motsi ya juyo da sauri sai kuwa ya yi arba da Saddiqa, ga shi dai ta ganshi amma kuma sai ƙoƙarin wayincewa yake, yi ta yi kamar babu wata halitta a wajen, sai dai idanunta sun sauka a kan tuwon da aka yi wa abokan Aminu da aka ajiye farantan a kicin, tana gani ta gane abincin ne ya kasa ciyuwa, don ta fahimci kenan dalilin rashin iya girkin amarya ne ya sa, ya je mata da batun ta yi wa abokan nasa girki saboda bata san ciwon kanta ba.

Ta ajiye plate ɗin za ta fita, sai kuwa ya matso don ƙamshin turarenta ya gama haɗe kicin ɗin, cikin ƴar murya ya ce

"Saddiqa" Wannan furucin ya yi daidai da zuwan Zulaiha ƙofar kicin ɗin, hakan ya sa Aminu dakatawa yana ciccira ido kamar an kama kwarto a gidan amarya.

Saddiqa kuwa tuni ta fahimci tsoron matarsa yake, baki ta taɓe ta raɓa ta gefen Zulaiha da ta tsaya ƙiƙam tana musu kallon tuhuma, ita Saddiqa warin jikin Zulaiha da ta shaƙa ne da kuma kayan jikin Zulaihar suka saka ta a zuciyarta ta ce

'Cakwakiya lallai zani ce ta tarar da muje mu'

Zulaiha kuwa bayan wucewar Saddiqa ta kalli Aminu, rai a ɓace ta ce

"Wato amanata za ku ci, ranar girkina ka zo kun laɓe kuna ƙusƙus a kicin, saboda ka zubar mini da mutunci ka zo kana cin abincinta, bayan ga tuwon da na muku nan kun bar mini" Tsabar takaici ma ya rasa mai zai ce hannu ya wanke ya fice ya bar ta tsaye a wajen. Fuuuu ta bi shi ɗakin tana zuwa cikin tsiwa ta ce

"Kar ka ƙara mata magana ranar girkina, tun da kai ka cw sati biyu zan yi, don haka babu kai babu ita sai ranar girkinnta" Galala yake kallonta a ƙufule ya ce

"Zulai baki fahimci wa kika aura ba har yau ko? Saboda ban fito na nuna miki asalina na Aminu ba... Kiranta da Zulai ya ƙara dagula lissafin hakan ya sa ta ce

"Wallahi ka daina ɓata mini suna, kuma da kake cewa ban sanka ba kana da wani suna ne da ya wuce Aminu ƘAZAMI... Rai ɓace ya yi wajenta zai kai mata duka ta kama ƙugu ta ce

"Ba irinmu bane matan da ake duka, wallahi yadda kake ji da tsagiranci haka nake tantiriya" Kallonta ya yi ya ɗauke ka, yana ji da kansa yana ganin, kamar dai shi Aminu za ta rainawa wayo, shi da Yayunsa ma bai ƙyale ba tabbas bata so zama lafiya ba a gidansa.

Jin zuciyarsa tana masa zafi ya fice daga gidan.

La'asar lis Saddiqa ta shiga kicin za ta wanke ƴan kwanukan da ta ɓata, tana cikin wanke-wanke Zulaiha ta shigo kicin ɗin, ganin kwanukanta a gefe ta ce

"Malama ya za ki ware mini kaya a gefe, nufinki waye zai wanke" Bango Saddiqa ta ba ajiyar Zulaiha, don ta lura irin matan nan ne masu shegen kishi, ita kuma yanzu gani take Aminu ba ya cikin mazan da za ta yi kishin su. Haushi ya sa Zulaiha ta ƙara cewa

"Ba da ke nake magana ba?" Ganin Saddiqa bata tanka ba, sai Zulaiha ta fara jidar kayan tana kaiwa wurin Saddiqa. Juyowa Saddiqa ta yi cikin muryarta mai sanyi ta ce

"Na miki kama da mai aikin wanke-wanke?" Zulaiha ta ce

"To da wa kike kama? Ni fa ba na ɗaukan ki matsayin kishiyata, baki ga ko da na zo gidan nan mijina Aminu bai haɗa mu waje guda ya nuna ki a matsayin matarsa uwar gidansa ba, wannan dalilin ya sa na ga baki da maraba da mai wanke-wanken, kuma ga shi dai cikin kwananki ya ƙara mini sati guda, kin ga kenan baki da wani muhimmanci"

Tun da ta fara faɗar baƙaƙen maganganu, abin ya yi wa Saddiqa ciwo amma kuma sai ta raina Zulaihar don haka take ganin ɓata lokaci ne da rashin girmama kai ta tsaya sa'insa da ita, amma sai ta yanke shawarar faɗa mata magana ɗaya zuwa biyu hakan ya sa ta ce

"Ni fa in na raina kasuwa ne ko sautu ba na bayarwa, kuma ina so ki sani kayan da suke samun wanki da guga ana tsafta ce su koyaushe, su ne kayan da mutum yake jin yana so ya sanya a jikinsa, amma in har kaya basa samun abubuwan da na lissafa to koyaushe mutum zai ji ba ya ma son au raɓe shi" Tana kaiwa nan a maganarta, ta juya ta cigaba da aikin gabanta.

Zulaiha kuwa saboda tsabar toshewar basira, bata fahimci kurman baƙin da Saddiqa ta karanta mata ba, bare ta gane magana Saddiqa ta faɗa a kan cewar Amunun da take kishi tun da ƘAZAMI ne ita bata ma sha'awar ya kusanci inda take.

Buguzum-buguzum ta juya ta bar kicin ɗin.

*BAYAN KWANA BIYU*

Aminu ne bayan ya dawo daga kasuwa, suka rinƙa bala'i shi da Zulaiha, hakan ya sa ya fito ya bar mata ɗakin, don ya ga ko kaɗan bata raga masa.

Ɗakin Saddiqa ya nufa, ƙamshin turaren wuta ya cika ɗakin, tana zaune sanye cikin fararen riga da wando, gaban rigar an yi pink ɗin flower. Da sallama ya shigo tun da ta amsa masa ta maida hankali ga cin gaɗar da take. Zaunawa ya yiannu ya miƙa ya tsakura ya kai bakinsa.

Tun da ya zauna ta tsaya cak da cin gyaɗar, saboda warin rana da yake tashi daga jikinsa, amma haka ta daure, wani kallo ya yi mata mai cike da shauƙi sai ƙare mata kallo yake, cikin ƴar murya ya ce

"Saddiqa manyan mata, ana nan ana caɓa ado da kwalliya, kin yi kyau ɗakinki ƙamshi ko ina" Ya faɗa yana baza hanci, tare da tuno yadda ya baro ɗakin amarya da rabon ɗakin da shara, tun shekaran jiya da ya share da zai yi baƙi. Kallonsa ta yi ta ce

"Anya kuwa, ni ɗin ko dai ɓatan kai ka yi" Yana kafe ɗan ƙaramin bakinta da yake sheƙin lipstic ya ce

"Da ke nake mana" Duk kallonta da yake sai ya ji yana buƙatarta. Ƴar dariya ta yi ta ce

"Na gode" Yana wani ɗan kashe mata ido ya miƙa hannunsa zai kai jikinta, da sauri ta ɗan ja baya, cike da mamaki ya ce

"Kamar zan aikata haram" Ta ce

"Ni dai ban ce ba, amma dai a iya sani na, sai nan da kwana huɗu ne kwanakin amarya za su ƙare" Kamar ta ambaci sunan maƙiyarsa ya ce

"Wace amarya kuma" Banza ta masa.

Nan ya zauna yana ta ƙoƙarin kai hannunsa jikinta, amma ta ƙi bashi amsa, da ta gaji ma sai ta fito ta bar shi a ɗakin don duk ya haɗe ɗakin da warin rana.

Lokacin da ta dawo, don dama ɓangaren Sumayya ta tafi, sai ta tarar da shi ba ya nan, baki ta taɓe ta ƙasa saka turaren wuta, ita tunaninta ma in sati biyun ya ƙare yadda za su dawo su yi rayuwa da shi.

Misalin ƙarfe biyu na dare, Aminu ya kasa bacci tun da ya ga shigar Saddiqa ya saka a ransa yau a ɗakinta zai kwana, sai dai Zulaiha uwar ƴan kishi yake tsoro, hakan ya sa ya yi bakam kamar mai bacci. Yanzu jin tana ta munshari ya lallaɓa ya sauka daga gadon, a hankali ya buɗe ɗakin ya fito ya mayar da ƙofar ya rufe.

Ɗakin Saddiqa ya je cikin sanɗa ya tura ƙofar ya shige, cike da farin cikin zai biya buƙatarsa a waje mai tsafta ya hau kan gadon. Saddiqa tana cikin bacci ta ji hayowar mutum kan gadon, kafin ta yi yunƙuri ta ji warin jikinsa ya sanar da ita wane ne. Tana shirin magana ya rungumota.

Zulaiha cikin bacci ta miƙa hannu don taɓo ango amma ta ji babu shi babu dalilinsa. Matsawa ta yi don duk tunaninta ko ya bata tazara ne, duk da ta san a kusa da juna suke kwana.

Tana mirginawa ta ji wayam, idanu ta buɗe don duk abin da take idanunta a rufe suke, kaf kan gadon ita kaɗai ce.

Cike da mamaki ta tashi ta kunna fitila, ɗakin ta shiga ƙarewa kallo babu Aminu babu alamarsa, ko kan gadom sai wata singiletinsa da ta ci wani uban datti.

Bayi ta nufa amma Aminu ba ya ciki, cike da mamaki take tunanin ina zai je a cikin daren nan, don ta duba agogo ta ga ƙarfe biyu har ta gota.

Idanunta ta sauke a kan ƙofar ɗaki, ai kuwa ta ga alamar an buɗe ɗakin don ƙofar bata rufu sosai ba, a zuciyarta ta ce

'Ina Aminu yake? Wallahi yau za a yi bala'i idan har zargina ya zama gaskia' Ta faɗa a zuciyarta tana buɗe ƙofar ta fito....

ƘAZAMIN MIJI BOOK 1 FREE ne BOOK 2 NA KUƊI 500 MAI BUƘATA ZAI BIYA TA ASUSUN

Faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta *** [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****