Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 16
Mamaki fal a fuskar Aminu ya ce
"Ba dai kiyashi ne a shigar mini kai ba kwana da kwanakin nan da nake fama?" Ya faɗa yana kafe Umma da har lokacin ta ras bakin magana, rai a ɓace da haushin maganarsa jin wai yana batun kiyashi cikin masa gatse ta ce
"Tururuwa ce (Ant) Ta yi gida a cikin gashin naka" Aminu da bai fahimci gatse Umma ta masa ba cikin mamaki yana mai sosai kan tare da nutsa yasunsa cikin gashin ya ce
"Tururuwa Umma? Amma abar nan ta cuce ni wallahi, baki ga yadda nake ta fama ba amm dama Umma tururuwa tana shigarwa mutum kai, ko dai ba ta lafiya ba ce?" Haushi ma dakyar ya bari Umma ta ce
"Aminu to ƙwarƙwata ce a cikin kanka cunkus, gata nan har wata ta zo wuyanka daga cikin kan kuma ta ganganro" Da sauri Aminu ya cire hannuwansa daga kan nasa yana mai miƙewa tsaye a kiɗime, don maganar da dake shi matuƙa ya ce
"Kwarkwata Umma? Dama kwarkwata tana fitowa maza na shiga uku" Ya faɗa har lokacin yan tsaye hankalinsa a tashe. Cikin halin ko in kula Umma ta ce
"To mene ne na kiɗimewar? Abin mamaki ne don an samu shazumamu a wajen da aka zubar da suga? Ai ba zai zama abin mamaki ba, tun da in dai an ga zara za a ga wata, in har an zubar da suga ko abu mai zaƙi dole shazumamu ya baibaye wajen, to haka ma tun da kwarkwara ƙazanta ce take kawota ka ga babu ruwanta da kan mace ko kan namiji, duk inda ta samu ƙazanta ta samu mafaka kenan" Umma tana mas wannan jawabin shi kuma ya tafi tunani kamar wanda ya tuno wani abu ya ce
"Wallahi Umma wannan kwasa mini aka yi, tun da Zulaiha ta tare take soshe-soshe a kanta da jikinta, wallahi sai dai in ita ta kwasa mini"Sheƙeƙe Umma ta kalle shi ta taɓe baki ta ce
"Abubya haɗu dai guda biyu, dama can kwarkwatar ta samu mafaka ne saboda tsabar taka ƙazantar" Komawa ya yi ya zauna ransa yana ƙuna, yana hango yadda za su kwashe da Zulaiha don sosai ya ƙara tunzura. Umma ta ɗora fa faɗin
"Yanzu Aminu kana magidanci da mata har biyu, ɗaya tana da ciki amma a ce wai an samu kwarkwata a cikin gashinka? Shin ya kake so in yi da kai? Ka mallaki hankalinka ma sai ina maka faɗan ka gyara jikinka, ko so kake in ke binka gidan naka ina maka wanka ina saka ka gyara jikinka, don Allah dubi kanka kamar tukufar tsire, babu aski babu gyara wari jir ko yanzu baka ji wurin nan yadda yake tashin wari ba, ina amfanin baɗi babu rai, yanzu wa ya san tsawon lokacin da ka kai baka yi aski ba, kuma wa ya san lokacin da ka kwashe baka yi wanka ba...
"Jiya da abokaina za su zo na yi wanka wallahi Umma, ni fa kawai gani nake wankan nan don a ji sanyi da iska ake yi, kuma tun da Allah ya kawo mu, lokacin sanyi ba sai mutum ya huta ba" Tsabar takaici ma sai ta rasa bakin magana, ganin bata ce komai ba ya ɗora da faɗin
"Maganar aski kuwa Umma yanzu ai zamani ya sauya, ba a wani aske gashi, duk mai askewa ma kallon kidahumi ake masa wanda bai waye ba" Baki kawai ta saki tana kallonsa jin bata ce wani abu ba ya ɗora da faɗin cewa
"Ko kuma a yi wa lan wani gyara ki ga kamar kalba, duk ya dunƙule waje-waje haka ake yi... A tsawace ta ce
"Wayewa ko ƙazanta, ai gashin da ake bari wanke shi ake tas a shafa masa mai a taje, amma ba naka ba kai da baka yi wanka ba ma za ka wanke kai? Yanzu a haka ma gashinka ya samu kwarkwata bare aka maka gyaran curi-curi ai ina ga har ƙudan cizo sai an samu a cikin kanka" Yana kallonta yana susa hannu bibbiyu. Ta cigaba da faɗin
"Ka gyara halinka, ƙazantarka kaɗai za ta sa mace ta rainaka, yanzu a ce miji ba zai yi wanka ya saka kaya a wanke ba, kalli haƙoranki har wani iri suka yi kamar mai cin goro, don Allah wace mace ce za ta ji daɗin ganinka a matsayin mijinta?" Shiru ya yi yana wani harhaɗa rai ya ce
"Ni fa Umma babu wata mace da ta isa ta ja da ni, ko ta kawo mini raini a cikin gidana, in kuwa ta ce haka za ta yi wallahi Umma sai ta gwammace kiɗa da karatu... Katse shi Umma ta yi da faɗin
"Dalla rufewa mutane baki, shi ya sa ai na ga yanzu ma matsalar gidan naka ce ka kawo, kuma shi ya sa na ga tsabar isarka ce gashi nan matarka a gidanka ta bika har ɗakin matarka ta maka ihun kwarto" Shiru ya yi yana tuna yadda ya so yau ya kwashe ganima a wajen Saddiqa da jikin nan nata tsaftatacce mai daɗin ƙamshi amma kuma Zulaiha ta katse masa hanzari har yanzu in ya tuna ji yake kamar ya je ya yi ta bugunta har sai ya ladabtar da ita, amma duk da haka yana nan a kan bakarsa na ba zai yarda da raini a gidansa ba, dole duk wacce ta so ta taka shi ya taka ta son ransa.
Jin ya yi shiru Umma ta cigaba da faɗin, ban maka baki ba Aminu amma na tabbata ba za ka taɓa samun mai hankali da nutsuwa haɗe da haƙuri da juriya kamar Saddiqa ba, amma yanzu kai wannan kwarkwatar ma ina za ka je da ita, cunkus a kanka wace mace ce za ta yarda ka raɓe... Shigowar Fatima ce ta katse maganar da Umma take, gabaɗaya Fatima ta ji abin da Umma ta ce, hakan ya sanya ta zaro idanu haɗe da toshe baki ta ce
"Umma kwarkwata kuma a kan Yayan? Na shiga uku wayyo Aunty Saddiqa kin gamu da jarab... Hararar da Umma ta bita da ita ce ta sanya ta haɗiye sauran maganar.
Aminu kuwa jin furucin ta sai ya tashi tsaye a ƙufule yana nuna ta da yatsa ɗaya ɗayan kuma yana susa ya ce
"To magulmaciya, wallahi kika sake wannan maganar ta fita sai na sauya miki kamanni, don wallahi dukan tsiya zan miki" Fatima da sauri ta koma bayan Umma ta raɓe tana cewa
"Umma ni fa ba wani na ce zan faɗawa b... Katse ta Aminu ya yi da faɗin
"Ki faɗa mana, uwar shgen shishshigi" Umma ganin yana kumfar baki ta ce
"Fatima fita ki ba mutane wuri" Fita ta yi tana kallonsa ƙasa-ƙasa da sakin dariya a ɓoye, da sauri ya bita zai kai mata duka Umma ta ce
"Dawo nan, wai kai yaushe za ka nutsu yanzu ƙarya aka maka kalli yadda kake sosa kai, ai abin kunyar ya yi yawa ni takaicin ma kamar in yi kuka nake ji na rasa ya zan yi da kai Aminu, tun kana ƙarami nake fama da kai, amma har yanzu ka kasa gyara rayuwarka da tsafta, komai ƙazanta bakya jon kunya, ko kaɗan" Jin tana faɗa ya koma ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai amma fa har zuciyarsa shi bai ga abin da ya yi wanda za a ke masa wannan maganganun ba tun da gani yake a kan daidai yake.
Suna nan tana ta masa faɗa, har ta koma masa nasiha don abin ya fi ƙarfin faɗa, da a ce Aminu yana jin faɗa da an wuce wannan wajen, shi kaɗai ne Allah ya bata ƙarami a cikin ƴaƴanta kuma marar jin magana, ga taurin kai tun yana ƙarami yake bata wahala, amma har yanzu ana fama da rashin tsaftarsa ta ɗauka idan ya yi aure abij zai yi sauƙi amma ga shi abu yana cakuɗewa har kai da kwarkwata.
Ranta duk a ɓace ta shiga tunanin tun yana ƙarami, kowa zai yi brush amma shi ba zai yi ba, in har zai yi wata da watanni bai wanke baki ba to bab ruwansa sai dai an ce ya wanke, wani lokacin ma sai Umma ce za ta saka masa makilin a brush ɗin, amma in ya faki idanunta sai ya saka ruwa ya wanke makilin ɗin daga jikin brush ɗin a ajiye. Ta sha fama amma a banza, mai ya fi takaici a ce mutum da iyali amma kana masa faɗan wanka. Ɗagowa ta yi idanunta sun i ja ta ce
"Yanzu Aminu kalli farcenka, zaƙo-zaƙo kai baka san cewa farce inuwar shaiɗan bace? A jikinka kai to mene ne kake gyarawa? A haka za ka ji daɗin gabatar da ibada anya kuwa?" Shigowar Baba da sallama shi ya katse maganar da suke yi.
Waje ya samu ya zauna, yana kallonsu Aminu yana ta faman susa, Aminun ne ya gaishe da shi ya amsa, yana kallon yadda yake sosa kai, duk da Aminu yana ƙoƙarin danne ƙaiƙayin kar ya yi susar amma abin ya ci tura.
Kafin Baba ya fara magana Umma ta ce
"Gashi nan ya kawo ƙaran matansa" Nan ta kwashe komai ta faɗawa Baba, buɗar bakin Baba sai cewa ya yi
"Aminu da yardar Saddiqa ka ƙarawa amaryarka kwanaki?" Ƙoƙarin saita kansa ya yi ya ce
"Eh, eh, eh Baba" Shiru Baba ya yi Umma kuma ta shiga aikawa Aminu harara yana sadda kai ta ce
"Ƙarya yake" Nan Umma ta shiga faɗawa Baba dalla-dalla. Baba ya rufe shi da faɗa ya ce ba ya son rashin adalci in rashin adalci zai yi to gwara ya sawwaqewa ɗaya, jin haka sai Aminu ya yi zuruf ya ce
"Amma Baba banda Saddiqa ko? Sai dai Zulai... Katse shi Baba ya yi da cewa
"Aminu gatse na maka fa, ni yanzu kana ganin zan iya saka ka saki matarka babu wani dalili? To ka buɗe kunneka ka jini, tun da ka aure su su duka mutuwa ce za ta rabaku, sannan ina so ka sani duk rashin adalcin da ka yi musu ko ka dannewa wata haƙƙinta Allah ba zai barka ba" Kai ya sunkuyar Baba ya masa tas ya ce da Yamma Umma ta je gidan ta sasanta matsalar.
Umma ta faɗawa Baba maganar kwarkwatar Baba kaɗan bai kai masa duka ba saboda haushi. Nan ya ƙara masa gargaɗi a kan tsafta ya ce ya kama hanya ya tafi kasuwa, haka ya musu sallama ya fita Umma tana cewa idan ya je kasuwa ya saya maganin kwarkwatar ya kai wa ita Zulaihar sannan shi ma ya yi wanka kuma ya wanke kan nan tas ya saka magani, da to ya amsa ya fito.
Yana cikin tafiya a tsakar gidan Fatima ta leƙo tana danne dariyarta ta ce
"Yaya Aminu in ɗakko maka shantos idan ka je gida ka fesa a kanka" Da sauri ya juya ta tahonda gudu ta saka sakata a ɗakin, ya tsaya yana ta masifa yana cewa kar ta kuskura su haɗa hanya, ya rasa mai ya sa Fatima take masa haka ko do ta ga ita take binsa daga shi sai ita.
Kasuwa ya wuce.
Da yamma Umma ta shirya ta biya ta gidan ƙawarta suka wuce gidan Aminun. Sun shiga ɗakin Saddiqa inda ta gaishe su cikin mutunci, ta kawo musu ruwa mai sanyi sai dai waina ta yi kuma ta cinye babu hakan ya sa bata kawo musu abinci ba. Bayan sun gaisa Umma suka shiga tambayarta ba'asin abin da ya faru, kai Saddiqa ta sunkuyar tana jin wani ɗaci a zuciyarta ji take tamkar ta roƙi Umma cewa ta sanya Aminu ya sawwaqe mata, saboda ta lura Aminu ba mijin aure bane, indai za su cigaba da zama a haka tabbas za take cutuwa, duba da yadda yake ƙazamin nan, dama ita yanzu daɗin da take ji bai wuce cewa komawa ɗakin amaryarsa ba ƙaramin daɗi ta ji ba saboda haɗa makwanci da Aminu akwai damuwa.
Umma ce ta ce
"Saddiqa da amincewar ki Aminu ya ɗauki kwanaki ya ba Zulaiha? Bayan nata kwanakin bakwai sun ƙare matsayinta na amarya kuma budurwa" Shiru Saddiqa ta yi don ta tasa abin cewa saboda na farko dai kwanan nan umarni ne aka bata ba a shawarce ta ba, ta wani ɓangaren kuma za ta iya cewa taimakonta aka yj don ita da, da hali ma da ta ƙauracewa Aminu har abada!. To mai ma za ta ce? Mutumin da ya yi amarya ko ya haɗa su ya gabatar da ita a wajen amaryar ba matsayinta na uwar gidansa ba, sai a kicin ta ga amaryar, sannan ya yi watsi da duk wasu buƙatunta hatta abin cikinta ya nuna bai shirya haifarsa yanzu, to ita wace irin magana za ta yi a kan Aminu? Ta ce mai, ita yanzu kishin Aminun ma bata ji sai wanda ba a rasa ba ga matarsa marar kamun kai duba da yadda jiya ta zo ɗakinta ta yi wa Aminu ihun kwarto a cikin gidansa a ɗakinta, kawai saboda tana ganin satar kwana ya mata.
Ƙawar Umma ce ta kalle Saddiqa da tausayawa ta ce
"Saddiqa ana tambayarki amma kin kasa bada amsa?" Ta faɗa tana kallon yadda fuskar Saddiqar ta bayyana asirin zuciyarta, amma duk da haka sai suka tsaya sauraron jin ta bakinta, cikin muryarta mai sanyi cike da ladabi ta ce
"Umma da amincewa ta ya ƙara mata kwanan, shi ya sa jiyan ma na ce na ƙara musu sati biyu" Ta faɗa idanunta suna kawo ruwa amma ta danne bata basu damar zubowa ba, tana tuna irin so da ƙaunar da zuciyarta ta yi wa Aminu amma yanzu ya dishashe komai, da a ce bata zo gidansa ta samu halayen da bata yi zaton samunsa da su, da babu yadda za a yi ta bari a nisanta da shi, duk yadda za ta yi sai ta ƙwato mijinta amma ita yanzu neman kai ma take da shi, so take a barta ta ji da cikin jikinta da take ɗawainiya da shi.
Kallonta Umma ta yi ta ce
"Saddiqa kowa ya kalli fuskarki ya san ƙarya kike, a yadda hasashena ya nuna Aminu ya ba amaryar kwanakin naki ne ba da amincewarki ba kuma wannan tozarci ne a ce namiji ya karɓi kwananaka ya ba kishiyarka" Ƙawar Ummar ce ta ce
"Alamomi masu yawa sun yi nuni da hakan, amma Aminu bai kyauta ba" Umma ta ce
"Zai zo ya same ni sai an rama miki kwanakin ki da aka ƙwace, ma'ana idan kika karɓi girki gobe sai kin yi kwanakin da ta yi a cikin naki sannan miji zai koma bakinta" Da sauri Saddiqa ta ɗago kai tana kallon Umma ta ce
"Umma wallahi na bar mata ba sai na rama ba, idan suka yi wata gudan sai mu fara rabon kwan... Umma ce ta y saurin katse ta da cewa
"Saddiqa me kike ƙoƙarin yi ne? Mijinki kamar kina neman kai da shi? Ya za a yi mace ta barwa kishiyarta har sati uku kamar wani shirin wasan kwaikwayo ko littafin hausa? Hakan fa tozarci ne da jan raini a wajen kishiya, za ta ga baki isa a gidan mijinki ba" Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata ba tare da ya shirya zubowarsu ba ta ce
"Umma ni alfarmar da nake nema a wajenki, don Allah Umma ki faɗawa Aminu yake yin tsafta" Ta faɗa tana mai jin nauyin furucin sai dai babu yadda za ta yi hakan ya zama dole ne domin yanzu mafita take nema a kan ƙazantar Aminu, ta tsani warin jikinsa ta duniya tana baƙin cikin shaƙar warin bakinsa, mai za a yi da ƘAZAMIN MIJI babu wanda zai gane halin da take ciki sai matar da ita ma mijinta ya kasance ƘAZAMIN MIJI.
Shiru Umma ta yi don ta rasa bakin magana, sai ta ji tana jin nauyin Saddiqa, tana tuno yadda ta ga kwarkwata a cikin kansa da yadda jikinsa yake tashin wari, ita ce mahaifiyar Aminu ita ce za ta bayar da shaidar cewa Aminu ƘAZAMI ne na ajin ƙarshe. Cikin lallashi ta kalli Saddiqa ta ce
"Saddiqa na san kina haƙuri sai dai in ce ki ƙara haƙuri a kan haƙuri, sannan ko yau da Aminu ya je na kwashe tsowon lokaci ina masa faɗa da nasiha a kan ya gyara halayensa, amma yanzu ma zan ƙara nannaga masa, na san akwai damuwa amma ki yi haƙuri watarana sai labari, amma ina roƙon ki arziƙi ki yi haƙuri mijinki ya dawo ɗakin ki yau" Ba za ta iya cewa Umma a'a hakan ya sa ta ce
"To Umma babu komai na amince" Ta faɗa tana sadda kai. Ƙawar Umma ta ce
"Allah miki albarka, ya sa hanyar shigarki aljanna ne auran, Allah ƙara miki haƙuri, domin haƙuri shi ne matakin cimma nasara a rayuwa" Da amin Umma da Saddiqa suka amsa kafin suka mata sallama suka fita, ɓangaren Sumayya suka shiga, tana zaune da ɗaurin ƙirji tana shan take, Ruma ma tana shan raken ruwan raken duk sai zuba yake ya gama ɓata mata gaban rigar, duk ta ɓata ɗakin dama daga gani babu shara ga kayayyaki nan zube a ƙasa da kan kujera.
Shigowar su Umma ne ta ɗakko hijabi a kan kujerar wani da ya gama shan uban datti, kana iya ganin datti a fuskar hijabin. Zaunawa ta yi ta shiga gaishe da su, ɗakin sai tashin warin jikin Sumayyar yake.
Bayan sun ɗan taɓa hira, Umma ta ba Ruma biskit da alewar da ta kawo mata, haka suka wuce ɓangaren Amina ma suka gaisa suka ba su Albani nasu biskit da alewar, suna fitowa suka nufi ɗakin Zulaiha.
Zaune take a tsakiyar ɗaki, jikinta da rigar buba ta yadi kanta babu ɗankwaki, duk ta cukurkuɗa shi duk ya tashi tsaye da alama ma susa take yi. Bayan sun zauna ta gaishe da su, Umma tana lura da ita yadda bayan ta saka hule a kan mata amma ta cigaba da susa, sai sosawa take a kai- a kai, Umma kallon tsaf ta mata a zuciyarta ta ce
'Tsakanin ke da Aminun a samu wanda ya kwasawa wani kwarkwatar don ita ma alamomi sun nuna hakan. Umma ce ta yi gyara murya ta ce
"Zulaiha Aminu ya faɗa minj saɓanin da aka samu a gidan nan, shi ne na ce bari in zo in bincika in ji" Tun kafin Umma ta rufe bakinta Zulaiha ta ce
"Umma shi ne bashi da gaskiya, bayan ya bani sati biyu amma na kama shi yau ya munafurce mi Umma turmi da taɓarya na tarar da shi da matarsa" Ta faɗa babu jin nauyin Umma ko wani ladabi
Umma ta ce
"Amma ai kwanan Saddiqa ne, ita mun je min mata magana kuma komai ya wuce, don haka yanzu ki bari yau Aminu ya koma can idan ta yi kwana biyu sai ya dawo bakin ki" Kallonsu take tarrr da wankakkun idanunta ta ce
"Haba dai Umma abin har da zaɓunta, ai maganar fari ita sarki yake karɓa, kuma ko jiya ita matar tasa da bakinta ta ce ta ƙara masa sati biyu, don haka yanzu kuwa sai na yi ƙarasa kwana ukun sannan na ƙarasa sati biyun, ai baki shi yake yanka wuya" Baki sakkak suke kallonta saj da ƙawar Umma ta ce
"Haba ke kuwa ana yin sulhu kuma kya ke wannan maganar, ko ba komai wannan ai surukarki ce" Shiru ta yi tana haɗe gira alamar maganar bata shige ta ba, tashi ta yi ta je kicin ta ɗakko jallof ɗin wake da shinkafa a plate ta rufe da wani plate ɗin sai cokula biyu da pure watar biyu, ta kawo.
Bayaj fitar ta sun jinjina rashin ta ido irin na Zulaiha, don kar ta zargi wani abu suka buɗe abincin, tana gefe tana danna waya, su duka suka yi cokali ɗaya, guntse da abincin suke a bakinsu, don waken bai dahu ba, ita ma shinkafar kamar ta jiƙu ga wani gashiri, kallon juna suka yi dakyar suka haɗiye, Umma tana ƙara ɗakko cokali na biyu sai ga gashi dogo a ciki.
Da sauri Umma ta ajiye tana ɗaukan plate ɗin ta rufe tare da ɗaukan pure water ta shiga sha, ita ma ƙawar Ummar ruwan ta sha, Zulaiha ta ɗago tana kallon plate ɗin da suka rufe ta ce
"A ƙaro muku ne Umma?" Da sauri ƙawar Umma ta ce
"Ah Alhamdulillahi, ai da yake kafin mu fito mun ci abinci" Ba ta taɓe a ɓoye ta tashi ta kinkimi plate ɗin ta ajiye a kicin sai gata ta dawo, daidai nan Aminu ya shigo da sallama. Jir da warin gumi ga jikin nan butu-butu da fulawa. Gaishe da su Umma ya yi, nan Umma suka ƙara musu nasiha da kuma tabbatar da cewa Saddiqa ce za ta karɓi girki, Aminu sai washe baki yake yana tuno yau zai yi kwanan wuri mai tsafta ga kuma tsaftatacciya Saddiqa a gefe, tabbas ya yi kewar ɗumin jikinta da fatarta mai laushi da santsi tamkat kifi tarwaɗa.
Sallama suka musu suka tafi, suna fita suka shiga suka yi wa Saddiqa sallama suka tafi. A can ɗakin Zulaiha kuwa su Umma suna fita ta tashi tsaye ta buga cinya ta ce
"Babu wanda ya isa in ba da kwanakin nan sai na cike sati biyun nan da ka ambata, ai baki shi yake karya wuya, wato saboda an fi son Saddiqar ni za a nuna mini wariyar launin fata" Shi ma a ƙufule ya miƙe tana jin haushin cikas ɗin da take kawo masa na hana shi zuwa kwana ɗakin Saddiqa ya ce
"Yanzu ke uwata ta taso tun daga gidanmu, ta zo ta yi sulhun amma ki ce ba zai iyu ba?" Kallon sheƙeƙe ta masa tana riƙe da ƙugu ta ce
"To in ma ita ce ta zo ɗin, tun da ba adalci ta mini ba ai dole na ɗauki hukunci a hannuna" Yana wani zaro ido ya ce
"Wallahi baki isa ba, wai ke a ce ko sati biyu baki cika a gidan nan ba, kina matsayin amarya amma mu zauna muna sa'insa ke irin ɓoye halin nan na farkon aure ma ba za ki yi ba" Dariya ta sheƙe irin ta rainin hankali ta ce
"Ai yanzu shiru -shiru ƙauyanc ne, kuma ɓoye halayya munafurci ne, na lura kamar ka gaji da ni, ne shi ya sa kake kwaɗayin komawa wajen matarka kuna ko sama da ƙasa za ta haɗe baka isa ba" Cike da haushi ya kalleta ya ce.
"Idan na je sai ki je ki janyo ni ki maido da ni" Yana kaiwa nan a maganarsa, ya juya ya shige banɗaki, jikinsa ya wanke, ya fito ya je kicin ya zazzago klin a hannunsa ya ɗauki mataji(Kumb) Ya shiga bayin ya zuba klin ɗin a kan ya zuba ruwa yana tajewa yana wankewa, kwarkwata tana ta zubowa, sai da ya gamsu cewar ya wanku kan tas, amma maimakon ya saka sabulu ya yi wanka sai ya saka baƙin ruwa ya shashsheƙa, ya fito yana aikawa Zulaiha harara tana sosa kanta ya ce
"Zulai" A ƙufule ta ɗago ta kalle shi don ta tsani Zulan nan da ya tsiri faɗa mata, ya daina kiranta ƴar aljanna yanzu ta ce
"Zulaiha ne sunana, in ba za ka kirani ƴar aljanna ba ka daina mayar mini suna kamar wata tsohuwa" Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya ce
"Ƴar aljanna ai mace mai jin maganar miji ce" Ƙaramin tsaki ta ja ta ce
"Indai a kan maganar rabon kwanane sai daj ka kaini ko ina in ba za ka kaini aljannar ba" Yana binciko kayansa na wanki ya samu wata riga jallabiya yana cikin karkaɗewa ya ce
"Yanzu ke ba abin kunya bane, a ce kin kwasawa miji kwarkwata" Cikin halin ko in kula ta kalle shi ta ce
"Haba ni na ji ƙaiƙayin kaina ya dawo, duk tunanina ba kwarkwatar bace" Baki sake ya juyo yana kallonta da jallabiyar da ya saka a wuyansa bai ƙarasa sakawa ba ya ce
"Wai dama kin san kina da ita?" Ta ce
"Eh mana, ai da za a yi bikin nan aka saka mini relaxer a wajen gyaran kai aka ce za ta fita, ashe dai likimo ta yi" Kamar zai yi kuka ya ce
"To wallahi kin kwasa mini" Dariya ta yi mai sauti ta ce
"Yo ladan amarci ne ka kwasa" Harara ya aika mata, ganin ko shi namiji ya ji ciwon kwarkwatar ita amma hankalinta a kwance ko don ta saba ya ce
"Daga yau idan na dawo ɗakin nan, da kwana sai dai muke kai da ƙafa, don ba za ki ki kashe mini kasuwa ba, in je ina awon fulawa ina susa waye zai siya ina susar kwarkwata" Miƙe ƙafa ta yi bata ƙara masa magana ba ya ƙari mitarsa ya fita.
Da daddare tana kallonsa yana haɗa kayansa wanda ciki babu wani mai wanki, haka ya kwasa niƙi-niƙi ya fita ta taɓe baki tana yin ƙwafa. Wajen ƙarfe takwas da rabi ta ga shiru bai dawo ba, haushi da kishi ya ishe ta don ta san ɗakin matarsa ya tafi, kishi duk ya turnuƙeta tana tuna irin rigar baccin da ta gani a jikin Saddiqa da ta je ɗakin, da irin ƙamshin da ɗakin yake, wannan dalilin ya sa wani kishi ya tokare mata maƙoshi, ta rinƙa juyi tana jin takaici.
Har wajen ƙarfe goma saura amma shiru bai dawo ba bizigir ta sakko daga kan gadon ta fito, ɗakin Saddiqa ta nufa ranta yana ƙuna, tana zuwa da ƙafa ta hangaza ƙofar, yana zaune a bakin gado Saddiqar tana tsaye, magana suke kamar dai jayayya amma dai bata ji abin da suke faɗa ba, idanu ta kafe Saddiqa da shi ganin tana sanye da wani riga da wando na bacci masu laushi, daga wajen ƙirjin rigar gabaɗaya net ne kana iya hangar har bra ɗin Saddiqar wacce dare bai hana ka gane fara ce bra ɗin tas ba.
Kallo ne ya koma kan Zulaiha, ran Aminu in ya yi dubu ya ɓaci, sanye yake da gajeran wando, da singileti don shi tun da ya ga ya ɗauki kayansa a gabanta bata ce komai, kuma ya tafi kusan awa biyu amma bata zo ba sai ya cire rai da zuwanta, tun da ya zo yana ta fama da Saddiqa , sai danya shawo kanta ta amince da shi suna shirin keɓewanya kwashi ganima a wajen aiwatar da sunna, shi ne ta kawo masa cikas.
Saddiqa ita ɓacin ranta yadda Zulaihar take halayya kamar dabbobi, ka bankowa mutum ɗaki babu sallama babu neman izini kenan haka za take mata, abu babu kamun kai, da a wani halin ma suke haka za ta shigo hakan ya sa Aminu cewa
"Wai lafiyarki kuwa Zulaiha" Tana wani taɓe baki tana ƙare musu kallo ta ce
"Lafiyar ce ta kawo haka, na faɗa maka cewa baki shi yake yanka wuya, da ka san kana son zuwa wajen matar taka amma ka ce ka bata dubu biyu ta bar maka sati gudan, yanzu kuma ka dawo sati biyu bai cika ba, in haka ne ai sai ta kawo dubu ɗayar a bar mata kwana ukun" Zulaiha ta sako maganar dubu biyun ne saboda ta ci wa Saddiqa fuska. Cike da jin haushi Aminu ya ce
"Ni na ce miki na bata dubu biyu ta siyar mini da kwananta na sati guda?" Ya faɗa jin ta ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa. Kafin Zulaiha ta ce wani abu Saddiqa ta taka zuwa wajen Zulaiha ta miƙa hannu ta dafa kafarɗata ta ce
"Zaliha kike ko Zulaiha, nan ba ɗakin ki bane, kuma ba ba filin ƙwallo bane, da za ki shiga a lokacin da kika zo, ina miki kashedi daga yau da rana irin ta yau karki ƙara taka mini ƙafafunki a ɗakina, ki tsaya a waje har shi wanda ya ajiye ki ɗin ya fito, sannan batun dubu biyu da kike magana ni na fi ƙarfin in siyarwa wata ƴa mace kwanana a kuɗaɗe ƙalilin marar daraja, ni sai dai ɗa namiji ya bibiye ni kin ga kuwa ai ba zan sayar da kwana ba, yanzu ga ki ga shi nanki tambaye shi tun zuwansa yake fama da ni sai na yarje masa" Saddiqa tana kaiwa nan a maganarta ta ɗan tunkuɗa kafaɗar Zulaiha ta juya ta koma kan kujera ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Haushi takaici ɓacin rai, su ne suka turnuƙe Zulaiha, jin cin fuskar da aka mata, babu abin da ya fi tsaya mata a rai irin yadda wai Aminun yake bin kan Saddiqa wato ita ce bata kai ya bibiyeta ba ita ce take binsa ɗakin matarsa, idanunta ne suka tara ƙwalla, Aminu ya tako ya zo gabanta ya ce
"Ki je ɗakinki kin ga ta ce kar ki ƙara zuwa mata ɗaki" Juyawa ta yi ƙafafunta tamkar ba za su ɗauke ta ba, bin bayanta ya yi zai rufo ƙofar amma sai dai me? Suna zuwa ƙofar ɗaki Aminu bai ankara ba, sai ji ya yi ta kama hantsar gajeran wandonsa, ta shiga jansa ƙiiiii za ta mayar da shi ɗakinta ta ƙarfi da yaji, don ta rantse da Allah ba za ta bar shi ya kwana a ɗakin Saddiqa ba....
MUNA DAB DA GAMA BOOK 1 BOOK 2 500 KACAL GA MAI SON JIN BADAƘALAR DA ZA TA CIGABA DA FARUWA A WANNAN LITTAFIN
ZA A BIYA TA ASUSIN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA *** NA GODE MUTANENA😍🤝 [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****