Waheedah

Chapter four

by @deejarthabdoul12

A hankali Waheedah ta fito daga ɗakin tana jin kalaman Dada suna sake raunana mata zuciya. Duk da haka ta haɗiye komai ta nufi aikin da ke gabanta. 

Saboda idan zagi da cin mutuncin Dada ne yanzu yaci ace ta saba, tarin kwanukan da aka tara tun daren jiya ta durƙusa ta fara wankewa cikin sanyin safiyar da har yanzu ke ratsata.

 Wata matashiyar yarinyace wacce daga gani ta girmi Waheeda sosai ta fito daga dakin Dada tana mika tare da hamma bakin nan duk yawun baccin dage nuna alaman ko sallahn Asuba bata yi ba.

Wani shegen kallo take bin Waheeda dashi da bama tasan tanayi ba dan ko dago kanta batayi ba duk da taji an tsaya a kanta saboda ta riga da tasan waye ne.

Kafa matashiyar me suna Waseela tasa ta ture ta tana rige kugu cikin masifa tace ke dan uban ki ni kike jira na gaishe ki ne ko zaki ce baki ganni bane shegiya me halin uwarta.

Dago kai Waheeda tayi tana kallon ta da idanun ta da sukayi ja sosai a hankali tace kiyi hakuri Yaya Waseela.

"An tashi lpia.

Daban tashi lpia ba ai baza ki ganni ba munafuka kawai Waseela tace tana jan tsaki tabi gefenta ta wuce.

Girgiza kai Waheeda tayi ta cigaba da aikinta harta gama wanke kwanukan ta kaisu cikin dan karamin madafin su.Tana fitowa daga madafin dai dai lokacin Baba kuma yake fitowa daga dakin sa yana gyara rikon fartanyan sa. 

Waheedah na ganin sa wani kyakkyawan murmushi ya wanzu a fuskan ta da sauri ta karasa inda yake tsaye ta tsunguna a gaban sa cikin muryan ta me sanyi tace.

"Baba Ina kwana"

Lpia qlau, Waheeda kin tashi lpia Baba ya fada shima da murmushi akan fuskansa.

"Alhamdulillah "

Dan kallon ta Baba yayi na wasu dakiku duk yadda take kokarin kirkiran murmushi a fuskanta amma yana iya hango rashin walwala a idon ta ga kuma hijabin dake jinta da har yanzu yake dan dauke da alamun ruwan da Dada ta watsa mata.

Me ya same ki? Ya tambaya duk da yasan dama koda yaushe cikin damuwa take amma hakan bashi zai hana shi tambayan taba.
Da sauri ta girgiza kai.

"Ba komai Baba"

Kafin Baba ya sake magana Dada ta fito daga dakin ta.
To me zai same ta kuwa Malam ta fada tana gyara daurin zanin ta daya ke kokarin suncewa wllh na lura kai kake daurewa yarinyar nan gindi take abun ta take so a gidan nan saboda tsabagen ka raina ni har jiya yarinyar nan zata min laifi nace mata ta fitamin daga gida amma ka sake dawo min da ita ko to wallahi mu zuba nida ku a gidan nan shege ka fasa Dada ta karasa fada tana nufan hanyan madafi.

Ajiyan zuciya Baba ya sauke yana girgiza kai sanna yace

"Allah ya kyauta"

Yana nufan hanyan fita daga gidan shima yabar Waheeda a tsaye tana mejin yadda zuciyan ta take zafi akan kalaman Dada.

#Waheedah
***