Labari mai cike da soyayya, ƙalubale, al,ajabi
PAGE 18
*END OF BOOK 1*
*YAYA SULE*
Saurin saita kansa ya yi daga duniyar rashin gaskiyar da ya bayyana daga gare shi, ɓaro-ɓaro yana sakin wani murmushi ya ce
"Kai typin error ma bai yj ba, wai fa Abokiyata zan rubuta, shi ne na rubuta abokina" Ya faɗa yana kafe Salaha da idanu don ganin yadda za ta ɗauki maganar. Shiru ta ɗan yi tana nazartar maganar kafin ta ce
"Kai dama abokiya kake son saka mini, dama wani saurayin ƙawata ne suna hira sai ta karɓi wayarsa ta kira shi da wayarta, a take sunan GARZALI ya bayyana ɓaro-ɓaro, to da ta bani labari shi ne ni ma na ce zan gwada shi ne na ga ni kuma ABOKINA aka yi saving" Ƙoƙarin saita kansa ya yi ya ce
"Haba Baby ni ya za a yi ma in yi saving numberki da wani suna da ban wataƙila shi ma wancan saurayin ƙawar taki ko yana da aure ne, ba ya so matarsa ta gani... Tun kan ya kai ƙarshen maganar ta yi saurin katse shi da faɗin
"Kenan maza masu aure ne suke yin haka?" Da sauri ya ce
"Ba haka bane yawanci dai an fi samun hakan" Baki ta taɓe ta ce
"Ni fa shi ya sa kwata-kwata namiji mai mata ba ya birgeni" Wani yawu ya haɗiye sannan ya ce
"Ai dama ku mata bakwa son kishiya" Kallonsa ta yi ta ce
"Yo mai za a yi da auren mijin wata?" Yana ƙoƙarin danne abin da ya ji ya ce
"Kenan za ki iya bari a auri naki mijin? Na wata ne ba za ki bari ki aura ba... Ranta a ɓace ta ce
"Ka ga Sule ni fa ba na son irin wannan wasan, idan na shiga gidanka babu wacce za ta shigo" Galala yake kallonta a zuciyarsa ya ce
'Akwai cakwakiya, tabbas iska tana yawo da mai kayan kara, wannan ai shi ake nufi da rana zafi inuwa ƙuna' A fili kuma ya ce
"Ai babu ma wacce ta isa ta shigo" Daga haka suka cigaba da hirar soyayyarsu.
Soyayya ta cigaba da wakana babu kama hannun yaro, a inda Amina duk inda ta ji wata ƙawa ko da a ce ƙawar-ƙawarta ce mijin zai ƙara aure sai ta je ta ga ƙwaƙwaf, shi kuma Yaya Sule sai ya iya takunsa yanzu duk lokacin da zai shigo gidan sai ya sanya wayarsa airplane mode domin ya gwammace kar kiran kowa ya shigo wayarsa a kan rigimar Amina. Ai kuwa hakan da ya yi ba ƙaramin shakku ya cire mata ba, saboda yanzu ganin babu wani mai suna namiji da yake kiransa sai abin ya daina ɗarsa mata zarginsa, a inda shi kuma yake cin karensa babu babbaka.
A ɓangaren Salaha kuwa ko da ta masa ƙorafin ta nemi wayarsa bata samu ba, sai ya ce yanzu bai san mai ya sa idan ba waje ya fito ba, sai network ɗin wayarsa yake ɗaukewa, da hakan ya kuɓuta daga nata ƙotafi.
A ranar da ya samu Baba da maganar cewa, yana son ya ƙara aure, Baban farinciki ya yi, tun da shi al'adar Baba babu ruwansa da hana ɗansa ƙarin aure matsawar ɗan yana da halin riƙe matan nasa, domin a ganinsa hana ɗa ƙara aure tamar tauye masa haƙƙi ne, kuma bayan hakan halal ne kuma dai a nasa ganin hana hanzari a kan ƙara auren zai iya jefa yaron a halaka, sai dai abu ɗaya ne zai sanar da kai shi ne ka yi adalci.
Umma da ta ji hakan ba ƙaramin ranta ne ya ɓaci ba, a nata ganin ita indai namiji ya samu mace ta gari suna zaune lafiya ai ba a bar shi ya ƙara aure ba, tun da wani auren ƙarinsa fitina zai zama tun da duk namijin da ya haɗa mace sama da ɗaya to tabbas dole ya fuskanci ƙalubale, idan kuwa ya haɗu da mata mararsa imani da tsoron Allah, a nan kowacce saboda kishi za ta baje hajarta gaban malamai da bokaye shikenan fa, sai ka ga ya koma wani sha ka tafi, kowacce tana ƙoƙarin ta maido da hankalinsa kanta ta zama ita ce tauraruwa kuma ta sha gaban abokiyar zamanta a wajen miji, daga haka sai ya koma kamar wani zararre saboda an rikita masa ƙwaƙwalwa.
Baba ne ya dakatar da Umma a kan maganar, kamar yadda ya taka mata birki lokacin da Aminu ya zo da nasa batun ƙara auren, har yana nuna mata cewa Aminu ma shi ne ƙarami kuma bai daɗe da yin auren fari ba ya ƙara aure, sannan yanzu zai yi ta uku, bare kuma Sule da dake shi ne babba kuma har yana da yara biyu, don shi a tsarin Baba ko rana ɗaya ka ce za ka auri mace biyu ba zai hanaka ba.
Addu'a Umma ta yi da fatan zaman lafiya, wannan ya sanya Baba ya ce
"Haka ya dace iyaye su dawwama wajen yi wa ƴaƴansu fatan alkairi, a duk abin da suka sanya gaba su basu ƙwarin gwiwa, matsawar bai saɓawa Allah ba, duk abin da Allah ya halatta bai kamata a tauyewa wani ba" Ya faɗa yana kallonta, nuna masa ta yi ta gamsu da hakan, saboda ta lura Baba gani yake kamar don tana mace ne kishi ne yake sakawa take nuna rashin amincewarta idan yaran za su ƙara aure.
A nan Baba ya ya ce za su je nema masa auren, bayan ya gabatar musu da iyayen da unguwar su yarinya, sai Baban ya ce da zarar ya gama bincika wace ce yarinyar da nagartarta da ta iyayenta za su nema masa aurenta. Cikin wasa ma Baban ya kalli Yaya Sule ya ce
"Saura Malam Shafi'u kuma, tun da na san matsawar ya ƙyalla ido ya ganku da matan shi ma zai ce zai ƙara" Gabaɗaya suka yi dariya har Umma daga nan ya musu sallama ya tafi, bayan ya bayyanawa Umma a kan cewa yana son komai ya kasance a ɓoye, da ta tuhume shi ma a kan dalilin da zai ɓoyewa matarsa zai ƙara auren, sai ya fito mata da manufa da halayyar Aminar a kan kishiya, jin hujjojinsa ya sanya iyayen suka amince tun da Baba ya ce ita fitina kwantar da ita ake yi, musamman ma da Yaya Sulen ya sanar da su ba a gida ɗaya zai haɗa su ba, haya zai kamawa Salahar kafin Allah ya hore masa in yana da halin gina babban gida sai su tare.
Sun gansu kuma sun amince.
Tun da Baba ya yi bincike ya gano gidan su Salaha ƴan mutunci ne da dattako ga tarbiya, sai ya yi farinciki a inda aka je neman auren Yaya Sulen aka sanya daidai da ranar na Aminu, kasancewar ɓangaren amarya sun gama shirye -shirye.
Kwanaki suka shuɗe, suka rikiɗe suka zama satika, inda satika suka zama watanni, har ya rage saura sati biyu a ɗaura auren Yaya Sule, a inda har lokacin Amina bata da labari, don ko Sumayya bata faɗa mata ba, tun da Yaya Shafi'u ya gargaɗe ta a kan cewa ba a so ta sani, ita ma kuwa sai ta ja nata bakin ta yi shiru, idan Amina ta je wani bikin dannar ƙirji ta dawo tana ɗaga kai tana murna da nuna jin daɗin na yadda ta ga uwar gidan da ta je dannar ƙirjin cikin damuwa, sai ta zo tana bada labari tana dariya, Sumayya a zuciyarta ta ce
'Ke ma taki tana tafe, wannan shi ake kira rashin sani ya fi dare duhu'
Gidan da Yaya Sule ya kama ciki da falo ne, sai ɗaki ɗaya da bayi a ciki akwai wani a waje sai kuma kicin, irin gidan da ake yi wa laƙabi da gidan mace ɗaya.
Salaha har yau Sule bai sanar da ita yana da mata ba, daga ya yi yunƙurin faɗa mata, sai ya fahimci za ta iya fasa aurensa, su kuma su Baba sun ɗauka ya sanar da ita shinya sa ma ko da suka je neman auren basu faɗa musu ba. Tun da a nasu ganin duk inda aka yi soyyayya har ta kai ga an amincewa juna za a yi aure haƙiƙa an sanar da komai har hakan ya sanya yarda da amincewa na ƙulla auratayyar.
Ana saura sati ɗaya biki, lokacin har su Saddiqa sun tashi daga gidan, Yaya Sule ya shigo da wasu manyan shaddodi da ya ɗinka, set biyar ne, dama a satin Amina ta faɗa masa za ta je wani bikin dannar ƙirjin wata ƙawar, ƙawarta, tana faɗa masa ma bikin na yi ne don su Yusuf ma da Albani gjdansu za ta kai su, wannan dalilin ne ya sanya ya haɗu da wasu shaddodi guda biyu ɗinkakku da less ɗinkakke, duk shi ya bada aka ɗinka, Yusuf kala biyu Albani ma kala biyu.
Lokacin da ya shigo bai san mai ya sa ba, da ta amsa masa sallamar sai ya ji gabansa ya faɗi kawai sai yake ganin kamar za ta hango jirginsa, amma duba da yadda ya gama tsara maganar da zai faɗa mata sai ya ji ɗan dama-dama.
"To fa yau kuma Abban Yusuf ledoji riƙi-riƙe haka mai muka samu" Ta ce tana linke kayan yaran da ta kwaso daga shanya. Ƴar dariyar ƙarfin hali ya yi gabansa don faɗuwa yake amma haka ya dake ya ce
"Ke dai bari cikin wasu kuɗaɗe da na samu, na mana ɗinkuna, kin san satin nan muna da bikin abokinmu, ga kuma ɗaurin auren Aminu, kuma ke ma na ji kin ce za ku yi bikin dannar ƙirji" Ya faɗa lokacin da ya samu waje ya zauna don tun kan ya zauna ne suke wannan maganar. Kayan ta ajiye ta fasa linkin ta ce
"Inyeee lallai shagali wan duna, gaskiya ka faranta mini, don dama ina son yin shigar kece raini yadda zan nunawa duk masu kishiya ni matar mijin mace ɗaya ce" Ta ce tana matsowa wajenta. Yadda ya ga tana rawar kai sai da dariya ta kusa kufce masa don har ya hango dirama da bidirin da za ta yi in ta ji shi ma auren zai yi, ya san tabbas har ƙaramar hauka sai ta yi. Cewa ya yi
"Ai dama na san za ki yi farinciki, ni ma yadda za mu yi ta shige sa fice shi ya sa na yi ɗinkunan" Tana ɗaya leshin ta ce
"Kai amma leshin nan ya tafi da ni wallahi, amma mai ɗinkina ka ba ya ɗinka mini ko?" Amsa mata ya yi da eh kafin ya ta ce
"Kai amma naka ma sun yi kyau, na yaran ma haka, bari na zaɓa maka wanda za ka saka ranar dinner da kuma ɗaurin aure" Ta faɗa tana duba kyan kayan har ta hango yadda za su masa kyau ta ce
"Dan Allah Abban Yusuf kar ka kalli kowacce mace a wajen bikin nan, kuma kar ka shiga hoton abokai in dai da mata a ciki, ban amince ba, sannan kake sunkuyar da kai in ka ga mata za su wuce" Cikin zolaya ya ce
"Ke kuma da za ki je naki bikin ƙawayen waye ya saka miki dokar kallon maza?" Ƴar dariya ta yi ta ce
"Ai ni duk mata ne" Dariyar shi ma ya yi ya ce
"Mu ma duk mazan ne" Su duka suka yi dariya, haka ta zauna ta ware kayan nasa tana ta yabawa da kyawun su, ta ɗauki nata da na yaran shi ma ya ɗauki nasa, har wata ajiyar zuciya ya sauke ganin bata zargi komai ba.
Ranar alhamis haka ya saci jiki ya je wajen ƙauyawan da su Salaha suka shirya, har aka je ka yi hotuna aka tashi ya dawo bata fahimci komai ba, tun da ya ce mata suna hidimar bikin abokin ne ita kuma da yake dama shirme ne da kishin kawai a ranta bata damu da mijin ba, hakan ya sa bata zargi wani abu ba.
Ranar juma'a da ya kasance ranar kamu, tun wajen ƙarfe goma ta shirya ta ɗauki yaran a cewarta, wai gidansu za ta kai yaran, sai a lokacin ma take ce masa ta je za a yi wa wata ƙawarsu kishiya, gidan su Saddiqa kuma sai ranar ɗaurin aure za ta je musu, tana son ta je ta jajanta mata in ta fita, kuma daga gidansu za su wuce gidan wacce za a yi wa kishiyar saboda aikin abin da za a raba gobe ɗaurin aure. Shi ma da yake dama haka yake so ta kama gabanta sai ya amince har da bata kuɗi masu kauri, duk da wani ɓangaren yana jin tausayinta a ransa amma in ya yi duba da cewa, laifinta ne zai saka shi ƙara aure, yadda ya rasa wasu abubuwan da ya faɗa halaka gwara ya yi aurensa, sannan yana ganin ma hakan izna ne a gare ta, da bata da aiki sai bibiyar gidan wanda za a yi wa kishiya ko da basu da wata makusanciyar alaka, kawai don ta je ta kashe ƙwarƙwatar idonta.
Da yamma lokacin da ya yi wanka ya shirya, abokansa suna ta kiransa a kan cewa suna jiransa domin tafiya wajen kamu, ga amarya ma tana ta doka masa kira a kan cewa su zo a tafi wajen kamun don tuni mutane sun kun ƙagu a tafi saboda wajen kamu ya gama kankama, jere kuwa dama tun ranar laraba suka je suka yi.
Fitowar da ya yi yana cikin rufe ƙofa ya ji, an saki wata uwar guɗa, gabansa ne ya yanke ya faɗi yana tunanin waye kuma zai saka shi a matsala, duk da ya san Amina bata nan amma dai guɗa ta hautsina masa ciki yana waiwayowa ya ga Sumayya ce sanye cikin wani koran leshi mai jajayen fulawoyi an sha uban jambaki, tana riƙe da hannun Ruma. Sai danya ɗan waiwaya ya ga babu kowa.
"Irin wannan guɗa haka kamar za ki cire hanci" Ya faɗa cikin wasa. Dariya ta yi ta ce
"Ango ka sha ƙamshi, mijin mace biyu ka fi mai mace ɗaya, mai mace ɗaya ya fi gwauro" Ta ce tana dariya. Shi ma dariyar ya yi yana sauri ya juya ya fita tana cewa a gaishe mata da amarya.
Sumayya ta shiga tunano ranar da za su je gidan Ummar Aminu su gaishe ta, da ta biyawa Zulaiha don kafin su bar gidan ƙawance ya ɗinke a tsakaninsu, lura da ta yi ita Saddiqa bata iya gulma ba kuma dai ta ga kamar Saddiqar bata son take shigar mata ɗaki, kuma ita ma Saddiqar ba zuwa ɓangaren Sumayyar take yi ba sai da dalili, abin da ta fahimta kamar dai Saddiqa tana gudunta ne saboda tsantsanin ƙazantarta hakan ya sa yanzu sai suka haɗe kai da Zulaiha amma ba wai ta daina kulata ne bane kwata-kwata.
ta tuno lokacin da ta shiga ɗakin Zulaiha ta nufa ta shiga da sallama, aka amsa mata, tana shiga ɗakin Zulaiha ta tashi da sauri bakin nan fal cike da yawun da ya taru a bakin, dama a hakan ta ɗaga bakin dama gudun kar yawun ya zubo ta amsa sallamar. Banɗakin ta shiga ta tofar ta dawo tana ɗan kiran sunan Ruma ta koma ta zauna, Sumayya ta kalle ta ta ce
"To ke baki shirya ba mu wuce gidan Ummar" Ɗan yatsina fuska ta yi ta ce
"Yanzu zan saka kayana" Kallon ƙafarta Sumayya ta yi ta ga furu-furu kamar ta yi tsere a sahara ta ce
"Yau ɗaya dai ki mulke ƙafar nan da mai kar mu je ake mana kallon ɗaya saura kwata" Kallonta ta yi ta ce
"Shiga zan yi ai in wanke ƙafafu da fuska da hannuna, sai na shafa mai ai dama ni ina ni ina watsawa jikina ruwa, taɓ ni na yi sati ma ban yi wani abu wanka ba, in kinga ruwa ya taɓa jikina to alwalar sallah ce, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, dama can bana ƙaunar wanka kuma yanzu sai abin ya haɗu da cikin nan da na samu sai in ji babu abin da yake saka ni sai ƙyamar wanka" Dariya Sumayya ta yi ta ce
"Dama fa wahala da rai ne wanka, ni yau kwanana tara ban yi ba wallahi Shafi'u har ya gaji da mita ya zuba mini ido yo dama wankan dai na tsarki ne aka fiya yi, yanzu kuwa ya tsiri wani hali in zai kusance ni sai ya ce sai na yi wanka na wanke baki in na ƙi sai ya haƙura har falo ya ƙaura saboda ba ya son haɗa makwanci da ni, ni kuwa na ce ta fi nono fari gaba ta kaini gobarar titi, bare yanzu da nake fashin sallah ma kin ga ba zai wani zo neman buƙtarsa ba" Baki ta taɓe Zulaiha ta yi tsaki ta ce
"Rabu da gulmammu shi ma wannan sarkin ƴan rainin wayon Aminu, sai yake cewa wai in watsa ruwa ko ba zan saka sabulu ba ., ni kuwa in ce ya daɗe bai ga wanka ba, don ko sabulan kayan lefe na na saka na datse da mukulli na ɓoye mukullin, sai rai ya kai in na sauka lafiya, nake mulkawa in rabu da ƙarnin jego" Tana faɗar haka suka kwashe da dariya, ta shiga bayin ta yi wankin jiki, tana cikin wankewa ta ji wani hamami daga bakinta wanda ita kanta sai da ta ɗan runtse ido, hakan ya sanya ta lakuci makilin a yatsanta ta ɗan goga ta kurkure bakin ta fito, mai ta shafa ta saka atamfa riga da zani ta yafa mayafi suka fito. Da wannan tunanin ta bar gidan.
A ɓangaren Amina tun da ta shirya da yamna ta nufi gidan ƙawar tata, wacce ake yi wa ƙawar kishiya, haka suka wuce don uwar gidan tana ta musu waya a kan su iyi sauri saboda hall ɗin da ake kamun amaryar mijin za su je, don za su je su rawa su yi liƙi su nuna ko a kwalar rigarsu, dama kuma da sanin mijin uwar gidan za ta je.
Shi ma gudun fitina ya amince kuma da yake lallaɓata yake a rabu lafiya. Mota biyu suka cika da ƙawayensu, suna ta hira da zage-zage suna tsinewa maza wata ta ce
"Ai mazan ƴan buhun uba ne, sai sun hango wata za su aura su isheka da cewa ƙaddara ce" Wata kuma ta ce
"Ai ba za ki gane namiji munafuki ne ba sai ya ɗirka miki kishiya, shikenan fa sai ya shiga raina miki wayo, a wajenki ya nuna ke ce a gaba ita ma a nata wajen hakan ce za ta faru ai maza munafukan mata ne" Buɗar bakin Amian cikin cika baki ta ce
"Ai ni Allah ya taimake ni, kuma na taimaki kaina, na nunawa mijina babu ni babu zama da wata, shi ma kuma ya amince da hakan, yanzu ko sha'war kallon mace na ya yi bare a kai ga soyayya" Wacce ake yi wa kishiyar ce ta ce
"Raba kanki da namiji wallahi duk ƙarya ce, kawai suna raina mana wayo ne, nima nawan ba da haka ya fara ba, ban san da maganar auren ba sai da aka saka rana, shi ma auren ya rage sati uku" Kallonta Amina ta yi ta ce
"Naki mijin da ban nawa da ban, yo ni aka mini haka kuma ai sai gawata!" Uwar gidan ta ce
"Ko mushe za ki yi namiji babu ruwansa, in ma bai haɗa miki da saki ba in ya ga za ki tada masa hankali... Katse ta Amina ta yi da faɗin
"Ya isa wasa ya yi wasa ban da, tsikarin uwar miji"Da haka suka ƙaraso wajen da za a yi kamun, wurin guda biyi ne a jere kuma dama sun lura ana ta shiga kowanne kuma ba a buƙatar kowane get pass.
Da suka rasa wanne ne nasun, sai suka fito suka bi ayarin wasu ƴan mata, suna shiga ashe wajen kamun su Yaya Sule ne amma ango da amarya basu riga da sun iso ba, wajen dai an shriya komai gwanin sha,awa. Ana cikin wanna halin wayar uwar gidan ta yi ƙara, mijin ne yake sanar mata cewa ga sunan wajen idan sun zo, nan suka gane ba inda suma shiga bane suka fito domin zuwa ɗayan.
A daidai nan ne motoci suka zo reras, da alama motocin amarya da ango ne da kuma ayarinsu, amma dai mamallakan hall ɗin da su Amina suka shiga. Tun da a daidai wajen suka tsaya.
Amin tana riƙe da hannun ƙawarta, kamar an ce ta kalli cikin ɗaya daga cikin jerarrun motocin amarya da angon da suka tsaya a abin da ta gani ne ya hautsina hanjin cikinta, wanda ya so zautar da ita, jikinta ya kama rawa tamkar mazari cikin karkarwa baki ta shiga ƙoƙarin haɗa wasu haruffa....
*AMINU*
Ya yi gyara murya yana ƙara dakewa don kar su gane yana ɗan fargabar gabatar musu da ƙudurinsa, ya fara magana yana cewa
"Dama na tara ku ne domin in sanar da ku cewa, na kama mana wani gidan haya, kafin in samu in yi ginina in koma gidan kaina" Wani shu'umin murmushi ne ya suɓucewa Zulaiha jin za a sauya musu gida tana fatan dai can ba ɗaki ɗai-ɗai bane kamar wannan, don dama tana tunanin yin taron suna a gidan idan ta haihu, to yanzu faɗuwa ta zo daidai da zama. Saddiqa kuma bata ji komai ba a kan maganarsa don ta san ruwa dai ba ya tsami banza. Bai jira ta cewarsu ba ya ɗora da faɗin
"Ɓangare uku ne a gidan, kowacce tana da ciki da falo fa banɗaki, sannan abu na gaba ina sanar da ku cewa zan ƙara aure nan da sati uku... Dididimmm gabansu ya faɗi amma dai Zulaiha ta fi shiga ruɗani don Saddiqa dannewa ta yi tare da majewa duk da abin ya ɗaure mata kai. Zulaiha bata san lokacin da ta ganta a tsaye ba ranta yana mata ƙuna, Saddiqa kuwa wani shu'umin murmushi ta saki irin na an zo wajen, cikin hargagi Zulaiha ta shiga faɗin
"Au me? Aure fa ka ce, mafarki kake ko a falke kake, to idan bacci kake ka falka daga nannauyan baccin da kake don bani da kishiya" Ta faɗa tana tada jijiyoyin wuya kamar za ta kai masa masa duka. Kallon baki da hankali ya mata ya ce
"Kar ki nemi ki mini rashin kunya, dama mun yi da ke ba zan auri wata ba bayan ke? To idan mun yi ma na janye bare kuma ni babu wacce na taɓa yi wa alƙawarin ba zan mata kishiya ba, don haka ki shirya kishi da ƙabila ma kuwa" Saddiqa jin ya ce ƙabila sai da ta ƙanƙance ido tana mamakin wani sabon salo, Zulaiha kuwa kuka ta fashe tana mai yin kukan kura ta yi kan Aminu, wanda ganin haka ya miƙe tsaye yana taka mata birki da faɗin
"Kar ki fara haukar kishi fa, don in aika ki gida zuwa wani lokaci ba abin mamaki bane a wajena" Cike da jin haushinsa ta ce
"Wannan ai wulaƙanci ne wato an ci moriyar ganga za a yada korenta, daga yin auren har za a fara taryata da kishiya bayan wacce na tarar a gidan" Ta faɗa tana huci. Kallon sakarya ya mata ya ce
"Ita wacce kika tarar ba mutum bace, ko ita bata yi magana ba sai ke, ko ke kaɗai ce matata, to aure babu fashi ki yi duk abin da za ki yi" Kallonsu Saddiqa ta yi ta taɓe baki ita su duka ma tsantsaninsu take ji, ta rasa ma mai ya sa Zulaihar take wannan tsantsar kishin, iya wani lokacin idan ta tsaya ta ƙarewa Aminu kallo sai ta rasa abin so a jikinsa ko abin kishi, don yanzu ta fi karkatar da lamarin aurenta da shi a matsayin ƙaddara. Sai dai ita Zulaiha kishinsa take haiƙan, ko don ita ɗin ma ƙazamar ce oho, ita yanzu ai sallama musu Aminu za ta yi su jiƙa su sha ita yanzu hankalinta ya fi karkata ga yadda za ta ba ƴarta tarbiya. Zulaiha ce ta ce
"Ai ita don ba ita za a yi wa kishiya ba, ni za a yi wa ai ita ni ce kishiyar ta wacce za a auro yanzu kuma kishiyata ce" Tsaki ya ja ya ce
"Ke kika sani, in ma mene ne ita ma haka ta jure, ke ma ba zai gagare ki ba ita da har kwana bakwai na ƙara miki daga cikin kwanakin bakinta, ashe babu daɗi... Jin hakan sai Zulaiha ta harzuƙa tana faɗin
"In ka isa ka ƙarawa amaryar da za ka auro kwanakina shegiya uwata ta haifeni, na rantse da Allah uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho... Saddiqa ganin abin nasu yana neman wuce makaɗi da rawa ta kalli Aminun cikin sanyin murya ta ce
"Ni dai ina maka fatan alkairi, Allah sa a yi a sa'a amma don Allah ku ita mini daga ɗaki na gaji da jin wannan hayaniyar" Zulaiha jin wannan furucin ranta ya ƙara ɓaci ta harzuƙa ta ce
"Wato ga dabbobi suna faɗa ko, dama ai gajiya za ki yi da hayaniya tun da daɗi kike ji ba ke za a ƙarowa ba" Ko kallo Zulaiha bata ishi Saddiqa ba, ta koma kujera ta zauna ta harɗe ƙafafu, wannan abin ya yi wa Zulaiha ciwo, don ta so Saddiqa ta biya ta ta sauke fushinta a kanta, amma Aminu daɗi ya ji don haka sai ya fara bubbuɗawa ya fara tafiya da niyyar barin ɗakin, Zulaiha taku ɗaya biyu ta yi ta damƙo wuyan rigarsa ta shaƙe shi, yana ta faman ta saka amma ta ƙi dakawa wai sai ya fasa aure ai kuwa ya ɗaga hannu ya kwashe ta da wani gigitaccen marin da ta sakar masa wuyan da ta shaƙe babu shiri, tana sakinsa ya gyara rigarsa ya fita daga ɗakin, ita kuma ta buɗe baki tana sheƙa kuka, tamkar wacce aka yi wa mutuwa har da su Allah ya isa take ta faman yi.
Saddiqa ganin abin babu tsari, sai ta kama hannunta za ta fitar da ita daga ɗakin don hamamin da suka sanyawa ɗakin ya haifar mata da ciwon kai, wani irin cisge hannunta Zulaiha ta yi tana aikawa Saddiqa mugun kallo. Dariya ma abin ya ba Saddiqa ta kalle ta ta ce
"Shi fa rashin mutunci da kike gani biki ne, idan aka maka ramawa kake, amma ni bani da lokacin ramawa sai dai in ce ki je ki sha ruwan sanyi, amma ki saka a ranki auren Aminu babu fashi gwara ki kwantar da hankalinki ko don abin cikin ki" Harara ta aika mata ta ce
"An ƙi a kwantar ɗin, kuma da kika ce zai ƙara a bakinki" Tana kaiwa nan fuuuuu ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakinta, nan ta tarar ashe Aminu ficewa ma ya yi daga gidan.
Ta ɗaga hankalinta amma bata sauya zani ba, don sai abin da ya cigaba, Sumayya ta ji babu daɗi jin za a yi wa Zulaiha kishiya don dama yanzu ita ce abokiyarta dama an ce abokin damo guza.
Amina kuwa daɗi ta ji musamman ma da ya kasance an ce za su tashi daga gidan da zama. Shafi'u ya ji babu daɗi jin Saddiqa za si bar gidan, ɗan kwallin ganinta da yake yana jin shauƙi sai ya ji zai yi kewa, amma ya saka a ransa cewa duk runtsi zai ke zuwa gidan da sunan ziyara.
Ana saura kwana goma bikin suka kwashe kayansu suka koma gidan da ya kama haya, Zulaiha har lokacin bata huce ba tana ta hancini tana kuma mugun jin haushin Aminu. Da yake ɗakinsa da ban yanzu bashi da burin da ya wuce Aisha amarya ta tare domin hankalinsa ya yi kanta yana ganin da wuya a samu wata mace da za ta kaita ko ta fi ta don yana ganin ta mallaki komai, duk da ƙiba da kuma faɗin mazaunanta yana ɗan bashi fargaba sai dai ya sanya a ransa shi ba zai ɓata mata rai bama bare wani faɗa ya haɗa su, don ya lura tana da faɗa, gashi abu kaɗan ta hayayyaƙo shi tun kan a je gidan amma dai ya saka a ransa cewa wuyarta ta shigo gidan ne dole zai gyara mata zama kamar yadda ya ladabtar da sauran.
Yau ya kama asabar aka ɗaura auren Aminu da Aisha. Rawar kai wajen Aminu ko kallo su Saddiqa basu ishe shi ba, saboda yana cikin maza masu mayar da macen gida ba kowan kowa ba a lokacin da suka samu wata matar.
A yau ne za ta tare gabaɗaya ɓangaren amarya ya sha jere kasancewar suna neman na kansu daga ita har mahaifiyarta sai aka mata kaya na kece raini tamkar aurenta na fara, kujeru farare, kayan gado farare, labulayen Aisha ma farare ne. Kasancewarta mace mai son farin abu.
Da yake Aminu yana da ɗakinsa amma saboda tsantsani irin na Aisha tun daga gida ta faɗa masa cewa ita fa ba za take kwana a ɗakinsa a kan katifar da yake kwana da matansa ba, saboda tana da ƙyamar ƙazanta hakan ya sa take ganin kawai sharing ɗin katifar ba za ta iya ba, wannan lamari ba ƙaramin daɗaɗawa Aminu rai ya yi ba, don dama wani uban shirgin kayansa ne mararsa wanki da ya tare da tarkacen tsuffin takalmansa wasu ma tun nasa ne na gida, don tun da ya gabya samu turakarsa ya je ɗakinsa na gidansu ya kwaso sauran kayansa, duk ya libge daɗin dabya ji kuwa ba ya so Aisha ta fahimci halayyarsa ta ƙazanta tun da wuri don ya lura irin masu tsaftar nan ne ta innanaha.
Bayan kowa ya watse tana zaune a ɗakinta da ya sha turaren wuta, farar laffaya ce a jikinta mai flower golding, ɗakin fanka tana kaɗa ko ina. Bayan Aminu ya shigo ta ga yana ta ƙoƙarin rufe ƙofa nan take sanar da shi ya bata ga ya haɗasu da sauran matansa ya gabatar da ita ba, Aminu kuwa da ya san Zulaiha tana tamfa sai ya ce wai sai zuwa gobe. Haka dai ta ƙyaleshi
Bayan sun ɗan ci kayan maƙulashe, ta tashi ta buɗe wata jaka ta ɗakko sabon brush tana mai cewa
"Na hutar da kai siyan brush na taho da kayana, saboda ni bana son brush mai laushi na fi son mai tauri" Dariya ya yi abinsa, yana ganinta shiga bayi ta fito sai kawai ta tarar da shi ya yi mata saƙamƙam a kan gado, da mamaki take kallonsa don ita ta saba indai ta ci abu sai ta wanke baki amma shi ta ga ko bakin bai kuskure ba bare ya wanke da brush. Kuma yau da take ganin za a yi amarci dole za a buƙaci yin wani abu, kenan tsaftace ko ina ya zama dole saboda kar ɗaya ya cutar da ɗaya. Cikin ɗan jin nauyi ta muskuta mazaunanta, Aminu yana bin mazaunan da kallo ta ce
"Al'amin ya baka wanke baki ba" Dimmm gaban Aminu ya faɗi jin wata sabuwa da sauri ya shiga dariyar yaƙe yana cewa
"Ai na wanke da safe" Ya faɗa rashin gaskiya yana bayyana a tare da shi, don shi ko brush ma bashi da shi, a halin da ake ciki ma ba zai ce ga ranar da rabonsa da ya wanke baki ba. Bidik ya sauko daga gadon yana cewa
"Bari ki ga in je in yi, saɓi biyar zan yi, ina yi ina maimaitawa" Ya faɗa yana ƴar dariya gabansa yana faɗuwa, ita kuma Aisha tun da ya ce ya wanke da safe sai ta masa ayar tambaya tana ta mamaki.
Yana fita daga ɗakin, ya kama hanyar ɗakin Saddiqa sai dai ta rufe ƙofa amma haka ya buga ta buɗe, tana kallonsa ta ce
"Ango ka sha ƙamshi" Bai amsa ba ya ce
"Brush za ki aramin" Wata dariya ce ta so ƙwace mata amma sai ta dake ta ce
"Brush kuma? Dama ana aron brush?" A ƙufule ya ce
"Idan ba za ki aramin ba shikenan" Tana danne dariyarta a ranta ta ce
'To ni na ara maka brush kuma ai na sallama shi' A fili kuma ta ce
"Akwai wani sabo bana amfani da shi, bari na baka" Cike da murna ya washe baki, tana miƙo masa har da maikilin ya shiga saka mata albarka, ita dai bata ce komai ba kawai dai tana son ganin diramar auren ƙabila da Aminu.
Buta ya je ya cika ya tafi bayin tsakar gidan, sai da ya cika kan brush ɗin taf da makikilin, ya shiga wankewa, jini bakin ya ringa yi kasancewar bakin ba ya samun wanki. Sai da ya wanke sau biyar don har ya fara jin duk ya karce dadashi duk don ya birge amarya.
Da ya koma ɗakin ya same ta ta sanya kayan bacci, cikin ganin ta ruɗa shi ya ce
"Amarya ta ango" Yar dariya ta yi don har lokacin tana cike da tambayar dalilin da ya sanya tun da ya wanke baki da safe bai sake ba. Ta ce
"Na'am angona na biyu, ni ai na san daga kai na rufe wani namijin, dama can mijina na farko wanka yake yi sau ɗaya a rana, wannan ne babban dalilin da ya sanya muka rabu, ni duk inda ƙazanta take bana son in raɓe ta" Suuuttt wata tusa marar ƙara ta kufcewa Aminu lokaci guda ya haɗa zufa, murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce
"Amma wannan an yi ƙazami" Yana tuna shi da sai ya rufa sati jikinsa bai ga ruwa ba, ko jikin nasa ya ga ruwa to ba za a samu sabulu ba, to an rabu da mai wanka sau ɗaya ina ga shi, dariya ta ce
"Kai ma ka faɗa" Daga haka sai suka lula duniyar ma'aurata, tun daga fara ɗan wasanni kafin a je ga mai ɗungurugum, hannun amarya na dama ya sauka a tsakiyar hamnatar Aminu, inda ta ji lallausar fatarta ta sauka a cikin wani cumus ɗin gashi mai gaushi, idanu ta zaro shi kuwa gogan bai san mai ake yi ba, kafin ta gama mamaki sai ta ji mararsa ta gogu da jikjnta inda nan ma ta ji wani gashi, biyubiyu.
Hankalinta tashe ta shiga damuwa, tana mamakin yaushe mutum zai bar gashi haka a jikinsa, ita tun da ta kai munzalin gashi ya fito mata bata taɓa bari gashi ya kai ko rabin na jikin Aminu da ta ji ba.
Ana sunna tana kukan zuci, zuciyarta tana ƙuna, ta shiga tashin hankali amma dai tana son tabbatar da zarginta.
Da asuba bayan sun yi wanka sun yi alwala, Aminu da yake ƙoƙarin saka wando sai kare jikinsa yake kar amarya ta ga gashin nan, ai kuwa sai gani ya yi amarya tana kallonsa wajen ƙasa-ƙasa a ransa ya ce
'Ai indai baka yin abu ka ce za ka tarka to kuwa sai an samu matsala' Ya faɗa a ransa don yana ta zuci-zucin ya yi aski saboda amarya amma zumuɗi ya mantar da shi.
Amarya kuwa ta shiga kokwanto a kan ango, ta ɗora masa ayar tambaya. Haka suka yi nafila, don ma kar ya ƙara wani laifin sai ya saƙala takalmansa ya ce ya tafi masallaci, don ya lura Aisha ma tana da riƙon addini kamar Saddiqa. Tana masa a dawo lafiya ya tafi, bayan tun da suka tare a gidan ma bai taɓa zuwa masallacin asuba ba.
Ko da ya dawo dai ya lura da sauyi a fuskarta sai ya kasa sukuni, idanu ta ɗaga ta sauke a kan gashinsa wanda tun da fake zuwa wajenta yake ƙaƙaba hula, sai yanzu ta lura gashin ba ya samun gyara. Ganin gari ya ɗan waye suka koma bacci, bayan sun tashi suka sake yin wankan sabulu, wannan karon Aminu bai yi ha'ince ba ya yi wanka saboda yana son cirewa amarya kokwanto don ya lura kamar tana zarginsa ne.
Tun da ta kalli ƙafar Aminu ta ga wani ɓaskara-ɓaskaran faso tamkar ƙazangare zai samu mafaka a ciki, sai ta hau salatina ranta, don ta lura da Aminu bai taɓa zuwa wajenta da normal takalmi ba kullum da kambas yake zuwa, sai ya ce mata wai yana jin daɗin sakawa ashe faso yake ɓoyewa, don ƙafar kamar ta tsoho ko baƙauyen mutum marar gyara haka ta koma.
Bayan sun karya sai ya fita, ta shiga gyara ɗakin, ita abin da ta lura kayan da ya cire na jiya su ya mayar da ya yi wankan, abin da bata sani ba kayan wankinsa suna nan tare banda kayan jikinsa babu wankakke, dama duk masu dama-damar na fitar bikinta ne kuma duk ya saka. Dama ta kai ƙyallyen da suka yi amfani da su banɗaki ta wanke ta shanya, yanzu kuma tana son sauya zanin gadon ne, tana shirin cirewa sai ta ga ƙwaro ƙarami yana tafiya, da ta zuba ido da kyau ta gane kwarkwata ce, mamaki ruɗeni suka rufe ta, tana tunanin yadda aka yi kwarkwata ta zo kan gadon tun da ta san bata da ita. Tsantsani ya sa ta cukurkuɗa zanin gadon da rigunan filon da ta cire don kwarkwata uku ta gani raɗo-raɗo sun ƙoshi da jini.
Jikinta har karkarwa yake lokacin da ta fito tsakar gidan, hango Zulaiha tana harararta bai hana ta gaishe da ita ba amma ta ɗauke kai, ganin Saddiqa za ta shiga ɗakinta ta ƙarasa tana gaishe da ita, ta amsa mata cikin sakin fuska, tana ɗan jin nauyi ta ce
"Don Allah in ba damuwa ina son tambayarki, amma mu shiga daga ciki" Dama Saddiqa ta bata suka ɗhiga ɗakin, ta ɗauki Nihal tana mata waya zuwa can cikin muryarta da kake gane ba asalin bahaushiya bace ta ce
"Don Allah ke ce uwar gidan Aminu" Kai Saddiqa ta gyara alamar eh. Cikin sanyin murya ta ce
"Ina son sanin waye mijinki" Da mamaki Saddiqa ta kalleta nan ta shiga faɗawa Saddiqa abin da ta gani a kan gadonta, murmushi Saddiqa ta yi jin tana haɗata da Allah ta faɗa mata gaskiya, Saddiqa kuwa ganin matarsa ce sai bata ɓoye mata komai ba.
Tsabar karkarwa da hannun Aisha yake sai da Saddiqa ta karɓi Nihal, idanunta yana kawo ruwa ta ce
"Wallahi ba zan juri wannan abin ba, ai ni ba zan ma iya shan ruwa a inda Aminu yake ba, don haka a yau ba sai gobe ba zai sawwaqe mini" Ta faɗa tana share hawaye. Haƙuri Saddiqa ta bata, sai Aisha ta ce
"Ba ina kukan komai bane ina kukan yaudarata da ya yi matsayinsa na ƙazami, amma na miki alƙawarin sai na gyarawa Aminu zama, sai na saita Aminu, sai na zamewa Aminu dodo a gidan nan" Murmushin gefen baki Saddiqa ta yi ta ce
"Aisha kenan, ba za ki iya da Aminu ba, Aminu a ƙazamai ma shi dole a bashi mulki ko sarauta" Baki Aisha ta damƙe da haƙori, fitowa ta yi ta je, ɗakinsa ganin halin da ɗakin yake ciki ya ƙara tada mata hankali, ɗakinta ta ɗau waya ta kira shi.
Dama wajen su Kabiru ya je, don ya ɗan bata waje saboda baƙi, ganin kiranta sai ya ɗauka ko har ta yi kewarsa ne, sai dai jin tana batun zuwa duba mamanrta babu lafiya kuma ta ce kar ya zo yanzu za ta dawo, hakan ya sany Aminu ya mata izini.
Wayarta ta saka a jaka ta ɗauki kuɗi ta saka a jakar.
Napep ta hau ta nufi kasuwa, wajen masu siyar da soson ƙarfe na wanke bayan tukunya irin manyan nan ta je, guda uku ta saya ta kaɓata a waje guda. Ta wuce wajen masu siyar da klin viva manyan nan ta siyo guda huɗu, wajen da ake siyar da aska irin ta wanzamai da suke aski ta wuce ta saya wata mai kaifi ta, ta je wajen masu gugar kaushi ta siyo magogin kaushi, ta hau napep ta koma gida.
Tana shiga ta ajiye ledar a ɗakinta, ɗakinsa ta shiga bayan ta saka safar hannu, kayan Aminu karkaf mararsa wankin nan ta kwaso ta tare su libgi guda a tsakar gidan.
Wani ƙaton baho ta ɗakko sabo, ta cika da ruwa ta buɗe klin viva ta zazzage kusan rabi a ciki, ta kaɗa kumfar, duka kayayyakin da ta siyo ta fito da su ta ajiye a gaban bahon, aska, dutsin gugar kaushi, soson ƙarfe, sai kuma sheba da ta ɗakko a ɗakinta.
Saddiqa ce ta zo ta kalle ta da mamaki ta ce
"Ba dai ke kaɗai za ki wanke wannan kayan wankin ba?" Ta faɗa tana kallonta, yatsina fuska Aisha ta yi cikin hasusarta da bata fita ta ce
"Waye bawansa, ni? Allah sawaƙe, kin ga wannan klin ɗin Aminu ne zai zo yau sai ya wanje kayan nan duka tasss, ya ɗauraye ya shanya, wannan askar kuma wallahi yau sai na tattale wannan gashin kan nasa mai kwarkwata, na mayar da shi tanƙwal (Ƙwal uwar kwabo) Sannan sheba ɗin nan sai na aske masa wannan gashin hammatar da na mararsa, soson ƙarfen nan da shi zan saɓa jikin Aminu sau goma, don yadda yake sati ko fiye da hakan babu wanka na tabbata dauɗa tana nan nannage a fatarsa, sannan ya wanke kaushin wannan na ƙafarsa" Ta faɗa tana riƙe da ƙugu. Tsabar mamaki Saddiqa ta rasa abin cewa, hatta Zulaiha mamakin ƙarfin halin amaryar take don tana window tana ganin komai. Bata jira Saddiqa ta ce wani abu ba ta ɗora da faɗin
"Sai na zamewa Aminu ciwon ido a gidan nan, zai san ya auro gamonsa wallahi, sai na saka Aminu ya ƙyamaci ƙazanta da kansa ba don son ransa ba sai don dole uwar naƙi, Zulaiha ganin abin ba na wasa bane sai ta fito tsakar gida tana son ganin yadda wasan zai fara.
Ɗaki amarya ta koma, wata vest ta sako da wani shegen burgujejen wando tiri kwata, wanda ya bayyana asalin ƙibarta, da wayarta ta fito ta dokawa Aminu kira, Aminu yana surutu ya ga kiran amarya ya ɗauka sai ya tsinci maganarta cikin bada umarni tana cewa
"Ka zo gidan nan yanzun nan ina son ganinka" Zulaiha da Saddiqa suna jin yadda ya dirirce a wayar yana ta ambaton gashin nan zuwa.
Ba a jima ba sai suka ji ƙaran buɗe ƙofa, buguzum-buguzum Aisha ta wuce shi ya bi ta da kallo, kafin ya gama tunanin inda za ta je sai ya ji ta bankama sakata a ƙofar gida sakatar sama da ƙasa. Kamar an ce ya juya ya yi wa idanunsa masauki a kan gabaɗaya kayan da ta ajiye a tsakar gidan, don ganinsu ya bayyana masa dukkan aikin kayan saboda ya fahimta, idanu ya shiga gwalewa ya ɗaga kai ya sauke a kan fuskar Zulaiha wacce da alama dariyar ƙeta ce shimfiɗe a fuskarta, da sauri ya mayar da akalar ganinsa zuwa kan fuskar Saddiqa wacce hatta haƙoranta sun bayyana a dariyarta marar sauti, tun da ta baro Nihal tana bacci, yanzu kallon wasan da za a buga ya rage su ne masu gani.
Ƙaran takun dawowar Aisha shi ya sanya Aminu waigawa, gabansa yana dukan uku-uku.
*A NAN MUKA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 WANDA NA BAKU A FREE, KU NUNA KULAWARKU DA SOYAYYARKU GA MARUBUCIYARKU MAMAN AFRAH, WAJEN SAYAN WANNAN LITTAFIN BOOK 2*
*DA NAIRA 500 KACAL ZA KI MORE KARATUN ƘAZAMIN MIJI HAR ƘARSHE, DON JIN YA ZA TA KAYA, ANYA AMINU ZAI YARDA A YI WANKAN NAN, A WANKE ƘAFA A ASKI MASA GASHIN DA TAKE JI DA SHI, A SANYA SHI YIN WANKIN DOLE, SHIN AISHA BATA ƊAKKO DA ZAFI BA*
*YA CAKWAKIYA ZA TA KASANCE TSAKANIN AMINA DA YAYA SULE GA KUMA SALAHA A GEFE, SHIN GASHI DAI SALAHA BATA SAN YANA DA MATA BA HAKA ITA MA AMINA BATA SAN DA AUREN SALAHA BA*
*ZA A BIYA KUƊIN KARATU 500 TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA ****