Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 17
*AMINU*
Idanu ya shiga zarewa, jin ɗanyan aikin da Zulaihar take ƙoƙarin yi masa, cikin inda-inda don gabaɗaya hankalinsa ya tashi, cike da faɗuwar gaba ya ce
"Zulaiha, Zulaiha, ki mini rai kar ki nakasta mini rayuwa" Ya faɗa a kiɗime jin ta damƙo jikinsa da daidai inda ta haɗa da hantsar wandon. Ko sauraronsa bata yi ba saboda yanzu da hannu biyu ta damƙi wajen, shi kuma yana tsoron ya shiga ƙwatar kansa da ƙarfi a je a samu matsala don in akwai inda Aminu yake tattalawa bai wuce wannan wajen ba.
Kamar wani raƙumi da akala haka ya zama, gani yake Zulaiha tun da ta damƙi makasarsa to sai yadda hali ya yi, musamman da ya tuna cewa ya ce mata Saddiqa ta ce kar ta sake zuwa mata ɗaki. A daidai bakin ƙofar ya kama jikin ƙofar da hannu biyu yana ɗan waiwayen bayansa, a kan Saddiqa ya sauke idanunsa wacce take zaune hankali kwance ta ba bango ajiyarsu daga shi har Zulaihar, cikin ɗan ɗaga murya ya ce
"Saddiqa ki taso ki kawo mini ɗauki, in kuma abu ya gagare ki ki tafi ɓangaren su Yaya Shafi'u su kawo agaji kar ta lahantani a banza, domin gabaɗaya ni na san riƙon da ta yi wa wajen nan mai daraja yadda kika san ta damƙo wuyan tinkiya" Wani ɓoyayyan tsaki Saddiqa ta saki don yanzu daga Aminu har Zulaiha haushi suke bata, kwata-kwata lamarinsu babu jan aji tamkar basu taɓa zaunawa aji da sunan ɗaukan karatu ba.
Zulaiha kuwa jin yana cewa a kira ƴan uwansa, sai ta ƙara ƙaimi wajen jansa, saboda so take sai ya jigata kafin ta ƙyaleshi in ya so daga yau zai daina raina mata hankali. Aminu kuwa jiran amsar Saddiqa yake jin bata ce komai ba ya fara magana da cewa
"Shikenan dama an ce na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo, shikenan ni kuma sai yadda hali ya yi ɓarawo a hannun mata" Zulaiha ɗan sunkuyawa ta yi kamar mai jan abin da ya fi ƙarfinta, Aminu jin za ta lahanta shi ya shiga roƙonta, ko ta kansa bata bi ba ta fisge shi sai kuwa ya daina ja baya son ya ga za ta masa lahani a zuciyarsa ya ce
'Ɗakin Saddiqar nan dai ko ɗakin gwal ne, gwara in haƙura da kwanan yau, in ba haka ba sai dai a zo ana mini jaje, ko dai ta mayar da ni mata maza ko ta cisge mini mafitsarae ma ta sa in shiga uku, sai dai in ga ana aure ni kuwa da nake da niyyar sai na rufe ƙofa, wato mata huɗu' Ya faɗana ransa yana daina togewa daga jan da take masa, a haka suka fita bar ƙofar ɗakin Saddiqa, suna tafiya Zulaiha tana jaye da hantsar wandon, yana ji yana gani sai waiwayen ɗakin Saddiqa yake bayan ya san ya gama shawo kanta ta amince da shi amma Zulaiha ta kawo cikas.
Suna dab da ƙarasawa ɗakin Zulaiha wata dibara ta faɗowa Aminu, tunani ya yi a kan ya damƙi gashin Zulaiha tun da ya san tsawon lokacin nan bata yi kitso ba kuma ba mai take shafawa ta taje ta gyara ba, ya san kuwa dole ta ji ciwo, Zulaiha ta juya tana jansa hankali kwance a ranta tana jin daɗin ta raba shi da ɗakin Saddiqa tana ƙudurtar yanzu ta fara yin hakan, duk da gargaɗin da Saddiqa ta mata ya ɗan razanata, amma dai a nata ganin ta samu lagon Aminu da za ta ƙwace shi ya koma hannunta, Saddiqa ta zama ƴar kallo.
Tana murmushin jin daɗin a ranta sai ta ji kamar daga sama an damƙi gashinta, wani ƙara ta saki don sosai ya damƙa yadda za ta ji a jikinta, zafin da ya ziyarce ta sai ta manta da riƙon da ta yi wa Aminu don tuni ta sake shi, bai saka mata ba sai da ya bari ta sakankance ya saki.
Hannunta duka biyu ta kai ta dafe kan nata, kafin ƙiftawar ido Aminu ya fita da gudu, zai koma ɗakin Saddiqa don yau kawai hango shi yake ya kasance da ita. Sai lokacin Zulaihanta lura da abin da ya yi ta kuwa take masa baya, Aminu yana dab da faɗawa ɗakin Saddiqa a nufinsa yana shigewa zai saka sakata, sai dai mai kusan ƙarasowarsa ya yi daidai da tashin Saddiqa wacce ta burmawa ƙofar ɗakinta sakatar sama da ƙasa. Don haka Aminu gwaram ya bugu da jikin ƙofa, wanda hakan ya yi daidai da zuwan ƴar aljanna tana zuwa a maimakon ta damƙi hantsar sai ta kamo tsantsar wandon wato ƙugun ƙiiiii ta shiga jansa da baya, sai rafka salati yake jin tana jansa da ƙarfi kuma sai taka duwatsun tsakar gidan yake, tana zuwa ta tura shi cikin ɗakin ta garƙama sakata, daga shi har ita suka shiga mayar da numfashi kowa yana aikawa ɗan uwansa harara kamar idanunsa za su faɗo.
Banza ta masa ta zauna bakin gado tana ɗan taɓa kanta, don yanzu gabaɗaya kanta ma ciwo yake sanadin gashin da Aminu ya ja mata. Shi kuwa a tsakar ɗakin ya zauna yana buga tagumi hannu bibbiyu, Zulaiha kallo ɗaya ta masa ta taɓe baki ta ce
"Ai ko zinariya ce wannan matar taka, dole ka haƙura sai kwanaki bakina ya ƙare sannan" Tamkar ya saki kuka haka ya ji, yana ciro hannu ɗaya daga tagumin da ya buga ya kai hantsar wandon nasa ya taɓo jikinsa, yana son tabbatar da cewa Zulaiha bata yi masa illa ba, yana ɗauke hannun daga wajen ya kai ƙugun wandon wanda Zulaiha ya janyo shi baya ta saka hantsar kasancewar wandon ya ci uban tsufan shi ya sa jan da ta yi masa ya taɓe don yanzu har zamewa yake yi ma ba ya zama a jikinsa.
Idanu ya runtse yana jin daman bai auro Zulaiha ba don ta sanya shi a rijiyar matsala mai gaba dubu. Jin tafiya a cikin gashin kansa gabansa ya faɗi, don duk a tunaninsa yadda ya wanke kansa da klin ya taje to kwarkwatar ta fita amma wani ƙaiƙayi da ya ziyarce shi ya hau susa da hannu biyu.
Kallon Zulaiha ya yi wacce take susa tun ƙarfi kamar zai yi kuka ya ce
"Wallahi Zulai kin cuceni," Bata daina susar na ta masa kallon sheƙeƙe ta ce
"Da na maka me?" A ƙufule yana susa ya ce
"Da kika kwasa mini kwarkwata mana" Baki ta taɓe ta sosa tsakiyar kan nata, tare da dunƙule hannun ta ranƙwashi kan nata inda ta ji ƙaiƙan ya fi yawa ta ce
"Muka kwasawa juna dai, ni fa ba na jin ma cikin gashin nan naka za a rasa kyankyasai, don na san tsabar datti da wari kyankyaso zai ɗauka masai ne ya shige maka kai... Tsaye ya miƙe yana muzurai ya ce
"Wallahi Zulai kin ga makwancina da yawa, amma tun da kin rainanj zan fara banbance miki aya da tsakuwa don bana ɗaukan raini, Saddiqa sai yadda na yi da ita sai abin da na ce mata, kuma bata taɓa faɗa miki magana a kan ƙazanta don ta tozartani ko ci mini mutunci ba, amma ke kin zo da sabon salo kiran sallah da usur, ke irin kawaicin nan ma na farkon zuwa da amare suke yi baki yi ba... Dariyar da ta kwashe da ita ne ya dakatar da Aminu daga banbamin faɗan da ya ɗauka, sai da dariyar ta tsagaita mata ta ce
"Saddiqa ka ce, an faɗa maka kowace mace ce mai haƙuri ko kawar da kai, da can baka san abin da take maka ba sai da ka rufe ido ka rambaɗo mata kishiya, sai yanzu ne ka san halaccin da ta maka, ku dama maza ai bakwa gane halaccin mace a wajenku, to ni ba zan ɗauki duk wani soki burutsu ba, kuma da kkae batun bata maka cin fuska a kan ƙazanta wannan ita ta ga dama, kuma wallahi Aminu aurenka kaɗai ma sai dai in ce Allah ya sa kaffara ne" Ta faɗa tana tafa cinya.
Bai ji zai ita furta komai ba shi yanzu lamarin Zulaiha ya fara wuce masa makaɗi da rawa, yanzu tunaninsa ma ɗaya yadda ta je ta janyo shi, ba don Allah ya sa cikin dare bane gida ba su kaɗai ba ai da ta gama kunce masa zani a kasuwa.
Yana ji tana ta nasifar ya fara gudunta tun ba a cinye amarci ba, don munafurci yana ƙulafucin uwar gidansa. Zuwa ya yi zai canja wandon tun da ta taɓa ƙugun wandon nasa, amma sai ya tarar ashe duka ya kwashe kayan ya mayar ɗakin Saddiqa. Can gefe ya raɓe ya kwanta, zuwa can ita ma ta shiga zabga doguwar hamma, hakan ya sa ta kwanta a kusa da shi, da ya ƙyalla ido ya bucan kanta wanda babu hula bare ɗankwali a kusa da nasa kan, sai da ya bari bacci ya sure ta ya lallaɓa ya maida kansa wajen ƙafarta wato suka yi kai da ƙafa. Ashe ba nisan bacci ba ta yi, sai ji tashinta ya yi hakan ya sanyabya fara sakin munsharin ƙarya, bata bj ta kan munsharinsa ba sai ji ya yi ƙiii ta ja ƙafafunsa duka biyu, ta juya shi kamar wata waina a tanda, ta mayar masa da kansa inda ya ɗauke wato suka koma ga kanta ga nashi, kowa hannu a ka yana susa a haka bacci ya sure su.
A haka sai da Aminu ya ƙarasa ragowar kwanaki ukun nan na sari biyun Zulaiha, don addabarsa ta yi da masifa, zuwa wannan kwanakin kwanukan Zulaiha duk suna baje a kicin kaca-kaca don har ranar ko kwanunkan da baƙin Aminu suka ci abinci bata wanke ba. Abin da ya fara ci wa Saddiqa tuwo a ƙwarya kenan, ita gashi bata ƙaunar ƙazanta sai kuma ta haɗu da miji ƙazami kishiyar ma ƙazama. Har bata son zuwa kicin saboda yadda ƙudaje suke safa da marwa a kan kwanukan Zulaiha, farantina food flaks cokula tukwane babu wanda babu ta lodosu abinta, idan za ta yi amfani da kwano, saboda baƙar ganda da ƙazanta ba za ta ɗauka cikin mararsa wankin ta wanke, sai dai ta ƙara buɗe wani sabo fil ta yi amfani da shi. Ga rashin iya girkin da bata yi ba sai ta yi abincin wajen sau nawa, wani lokacin sai ta dafa shinkafa kusan sau uku kafin ta samu wacce za ta ci wata ta ƙone wata ta yi ɗanya-ɗanya wata kuma gata nan dai to ta hakan yake ɓata kwanuka masu yawa, ko mai za ta soya sai ya ƙone duk kayan garar da aka kawo musu ta ci ƙarfinsu.
Ranar da ta cika sarin biyu ne, Saddiqa ta shiga kicin za ta dafa ruwan zafi, abin mamaki sai ta ga Zulaiha ta ɗauki tukunyarta ta dafa indomie, da alama girkih da dare ta yi, cike da mamaki ta ga har fork da plate ɗin duk nata ne, sannan kuma da ta gama amfani sai ta kwasa cikin jibgin kayan wanke-wanken ta. Amma haka Saddiqa ta ware su ta wanke ba tare da ta ce komai ba. Da yamma kuma ta shiga kicin ɗin za ta ɗakko plate da wuƙa za ta yanka mangwaro tana shiga ta samu Zulaiha ta yi ɗanwake a tukunyarta, ta kwashe a robarta sannan tana zubawa a plate ɗinta sannan fork da spoon ɗin ma na kai duk nata ne.
Mamaki al'ajabi suka saka kanta ya ɗaure, ta ma rasa ta ina za ta fara magana, tana tunanin cewa wani abu amma sai ta ga ita Zulaiha ko a jikinta hasalima ta nufi wajen robobin Saddiqa wanda take zuba yaji da su maggi ta buɗe robar jan yaji ta saka cokali ta ɗakko za ta zuba a ɗanwaken da Saddiqar take yi kallon ɗanye, saboda kana kallonsa za ka gane bai dahu ba. Har Zulaiha ta zuba yajin ta ɗakko plate ɗin ta zo za ta gota Saddiqa, cikin dakakkiyar murya Saddiqa ta ce
"Wai ni malama mai yake faruwa a wannan kicin ɗin ne? " Yatsina fuska Zulaiha ta yi cikin rashin sanin manufar Saddiqa ta ce
"Ban gane ba mai kike tambaya" Zulaiha ta faɗa tana ƙarewa Saddiqa kallo ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake tashi daga jikin Saddiqar wanda ƙamshin ya haɗe wajen, saɓanin jikin Zulaiha da yake bada wani nau'in warin dauɗa da ban.
Saddiqa ta ce
"Shin bakya bambance tsakanin fari da baƙi ne?" Cike da wani kishin Saddiqa da ya tokare Zulaiha cikin zafin zuciya ta ce
"Wai mai kike nufi ne, ya za ki tare ni kina mini wani bayani marar kai da ƙafafu?Idan za ki tambayi abu ki yi da hausar da zan gane" Ɗan ƙanƙance ido Saddiqa ta yi ta ce
"Ina nufin ke bakya gane kayanku da kayan da ba naki ba? Ina nufin kwanuka, ya za kike ɗaukar mini kwanuka kina ɓatawa, sannan abin bai tsaya a nan ba har kike buɗe mini robar yaji kina ɗauk... Tun kafin Saddiqa ta kai ƙarshen maganar Zulaiha ta katse ta da faɗin
"Sai mai to? Idan ba a so kowa ya taɓa kayan kowa a kicin ake warewa, ke kuma naki mijin saboda tsiya ya haɗamu a kicin ɗaya kamar wasu sakarkaru, kwanukan da na ɗauka kuma wanda na gani a wanke ne, shi kuma yaji na ji daka da ɗanɗanonsa ya mini kin ga babu buƙatar sai matar gida ta san mini tun da ba almajiranci na zo gidan ba, gidan mijina ne, sannan kwanukan nan da suka taru na wanke-wanke za ki iya haɗawa da naki ki wanke, don ni wanke-wanke da shara basa ma cikin tsarina" Saddiqa ta ce
"Sannu zaƙaƙura wannan sai dai ki faɗawa wanda ya ajiye ki, ko shi yake wankewa ko ya ɗauka miki mai yi, don ni na fi ƙarfin bautawa kishiyar da za ta yi gadara da ni, batun yaji kuma wanda kike taƙamar da shi ba shi ya saya ba, ba shi ya daka ba don haka karki ƙara gigin taɓawa don sai na saka kin gwammace kiɗa da karatu" Tsaki Zulaiha ta ja, ta ce
"Ke banza ce sakar... Tun kafin Zulaiha ta ƙarasa sai ji ta yi ƙiii Saddiqa ta warce farantin hannunta wajen kwanukan nan mararsa wanki ta nufa ta ɗauki wani faranti a wajen ta ɗaga ɗanwaken za ta juye, da sauri Zulaiha ta ce
"Kar ki kuskura don wallahi ba zan yar... Kafin ta ƙarasa Saddiqs ta juye a kan farantin marar wanki ta nuna Zulaiha da yatsa cikin kalami na wanda ya san abin da yake faɗi ta ce
"Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, domin babban goro sai magogin ƙarfe, iya gani iya ƙalewa ki sani duk nisan jifa ƙasa zai faɗo, ni na fi ƙarfin ki kirani sakarya, ina so ki sani wanda ya rigaka da kwana ya rigaka da tashi, domin wanda zai je sama ya taka dutse haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya" Saddiqa tana kaiwa nan ta wuce ta ɗauki plate da ƙaramar wuƙar cokula ta juya za ta tafi, har ta kusa fita ta koma ta haɗa kayanta da Zulaiha ta ɓata a waje guda.
Ran Zulaiha ƙuna yake tana ji kamar ta shaƙe Saddiqa ta mata dukan tsiya. Tana juyawa ta hangi ɗanwakenta a faranti marar wanki, bayan ta shirya cin ɗanwaken, Saddiqa tana zuwa za ta wuce sai ta ji Zulaiha ta ja rigarta ƙiii ta dawo da ita baya saitinta. Rai ta haɗe tana aikawa Zulaiha wani kallo ta ce
"Daga yau kar ki ƙara kai hannunki jikina" Zulaiha tana jin wani tuƙuƙin ɓacin rai ta ce
"Mai ya sa kika zuba mini ɗanwakena a kwano marar wanki?" Cikin halin ko in kula Saddiqa ta ce
"Saboda shi wancan marar wankin shi ne mallakiinki kuma halaliyarki, kuma ai hausawa sun ce guntun gatarinka ya fi sari ka bani, sannan idan har tsafta da daɗi ka ga abu mai kyau ya baka sha'awa, to ya zamana dole ka koyi kintsa naka da tattala naka, ba wai ka mayar da kayan wani naka ba" Saddiqa tana kaiwa nan ta juya ta fito daga kicin ɗin, hakan ya yi daidai da shigowar Aminu gidan, wanda yau yake cike da murnar komawa ɗakin Saddiqa da kwana.
Wani ƙaramin kukan kissa Zulaiha ta rushe da shi, wacce ko sannu da zuwa bata masa ba ta shiga faɗin
"Ɗan aljannata, ka ga matarka tana mini wani irin cin kashi" Aminu da yanzu kawai dama cike yake da ita, jin ta kirashi da ɗan aljanna sai ya ce
"Ni fa bana son tashin hankali, ya tun da sanyin safiya na fita neman abin rufawa kaina asiri amma daga zuwana zan tarar da wani makararran faɗanki?" Bai jira cewarta ba ya juya zai tafi ɗakin Saddiqa rai cike da haushi Zulaiha ta bi bayansa da harara. Saddiqa ma baya ta take masa tana jin wani abu yana yunƙuro mata don zuwansa wajen ya sauya iskar da take kaɗawa.
Zulaiha ɗakinta ta nufa ranta yana ƙuna, ta ɗauka a matsayinta na amarya Aminu zai ƙuntatawa uwar gidansa saboda ita amma ta zo ta ga saɓanin yadda ƙawaye suke zugata sai dai bata gane cewa ko dai ita ce bata kai matsayin da za a ƙuntatawa wata dalilinta ba, don yanzu ta lura Aminu kamar an sauya mata shi.
A ɗakin Saddiqa kuwa Aminu ransa fari ƙal ya shiga, jin wani ni'imtaccen ƙamshi ya mamaye ɗakin, wani yadi ne ruwan toka a jikinsa saboda yadin bai cika nuna datti ba sai ya maimaita shi ya fi a ƙirga don shi dama bai damu da haske ko dauɗar abu ba. Yadda ya sha rana a kasuwa ya sanya bayansa jiƙewa hakan ya sa rigar har mannewa take yi. Yana ƙarewa ɗakin kallo ya ƙarasa bakin gadon ya zauna. Saddiqa da tun da ya doshi ɗakinta annaurin zuciyarta ya sauya ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Tamkar ya ari baki haka ya shiga amsa mata cike da ɗokin ganinta yana faɗin
"Saddiqa amaryar kuma uwar gida" Bata amsa masa ba ta ƙarasa ta zauna a ƙasa tana janyo wankakken mangwaron da za ta yanka, ranta yana ƙuna don ganin Aminu ya zauna a kan gadonta ta san zanin gadonta fari ya tashi daga aiki, don ko shigowarta ɗakin kaɗai ta san akwai wanda datti ya yi wa kanta a ɗakib nata. Bai damu da yanayin fuskarta ba ya ce
"Saddiqa ina mukullin banɗakin ki" Wani daɗi ta ji a ranta duk da tana taraddadin shigarsa banɗakin nata, amma dai duk tunaninta wanka zai ce zai yi bata san cewa har yau Aminu yana nan yana taka matsayinsa na Aminu kuma yana amsa sunansa ya ƘAZAMI ba, tana cikin tunanin hakan ya ce
"Ina son zan tsugunna" Dimmm ta yi jin wai kashi zai yi, ta fara tuno yadda banɗakin yake a wanke tass, yadda take amfani da kayanta ita kaɗai. Kallonsa ta yi tana tuna yadda ba ya ploshing wani lokacin da yadda yake ɓata shaddat kanta in ya tsubunna kamar wani ƙaramin yaro, ita dai ba don ba don ba da ta ce ta yafe Aminu a matsayin miji, sai dai ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta akan hakan cikin jikinta yana taka muhimmiyar rawa, duk da hausawa suna faɗin da babbar budurwa a gida gwara ƙaramar bazawara sai dai yanzu ta fara taraddadin komawa gida zawarci da ƙaramin ciki, har ta haife ta raine shi, sannan ta yaye in ma ta samu mai aurenta shin ya makomar rayuwar abin da za ta haifa zai kasance.
Mukullin ta miƙa masa, yana ta ƙoƙarin son ganin fuskarta amma ta ƙi bashi dama, fita ya yi yana rawar ƙafa ya nufi bayin. Zulaiha tana hangoshi ya shige bayin bayan ya buɗe, tana jin wani kishinsa yana taso mata. Ya daɗe a bayin kafin ya fito bayan ya yi wankin jiki haɗe da yin alwala ya rufe banɗakin ya fito. Ko kallon inda Zulaiha take bai yi ba, yana ganin lokacin da ta tashi ta nufi ɓangaren Sumayya.
Saddiqa tana zaune tana shan mangwaron ya dawo ɗakin, a ranta tana ta addu'ar Allah sa wanka yake da ta ga ya daɗe, sai dai yana shigowa ta gane jikinsa bai san da zaman wani abu ruwan ba, a ranta tana ƙiyasta mai hali ba ya sauya halinsa. Kabbara ya yi tana gani ya yi azahar da la'asar, tana hango a ce wannan uban ƴaƴanka ne shin mene ne wanda yaran za su koya a bayyane daga mahaifinsu, ƙazanta ko rashin kiyaye sallah a kan lokacinta, ko uwa uba rashin kula da addinin kansa, babu wani abin koyi daga Aminu, sai dai abin Allah wadai.
Ko da dare haka ya kwaɓe kaya ya hau mata gado tiƙiƙi, yana son haɗa jikinsa mai dauɗa da nata tsaftattacen jikin, wannan ya sanya ra ji duk ta tsani kanta, amma babu yadda za ta yi ta hana shi kanta saboda gujewa tsinuwar mala'iku, haka ya kusanceta damuwarta ma soshe-soshe musamman cikin kansa wanda duk tunaninta dauɗa ce bata san cewa kwarkwata bace.
A wannan daren mutane biyu ne suke cike da ɓacin rai kasancewar wannan daren da Aminu da Saddiqa suka raya, Zulaiha wacce kishi ya hana bacci tana ta saƙe-saƙen abubuwan da su Saddiqar suke gabatarwa, sai kuma Yaya Shafi:u wanda tun lokacin da ya yi arba da rigar baccin jikin Saddiqa ranar da Zulaiha ta yi wa Aminu ihun kwarto ya ji ya kamu da son kasancewa da ita, wani irin shauƙi da shaiɗan yake ƙiyasta masa a kan matar ƙanin nasa, hakan ya sa yake jin zafi da zugi a ransa don ya san yau Aminu ya koma ɓangaren Zulaiha.
Yana rayawa a ransa cewa an ce idan ka ga wata mace ta birge ka ka koma ga matarka ta gida, to sai dai a nasa ɓangaren abin ba haka yake ba, domin kuwa a halin da yake ciki yanzu da yake jin tunanin wata ya hana shi sukuni, watan ma matar auren, matar auren ma matar ƙaninsa, amma a sannan ne idan ya juya ga tasa matar da take kwance shame-shame a kusa da shi sai ya ji wani ɗoyin rashin tsafta da warin hammata yana tashi daga jikinta. Bakinta da ta buɗe wayam tana bacci wani warin baki ne yake fita, hakan ya sa daga ya doso gare ta sai ya juya can ƙarshe gadon da sauri yana mayar da numfashi tare da yin da na sanin a kan kasancewar Sumayya matsayin mata gare shi.
Tun daga wannan rana ya zamana rabon kwana ya koma kwana bibbiyu, wanda Zulaiha babu abin da ya yi saura a lamuran ƙazantarta sai abin da ya yi gaba, musamman da ya kasance ɓollowar ciki a jikinta, wanda ya dagulawa Aminu lissafi don shi dama cikin Saddiqa ma ba so yake ba bare kuma yanzu abu ya haɗe masa biyu. Ƙazantar Saddiqa ta yi tsamari da tunbatsar da komai ta cunkushe saboda laulayin ciki, hakan ya sanya Saddiqa ta sallama mata kicin, ta biya kuɗi aka mata kicin na langa-langa ta kwashe kayanta ta mayar can, saboda ba za ta iya cigaba da cuɗanya w kicin ɗaya da Zulaiha ba. A ɓangare ɗaya nata cikin yana girma, inda har ya kai matakin haihuwa, lokacin na Zulaiha kuma watansa uku.
Allah ya sauki Saddiqa lafiya inda ta haifa ƴarta mace, Babansu Aminu ne ya ce a saka mata Fatima sunan autarsu inda suke kiranta da Nihal. Tun da Saddiqa ta haihu aka kawi mata mai zaman wanka sai gabaɗaya Aminu ya ƙwaura ɓangaren Zulaiha, duk da ba haka ya so ba, amma hakan ya zama dole a gare shi, ga kuma tasa ƙazantar da babu abin da ya yi saura sai dai cigaba.
Bayan Saddiqa ta yi arba'in sai ta nuna masa dole sai ya canja halayya don ita ba za ta juri zaman wannan da shi a haka ba, ga kuma ƴarta kar ta taso a haka tana koyi da shi, lamarin da ya kawo musayar yawu da tashin hankali don sai Aminu ya nuna ita bata isa ta sauya masa ra,ayinsa ba ki ta sanya shi dole, dama tun da ta haihu yake jin haushinsa saboda yana ganin ta ƙara ɗora masa nauyi ne, ga kuma Zulaiha ita ma da nata guzurin cikin.
Hakan ya sa Aminu ya buɗe wuta, yake taka duk wanda ya so kuma yana nuna babu wanda zai saka shi ko ya hana shi daga Zulaiha har Saddiqa. Ita Saddiqa yanzu sau ta yi sati bata ga Aminu ya saka kaya mai wanki ba, duk ya yi baƙi haƙoransa sun yi yellow tamkar mai cin goro, ƙafafunsa faso babu kyan gani, hammatarsa kuwa tamkar za a yi kitso saboda tsawon gashi, hatta mararsa biyuyu da gashi, sannan tun lokacin da Saddiqa ta gane yana da kwarkwata, a washe garin ranar da ta karɓi girki da safe, tana gyaran gado ta ga kwarkwatar a kan filo guda biyu a kan zanin gadon kasancewar zanin gadon fari ne, ta shiga tashin hankalin da har sai da ta zubar da hawayen baƙincikin auren ƘAZAMI irin Aminu.
Ta nemi magani har sai da ta ga kwarkwatar ta mutu, amma da yake a kan Zulaiha ya kwasa yanzu ma ya sake kwaso wata kwarkwatar ita kuwa Saddiqa duk ranar da yake ɗakinta sai ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, tun da ta ga yanzu da ta haihu ma kansa rawa yake, kamar dai wanda yake kula ƴanmata.
Hakan ya sa yake mata wulaƙanci, bai san cewa ita ta fi kowa baƙincikin zama da shi ba, ga yayansa da yake mata kallo mai ma'anoni da dama hakan ya sa ta ji duk gidan ya gundure ta.
Watan ta biyu da haihuwa lokacin cikin Zulaiha yana da wata biyar, a sannan ne Aminu yake ganiyar neman macen aure wacce za ta maye masa gurbi, saboda yana ganin Saddiqa ta haihu yana mata ganin budurcinta ya kau, duk da wata budurwar ma ba za ta faɗa mata matsi ba, kasancewarta mace mai kula da kanta amma da yake hankalinsa ya yi gaba sai yake hangen wasu, tun da ita dama Zulaiha ma ba ya saka ta a layi don a ganinsa ita ta gaza ta fannoni da dama, tun ba a je ga haihuwa ba.
Aminu yanzu idanunsa da suka shiga yawon neman matar aure basu yi masauki a ko ina ba sai a gidan yarbawan unguwarsu, gidan gidan haya ne inda wani bahaushe ya gina yake bada haya shekara da shekaru. Maman iyabo sun dawo arewa ne daga kudu inda mijinta ya kama musu haya, suke zaune, asalinsu ba musulmi bane amma zaman su a cikin musulmi da yake Allah ya saka suna da rabo sai suka musulunta.
Maman iyabo da baban iyabo ƴaƴansu biyu iyabo wacce ta rasu tun tana ƙarama sai kuma Aisha wacce bayan sun musulunta suka haife ta. Aminu ya san gidansu kuma ya san Aisha, tun tana budurwa take gasa masara mamanta kuma ƙosai take yi. Aisha ta auri wani bahaushe inda auren bai je ko ina ba ya mutu, duk da shi Aminu bai san mene ne silar mutuwar auren ba.
Aisha irin manyan matan nan ne masu ƙiba da cikar haiba, amma baƙa ce tana da manyan gaɓɓai tamkar namiji haka yanayin jikinta yake. Aminu tun da ya ganta ya ji duk duniya bashi da wani buri da ya wuce auren wannan matar inda ya shiga mata hidima, yana ƴar tsafta da kwaskwarima don ya samawa kansa matsugunni a zuciyarta saboda aurenta yake son yi da gaske.
Bai sanarwa da su Saddiqa yana neman aure ba, duk da abubuwa da dama sun nunawa Saddiqa haka, don in har mijin mace yana neman aure duk takatsantsan ɗinsa na kar ta sani tana iya ganewa sai dai ba lallai ta fahimci hakan ba
Bai faɗawa Umma ba don ya san ita tamkar adawa take da aurensa, kullum maganarta ɗaya ita ce ya tsaya ya samawa iyalansa nutsuwa da shi kansa. Baba jin inda Aminu ya ɗakko dala babu gammo sai ma ya ji ya fi Aminun farinciki tun da mahaifin yarinya yana da kamala kuma kowa ya yaba da tarbiyar yarinyar kasancewar ana zaune waje ɗaya shekara da shekaru. Baba ya amince inda Umma faɗa tamkar ta ari baki, sai dai babu yadda za ta yi tun da ita ma ƙarƙashin Baba take umarni yake bata, shi Baba yana kafa hujjar cewar indai yaro aure zai yi ba zai hana shi ba da a ce yana zina gwara auren.
Ita kuma tana hangen na gidan ma da ya suka ƙare, bare kuma yanzu ya je zai auri wacce yarensu ba hausa ba, amma dai ta san kowa ya shiga rayuwar wani akwai darasin da yake ɗauke da shi, tana fatan Aisha ta shiga gidan Aminu da darasi mai ƙarfi wanda za ta zama silar warkewar ciwukannda zukata suke fama da shi a dalilinsa.
Gida ya kama haya, ɓangare uku ne a gidan kowanne ciki da falo da bayi, kicin ne guda ɗaya, sai kuma ɓangaren Aminu wanda ɗaki ɗaya ne babu bayi a ciki.
Kasancewarta bazawara aka yanke aure wata guda, yau da ya rage saura sari uku biki shi ne Aminu ya kirawo Zulaiha da Saddiqa domin faɗa musu auren da zai yi, saboda Umma ya roƙe ta faɗa musu ta ce babu ruwanta ya je ya yi abin da ya ga ya dace.
Zaune suke a falon Saddiqa don dakyar Zulaiha ta zo shi ma sai da Aminu ya mata muzurai, sanye take da zanin falle da riga tshrt wacce faɗin ya mata yawa amma saboda yadda take jin daɗin saka kayan a haka take sakawa.
Ita Zulaiha ta ɗauka sulhu ne zai yi, a kan rashin mutuncin da yake zai nemi yafiyarsu, shi ya sa take ta wani shan ƙamshi, saɓanin Saddiqa da dama tana lura da takunsa, ta san dai yana waya kuma tana ganin ana kiransa, amma bata san har yana da burin yin aure a kwana kusa ba wanda ya rage sati uku!
Gyaran murya ya yi hannunsa ɗaya a kansa yana susa ya fara magana kamar haka...
*MUN ZO GANGARA A BOOK 1 SAURA SHAFI ƊAYA MU KAMMALA WASU TUNI SUN BIYA KUƊINSU BOOK 2 SUNA ZAUNE A PAID GROUP DA ZARAR MUN DATSE ZA SU CIGABA DA SAMUN LITTAFIN HAR ƘARSHE. IDAN KEMA KINA SO ZA KI IYA BIYAN 500 KACAL DON JIN TIRKA-TIKRA DA CAKWAKIYAR DA ZA MU NUTSA A WANNAN LITTAFI NA ƘAZAMIN MIJI,*
*BAN CE NA IYA BA, BAN CE NA ƘWARE BA, NI DAI TAKEN ALƘALAMINA KAƊAI NA SANI WATO ALƘALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME*
*ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA **** [5/5, 6:39 PM] Mom mashkr & Afrah: ***
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *****