HIYAAM

Chapter 14

by @nimcyluv

Kasa motsi Innti ta yi saboda wani abu daya tsaya mata a ƙirji, ya daki zuciyarta ta kasa ko jan numfashi saboda tashin hankalin ganin yadda Daada ya cila Iftihal a cikin rijiya. Numfashinta ya shiga kakkatsewa jikinta ya ɗauki rawa idanunta rufe ta fasa wata iriyar ƙarar data farkar da Ana daga bacci ɓarawo daya ɗauke ta. Da ƙyar ta buɗe idanunta, ta miƙa hannunta zata taɓo Iftihal saboda numfashinta data daina ji yana sauka a fuskarta, wayam babu Iftihal.

Ta juya domin ganin ina ta Iftihal take, sai taga ashe a tsakar gida bacci ya ɗauke ta, bayan ta samu ta yi bacci, ita kuma Innti ta kira ta, kiran daya saka bata koma ɗakin ba. "Mahaɗita....

Ta kira sunanta da muryarta me sanyi, sai ta yunƙura ta miƙe tsaye, ita da fari ihun Innti a mafarki ta ji shi, sai ta ɗauka ko Anum ce? Tana ƙoƙarin shiga ɗakin Innti ta sake sakin wani ihun tana faɗin "Ka cilla mini yarinya a rijiya Daada, shikenan ka kashe mini Iftihal"

Dam! Ƙirjin Ana ya buga da matsanancin ƙarfi, sai Idanunta ya fara dishi-dishi tun kafin ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji, da wani irin sauri ta juya taga Innti a tsakar gidan wajan bakin rijiyarsu. Ta juya ta kalli Daada da ya yi baya yana sake tangaɗi ya ce "Au duk gargaɗin da na yi mata bata jiba shine ta dawo mini gida? Ni zata jawa jarfar Alhaji Baita? To ga sakamakonta nan" Ya yi shaƙuwa yana fashewa da dariya.

"Innti ai tunda kika haifi yara ba za ki taɓa jin daɗi a wajena ba, tun a cikin Muraad na faɗa miki ki tsayar da haihuwa kikai burus dani, kullum sai dai ki dinga haihuwa kamar akuya? Bani da ra'ayi ƴaƴa bani da burinsu"

Innti bata da lokacin tsayawa ta ji surutan Daada sai ta juya da sauri zuwa ɗakin yaran

"Yaya, Jaheed ku fito.....

"Muraad kana ina?"

Jikinta duk rawa yake yi.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ce tana dafe ƙirjinta tana jin kamar zuciyarta ce zata faso ƙirjinta saboda nauyin da ta yi a ƙirjinta da kuma yadda take buga mata tare da yi mata motsi tana fitar da wani irin numfashi.

"Innti....,

Ta kasa maganar tana ƙanƙame jikinta da tsoran yin tambayar da tsoran abin da za ta ji. Idanunta kamar za su faɗo saboda wani irin girma da suka yi suka zazzago Ana ta ce "Ina mahaɗita? Ina take? Akwai abubuwan da take faɗa mini wanda bata kammala ba ta yi bacci, Innti ki nuna mini mahaɗita tana ina?" Innti ta kasa amsa Ana, sai kurma ihun sunan Babban yaya take yi da Jaheed. A firgice Jaheed ya fito sanye da Jallabiya, ya bar Jadid a cikin ɗaki. Jaheed ya kalli Innti.

Ya ce "Innti lafiya? Wani abu ne ya faru?" Ya ce a tsorace

"Ya cilla Iftihal a cikin rijiya...

"Ya saka mini yarinya a rijiya"

Ta fusgo Jaheed zuwa gabanta ta ce "Jaheed na shiga uku, na shiga uku, na kashe ƴata da hannuna na rasa Iftihal, na rasa yarinya me haƙuri da biyayya" ta matse kafaɗunsa ta ce "Ina Yaya? Ina Muraad yake Jaheed" He can't believe it, ya ji me Innti ta ce tabbas, ya kuma san bata ƙarya, ya rasa dalilin da hujja na rashin yadda cewa Daada ya cilla masoyiya a rijiya, Iftihal ɗinsa? Abokiyar wasan shi. Ya yi cak ya kasa motsi, ya ƙurawa Innti idanunsa da sukai wani irin juyawa a karo na farko. Ganin shima kamar ya rasa kan shi ya saka Innti matse kafaɗunsa ta ce "Jaheed ina Yaya? Iftihal a rijiya, kar na rasa Ayshatuna"

"Babban yaya baya ɗaki"

"Innalillahi!" Tana dafe kanta.

Jaheed ya nufi rijiyar ta yi saurin riƙe shi tana girgiza kai. "Kar ka shiga Yaa Jaheed, ba zaka iya ba, rijiyar akwai zurfi, kar na rasa ku gabaɗaya" ta furta tana haɗiyar zuciya. Jaheed ya ce "Innti jinkirin zai saka wani abu ya faru, sai yaushe za mu jira?"

"Mu jira hukuncin ubangiji"

Ana tunda ta ƙurawa rijiyar idanu bata ko ƙiftawa, ko numfashi ta gagara ja da saukewa. Da wani irin yanayin tashin hankali idanunta rufe ta nufi rijiyar tana ambaton sunan Iftihal, ganin Ana na shirin faɗawa rijiyar ya saka Innti riƙota ta matse ta a jikinta. "Wallahi mutuwa zan yi idan na rasa mahaɗita, ki bari na shiga zan ceto ta, na miki alƙawarin babu abin da zai same ni, ki yarda dani Innti. Zan iya kamar yadda Abbaa zai iya" wani surutai take babu kan gado a ciki, idanunta rufe jikinta ya ɗauki rawa. Innti ta girgiza kai tana sake riƙe ta.

"Yaya ina ka shiga? Kana ina Muraad" Innti ta ce da nauyin zuciya, duk irin kukan da Innti take yi babu maƙocin daya shigo, hatta Yaa Sam da yake kodayaushe idanu biyu Allah bai nufe shi da jin abin da yake faruwa a gidansu Ana ɗin ba, Salati kawai Innti ke yi ta ƙanƙame Ana ta shiga kokawa da ita ganin yarinyar na shirin ƙwacewa, daga cikin ɗakima jikin Yaa Jadid ya rikice.

***

TAJMAHAR PALACE.

Masarautar ta yi shiru sai kukan tsuntsaye da sauran nau'in dabbobin da suke ciki, girma da faɗin masarautar ya kai a yi kwantance da masarautar Tajmahar a cikin jerin masarautun da suka africa, ba lokacin bayi bane, amma har yanzu Tajmahar suna bautar da jama'a kamar sune suka halicce su, yawanci kuma sun fi ɗora tsananin dokar tasu ne akan mata, suna siyan bayi mata daka ko'ina, musamman suke ranar kasuwar bayi a naɗa shugaban bayi ya je ya siye duk matan da aka kawo kasuwar, a cikin farashi me tsananin tsada.

Akaf cikin Tajmahar, babban part guda shine ya zama daban, komai na part ɗin daban, tsarin fari da ash ne, sai ya zama very different da sauran kuma yafi ɗaukan idanu saboda tsarin shi

Yana zaune akan kushin ya ɗan tanƙwashe ƙafafuwansa, daga shi sai three qauter, duk da farin fatar jikinsa da yadda take ɗauke idanu, wani sahihin fari na burge wa, bai hana gargasa kwanciya a saman cinyarsa ba, ta lulluɓe fatar sai sheƙi take yi baƙa suɗik da ita. Babu riga a jikinsa, A hankali ya miƙa hannunsa idanunsa rufe ya ƙaro gudun acn, bai san me saka shi dawowa Tajmahar a dai-dai irin wannan lokacin ba, da alama kafin ya fita sai ran kowa ya ɓaci daga ciki kuma har dana Mai girma Deborah. Yaja numfashi ta cikin bakinsa ya cika bakin da iska ya fesar a hankali.

Wannan karon ma yana ji ana sake knocking ƙofar da za'a shigo haɗaɗɗan ƙaramin parlourn nasa da yake hutawa ya yi burus.

Wayarsa ce ta shiga haske, saboda baya son ringtones a silent take kodayaushe kuma a DnD. Number Tor Tiv ya gani da ya yi saved da "World" kiran ya katse a karo na farko. Aka sake kira, ya miƙa hannunsa kaɗan ya shafi screen ɗin wayar ya saka a hands free, dakakkiyar muryar Tor Tiv me cike da iko da izza ta ratsa cikin kunnensa. "Idan ba ka yi haka ba, ai ba zan kalle ka matsayin jinin Tajmahar ba, jinin Imande, zuciyar Imande, ƙaunar Uji"

A hankali ya sake sauke ajjiyar zuciya saboda muryar abin da yafi ƙauna a zuciyarsa ta ratsa cikin wannan zuciyar dai.

"Our next Tor Tiv, Me Tajmahar gabaɗaya"

"World.....

Ya ce a kasalance.

"No agreement, my prince"

Tor Tiv kuma Uji ya yi saurin tare shi da faɗar hakan, babu hayaniya cikin muryar shugaba, a nutse take cikin zallar iko da isa da kuma izza na jinin mulkin Tajmahar dake gudana a jinin jikinsa yana kwaranya a zuciyarsa. Bai sake cewa komai ya yi shiru.

"Me ya samu Madaki yake hargagi a sashin Mai girma Deborah?"

Madaki ya ji tambayar da aka yi masa, wato har an kai maganar zuwa fada gaban Shugaban Tajmahar? To shi duka duka, da Tor Tiv ɗin, da kingmakers, ciyamomin fadar, da dattawan cikinta akwai me zummar tarar shi ne ya masa wannan birkitacciyar tambayar bai ɗaure mutum ya saka shi a kurkuku ba, shi kan shi Tor Tiv yana da zummar tambayarsa ne kawai ta cikin wayar ba fuska da fuska ba. Yi masa wannan shirman tambayar daidai yake da sabon tashin hankali a Tajmahar. Sai ya ɗan yatsuna zagayayyiyar fuskarsa me ɗauke da kwantaccen saje me laushi da kyawun gani.

"Ina son barin Tajmahar"

Shine abin da ya fita daga cikin bakin Madaki kamar baya son yin maganar, ya saka hannu ya tura gashin gaban goshinsa zuwa baya. Tor Tiv ya yi shiru, don baya jin zai sake bawa Madaki damar barin Tajmahar masifun da suke bibiyarsu kaɗai sun isa.

"Za ka iya banda yanzu"

"World amma....," bai ƙarasa faɗa ba, Tor Tiv ya kashe kiran gabaɗaya da ita kanta wayar.

Wani abu ya caki zuciyar Madaki, tsigar jikinsa ta shiga tashi tana mimmiƙewa da zubewa a farar fatar jikinsa, ya tsani hakan baya son hakan, wannan shi ne ƙarshen raini kashe waya mutum waya a fuska. Ajjiye wayar ya yi, ya miƙe tsaye yana saka kyakkyawan takalmi a cikin farar ƙafarsa, fuskarsa kamar zai ce ya shiga uku haka ya nufi ƙofar fita daga cikin sashin nasa, yana fitowa ƙofar farko gabaɗaya sojojin da suke gadin ƙofar suka yi saurin zubewa akan ƙafafuwansu, kan su a ƙasa, ko numfashi da suna da iko da kan su ba za su iya jan shi ba, da sassarfa yake tafiya, saboda kuzarin da ya yi wa jikinsa yawa, ba'a ganin fuskarsa sosai saboda gashin daya kwanto masa, a jinin jikinsa yake jin Tajmahar, amma deep down akwai abin da yafi Tajmahar muhimmaci a zuciyarsa a yanzu, ji yake kamar ana kiransa ana jan zuciyarsa zuwa wani waje daban, wani waje me muhimmaci.

Fada ta jima da tashi, don haka kai tsaye sashin Shugaba Tor Tiv Madaki ya nufa, daga shi sai gajeren wandon da yake jikinsa buɗaɗɗan jikinsa na motsawa, sojojin ko inuwar Madaki basa kuskuran gani balle shi da kan shi Madaki, ya fito a suffar da ba kowa ke ganinsa da ita ba, kamar yadda ba kowa ne ya san ya shigo cikin Tajmahar ɗin ba. Madaki yana middle of the age ne, amma arziƙi da gata haɗi da gidan sarauta, da sangartar da aka nuna masa, sun buɗe masa jiki sosai ya zama fiye da age ɗin nasa. Yana zuwa ƙofar da aka rubuta TOR TIV da manyan haruffa yaja ya tsaya.

Wani soja ne ya kira Tor Tiv ya ce "Shugaba, ga gudan jinin Tajmahar a ƙofar Tor Tiv da kan shi" ta cikin wayar da wata kasalalliyar murya Tor Tiv ya ja numfashi

"Kar a bar shi ya shigo"

Yana faɗin hakan ya ƙare da wani sauti na fitar hayyaci. Duk yadda ka kai da jin kan ka muddin Tor Tiv bai baka damar shigowa sashin ba, dole ne ka haƙura ko waye kai. Madaki ya juya zuwa can gefe, jikinsa ya ɗan fara ɗaukan rawa. Kamar ance ya ɗago kai sai yaga matar daya taɓa gani an fito da ita daga sashin Tor Tiv jikinta ɗaure da sarƙa, ya ware kasalallun idanunsa ya cigaba da kallon yadda ake janta kusan duk kayan jikinta a yayyage yake. Can wani waje da ake ajjiye dabbobi suka cillata sojojin kana suka juya. Ya ɗan taɓe jajayen laɓɓansa yana zura na ƙasa a cikin bakinsa ya tsotsa, kamar zai shige sai ya nufi wajan, da wannan karsashin nasa. Yana zuwa ya yatsuna fuska wajan ya yi datti da yawa, duk da ko tsinke babu. Yana shiga ya ganta ya rakuɓe tana cirar ciyawa tana ci kamar mahaukaciya, ya zuba mata maganaɗisun idanunsa kafin ya saka yatsu biyu ya murza

A gigice ta ɗago kai, cike da tsoran ko wajan Tor Tiv za'a sake mayar da ita, ta shiga girgiza wa Madaki kai tana ja baya kamar ma tsoran mutane take yi. Ya durƙusa inda take ya dinga kallon yadda fatar jikinta take duk shatin duka, faratanta ma duk an cire su. "Ka tafi, ka tafi ka bar nan ba zan koma ba" a tsorace take maganar tana girgiza kai da wani firgice ta ce

"Kar ka mayar dani....

"Bana so, ba zani ba"

Ya buɗe idanunsa, a karo na farko daya taɓa tsayawa da wata baiwa a cikin Tajmahar har ta ji muryarsa, murya a shaƙe da slow ya ce

"Wacece ke?"

Da sauri itama ta ce

"Wacece ke?"

"Ina nufin sunanki?"

Itama ta ce

"Ina nufin sunanki?"

"Huh!" Ya fesar da iska me zafi. Ya jima yana binta da kallo kafin ya taɓe bakinsa ya miƙe ya bar wajan. Yana barin wajan kuma aka fara kuke-kuke, yana ji bai bi ta kai bai ba, bashi da wani ra'ayi sosai akan Tajmahar ɗin. Gashi kuma shine namiji guda ɗaya wanda ya zama magajinta.

Kukan da ake yi ya saka shi miƙewa daga saman lafiyayyen gadon da yake kwance, mata guda uku suna yi masa tausa, ya sakko ƙafarsa, ɗaya ta miƙo masa rigar bacci ya saka, ɗaya ta shiga rufe masa botiran rigar, da wata sabuwar izza ya shiga takawa wajan bakin ƙofarsa ya fita zuwa wani part ɗin duk a ɓangare guda.

Yana shiga yaja ya tsaya ya kalli wacce ke shimfiɗe a ƙasa kafin ya yi magana ace

"She's died, ta mutu mun rasa ta itama"

Ɗaya yarinyar ta girgiza kai ta dawo kusa dashi ta riƙe shi ta ce "Yaushe Uwa Mamaa zata bayyana? Bana son na mutu kamar yadda Zizi ta rasu, yaushe Mama zata zo?"

Yaja idanunsa ya rufe.

"Terhemba, kana gani dai kana ji komai dake faruwa?"

A hankali ya ce "Mun ta ganin masifa kenan har sai Uwa Mamaa me ɗauke da Tsav ta bayyana a Tajmahar, Mama yaushe za ki zo?"

***

"Abbaaa.....

Ana ta daddage ta kurma ihun kiran sunan Abbaa, bisa mamakin Innti sai Babban yaya ya fito daga cikin ɗakinsu, yana tafiya a hankali idanunsa zube akan Ana wacce ya ji kiran da take masa yana fusgarsa, a nutse ya mayar da ganinsa kan Innti yana juya ido. Kafin ma ya yi tambaya Yaa Jaheed yace

"Daada ya cilla Iftihal a cikin rijiya" wani zaro ido Yaya ya yi waje yana yin baya kamar zai koma ɗaki a guje ya taho ya faɗa cikin rijiyar, daidai lokacin Yaa Sam ya shigo shima cikin shigar bacci, idanunsa bai gama buɗewa ba, ya kalle du ɗaya bayan ya ce "Jaheed meke faruwa ne? Ko jikin Jadid ne?"

Jaheed ya kasa magana sai rawar jiki yake yi. "Ai hukuncin bijirewa umarnina da ta yi kenan, tana fitowa kuma zata goma gidan Alhaji Baita. Idan ta yi rai a cikin rijiyar kenan" nan take Yaa Sam ya fahimci abin da yake faruwa, ya saurin leƙa rijiyar baya ganin komai saboda duhu amma yana jin motsin ruwa. Ya runtse idanunsa ya shiga addu'ar Allah Ya sa Iftihal ta fito lafiya, ya san kusancin dake tsakanin zuciyoyi biyu idan Ana ta rasa Iftihal akwai matsala, idan Iftihal ta rasa Ana nan ma wata sabuwar matsala ce. Ana na jikin Innti, da alama tsoron kallon rijiyar ma suke yi, Jaheed da Yaa Sam suna wajan rijiyar suna leƙawa, Daada kuma na tsaye sai surutan iska yake.

Yaa Sam na ƙoƙarin cilla igiya a cikin rijiyar sai ga Babban yaya ya fito, goye da Iftihal yana fitowa ya saka hannunsa wajan kunce rigar jikinsa wacce ya yaga ya yi amfani da ita wajan goya Iftihal, da hannu ya yi alamar a bashi tabarma, Jaheed ne ya ɗakko ya shimfiɗa, shi kuma ya kwantar da Iftihal akai, kallo ɗaya ya yi wa Iftihal ya ɗauke kai ya miƙe ya ce yana zuwa kar wanda ya taɓa ta, cikin ɗakinsu ya shiga, Ana kasa biyayya ta yi wa maganar Abbaa ta yi saurin nufar Iftihal ta zauna tare da janyota jikinta ta rungumeta sosai tana sauke wata wahalliyar ajjiyar zuciya. Sanda Yaya ya shiga ɗakinsu ya mance da Jadid ya zube akan ƙafafuwansa, gabaɗaya jijiyoyin dake kwance a goshinsa suka firfito, ya zaro harshensa ya haɗe da haƙoran sama dana ƙasa ya datse su da ƙarfin gaske har sai da ya ji ɗanɗanon jini a bakinsa, gabaɗaya jikinsa rawa da ɓari yake yi, baki yake son ya buɗe ya saki kuka sai ya yi saurin ɗora hannunsa a bakin yana girgiza kai dukkan wata jijiya da Ubangiji yake halitta a jikin mutum sai data jikin Yaya ta bayyana, idanunsa ya zama kamar ba nasa ba, ya yi wani irin ja kamar gaushin wuta, ya kasa zubar da hawaye. Jadid ya ji sautin tashin hankalin da Babban yaya ya shiga, amma ba zai iya motsa ko hannunsa ba shima ɗin.

Ana ta sake rungume Iftihal tana sauke ajjiyar zuciya, tana jin wani abu mai kama da relief yana sauka a jikinta sannu a hankali. A hankali ta shiga faɗin "Mahaɗita"

"Sannu Mahaɗita, in sha Allah kin bar gidan mutumin nan, idan ya zama dole zani ni"

"Kema babu inda za ki, babu wanda ya isa ya sake saka mini ƴa a caca ko waye shi"

Cewar Innti tana riƙe hannun Iftihal gam a cikin nata

Yaa Sam ya yi wa Iftihal ƙuri da idanu zuciyarsa na bugawa.

"Sahibarmu tashi Mahaɗita mu koma ɗaki"

Daada dake gefe ya ce "Ba dai ɗaki ba, wannan yarinyar sai ta bar gidan nan yanzu" wani irin ƙasƙantaccen kallo Innti ta yi wa Daada, bata ma da lokacin yi masa raddi. Ta juya kan Iftihal ta ce

"Indo,Aysha"

Sai taga bata motsa ba.

Yaa Jaheed ya ce "Ki danna mata ƙirjinta ko ta sha ruwa a cikin rijiyar ina tunanin haka"

Kamar yadda ya ce ɗin, ta saka hannu biyu ta danna ƙirjin Iftihal ta yi har sau uku amma babu ruwan daya zuba daga cikin bakinta ko hancinta. Ƙirjin Innti ya buga ta zubawa fuskar Iftihal idanu, sai taga ta yi mata kyawun da bata taɓa gani ba, fuskarta wasai alamar babu wani tashin hankalin da yake cin zuciyarta, alamar babu wani ciwo ko raɗaɗin da yake damun gangar jikinta. Wani haske fuskar yarinyar ke yi, me ɗauke da annuri. Ta kira sunan Allah a zuciyarta.

"Iftihal ɗita, Ayshatuna, Indota...

"Sannu Iftin Innti, sannu da jiki" ta ce tana sake riƙota sosai

Ana ta ce "Ta farka ne? Ya ba ta yi motsi ba?"

Sai ta ɗaga hannun Iftihal tana ɗagawa ya koma inda yake sharaf. "Ta karye a hannu" ta sake faɗin

"Hannunta ya karye" da sabon tashin hankali ta faɗi hakan jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta. A gigice take girgiza Iftihal tana kiran sunanta. Yaa Sam ya jima da fahimtar abin da yake faruwa, zuciyarsa ta fara rawa na tsananin tausayin Ana ya juya wajan saka hannu yana share hawayen da suka cika masa idanu. Jaheed ko ƙafa ma ya kasa ɗagawa yaja ya cake yana kallon Iftihal kamar zai kira ta amsa masa. Innti ce ta kira Ana tare da faɗin "A'a, bacci take yi kar ki tashe ta kuma ki batta"

"Bacci take yi?" Ana ta maimaita sai ta lumshe idanunta da faɗin "To nima zan yi bacci a kusa da ita, Innti nima bacci zan"

Babban yaya ne ya fito ya shiga takawa a hankali, fuskarsa babu walwala kamar ya ce ya shiga uku, wayar daya mance da ita a cikin alijuhunsa ita ce take ta haske, alamar shigowar kira Allah Ya sa a silent take, kuma irin wayar nan ce da ruwa baya kassara su. Bai bi ta kan wayar ba, ya janyo wani zani dake saman igiya, yana zuwa ya durƙusa dai-dai in da Iftihal take kwance a cinyar Ana, ya miƙa hannu zai ɗauke ta. Ana ta girgiza kai ta ce "Ka barta a jikina Abbaa"

Bai kalli ko fuskar Ana ba, balle idanunta ya sake miƙa hannu zai ɗauki Iftihal da ƙarfi

Ta ce "Abbaa.....

"Ina jin kamar zuciyata ce kake janye wa, bar ta a jikina don Allah Abbaa bar mini ita"

Sannu a hankali ya janye hannunsa ya zubawa waje guda idanu, da sauri kuma ya miƙa hannunsa ya zare Iftihal daga wani irin riƙo da Ana ɗin ta yi mata, ganin tana shirin bin Iftihal ya saka Yaa Sam ya yi saurin riƙe ta suka shiga kokawa zata ƙwace. Yaya ya kwantar da Iftihal saman tabarma, ya shiga yin addu'a a hannunsa ya tofa a tafin hannunsa ya shafi idanun Iftihal zuwa fuskarta, ya yi ƙasa da kan shi ya sumbaci goshinta, ya riƙe hannunta sosai kamar kar ya cika alamar ban kwana, ya jima cikin wannan yanayin, ya sake sumbatar goshinta daidai nan hawayen daya cika idanunsa ya sakko a saman fuskarta, a hankali ya ja zanin ya lulluɓe ta gabaɗaya.

"To me ya sa kake rufe ta haka Yaya?" Jaheed ya ce yana girgiza kai domin shima bai fahimci abin da yake faruwa ba.

Ana ta ce "Ya ce bacci take yi, Innti ma ta ce bacci take yi, nima zan kwanta ka rufe ni Abbaa" ta sake yunƙurin ƙwacewa daga hannun Yaa Sam. Miƙewa Innti ta yi ta matsa kusa da Babban yaya ta ce

"Meke faruwa?"

"Allah Ya yi mata rahama....,

Sai Babban yaya ya kasa ƙarasawa ya miƙe gently yana ɗan ja baya ya nufi inda Yaa Sam yake a hankali ta wata laushin murya me cike da kasala, kwarjini da haiba ya ce

"Allah Ya ji ƙan Ayshatul-Iftihal"

Dam! Ƙirjin Innti ya buga da ƙarfi ta ce

"Ta rasu ne Muraad? Na rasa Iftihal?"

Ya jinjina mata kai a hankali.

Cak Ana ta tsaya daga kokawar ƙwace kanta da take yi, ta ƙurawa gawar Iftihal idanu, bata ko blinking eyes ɗinta, ta san mutuwa tabbas, ta san yadda mutane suke faɗar raɗaɗin mutuwa, kuma ta san idan an mutu ba'a taɓa dawowa, mutuwa ɗaya ce, tafarkinta yana da yawan gaske, ita dai wannan mutuwar me raba uwa da ɗanta tun yana ciki, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar jariri a cikin jini, wannan mutuwar mai ɗauke miji ta bar mata da ƴaƴa, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar yaranta cikin maraici da kewa ta mahaifiya, ita ce me raba soyayya da iyakance jin dadi lokaci guda, ita ce me saka mikin da baya taɓa gogewa sai ya yin da naka lokacin ya yi, ita dai-dai wannan mutuwar me raba masoya, me raba mutum da arziƙinsa na duniya. Irin wannan mutuwar Mahaɗinta ta yi? To a cikin rijiyar ta rasu a cikin ruwa data kasa shaƙar numfashi? Ko kuma wani abu ne ya daki kanta a lokacin da Daada ya cilla ta rijiyar? Ita wanne irin bacci ne me nauyi ya ɗauke ta wanda bata taɓa yin irinsa ba har ya cilla mata rayuwarta a cikin rijiya? Ina Abbaa yake a lokacin, Innti me take a lokacin?

Ta yi wata iriyar shaƙuwa ta zubawa ƙawar Iftihal, ita sam bata yadda gawa bace ba.

That's meana Daada ya kashe mata mahaɗinta kenan? Ya raba su? Ita tana duniya ita kuma zata tafi lahira? Me ya sa Iftihal za ta yi mata haka? Duk soyayyar da take yi mata? Da ƙaunar da take nuna mata? Ta ɗauka ita da kanta mutuwa za ta yi mata halacci da alkunya wajan ɗauke idanunta daga kan danginta more especially Mahaɗinta? Ta ina zata fara rayuwa without her? Without Iftihal, itama mutuwa za ta yi.

Da ƙyar ta juya kanta ta zubawa Daada idanu, gabaɗaya ƙwayar idanunta ta jirkice ta shiga bin da Daada da kallon da ita kanta bata san dalili ba. Sai ta yi murmushi ta ce

"Yaa Sam"

"Uhm" kawai ya iya cewa.

Tana ta murmushi ta ce "Ka cikani ganinta kawai zan yi na tabbatar ta rasu ɗin ka ji?"

Yaa Sam yaƙi sakinta, Abbaa ne ya miƙo mata hannunsa, ganin hakan ya saka Yaa Sam sakinta kamar wacce ƙwai ya fashewa a haka take takawa, tsoron ganin abin da zuciyarta ta kasa ɗauka shine ya hanata yin sauri. Tana zuwa ta durƙusa a gaban gawar Iftihal ta miƙa hannunta wajan yaye fuskarta, ta zuba mata idanunta na wani lokaci. Ta juya ta kalli Babban yaya ta ce "I told Iftihal ai, sai Daada ya zama ajalinta, sai ya rabata da duniya, sai takaicin Daada da mugun halinsa ya kai ta zuwa lahira. Now..," sai ta yi murmushi tana shafo fuskar Iftihal da hannunta. "Abbaa..." Ta kira sunan Babban yaya ya matsa ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ta ce "Mijin Innti ya kashe mini wacce muka fito ciki ɗaya da ita, muka zauna a mahaifa ɗaya ita, muka fito duniya a rana ɗaya, Mijin Innti ya rabani da ƴar'uwata, ƙawata, aminiyyata, abokiyar faɗa da wasana. Abbaa ya zan yi?"

Ta sake shafo fuskar Iftihal ta ce "Ina so na mutu nima Abbaa ina son na bi mahaɗita, ina son na je inda Anum da Jarumi suke, ina son na je inda Iftihal zata tafi yanzu Abbaa"

Innti ji ta yi surutan Ana suna dukan tsakiyar kanta, kamar ana mata shocking a cikin ƙwaƙwalwarta haka take ji, kanta ya yi mata nauyi ta saka hannu ta dafe ƙirjinta.

As a mother, ya kamata ta ji baƙinciki, ta kuma zubar da hawaye na rashin Iftihal, madadin hakan wani abu me nauyi da girma da ciwo ta ji ya tsaya mata a ƙirjinta ya danne mata zuciya. Ana ta girgiza kai

"Abbaa kar ka binne mini Mahaɗita, ni ina son ganinta haka nan, zan zauna da ita"

Shifa ko motsi yaya kamar an yi masa dolen yi ni ne, da ƙyar ya iya matsawa kusa da Ana sosai ya ɗora bakinsa a kunnenta yana dafa kanta ya ce "Shetty" a hankali ta ce

"Abbaa"

"Pray for her" ya ce silently.

"To Abbaa" ta kalli Iftihal sai ta ce

"To me zan ce? Mece addu'ar? Ya ake yi?"

Yaa Sam ya ce "Anything, ki yi mata"

Bata kalli Yaa Sam ba idanunta akan fuskar Abbaa gabaɗaya ya ɗora goshinsa a saman nata ya riƙe kanta.

"Ni ban iya ba"

Da ƙarfi kuma ta ce "Allah Ya ji ƙan ki Mahaɗita, Allah Ya yi miki gafara, Ubangiji Ya saka miki tun a nan duniya, Ubangiji Ya duba kawaici da haƙurinki, yadda kika so mijin Innti ina addu'ar Ubangiji Ya hana shi sukuni da soyayyarki bayan bakya duniya" a hankali ta miƙe tsaye tana murmushi Babban yaya ya miƙe ta yi saurin riƙe hannunsa ta ce "Abbaa ina jin tsoro sosai"

Gam ya riƙe hannunta sai ta fara gani dishi-dishi ta miƙa hannunta ta shafo fuskar Babban yaya da take ganinta a wata suffa ta daban a hankali ta ce "Waye kai? Ina Abbaa?" Ta runtse idanunta, Babban yaya da yake riƙe da ita ya shafi fuskarsa sai ya ji suffar da baya so a san da ita, ita ce ta bayyana a idanun Ana. Ana ƙoƙarin sake buɗe idanu take ta kalli mutumin amma ta kasa. "Abbaa kana ina, bana gani, nima mutuwa zan yi zan bi mahaɗita Abbaa" faɗawa jikin Babban yaya ta yi dai-dai lokacin da numfashinta yake tsayawa a ƙirji, tana faɗowa jikinsa ya haɗe hannunsa biyu ya rungumeta ya ɗora fuskarsa a wuyanta domin baya son kowa yaga yanayinsa.

Da wata kamilalliyar murya ya ce

"I'm sorry Mamaaa...

Daidai nan Jaheed ya yake jiki shima ya faɗi babu numfashi zuciyarsa ta kasa ɗaukan mutuwar masoyiyarsa.

***

BIYA.

Taron jama'a ne masu ɗauke da jajayen kaya sama da mutane ashirin a ƙarƙashin bishiya cikin tsakiyar daren, layi bayan layi ake binsu da jini ana basu umarnin sha, ko da aka zo kanta ta zubawa jinin idanu ta yi kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta amsa ta shanye, suna gama sha suka hau kan wata dabba kamar jirgi ta tashi dasu zuwa sama. A firgice ta farka daga madadin da take yi, lokacin ana ta kiran sallar Asuba ne.

Hindatu ta yi shiru tana zabga uban tagumi da tuna mafarkin, wannan shine karo na uku tana mafarki, na farko ta yi mafarki an bata ɗanyen nama kyauta aka ce ta ci, kuma ta cinye, na biyu ta yi mafarki tana ɗaure rago da akuya. Yau kuma mafarkin shan jini ta yi. Abin duniya ya addabi Hindatu ta rasa wa zata faɗawa, da Gana kawai suke kirki a unguwar. Har gari ya yi haske tana zaune.

"Hinde, yau an ɗauke miki sallah ne?"

Da raunin murya ta ce "A'a malam"

"Sai ki fito kar mukutarinta ya shige ko?" Ta miƙe tana saka hijabi ta fito, wani ihu ta kurma sanda ta yi arba da kayan cikin Malam a sarari, da jinin da yake gudana a jikinsa. Ta dafe ƙirji tare da rarraba idanu.

Malam ya ce "Lafiya kike wannan ihun?"

Hindatu ta kasa magana kamar zata zauce ganin yadda kayan cikin Malam ke ta motsi, a guje ta juya zuwa ɗaki tana rufe idanunta.

***

BAFFAS ESTATE.

9:00 na safe.

Baffas estate ya yi shiru baka jin motsin komai da kowa, tun bayan dawowar Sayyadi Baffa, tun daga kan ma'aikatan gidan zuwa jami'an tsaro, da jama'ar gidan kowa cikin taka tsantsan yake yi, sun jaddada komai na abin da zai iya zamewar su matsala a gidan.

Hidaya ce ta kalli Diynaah wacce take sakawa Nadiyaah maganin ciwon idanu ta ce "Mamy ta ce an saka ranar auren Ukhty Azizah da Baffa, wai za'ayi musu aure tare"

Cak Diyanaah ta tsaya daga abin da take yi, Nadiyaah ma Idanunta da ya yi jaa ta watsa akan Hidaya kafin ta ce "Waya ya tsara haka?" Hidaya ta ce "Mamy tace Abba Malami ne, wai dole Baffa ya yi aure wai kuma ya auri Azizah"

"Ya Rabbi!" Cewar Diyanaah.

Nadiyaah ta yi ƙasa da kanta hawaye ya cika idanunta jikinta ya shiga rawa ta kalli Diyanaah ta ce "Baffaa am zai yi aure?"

"Shikenan Baffa zai yi aure mu dinga jin kunya a cikin abokanmu a dinga cewa Baffa ya yi aure? Kuma sai a haifa mana ɗan ƙani?" Diyanaah itama fashewa ta yi da kuka sosai suka haɗu waje guda suka dinga kuka, nan da nan jikin Nadiyaah ya ɗauki wani irin zafin zazzaɓi daman kwana biyu ba lafiya ce da ita ba, da sauri Diynaah ta ɗauki wayarta ta nemo number Baffa data saka masa Baffa am. Ta dinga kira baya ɗauka a kira na uku ta ji ya ɗauka ya yi shiru na ce wani lokaci. "Baffa am" ta kira sunansa da soyayya me ƙarfi dake huda zuciyarta ta ce

"Nadiyaah babu lafiya Baffa..," Ƙit ya kashe wayar bai bari ta ƙarasa faɗa ba. Ta kwantar da Nadiyaah. Ta ce "Ukhty ki narke sosai, ki ce wa Baffa bakya son auren za ki mutu muddin ya ce zai yi aure kin ji"

Diyanaah ta fi Nadiyaah wayo sosai, kamar yadda Diyanaah ta ɗakko sunan mahafiyarta, haka Nadiyaah ta ɗakko sanyin halin mahafiyarta, kamar yaran ɗaya sak. Tun kafin ya shigo suka ji alamar zuwan nasa ta ƙamshin da yake sanar dasu, jin hakan ya saka Nadiyaah rufe idanunta, ta ƙofar daya saka aka yi tsakanin shashinsa dana yaran nasa ya shigo, kyakkywar farar Jallabiya ce a jikinsa, fara sol da ita babu zanen komai a jikinta, sai wani sassanyan ƙamshi na musamman daya cika ɗakin tun sako ƙafarsa da ya yi zuwa ciki, jerarrun yatsun ƙafarsa Diynaah ta fara sauke idanunta akai, taja numfashi ta sauke, zata buɗe murya a ko'ina ta nuna wannan bawan Allan ta ce shi ne mahafinta farincikinta, irin uban da ake taƙama dashi da kuma tutiya. Asalin fatar Baffa ba zaka iya tantance ta turawa ce ko Larabawa ba, jin Nadiyaah babu lafiya ya saka ko rawanin da yake sakawa a kan shi bai samu dama ba, kan shi babu komai ya shigo cikin bedroom ɗin bayan ya samu izinin shigowa daga bakin Diyanaah.

Sumar ƙan shi baƙa ce sosai, a cuccure take ta yi gado gado ta murmuɗe ta saka har ƙasan wuyansa, wata tayo gaban goshinsa, akwai ratsin jaa a sumar gaban goshinta.

Baffa a tsaye yake sosai a saman ƙafafuwansa, cike da kuzari, izza, mazantaka taƙama da ilimin addinin da yake dashi, uwa uba kwarjini, haiba da salon nasa ra'ayin, har wani yellow yellow fuskarta take yi tsabar haske kyau wajan Sayyadi Baffa ba'a magana, duk kyan da yaransa suke dashi ko kwatan nasa basu ɗauka ba. Ya yi tsaye hannunsa ɗaya riƙe da ƙaramin carbi, ɗaya hannunsa yana zagaye a bayansa ya zubawa Nadiyaah idanunsa.

"Barka da shigowa Yaa Baffa"

Cewar Diyanaah tana yin ƙasa da kanta.

Ya juya launin ƙwayar idanunsa a kanta da wata kalar nutsuwa da yanayin da yake nuna magana kai tsaye yake mata da "Kar ki sake ɗora photo a Social media Diyanaah Sayyadi Baffa" cikin sauri ta ce "In sha Allah Baffa"

A jikinsa ya ji zai wahala ciwon idanun Nadiyaah idan ba Kambun baka bane. Ya ƙarasa ya zaune kusa da ita, jikinta zafi sosai don haka ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata. Nadiyaah ta girgiza kai ta ce "Baffa am, don Allah Baffa kar ka yi aure, idan ka yi aure zan iya mutuwa, za'ayi mana dariya ace mahafinmu ya yi aure, kuma har a yi mana ƙani" jin abin da ta ce ya saka su waro idanu sai kuma yaja idanuna ya lumshe, kishin mahaifiyarsu suke yi wacce bata raye ma.

Diyanaah ta ce "E, Baffa. We're 17 years fa, ai tun muna ƙanana za ka yi aure ba yanzu ba, kuma duk wacce ka aura zata rabamu da kai. Muna son ka Baffa don kar ka yi aure"

Ta zame zuwa ƙasa cikin sauri ma Nadiyaah ta sakko suka jeru a gaban Sayyadi Baffa.

Da wani irin kuka me narkar da zuciyarsa suka ce "Kuma muma idan mukai aure, matarka tana haihuwa mu muna yi? Ka tausaya mana Baffa,bama som ka auri kowa" Diyanaah ta ce "Ukhty ba kin ce ana aure a aljanna ba, kinga sai Baffa ya yi aure da Ammie a can aljanna ko? Please Baffa"

Kuka suke yi sosai, gani suke babban tozarci ne ace mahafinsu ya yi aure a age ɗinsa, Shugaban Hisba da kan shi, shi da yake gujewa mu'amala da mata baya saka so a tsarin rayuwarsa, duk wata mace Garzali ce a idanunsa. Ya dubi yadda suke kukan kamar za su rasa rai. Ya miƙe a nutse ya riƙo hannayensu, a hankali ya sumbaci kumatun kowacce kafin ya juya ya bar ɗakin nasu. Sanda ya fito direct babban parlornsa ya nufa saboda tun jiya yake ganin shigowar saƙon Mu'allim, sai ya bashi izinin zuwa, yana shiga yaga Mu'allim tare da Liman zaune, jin zuwan Sayyadi Baffa ya saka su miƙewa tsaye kan su a ƙasa? "Barka da zuwa" Suka ce a tare, ba tare daya kalle su ba ya nemi waje ya zauna. Shiru shiru babu wanda ya yi magana, a hankali ya ɗaga kai ya kalle su, ya juya ya kalli Liman a nutse

Gaban Mu'allim sai faɗuwa yake yi, ya ɗan zunguro Liman

"Liman Please, ka faɗa masa"

Liman ya kalli Mu'allim sai bai ce komai ba.

Baffa ya harɗe ƙafa idan ya kalli wannan sai ya kalli wannan. A nutse ya miƙe zai fice. Mu'allim ya ce

"Na samu matar aure ne Baffa, a unguwar Kankarofi, sunanta Aysha......," ya ɗauke labarin komai har abin da Babban yaya ya ce ya faɗawa Baffa ya ɗora da "Baffa Please, ko dan ciro yarinyar daga faɗawa wani hali ka amince na aure ta, wallahi ina son ta da gaske. Amma idan ka ce a'a shikenan"

Baffa ya yi shiru bai ce komai.

Liman ya ce "Ka taimaka Baffa"

Ya juya ya kalli Liman, juyawa ya yi sai da ya je bakin ƙofa ya yi musu yanayin da yake nufin "Ka shirya mota ina fitowa yanzu" wata ajjiyar zuciya Al'ameen ya sauke cikin sauri ya rungume Liman yana faɗin "Finally.... Allahamdulillah!"

"Congratulations"

"Thank you Akhy Asad Hafiz Hafiz Baffa Jazakalla bil khair"

Cikin ƙaramin lokaci Malami ya zo da sauran ƴan'uwa. Liman ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda domin har dashi za'a je ɗaurin auren na Mu'allim. Sanda ya fito Hajiya Umaimah ta ce "Zai wahala idan matar Asad ƴar arziƙi ce, kina ganin Baffa yaƙi zuwa neman auren Liman gashi zai je na Mu'allim. Kuma ka tabbata ka biya ta gidansu yarinyar ka kawo mini ita, tunda wancan zuwan bana nan tazo" shi dai bai ce komai ba ya fice. Malami ya shigo yana faɗin. "To yanzu ya ce baikon ma an warware baya son auren, when he's ready zai yi magana, bai duba cewa Azizah ƙanwar Hajiya Umaimah bace ba, kalli abin da ya yi" Hajiya Umaimah ta ce

"Malami me nake ji kana faɗa ne haka?"

Yana gyara babbar rigarsa ya ce "Baffa ya fasa auren Azizah an warware baikon"

Kafin ta yi magana Al'ameen ya shigo cikin farar shadda me ɗauke da babbar riga da hula kana ganinsa kaga ango ya ce "Baffa ya fito, baya jira kun san dai ko?" Yana faɗin hakan ya fice. Asad ma ya yi waje abinsa.

Wata baƙar mota Baffa ya shiga me duhun glasses shi ɗaya a Baya sai Al'ameen matsayin driver, Malami da sauran suka shiga motar Asad ya shiga yaja. Suka nufi Kankarofi.

Sanda suka isa suka tarar da unguwar a cike da jama'a, Al'ameen ya sake jin daɗi wato ma an san da zuwan nasu gashi an yi taron ɗaurin aure. Liman ya fito yana ɗan duba lokaci domin yau suna da taron ƙarshen shekara na ƴan jarida. "Ina ne gidan"?

Al'ameen ya ce "Gashi.....," bai ƙarasa faɗa ba yaga an fito da makara Babban yaya ne a gaba shi da Yaa Sam suna riƙe da Gawar Iftihal.