Chapter 12
by @nimcyluv
Kamar kodayaushe yara sun cika a dandali suna harkokinsu. Batty dake gefe guda ta kalli Shatu ta ce "Yau ma kika ci abu ba ki bani ba ko Shatu?" Far Shatu ta yi da Idanunta cikin wani irin nishaɗi da jin daɗin yau zata ƙure Batty da take cewa tana gani har hanji. "Batty in manshe ki tambaya?"
Batty ta murmusa ta ce "Ingizo ta ina jinki" Shatu ta ɗan gwame numfashi ta yi ƙasa da kanta kamar me son yin raɗa ta ce "Yau me na ci waɗe mini, idan kin yi daidai ina ba ki abin daɗi walle Allah" Batty ta kalli cikin Shatu sannu a hankali kuma ta fara murmushi domin fura da nono ne Batty tasha sai kwaɗon zogale da tumatur wanda suke cikin har yanzu basu gama narkewa ba. "Kin yi shiru ko ba ki sani bane Batty?" Batty ta girgiza kai a hankali sannan ta ce
"Na sani. Kin sha kindirmo me zafi a jikin nagge, shai aka dama miki fura da wani kindirmon, ɗanɗanon bai gushe a bakinki ba kika ɗauki kwaɗon zogala kika ci da tumatur na gona. Shatu nima ina so ki bani yunwa ina ji, cikina ciwo yake yi mini"
"Laaa....laaaa....laaaa" shine kawai abin da Shatu take iya cewa saboda wani mahaukacin daɗi da ta ji yau ma Batty ta faɗi abin da ta yi kari dashi ta lumshe idanunta ta buɗe su tarwai akan Batty ta ce "Daga yau sunanki bokanya, a dinga ce miki karaba kin ji kyakkyawar Batty?"
Da rashin fahimta Batty ta ce "mene bokanya? Da kuma karaba?"
"Muna da ƴan'uwa a binni, Innata ta taɓa zuwa dani kin san su suna yin kallo a wani abu. Sai aka saka mana wani kallo a ciki na ji ana cewa bokanya da karaba" Shatu ta labarta mata kafin ta muskuta ta ce "Zo kiji" Batty ta ɗan matsa, Shatu ta kara bakinta a kunnen Batty ta ce "Kawai ki dinga bada magani, da yin asiri sai mu tara kuɗi sosai mu siyi nagge da yawa su dinga haihuwa muna samun ƴaƴa" Batty ta kalli Shatu ta ce
"Ina zan samu maganin?"
"Ke muna da ganyayyaki har da su rai ɗore su tunfafiyya. Ki yadda dani Batty zan dinga kawo miki mutane, idan mun samu kuɗi sai mu shiga kasuwar yamma ya kika gani?" Ta yi narai narai da fuska cike da tsoro da rashin gamsuwa. Da tsoro a tattare da ita ta ce "Idan aka gano ni mayya ce fa?" Shatu ta ce "mene mayya kuma? Daga yau sunanki bokanya karaba. Za ki lulluɓa ganye a jikinki, a shafa miki bayan tukunya a fuska ana shigowa sai ki ce "Bokayan karaba tana muku maraba meke tafe dakai ko ke, me kake so mene damuwarka kuma? Hahaha"
Ta ɗora da "Sai ni bokanya karaba me gani har hanji kuma me abin mamaki hahaha" Batty ta sauke ajjiyar zuciya "Amma wannan ya zama sirri tunda mun zama ƙawaye ko? Daga yau zan dinga ce miki mutuniyar"
"Ke kuma masoyiyar" inji Shatu.
"To mu ƙulla kar ki ciki amanata ki sauya ƙawa, kinga daman ni bani da yaya bani da ƙanwa bani da kowa sai Yaaye kuma ta tsane ni ta saka an kore ni daga rugarmu ta Yari don taga Innata ta mutu" kamar wasa sai ta hau kuka wiwi har da majina tana murza ƙafa da yarfe hannunta ta narke gabaɗaya. Shatu ta saki baki tana kallon ta, da yawan mutane idan suna kuka muni suke yi, akasin hakan wani irin kyau Batty ta yi mata tana kuka tana shigar da leɓenta na ƙasa tare da tsotse shi ruf kuma take rufe idanunta, dogwayen gashin idanun da suka kwanta sai su bi fatar idanun su lafe gwanin sha'awa. "Ba za ki ce na yi shiru ba?" Ta yi furucin cikin raunin murya.
"Ki yi shiru masoyiyar"
"Na yi mutuniyar. Ina Ramu?"
"Laa ba kin ce daman hanjinta ciwo yake ba? Tana can ta kwanta lalura abin tausayi ko za ki ke duba ta?" Batty ta girgiza kai "Ki faɗawa Innar Ramu ta kai ta wajan Bokayan karaba zata samu waraka" Shatu ta ce
"To"
"Hawwa fa?"
Wani irin hangame baki Shatu ta yi ta ƙanƙame idanu kafin ta ce "Don ki ji aure za'a yi mata, a kwarkwaɗa aka kamata da Iro yana mata maɗe shine Baffan Hawwa ya ce aure zai yi mata, daman ko a dandali idan Hawwa na rawa Iro ne yake mata manne, to duk wanda yake manne a dandali alama ce ta yana son ka, shine take ta kuka wai tsoro take ji ni kuma na ce bata da wayo dama ni ce za'a yi wa auren kullum na dinga girki da share gida na gyara bukkarmu idan gari ya waye na gaida mijin sai na dawo gidanmu, da sassafe na koma gidan mijin, kuma ya dinga kawo mini tsaraba na dinga cin abinci ina ƙoshi sosai" Batty ta yi shiru tana tunani da nazarin maganar Shatu kafin ta nisa tace
"Idan akai auren a gidanku kake kwana?" Shatu ta ɗan jujjuya taga ba kowa cikin raɗa ta ce "Daga safe zuwa yammaci kana gidan mijin idan almuru ya yi sai ka tafi gidan Baffanku saboda babu kyau zama waje guda da namijin shaiɗan ke shiga tsakani Inji Innarmu sai kiga an yi miki maɗe a yi miki iskar balo ki mutu" Batty ta haɗe fuska
Ta ce "Ce Allah?"
"Na rantse masoyiyar"
"To na yarda mutuniyar"
Shatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta "Muje wajan Innata ta ba ki abinci ki yi kari" ta kama hannun Batty suka nufi gidansu.
*
Tsoron daya gama rikitowa duniyar Iftihal ya gama razanar da ƴar nutsuwar da ta yi mata saura, da kekketa zuciyar data riga ta gama macewa da rauninkan da ƙaddara ta wanzar mata dashi ta haɗaɗɗan rubutun daya samu waje,a inda ba'a rubuta ƙarya na abin da Ubangiji ya wanzar a rayuwar bawa a allon Lauhil Mahfouz. Wannan tsoran ya ɗauke ganinta na wani lokaci kamar yadda wannan tsoran ya saka fitsari sakin kan shi daga cikin mararta, ta jiƙe sharkaf. A firgice ta ce "Na shiga uku....," sai ta kasa ƙarasa maganar saboda wani abu daya tukare mata maƙoshi ko numfashi ta gagara ja da saukewa, hatta iskar dake cikin daƙin a gurɓace take shaƙa, da ɗan ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta lallaɓa tana jan jiki zuwa inda Alhaji Baita yake tsaye ya riƙe ƙugunsa tare da zuba mata ƴan iskan idanunsa masu ɗauke da manufofi da yawa. Tana ƙarasawa inda yake ta haɗe hannayenta biyu alamar neman alfarma, alamar dake nuna ƙasƙanci da karayar zuci ta ce. "Idan na ce ka ji tsoron Allah na san na makara, sai dai an ce fazzakir fa'innal zikira tamfa'ul mu'uminun" Ya kalle ta ya ce "Ka tunatar domin tunatar wa tana amfanar Musulmai" ya ƙare da shafa tsakiyar jikinsa daya kwanta ya zame masa kaya. Ji ta yi ɗan raguwar hope da confidence ɗin da suke rage mata sun yi nasu waje ta kuma neme su ta rasa su. A tsakanin mutuwa da rayuwa bata san a wanne ɓangare ta fi ƙarfi ba a yanzu, tana buƙatar ta rayu saboda Mahaɗinta da kuma Innti sai taurarinta Yaa Jaheed da Yaa Jadid da Babban yaya. Tana buƙatar rayuwa ko zata zama silar shiryuwar Daada, ita kam tana son mahaifinta sosai, so mara algus mara kuma wa'adi, idan ta rayu, za ta yi rayuwa ne da wannan soyayyar ko da bai sauya halinsa ba, idan kuma ta mutu zata mutu ne da begen babu shi a tsaginta a yanzu haka kuma har zuciyarta ta yafe masa dukkan wata musgunawa da ya yi wa rayuwarta. Ta kalli Baita ta ce
"Me kake buƙata a wajena?"
Ya ɗan gwame numfashi da ƙoƙarin sarrafa nutsuwar dake shirin kwance masa yace "ke nake buƙata, ki saki jiki kuma ki tsayar da zuciyarki waje guda. Ki kuma zama jaruma"
Ta ɗan dube shi. "Yes, ni mabuƙaci ne a ƙalla zan iya buƙatarki sau biyar haka a rana"
A kiɗime ta ce "Ba zan iya ba, ban ma san mene buƙatar ba, ba zan jure ba, ba kuma zan iya sakin jikin nawa ba ban ma san me kake nufi da kalamanka ba. Duk abin da za ka yi Bisimillah na san Ubangiji yana kallo yana kuma ji ya kuma fini sanin abubuwan da suke yawo a zuciyarka. Duk abin da ya same ni ƙaddarata ce, Innti ta ce bawa baya taɓa shige ƙaddararsa, faman ƙaddarallahu haƙƙa ƙadirihi. Ba wani abu da zai samu bawa face abin da Ubangiji ya hukunta masa" tana faɗin hakan ta yi ƙasa da kanta ilahirin jikinta rawa da ɓari yake yi kamar an jona mata hutar lantarki. Idan abin da Iftihal take ji a yanzu shine daidai bai shige zaucewa da ta yi kamar tunaninta ya yi ƙaura a jikinta, ta amince da ƙudurin Baita, amma zuciyarta ta gaza ɗaukan tashin hankalin da yake neman kunno kai cikin rayuwarta... "Tashi ki cire kayanki"
"Ba zan iya ba" ya buɗe ido sosai. Sai kuma ya ce "Ni ina da hannaye har biyu"
Ganin da gaske kayan yake shirin cire mata ya saka ta riƙe hannunsa a ƙyamace ta shiga girgiza masa kai, "kalle ni" rashin sanin rashin kallon nasa shine fa'ida a gare ta aka yi rashin sa'a ta ɗago ta kalli cikin tsakiyar idanunsa, a hankali komai ya shiga warware wa a kanta jikinta ya saki, komai nata ya tafi ya barta babu abin da ya yi mata saura sai tunaninta da raɗaɗin zuciyarta, Allah take kira da Innti da kuma Anarta, abokiyar haihuwarta wacce suka gama tsara kalar rayuwar da za su yi tare daga kan girma, karatu, cigaban da za su kawowa rayuwarsu.
"Ban san me kake shirin yi mini ba" ta ce da ƙyar Idanunta na tsiyayar da hawaye daga gefen fuskarta, ta ƙarasa buɗe idanun da ya yi mata nauyi a fuskarta, ta dubi yadda ya yi mata tsaye a saman kanta, baƙi ne shi sosai, yana da buɗaɗɗan jiki da kuma ƙaton tumbin da yake fara shaida zuwan shi waje, sai jajayen idanunsa da suke manyan gaske wanda yake rambaɗa musu farin ƙwallin da bata san na menene ba. Dole ta shaida kamannin mutumin daya zama silar rusa duniyarta. Ya gyara tsaiwa yana washe mata bakinsa da faɗin "Ki kwantar da hankalinki, abin da zan miki shine abin da kowacce mace ake mata idan ta girma idan an yi mata aure, budurcinki zan ƙarba saboda kin kwanta mini, dalilin daya saka na saka miliyan ashirin saboda makwaɗaicin ubanki ya faɗa cikin cacar na kuma yi sa'ar gaske ya sakaki ni kuma na yi nasara, daman nasara a jinin Alhji Baita take Ƴan'mata. Sai kuma buri na biyu yi, wanda idan na aikata zan samu biliyoyin kuɗi, wani sirri ne da ko matana basu taɓa sani ba, sai abu kaɗan dana shaidawa matata kuma uwargidana wato Jummai, macace azzalumar gaske, mun haɗu da ita a yawan da nake yi na gari-gari har muka yi aure, tana shan taba, sigari, tana kawalcin mata da niyyar samar musu aikin yi sai a buƙe da safarar su zuwa ƙasar waje, ko kuma ta siyar dasu kamar yadda ake siyar da bayi a zamanin baya, ina yi mata aiki na rufe bakin iyayen yara dama su kan su yaran, duk abin da aka ce musu ba za su taɓa bijirewa ba, iyayen kuma ba za su taɓa neman yaransu ba har abada, idan kin ga sun yi magana to na lahira ne ya dawo"
Ya ɗan murmusa yana durƙusawa daidai kan Iftihal da take kwance kamar gawa saboda sakin da jikinta ya yi babu abin da yake motsi a jikinta sai Idanunta da laɓɓanta, kallon shi kawai take yi da fuskar dake nuna tashin hankalin daya gama mamaye rayuwarta da zuciyar dake ƙuntacce a tsakiyar ƙirjinta. Fat! Fat! Haka zuciyarta ke bugawa, bugun da take jin kamar zata yaye fata bakwai dake lulluɓe da ita ta fito zuwa sarari. Ya miƙa hannu kaɗan ya shafi fuskarta ya ce "Sorry fa. Kina ganina kamar bagidajen ƙauye ko irin mutumin ƙawayen da yake da kuɗi amma babu ilimi?"
"...... haka kike tunani ko? You have to think gaskiya ni da kaina tsoran kaina nake yi"
Ta lumshe idanunta ta buɗe a kan shi. "Yeah; when it comes to money gaskiya bani da imani ne ko kaɗan akan hakan. Na yi niyyar na zauna dake ki dinga bani nishaɗi kina ɗebe mini kewa da hutawa a jikinki, haka nan kike birgeni fa Ƴan'mata. Ranar dana fara ganinki aka shaida mini ko biyu ne nazo na buga ƙasa, kuma ƙasa ta shaida mini naso sauya ƙudirina zuwa kan uhm"
Sai ya ɗan murza goshinta alamar tunani, a hankali ta dinga girgiza kai jikinta ya shiga rawa, idan wani abu ya samu mahaɗinta ba zata iya yafewa kanta ba, duk da cewa basu san wacece babba ba a cikinsu, amma tuni ita ta ɗauki girma, Ana da kanta take cewa
"Haƙurinki dabanne mahaɗita, kece yayata zan iya kallon ki a matsayin Innti a lokacin da babu Innti a kusa dani, ke yayata ce ta"
Ƙoƙarin tashi take ta kasa idanunta na zubar da ruwan hawaye ta ce "Karka taɓa mini Anata, ita ɗin rayuwata ce kar ka...," Ya yi saurin ɗora yatsarsa ɗaya a saman laɓɓanta ya ce "Shhhh, duk yadda nake son abu idan na duba naga taurarina dana mutum bai zo ɗaya ma ina haƙura dashi. Ki kwantar da hankalinki babu ruwana da ita"
Ajjiyar zuciya ta sauke a wahale alamar relief. Ya ɗora da; "Bayan matata Jummai na auri Karime, a kanta kuma na buƙaci zama abin da nake a yanzu, me kuɗi kuma bagidaje kuma hatsabibi sirrin manyan ƴan ƙasar nan. Fulani, ita ce sunan aljanar data aure ni a jerin Jinnul Ashqie na mata, ita ta bani umarnin sai na fara kwanciya da ƴata da take shekara shida a haihuwa, ƴar gidan Karime ce, sunanta Anisa, kaf cikin yarana tafi kowacce kyau ita ce fara kamar ka wanke hannu ka taɓa, tun tana yarinya bata da rigima tana da haƙuri gata da farinjini, na taƙaita miki kaf yarana ba wacce nake so sama da Anisa. Sai dai kin san wani abu?"
Iftifal ta kasa magana sai kallon shi kawai da take yi zuciyarta na rarrabewa. "Anisa na wata shida na yi mata fyaɗe, kuma na tsafa ce ta, ita ce take bani kuɗin da nake dasu a yanzu, har gobe ina kukan rashinta akanta kuma zuciyata taƙeƙashe, yarana duk suka zama kangararru, Jummai ta yi kawalcin mata, Marka babbar ƴata ce, taƙi aure zaman kanta take yi, tana shigowa da duk namijin da ta yi niyya kuma ta fita dashi, ni ne da kaina na gyara mata ɗakin, sai Lamratu tana siyar da wiwi itama bata da kunya ba'a taɓa ta a zauna lafiya kowa ya shiga gonar ta ni da kaina nake saita masa hanya, sai Kasko namiji ne shi. Bari na bar ki haka abubuwan da za ki ji zuwa gaba zai iya sanadin rayuwarki a yanzu, ni kuma ina buƙatarki da kuma aikin da zan yi akan ki"
"Don Allah.....," sai ta kasa magana saboda hawaye da bugun zuciya. "Innti ta ce duk namijin daya kaɗaita na mace tana ɗaukan ciki, duk macen da ta yi ciki kuma tana rasa ƙimarta a idanun Ubangiji da jama'a, ban san me take nufi da kaɗaita ba sai yanzu, don Allah ka tausaya mini ka kashe ni kafin ka ci mutuncina" ta shiga girgiza kai a razane
"Ba zan iya ba, da gaske ba zan iya ba, zuciyata zata iya bugawa idan kaci zarafina. Innti ta ce girma da martabar mace gidan mijinta" Alhaji Baita ya yi shiru yana tunani.
"Nice. Gaskiya Innti ta cika uwa ta gari ta baku biyayya iya iwarta she's a good mother"
"Ka aure ni. Na yarje maka ka aure ni daka aikata ba daidai ba dani, gwara na zama matarka ba zan iya saɓa umarnin Innti na ƙin biyayya ga Daada ba, da tabbas na gudu daga gidan nan. Ina son Daada sosai da sosai wallahi ina matuƙar ƙaunar mahaifina. Wacce ta kashe kanta ta mutu kafura da tuni na raba kaina da wannan duniyar. Don Allah ka aure ni ka ceci martaba da kimar ɗiya mace, ka ceci tarbiyyar Innti Please"
"I can't do it".
Ya jinjina kai "Ba zan iya wani auren ba, wannan sharaɗin Fulani ne da kanta"
Yana faɗin hakan ya yi kanta wani irin gigitaccen ihu ta saka tun bai fara yi mata komai ba, bata da ƙarfi don Allah kuka take tana kiran sunan Allah da Innti da Anarta, dukkan wasu ƴan gidansu sai data kira su, hatta Diyanah da bata da wata alaƙa sai data kira sunanta, jikinta na waia irin rawa da ɓari da kakkarwa saboda tsananin tsoran daya gama raza zuciyarta ta wanzu a gaɓɓan jikinta, ta ƙanƙame jikin da ƙarfi wanda ya saka Baita jan uban tsaki ya ce "Don ƙaniyarki ba za ki buɗe jikinki ba sai kin ɓata mini aiki? Kin san girman aikin da yake gabana ba, idan ba ni ba, babu mai iya yin aikin nan sai an je can kusa da Tajmahar" bata hayyacinta tuni tun kafin ya shiga jikinta firgitar da ta yi ya ɗauke ji da ganinta, bata taɓa tunanin irin wannan yana wanzuwa a tattare da mace da namiji ba sai yau, ita tausayin Anarta take yi, Ubangiji kada ya ƙaddara mata wannan abin. Yin duniya ya yi abin da yake so na shiga jikinta abu ya gagari kundila, sai daya zura yatsarta sai kuma ya yi cak yana nazari. Kafin ya ce "Lalle uwarku Innti ta iya maganin ƴan iska, amma na yi mamaki fa"
Ganin bashi da cikakken lokaci ya miƙe daga kanta ya ɗakko wani hayaƙi ya bunka a ɗakin ya ƙarasu daidai inda take ya kara hayaƙin a al'aurarta wani irin tsuma naman jikinta ya shiga yi, ta zaro harshenta waje ta datse har bata san haƙoranta sun nutsa cikin harshen na sai da jini ya fara fita, azabar hayaƙin ce kuma ta saka ta farfaɗo daga suman da ta yi. Ajjiye hayaƙin gefe ya yi ya sake kwantar da ita kamar matacciyya a wajan, sai daya fara tura yatsarsa jikinta ya ji ta saki ƙara tana zabura sannan ya ce
"Good!" Ya janyo wani jan ƙyalle ya ajjiye a daidai gabanta, ya kalli jan zakarar dake gefe guda me rai sai ɗaga kai yake sama an ɗaure shi da igiya. Sosai da sosai Alhaji Baita yake haɗa zufa, wannan karan ma kasa yi ya yi yaja siririn tsaki ya ɗauki wata reza dake gefe babu tausayi babu imani ya saka rezar a gaban Iftihal ya yaga fatar wajan, wata kururuwa data amsa dukan gidan Iftihal ta saka, a zabure cikin fitar hayyaci ta damƙo wuyan Alhaji Baita ta kafa masa haƙora a wajan tana me kiran sunan Ana da Innti, har tafi kiran sunan Ana ma akan mahaifiyarta daidai nan ta sake wani irin ihu ta datse bakinta numfashinta ya tsaya cak. Wani numfashi Alhaji Baita ya yi yana sakin murmushi da ihu da kururuwa yana kiran sunan Jummai, Allah ya taimaka yaran gidan babu kowa sai matan nasa.
Jini ya zuba akan ƙyallen ya zare, ya miƙa hannunsa ya damƙo zakaran bai jira komai ba ya murɗe wuyan zakaran ya cike ya ajjiye uwar jikin a gefe, ɓare bakin zakaran ya yi ya tara jinin budurcin Iftihal ya zuba a jikinsa, nan take daga kan zakaran har uwar jikin suka ɓace ɓat daga ɗakin, ya samu nutsuwa da gamsuwa ya miƙe ya faɗa kan katifa sai baccin daya rasa tantance na wahala ne ko kuma da farinciki da nutsuwa?
*
Emama dake zaune a tsakar gidan tana juya ruwan shayi daya sha madara da milo ga soyayyiyar doya gefe ta kalli Innti ta ce "Ina ganin masifa da bala'i ni Emama, wai da kika zo mini gida da maraican nan uban me kike so na yi miki bayan kin riƙa da kin gama mini da yaro, ban taɓa sanin ke na haifawa Daada ba billahil azim sai yanzu, ya zama mijin tace baya jin maganar kowa sai taki, yanzu me kike nema? Ci sha, magani suttura duka ya ɗauke muku da yaranki saboda rashin godiyar Ubangiji kike nuna rashin gamsuwa da hakan ko?" Hanna yayar Daada ta ce "Kina fa gani Emama mu da gidan ɗan'uwanmu amma bamu da mutumcin da matar nan za ta yi girki ta kawo mana" Liya da take ƙarama a cikinsu ta kalli Innti a sheƙe kamar kashi ta ce
"Ai wani auren zumuncin sam bai yi ba, banda iyayenki sun rasu ai dana ce musu Allah Ya isa da suka ƙaƙabawa Daada ke"
Innti ta ce "Liya iyayena me suka yi miki? Me na yi muku da zafi ne wai har haka? Shi Daada ya ce ya ɗauke mana buƙatunmu?"
"La'ilaha ilallah kun ji munafuka ko? Kai wasu surukan akwai mugwaye azzalumai, a haka aka auro ki da? Wannan ƙugun a gidan uban wa kika same shi idan ba gidan yayana ba? Akan idanunmu kika dafa ƴar murji"
Idanun Innti ne ya ciko da hawaye ƙirjinta na ɗagawa ta saka hannunta ta dafe ƙirjin ta kasa cewa komai, da ƙyar ta ce "Allah shine shaida, me ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Jikin Yaa Jadid ne ya tashi kuma alamu ya nuna wankin ƙoda yake buƙata, an sace mini kan keken ɗinkina yau da safe na rasa kuɗin dashin jama'a bani da komai hatta abin da za mu kai bakinmu bamu dashi wallahi. Emama don Allah ki taimaka akai yaron nan asibiti na baro shi a cinyar ɗan'uwansa yana ta suma kece kakarsu basu da wani a duniya bayan mahafinsu sai ke. Ki tausaya kada na rasa yarona don Allah" ta fashe da wani irin kuka tana durƙushewa a wajan zuciyarta sai bugawa take yi.
Hanna ta ce "Kan uba an sace kan keke ko dai kin siyar a yawon bin bokaye da mallake Daada? Wai har da kuɗin adashi ma kamar"
Liya ta buƙa tsalle da tafi ta ce "Bala ba a wajanta yake yin adashi bane wai Yaya?"
"A wajanta ne. Har da kuɗinsa kenan?" Cewar Hanna tana riƙe haɓa.
Murya a karye aka ce "Me nake ji haka babu daɗin ji wai arne da yin asuwaki, yaya ne ya akai kuma"
Liya ta juya ta kalli Sukunbiya daya shigo yana yarfe hannunsa da murya a karye ya dire kayan cefanan hannunsa yana faɗin
"Wash ƙirjina, me haihuwar fari a farin shigar shayarwa ta ce wash ƙirjina. Liya ya akai wassafa mini a gajarce do Allah"
Liya ta ce "Bala wai kuɗin adashinku na wajan Innti aka sace kuma ƙarya take yi yawon malamai ta yi da kuɗin wallahi"
"Kuturun uba, da fari Liya wuta balbal da sunan da kika kira ni, idan ba za ki iya cewa Sukunbiya ba ki ce ke. Me nake ji haka wai kwarto ya yi wa uwarsa fyaɗe ya ce me nake jin haka, billahil azim ba zata saɓo ba, ba'a isa a cinye mini kuɗin da nake ganganɗawa zan buɗe wajan cin abinci ba, duk inda suke dole ne a fito dasu ni za'a yaudara? A ci amana" sai ya fito da waya ya kira wata number ana ɗagawa ya ce "Ahhayyyye cas" Daga cikin wayar aka ce "Cas mutuniyar ya aka yi ne?" Muryar Abar ƙauna ce a wayar
"Ki biya ki ɗakko ƴar Beauty tare da polices zuwa gidanmu na gado, ni za'ayi wa hau ni za'a yi wa bariki, ni za'a ciwa kuɗin adashi ina daku a raye a duniya" ya ƙare maganar da yarfar da hannu a gefe can kuma ya saka hannun ya tallafo ƙirji yana karya wuya.
Abar ƙauna ya ce "Ni na rasa ta cewa yaya Sukunbiya wai uwar gulma ta yi cikin shega, ai dangi guda zan haɗo tunda abin na jinsi ɗaya ne" yana faɗin hakan ya kashe waya
Hanna ta ce "Ai nasan abin babu sauƙi dama matuƙar Sukunbiya yazo"
"Wai mayya da kaɓar haihuwa, ban ci nanin ba nanin ba zata cini ba, bikin ƴar aminiyyata za'ayi aka fasa shine zan buɗe restaurant da kuɗin amma matar nan zata kunyatani a idanun duniya" Liya ta saki dry "Kar ka kuskura ka yarda Bala"
Wani irin kallo ya cillawa Liya sai ya je ya ɗakko tsinke ya miƙa mata ya ce "Cire abin da yake miki kama dana namiji a jikina da kike kirana da Bala ba kunya da tsoron Allah" girgiza kai kawai ta yi tai dariya. Juyawa Innti ta yi zata fita ya yi saurin miƙa hannu zai riƙe ta, ta yi saurin ɗaga hannunta ta kwaɗa masa mari ta ce "Mara ta ido fitsararre kawai....," bata ƙarasa maganar ba Hanna ta ɗauke Innti da mari.
*
A nutse ya duba agogon dake maƙale a tsintsiyar hannunsa, yaga lokaci yaja yamma ta kawo kai tun yaushe suke wajan nan? Gashi ko mutum ɗaya ba'a yi wa Interview ba, sai dai a dinga kiran mutanen da aka ga dama. Ya saki siririn tsaki tare da miƙewa ya ƙarasa wajan mutumin ya ce.
"Wai What's going on here? Tun safe muna wajan nan, kune kuka kira mu bawai mu ne muka kawo kan mu ba. Idan yaudara ce abin ai gwara mu sani mu cire rai" wanda yake zaune akan kujera ya juya ya kalli Yaa Sam
"Shine zaka zo kana mana ihu a saman kai saboda rashin kunya? Shi talaka duk inda yake sai ya nuna halinsa ne?" Yaa Sam ya tattare baƙar ƙirarsa ya cure waje guda yana fito da idanunsa waje ya kalli mutumin sosai cikin turanci ya ce "Kuma wannan talakan yasan limit ɗinsa ya kuma iya talaucinsa, yana da zuciyar nema. Gwamnati ta neme mu, ita kuma Gwamnati ta kowa ce, haƙƙinta ne yin abin da take yi, tunda mune muka kafa gwamnatin. Kuma wallahi a shirye nake da shiga rediyo na faɗi irin wulaƙancin da kukai mana. Ai na haddace sunanka tsaf a kaina"
Jin furucin Yaa Sam ya saka mutum miƙa hannunsa ya ce "Have a seat, muga ducoment ɗin naka?" Ya miƙa masa ya shiga dubawa, a hankali ya ɗago kai ya kalli Yaa Sam ganin tun daga kan primary school har University result ɗinsa masu kyau ne, irin wanda ake buƙata. "Ina zuwa"
Ya ce yana miƙewa gefe ya koma ya kira waya yana ɗagawa ya ce "Sir an samu exlty irin ducoment ɗin da kuke so, har bangaren karatun na Accounting. Ka faɗawa wanda ya ce sai siya ya bada 3 millions a cire sunan Haysaam a ɗora na yaronsa, ko kuma ya tafi akan sunan na Haysaam" ya yi jim.
Can ya ce "Sure sir, ok I'll in sha Allah"
Few minutes ya dawo ya kalli Haysaam ya ce "Malam Haysaam, zuwa gobe ka dawo da za'a yi maka takadda na offer later congratulations"
Sak Haysaam ya yi yana kallon mutumin, wani irin hamadala yake yi a zuciyarsa, ashe yana da rabon cin muriyar karatunsa? Ashe iyayensa za su ji daɗi tun suna raye? Ashe zai samu kuɗin da zai kula da Ana? Sai samu kuɗin da zai auri yarinyar da yake mutuwar so da ƙauna kamar numfashin shaƙarsa. Ya zame ya yi sujudur shukràn kana ya tafi yana hamdala.
*
A can rugar Biya a gidan Moddibo, Mado ne kwance jikinsa ya rikice babu yadda yake jikin ya ɗauki zafi rau kamar gaushin wuta saboda zafi, sai sambatu yake yi yana faɗin "Ga kura nan ga doki nan, za su kama ni ga wuta nan tana bini gata nan zata cinye ni" Malamin da aka kira ya girgiza kai yana zubawa Mado dake kwance idanunsa rufe ido, kaya ne a jikinsa irin yadin nan me kyau da aka goge masa jikinsa aka saka masa. Moddibo ya nisa ya ce "Ka gani Malam Horo, ɗazo jikin gwanin sha'awa sanyi ƙalau har aka bashi kindirmo ya ɗan sha amma duba ka gani yadda ya rikice lokaci guda"
Malam Horo ya ce "Sannu Mado, sannu ka ji. Allah yo jam tan" ya faɗa yana taɓa Mado “Malam Hooro, too aljannu’en ngari natti dow ɓandu Mado naa?” Horo ya yi shiru yana kallon Mado da nazari ya kalli yadda yake zabura da surutai marasa ma'ana.
"Sune, abubuwan da yake yi duk sharrin Aljanun ne, za'ayi masa Ruƙiyya idan Allah Ya so za su bar jikinsa. Sannu Mado, Allah yo jam tan" jakar kayansa ya buɗe ya ɗakko wata kwalba me ɗauke da maganin zafi ya ajjiye a gefe, sai dogon carbi irin me guda dubu ɗin nan ya ce "ku riƙe shi da kyau, babu mamaki shaiɗanun jinnu ne ke addabar shi da bibiyar rayuwarsa" Mado ya ƙurawa Malam Horo ido kamar ya buɗe baki ya sace masa bashi da wata iska kar ya yi masa ruƙiyya amma babu bakin magana, suka riƙe shi Malam Horo ya shaƙa masa man zafin cak numfashin Mado ya tsaya na wani lokaci, saboda yadda maganin ya ratsa ƙwaƙwalwarsa ya gigita mata lissafi, jikin ya ƙara birkicewa ya fara fusge fusge da wani irin numfashi yana samƙamewa. Moddibo ya riƙe shi gam ya ce "Sai kun tafi inda kuka fito, ku bar jikin bawan Allah ina faɗe muku tun tuni amma kun manshe ni ɗanbaza ko? Ga Malam Horo nan gare ku ai" tsananin azaba ta saka Mado riƙo hannun Moddibo da kyau yana fidda wani irin numfarfashi, Malam Horo ya saka hannunsa a goshin Mado ya danne ya fara addu'a yana tofa masa, ba'ayi minti biyu da danne goshin ba, Mado ya yi wata fusga da salati da ƙarfi jikinsa ya saki alamar rai ya yi halinsa.
Malam Horo ya ce "Allahamdulilah bacci ya ɗauke shi kar a tashe shi sai ya farka da kan shi, idan ba haka ba za'a samu matsala"
"A'a Malam Horo idan Allah Ya so babu me tashin shi. Mun gode miyyeti masin" sallama ya yi musu ya fita, Moddibo kuma ya fito daga bukkar Mado ya saki assabari ba tare daya san gawa ya rufe ba.
*
Tunda ya shigo gidan yake surfa masifa kala-kala. Girgiza kai kawai ta yi kafin ta ce "Yanzu shi ya ce maka aurenta zai yi ko me? Me yake dashi da zai ɗakko wa kan shi maganar aure? Ji nake a can Lagos ɗin ba wani aikin kirki yake ba Masinja ne shi a bankin" Ya ka da baki wajan faɗin "Ai na ga take takensa, ko yana da halin yin ban lamunce masa auren ƴar mashayin mutumin nan ba, mara kunya fitinannen mutum. Haka jiya akan idanuna ya shige da wata shiryayyiya. Ba zan iya haɗa iri dashi ba" ita dai abin da take yi ya cigaba da yi.
Dai-dai nan ya sako kan shi cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, gogaggen yadi ne a jikinsa daya sake fito da kwarjininsa, sai ƙamshi yake fitarwa dawowarsa kenan daga Interview ya shiga ya yi wanka. Baba ya ce "ka shigo a dai-dai"
Kallon mahaifin nasa ya yi ba tare da ya ce komai ba. "Yaushe zaka koma can Lagos ɗin?" Haysaam ya kalli Baba sai ya yi shiru
"Magana nake ka tsare ni da ido?"
"Sai na haɗa kuɗin mota in sha Allah" Baba ya dube shi ya ce
"Nawa ne zuwa Lagos ɗin?"
A ɗan taƙaice ya ce "Ya danganta"
"To Allah Ya taimaka ya yi muku albarka. Bance kar ka taimaki yarinyar ba, amma rai na baya mini daɗi ganinka da ita, yanzu ɗan mutum ake kiwo ba dabba ba, ka lura" Yaa Sam ya yi kamar bai fahimta ba da kamala a tattare dashi ya ce "Wacece?"
"Ladidi yama sunan yarinyar?"
Caraf Walid ya ce "Ana sunanta Baba" Yaa Sam ya juya ya kalli Walid sai yaron ya yi saurin yin ƙasa da kai. "Ka kawo mini abinci shago" yana faɗin hakan ya fice zuciyarsa babu daɗi. Shagon nasa da yake jikin ɗakinsu ya nufa, yana jin baba yana faɗin shi sam bai ga amfanin karatun Haysaam ba, an ƙare karatu babu aiki, ganin takaddar ƙosai yafi faranta masa akan takardun Sam.
Kwanciya ya yi a katifar ɗakin ya lumshe idanunsa ya rufe fuskarsa da hula yana jin Walid ya shigo shagon ya ajjiye masa abinci. Yaron ya dinga kallon ledar dake ajjiye kamar ya ɗakko sai ya fasa. Yana ta kwance tunani ya yi masa yawa a zuciya ya ji alamar an buɗe ƙofar an shigo, bai motsa ba kuma bai buɗe idanunsa ba, har ta ƙarasu gefen wajan ta durƙusa kanta a ƙasa yana jiran ya ji ta yi masa magana amma shiru. A hankali ya cire hular ya buɗe gargasar idanunsa tare da kallon inda take daf dashi, tun kafin ya yi magana ta rushe masa kuka, ya san yadda take ƙoƙarin danne rauninta bata bari aga gazawarta kukanta sai ya riƙe ta shi
"Nanah.......
Ta kasa amsawa sai ta kifa kanta a cinyarsa ta sakar masa wani irin kuka me raunata zuciya, yaja idanunsa ya lumshe su yana jin zuciyarsa na buɗewa. Bai sake magana ba sai ɗora hannunsa da ya yi a saman kanta.
Ganin kukan zai iya haddasa mata ciwo a hankali ya ce "Enough, daina kukan hakan" "Yaa Sam...,"
"Shhhh" ya katse ta wajan ɗora yatsarsa a bakinta ya zaunar da ita kusa dashi ya janyo kwanon abincin ya buɗe, banɗashen gurasa ne ya ji mai da ƙuli an yayyanka masa ita. "Muga hannunki?" Ta nuna masa bai gamsu da tafin hannun ba ya tanƙwashe ƙafarsa tare da saka kwanon a tsakiya ya shiga ɗakko gurasar yana bata a baki shima yana ci, idan ya bata sai ya saka a nasa bakin. Ya sake ɗakko ya miƙa mata har ta saka a bakinta ta turo ta faɗo hannunsa ta ce masa
"I'm full" ya ɗan kalle ta anutse.
"Kuma kika fara sata a bakinki?"
Ta ɗauke kai "To ba sai ka cinye ba kar a yi asarar abincin" ya kalli gurasar duk yawon bakinta kamar ba zai magana ba sai kuma
Ya ce "Abin baka zan ci jaririyar Innti?"
"Yap. Ai ni na ci fa"
"And.......?"
Ya ɗora da "I mean who are you to me?"
"Uhm mmm ba budurwa ba, ba mata ba, hmm ƙawarka ce ni, I'm your friend" girgiza kai kawai ya yi yarinyar da a haihuwar awaki ya yi jika da ita maybe. "Miƙo mini ledar can" tana juya ya cillar gurasar a bakinsa ya cinye tas. Ledar ta ɗakko Apple ne guda ɗaya a ciki sai Yougurt da Biscuits biyu.
"Ina gurasar bani abata na cinye" bai kalle ta ba ya miƙa mata Yougurt ɗin bayan ta kafa baki tasha ya miƙa mata hannunsa ta ce "ba siya mini ka yi duka ba Yaa Sam?" Bai tanka ta ba ta dire masa Yougurt ɗin tana ajjiye ya miƙa mata Apple ɗin daya ciro a bakinsa sai ɓata rai take yi bai bi ta kanta ba, ya ɗauki Yougurt ɗin ya sha ya sake miƙa mata, karɓa karɓa suka dinga yi har ta ce ta ƙoshi ya rufe ya ajjiye. "Oya tashi ki koma gida kar Abbaa ya neme ki" ta yi shiru
"Nanah.....
"Ina ganin Abbaa a cikin mafarkina ta wata siga sai ya dinga ce mini shi mijina ne. Innti bata gida Mahaɗita ma haka" ya yi jim. "Ina Iftihal ɗin ta je ta bar ki?" Kwanciya ta yi a gefe tana hamma "Mijin Innti ne ya sakata a caca, wai zai ci miliyan ashirin shine Alhaji Baita ya ci cacar aka bashi Mahaɗita, Innti ta ce koda wasa na je gidan xan haɗu da fushinta, kuma kar na faɗa maka" ta ɗan yatsuna fuska tana jujjuya kai ya saka hannunsa ya riƙe kan, zafi sosai ya ji ita kuma ta zuba masa ido har bata san lokacin data ɗora kanta a cinyarsa dake miƙe ba. "Abin dai sai ita da mijin nata, i told Iftihal Daada shi zai zama ajalinta but she refused to understand that" tana faɗin hakan ta rufe idanunta ruf babu jimawa ya ji saukar numfashinta alamar bacci ya ɗauke ta. Ya dinga kallon fuskarta ta torchlight ɗin daya kunna ya ja numfashi ya sauke ya ji ta mirgina a hankali ta shige can ƙurwar ɗakin tana riƙe hannunsa sosai a cikin nata, ya wanzu yana kallon ta sosai, yana sake tuna ƙuruciyarta da ta yi akan idanunsa ya ɗan ranƙwafa goshinsa ya sauka akan nata a hankali ya mayar da idanunsa kan laɓɓanta....