Chapter one
by @aysharano22
🤍SIRRIN ZUCIYA🤍
By Aysha Rano✨
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Book 1.
01
LAGOS, NIGERIA.
Cikin wani wawakeken bedroom mai ɗauke da duk wasu abubuwa na more rayuwa na hango wata budurwa zaune kan vanity chair tana shafa powder a face dinta. Tana gamawa ta ɗakko eye pencil tayi lining idonta da shi, sannan tayi wearing nude lipstick a bakinta.
Daga nan kuma ta ɗauki wig dake ajiye kan vanity table ta shiga ƙoƙarin ɗorashi akan ƙananun kitson dake kanta. Sai da ta tabbata wig ɗin ya zauna sosai sannan ta ɗauki comb ta shiga gyara gashin tana sake kwantar da shi. Nan take kuwa ya sake bin kan nata ya kwanta yayi wani luf-luf har shinning yake yi yana ɗaukan ido, sai ka rantse gashinta ne kamar ba ɗorashi tayi ba.
Bayan ta gama ta mike daga zaunen da take tana sake duban kanta cikin mirror. Aikam har wani haɗaɗɗen murmushi ta saki saboda ganin wannan shahararren kyau da tayi. Doguwar riga ce a jikinta har ƙasa light purple, amma fa tun daga wajen cinyarta na hagu har ƙasan rigar a tsage yake. Hakan yasa ko yaya tayi motsi sai cinyarta ta fito waje.
Gashi rigar ta matseta sosai kasancewar body hug ce. Babu abin da bai fito ba a jikinta. Duk da ba wani ƙiba ne da ita ba, tana da dirarren jiki daidai misali kuma dududu a shekaru bata fi irin 21 ba zuwa 22. Sannan a kallon farko da kayi mata zaka gane Christian ce ba musulma ba, and ba bahaushiya ba, domin ko da take da choc skin ko kusa batayi kala da hausawa ba. Cikakkiyar bayerabiya ce.
Juyi ta shiga yi gaban mirrorn yadda zata gano bayanta da kyau. Sai da ta tabbata komai nata is set sannan ta fesa perfumes a jikinta da sauri ta nufi inda ring light dinta ke ajiye ta shiga ƙoƙarin makala wayarta a jiki, don so take tayi video da safen nan tayi posting ma fans dinta kamar yadda tayi musu alƙawari zata sanar da su winners na giveaway da tayi this morning before ta wuce school.
Ba ta da tsayi sosai, haka zalika bazata shiga sahun gajeru ba, amma fa kyakyawa ce sosai ta bugawa a jarida. Tana da wani irin golden brown complexion da kai tsaye bazaka ce mata baƙa ba sannan kuma ba fara bace. Wani irin mixed chocolate skin gareta da kana ganinta zaka san har da hutu ma cikin abubuwan da suke sake fiddo da kyan skin ɗin nata. Wannan dalilin yasa da yawan ’yan makarantarsu ke kiranta da Butter tsabar kalar ’yan gayun da take da shi.
Tana da small nose da kuma small mouth. In short, komai na face dinta ƙarami ne har da idanunta, amma kuma a kallon farko ake iya ganin kyawunta duk da kasancewar kananun kyau gareta. Irinsu ne mutanen da zaka ga gaɗai kyau nan suna da shi kamar su suka yi kansu, kuma idan ka ƙare musu kallo ma sai ka rasa daga ina kyawun yake, musamman da yake ba dogon hanci ko manyan idanuwa garesu ba. Amma tsayawa faɗar irin kyawun da suke da shi ɗin ma bata baki ne.
Tana gama makala wayar ta shiga TikTok dinta tayi setting camera yana fara reading. Ta gyara zama tare da ɗora wani kyakyawan murmushi a fuskanta before ta fara da cewa:
“Hello guys, it’s your girl Suhana aka Butter aka the Gen Z baddie. How are you all doing? I hope you are enjoying your day. So, this video is to inform you about the winners of the giveaway I did last week and the names of the winners are Michael P, The Real Odogwu and Miss Mary.
So, if you are among the winners all you need to do is slide into my DM, send your account details and I’ll send you your 100k instantly.
Lastly, I want to thank all of you that took part in the giveaway. Thank you so much guys and do not forget to keep following because trust me, I’m going to do more giveaways and who knows, you might just be among the lucky ones if you keep pushing.
I wish you all the best of luck and yes, you know I love you guys right? Yeah, I love you a lot. Make sure you don’t forget that. Bye and enjoy the rest of your day. Muahh.”
Ta ƙarasa maganar tare da blowing kisses wa cameran nata sannan tayi ending videon. Sai da ta fara duba videon ta tabbata it’s good sannan tayi posting nashi a page dinta. Yana gama zuwa tayi saving tare da exiting TikTok ta tafi Instagram dinta. Nan ma tayi posting ɗinshi.
Tana ƙoƙarin kashe data wata dattijuwar mata da zata iya kai 50 ta shigo cikin ɗakin. Turus tayi a bakin ƙofa tana kallon yarinyar data kira kanta da Suhana saboda ganin ba ma shirin tafiya school take ba, zama tayi tana magana da fans dinta.
Suhana na daga ido taga yadda taja ta tsaya bakin ƙofa. Ba ta san lokacin data saki murmushi tana miƙewa daga zaunen da take ba. Cikin hausar da ka ji dama zaka san ba wai ta iya hausan bane tace:
“Na gama fa Nanny.”
Karasowa cikin ɗakin nanny tayi tana harararta tace:
“So you are still here checking your social media instead of you to get ready for school.”
Karasawa kusa da nannyn tayi ta kamo hannunta tana cewa:
“Come on nannyy, I’m an influencer. I can’t do without social media.”
Buɗe baki nanny tayi zata sake magana, tayi saurin ɗora hannu akan bakin nata tana wani langwaɓe mata wuya tace:
“Don’t say anything plss. Besides, nayi gama shiri school. Let’s go have breakfast.”
Dariya nanny ta saki saboda jin yadda tayi hausan tace mata:
“It’s na gama shirin school, not nayi gama shiri school.”
’Dan tura baki tayi tana cewa:
“To ai ke ce nace kina min zance da hausa ba kya so.”
Har sannan dariya nanny ke yi mata tace:
“Don Allah Suhana ki bar yin hausan nan tunda ba iyawa kikayi ba.”
Sake kwaɓe bakin tayi before tace:
“No… I want to learn.”
Murmushi nanny ke yi tana gyada kanta tace:
“To na ji, amma dai yanzu kiyi sauri ki ƙarasa shiryawa, zan je inyi setting table.”
Har ta juya zata tafi, Suhana tayi saurin riƙo hannunta ta shiga juyi a gabanta har wani fari take yi da ido tace:
“Baki faɗa min how I look ba.”
Kama cheeks dinta nanny tayi tana ci gaba da murmushi tace mata:
“You look as stunning as always my sweet baby girl.”
Wani farrr ta sake yi da ido tana wani lankwasa murya tace:
“I’ll take my flowers nanny… thanks for the compliment.”
Murmushi sosai nanny ke yi tana dubanta. Da gani ba ƙaramin so take yi mata ba tace:
“I’m sure your mom would be so proud if she were to see you like this.”
Tun bata ƙarasa magana ba, Suhana ta wani ɗinke fuska tsaf kamar ba ita ce ke murmushi gami da fari da ido ba yanzu nan saboda an ce tayi kyau. Lokaci ɗaya ta dawo a totally different person.
Juyawa tayi fuska a haɗe ta ɗauki ring light dinta ta maidashi inda yake sannan ta nufi bag hanger dinta ta shiga ƙoƙarin ciro jakar da zatayi amfani da ita.
Da kallo kawai nanny ke binta, ganin ta fara displaying waɗannan attitudes da bata taɓa gajiya da displaying ɗinsu ba duk ta sako maganar mahaifiyarta.
“Suhana…”
Ta kira sunanta a hankali. Maimakon ta amsa sai cewa tayi:
“Nanny please I don’t want to talk about her this morning, I don’t want to spoil my mood plsss.”
Kai kawai nanny ta iya gyadawa before tace:
“Ok… hurry up and come out for breakfast.”
Kai ta gyada mata tare da cewa:
“Ok.”
Daga haka nanny na fita daga ɗakin, yayin da ita kuma Suhana ta saki wani tsaki can ƙasan maƙoshi tana furta:
“I’ll never consider that woman as my mother ever… she’s not worth it.”
Ta ƙarasa maganar tana sake daddaure fuska kamar ba ita ke dariya ba ɗazu.
Bag dinta kaɗai ta ɗauka haɗe da wallet. Ta sa wani high heel takalmi da yayi matching da bag ɗin sannan ta fita riƙe da car key dinta, don duk su handouts da sauran kayan karatunta cikin mota take barinsu.
Ko breakfast ɗin bata samu tayi ba don ta kusa makara. Don haka nanny tayi mata packaging ta kai mata har cikin mota tace ta tafi da shi idan yaso sai taci a school ɗin tare da ƙawayenta.
Ba tayi mata musu ba ta amsa, don ta san yadda two besties dinta Esther da Lilian ke bala’in son abincin nanny. A cewarsu ita ɗin ba ƙaramin iya girki tayi ba. And yes, ita kanta ta san nanny is a great cook ’cause she has been a mother figure to her tun tana ’yar yarinya.
Saboda nisa dake tsakanin gidansu da makaranta ga kuma Lagos hold up ɗaya makaleta, ta kusa one hour a cikinsa. Ba ita ta isa UniLag ba sai da tayi missing first lecture.
Tana gama parking a parking lot, ko kashe motar bata yi ba wayarta dake ajiye kan cinyanta ta fara ringing. Duba wayar tayi sai taga “My Daddy ❤️” akan screen.
Nan take ta daure fuska ƙwarai ta shiga ƙoƙarin kwaso handouts dinta dake backseat. Ko kallon wayar bata sake yi ba balle tayi picking.
Kiran na katsewa wani ya sake shigowa. Har zata sake ignoring sai kuma taga bazata iya ba, kuma ta san shi ma bazai taɓa dena kira ba in har ba dagawa tayi suka yi magana ba.
Tsuke fuska tayi tamau tamkar yana ganinta kafin tayi picking call ɗin gami da kara wayar a kunnenta tace:
“Hello.”
Daga ɗaya ɓangaren daddyn nata yace:
“Moremi, why are you not picking my calls?”
Sake tsuke baki tayi before tace:
“Saboda ina class.”
Shiru taji yayi for some seconds kafin can yace:
“Ha’ah, this one you are talking like you are angry with me. What did I do again?”
Da mamaki sosai take sauraronsa tace:
“Really dad?… Are you even asking me?”
Kwantar da murya yayi kamar ba shine ubanta ba yace:
“Na zata mun gama da maganar nan Moremi, or are we still on it?”
Yana rufe baki tace:
“Yes, we are still on it daddy. This thing you are doing is not cool at all. For goodness sake, I’m your only child amma bana taɓa samun time ɗinka. Ba ka sparing even the smallest time for me. You are always busy with your work, always out on your business trips.
It has always been like this tun ina yarinya. You hardly spend two weeks with me. Duk da ka san you are my only parent amma still ba ka taɓa bani lokacinka. This is super uncool dad, and I’m super unhappy.”
Shiru daddy yayi yana sauraron yadda ta rufe shi da masifa kamar ita ta haife shi ba shi ya haifeta ba, tunda dai ya san gaskiya take faɗa mishi.
Sai da ya bari ta gama tsaf sannan ya sake kwantar da murya yace mata:
“Na san kina da buƙatar kulawata Suhana, kuma na san kina da buƙatar lokacina fiye da na kowa a duniya, and trust me I want the same too. But ya kamata ki san ni ɗan kasuwa ne kuma akwai abubuwa da dama da suke buƙatar kulawata suma.
I can’t just be staying at home letting someone handle my business for me. It’s not going to work that way.
But I’m sorry for making you feel that way and this time zan yi ƙoƙari in dawo next week so we could celebrate your birthday together. How about that?”
Wara idanuwa tayi tana jin abin da yake faɗa kamar ba ta yadda da shi ba tace:
“I don’t believe you daddy. Last year ma haka ka ce and you didn’t come back.”
Tana rufe baki yace:
“Trust me, I’m not going to repeat that mistake ever again in my life. I would never miss your birthday for anything in the world.”
Wani irin excitement ne ya bayyana kan fuskanta all of a sudden kamar ba ita ke cin kunu ba, amma bata bari excitement ɗin ya fito fili ba. Ta sake cewa:
“Ni dai in dai ba ganka nayi ba, I’m not going to believe that.”
Tana rufe baki yace:
“So your nanny is still teaching you this language ko?”
Tana turo baki tace:
“I asked her to teach me.”
Gyada kai yayi kafin yace mata:
“Okay, so now tell me, how are you? And how’s school?”
Ajiyar zuciya ta sauke before saying:
“I’m fine daddy, but school is not fine. It’s even becoming more tiring than usual.”
Girgiza kai yake yi yana murmushi, sanin da yayi dama tun tana ’yar ƙarama ba son makaranta take ba gashi har girmanta.
A hankali yace mata:
“Eyyah sorry my love… ya social media ɗinki fa?”
Nan take sai ga wani murmushi ya bayyana akan fuskanta saboda an yi maganar abin da take so.
Cike da excitement tace:
“Dad, you can’t believe what I’m going to tell you right now. Dad, ka san na samu almost 5k additional followers for the giveaway I did last week?”
Wara ido shi ma yayi kamar tana ganinsa yace:
“Really Moremi?”
Bai jira amsarta ba ya ɗora da cewa:
“I saw your post this morning my darling, you look so pretty and I’m glad this social media thing is making you happy ‘cause I’m happy too.”
Murmushi ta saki don tana jin daɗin yadda yake supporting harkar influencing da take yi tace:
“Nagode daddy.”
Yace:
“You’re welcome. So yanzu 300k zaki ba wa giveaway winners ɗin ko?”
Tace:
“Yeah, 100k each.”
Yace:
“Okay then, zan tura miki k…”
Bai ƙarasa ba ta katse shi da cewa:
“Ba kuɗi nake buƙata ba daddy. I have more than enough in my account. I just want you to come home before my birthday plss.”
Ta ƙarasa maganar kamar zata sa mishi kuka.
Yace:
“Don’t worry my child, na faɗa miki I wouldn’t miss your birthday for anything in the world.”
Ta saki wani murmushi kafin tace:
“Thank you so much daddy, I love you.”
Yace:
“Love you too Moremi.”
Tace:
“Okay zan koma class daddy, it’s almost time for my second lecture.”
Yace:
“Alright baby, don’t forget to call me when you get back home.”
Tace:
“Sure I will dad… bye.”
Shi ma ya amsa mata da:
“Bye.”
Daga haka ta katse kiran sannan ta fita daga motar bayan ta kwashi duk abubuwan da ta san zatayi amfani da su ta haɗa da school bag dinta.
Tana rufe motar kai tsaye ta ɗauki hanyar class ɗinsu.
Ko kafin ta ƙarasa class ɗin sai gaisawa take yi da mutane. Kusan duk wanda ya ganta sai ya mata magana sun gaisa, don da yawa daga cikinsu sun santa a social media. Wasu ma har requesting picture suke yi da ita. Haka zata tsaya su yi sannan ta ci gaba da tafiya.
(Ina ruwan celebrity 🤣)
Koda ta isa class lecturer ɗinsu na ciki, don haka silently ta nufi inda ta hango two besties dinta ta zauna kusa da su.
Esther ce ta kasa haƙuri da abin da take son faɗa. Tayi ƙasa da murya tana ɗan kare baki da hannunta don kada lecturer ya gane tana surutu tace:
“Su, yanzu da gaske zaki bada 300k just like that?”
Satar kallonta Suhana tayi, ita ma tayi ƙasa da nata muryar tace:
“What do you mean just like that?”
Ɗago waya Esther tayi ta nuna mata videon da tayi posting a while ago tace:
“This.”
Suhana tace:
“Oh, it’s for the giveaway winners.”
Esther tace:
“Exactly my point. Kan me zaki bada whole 300k for just a giveaway?”
Juyawa Suhana tayi ta ɗan kalli Lilian before ta maida idonta kan lecturer ɗinsu kamar sauraron abin da yake take tace:
“Lilly can you hear this girl?”
Ita ma tayi ƙasa da nata muryar, idanuwanta akan board tace:
“Esther is right Su. I mean why not ki basu 50-50k, sai ki bamu sauran 150k ɗin?”
Girgiza kai Suhana ta shiga yi tana cewa:
“You girls are not serious. Alƙawarin 100k nayi and I’m not going to break that promise but, ina da good news for you two.”
Cike da zumuɗi Esther tace:
“Good news fa? Please tell us.”
Ita ma Lilly tace:
“Yeah, faɗa mana plss.”
A hankali tace:
“Well, the good news is… ina nan ina shirya mana tafiya zuwa South Africa the day after my birthday.”
Rano✨