Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 15
*YAYA SULE*
Soyayya mai ƙarfi ta ƙara kankama tsakaninsa da Salaha inda yake ƙara iya takunsa ga duka matan guda biyu, wato Salaha mai shirin shigowa gidansa sai kuma ita mai gayya mai aiki Amina, ta hakan yake cin karensa babu babbaka.
A inda Amina, har yanzu tunaninta yake ƙara tabbatar mata da cewa ita kaɗai ce mamallakiyar Sule kuma ita kaɗai za ta rayu da shi, daga ita sai ƴaƴanta wannan ya sanya take cin duniyarta da tsinken tsire, tana huce hanci kanta yana fashewa ita a nata ganin ita ce mace ɗaya tamkar dubu a wajen mijinta. Hakan ya sanya idan zama ya haɗa su da Saddiqa take jefar mata da magana a fakaice, duba da yanzu Saddiqa bata fiya zuwa ɓangarensu ba, sai take cewa Saddiqa baƙin kishi ne yake nuƙurƙusarta shi ya sa bata son shiga cikin mutane, ta gwammace ra zauna a ɗaki ita kaɗai, idan ta faɗawa Saddiqa hakan sai dai ta yi dariya, don ita Saddiqa ta sani bata wani jin kishin Aminu, duk da dai idan ta ce bata son sa ta yi ƙarya tun da auren soyayya suka yi, amma kuma a duk sanda ta tuna ƙazantarsa da kuma irin mugayen halayensa da ya mata, na watsar da wasu daga cikin buƙatunta da Allah ya ɗora masa, sannan a gefe ɗaya ba ya son cikin jikinta haɗe da wulaƙanci in har ta tuna hakan tana jin son sa ya ragu da kaso mafi yawa daga cikin wanda take masa.
Amina ce zaune a bakin gadonta tana daddanna waya, hira suke da ƙawarta a akan zancen za a yi wa qata ƙawarsu kishiya, shi ne Amina take ta cika baki, tana cewa macen da ta isa ba a mata kishiya, tun da ga shi nan ita ko alama Sule ba ya ma sha'awar kula mace.
Murmushi ƙawar tata ta turo mata kafin ta mata rubutu kamar haka ta ce
"Amina, ki kiyayi namiji fa, shi namiji ɗan kunama ne baka gane zafin dafin jikinsa sai lokacin da ya harbeka, amma fa son mata da kuma ƙarin aure a ran kowane namiji yake, sai dai idan bashi da halin yi ko kuma lokacinsa bai yi ba, ko kuma dai bashi da rabon ƙarin auren har ya bar duniya" Amina tana gama karantawa ta mata replaya da cewa
"Ba za ki gane irin ɗinbin son da Sule take mini bane, ba na jin akwai wata ƴa mace da zai kalla da sunan soyayya bare har ya ji yana son aurenta, ni shaida ce babu abin da yake ɓoye mini" Ƙawar tata ta ce
"To ke in zai yi auren ko in yana kula ƴan matan faɗa miki zai yi, bayan ya san bakya so kuma dai ya san yadda yake koɗa ki, ai akwai mazan dansuke baka komai a rufe" Amina ta ce
"Ki daian faɗa mini hakan Fauziyya, mijina nawa ne na ni kaɗai, sannan mijina yana cikin mazan da basu da rabon ƙara aure har su koma ga Allah, don haka mu yi wata hirar ba wannan ba, duk wacce kika ji za a yi wa kishiya a cikin ƙawayenmu ki faɗa mini, ni kuma ki ba a gayyace ni ba ,an je dannar ƙirji!"
Suna cikin chart ɗin ne wayar Sule da take a kan madubi ta shiga yin vibration, har ta share bata je ta duba ba, har kiran ya katse tun da shi yana wanka. Jin kiran ya ƙara shigowa a karo na biyu sai ta ajiye wayarta ta je kan madubin ta leƙa wayar, MAMUDA sunan da ta gani kenan yana yawo a kan screen ɗin wayar, mamaki al'ajabi haɗe da faɗuwar gaba suka dirar mata lokaci guda, tana tuna cewa jiya da dare ma har sun kwanta sai da ta ga MAMAUDAN nan ya kira shi, ƙarshe ya ce mata zai fita ya siyo panadol jikinsa yana masa zafi, da haka ta manta da maganar kiran tun da tun kiran farko ba a sake kira ba.
Ita kuma jin ya ce jikinsa yana zafi sai tausayinsa ya kamata, ta manta batun kiran MAMUDA. Yanzu ma sai ta fara tunanin dalilin da ya sa shi MAMAUDA zai ke kiransa koyaushe, duk da MAMAUDA ba suna mace bane amma dai ta ɗan shiga shakku da taraddadi.
Hannunta ne ya fara karkarwa jin zuciyarta tana ɗarsa mata wani zargi, duk da ta ƙaryata zuciyarta amma dai sai ta ji tana son sanin dalilin kiran da MAMUDAN yake yi wa mijin nata.
Tana ɗaga kiran sai wayar ta mutu, da ta duba sai ta ga cajin ne ya ɗauke gabaɗaya. Jin ƙaran sheƙa ruwan Sule a banɗaki da alama ya gama wankan ma, sai ta ajiye wayar, tana shirin barin gaban madubin sai ga shi ya fito daga bayin, abin da ya ɗaure mata kai shi ne yadda ta ga alamomin razana a tare da shi, wannan ya sanya ta ji hankalinta ya tashi, tana tambayar zuciyarta shin idan har babu wani abu da yake ɓoyewa a wayar mai ya sa da ya ganta a kusa da wayar zai razana.
Kafe shi ta yi da idanu tana son gano gaskiyar lamarin, shi ma Sule a nasa ɓangaren tsorata ya yi, don tunaninsa ko ta masa bincike a wayar tasa amma kuma tunowa da ya yi cewa yau da safe ya canja passward na buɗe wayar sai ya ji daɗi a ransa, hakan ya sanya ya yi saurin kawar da tsoro daga fuskarsa, matsowa ya yi yana zuwa sai ya riƙo ta tare sa rungumota jikinsa ya sanya lemar hannunsa ya shafe mata fuska tare da juyo da ita suke fuskantar juna, ita kuma da bata gama dawowa daga nisan kiwon tunanin son sanin alaƙarsa ta yawan kira da MAMUDA yake yi ba, sannan uwa uba dama ita ta tsani soyayya sai kishin tsiya ne kawai da ita amma mijinta ba ya samun kulawarta, ko soyayarta wanda hakan ya sa shi kuma yake cutuwa, har ya sa ya fara tunanin mafita wato ya auro wata macen ko ya samu yadda yake so.
Hannunta ta fincike saga riƙon da ya mata ta ce
"Na sha faɗa maka ni ba ma'abociyar soyayya bace, amfanin soyayya aure ne, kuma mun yi aure to mene ne saura?" Da kallo ya bita duk da ya saba jin kalamanta masu tsauri irin wannan, amma bai san mai ya sa yau suka masa zafi fiye da kullum, kafin ya ce wani abu har ta ɗora da faɗin
"Shin waye MAMAUDA?" Tambayar ta zo masa a bazata, tunanin ya fara kan cewa ko dai ta samu damar buɗe passward ɗin wayar ne, har take tuhumarsa kuma ba a kan kowa tuhumar ba sai a kan Salaha(MAMAUDA) Idanunta ya kalla yana son tantance tambayarta domin ya san irin amsar sa ya kamata ya bata, yana cikin wannan halin ta katse shi da faɗin
"Magana nake maka fa, waye MAMUDAN nan wai yanzun nan ma na ga yana kiranka" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya san dama sai dai in kiran ta gani amma da bincike ta masa a wayar ta gano abubuwa da dama na soyayyar da suke zubawa da Salaha ai ya san ya kaɗe har ganyensa kuwa, don irin musayar zantukan soyayyar da suke masu tsayawa a zuciya ya san da wataƙila ta suma in da gani. Jarumta ya aro ya ce
"Kai Amina, wallahi ni na ɗauka ma wani abu ne ya faru, yanzu a kan MAMUDA ya kira ni kika tsare ni da tambaya haka, kamar dai wata macen... Wani kallo ta aika masa kafin ta katse shi da cewa
"Kar ka ma fara, don ba a haifi macen da za ta kira ka ba, kuma har abada ba za a haifeta ba, kai nawa ne" Murmushi ya yi yana jinjina kishi irin nata ya ce
"Maganarki dutse, ai ni kaina na san babu wacce za ta kira miki ni, kisha kuruminki amanarki ta riƙu, MAMUDA dai ni ban san me ya sa yake damuna ba, shi bashi da aiki sai neman rancen kuɗi... Katse shi ta yi da faɗin
"Amma ranar nan cewa ka yi za ka yi blocking ɗinsa" Dakyar ya samu dabarar faɗin
"To ai bayan na yi blocking ɗin da wata lambar ya kirani yana cewa, ya gode da na rufe hanyar da zai sameni, don na ga bashi da kuɗi, wannan dalilin ne ya sa na sake saved sabuwar lambarsa" Shiru ta yi tana nazari shi kuka ganin maganar ta yi tasiri ya sake cewa
"Babu daɗi din baka da shi a gujeka" Ajiyar zuciya ta sauke mau ƙarfi ta ce
"Haka ne kuma, amma dai kiran koyaushe bashi da wani amfani, ni sai in ke jin faɗuwar gaba" Ya ce
"Ki kwantar da hankalinki ni naki ne har abada, ko ana ruwa ana iska, ana ruwa da ƙanƙara daga ke babu daɗi na kulle ƙofa tuf da mukulli" Wata dariya ta saki mai sauti, don ta ji daɗin yaudararrun kalaman da ya tsarata da su bata san cewa rami ya mata ta faɗa ba don MAMAUDA ba kowa bane sai matar da yake son aura, yana ta tunanin wannan cakwakiya ta yaya zai sanar da amarya cewa akwai uwar gidanta har suna da yara biyu, sannan ita mai gayya mai aikin sarkin ƴan kishi Amina ta wacce hanya zai faɗa mata yana neman aure, ya san duk ranar da ƙwan nan ya fashe tabbas akwai ɗan jijjiɓin rikici, shi ya sa ma ya iya takatsantsan, sannan ya iya takunsa don ko da a ce zai sanar da su, su duka biyun to sai aski ya zo gaban goshi, wanda bahaushe yake cewa aski in ya je gaban goshi ya fi zafi.
Tun da ya fahimci Amina ta gama gane yawan kiran da MAMUDA yake yawan yi masa, gashi shi kuma ba zai iya sanar da Salaha cewa ba koyaushe za take kiransa ba, tun da bata san yana da iyali ba duk da wasu ƴan matan ko sun san namiji yana da mata basa fasa kiran wayarsa koyaushe, domin wata a lokacin da ta san namiji yana da mata a sannan ne za ta buɗe ƙofofin rashin mutunci ba za ta tsiri kiransa ba sai yana gidansa don haɗa fitina da husuma. Idan aka samu uwar gidan mai ƙarfin zafin kishi shikenan sai a rinƙa bala'i da miji wata daga wanann har saki a gifta tsakaninta da mijin, don abu guda da mata basa ganewa shi ne, duk lokacin da namiji yake neman aure idanunsa rufewa suke ba ya ji ba ya gani, ko a mutu ko a yi rai.
Goge sunan MAMUDA ya yi ya maryar da shi MARAINIYA, bayan an yi hakan da sati biyu, wayarsa tana caji ya jona, sai kuwa ta fara ƙara, ya tashi da ɗan hanzari zai ɗakko Amina ta ce
"Bari in yi aikin lada in miƙo maka, ba sai ka tashi ba" Murmushin yaƙe ya saki yana komawa ya zauna gabansa yana faɗuwa, Amina tana ɗaukan waya ta ga sunan MARAINIYA da manyan baƙi yana yawo a kan screen ɗin waya.
A ɓangaren Sule kuwa yana ta addu'ar Allah sa wani ne daban yake kiransa ba Salaha ba, yana wannan halin sai ta ji Amina ta ce
"Sule wace ce kuma MARAINIYA" Gabansa ne ya faɗi, shi a nashi ɓangaren ya saka sunan ne don yana ganin ba lalai hakan ya ɗauki hankalinta ba, amma ganin hannunta har karkarwa yake wayar tana neman suɓucewa cikin dakiya ya ce
"Wai dama MARAINIYA na saka?" Ta ce
"Ban sani ba, kai za a tambaya" Sai ya ce
"Kai amma fa typin error sai ya haɗa maka ɗan jijjiɓin faɗa, MARAYA fa zan rubuta, wani abokinmu ne tun muna primary babansu ya rasu to shi ne fa kullum aka masa abu sai yake cewa, don mun san shi maraya ne, shikenan daga nan sunan maraya ya bi shi" Yana kai wa nan ya kafe ta da ido, idanu ya ga ta runtse, tana jin yadda ƙirjinta yake bugawa, sai kuma ta buɗe a hankali tana shirin miƙa masa wayar wani kiran ya shigo, wayar ta kafe da ido har sai da ta ji ta gamsu da maganarsa, ta miƙa masa tana faɗin
"Wallahi na tsani abin da za a ke saka mini shakku" Karɓa ya yi yana cewa na sha faɗa miki ki kwantar da hankalinki" Komawa ta yi ta zauna tana faɗin
"Ba dole gabana ya faɗi ba, na ga an sanya MARAINIYA. Idanunta ya faka ya danne wayar ta mutu gabaɗaya, sai ya kara a kunne yana cewa
"Babu MARAYA sai rago" Yana faɗar hakan ya ɗan yi shiru alamar kamar amsa ake bashi daga ɗaya ɓangaren. Sai kuma ya ce
"Allah sarki kowa lpia" Daga haka ya shiga yin ƴar hira yana dariya, tamkar da wani yake yi, yana gamawa ya tashi ya mayar da wayar caji.
Daga haka suka ɗan shiga hira da ita, yana ƙara faɗa mata babu ita babu kishiya a gidan duniya, tashi ta yi daga jinginen da take ta ce
"Mene ne nufinka? Kenan a lahira ba da ni kaɗai za ka zauna ba?" Tambayar ta so bashi dariya, amma ganin haka sai ya dake ya ce
"Baki san akwai matan aljanna ba?... Tun kafin ya kai ƙarshen maganar ta ce
"Ni a aljannar ma ni kaɗaice " Dariya ya yi ya ce
"To Aminatu sarkin ƴan kishi, wato har da matan aljanna ma" Ita ma dariyar ta yi ta ce
"Yo su ma ai mata ne" Bai ce komai ba ya ɗan yi murmushi a zuciyarsa yana cewa
'Iska tana yawo da mai kayan kara, ni da nake son mace ƴar soyayya wacce za ta shagwaɓani ta tarairaye ni, in ɗanɗani zumar soyayya da ta lobayya, ni ma in nuna mata tawa kulawa da soyayyar, amma ke kin zo kin mini dikim, in an yi batun soyayya ki ce ba haka ba, amma batun kishi ke ce a gaba, baki san ya za ki ɗauke hankalin mijinki ya dawo kanki ba' Ya faɗa a zuciyarsa yana yi wa Yusuf magana ganin yana ɓarna.
Yana fita daga gidan ya sauya sunan Salaha daga MARAINIYA zuwa, ABOKINA washe gari kuma sai ya sha kwalliya tare da fesa turare ya cewa Amina zai je wajen walima da abokinsa ya shirya musu saboda yana ƙara aure, Amina jin haka ta washe baki don ita a rayuwarta tana so ta ji an ce za a yi wa wata mace kishiya amma ban da ita.
Hakan ya sa bata hana shi ba, kuma bata nuna damuwar kwalliyar da ya ci ba, har da ɗakko wani turare da ta saya mai bala'in ƙamshi ta fesa masa sosai, wai bata son ya je wajen abokai a raina shi.
Yana fita ya dokawa Salaha waya ya ce yana hanya. Suna cikin hira da Salaha tana ta yaba ƙamshin turaren, zuwa can sai ta ce ya ara mata wayarsa za ta tura wata waƙa da ta ji ranar nan ana kiransa da ita, hankali kwance ya miƙa mata, tana cikin danne -danne sai wayar ta ɗauki ƙar gani ya yi Salaha ta zaro idanu sai ta ce
"Me zan gani wane suna ne wannan?" Ta tambaya tana tashi tsaye, gabansa ne ya buga da ƙarfi yana jin wani tashin hankali don ya san ba zai rasa nasa ba da kiran Amina ba ne ya shigo wanda ya yj saved na sunan da MY WIFE, cikin karkarwa hannu ya miƙa hannun yana cewa
"Wane suna kuma? Bani in gani, tana aika masa wani kallon tuhuma ta miƙa masa wayar, sunan da ya gani ne ya sa hankalinsa tashi, ya fara tunanin amsar da zai bata...
*ZULAIHA*
Ɗakin ta koma ta ɗauko fitila, ko tsoro bata ji ta fito daga ɗakin ta shiga baza idanu amma babu kowa, ƙwafa ta yi ta kama hanyar ɗakin Saddiqa duk da bata taɓa shiga ɗakin ba wannan ne karon farko amma yau ya zame mata dole ta je tun da a nata ganin ai neman kadararta za ta je, wato mijinta.
Tana zuwa ƙofar ɗakin ta ganta a rufe, amma tun daga hanyar take duba sawun Aminu, ko takalmi babu, kuma ta ga sawun nasa ya yanke ne daga lokacin da ta zo ƙofar ɗakin Saddiqa sai ta nemi sawun ta rasa.
A can cikin ɗakin kuwa Saddiqa, jin Aminu ya rungume ta, ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga gare shi, saboda yadda warin jikinsa ya gama cika mata hanci ba abin da ta fi buƙata illa ya sake ta, ko ta shaƙi wata iskar mai daɗi wacce ba gurɓatacciya ba irin ta jikinsa. Shi kuma jin tana son raba jikinta da nasa, sai ya bada ƙaimi wajen yi mata wani irin riƙo, cikin murya raɗa-raɗa ya buɗe bakinsa mai warin da ya sa ta fara jin kanta ya fara juyawa ya ce
"Saddiqa ni ne Aminunki fa, ki saki jikinki yau na zo na share miki hawayenki na kewata, na san tabbas! Kin yi kewar mijinki da ɗumin jikinsa" Yana faɗar hakan ta ji amai ya taho mata jin aman yana barazanar zubowa sai ta shiga girgiza masa kai.
Bai damu da yanayin da take nunawa ba, shi dai buƙatar maje hajji sallah wato ya samu biyan buƙatarsa. Rigar baccin jikinta ya shiga ƙoƙarin raba ta da ita. A daidai wannan lokacin ne a halin da suke ciki, suka ji an banko ƙofar ɗakin ba Saddiqa ba hatta Aminu dai da ya razana da bugo ƙofar, kafin su yi wani yunƙuri an dalle su da wata fitila mai haske.
Zulaiha kuwa ganinsu a manne da juna ya mugun ɗaga mata hankali, ga wani tuƙuƙin baƙin cikin da ya tokare mata maƙoshi a take ta fara jin wani jiri yana juyata, da sauri ta juya ta je kicin a guje ta ɗakko taɓarya dawowa ta yi ta shiga cewa
"Ihu mutanen gida, kwarto, kwarto a kawo ɗauki ihu kwarto" Aminu duk tunaninsa bayan fitowarsa ne kwarto ya kaiwa Zulaiha farmaki, ashe bai san iya shege ne ba da shi take.
A ɓangaren Sule jin ihun kwarto sai ya fito daga ɓangarensa ɗauke da wata ƙatuwar sanda, haka Yaya Shafi'u ma ya fito ɗauke da wata zarɓeɓiyar wuƙw da take cikin gidanta. A gigice suka iso wajenta, don sun gane amaryar gidan ce amma ganinta a ƙofar ɗakin Saddiqa sai suka fara tunanin ko ɗakin Saddiqa kwarton ya shiga, shi ya sa ta tsaya a wajen, suna zuwa a kusan tare suka ce
"Yana ina ko ya fice" Cikin muyarta wacce tamkar kuka zai fito ta ce
"Yana ɗakin wannan" Ta faɗa tana musu nuni da ɗakin Saddiqa, su kuma sai suka jinjina mata, ganinta ɗauke da taɓarya sannan kuma tana gadin ɗakin da kwaton yake.
Aminu kuwa jin muryoyin Yayunsa bai sanya ya yi girgizu ba, Saddiqa ce ma jin ya sakar mata jiki sai ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon. Tana sakkowa su duka ukun suka kawowa ɗakin farmaki, Yaya Sule, Yaya Shafi'u da kuma Zulaiha kowanne ɗauke da makami.
Yaya Shafi'u ganin Saddiqa cikin kayan bacci, da yake suna shigowa Yaya Sule ya kunna fitilar ɗakin, ga kuma hasken fitilar hannun Zulaiha. Jikinta kawai Shafi'u yake bi da kallo don ba ƙaramib kyau ta masa ba cikin rigar baccin, duk da doguwa ce amma dai ta bayyana asalin suffarta.
Zulaiha kuwa ta shagaltu da kallon ɗakin ne, tana wani taɓe baki jin yadda ƙamshi ya zauna a ɗakin tamkar yanzu aka saka turaren wuta.
Yaya Sule kuma ganin Aminu zaune dirshan a kan gado yana sanye da gajeran wandonsa, sai abin ya ɗaure masa kai, shi ma Yaya Shafi'u da ya mayar da ganinsa wajen mamakin ne ya dirar masa. Cikin Kakkausar murya Yaya Sule ya katse Zulaiha da faɗin
"Ke Zulaiha mene ne wannan ɗin, Aminun ne kwarto, haka kawai muna bacci kin zo kin ɗagawa mutane hankali" Yana kaiwa aya Yaya Shafi'u ya ɗora da faɗin
"To wai mai hakan yake nufi?" Jin kalamansu cikin tsiwa ta ce
"To amma haka za ku ce ko tambayata za ku yi dalilina na yin hakan?" Da hanzari Yaya Sule da ya fi jin zafin ɗaga musu hankalin da ta yi ya ce
"Mai za a tambaye ki a nan to, bamu ga kowa ba sai Aminu kuma kin ce kwarto yana ɗakin" Ita ma cikin fitsara da rashin girmama na gaba ta ce
"Ai ba kowa bane ƙasurgumin kwarton illa Aminu" Su duka da kallo suka bita ganin ko a jikinta. Yaya Sule a zuciyarsa ya ce
'Taɓ lallai Aminu ya auro mace daidai shi' A fili kuma ya ce
"A ina ya yi kwartancin" Shi kuma Aminu ya rasa ma bakin magana, ba komai ne ya bashi haushi ba illa yadda aka katse masa wani yanayi mai ban al'ajabi wanda ya san a wajen kaɗai ne yake samun wannan yanayin, bai tantance haka ba sai da ya auri Zulaiha ya gane Saddiqa ta keta Zulaiha da tazara mai nisan gaske.
Yaya Shafi'u ne ya ce
"Kin san me kike faɗa?"
Cikin harzuƙa ta ce wai ku haka ake alƙalanci, ba za ku tambaye ni dalili ba sai kawai kuke yanke hukunci, to bari ku ji abin da baku sani ba, Aminu tun kafin in tare a gidan nan ya mini alƙawarin sati biyu zan yi ina amarci, amma yau saura kwana huɗu shi ne zai yi satar hanya ya mini satar kwana" Ta faɗa tana aikawa Aminu harara. Su duka mamaki suke inda Saddiqa ta sunkuyar da kai.
Yaya Sule ne ya ce
"Wai haka ne Aminu?" Aminu yana jin kamar su duka ya rufe su da duka, ganin sun hana shi rawar gaban hantsi ya ce
"Haka ne" Kai Zulaiha ta kaɗa irin ai kun ji da kunnenku. Yaya Sule cikin ɓacin rai ya fara magana
"Kai yanzu Aminu ka kyauta kenan, ka yi wa Saddiqa adalci a ce ka ɗauki kwananta ka haɗawa amaryarka, muna gidan nan amma bamu san wannan cakwakiyar da ka haɗa ba" Aminu ya buɗe baki zai yi magama Saddiqa ta yi saurin faɗin
"Yaya da sanina kuma da yardata aka yi hakan, yanzu ma na ƙara masa sati biyu ka ga wata ɗaya kenan" Ta faɗa don ita zuwansa yau da ta ji warin da ta shaƙa sai ta ji ta ƙara son nesanta kanta da shi.
Da sauri Aminu ya diro daga gadon cikin ɗaga murya ya ce
"Wallahi baki isa ba, daga kwana goman nan dole ki karɓi girki"
Zulaiha jin haka ta sakin taɓaryar hannunta ta ce
"Idan akwai shegen da ya isa ya yanke wannan hukunci shegiya nake" Yaya Sule kai ya sunkuyar yana danne dariyarsa ganin ƙanin nasa ya samu daidai da shi in ba don sakayya da Allah ya yi wa Saddiqa ba, ya za a yi a ce amaryar kwana goma tana wannan masifa.
Sosai hargitsi ya kaure na faɗi in faɗa, tsakanin Aminu da Zulaiha, dakyar Yaya Sule ya sasanta amma abin ya ci tura!.
A ƙarshe dai Aminu ya yi wa su Yaya Sule rashin kunya saboda suna masa faɗan rashin kyautawar da ya yi wa Saddiqa, hakan ya sa kowa ya kama gabanshi suka bar Zulaiha da su Aminun a ɗakin Saddiqa.
Zulaiha ta ce
"Wallahi ina ɗakin nan babu inda zan je" Ta faɗa tana samun kan kujera ta zauna tana riƙe da taɓarya, ta ce Aminu idan ya yi gigin taɓa ta kai za ta ɓare masa, don sosai kishi yake nuƙurƙusarta musamman da ta ga Saddiqa rigar jikinta ta mata kyau, sannan har lokacin bata daina hango hotonsu a idanun zuciyarta ba, yadda ta same shi rungume da Saddiqar hakan ya sa take jin tamkar ta same su da taɓaryar ta yi ta duka ko ta samu rangwamen abin da take ji.
Aminu yana tsakiyar gado a zaune, ya kifa tagumi don yau ya ga abin da ya turewa buzu naɗi, Saddiqa kuwa wuri ta samu ta zauna tana kallon ikon Allah, amma yadda amarya da ango suka ɗumama ɗakin da warin dauɗa kaɗai ya isheta.
Zulaiha har aka kira assalatu tana zaune a wajen, ita kuwa Saddiqa ta fito ta barsu a ɗakin, bayinta ta buɗe da yake kullewa take da mukulli ta je ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin ta ɗauki sallaya da hijabi ta fita waje ta kabbara sallah. Shi kuwa Aminu lokacin har ya fara gyangyaɗi jin sanyin asuba yana ratsa shi, hakan ya sa sai yana cikin gyangyaɗin Zulaiha ta ce
"Wallahi Aminu ka tashi, don ba zan bar ɗakin nan ba sai tare da kai" Ganin ta kaɗe masa hankali jin an shiga sallah ya fito daga ɗakin ya barta a ciki, banɗakin Saddiqa ya nufa amma cikin rashin sa'a ya same shi a kulle, dawowa ya yi lokacin ta idar da raka'atainil fajr ya ce
"Saddiqa ina mukullin banɗakin?" Cikin rashin fahimta ta ce
"Mai za ka yi da mukullin banɗakina" Ya ce
"Shiga zan yi mana" Ta ɗan yi jim sai ta ce
"Ai ba a bakina ba kake, don haka ka je ka shiga banɗakin amaryarka, kuma ina ƙara maka tuni sai nan da sati huɗu da kwana uku ne za ka dawo kwana ɗakina" Tana faɗar hakan ta tashi ta kabbara sallah, hakan ya yi daidai da fitowar Zulaiha, yana ganinta haushinta ya cika shi, ya juya ya nufi ɗakin Zulaihar ransa yana ƙuna ita kuma Zulaiha ta mara masa baya.
Tun da ta shiga ɗakin take balbala masa masifa, wai ya ci amanarta ya satar mara kwana, dakyar ya yi sallah tana masa masifa ita kuma ko sallar bata yi ba, da ya idar ya kalle ta ya ce
"Ke yanzu Zulai...
"Wallahi ka daina faɗa mini Zulai na faɗa maka" Sai ya sake cewa
"Yanzu Zulaiha abin da kika yi kin kyauta, waɗannan fa yayuna ne amma kika faɗa musu magana son ranki ko kunya bakya ji" Kallonsa take sheƙeƙe ta ce
"Kunya? Wace irin kunya, ai ni abin kunya gaba na bashi ba baya ba, kuma da kake kiransu yayunka ai ba iyayenka bane, sannan ni ko daga wajenka ban ga kana girmama su ba, ni ma don ban yi ba ai ba za ka zargeni ba, sannan ina so ka sani batun karatun da na ce zan cigaba da yi a gidanka na fasa dama tun a gida na sanar cewa babu batun karatu kuma an amince mini, don ba zai yiwu in zo ina tafiya makaranta kuna keɓewa da kai da wancan matar taka kuna cin amanata" Tun da fara yake kallonta ganin ba saurarawa za ta yi ba ya ce
"Zulaiha takun da kika shigo gidan nan da shi kinwatsar, saboda ba zan ɗauka ba, sannan ina so ki sani ni nan Aminu bani da mutunci nima don ko matata Saddiqa tsorona take ita da ta shafe watanni ma a gidan bare ke da ko sati biyu baki haura ba" Kallon sakarai ta masa ta ce
"Saddiqa ka ce ni kuma Zulaiha nake, tsakanin harafin sunana da sunanta akwai tazarar haruffa bakwai, don haka ka sani babu gudu babu ja da baya" Banza ya yi da ita ya ce
"Ki je ki yi ta yi amma ki sani za ku zuba ne ɗan halak ka fasa" Ta yatsina fuska ta ce
"To shikenan, ina ƙara maka gargadi da cewa muddin ka ce za ka koma wajen waccana matar taka a cikin kwanakina da ka mallaka mini to ka sani za a yi faɗuwar baƙat tasa, za a yi haihuwar guzuma don wallahi babu wanda ya isa ya taka Zulaiha" Ganin da gaske take faɗan har jijiyoyin wuyanta suna tashi sai ya ƙyaleta a kan cewa zai je gidansu ya sanar da Umma halin da ake ciki, don shi ya fara takura da rashin Saddiqa.
Har wajen tara sannan ya fita, ko wanka bai yi ba wani farin yadinsa da ya koma milik ya saka, don ko abin karyawa bata yi ba tana zaune sai uban soshe -soshe take.
Gidansu ya wuce yana so daga can sai ya wuce kasuwa wajen sana'arsa. Umma ya samu tana zubawa tattabaru abincin, da sallama ya shiga ta amsa, ganinsa sanyi ƙalau sai ta ji duk babu daɗi don dama ta san duk namijin da ya ce zai haɗa mace sama da ɗaya to tabbas ba zai rabu da damuwa ba, duk da ta san Saddiqa tana da haƙuri amma dai ba za a rasa kishi ba.
Bayan ya gaishe ta, ta kalleshi ta ce " Aminu lafiya dai?" Hannu ya kai ya sosai gashin kansa da ya taru ba ya samun aski ya shiga zayyane mata halin da gidan nasa yake ciki. Kallonsa Umma ta yi ta ce
"Hmmm! Dama ai duk wanda ya saya rariya ya san za ta zubda ruwa, yanzu kai saboda rashin adalci da kuma rashin tsoron Allah, ka ƙwacewa Saddiqa kwanan sati guda, anya Aminu kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Rarinyar nan ko shekara bata yi ba da aurenka ka mata kishiya, sannan baka tsaya a nan ba don ka musguna mata za ka ba kishiyarta bakin kwananta?" Tunda ta fara magana ya sunkuyar da kai, lokaci zuwa lokaci yana sosa kansa da yake ta masa ƙaiƙayi, ya ce
"Umma ni fa ba don musguna mata na ce hakan ba, ai gani na yi ita Zulaiha amarya ce" Umma ta ce
"Wato amarya sai a bata kwananta wata? Yanzu don Allah kalli kayan jikinka, ko wanki babu baka ji yadda warin dauɗa yake tashi ba Aminu, yanzu a ce wannan kayan mai datti a jikin magidanci mai mata biyu, shin sai yaushe za ka gyara wanann ƙazantar da kake fama da ita, ai wallahi mace mai zama da kai sai ta kai zuciya nesa, kuma dole ka siyawa kanka raini wajen mace shi ya sa ma Zulaihar ta rainaka" Da sauri ya ce
"Umma dama fa Zulaiha ita ƙazama ce, wallahi da na yi baƙi ranar nan baki ga kwamacalar da ta haɗa musu ba, wai ta kaɗa lalle a matsayin kuka, ta dafa zabuwa da suga Umma wai girkin indiya da na marocco ta musu... Dariyar da Umma ta fara shi ya katse masa maganar ya ɗago yana kallonta. Sai da dariyar ta tsagaitawa Umma sannan ta ce
"Kuma sun ci girkin ƴan indiar ko na maroccon suka ci" Ta tambaya cike da gatse. Aminu da bai fahimci magana Umma ta faɗa masa ba sai ya ɗora da faɗin
"Wallai basu ci ba Umma, hasali ma ƙusa ta saka wai don naman ya yi saurin dahuwa amma bata cire ƙusar ba ta zuba musu a ciki, ranar na kunyata Umma, abin haushin har rigar nono ta je... Kafin ya kai aya Umma ta dakatar da shi don duk ta fahimci inda ya dosa ta ce
"Babu ruwana da duk wani ƙorafinka Aminu, yanzu wannan maganar da ka zo danita a kan maganar kwana shi ma zan je in kashe case ɗin ne saboda Saddiqa, tun da haƙƙinta ne amma sauran sai dai ka faɗawa Babanka tun da ni baka ji shawarata ba lokacin da ka ƙara aure" Kai ya shiga sosawa hannu biyu ya ce
"Umma ita fa Saddiqar da bakinta yau ta ce, sai dai in ƙara sati biyu a kan wanda na ɗaukawa amarya, wai ya zama wata guda, kuma wallahi amaryar nan bata son gyara kanta Umma wanka ma wai ba za ta yi da sabulu ba wai ɓarna ce gwara a cancanta" Baki Umma ta cije ta ce
"Ka ce tuwona maina aka yi kai da Zulaiha, wato zani ce ta tarar sa muje mu, ita ƙazanta kai ƙazanta dama ai gwano ba ya jin warin jikinsa, ita kuma Saddiqa haushin abin da ka mata ne ya sanya ta faɗi hakan amma zan je in lallasheta" Kai ya kaɗa yana sosa kai da hannu ɗaya, ɗaya hannun yana sosa wuyansa, kallonsa Umma ta yi ta ce
"Wai ni Aminu susar nan kuwa ta lafiya ce kake yi?" Yana susar ya ce
"Umma kaina ne yake wani mugun ƙaiƙai wallahi, kuma sai in ke jin kamar wani abu yana yawo a cikin kan, har sai na sosa, kuma wallahi ko a cikin mutane haka nake fama Umma" Mamaki ta yi tana ta kallonsa ta ce
"Inda miƙo mini kan naka in gani" Kan ya miƙa mata, tana jin warin gashij da gumi da ya cakuɗe, ga warin jikinsa na rashin wanka, haka ta shiga buɗe cikin gashin don ganin mene ne, cike da mamaki a maganarta ta ce
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Aminu ka san mene ne a cikin gashinka? Ka san mene ne cunkus a gashin?" Da mamaki ya ɗago yana son jin mene ne wannan wanda ya sanya Umma faɗin haka ya ce
"Mene ne a ciki Umma?" Umma da ta ga abin da ta gani, har guda ɗaya ya gangaro wuyansa yana yawo a jikin farin kayansa....
*MUNA GAB DA GAMA BOOK 1*
*GA MASU BUƘATAR BOOK 2 NA ƘAZAMIN MIJI ZA SU BIYA 500 KACAL DOMIN JIN LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA, SARƘAƘIYA, TURKA-TURKA, ZAN IYA CEWA A GABA ZA MU NUTSA CIKIN LABARIN*
*ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY* *SHAIDAR BIYA TA ****
*INA SAYAR DAMAGUNGUNAN MATA MASU INGANCI NA KAMFANIN MEERAH B HERBS, AKWAI MAGANIN MATA, AKWAI NA RAGE TUNBI AKWAI NA RAGE ƘIBA, AKWAI NA GYARAN NONO, AKWAI NA ƘARA ƘIBA, AKWAI MAGANIN CIRE NANKARWA, DA SAURANSU*
*AKWAI ZANNUWAN GADO, LABULAYE, FRAMES MAYAFAI MASU BEAD WORK, MAYAFAI NA SHAGO, KAYAN YARA, TAKALMA, LESUNA, ATAMFOFI* *DA* *SAURANSU*
*MAI BUƘATA YA MINI MAGANA **** [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****